Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamu wuce dake, amma saboda wasu ƴan dslilai muka bar tariyar taki sai satin sama idan ALLAH ya kaimu, aidaita haƙuri da rayuwa kinji, zan aiko Isa da saƙo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, tashi ki koma ciki, ALLAH yay miki albarka”.
Kai kawai ta iya kaɗa masa, kafin da ƙyar tace, “Amin Dady, na gode da karamcinka gareni, ALLAH ya ƙara girma da lafiya mai amfani, ya sakanka maka da mafificin alkairi”.
Karo na farko danaga yayi wani ɗan guntun murmushi wanda saika saka masa ido zaka fahimci yayisa, idonsa a kanta yace, “Tashi kije ciki, muma wucewa zamuyi yamma tayi”.
Nanma kanta ta ɗaga masa tamiƙe tana tangaɗi da ƙyar ta iya isa inda Inna harira ke jiranta.

Tunda Ummukulsoom ta koma ciki saita ƙunshe kanta a ɗaki tana cigaba da tunanin yanda rayuwa zata gudana a gidan Alhaji Mahmud, yanzu haka tana kula yanda Ameer yake jifanta da kallon ƙyama da tsana, ta rasa miyasa Alhaji Mahmud yagaza fahimtar wutsuyar raƙumi tai nesa da ƙasa tsakaninta da ɗansa, sannan baba yagaza fahimtar ita abinda take hangowa.
Har yamma tana ɗaki, sai ƴan biki dakan leƙo su gaisa irin ƙawayensu da sukai rayuwar yarinta, waɗanda mafi yawansu a yanzu idan ka gansu saika ɗauka yayun Ummukulsoom ne, wasuma tamkar sun girmeta sosai, su Azima kansu dake aure a birnin duksun wani tsofe mata a ido, dan Azima ma fama take da ƙaton ciki na huɗu yanzu haka.
Zuwa yamma su Murja suka saka waƙa a redio sunaji ana kwasar rawa da guɗa, tareda shewa da dariyar yaran mata.
Sune ma sukaje suka kinkimo Ummukulsoom daga ɗaki dole ta fito tsakar gidan dake cike da mata, saboda anan inna laraba ke karasunta matsayin Uwar ƴa tunda babu mahaifiyar Ummukulsoom a duniya.
Ga ƙatuwar tukunyar tuwo masara fari ƙal anata tuƙi, sai miyar taushe da kunun zaƙi da zoɓo, duk dai dangin mahaifiyar Ummu ne sukayi dan itama tayi farin ciki, karkuma tayi kukan rashin Uwa.
Cigam ɗin dasu Murja suka siyo itadasu Aziza sukazo kan Ummu suna zuba mata suna tiƙar rawa, wai cingam ɗin shine matsayin kuɗin liƙi.
Batare da Ummukulsoom ta shiryaba tasaki murmushi tana ture murja dake callara mata buɗa a kunne, yayinda Aziza da Nusaiba da Hadiza ke zuba mata cingam.
Manyan iyaye irinsu baba yalwa da gayyar ƴan biki suna kallonsu, wasu kuma na aikin abinci, yayinda wasu ke gulmarsu group-group, irinsu baba yalwa kuwa danne zukatansu kawai sukeyi, dan wani sashe na murna wani sashe na baƙin ciki.
Har dare kusan tara gidan anata kujiba-kujiba irinta biki, yayinda wasu ke kwasar ƙafafunsu suna wucewa gida ana barin ƴan uwa irinsu Murja da suka cigaba da cashiyarsu.
Itadai Ummu tunda tagudu ɗaki sallar magriba bata sake dawowa ba ma. Sai wajen tara da rabi yunwa ta isheta ta leƙo kozata hango Aziza, amma tagaza ganinta, danma garin ƙwanyar yake da hasken farin wata kasancewar yau daren sha biyar.
Ruwa ta ɗiba a buta tanufi bayi, tafitone ta hangi Murja can gefe tana wankema ɗanta Amadu kashi tana masifa saboda a wando yayi.
Ƙarasawa Ummu tayi taimata dundu a baya, Murja ta ɗago tana sosa wajen zatai masifa saitaga Ummukulsoom ce.
“Kai kai wlhy dama ance ƙashin amare ƙwarine dashi, amarya karki ƙarasani kijama mijina salalan tsiya”.
Ummu ta harareta tana ɗaukar Amadu daga gabanta ta ƙarasa ɗauraye masa jikin da butar hannunta, cikin dusashshiyar muryarta da kuka ya dishe tace, “Kindawo nan kinama yaro mugunta, ALLAH ya isarmu”.
“ALLAH Umma bazaki ganeba, tunfa ɗazun nace yaje ya hau fo amma yay kunnen uwar shegu dani, dan wulaƙanci da wayonsa yay kashi a wando, dashi zanji koda Sa'a?”.
Ummu data kammala masa ta ɗaukeshi a hannu tana faɗin, “ƙila to baiga fo ɗinba, kinacan kina tiƙa rawa zaki nutsu ki bashine, mizan samu a gidannan inci nasha magani, yunwa nakeji”.
“Tab aiko sai tuwo, kuma kinsan yagama hucewa, ba ɗazun naga Halima da kwanoba tace kezata kaima fura inji baba furera?”.
Ɗan yamutsa fuska Ummu tayi tana gyara tsayuwa, “Kinsan bancika damuwa da furaba Murja, kuma lokacin banajin yunwa, da Jummai tashigo itada kishiyarta naga ƴarta nata kallon kwanon shine nace ta zauna tasha”.
“A to lallai bakida mankai, to yanzu da furar haki ce kumafa? Ke bakisan shegan son banzar Jimmai ba ashe, itada bata wuce tayi duk gidan data shiga saboda shegen kwaɗayinta datayi sallama ake kife kwano da murfi”.
Karo na farko da Ummu tai dariya har haƙoranta suka bayyana tunda tadawo garin ɗilau, “Kai Murja ALLAH ya shiryaki, nidai samomin ko tuwon ne naci dan ALLAH”.
“A'a ba ayi hakaba amarya da cin tuwo, bara na mayi ango tunda baya kusa, ina zuwa naba Kamilu ya siyo miki shayi wajen idi na bakin yara”.
Duk kiran da Ummu take mata akan karta bada bata sauraretaba, ta karɓi Amadu daga wajenta dantaje ta saka masa kaya.
Ummukulsoom ma wuce yaran dake rawa tayi takoma ɗaki, bayan yunwa ma har wanka tanada bukatar yi kodan nauyi da jikinta yay mata, rabonta da wanka tunna safe bayan sun dawo a sibiti, da yamma ma dazata canja kaya daga alwalar la'asarne tashafa mai ta canja kayan.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Su Alhaji Mahmud sun iso kaduna gab da magriba, baima shiga gidaba ya tsaya masallaci, saida yay har sallar isha'i sannan ya ƙarasa ciki.
Duk ƴan uwan hajiya Jamila da sukazo sun wuce, daga ita sai ƴaƴanta yanzu a gidan harda Ummi babbar ƴarsu Aneesa, saikuma ƙannen Alhaji Mahmud su uku da sukazo daga Ajiwa, da wata tsohuwa gwaggonsu. Kasancewar ba sakewa suke a gidanba idan baya ciki duk suna ɗaki, saisu Aneesa dake a falo suna kallo da hajiya Jamila da ƙanwarta Mansura dake aure a kano, dama tun jiya tana gidan, ita keta kuma tunzurata akan ƙin auren na Amaan da Ummu.
Duk nutsuwa yaran sukai suna masa sannu da zuwa, fuskarnan tashi babu walwala kamar kullum ya amsa, Mansura ma ta gaidashi damasa ALLAH ya sanya alkairi.
Ganin babu danginsa a falon ransa ya sosu, harya kama kafar benen zai hau ya juyo yana kallon hajiya jamila da gabanta yafaɗi lokaci ɗaya saboda yanda taga idanunsa.
“Su su Faɗima suna ina? Naji banji motsinsu ba?”.
Cikin inda-inda hajiya jamila tace, “Sallar isha'i sukashiga yi, da duk muna zaune a falo muna hira”.
Yasan halinta sarai, kuma yanayinta yasashi sanin karya take, baice uffanba ya ida haurawa yabarta nan tsaye tana binsa da kallo. Saida taga ya ɓacema ganinta sannan ta juyo suka haɗa ido da Mansura suna wani ƙyaɓe baki.

Koda ta biyoshi harya cire kayansa zai shiga bayi wanka, ko kallonta baiyiba ya shige abinsa, dukda taji takaici haka ta zauna a bakin gado zaman jiransa.
Wayarsa data fara tsuwwa alamar kira ta kalla, ganin sunan *Fodio* ya sata ɗaukar wayar ta ɗaga kiran.
Daga can Jarumar muryarsa ta fidda sautin sallama tareda faɗin “Dad kun dawo gida lafiya?”.
Takaici yasaka hajiya jamila miƙewa tafita da wayar falo dan kar Alhaji Mahmud yaji mizata ce, a falonma saida taje can ƙarshe kafin tace, “Lallai Fodio, nadai lura kai bama ka kishin kanka akan aurennan ko?, ɗazun kuma na kiraka kaki amsamin waya saboda ka maidani ƙawarka”.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke daga can yana lumshe manyan idanunsa daya gada a wajenta, kafin yasa hannu ya dafe kansa, “Momcy Ina yini”.
“Lafiya lau” ta amsa a ƙufule.
dukda yaji yanda ta amsa saiya basar yace, “Dad fa?”.
Cikin gatse tace “Na dafashi na cinye, Fodio banason wulaƙancinka fa na basar da abu, namaka magana baka bani amsaba kana kawo wata tambaya daban”.
Muryarsa mai nuna tsantsar jarumtarsa daya gada ga Alhaji Mahmud da nutsuwa ya kuma sanyayawa, “Momcy banida abin faɗane shiyyasa”..
Haushi ya ƙara kama Hajiya jamila, tace, “Ni wlhy Fodio dama kurma ALLAH yayoka danafi jin daɗin haka, koba komai nasan kurma na haifa, dan iskanci mutum yamaka magana goma ka bashi amsar ɗaya”.
Rasa abinda zaice mata yayi, sai yace “Yi haƙuri to” abinda kawai yace kenan yay shiru, danshi mutumne bamai yawan magana ba, sunema yake ɗan daurewa yay magana mai tsawo dasu itada dad.
Jin kamar motsin fitowar Alhaji Mahmud yasata komawa ɗakin da sauri tana faɗin, “Yana wanka, amma gashinan fitowa”.
Fodio dake saurarenta daga can ya yanke wayar kawai yana sauke numfashi tareda gyara kwanciyarsa a doguwar kujera..
Alhaji Mahmud baibi takantaba yahau shiryawa cikin jallabiya doguwa.
Ganin hakan ne yasata cewa, “Fodio ya kira kana wanka, gakuma abinci yana jiranka”.
Batareda ya bata amsar farkoba yace, “Bazanci abinci ba, akwai fura da muka dawo da ita a ɗiba a dama min”.
“Fura kuma? Yanzu Abban Fodio duk irin munin ƙauyennan da Ameer ke faɗamin haka zaka iya shan furar da akayo daga can, inama laifin afita asiyo maka mai tsafta wajen Hamza”.
Wata banzar harara ya watsa mata, ya tsallakota ya fito abinsa.
Tamkar zata makesa tabiyo bayansa da sassarfa. A falo ta iskeshi yana ƙokarin kiran Fodio. Ganin yanda ya kuma kicin-kicin da fuska yasata ƙokarin ficewa ta cika Umarninsa.
“Ki turomin su Asiya”.
Wani takaicinne yakuma rufeta, ta amsa da kyar tana fita, gata a gidan amma dan wulaƙanci zaice ta turo masa ƙannensa. Shiyyasa bataso suzo gidan kwata-kwata.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Washe gari ma ancigaba da ƴar hidimar biki daba a rasaba, dukda babu ango babu danginsa, zuwa yamma kuma baba yace Ummu ta shirya gidan gwaggo Hinde kakarta zata koma da zama har zuwa rar tarewa. Tayi murna da hakan sosai, dan ta lura zaman gidansu babu abinda zai ƙara mata sai baƙin ciki da damuwar tunawa da basiru, dan habaici da gugar zana kawai ake zuba mata tun jiya akan fasa aurenta da yayi, tun tana hawaye akan ƙananun maganganun harma zuciyarta ta dake tabar jin kukan. Musamman ma dayake Aziza na kusa da ita a ko yaushe tana ɗebe mata kewa.
Da daddare tareda Aziza suka tafi gidan gwaggo Hinde, dama kayanta dukta tattara ankai can tunda yamma.
Wannan komawa gidan Gwaggo Hinde da Ummukulsoom tayi yajawo ƴar hayaniya tsakanin Baba da matansa, wai wani munafuncin yake shiryawa shiyyasa yace Ummu takoma gidan kakarta.
Banza yaymusu yaƙi kulasu, dan ya lura hassada ke cin ransu kawai, da akace an fasa auren Ummukulsoom da basiru ai cikin farin ciki suke, ko jiya da safe dasukaji zancen ɗaurin aurenta da wani basu damuba, saida sukaji labarin yawan motocin da sukazi ɗaurin aure da manyane mutane sannan hankalinsu ya tashi, dukda sunjin daɗin angon baizo ɗaurin aureba.
Shirun baba yakuma sasu takaici, saisuka zauna da ƴaƴansu su Nusaiba suna gulma. Zainaba ce dama kawai babu ruwanta, dan ita harga ALLAH tana ƙaunar Ummukulsoom matsayin ƴar uwarta Uba ɗaya.

★★★★★

Komawar Ummukulsoom gidan gwaggo yaɗan sake bata nutsuwa, yayinda gwaggo ta duƙufa gyarata da maganin sanyi, ko yaushe suna tare da Aziza dan suma basu komaba sai randa za'a tafi da Ummukulsoom.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Kwana biyar da ɗaurin auren Ummukulsoom sai ga Baseer ya danno ɗilau da dalleliyar motarsa fara sol.
Yawani ƙara ƙyau da ƙiba ɗan zaman dayay na kwana takwas a gidansu Suhailat.
Sai wani faɗi yake da fankama, yayinda yara suka zagaye motar suna kallo.
Baba yana zaune a ƙofar gida yana kallonsa, ya gaza cemasa uffan sai ido daya zuba masa ko ƙyaftawa bayayi.
Gabansa yazo ya durkusa yana gaidashi ido a ƙasa.
Baba ya amsa yana faɗin ”Kaiko Basiru ina kashige haka dan ALLAH?, kana ganin wannan rayuwar ta dace dakai? Kofa sallama bakai manaba kabi mutuminnan saboda yafimu yanzu a wajenka ko?”.
Ɗan juyawa Baseer yayi gudun kar wani yaji abinda baban nasa ke faɗa, ganin duk taron yarane saiya juyo yana kallon baba cikin ɓata fusaka yace, “Please baba kabari mushiga daga ciki zan maka bayani ai”.
Kaɗa kai kawai baba yayi yacigaba da rubutunsa da yakeyi a allo. Basir kuma yamiƙe yashiga cikin gida yana ƙunƙunin baba yaƙi ya waye, arziƙi na kiransu amma suna rintse ido.........?

NO. 10

Inna dake tsakar gida tana surfen ƴar masarar tuwonsu ta ɗago ta kalli basiru batareda ta amsa masa sallamarsaba, harya ƙaraso gareta bata iya janye idontaba, hannunta ɗaya da taɓarya ɗaya kuma tana ƙokarin janye kan akuya dake saka kai a turmin da take dakan, ƙarasowa yay yana girgizama Inna makullin motar hannunsa, fuskarsa washe da murmushi.
“Innata kuma fa ALLAH ya kaiku matsayin dawani mahaluki bai taɓa takawaba a garinnan”.
Ɗauke idonta tayi daga kallonsa tacigaba da dakanta tana faɗin, “Nagani kam, yaka baro su baban naka?”.
Duk da maganar tata ta doki zuciyarsa saboda fahimtar gatse tamasa amma saiya basar ya amsa da “inna suruki dai, iyayena kam ai kune, amma suna lafiya lau, sunce na gaidaku da ƙyau, wani satin zasuzo maganar auren”.
Inna tasaki murmushin takaici da jinjina maganar a ranta, gidan mazane ke zuwa neman aure, amma su yau ga sabon salo suna gani, gidan mace suna zuwa neman aure gidan namiji.
Bata sake bi takansaba tacigaba da dakanta, shima saiya miƙe yana mitar ƙurar ƙasa da turmin ke tayarwa zata ɓata masa jiki.
Ci kanka inna bataceba itadai.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Ummukulsoom batada labarin dawowar Basiru ɗilau sai a washe gari, shima Mariya ce datazo gidan take faɗa mata, dan itama tazama budurwa yanzu, sunema ƴammata masu tashe a ɗilau, dukda kuwa shekarunta 14 yanzunema suka shiga js3, amma Ummu tasan daganan ba gaba zasuyiba.
Sosai zancen dawowar basiru da dalleliyar mota ya tsayama Ummukulsoom a rai, ta ɓoye a bayi tasha kukanta dataje wanka, tasan fidda son Basiru aranta abune mai matuƙar wahala da fama, amma zatayi ƙoƙarin kamantawa koda da kokawane da yaƙin ƙwanji dana zuciya.
Tsaf gwaggo ta lura da halin da take a ciki saboda taji lokacin da mariya ke sanar mata, amma saitayi tamkar bata gantaba, dan tasan yimata maganar tamkar cigaba da fama mata gyambon dake zuciyartane.
Zama Ummukulsoom tayi ta rubuta doguwar wasiƙa ta ajiye, da nufin gobe kafin a wuce da ita zata bada akaima Basiru.

★★★★★

Shirye-shiryen miƙa Ummukulsoom kaduna yanata kankama, duk abinda yakamata anmatashi, ƴan gyararraki na jiki gwaggo hinde tamata iya iyawa, maganar kayan ɗaki dai Alhaji Mahmud yace su baba karsuyi komai, dan Ummu ma ba kaduna zata zaunaba, legas zatabi mijinta..

★★★★★★

Washe gari sukuku Ummu ta tashi tamkar mara laka a jiki, ita kaɗai tasan halin da take ciki, sai Aziza datasan halin mutanen gidan Alhaji Mahmud, dukda gaskiya itama bata taɓa ganin mijin Ummu ba.
Aranarma dai baba yazo har gidan gwaggo yasake ma Ummu nasiha shida sauran iyayeta ƙannen mamanta, daga nan yace Ummu ta shirya bayan sallar zuhur taje can gida tama su baba yalwa sallama.
Da to ta amsa masa tana sharar hawaye.
Gaba ɗaya sai Ummukulsoom ta daina fahimtar komai dake faruwa a gidan, hatta faɗan dasu gwaggo hinde sukai mata dasu inna laraba da babanta babu abinda ta fahimta, saima nanuƙema Gwaggo himde da tayi akan itafa sai da ita indai anason taje.
“Haba Ummukulsoom kiyi haƙuri mana, kinga yanzu an yanke da mutum biyar kawai za'aje, insha ALLAHU namiki alƙawarin idan ƙura ta lafa zanzo naga matsugunninki kinji”.
Ummu na kuka tace, “Nidai Gwaggo ban yardaba”.
“Karki yarda ɗin dan Ubanki, ke koma banzar halayyar matan ubanki bazaisa kiji ɗokin barmusu gidanba yau suci baƙin halinsu suda ƴaƴansu, ga cin fuska da basiru yay mana, amma ubangiji ya nuna masa shine gatanki, ni tashi muje ki canja kaya konayi kutufon lahadi bakwai dake”.
Jikin Ummu na ɓari tabar jikin Gwaggo tabi Umarnin Inna laraba, dan itace mai masifar.

Ƙarfe biyu dawasu mintuna Ummukulsoom da Aziza suka fito daga gidan gwaggo tana sharar ƙwalla, yayinda su inna laraba kebinsu a baya, dan bazata sake dawowa gidan gwaggo ba, daga can gidansu za'a wuce da ita kaduna.
Babu abinda zuciyarta keyi sai lugude da dukan goma-goma, saboda dole sai sunbi ta ƙofar gidansu Basiru, fatanta da addu'arta ALLAH yasa karta gansa.
Sai dai kuma addu'arta bata karɓuba, dan tana karyo kwana dashi tafara tozali, ta sauke manyan idanunta bisa ƙyaƙyƙyawar farar fuskarsa ta asalin jinin fulani, hakan yai dai-dai da ɗago tasa fuskar shima suka haɗa ido, daga ita harshi saida gabansu ya faɗin, Ummu ta sakar masa wani murmushin takaici daya zauna bisa ransa tamkar zane akan dutse. shine yay saurin janye nasa yana wani tamke fuska tamkar yaga mutuwa, danshi fa har yanzu babu wanda ya faɗa masa an ɗaura ma Ummu aure, to baya mu'amula da kowa a matasan garin, dan gani yake shi yafi ƙarfinsu, Inna da baba kam ma ko kallon arziƙi basa masa, daga amsa gaisuwarsa basa daɗawa basa ragawa, hakan kuma bai damesaba, a cewarsa idan sukaga kuɗi zasu sakkone.
Ummu kam ƙoƙarin haɗiye hawayenta takeyi da wani bahagon ƙududu daya tokare maƙoshinta, saida suka ɗan gotashine ta zaro takardar data rubuta a hijjab ɗinta tabama Aziza da nuna mata basiru da hannu tai gaba.
Fahimtar da Aziza tayi ne yasata amsa takoma baya tana tamke fusaka dan bama ta buƙatar basiru ya kawo mata raini, ita ƙyansa bawai ruɗarta yayiba.
A saman motarsa dayake ƙokarin buɗewa ta ɗora masa tana jifansa da harara, “Gashinan inji Ummukulsoom ”.
Bata jirayi amsarsaba tai gaba saboda kusantowar su inna laraba, bayanta yabi da kallo cikin takaici, wlhy data tsaya da sai ya kifa mata mari, cikin jan tsaki ya ɗauki takardar ya jefa a mota yashiga yana faɗin “baƙauyar banza, dama kinbar wahal da kanki wajen rubutamin wasiƙa, dan ayanzu dai tsakanina dake *Wutsiyar raƙumi tai nesa da kasa*. ban ƙiba zuwa nan gaba ƙila na dawo gareki kema ki dandali arziƙi”.
Shi kaɗai yake sambatunsa a mota ya na tuƙi, dan zaria zaije.

Haɗuwa da basiru ba karamin miki ya tadama Ummukulsoom ba, shiyyasa kwata-kwata bata fahimtar faɗan da ƴan uwan baba suke mata, itadai tana saurarensune kawai.
Gab da la'asar motoci uku sukazo na ɗaukar amarya, dan babane yacema Alhaji Mahmud ba mutane da yawa bane zasu rakota, shi soyayma akaita da safe baƙi su juyo da yamma.
Amma sai Alhaji Mahmud yace sam bazai yuwuba, saisun kwana itama kowa yasan ƴar gatace.
Bayan an idar da sallar la'asar ne aka fito da Ummukulsoom dake kuka tamkar ranta zai fita, mata sai leƙe suke ta katanga, marasa haƙuri kuwa sunfito tsakar santa inda yara suka baibaye motocin ɗaukar amaryar.
Mota ɗaya kayan Ummukulsoom aka loda, na gara da wanda zata iya buƙata da kayan sawarta, ɗaya kuma mutum huɗu suka shiga, uku mata namiji ɗaya cikin yayunta.
Ɗayar motarma mutum biyu sai ummu ta Uku, sai aziza a gaba.
Kamar haɗin baki yara suka fara raira waƙar amarya ta bankwana, hakan saiya kuma janyo hankalin mata suka makalƙale katangu suna kallo har motocin ɗaukar Ummukulsoom suka lula.

★★★★★

Ganin basiru ba ƙaramin tsayama Ummukulsoom yayi a raiba, har suka ɗauki hanyar kaduna tana kuka ƙasa-ƙasa na tausayin kanta, shikenan yau tabar ahalinta gaba ɗaya tatafi gidan aure, gidan Aurenma inda akafi ƙarfinta, kallon lamari take tamkar wani almara ko film.
Abu ya haɗe mata goma da ashirin, kukan rabuwarta da tushenta da mahaifinta datafi ƙauna fiye da kowa da dangin mahaifiyarta, kukan rabuwa da masoyinta basiru wanda alamu sun nuna da gaskefa sun rabu har abada, yaya zatayi da ɗunbin so da ƙaunar da take masa kenan?, ga rashin jin daɗin jiki, sai fargabar sake sabuwar rayuwa a gidan Alhaji Mahmud, ga tsananin tsoro da firgici idan tama tuna wata aura?, dawa zata zauna?.
Kwata-kwata tarasa jinta da ganinta dama dukkan tunaninta har suka bar garin zaria, tunma tana jin fitar iska sama-sama har idonta ya rufe ruf taji ɗif sai duhu daya mamaye jinta da ganinta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Momcy zaune a ɗaki itada ƙanwarta Mansura da bata wuceba, sai Ummi babbar ƴarta.
Kallo ɗaya zakai musu ka fahimci duk ransu a ɓace yake, Mansura ta sauke numfashi tana janye tagumin da tayi.
“Aunty Jamila ga shawara, nifa a ganina kibi gargaɗin da mijinki yay miki, dan kinfi kowa sanin halinsa. Mu tarbi amarya tamkar ranmu babu komai, idan zata wuce legos ɗin nan ne zamu samu damar gudanar da shiri na gaba kuma”.
“Hum mansura kenan, da kinsan yanda nakejin wani baƙin ciki akan aurennan na Fodio da bakice na danne zuciyata na tarbi shegiyar yarinyarnan da danginta ba, amma kuma ba a ƙin ta mutane inji masu ida magana, minene shirin namu na gaba?”.
“Yauwa auty, abinda dama nakeson ki tambaya kenan, bayace nanda kwana biyu za'a kaita wajen Amaan ɗinba?”.
“Eh haka yace”.
“To Aunty anan ne kekuma zaki lallaɓasa akan kinaso kuje duka gidan rakata, zaki samu damar ganawa da Amaan ɗin kema, idan kun tashi tahowa abaro masu Ummayya da Aneesa su zasu ƙarasa mana sauran aiki su hana tsinanniya zaman lafiya, tunda ba koyaushe Amaan ke a gidaba dama”.
Ummi da tun ɗazun batace komaiba

Please Login or Register in order to submit comment