Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa'an wasanki, I mean yaushe na fara miki wasa da zaki min kara a kai ki gudu, kuma kukan da kikeyi sai ki faďa min na meye, wato ke har yanxu baza ki canja ba ko?", shiru tayi tana saurarenshi har tana jiyo heartbeat ďinshi, sai da taji yayi shiru tukunna ba tareda da ta ďago kanta ba ta fixge jikinta daga rik'on da yayi mata ta shige palo da sauri, inda tayi yabi da ido, da kamar zai koma sai kuma ya fasa ya tura k'ofan palon, dai dai nan Aunty ta fito daga kitchen, da mamaki a fuskanta ta buďe baki tace "Lalala, wa nake gani kamar Abutturab", murmushi yayi tareda sunkuyar da kai k'asa ya k'arasa shigowa cikin palon,sai da ya zauna tukunna ya gaisheta, ta amsa da fara'a ta shigo falon ta xauna tana tambayarsa yaushe ya shigo gari, hira sosai sukayi da Aunty , Janet Aunty ta k'ira tace ta k'ira mata Batuul, dawowa tayi tace tana zuwa, sai da ta canja kaya ta saka straight skirt baqi da peplum blouse peach, ta sauk'o, kanta da ta taje take tattarewa ta sauk'o ba tare da sanin yana gidan ba, turus ta tsaya ganin mutum zaune yana hira da Aunty a gidansu, ita a zatonta ya wuce tun ďazu, ta hade rae a hankali ta karaso wajen Aunty tace "Na'am Aunty, Janet tace min kina k'irana", cewa Aunty tayi "Ehhh, kitchen nakeso ki shiga kiyi Assisting su Esther ku k'arasa mana abinci, mik'ewa tayi daga hannun kujeran da take tayi hanyan kitchen, ya bi ta da kallo, Aunty ce tace mata "Batuul ya haka, bakya ganin Yayanki ne zaune baki gaidashi ba" juyowa tayi tace "Aunty mun gaisa, shi ya dawo dani gida ma fa", ta faďa ba tareda ta bari sun haďa ido ba ta juya ta ci gaba da tafiyanta, har ta shige kitchen bae daina kallonta ba, a gidan ya zauna har akayi sallahn magriba sukaje suka dawo, suna ta hira shida k'annenta dan yana da son yara, Batuul kam duk aikin da takeyi ranta a b'ace yake , kwata kwata she is not comfortable don da ta fito kitchen sae sun hada ido, dama ga wannan masifan heartbeat ďin nata da ya fara dawowa bayan tsawon lokaci, gaba ďaya ya sata ta sake takura, k'ara b'ata rai tayi ta fito tana jera abincin da suka girka a dinning, suna haďa ido ya sakar mata harara, ďauke kanta tayi bata sake kallon inda yake ba, tana gamawa ta haura sama bata sake sauk'owa ba har ya bar gidan bayan Aunty ta tilasta shi cin abinci har tana ce mishi ko dai sabawa da yayi ne da girkin Ajiddeh yasa baya jin daďin wani abincin sai nata, murumushi yayi a ranshi dan shi baisan ma ya taste đin abincin Ajiddeh yake ba dan ba iyawa tayi ba, haka ya hak'ura ya zauna yaci dan babu yadda ya iya, bazai iya yiwa Aunty musu ba

Bayan anyi sallahn Isha Abui ya shigo gida, dama Ammah duk ta matsu ya dawo ta faďa mishi abinda ke ranta, bayan ya dawo saida ya sauk'o palon k'asa tukunna Ammah ta kawo mishi abincinshi har palon, sai da tayi serving ďinshi yana ci tukunna ta fara magana, shima dama ya lura da magana a bakinta, cewa tayi "Abul Aliyu", ďagowa yayi bayan ya cinye spoon ďin abinci da ya saka a bakinshi yace "Na'am Umm Aliyu", ya tsaya yana kallonta yana jiran yaji mey zatace, sai da tyi ajiyan zuciya tukunna tace "dama wani shawara nayi đazu akan yaran nan namu, kuma ina ganin its beneficial to both families, mey zai hana mu nemawa Abutturab auren yarinyan nan Batuul, yarinyar nutsatsiyace sosai kuma gidan da ta fito nan aka fara yiwa Abutturab tarbiya, a gidan ya fara koyon komai na rayuwanshi, kuma ko babu komai in suna tare a can , toh nasan lallai zata na watching moves ďinshi dan tana da lura da sanin ya kamata, xa kuma tana nuna masa what's right nd wrong, gata kuma da hankali, kaga inma shi ya tafi yaqi dawowa toh ita ba yadda zatayi tayi ta zama babu ganin gida dole sai ta dawo, toh ,kaga a haka zai biyota su dawo ko dan kunyanmu", tunda ta fara magana ya maida spoon ďin abincin cikin plate ďin, murmushi ďauke a fuskanshi yace "Masha Allah, wannan ai abin farin ciki ne sosai kuma nima zanfi kowa murnan ganin wannan al'amari ya faru, kamar Farida haka nake jin Batuul a raina, gobe in Allah ya kaimu zanje in tuntub'i mahaifinta akan zancen muji in babu matsala ko kuma da akwai wanda takeso ", Ammah tace"Abul Aliyu in sun yadda ma kawai a ďaura auren su tafi in yaso daga baya ayi biki , sai taci gaba da karatunta a can,", yace "okay duk zanyi trying inji, Allah dai ya taimaka" haka dai sukayi ta zancen haďa Abutturab da Batuul aure har Ammah na cewa ai da tun farko ma sunyi tunanin nan da duk yanxu basa cikin matsala

Washe gari ranan juma'a bayan an idar da Sallah a masallaci Abui ya haďu da Baba, bayan sun gaisa Baba yace "Alhaji mu dai bama tab'a haďuwa dan kanmu sai dai ko masallaci ko kuma meeting",dariya Abui yayi yace "rayuwan kenan Alhaji, in mukace zamu zauna gida abin bazai yi kyau ba, da shike ma yanxu girma yazo, mun kusa sauk'a mu huta ai", duk su biyun suka sa dariya, Abui ne yacewa Baba " *Alai wa office lan gèrezain, dai fatoro iske kèla kwamnyen* , Alai ana jirana office yanxu, amma anjima zanzo gida, there is this issue i want to discuss with you", da haka sukayi sallama, da yamma wajen k'arfe biyar Abui na tashi daga office yayi gidansu Batuul ko gida bai je ba, lokacin Baba na gida saboda its a short day duk sun tashi aiki da wuri, fitowan Batuul kenan daga backyard đin gidansu, tayi mamakin ganin Abui a gidansu, har k'asa taje ta tsuguna ta gaisheshi sannan ta tashi da taje tayi serving ďinsu drinks da snacks, bayan ta ajiye zata mik'e Abui yake tamabayanta ya makaranta, tace Alhmdllh, nn yayi ta sa mata albarka har sai da taji kunyanshi sosai , bayan ta tafine Abui ya fara magana , sai da ya gama baynin abinda ya kawoshi tukunna Baba ya fa'da'da murmushin fuskarsa yace "Alai nidai b'angarena babu matsala dan babu abinda zaka nema matsawar inada iko akan abun in hanaka, kuma ma ai Abutturab yaron kirki ne sosai, dama dai akwai wani yaro da naga ya fara zuwa wajenta tun wancan watan amma bansan ko sunyi maganan aure ba, kuma tunda ga na gida da aka san halinshi ai yafi da a bawa na waje da ba'a san halinshi ba, dan ma dai naga yaron nada hankali amma zamu bashi hak'uri, yanzu dai ni zanje inyi shawara da y'an uwana da manya na sai mu san abin yi dan Yayya ma ta matsa tafi kowa son a aurar da Batuul sai gashi Allah ya taimakeni akai", godiya sosai Abui yayiwa Baba daga nan suka shiga hirar politics da matsalolin dake damun Nigeria.

Batuul na kwance kan gado wajen k'arfe 8 na dare bayan tayi sallah isha, kayan bacci ne jikinta dogon wando da y'ar riga, kan gadon duk ta baje takaddu sai Macbook ďinta daga gefe, chocolate bowl ta janyo ta ďau twix ďaya ta b'are ta jefa a bakinta tukunna taci gaba da duba takaddan, tana ci taji wayanta na ringing, tashi tayi ta ciro wayan daga caji, Recieving tayi tareda komawa kan gadon ta kwanta, kamin tayi magana daga ďaya b'angaren akayi sallama tareda da faďin "Ranki ya daďe Habibty, i cant imagine life without you", murmushi tayi har ana jiyo sautin daga ďaya b'angaren tace "tareda naka, you can live normally mana tunda ai da can ma baka sanni ba and you were living", dariya yasa yace "that was then, amma ai yanzu tunda na sanki, life is gonna be hard without you, promise you wont leave me", ji tayi gaba ďaya ya gama bata tausayi, ita tasan ba sonshi takeba but tana respecting ďinshi sosai, avoiding promise ďin da yace tayi mishi tayi tace "Ya jikin Mummy, ta k'ara samun sauk'i ko?", da sauri ya tareta yace "Ba kinqi zuwa in kaiki wajenta ba, kullum sai ta tambayeni yaushe zan kawo mata kene, har banaso tana tambayana dan bansan mey zance mata ya hanaki zuwa ba", kai ta girgiza kamar yana gabanta tace "No fa ba naqi zuwa bane, we have time , kuma i dont think its right muje gidanku tun yanzu , i will come when its time", tambayanta yayi mey takeyi dan yaga mind đinta is not with him, tace mishi assignment takeyi, da haka ya barta tace they will talk ltr

Bayan Abui ya tafi, Aunty ce ta sauk'o k'asa ta sami Baba zaune yana kallon CNN channel, daga gefenshi ta samu waje ta Zauna tayi mishi sannu da gajiya tareda ajiye. abinda ke hannunta, volume ya rage ya juyo ya dubeta ya faďa mata yadda sukayi da Abui, ita gaba ďaya bata expecting haka, ta k'asa daina kallon mai gidan nata, hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba jin xancen Baba kuma tasan babu yadda za ayi yaqi bawa Abutturab Batuul tunda har gida Babanshi yazo nema mishi aurenta, ajiyan zuciya tayi cike da damuwa tace "Uncle Batuul ďin kuma, shi da yayi aure ko shekara bai wuce ba, ai sai ya bari ko matar tasa in ta haihu ne sai ya fara zancen k'arin aure amma ba daga aure ya bijiro da sabo ba", ta faďa tana jiran jin mey Baba zaice, cewa yayi "indai zai kula dasu duka biyu ai bamu da matsala, kuma ai ba sanin matsalarshi mukayi ba na son k'ara aure, kuma ma dai yaron nan ďanki ne, kinfi kowa sanin halinshi, ya kamata kifi kowa murnan kasancewar wannan al'amari, kinsan ko shekaran jiya kina zaune kina ji sai da Yayya ta k'irani akan Batuul, toh yanxu mafitar addu'an da nayi na samu, nasan Aliyu yaron kirki ne zai kula da Batuul in sha Allah", ido kawai Aunty ta zubawa Baba yana magana hankalinta na dađa tashi, Batuul tayi yarinya da auren mai mata, barema irin su Ajiddeh, cutan Batuul kawai za ayi indai ta zauna a gidan nan a matsayin matar Abutturab, dan tasan yadda familyn Ajiddeh suke akan kishiya, mik'ewa kawai tayi ba tareda ta sake cewa komai ba ta haura sama don bata jin xata amince da wnn batun at all, idonta ya kaďa har ya canja kala.
💖💝BATUUL 💖💝

28

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Tana fita ta wuce gidansu daga hotel din, cike gidan yake da mutane da suka zo biki, wucewa takeyi tana ta daga kai ita a dole matar mai kuďi, matan dake zaune sai gaidata suke wasu kuma suyi gulmarta, ďakin da tasan zata samu Mum straight ta wuce, ba ko sallama ta saka kai cikin ďakin, Mummy na ganinta ta taso cike da murna ta rungumeta tana faďin "Yar albarka baki min waya kince kun iso ba " ta fadi tana K'arewa Ajiddeh kallo ganin yadda ta canja lokaci kaďan, ga wani kyau da ta k'ara dama can Masha Allah, Hannunta ta jawo bayan ta saketa daga rungumar da tayi mata taja hannunta suka shiga bedroom, Junaiba dake zaune ce ta bisu cikin ďakin, a tsakiya suka sa Ajiddeh, Mummy ce ta fara ce mata "Ajiddeh kinga yadda kika canja , lalalala Masha Allah, kin zama matar manya, duk komai yana tafiya yadda muka shirya ko? , Jainaba ce tayi maza ta karb'e maganan da cewa " Mummy ai ko baki tambaya ba gashi kin gani, yarinya zata cuci kanta, ana so a ayi miki abin kirki a taimakeki kina ke mijinki, kefa kina sonshi, toh da mun barki haka da yanxu duk ba haka bane, yanxu faďa mana muji inda matsala mu san yadda zamu b'ullowa matsalar mu magance ta" , tunda suke surutun su bata ce komai ba sai danna waya da take tayi , sai da ta gama ta ďago tana kaďa hannu tace "Mummy ai Aliyu sai abinda nace, tun farkon aurenmu da ya fara min masifa kullum ni k'azama ce, na faye son jiki, bbu abinda na iya, gashi da bak'in halin jaraba sam ba a zama ayi hira dashi , amma tun bayan nayi muku complain ďinnnan da kukace in turo kuďi , everything have been fine since then, kuma sam baya tambayan mutum mey zakayi da kuďi komi yawansu bayarwa yakeyi shiyasa bamu samu matsala ba, maganan da nakeyi muku yanxu haka Mummy tunda mukayi aure sau ďaya yaje gida, waya kam dama babu magana, ai na gaya muku wannan watan sun turo k'anwarshi tazo, itama ďin dai bata daďe ba Nasa ya maidata , wannan zuwan ma da zamuyi ban yadda mun zauna a gidanmu ba saboda Kar ma susan da zuwanmu " "Jainaba ce tace "ai hakan ma yayi daidai da kikayi, toh ya akayi da wancan abinda nace miki na abincin shi ne, wannan na naman, tunda cewa kikayi ba kya girki, ko kinyi bayaci" , dariya tasa tace "Jainaba kenan, ai in yasan wata baisan wata ba, shi yake dafawa kanshi abinci ko kuma ya siyo, toh watarana yakan ajiye na dare da safe yayi warming yaci, ni dama bana bi ta kanshi, kuma dama ba iya dafawa nayi ba, sai dai kullum in rik'a ordering don of recent ya sallami cook din gidan" , Mik'e wa tayi tana dariya tace "Mummy ,Jainaba, ku bari mu dawo daga dinner in mun nutsu zan faďa muku duk yadda ake ciki, ni sam ban maje naga Amarya ba, tunda aka saka ranan nan ya ďaga mun hankali wai sai nayiwa Ufa magana ayi bikin aurenta a gidannan saboda bata sn y'an uwan mijinta su rainata " , Mummy ce tace "ai da gaskiyarta, Ina zata yadda da raini, gara da ta bar gidansu tazo nan ďin ayi komai a gama, ko ba komai itama tana da y'an uwanta masu akwai " Da haka suka fita daga ďakin, Mummy da Jainaba suka tsaya daga falo Ajiddeh taje side ďin da Amarya da k'awayenta suke.

Babu abinda ke tashi a wajen nan sai sautin kiďa, Hall ne mai girma da aka yiwa ado sosai na gani na faďa dan da gani kasan yaci Naira, Tun daga mota Abutturab yake k'iran number Ajiddeh amma bata receiving, fitowa yayi daga cikin motan yayi heading cikin hall, mata ne tare da maza kowa yana displaying talent ďinshi na rawa, Ajiddeh ya hango daga cikin y'an rawa sai kaďa waist takeyi, ranshi ba K'aramin b'aci yayi ba ganinta cikin maza tana rawa ga wasu shegun kaya da ta saka duk bayan ta a buďe, ji yakeyi kamar yaje ya fincikota amma babu hali, waje yaje ya samu ya zauna daga gefe yana jiran lokacin da zata gama, sai da suka gama tik'a rawansu tukunna bayan Dj ya k'are suka bar filin rawar, tana juyowa idonta ya sauk'a kan Abutturab, haďe rai tayi kamar ba ita ke dariya ba yanxu, k'arasowa tayi inda yake zaune ta tsaya mishi a ka k'erere tana ďan karkaďa k'afa, ďagowa yayi ya dubeta tare da cewa mata "Babe har kun gama rawan ne? " wani Harara ta sakar mishi tace "Kai fa ka cika wulak'anci, tun ďazu muyi da kai zaka zo shine sai yanxu ka wani ďebo k'afa kazo, y'an uwana sai tambaya sukeyi ina kake, kowa yazo da mijin shi sai ni kaďai ce babu mijina, ni tun farkon nasan wulakantani kaso yi dama bada son ranka muka zo ba....." katse mata maganan yayi tareda kamo hannunta ya zauna da ita kan kujeran dake kallon nashi, magana ya fara yace "Babe c'mon, tun ďazu fa nake wajen nan ina k'iran wayanki baki ďauka, da na shigo kuma na ganki you guys were busy dancing" , a ranshi yana son yi mata maganan cewa ita matar aurece, bai kamata tana irin wannan shigar ba har tana Cuďanya da maza, amma bazai iya ba, kawar da zancen yayi yaci gaba da cewa "so bana so in dameki shiyasa na bari sai kin gama tukunna sai ki ......" bai k'arasa ba yaga ta warce hannunta daga rik'on da yayi mata ta bishi da harara ta juya daga wajen ta nufi tsakiyar hall ďin Jin an ambaci cewa y'an uwan Amarya suzo ayi hoto da ita, wani irin bak'in ciki yaji a ranshi wai shi Ajiddeh ke yiwa abubuwan nan da takeyi haka "toh meye ke damuna ne? " ya tambayi kanshi, inda tabi shima yabi da ido ya ganta ita da sauran y'an uwanta maza sun sata a tsakiya cameras nata haskasu sai washe baki takeyi yana cikin tunani yaji an da dafashi daga baya, a ďan firgice ya juya yaga ko waye, kanshi ne yaji yayi dammm tare da zaro ido ganin mutumin da yake expecting gani least a wajen, zagayowa yayi ya zauna daga ďayan kujeran murmushi ďauke a fuskanshi yace "Ashe kana gari, Well i can see you are surprised to see me here ko bro? , bai bashi ansan tambayan da yayi mishi ba sai ma jifanshi da yayi da nashi tambayan shima "What brought you here Sadiq? Mey kazo yi?" Shima bai bashi amsa ba sai ce mishi da yayi "Answer me first bro, ni na fara tambayanka kuma your question is irrelevant, yaushe ka shigo Nigeria, ko da shike dama ance mana kana shigowa mune dai bama ganin ka " ďagowa yayi da sauri ya dubi Sadiq Jin abinda Sadiq ďin yake faďi , cikin rashin Jin daďin abinda Sadiq ya faďa mishi yace "ance muku ina zuwa Nigeria? Su waye ke faďa muku cewar ina zuwa" murmushin takaici Sadiq ya saki yace "Allah sarki these doesn't matter now, Ni auren Abokina Muhsin nazo, shine angon, so banma jima da shigowa ba, but tunda na shigo na ganka wani xuciyar ke cemin ba kai bane, I thought ma gizo kake yimin ba kai bane cus I wasn't expecting you " , sai da yayi shiru tukunna Abutturab yace mishi "Ai Amaryar k'anwar Ajiddeh ce, so shine muka zo Dan kusan Ajiddeh ce tayi sponsoring biki saboda mamar yarinyar ai ta rasu" kai Sadiq ya kaďa yace "Ohhh , that's nice then, toh yau ďin zakaje gidane ko kuwa zaka koma ba tare da kaje ka gaida Ammah ba " jikinshi ne yaji ya daďa sanyi Jin an ambaci sunan Ammah, ba tare da ya yadda sun haďa ido da Sadiq ba yace "toh shikenan bari in faďawa Ajiddeh zamuje yanxu, k'ar inje kuma bata sani ba hankalinta ya tashi " , da tausayin ďan uwan shi a ranshi yace "gaskiya hakan ma yayi kyau, kaga kar tazo tana ta nema ai babu daďi" , yace "Ehhh shine yanxu zan k'irata, naga ma she is so busy yau ďinnan" , yaci gaba da dialling ďin number ta, da k'yar aka samu ta ďauki wayan bayan ya k'ira kamar sau bakwai , tana ďauka tace mishi "baby wai meye haka, baka ganin am busy ne ? Kasan fa ni nayi komai na auren nan kuma na daďe ban haďu da y'an uwana ba ai sai ka barni in huta, da ka k'ira kaji ban ďauka ba ae sai ka hak'ura, amma ka ta wani k'irana sai kace ladan a masallachi" , sai da ta gama ya kwantar da murya yace "sorry Babe, something came , zanje wajen su Ammah ne in duba su, ya daďe da na gansu, I will go briefly and come back " , batasan lokacin da ta mik'e daga zaunen da take ba, gumi ne taji gaba ďaya ya fara tsatsaffo mata, Ce mishi "Aliyu ba muyi haka dakai ba, mu da zamu koma gobe mey zakaje yi, toh ni dai bana son zuwanka, kuma baxa kaje ba " , samun kanshi yayi da katse wayarta, har sai da yayi mamakin kanshi shima, mik'e wa yayi ya cewa Sadiq "muje ko? " kallon mamaki yabi Abutturab dashi wai wannan shine yayanshi da yake takawa maza ma birki amma yau shine da kanshi mace ke mishi tsawa har yana ji a waya, ji yayi hawaye na son zubo mishi yayi maza ya maidasu yace "Yaa Abu muje" , ya shige gaba Abutturab na binshi daga baya,

Wani ihu ta saka tare da fashewa da kuka, hankalin su Mummy yayi kanta a tashe, tambayanta suka shiga yi lafiya take ta ihu haka amma tak'i magana, Yaa Zee ce tace mata " a k'ira miki mijin nakine ko wani abin ne ya sami mijinki", wani irin kallo ta Watso mata tace "Da wani abun ne ya same shi ai duk mai sauk'ine akan abinda yake shirin faruwa" taci gaba da kurma ihunta, su Mummy ganin tana Janyo hankalin mutane kansu tayi maza tasa su tafi da ita gida, har suka isa gida tana kuka suko sun sata gaba suna kallonta suna jiran Jin meye ke damunta, sai da tayi shiru tukunna tace " Mummy Aliyu ya tafi gidansu, duk k'ok'arina na kar yaje sai da yaje kuma gashi malamin nan sai da yace indai nayi mishi toh ko kar in yadda ya haďu da ďan gidansu ko ďaya in ba haka ba Babban Al'amarine zai biyo baya, Mummy ni ban san meye Al'amarin ba amma duk yadda akayi ba mai kyau bane, gashi kuma ya tafi, Mummy ya tafi na shiga uku, bige mata baki Mummy tayi tace "akan wannan abin kika ďagawa kanki hankali, mu inane bamu shiga, ai in yasan wata baisan wata ba, ki kwantar da hankalin ki ba gobe zaku koma ba, toh babu abunda zai sameku daga ke har shi ďin " a haka dai suka ci gaba da bata hak'uri da baki har suka samu tayi shiru amma ba Dan hankalinta ya kwanta ba, Dan gaba ďayansu basu san waye Aliyu ba, ita tasan yadda ta wahala a hannunshi farkon aurensu , tasan idan asirin nan ya karye toh nata ya k'are

Tafiya sukeyi babu wanda yace da wani komai, Abutturab ne ya ďago ya dubi Sadiq yace "Farida ma last month taje wajena ai, amma kai ko sau ďaya baka nemana ko? " wani siririn dariya Sadiq yayi, yasan yayanshi is feeling guilty of himself shiyasa baisanma mey zaice ba, Sadiq yace "No Yaa Abu, abubuwa ne sukayi min yawa, ga hidiman Ammah, Abui da kuma na wasu shiyasa, amma in kuka koma har can zanzo , In shaa Allah" , jikin Abu ne ya kuma yin sanyi yace "Allah ya yadda " a ranshi yana tunanin mey zai fara cewa su Ammah, sai yanxu yake sake ganin rashin kyautuwar abinda yayi, a haka suka isa gida suna hira jefi jefi, a k'ofar gida Sadiq ya tsai da motar tare da yiwa masu gadin horn, da sauri saurinsu suka taso suka buďe, ba K'aramin mamaki sukayi ba ganin Abutturab, da sauri suka faďaďa fara'arsu suna "Alhaji K'arami sannu da zuwa , an sha hanya to ya iyali , fitowa yayi daga motan ya mik'a musu hannu suka gaisa , sai murnan dawowanshi suke dan yana da kyauta sosai duk rashin dariyarsa, wucewa Sadiq yayi tukunna Abutturab yabi bayanshi, a hankali yasa kai cikin falon har wani faďuwa gabanshi yakeyi, Farida ce ta fito daga kitchen da tray a hannun ta, to abin ka da jini batasan lokacin data ajiye trayn ba tazo da gudu ta rungume shi ba, har da hawaye a idonta bayan ta sassauta rik'on da tayi mishi ta kalleshi tace "Yaa Abu ashe za kazo, Dan Allah kana zuwa gun mu kaji" Janyota ya sakeyi jikinshi yace zan rik'a zuwa kullum kinji Autan Abui" Dariya tasa ta goge guntun hawayen

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

11 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment