Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake idonta tace "yawwa Yaa Abu, gidanmu babu daďi da baka nan, gaba ďaya abinda yayi mata da taje wajenshi last month ya rik'a tunawa, sae yaji bai kyauta ba, duk rashin shirin su da Farida amma cikin k'annenshi yafi sonta, haka itama tafi sonshi, masifanshi ne kawai bataso, juyawa tayi tace "bari in kira Ammah ya Abuu tana daki" k'asa cewa komae yyi sae bin ta da kallo da yyi, dai dai nn Ammah ta shiga sakkowa daga stairs.
💖💝BATUUL 💖💝






27






By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





K'arfe biyar suka sauk'o k'asa ita da Farida zatayi wa Ammah sallama ta wuce , a kitchen suka tarar da Ammah ita da wasu y'an aiki tana masu magana, ganin Batuul da shirin tafiya tace "Bitti ba dai tafiya bako, ko Baa Alai din yazo ne, in baizoba ki bari anjima ko Sadiq ne ya mayarda dake", murmushi Batuul tayi tare tareda da girgiza kai tace "Ammah da kaina nazo, kuma Aunty tace in dena zama a waje har six, shine nakeso in koma gida kamin shida " tace "toh shikenan yayi kyau bitti, yanxu driving din yayi kyau sosai ko" tace "Ehhh Ammah muna trying", tace yayi kyau toh, Allah ya taimaka,muje parlour bari in hau sama in dawo " haks suka koma daga parlour suna jiran Ammah , suna zaune ta sauk'o rike da Babban farin leda a hannun ta, a tare suka mik'e suka isketa, Batuul ta mik'awa ledan tace "gashi bitti, useki kinji, nagode sosai, ga wannan kinji nakine", gaba ďaya sai taji wani irin da yadda Ammah ke mata magana, hawayene ya taru a idonta, kamar tayi laifi haka ta rik'a ji', maza tayi ta maida hawayen dake shirin zubo mata ta karb'i ledan daga hannun Ammah, jiki a sanyaye tace "nagode Ammah" , "Babu komai Bitti, ki rik'a zuwa akai akai kinji, ki gaida Aunty in kin koma da sauran yaran kinji" kasa motsawa tayi daga wajen har sai da taga Ammah ta haura bene tukunna ta juya a sanyaye tayi waje dama Farida ta dade da fita, a cikin mota ta tarar da Farida zaune ta k'ure wak'ar Ed sheeran ta shape of you a motar tana ta rawa, sau uku tana k'iran sunanta bata ji ba, har sai da ta zauna tukunna tace "Dadin abin ke da Affan ďin duk halinku ďaya da ya wahala sosai " juya ido tayi tace "ai inma ba ďaya ba haka zai hak'ura dani, babu yadda ya iya" tana ďaga gira ta k'arashe maganan, Sai da Batuul ta tada mota tukunna tace "Alhamdulillahi ma da halin naku ya zamo ďaya", dariya Farida tasa ta fita a motan tace 'toh ni dai ban shiga school this week , sai next week, Yauwa I forgot to tell you, Guess? Ta tambayi Batuul tareda daga mata gira ďaya, "kinsan I always get it wrong when I guess, so just tell me, time is going" Farida tace "toh naji, Mrs, Yaa Massa is getting married, ďazu Ammah ke faďamin wai da na tafi, y'ar Sultan ďin Sokoto zai aura wai sunanta Rahama" sai da ta gama Batuul tace "Allah sarki Yaa Massa, ashe......" , bata gama faďan abinda zatace ba Farida ta katse ta "wani irin Allah sarki, ke da kika k'ishi kememe kice baki sonshi shine harda wani tausayinshi, shima ďin nei dai ya barki , ai da nice shi Allah straight away Baba zanje in samu, sai dai kawai kiji ance an ďaura miki aure, wai shi tunda baki sonshi zai hak'ura da azo ayi abinda za azo ana magana daga baya , ni haushi ma yake bani , he was very lenient on you ke kuma kikayi ta gwara shi ,muna nan dai muna jiran Jin wanda zaki aura, Kai Allah yasa ma Baba ya badake Sadaka tunda ke kowa bai yi miki ba" Dariya maganan ya bawa Batuul tace " toh muguwa haba dai sadaka, that is not happening , not with me, ni kinga tafiya zanyi before Aunty ta faramin waya" , dariya Farida ma tasa tace "zaki sanine bari mu gaji dake Kiga ikon Allah " Sai da tayi reverse tukunna ta cewa Farida "Dan Allah turomin number shi Yaa Massa inyi congratulating ďinshi dan tun lokacin da yake ta damuna nayi deleting sai kuma number shi ta Germany shi kuma bazai yi Amfani ba", juyawa Farida tayi tana komawa ciki tace "fadi gaskiya dai Dan yanxu yana da matarshi , Dariya sukayi a tare kowannensu na dariya Batuul tayi sallama da Farida ta koma gida.






Daidai ana k'iran magrib ta isa, A cikin gida da taje parking taga kamar motan ďazun nan ne pake, sanin babu yadda za ayi yazo gidansu kawai ta tab'e baki ta shige cikin gida, Aunty na alwala Batuul ta shigo da Sallama tace "Aunty na dawo ", Aunty tayi mata sannu da zuwa, ta juya zata koma ďakinta Aunty ta tsayar da ita ta hanyan cewa "in kin idar da Sallah kinada bako , ji tayi k'irjinta ya bada sauti Dam! Ita?, bako kuma? , toh shi waye ?, ita dai babu wanda yace mata zaizo wajen ta ko a y'an ajinsu , maza maza hankalinta ya tuna da motar dan ta gani pake , toh in shine bakon ni ina na sanshi ta ďan ja siririn tsaki, da sauri tace "Aunty ba wajena yazo ba, ni ban sanshi ba, "matsar min daga k'ofan toilet in wuce ni, waje na yazo tunda nice Batuul " marairaicewa tayi tana girgiza kai tace "Aunty dagaske fa ni ban sanshi ba ", bayan Aunty ta saka hijab zata tada Sallah tace mata "toh naji baki sanshi ba, wuce kije kiyi Sallah", jiki a sanyaye ta fita tayi ďakinta, tana tafiya tana ta sak'e sak'e a ranta "toh shi wannan mutumin what does he want with from me, ni ban sanshi bama gaba ďaya inba da na ganshi ba ďazu a traffic, am not even sure ko shi ďin ne bama" Alwala tayi ta tada Sallah, tana idarwa ta tub'e kayan jikinta ta shiga wanka, wani dogon riga mara nauyi ta kuma maidawa mai hula purple, ta ďan fesa turarenta mai sanyin k'anshi, kamin ta sauk'o Mahir ya shigo yace "Yaa Batuul Mama tace kizo", K'aramin gyale ta yafa bak'i tace "muje toh " tare suka isa ďakin Aunty dashi , da sallama ta shiga tace "Na'am Aunty" , ďagowa tayi ta dubeta tace "kije Guest room, bak'on naki na can na faďawa su Janet su kai mishi drinks kuma bana son gardama" tsayawa tayi bayan Aunty ta gama ta kasa tafiya, dubanta ta sakeyi tace "baza ki wuce ba, mutum na jiranki tun ďazu " kamar mai shirin kuka tace "Aunty Allah ban sanshi ba, maybe ma mistake ne bama ni yake nema ba", Hararan da Aunty ta sakar mata ne ya sata yin shiru ta juya zata tafi, tafi minti uku tsaye bakin k'ofan ďakin ta kasa shiga daga k'arshe dai ta ďaga labulen tare da sallama tasa kai ciki, bata ďago kai ko sau ďaya taga mutumin dake zaune ba, kujeran dake nesa dashi taje ta zauna tareda da sadda kanta k'asa, shiru ďakin yayi babu wanda yayi magana, tunda ta shigo ya k'ura mata ido yake kallonta, ita bata ma San yanayi ba, ji tayi ya k'ira sunanta daga inda yake zaune "Batuul ", bata amsa ba kuma bata ďago ba sai ma mamakin da take na yaushe yasan sunanta, Sai da ya k'ira a karo na biyu tukunna ta amsa ba tare da ta kalleshin ba, murmushi ta bashi ta k'ara burgeshi dan komai na Batuul na burgeshi, from d very first time he set his eyes on her , cikin nutsuwa ya fara mata magana "Well it seems you are not ready to respond, okay then ni....." , ďagowa tayi ta kalleshi , mutumin nan ne na ďazu a traffic kuwa "Hasbunallahu Wa ni'imal wakil ", dama haka yake, k'yak'yawa ne sosai ba kaďan ba , kuma fari ne sosai. .....", katse mata tunani yayi ta hanyan ci gaba da maganan shi " Ni sunana Abdallah , I know baki sanni ba but though may be you have seen me once, that is ďazu kenan if you could remember, I can't deny the fact that am in love with you, shiyasa I did all possible things to get to you today, Am praying and hoping that babu wanda ya rigani, ita gaba ďaya mutumin nan ya sata Jin wani iri , da k'yar ta samu ta ďago tace mishi "okay i will think about it " ta mik'e, gabanta yazo ya tsaya yace "toh tsaya mana, kamar wacce ake Kora, in kika tafi a ina zaki sameni in kinyi tunanin, kinga yanxu ki bani number ki, then anjima sai we will talk Dan naga you are not comfortable " Da sauri ta kaďa mishi kanta har sai da ta saka shi yin murmushi, a lokacin ta karanto mishi ta juya ta tafi, da ido ya bita a ranshi yana faďin "Alhamdulillahi yayi mata, yau zai faďawa Mummy wannan great News ďin dai ta daďe tana jira" , Murna fal ranshi shima ya fita daga ďakin






Ranta b'ace ta shigo cikin gida, ignoring kowa tayi zata haura sama Aunty tace "zo nan Batuul" , dawowa tayi ta zauna daga gefe kanta a k'asa, "kikace baki sanshi ba, ya akayi yasan sunanki, har parlour ya shigo ya sameni yace min Batuul yake nema " , "Aunty nima ban san ya akayi yasan sunana ba , ni ban sanshi ba " ido Aunty ta k'ura mata da taga taqi magana tace mata "tashi kije" ranta gaba ďaya a dagule, ta rasa mey ya hanata cewa mutumin bata sonshi, ko dan ta ganshi matured ne not like the other guys da suke binta, alwala sallah Isha tayi ta tada Sallah, tana idarwa ta kwanta, tunanin abubuwan da suka faru a yau ta rik'a yi, abinda ke damun Ammah ne ya dawo mata, mesa Yaa Abu zaiyi haka, shi ko tsoron hakkinsu baya ji gashi har yasa Ammah a damuwa matar da take very jovial and authoritative ta zama very silent just because of Abu, tsaki taja tareda juyawa ďayan gefenta, dama can mugu ne shi ita ta dade da sanin haka, haka taci gaba da tunane tunanenta har bacci ya ďauketa, cikin bacci taji kamar wayarta na ringing , tashi tayi ta zauna ta duba screen ďin wayar, sai sabuwar number ta gani, har ya katse bata ďauka ba sai da aka sake k'iranta , ďagawa tayi bayan tare da tace komai ba, daga ďaya b'angaren taji ance " salamu alaiki Noor " cire wayan tayi daga kunnenta ta sakr duba number, cikin muryan bacci tace "ba Noor bace, it's a wrong number " zata ajiye wayan taji ya sake cewa "toh ai ke ďin Haske ce shiyasa na saka miki suna Noor " , cikin kosawa da surutun da yake mata tace "who are you " , murmushi yayi daga cikin wayan har tana jiyowa yace "It's Abdallah, tunda kin kasa ganewa let me tell you, well as it is, nakasa bacci because of tunanin ki na kasa bacci " ita dai bata ce komai ba sai shiru da tayi tana sauraronshi, "baza kiyi min magana inji muryan ki mai dadi ba Noor " a hankali tace "bacci nakeji yanxu bazan iya doguwar magana ba, am sorry you should call me tomorrow " , murmushi ya sakeyi yace "Alright Noor, it's okay kiyi bacci but gobe zan kiraki kuma zakiyi min magana but for now you should go to bed , okay? " a hankali ta amsa mishi da "toh" , yace mata "good night sleep tight" ya katse wayan, mamaki ta rik'a yi mesa shi wannan mutumin baya bata haushi kamar sauran mazan dake cewa suna sonta, ganin babu mai bata amsa yasa ta kwanta ta koma bacci






B.A flight ne ya iso Nigeria K'arfe 6 na yamma, cikin mutanen dake fito fitowa daga ciki harda Abutturab da matarsa Ajiddeh, tafiya suke cike da nutsuwa, sunyi kyau sosai, kanta kwance yake kafaďanshi gashin nan da yasha gyara an barshi iska sai kaďawa yake , wani mutum ne yazo cikin hanzari ya karb'i Jakar dake hannun Abutturab yace "Sir this way please, the car is parked down there" bayan mutumin nan suka bi har wajen motar da zata kaisu, bayan ya buďe musu sun shiga sun zauna ne Ajiddeh tace "Babe, bana so muje gidanmu saboda y'an sa ido, kar aje ana cewa mun shigo gari, we should lodge in a hotel, kuma ma tunda babu wanda yasan muna hanya sai y'an gidanmu Mum da Yaa Zee kaga it will take time before a gyaggyara kuma ma ai ba daďewa zamuyi ba ana gama bikin nan zamu koma, so we should stay in the Hotel " gefen fuskanta ya shafa yace " alright then, hakan ma zaifi" Hotel ďin dai suke so su sauk'a suka faďawa mai tukin motar, ba b'ata lokaci ya juya yayi hanyan Hotel ďin da aka faďa mishi , suna isa bayan sun kama ďaki tayi ordering abinci taci tayi wanka tasa aka turo mata driver daga gidansu, Ce mishi tayi ya tashi su tafi yace mata "No he is exhausted, bazai iya zuwa ba , amma zaije dinner " ganin kaman ranta ya fara b'aci yayi maza ya taso ya rungumeta tare da mata peck yace "baby na gaji ne yanxu; I can't come but anjima zanzo dinner da za ayi I promise, kuma zan baki what you asked for " sai a sannan ta sake fuska tace "toh zaka K'aramin akan na da" yace "yeah , everything for you " juyawa tayi ta fita daga ďakin, da ido ya bita a ranshi yasan something is not right but ya kasa ganewa ko menene, ya rasa gane mesa baya iya yiwa Ajiddeh faďa akan abubuwan da takeyi , yanxu ko kayan jikinta ma bai kamata tana matar aure ta rik'a fita babu ďan kwali ba amma bazai iya ce mata komai ba, kan gadon ya koma ya zauna tareda da dare kanshi Dan mugun Sara mishi ya fara.
💖💝BATUUL 💖💝

26

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

A YEAR AFTER

K'aran Alarm ne ya cika dakin gaba ďaya, kwance take tana bacci har sai da K'aran ya kusa katsewa tukunna taja tsaki, ta Janyo wayar da k'afarta, ko kallon fuskar wayar bata yi ba ta saka hannu ta katse karan tukunna ta maida wayan, duk abin nan da tayi bata bude ido ba, sai da ta mike ta zauna daga bakin gadon tukunna ta buďe idonta a hankali wayar ta sake ďauka taga 7:09, tafi minti biyar a zaune daga bisani ta mik'e tana fadin "mutum da kanshi zai saka abinda zai dameshi", gashinta ta tattare ta haďe su waje ďaya, ta isa inda bathrobe dinta ke rataye ta cire kayan baccin dake jikinta ta saka bathrobe din ta shige toilet, sai da tayi brush tukunna tayi wanka, gaban mirror ta zauna bayan ta fito daga wanka ta shafe duk jikinta da mai,ta fesa body spray tukunna ta je saka kaya, closet dinta ta buďe ta ciro wata coffee abaya mai Babban hannu da adon milk daga jiki, sai da ta saka kayanta tukunna tayi inda jakunkunanta ke rataye ta jawo d'aya daga ciki ta zuba tarkacenta a ciki sannan ta yafa gyalen abayar a kanta sannan taje ta saka slippers din Laura Ahman shima milk, har ta fita ta tuna da key ď in mota da wayarta ta koma cikin hanzari ta ďauko lokacin 8am daidai, k'asa ta sauk'o babu kowa a gidan shiru, ta tasan kowa ya tafi makaranta, Aunty da Baba kuma mayb suna bacci, ta nufi dinning area, sai da ta bubbuďe duk kwanun dake dinning din tukunna ta ďauki soviet ta ďauki sandwich ďaya a cikin wani transparent bowl, ta ďauki disposable cup ta tsiyayi fresh orange juice a juice dispenser, har ta zauna zata fara ci taga time zai k'ure maza ta mik'e ta yi hanyan waje , sai da ta taje dab bakin k'ofa zata fita Taji muryan Aunty a zaune a parlour tana ce mata "sannu Batuul , kin kyauta , cin abinci a waje ko ? Nasha fada miki banaso babu kyau shine kika wani ďauki sandwich a paper kamar wacce ta rok'o toh yayi miki daidai", sai da Aunty ta gama maganan da takeyi tukunna ta juyo da murmushi a fuskanta ta dubi Aunty tana k'arasowa cikin parlour ta ce "Aunty Nda wattu, nifa banma San kin tashi ba, Ina kwana" ta sake maimaitawa bayan ta zauna kusa da Aunty, Da lafiya Aunty ta amsa mata sannan tace "Batuul ba kya Jin magana ko" Da sauri Batuul ta girgiza kai tace "Aunty ba haka bane fa, har na zauna zanci naga time ya kusa k'urewa zanyi latti shinefa zanje mota dashi , bama a layi zanci ba fa" ta gama maganan tana sadda kanta k'asa dan tasan Aunty ta hanata, Sai da Aunty ta dubi hannunta taga ma abinda ta ďauka din tukunna tace "mota ba layi bane ko ? Ai cikin gidane, kuma waye ya hanaki tashi da wuri har kika kusa lattin ke da ba sllh kike ba bare ace baccin asuba kika koma kika makara, kin wani ďauko Sandwich ďaya kamar wacce ta rok'o" ganin faďan baya k'arewa kawai ta fara cin Sandwich ď in tana tunkud'awa, haka ta gama ci tana kurb'an juice ď in har ta gama, mik'e wa tayi zataje ta ajiye sauran juice da ta rage, dama tunda ta fara cin abincin Aunty bata kalleta ba sai da ta gama ta mike tukunna ta dubeta tace "sauran Juice din kuma fa? wa kika ragewa" marairaicewa tayi tare da da juyowa tace "Aunty na koshine zanje in ajiye", "Da kinsan bazaki iya shanyewa ba kika ďebo dayawa, dawo ki zauna ki shanyewa shi", haka ta dawo ta zauna ta shanye a ranta tana addu'a Allah yasa bata yi latti ba, bayan ta gama shanyewa a dustbin ta jefa cup din da tissue ta dawo tace "Aunty zan tafi" ďagowa tayi ta kalli Batuul tace "A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a" ta amsa da Amin ta wuce, har taje bakin k'ofa Aunty ta sake k'iranta "Batuul", juyowa tayi tare da cewa "Na'am Aunty", "What time zaki gama lectures" Aunty ta tambayeta, "10:30 zan gama, class ďaya dani yau, by 11am zan dawo", "okay in kin gama inaso kije ki gaida Ammah, jiya munyi waya tana tambayana ke, so ki wuce daga can sai ki dawo da yamma" toh kawai tace ta fita, Parking area ta nufa taga ďaya daga cikin masu aikin gidan na goge motar, farar BMW, k'arasawa tayi wajen motan tana laluben makulli daga cikin jakan, ďagowa tayi bayan ta samu makullin ta amsa gaisuwan da mai aikin ke mata "Yauwa Friday sannu da aiki" ta danna button din motar, kamar jira yake dama tana dannawa ya buďe mata, sai da ta shiga ta zauna tukunna ta ciro ďari biyar ta mik'a mika mishi, murna ya dinga yi yana mata godiya, murmushi kawai tayi ta jawo motar ta ta tafi, a bakin gate ma sai da ta mik'awa masu gadin ďari biyar biyar tukunna ta fita daga gidan, a wajen wani traffic ta tsaya tana jira a basu hannu su wuce, wani super tint AMG ce ta tsaya daga gefenta nata, bata kalli motar ba saima wayarta da ta ďauko daga ďayan kujeran zata duba time, jiya tayi kamar ana kallon ta ta gefe, a hankali ta juya ta dubi gefenta, k'irjinta ne taji yayi dam , wani mugun faďuwa gabanta yayi, sosai ta tsorata da mutumin dake cikin motar dan wani irin kallo ya tsaya yana yi mata, sunan Allah ta shiga jerowa tare da fatan traffic ď in ya basu daman wucewa ta wuce, bata sake k'ok'arin kallon gefen ba, a haka traffic ď in yayi signalling ďinsu da su wuce, a guje ta figi motar kamar mai shirin tashi, Sai da tayi nisa sosai tukunna ta ďago ta rear mirror ta duba ko mutumin na binta a baya amma bata ga alaman motanshi ba, wani ajiyan zuciya tayi tare da faďin Alhamdulillah a fili, 8:34 daidai ta isa school, dpt dinsu taje tayi parking sannan ta fito tayi hanyan class ďinsu, a tare da lecturer ďinsu dai dai suka iso, ta k'ofan baya ta shiga ta samu waje ta zauna , nutsuwa kowa yayi a ajin har malaminsu ya fara lecture, 10:30 dai dai ya gama ya fita suma suka mik'e suka fito, sai da ta ďan gaggaisa da y'an ajinsu da ta sani tukunna tayi hanyan motan ta , bata tsaya yin komai ba ta shige ta wuce abinta, hanyan gidansu Farida tabi, a hanya tana driving tana tambayana k'iran number Farida tasan duk yadda akayi dai ta tashi daga bacci yanzu dan can gari yanxu 2 biyu tayi, sau biyu tana k'ira bata ďauka ba, cikin minti 18 ta isa, har cikin gida ta shiga tayi parking , da sallama ta shiga parlour babu kowa a ciki sai kanshi da yake tashi, hanyan stairs tabi zata hau sama wata mai aiki ta fito daga kitchen ta gaisheta sannan ta tambayeta Ammah na gida, Ce mata tayi ehh tana sama, godiya tayi mata ta k'arasa hawa Saman, a hankali ta buďe k'ofan ďakin Ammah tare da sallama, su biyu ta tarar a zaune, da gudu Farida ta taso ta rungume Batuul tana ce mata "dullop head I missed you, you didn't tell me zakizo" murmushi Batuul tayi tace "ai yanzun ma ba wajenki nazo ba" bata rai Farida tayi tace "Really? well am not hurt, nasan zaki dawo ki nemenin nima" ido Batuul ta juya tare da mata gwalo tace "not in this life" Ammah na daga zaune tayi murmushi ta girgiza kai, gaban Ammah Batuul taje ta zauna tace mata "Nda dubdo Ammah" , "Lafiya kalau Bitti, ya gida ya Aunty, ya kuma karatu, ana dai yi lafiya ko'? kai ta gyaďa mata tare da cewa "Alhamdulillah Ammah , duk lafiya " dubanta Ammah tayi tace "kin buya Bitti, sam ba a ganinki ko kuma makaranta ne? " Da sauri ta sadda kanta k'asa dan tasan bata kyauta ba, rabonta da gidan ta kai wata biyar, kuma kullum suna haďuwa da Farida a school, jiki a sanyaye ta girgiza kai tace " Ammah, zan rika zuwa yanxu" Ammah tace "toh yayi kyau, ai Faridan ma ďazu da asuba suka iso, ni yanxu zan shiga in kwanta dan yau ban samu nayi bacci ba tunda Farida ta iso ta isheni da surutu" ta faďa tare da mik'e wa zata kwanta , da ido Batuul ta bita ganin yadda maganan Ammah yayi sanyi gashi har ta ďan rame, ganin zata juyo ne ya sata tayi maza ta ďauke idonta daga duban ta, Ce musu ta sakeyi " Farida in kun sauk'a ki turomin Yaa Bawa" tare suka amsa da toh dukkansu biyun, tana shigewa Batuul ta Janyo hannun Farida tana tambayanta "Ke da muka turaki Uk kiyi wata ďaya shine ko sati ďaya baki cika ba kika dawo " Suna fita suka haďu da Yaa Bawa ta tattaro kaya zatayi k'asa suka ce mata Ammah na nemanta sannan suka shige ďakin Farida "Batuul ce

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

11 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment