Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“Ban saniba, Mi yarinyar can tamaka kaji mata ciwo a ƙafa!?”.
Kansa ya dafe cike da tsantsar takaici, ɗan abunda ya mata har yakai na a hau kansa irin haka?.....
“Fodio da kai nake, banason iskanci fa?”.
Idonsa harya fara canja Cala, da ƙyar ya iya furta “Dad ni minai mata to?”.
Dad ya yunƙuro zaiyi magana Momcy data shigo tai azamar tararsa da faɗin, “Abban Fodio dan ALLAH kayi haƙuri, mubi a hankali”.
“Anƙi abi a hankalin kekuma, in banda iskanci da tsabagen zalunci daga zuwan yarinyar gidan ziyara saiya kama cutar da ita, kai wai a rayuwarka bakajin daɗine idan bakai zalunci ba? To wlhy wannan yazama farko da ƙarshe da ko harar banza ka sake mata, shashasha kawai mai baƙar zuciyar tsiya. Ke kuma ki gargaɗi ɗanki ya kiyayi taɓa yarinyarnan, akanta zan iya saɓa masa wlhy”.
Fuuuuu Dad ya fice yabar musu sashen.

Kafe ƙofar da Dad ya fice yay da kallo, yakasa koda motsi daga inda yake tsaye, akan wannan yarinyar Dad kemasa waɗannan kausasan kalaman? Bayan kuma itace taja yay mata hakan........
Ita kanta Momcy kalamansa sun girgizata, to ita yarinyar wacece ita da har yake tada jijiyar wuya a kanta?.
“Fodio wacece ita wannan ɗin? Dan na fahimci daga kai har Alhaji kunsanma wacece kenan?”.
“Momcy ni ban santaba”.
“To in bakasan wacece itaba miyasa kai wannan gangancin? Miya haɗaka da ita?”.
Kallonsa ya maido akan Momcy amma ya kasa bata amsa. sanin ransa a ɓace yakene ya saka Momcy kama hannunsa ta kaishi har rukunin kujerun dake falon, ya zauna. Itama zama tayi gefensa, “Fodio kayi wauta, yarinyarnan dama itace nake fatan kaje ku daidaita, gashi tunkan aje ko ina kafara ruguzamin shiri, dan ALLAH Fodio ka rage zuciyarnan taka......
“To amma Momcy sai kawai na zauna ƙaramar yarinya taitamin rashin tarbiyya.”
“Wane irin rashin tarbiyya kuma Fodio? kai yaushema ka santa da zakace haka?, irin waɗannan yaranfa abun tattaline, Ko dai ka santa ɗin da gaske kuna ɓoyemin ne?”.
Idanu ya tsura mata kawai, yana maimaita kalmar tattalin data ambata a zuciyarsa tareda rarrabe ma'anoninta a ransa.

A tsakar gida kuwa Baba Halima ce ta duba ƙafar Ummukulsoom, dan ta iya gyara, sai taga ashe targaɗene kawai tayi a ɗanyatsa, kuma ya maida ƙatsin lokacin daya matsa ƙafar, magani taje ta ɗakko ta shafa mata, a ranta tana mamakin halin Amaan, shikam yama zarta mahaifinsa murɗaɗɗen hali, ina daɗi daga zuwan yarinya gida kai mata wannan ganganci haka in banda dai ƙarfin hali.
Bily tayi zuru-zuri, sai tsoron Amaan ɗin ya kuma kamata itakam.
Ana gama gyarawa Ummukulsoom tace itadai gida zataje gaskiya, Dad bai hanaba yace suje ɗin.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*_Birnin Paris_*

Dur ƙushe yake a gabanta tamkar ɗa mai neman gafarar mahaifiya, ya rame ya lalace matuƙa gaya, tamkar ba Baseer ɗinnan ba ɗan ƙwalisa mai bama mata pepe, babu wannan kwarjinin da cikar haibar da kwanciyar hankali ke samarwa.
Hawayen dake tsiyaya a fuskarsa wasu na bin wasu ya share, ya kuma gurfana a gabanta yana roƙo, “Dan ALLAH hajiya kimin aikin gafara, wlhy tallahi ƙarfina ya ƙare bazan iya ba, dan ALLAH ki bani dama na sawwaƙe miki na koma ƙasata wajen iyayena da kika nisantani dasu tsahon shekara Biyar, wlhy nayi nadama.........”
“Wlhy bakayi nadama ba Baseer, dan har yanzu baka gama magantuwa ba, baka kai ƙarshen littafin rarrabe shu'umcin maceba.......”
Muryar da bai zato ba ta katse masa zancensa, a matuƙar rikice ya juyo jikinsa na wani irin ɓari da rawar mazari, cikin tsantsar tashin hankali da gushewar tunani ya furta *“Suhailat!!”* saiya sulale wajen a sume kawai.

Suhailat dake tsaye a bakin ƙofa ta tako cikin tsantsar ƙasaita zuwa gaban Baseer dake kwance wanwar a ƙasa, murmushi mai ƙayatarwa tayi kafin ta maida kallonta akan Meenal dake tsaye itama fuskarta ƙawace da lallausan murmushi, hannu suka bama juna cikin kashe idanu......😬

🙀🙆🏻‍♀️ Tirƙashi, nasan babban burin kowannenku sanin mikuma ya maida Baseer haka bayan barinsa ƙasarsa ta haihuwa🤔🙆🏻‍♀️, to lallai yanzune zaku sani kuwa tamkar yanda kuka matsu da cigiyarsa a kullum.😳😉


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

“Yaya Zaid ya naga Yaya Attahir ya nufi hanyar gidan Hajiya yaya kuma?”.
“Wlhy nima ban saniba Bily, amma bara dai na kirashi a waya naji”.
Ummukulsoom na kwance cikin kujera a baya tana jinsu, sai dai kuma bata tankaba, dan dama ta daɗe tana son zuwa gidan Hajiya yaya ɗinnan, amma tarasa miyasa Abba kamar yake ƙin son zuwanta? Ƙyaƙyƙyawan zaton da take masane ya sata bata zargi hakan a matsayin komaiba sai ƙyaƙyƙyawan dalili wanda shine kaɗai ya barma kansa sani.
Tunanin da tatafi ya hanata jin mi wayar Zaid ta ƙunsa, dan haka taci gaba da tunanin shika-shikan rashin mutuncin datake tanadama wannan azzalumin (Amaan) (maganar gaskiya masoyan Ummu kune bakuda gaskiya a wannan gaɓar😂, dan kuwa Ummu ce ta takalo faɗan dayafi ƙarfinta).

Bara nayi ta kaina karnasha suburbuɗa a hannun gayu
⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😝

★★★★★★

Gidane madai daici ammafa mai tsari tamkar ba tsohuwa ke a cikiba, da taimakon Bily Ummu ke takawa zuwa cikin gidan daya ƙayatar da ita.
Falo tsaf tamkar bana tsohuwa ba, sai ƙamshi ke tashi na musamman.
Sallamar da suke rangaɗawa wata dattijuwar murya ta amsa daga wata ƙofa.
Bily ce cikin ɗaga murya tace, “Tsohuwa mai ran ƙarfa kimazafa kinada manyan baƙi yau a gidannan”.
Hajiya yaya tsohuwa mai tarin dattako ta fito cikin shigar kamala tana faɗin, “Ja'ira mai ɗan karen ƙaudi, kune baƙin nawa?”.
Zuwa bily tayi ta rungumeta, Hajiya yaya ta tureta, “Bilkisu kinci garinku, karyani zakiyine?”.
Bily dake dariya tace, “Waceni da wannan gangancin Abba ya ci ƙaniyata”.
“A'a kice gidanne du gaba ɗaya, Zaidu lafiya naganka yau rai a ɓace?”.
Duk kallon Yaya Zaid ɗin sukayi, shiko dai yakasa fara'a tun abinda ya faru gidansu Dad ne kecin ransa, yayma Hajiya yaya murmushin yaƙe kawai.
Duk wannan abun dake faruwa Ummukulsoom ta fita a hanyyacinta, dankuwa tun fitowar Hajiya yaya ta ƙureta da ido baki sake.
Attahir ne ya fara lura da halin da Ummukulsoom ke ciki, dan haka ya taɓa Hafsat dake a kusa dashi ya nuna mata Ummu...
Miƙewa Hafsat tayi ta nufi Ummukulsoom da ɗan hanzari ganin tayi baya zata faɗi saboda tsabagen firgici da take a ciki, wannan ne kuma yaja hankalin sauran har Hajiya yaya da ita sam bama ta lura da Ummukulsoom ba sai yanzun........


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Tunda suka bar gidan sai ya rasa inda zai tsoma kansa yaji daɗi, miyasa ya aikata mata hakan? Anya kuwa ta cancanci hakan duk da itace ta fara aikata masa laifi? Ya rintse idanunsa da ƙarfi tareda tafe kansa, batareda ya shirya suɓutowar maganar dake kan harshensaba yace,
“Zuciyata bakimin adalci ba, kin jefani a halin da gangar jiki da ƙwaƙwalwa bazasu iya juraba, ni ban shiryaba! Ban shirya ba nace.....!!!”.
Ya faɗa a matuƙar harmutse yanajin kansa tamkar zai fashe gida biyu, tun daga randa yaji muryarta komai ya fara canjawa a rayuwarsa, abubuwansa masu muhimmanci dake da alaƙa da gangar jikinsa sun kasu gida biyu wajen yin aiki, *ƙwaƙwalwa da Zuciyar sa* duk sun raba tunaninsa tare da nata, wane irin jarabawace wannan ta sartse mai wahalar fiddawa koda da tsinin allurane. Shika ɗai yasan a halin da yake ciki, miskilancin sane kema damuwarsa hijjabi da fahimtar mutane, duk yanda yaso yakiceta ya kasa, kullum lamarin ƙara ruruwa yake da girmama a duniyarsa.
Wanene zai tunkara? Wazai fahimcesa? Ta yaya zai fiddo abinda ke ransa? Dad ne yay masa katanga ta baƙin ƙarfe akan dukkan maganar data shafi kalmar aurensa.............✍🏻


NO. 31

..........“Ai ta suma”. ‘cewar Maman Ahmad a matuƙar harmutse, da gudu Zaid ya nufi kicin ɗin Hajiya yaya ya ɗakko ruwa. koda ya buɗe sai Hajiya yaya da itama jikinta ke mazarin rawa saboda ganin fuskar Ummukulsoom ta amsa ta shafa mata a fuska.
Nannauyan numfashi Ummu ta sauke, kafin ta buɗe ido a hankaki ta saukesu kan hajiya yaya.
Dukansu numfashi suma suka sauke.
“Da ana mutuwa a dawo da yau nace mahaifiyata ce ta dawo gareni, duk da a hoto kawai nai mata farin sani ba'a zahiriba. Dan ALLAH yaya Attahir idan mafarki nake ku tadani daga wannan nannauyan barci kafin sauran hankalin da ya rage a ƙwaƙwalwata ya ida tarwatsewa”.
Hajiya yaya da har yanzu jikinta ke rawa ta kamo hannun Ummukulsoom cikin nata, idanunta kafe a kan fuskar Ummukulsoom, lallai tanaji a jikinta ko tantama babu wannan yarinyar jininta ce, amma ta yaya ta kasance a cikin family ɗinta bayan babu wani mahaluki daya san inda take tunda ta juyama jiyanta baya, tai wani murmushi mai ciwo, a hankali ƙwallar da suka cika mata ido suka sulalo a dattijuwar fuskarta.
Hakan sai yakuma saka jikin su Attahir yin sanyi ganin Hajiya yaya na kuka, lallai hakan yana nufin akwai abunda basu saniba kenan.
Kallon Attahir hajiya yaya tayi, “Attahiru ina kuka samo wannan yarinya?”.
Numfashi Attahir ya sauke a hankali, kafin ya kalli maman Ahmad da Zaid da Bily yay musu nuni da su fita.
Harsun yunƙura zasu fice Hajiya yaya ta dakatar dasu, “Kunga ku dawo ku zauna. Kai kuma mushiga ciki”. Tai maganar tana jan hannun Ummu, bin bayansu Attahir yay har bedroom ɗinta.
Jikin Ummukulsoom yakuma yin sanyi ƙalau, ga ƙafarta na mata zugi dan sai yanzu ma takejin zafin har a zuciyarta.
A bakin gado hajiya yaya ta zaunar da Ummukulsoom itama ta zauna, Attahir kuma ya zauna a kujerar dake ɗakin mara tudu sosai, an mata itane kawai dan hutawarta.
“Attahiru ina saurarenka”.
Guntun murmushi Attahir yayi, kafin yace, “Hajiya yaya da son samune ace Abba yana tare damu, dan nidai shine silar komai, ko dai a kirasu a waya ne?”......
“Basai an kirani ba gani a kusa”.
Dukansu ƙofa suka kalla inda Abba ke a tsaye, ya ƙarasa takowa cikin ɗakin, Attahir yay saurin sauka a kujera ya koma ƙasa, itama Ummukulsoom ganin haka sai ta sauka ƙasan.
Hajiya yaya dake kallon Abba tace, ”Abubakar ina saurarenka”.
Murmushi Abba yayi, kafin yace, “Hajiya ki gafarceni, ni mai laifine a gareki wajen tone abinda kiketa ƙoƙarin binnewa”.
Sosai ta kafeshi da idanu, “Abubakar!”.
“Na'am Hajiya”.
“Ya akai hakan?”.
“Kiyi haƙuri hajiya, komai na rayuwa yanada sanadi, ni nawa sanadin shine auren Ummukulsoom da Fodio na wajen Alhaji Mahmud abokina. Tun randa Alhaji Mahmud yazomin da zancen ya samawa Fodio matar aure a garin Ɗilau tunanina ya dawo gareki”.
“Ɗilau Abubakar? Dama acan Usman yayo aure?”.
“Eh hajiya a canne, bayan munkai kuɗin auren mun dawo nazo na faɗa duniyar tunani, tareda samun ƙwarin gwiwa bisa wasiyyar mahaifina da bai samu damar ƙarasa faɗaba ciwo ya gala baitar dashi, *(Abubakar mahaifiyarka ƴar wani ƙauyece ɗilau, amma an haramta mata z....)* iya abunda ya faɗamin kenan tari ya sarƙeshi, daga nan kuma harshensa bai sake furta wata kalmaba har ranar barinsa duniya, ban fahimci ƙarshen zancensa ba ko ma'anarsa shiyyasa a koda yaushe nake ɗakko miki hira akan sunan garin, amma sai kikan nunamin ɓacin ranki akan hakan, wannan dalilinne yasani daina miki maganar, sai dai a kullum neman inda zansan garin ɗilau nake, sai a dalilin auren Fodio na sani, ashema kusa take damu. Bayan bikin Fodio ban sake wani yunƙuri akan komaiba, saboda bansan ta inane zan fara ba, amma na kira Attahir akan yay ƙoƙari ya kusanta matarsa da matar Fodio, ƙila kota sanadinta zansan wani abu gameda wasiyyar mahaifina. Ban san fuskar matar Fodio ba, saboda ko a lokacin da tazo gaishemu ranar ɗaurin aurensu fuskarta a rufe take. Babu wani bayani mai gamsarwa dana samu a wajen Attahir kusan watanni shida, sai kirana da yay yake sanarmin saɓani daya shiga tsakanin matar Fodio dashi Fodio ɗin, hakanne yasa nace duk yanda zaiyi yayi tazo gidana ni da kaina saina maidata ga iyayenta, wataƙil ta sanadin haka nima na samu haske a nawa binciken. Wannan shine dalilin dawowar Ummukulsoom gidana, tunda naga yarinyar hankalina saiya kuma tashi, dan tabbas akwai kamanni a tsakaninku, sai mutum ya maida hankali sosai zai fahimci hakan, wannan ne yasa nai duk wani ƙoƙarin ta zauna tare damu domin jifan tsuntsu biyu da dutsi ɗaya, ta samu cikar burinta, nima na samu cikar nawa burin. Zuwan su Bilkisu garin ɗilau rakkiyar Ummu ne ya kuma tabbatar min da akwai ɓoyayyen sirrin da ban saniba game da mahaifiyata, amma gudun ɓacin rankine yasa na hana akawo Ummukulsoom gidannan a tsawon shekarun da tai tare dani, anawa tunanin saina gama gano komai, to gashi kuma ban gama gano komanba Attahir ya kawota”.
Hawaye sosai Hajiya yaya take sharewa, haka ma Ummukulsoom da duk mamaki ya kamata, itako ashe lallai haukar ƙuruciya na ɗawainiya da ita, dan bata taɓa kawo komai gameda zamanta gidanba, hakama sometimes mutane kance tana kama da Bily, amma bata taɓa gasgata zancenba saboda ita bata ganin kamannin.
“ALLAH yay maka albarka Abubakar, ba abun kunya yasani ɓoye maka komaiba, bin Umarnin mahaifinane, inason garinmu, inason zuwa cikinsa, inason ahalina dake cikinsa, sai dai wani furuci yay min hijjabi da tsintar kaina a cikinsa”.
“Sunana Ummukulsoom na yanka”.
Gaba ɗayansu suka kalli hajaiya yaya da mamaki.
Murmushi tai musu tareda jinjina kanta, “Ƙwarai da gaske sunana kenan Ummukulsoom, Mu uku mahaifinmu ya haifa a duniya wato malam Ado ba rinji”.
Da sauri Ummukulsoom ta kalli hajiya yaya jin sunan wanda ta ambata.
Nanma murmushi Hajiya yaya taima Ummukulsoom ɗin, sannan ta cigaba da faɗin, “Ni ce babba a gidanmu, sai ƙanwata Hindatu, sai autanmu Lirwanu. Muna samun gata a wajen mahaifinmu dan mahaifiyarmu tun a wajen haihuwar Lurwanu ALLAH yay mata rasuwa, kulawar da mahaifinmu ke manace ya saka iyami tsanarmu, wato matar babanmu, a haka muka rayuwa cikin wata bahaguwar rayuwa a hannun Iyami, a wajen baba kawai muke samun sauƙi. Shekarata 12 baba yay shirin aurar dani, dan haka ya bada sadaka ta ga Ɗan-asabe, anyi baikonmu da ɗan-asabe duk da ba sonsa nakeba, amma biyayya ta saka ban musaba. Bayan baikon mu da sati guda na tafi kiwon dabbobi daji ni da Hindatu kamar yanda muka saba a kowacce damuna, dan anayin ɗaurene, zalincin iyami yasa da ta sai ciyawa gwamma ta sanu kwance dabbobin mu tafi kiwonsu daga safiya har yammaci, randa mukayi gigin dawowa da wuri ta lakaɗa mana duka tace cikin dabbobinta bai ƙoshiba, idan kuma lokacin rani ne bata sakinsu, saidai muje daji muyo musu abinci, hakan ba komai bane face salon ƙuntata mana. A wannan ranar da muma fitane muna tsaka da kiwo sai maciji ya sareni, take a wajen na zube, dan haka hankalin hindatu ya tashi ainun, tashiga kuka da kururuwar neman taimakon wani. Ana haka ALLAH ya kawoshi cikin mota”.
“Hajiya yaya wake nan?”. Cewar Attahir.
Murmushi hajiya yaya tayi tana gyara zama, “Attahiru mi kakeci na baka na zuba, ai yanzu zaka sanshi. Ba kowa bane face kakan ku, shine ya taimakeni bai saurari komaiba ya ɗaukeni yasa a mota tare da Hindatu ya nufi Zaria da mu. Ni bamma taɓa zuwa zaria ba sai ranar, ALLAH ya taimaka dafin macijin mai sauƙine, sai aka samu kaina cikin amincin ALLAH, amma dai an kwantar dani a asibitin. Shine ya koma da Hindatu Ɗilau suka sanar da halin da nake a ciki, hankalin baba ya tashi matuƙa, yay ta sakama kakan ku albarka tare da godiya. Amma Iyami gareta ba hakan baneba, ita masifa ma take ina dabbobinta? Sai a sannan kakanku ma yasan abinda yakaimu jeji har wannan lamari ya faru. Gidan maigari baba yakai cigiyar dabbobinta, kaifin yabiyo kakanku su dawo Zaria wajena. Indai taƙaice muku zance shine yayta ɗawainiya da hidimar asibitinmu harna warke, sai dai kuma Ubangiji mai hikimane, dan kuwa shiyya saƙa soyayya mai ƙarfi tsakanina dashi a wannan jiyya, bayan warkewata muka dawo ɗilau, sai ya zamana duk sati saiyazo ɗilau. Hakanne ya tashi hankalin Iyami, dan kuwa ta ɗau alwashin waninmu bazai taɓa samun cigaba ba, yanda bata haihuba a gidan mu da aka haifa sai dai muƙare rayuwarmu a wahala. Ita ta fara fargar da baba wai soyayya nake da Ibrahim. Hankalin baba saiya tashi saboda yana ganin yarigada ya badani, janye waccan maganar kuma tamkar zubar da kimarsa ne, sannan hana Ibrahim ni tamkar butulcine, sai yay yunƙurin datse alaƙar da hanzari, amma kuma sai hakan bata faruba, dan kuwa yana tunkarata danson jin gaskiyar zance na sanya kuka akan nifa lallai Ibrahim nake so, dama kuma banason Ɗan-asabe kowa ma yasan hakan. Da farko Baba kam lallaɓani ya farayi, ganin naƙi saurarensa saiya canja salo saboda zugashin da Iyami keyi. tun anayin abu iya gidanmu harya fito ya fara yawo a garin ɗilau, kowa ya samu abin faɗa. Hakan ya kuma birkita baba ya gaza fahimtar ba laifina bane, zuciyata ce, yagaza fahimtar sheɗancin Iyami. Ibrahim shima yana matuƙar sona sosai, dan kullum cikin zuwa roƙon baba yake amma baba ya baɗe idonsa da toka yaƙi saurarensa. A wani dare sai hindatu ta tadani na rakata banɗaki amma sam naƙi, nace in bazatajeba sai dai tayisa a wando. Ƙyaleni tayi ta fice dukda tanajin tsoro, batafi mintuna uku ba sai gata tadawo, “Yaya, yaya tashi kiga mi Iyami keyi”.
“Tashi nai zaune da sauri, nace, “Mi Iyamin keyi?”.
“Ke dai taso ki gani Yaya, dan bayanina bazai gamsar da keba”.
“Ban musaba na tashi na bita, ta can bayan ban ɗakinmu inda Rumbu yake muka iske iyami tana haƙa rami, laɓewa mukayi ta gama tsaf ta saka wasu layu a ramin, sai da tagama harda yayyafa ruwa ta maida ƙasa ta rufe kafin ta miƙe tana ƴar dariya, “Umma ɗan-asaben ma basamun damar aura zakiyiba balle wani Ibrahim ɗan birni, kamar yanda malam ya sanarmin layunnan na cika kwana goma a ƙasa Ibrahim zaiyi iskanci dake, na tabbata hakan ne zaisa kowa ya tsaneki a ƙauyennan idan kikayi cikin shege, mahaifinki ya tsine miki ya koreki, na gama da babinki, saura Hindatu itama”.
Gaba ɗayanmu mun tsorata da kalamanta, danni harma na fara hawaye, da ƙyar muka ɗauke numfashi yayinda zata wucemu, a ranar bamuyi barcin sauran darenba daya rage. Washe gari tunda safe muka nufi gidan ƙanwar mahaifiyarmu muka sanar mata abinda mukaji, itama hankalinta ya tashi, dan haka tace mu turo mata Ibrahim idan yazo. Dato muka amsa, cikin amincin ALLAH kuwa washe gari saiga Ibrahim, dayake a lokacin a ɓoye muke haɗuwa, shine na sanar masa da zancen Innarmu. Bai musaba mukaje wajenta. Bayan sunyi gaisuwar mutunci tace, “Bawan ALLAH da gaske kake son ƴata kuwa?”.
Cike da ladabi Ibrahim yace, “Wlhy Ina sonta Inna, kuma a shirye nake na aureta ko a yanzunnan ne”.
“To Alhmdllhi, yanzu inaso ka ɗauki Umma kuje garin ɗan-gamau a katsina, idan kunje garin kuyi tambayar gidan Malam Baushi, kuyi masa bayanin komai daya faru, kuce masa nace ya ɗaura muku aure, Ibrahim ga amanar Umma nan, idan kaci ALLAH ya ci taka, karku zo Ɗilau saita haihu”.
Godiya mukai mata muduka muna kukan jin daɗi, a ranar muka tafi babu wanda yasani har Hindatu, duk yanda Inna tace muyi haka kuwa mukayi, Malam Baushi ya ɗaura mana aure, satinmu ɗaya a can Ibrahim ya ɗaukeni muka wuce legas wajen aikinsa, ban fuskanci matsala a wajen danginsa ba danshi marayane. Ban sake waiwayen garin ɗilau ba, dukda kuwa ina matuƙar kewarsu, sai da na shekara biyar, dan har lokacin ban haihu ba, saida na shekara biyar da wasu watanni nasamu cikin Abubakar, bayan haihuwarsa naso zuwa Ɗilau domin cika alƙawarin inna amma sai wani aiki ya riƙe Ibrahim, dan haka ya bani haƙuri, dan shi burinsa muje tare mu nemi gafarar baba, zamu-zamu tafiya bata yuwuba har na yaye Abubakar, kwatsam kuma saiga wani cikin, ganin haka sai Ibrahim ya lallabani akan nai haƙuri na haihu saimu tafi, ƙilama Baba yafi karɓarmu. Hakance ta faru kuwa, dan saida na haihu tagwaye duk mata sannan muka shirya zuwa ɗilau. Komai ya canja mini daga yanda na sanshi, abubuwa da yawa kuma sun faru, dan ansha tashin hankali bayan nemana da akai aka rasa, a maimakona sai aka ɗaurama Hindatu Aure da ɗan-asabe, baba kuma yace ya barma duniyani, har abada ya cureni cikin ƴaƴansa. Har zuwanmu ɗilau baba na akan bakansa na ƙin karɓata, dankuwa muna fita a mota bai bari nataka koda zauren gidanmu ba yace mu juya, tareda furucin inhar na sake dawowa garin ɗilau ALLAH ya isa bai yafemin ba.
Hajiya Yaya ta fashe da kuka mai tsuma rai, wanda yasaka su Ummukulsoom da Attahir harma da Abba kuka suma, da ƙyar Hajiya yaya ta tsagaita taci gaba da faɗin, “Bansan yanda zan fassara muku halin dana shigaba dagani har ibrahim, da ƙyar nasamu wani ya faɗamin inda Hindatu take aure, Lurwanu kuwa na iske ya rasu sanadin zazzaɓi da yayi. Naje gidan Hindatu, muka rungume juna muna kuka, na isketa har tayi haihuwa Uku ita, ƴar da take goyo ma tsakanin haihuwarta da ƴan biyuna kwana ukune, na amshi ƴar saina ganta a langaɓe, hankali tashe na kalli Hindatu da itama take kallona tana kuka.
“Hindatu miya sametane?”..
“Yaya ta rasune yanzunnan, ina kukan mutuwartane ma kika shigo”.
Sosai hankalina ya tashi nima, na rungume yarinyar a jikina ina hawaye, muna cikin haka saiga ɗan aike daga baba, yace inhar ban zo nabar garinnanba yazo gidan hindatu ya iskeni saiya min abinda ban taɓa tunaniba, kuka na kuma fashewa dashi, na kalli hindatu da itama kukan takeyi.
“Hindatu dan ALLAH kimin wani taimako kafin nabar garinnan”.


Please Login or Register in order to submit comment