Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aunty ta sake maimaita tambayan jin tayi shiru, a hankali tace "Aunty tana lafiya, ai tana ďakinta", Aunty tace "yayi kyau Batuul, in kin huta zamuyi waya kinji, inason muyi magana", Batuul tace "Toh Aunty, Baba fa, yana gida?", Aunty tace gashi nan Batuul, tayi rau rau da ido tace "Aunty shine baice zaiyi magana dani ba", Aunty tayi dariya tace "ai gashi nan faďa mishi da kanki", kamar zatayi kuka bayan Aunty ta mik'awa Baba wayan tace "HellO Baa, nda dubdo", da murmushin shi na manya yace "Mamana nda dubdo, ya sabon waje", a hankali tace "Baa Alhamdulillah", yace "Masha Allah Batuul, Allah yayi miki albarka, ki kula da ibadunki, ki girmama na gaba dake kinji, babu ruwanki da tsokana ko tadawa mijinki hankali, ki zama mai biyayya kuma kiyi ta hkuri kinji, Allah ya taimaka", tana kuka da k'yar ta iya buďe baki tace "In sha Allah Baa, nagode", da haka suka katse k'iran, kuka sosai ta sa bayan sun gama wayan, shikenan rayuwanta ya canja kenan, ta dde xaune ganin yunwa ya dameta don har uku na rana yyi yasa ta mike a hnkli da Hijab jikinta ta tura kofan dakin ta fito, downstairs ta nufa a xuciyarta tana addu'an Allah yasa Ajiddeh bata nn, xaune ta sameta falon tana kallo tana cin sauran pizzan ta, duk irin faduwar da gabanta yyi hkn bae sa ta koma ba, cikin natsuwa ta tako har cikin falon ta kalleta a hnkli tana ci gaba da tafiya tace "Ina yini Anty?" Wani matsiyacin kallo Ajiddeh ta bi ta da shi har ta shiga kitchen din, snn ta mike, sae da ta fara kallon stairs snn ta bi ta cikin kitchen dib, Batuul na tsaye tsoro ya cikata don xuciyarta ya bata sae ta biyota, lallai tayi gangancin sakkowa Ajiddeh na falo, daga bakin kofa ta tsaya tana kallonta tana murmushin rainin hankali tace "Ke a tunanin ki kin samu gun xama a gidana koh? To yhu are mistaken yarinya, don sae kin gwammace da baki shigo gidana da sunan xama kiyi karatu ba, banda kinibibi, gulma, da munafurci irin na iyayen ki sun san basu da halin kama maki hostel me xae kai su karambanin turo ki UK karatu, shine xa a wani xo a daura ma miji na nauyi da wahala to wllh kun yi kadan, duk uban da ma ya kawo wnn shawarar zae saketa ne, don sae sai kin gwammace da titi kike kwana kan gidana, makwadaita kawae" Ae Batuul bata san lkcn da ta fashe da kuka jin xagi da cin fuskar da Ajiddeh ke ma iyayenta, ita din ba mai son fada bace bare ta mayar mata da martani, durkushewa gurin tayi ta dinga kukan takaici da tausayin rayuwarta, ran Ajiddeh yyi fari don har da murmushinta, ta cigaba daga inda ta tsaya.


Abuturrab kam na daki kan system wayarsa ta hau kara, dauka yyi ganin Ammah yasa shi saurin d'agawa da sallama, Ammah tace "Abu kun isa lafiya, shine ba kira?" Yyi k'asa da kai yace "Kiyi hkuri Amnah ynxu nake da niyar kiran ki, gajiya ne yasa hka", Ammah tace "Shknn Babana, ina Ajiddehn, kun sameta lafiya", yace "Alhamdulillah Ammah she is doing good", tace "toh Abu, bazan gaji da yi maka Nasiha ba, ka kula dasu ka zauna tsakaninka da Allah dasu, Allah zai tayaka rik'on indai niyyanka is pure, sannan Fatima yarinyace k'arama, hankali bai gama game ta ba, in ka cuceta akan matarka, toh Allah sai yayi mata sakayya, kaji tsoron Allah Abu, kuma makaranta Abui yasa Sadiq ya turo maka, in ka duba kaje kayi mata necessary abubuwan da duk ya kamata" sai da yaji tayi shiru tukunna yace "In sha Allah Ammah nagode, Allah ya k'ara nisan kwana", ta amsa da "Amin, Allah yayi muku albarka, bata wayan inyi magana da ita", yace "Ammah tana ďakinta, sai dai in kai mata", tace kai mata ina jira", yace " Toh xan kira ki" daga hka ya katse wayar ya fita yayi hanyan ďakinta, ganin bata ciki yasa ya sakko falo, tsayawa yyi daga stairs hango Ajiddeh da yyi tsaye kofar kitchen din don yasan ba arxiki ya kai ta ba, Karasowa yyi Ajiddeh na hango sa tayi tsit daga cin fuskar da take ma Batuul cike da faduwar gaba, shiga kitchen din yyi yana kallon Batuul dake durkushe har lkcn a kitchen din tana kuka, Ajiddeh ta juya ta bar bakin kofar da sauri ya bi ta da kallo, murmushi yyi yana kallon Batuul dake kuka kmr xata shide yace "Yhu see! Kinga abinda nake guje maki knn, kika rufe ido kika ce sae ni, don hka yhu have to endure duk me xa ki fuskanta daga matata tunda kika ce kin ji kin gani...." kallonshi tayi da idonta da yyi jajir ta mike da kyar ta fice daga kitchen din hawaye na bin kuncinta, murmushi ya shiga yi yana jujjuya wayar hannunsa, wayar ya fara ring, sae a snn ya tuna abinda ya sakko da shi, xaro ido yyi ya bar kitchen din da sayri ya hau sama ya nufi dakinta, kwance ya sameta tana kuka ssae, ya karasa gadon ya xauna yana kallonta yace "Wae kukan me kike ma mutane hka daga an gaya maki gskya" kin cewa komae tayi, ya kalli wayar hannunsa jin ya katse, yasan Ammah ba hakura xata yi ba, sake bugowa tayi, ya ajiye wayar ya dago Batuul ya daura hannu kan kafadarta ya runtse ido yace "Alryt! Kiyi hkuri" ko kallonsa bata yi ba kuma bata daina kukan da take ba, a tsawace yace "Nace kiyi hkuri" ae sae ta kuma fashewa da kuka, rungumeta yyi ba tare da yyi wani tunani ba, yana patting bayanta a hnkli kmr me rada yace "Am.. am srry" ita kanta ta rasa dalilin da yasa ta tsaida kukan nata sae ajiyar xuciya da take saukewa, tana jikinsa ya jawo wayar da har ya katse, sae ga shi Ammah ta kuma kira, d'agawa Ammah tayi cikin fada tace "Walakanci ne hka Abuu?" Yace "Kiyi hkuri Ammah tana bayi ne, gata" kara wayar yyi a kunnenta yana rungume da ita, jin muryan Ammah yasa hawaye sake gangarowa a hnkli cikin sanyin murya tace "Ammah ina wuni", Ammah tace "Lafiya lau Bitti, ya gajiya, duk gajiyan ne naji muryar ki hka", kallon fuskarta Abuturrab ke yi kawae, tana sharen hawayenta tace "Alhamdulillah Ammah, babu gajiya ya su Abui da Farida", Ammah tace "suna lafiya Bitti, babu dai matsala ko", kai ta ďaga tana kallon Abu da suna haďa ido ya kuma mannata jikinsa, jiki a sanyaye tace "Ehh Ammah babu komai", Ammah tace "haka nake son ji dama, kiyi hak'uri sosai kinji Bitti, sai kiga komai yazo miki da sauk'i, makarantarki ma soon zaki fara zuwa kinji, ki manta da komai kiyi abunda ya kaiki, as i told you, don't hesitate in telling me your problems kinji, koh na meye", kai ta gyaďa kamar Ammahn na ganinta hawaye na xubo mata tace "Toh Ammah zanyi nagode", tace "Yawwa Bitti", daga haka ta mik'awa Abu wayan, ji tayi yace "Yeah gobe Monday zamuje a gama processing komai, sai Anjima Ammah mun gode", ita kam Batuul bata ďago ta kalleshi ba sae kkrin janye jikinta daga nasa da ta shiga yi amma ya ki saketa, cikin kakkausar murya yace "Wae ma kukan mey kike yi ma mutane daga an fada maki gskya,", sake fashe mishi tayi da sabon kukan takaici, lumshe ido yyi yana murmushi, lkci daya ya bude ido ya dafa kafaďunta yace "okay naga alamar kina son hada ni da Ammah ne, today shud b the last time da xa ki min kuka a gidana, its not going to b good for you idan na sake ganin kin yi hka, ba gidan ku bne nn, tunda kika zab'i aurena yhu have to endure everything yhu will come across" Shiru Batuul tayi tana saurarensa, duk taji yace ita ta xabi aurensa sae ranta ya baci, ido yabi fuskanta dake jik'e da hawaye, ďan k'aramin lips ďinta ya koma ja, yace "clean your face and hear me out", a hankali tasa hannnu tana goge hawayen, sai da ta gama yace "nasan dai kinsan zancen komawanki makaranta, gobe zakije a fara komai, it doesnt mean komawanki makaranta zaisa kiyi min yawo a gida ba, am not tolerating that, sannan babu ruwanki da matata inba girmamawa ba i cant take duk wani raini da zakiyi mata, ban yadda ki rainata ba, sannan ban yadda da tarkacen k'awaye ba, not in my house, abinda ya kaiki shi zakiyi ki dawo, inma zakiyi toh ya tsaya daga can makaranta, in kuma baki yadda da all i said ba, try me and see what will happen", har sai da taji yayi shiru tukunna ta janye daga rikon da yyi ma kafadunta tace "ai dama nasan you are always against my happiness, you snatched it all away from me, kuma da kake cewa kar in raina matarka ai nima duk sunanmu ďaya da ita, am also your wife kammar yadda kace an lik'a maka ni, and as it is, zan ďauki komai daga wajenka but not from her ka ja mata kunne bbu ruwanta da ni, kar ta kuma involving iyayena a abunta yawo kuma ba halina bane, k'awaye kuma, nobody can live in isolation, ba kowa na sani ba,", cikin k'arfin hali tayi duka wannan maganganun dan idonta rufe tayi duka wannan maganan, chest ďinta sai heaving yake, tsaf ya gama kalleta yana kallon yadda zuciyanta ke bugawa, dariya ta kusa bashi, a hankali ta buďe idonta, cikin hanzari ta tashi zata gudu dan sai yanzu maganganun da tayi suke dawo mata, hannu yasa ya fincikota jikinshi, a tsorace tace "Ni ja kyaleni xan hada ja da Ammah" sake janyota yayi jikinshi daidai kunnenta ya sunkuyo yace "fine if thats what you actually said, just try me and see", jin sauk'ar numfashinshi a wuyanta yasa duk tsigar jikinta tashi, kan gadon ya jefata ya juya xae fita daga ďakin, daidai bakin k'ofa yana fitowa suka ci karo da Ajiddeh ta shiga masa wani kallo, bai ce mata komai ba yayi tafiyarshi, da ido tabi k'ofan ďakin sannan tabi bayanshi da ido, hankali tashe tayi hanyan ďakinshi itama, ae ko baxa ta yi tolerating wnn ba.
[8/22, 14:46] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝






46






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





A hargitse ta tura k'ofan ďakin, yana kwance kan gado ya lumshe ido kamar ba shine ya shigo yanxun ba, dai dai kanshi tazo ta tsaya tana huci, ranta b'ace har wani gumi takeyi ta shiga yi masa magana, "Aliyu nifa bazan yadda da wannan abinda kuka tsira ba, wlhy ni bazan yadda da zamanta ba a cikin gidan nan, inma kai baza ka iya faďawa iyayenta baka son zamanta gidanka ba sai ka kama mata hostel ďin da kanka kawae, amma ba dai tayi ta zama min a gida ba dan dama nasan munafirci ya kawota", sai da yaji tayi shiru tukunna ya buďe lumsassun idanunshi dake rikitata yace "tunda gidanki ne sai ki koreta", ido ta wara tana kallonshi hawaye na bin kuncinta, cikin rashin damuwa da hawayen nata yaci gaba da cewa "tsabar rashin hankali da rashin sanin ciwon kai shine ki kaje kika tsareta a kitchen kina gaya mata maganganu koh, toh duk kika yrda ta raina ki baxa ki ji da dadi ba kuma bbu ruwana baxan kuma ce mata don me ba ", hankalinta ne ya k'ara tashi wai yau ita Abu ke k'ira mara hankali akan wata can y'ar iskar, wlhy Allah sai tasan yadda tayi da Batuul, sai ta wulak'anta ta fiyeda tunaninta, k'wafa tayi ta juya a fusace ta banko mishi k'ofar ďakin a xuciyarta tana cewa xaka rashin hankali kuwa, tabe baki yyi ya sake lumshe idanunshi ya gyara kwanciya yana shak'ar k'amshin Batuul da ya mannne mishi a kaya da yayi hugging ďinta.





Tana fita ďakin tayi hanyan ďakin Batuul a fusace kamar wacce zata tashi sama, kai tsaye ta tura k'ofar ďakin da Batuul ke ciki, tana zaune kan gadon a takure ta haďe kanta da guiwa, bata ďago kanta taga ko waye ba dan tasan shine ya dawo, ji tayi ance "tashi ki fita dan ubanki tunda ba ubanki ya gina min gidan ba", a tsorace Batuul ta ďago tana kallonta da mamaki shimfiďe a fuskanta, gani tayi tana k'ara shigowa ďakin, da sauri Batuul ta mik'e tana kallonta, inda akwatinan ta ke ajiye Ajiddeh ta nufa ta ďauka tana watsarwa, a tsorace Batuul ta tsaya tana kallonta, hawaye ya taru a idonta, ita wane irin masifa ne wannan yake tunkarota ko kwana daya bata yi ba, hawayen dake k'ok'arin zubo mata ta maida ta sauk'o daga kan gadon tana ganin yadda Ajiddeh ke watsar da kayan tayi hanyan waje, wai wannan ma fa dan bata san matarsa bace ita, hanyan waje tayi zata fita daga ďakin, hannu Ajiddeh tasa ta rik'ota tana cewa "ga y'ar iska na miki magana koh, toh dan ubanki kisan inda dare yayi miki dan gidana ba gidan ajiye y'an iska karuwai bane", ido Batuul ta rintse jin abunda Ajiddeh ta kirata dashi, zata iya rantsewa gaba ďaya rayuwanta bata tab'a jin an ambaci wannan word ďin a gidansu ba wai sai yau gashi ita ake k'ira da word ďin, hawayen dake idontane ya shiga gangarowa, hannunta tasa ta goge fuskanta, tasa hannu ta murďa k'ofan zata fita, wani irin force taji Ajiddeh ta tunkuďata dashi , ido ta rintse tana k'iran sunan Allah lkci daya ta fasa ihu tana jiran jinta a k'asa, amma ta ji akasin hka don jikin mutum ta faďa baya tayi zata faďi yayi hanzarin rikota ya rungumeta, shigewa jikinshi tayi tana boye fuskanta a kirjinsa, sai a lkcn ta fashe da kuka jikinta na rawa tsabar tsorata da tayi, kuka sosai ta shigayi tana cewa "Yaa Abu dan Allah ka maidani gida, dan Allah inaso inga Aunty, hannu yasa ya daďa haďe jikinsu dan yasan tsorata tayi ba da wasa ba, neman kukan da takeyi tayi ta rasa jin kanta faffaďan k'irjinshi, sai da yaga ta fara nutsuwa sannan ya saketa yana kallon fuskanta da hawaye ya gama wankewa, saketa yayi ya matsar da ita gefe ya zaunar da ita kan kujeran dake tsakanin ďakunan biyu, mutuwar tsaye Ajiddeh tayi ganin Aliyu ya kare Batuul, sam ba haka taso ba, taso koda Batuul bata mutu ba ta nakasa ta in yaso iyayenta suzo su ďauketa amma wannan jarababben ya taimakota, juyowa yayi ya shigo ďakin yanayinshi da ta gani ne ya sata tsorata, baice mata komai ba yasa hannu ya rik'o hannayenta tana binshi a baya kamar wata doluwa yayi ďakinshi da ita, kallonsu Batuul tayi hawaye cike idonta, ita dama tasan abin tausayi zata zama a gidan nan, duk abin nan da matarsa tayi baice mata komai ba sai ma rikota da yayi su tafi abunsu, kuka sosai ta kifa kanta kan cinyarta tanayi, sai sunan Aunty take k'ira da Baba, yana shiga ďakinshi da ita ya sake mata hannu, magana ta fara mishi cike da masifa "wllh Aliyu yarinyar nan ta barmin gidana dan....." bai bari ta k'arasa maganan ba ya wanka mata mari lafiyayyu guda biyu, a gigice ta ďago kanta da idonta da ya rine yayi ja tana kallonshi, wani shegen murmushi ta saki tana hawaye tace "koh baka dakeni ba nasan karuwarka ce ko daga yadda ka rik'eta a jikinka, ni za a yiwa bariki a wani ce karatu tazo yi, munafiki kawai azzalumi, Kuma wlhy kaji na rantse sai na illatata, mugu kawai.....", wani irin fixga da yayi mata yasa ta kasa k'arasa maganan da takeyi, idonshi ya sake yin jaa, yana kallonta yace "ai ke gidan na ubankine koh, dan bakida hankali kashe y'ar mutane zakiyi xa ki hankaďata hka, kinsan zaki iya barin gidan nan ita ta zauna, jahila kawai wacce bata aiki da hankalinta, kika sake min shirmen nan a gidana sai na b'ata miki yadda baki zato ba, mahaukaciya jahila", yana kai wa nn ya jefar da ita ya fice daga ďakin, inda ya barta kan kujeran nan ya dawo ya sameta sai kuka takeyi, ce mata yayi "kukan mey kike ma mutane ke kuma har ynxu", bata ďago ta dubeshi sai kukan da ta ci gaba dayi, cikin tsawa ranshi b'ace yace "ba magana nake yi miki ba", rinannun idanunta ta ďago ta kalleshi cikin sanyi hawaye nata zuba tace "Yaa Abu dan girman Allah da Annabinshi ka mayar dani wajen Aunty", hararanta yayi ya kamo hannunta, komawa tayi baya da sauri ta janye hannunta, tsayawa yayi yana kallonta yace "you thought all i was telling is lie huh, gashi nan kin fara gani tun ba aje ko ina ba, its just your first day and you have already faced soo much, sai da na faďa miki babu ruwanki da ita, mesa kika nemi magananta", haushi ne ya cikata ta tsananta kukanta tabi ta gefenshi zata shige ďakin yayi saurin rik'ota, wayantane taji yana ringing, fixge hannunta tayi tayi ďakin, bayanta yabi a hanzarce, hannu yasa ya rigata ďaukan wayan yana kallon mai k'iran, Affan ya gani rubuce in bold da hrt emoji daga gaban, kin bata yayi har sai da wayan ta katse, batare da ya kalleta ba ya jefa wayan kan gado, tsayawa tayi tana kallonshi , Juyawa yayi yana k'arewa ďakin kallo yadda kayanta ke zube a k'asa, ce mata yayi "da kika zauna kina yiwa mutane kuka waye zai tattare miki kayan da aka zubar garin neman faďanki, kinsan baki da k'arfi kika nemi tsokananta", bata ce mishi komai ba ta nemi waje ta zauna daga bakin gadon tare da janyo wayarta, dubawa tayi taga wa ya k'irata, ganin Affan ne ya sata ajiyan Zuciya, cikin kakkausar murya yace mata "ba magana nake yi miki ba, waye zai tattara miki kayan", zumb'uro bakinta tayi ta juya tana gyara zamanta kan gadon tace "Ai ba ni na zubar ba, suna zamansu ta shigo ta watsar, a k'irata ta gyara mana", da mamaki ya ke kallon yadda take mishi magana, matsowa yayi gaban gadon, da sauri ta shige cikin bargon tana cewa "nikam in ka tab'ani zan faďawa Ammah", ce mata yayi "tashi ki tattare kayanki", ba musu ta yaye bargon ta taso ta shiga kwashe kayan, juyawa yayi zai fita daga ďakin, har yaje bakin k'ofa ya juyo yace "kin nemi abinda zaki cin ko kuma baki gama jan maganan ba", ganin batace mishi komai ba ya fita daga ďakin ya barta anan





Tana zaune ďakin har k'arfe 8 ďin dare, ga yunwa da ya addabeta, tsoron fita takeyi dan batason ko sake kallon Ajiddeh tayi, ta rasa mey zatayi kuďin wayarta ma ya k'are da ta k'ira ko su Aunty taji daďi, Affan ďinma da ya k'ira ďazu yaki k'ira har yanxu, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala ta tada sallah isha, sai da ta idar ta gama addu'anta tasha kuka ta tashi ta hau gado ta kwanta bayan ta kashe wutan, ta gwammace ta kwanta da yunwa da ta fito su haďu da Ajiddeh, jin an murďa k'ofan ďakin yasa ta k'ara tsorata, a hankali ta sauk'o daga kan gadon zata shige toilet taga haske ya gauraye duka ďakin, tsayawa tayi a tsakiyan ďakin ta kasa motsi, k'arasowa yayi cikin ďakin ya ajiye mata daya ledan dake hannunshi yace "in kin gama tsayuwan naki ga abinci ki ďauka kici, you get ready gobe by 11 zan kaiki school and mind you kina rufe k'ofar ďakinki da makulli", wani irin ajiyar zuciya ta sauk'e jin shine, bata juyo ba har ya gama maganan da zaiyi sai ji tayi an juyo da ita, "kina jina ina magana kika min shiru, na fara wasa da ke koh", a hankali tace "Ai naji", saketa yayi ya juya ya fita daga ďakin tare da kashe mata wuta. Dakin Ajiddeh ya nufa rike da wani ledan ya murda kofar ya shiga, xaune ya sameta can karshen gadonta idon nn nata ya kumbura tsabar kuka, ya ajiye ledan hannunsa tare da sauke ajiyar xuciya ya nufeta, tana ganin hka ta mike da sauri xata bar wajen yyi hanxarin rikota tare da hade ta da jikinsa, ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa tace " let me be Aliyu, ka kyaleni, 1st thing tomorrow morning am leaving yhur goddam house, with or without my divorce prove, bna auren kuma, ae ba kai kadai bne namiji a duniya, sae ka xauna da 'yar uwar taka....." Ya runtse ido yace "Stop this Jiddah, yhu pushed me into behaving the way I did, meyasa baki saurarata ne wae, na gaya maki Batuul is only here for sometime, karatu ta xo yi tana gamawa xata koma Nigeria, I love yhu Jiddah bana son duk abinda xae bata maki rai, had it been we are not this close da iyayen Batuul da baxan yrda da xaman ta gu na ba coz it's also a burden to me, plss nd plss Ajiddeh kiyi hkuri ki bar ta tayi karatun ta, her being here is nt for ever, if yhu love me do me this one favour pls babe," tsuke fuska tayi ta kauda kai, ya marairaice yace "Plss babe!" Kuka ta fashe da tace "Shine xaka mareni Aliyu" ya kuma rungumeta yace "Ohh! Am srry babe sharrin shaidan ne plss, idan kuma baki hakura ba ki rama" shiru tayi bata ce komae ba, kissing wuyanta ya shiga yi a hnkli yace "Say something mana babe" lumshe ido tayi don kiss din Aliyu na rikitata, cikin sarkewar murya tace "Naji" bae daina abinda yake mata ba yace "kin amince ta xauna gidan ki har ta gama karatun?" Runtse ido tayi tace "Yeaa!" Yace "Promise!" Da kyar tace "I do love" Kiss din bakinta ya shiga yi passionately tana mayar masa da martani, kan kace me sae ga su kan gado.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝

47

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Yana fita Batuul ta sauk'e ajiyar zuciya ta dawo kan gadon ta zauna, wayarta ta ďauka ta haska ledan da ya ajiye mata taga tambarin Mc donalds a jiki, ďan tsaki taja dan bata cika son abincin Mc donalds ba, amma tunda yunwa takeji babu yadda ta iya haka zataci, janyo ledar tayi ta shiga buďewa, kwalin chips ne a ciki sai chicken wings da dip in sauce, sai wani cup da aka sa strawberry shake da ruwa da pine apple drink, kaďan taci chips ďin, shake ďin kawai tasha da ďan yawa ta tashi ta ajiye sauran da bataci ba kan fridge, toilet ta koma tayi brush ta fito ta kwanta, tafi awa a kwance amma bacci ya k'auracewa idonta, hawaye ne ya fara zirara a idonta, she have never been this lonely gaba ďaya rayuwanta, dukda ba mai son surutu bace tafi son zama ita kaďai amma na yau ya dameta, ko ba komai a gida tana jin motsin y'an uwanta, amma yau hakan ma ya gagareta, tunanin gidane ya sata fashewa da kuka, wayanta ta janyo tana ganin hotunansu da shirmen da sukeyi, tanayi tana kuka wani kuma tayi dariya, tana nan zaune har k'arfe uku, yadda taga rana haka taga dare, gara ma da rana ta ďan samu ta rintsa, amma yanxu baccin ma ya k'aurace mata, tashi tayi taje tayo alwala, sai da tayi nafilfili tukunna tayi karatun Qur'ani a wayanta, tana nan zaune kan abin Sallah har asuba, tana idar da sllh taji wani irin bacci na fizgarta, nan kan abin Sallah ta gyara tayi kwanciyarta, tana kwanciya bacci ya kwasheta, cikin baccinta kamar a mafarki taji k'aran buďe k'ofarta, a ďan tsorace ta tashi ta zuba mishi lumsassun idanunta , k'arsowa yayi cikin ďakin yana binta da kallo, sai da ya shigo tsakiyar ďakin ya tsaya yace "wane irin bacci kikeyi anata knocking baki buďe ba", juyawa tayi ta duba inda ta ajiye makullin ďakin taga yana nan, k'ofan ta sake kallo taga shima

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

11 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment