Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai fimu son Batuul ďin kikayi, in baza kiyi abinda na saki ba tashi ki bani waje in Sadiq yazo anjima in sashi yayi min, xancen banxa kai", jiki a sanyaye tace "zanyi Ammah,mey za a duba miki yanxu, tace "customised designer akwatuna nakeso kimin order, wanda babu wani da za a sake yiwa irinshi sai ita", murmushi Farida tayi ta shiga surfing sai gashi ba b'ata lokaci tace "Ammah gasu nan da hotunansu, wai akwai na Macs n spencer, sai D&G, LV, Mandarina Duck, Versace, paclane, cartier, ralph Lauren da BOSS, Ammah suna da yawa mafa", sai da Ammah ta karb'i Laptop ďin ta ga pictures ďin tace "ki zab'i ten best kiyimin ordern su, kije credit card ďina yana kan shelf a ďakina ki dawo ki gama", Farida na fita Ammah ta ďau waya ta k'ira Aunty Amna dake Paris, sai da ya kusa katsewa ta ďauka, Ammah ce tace mata "keh kullum sai waya ya kusa katsewa kike ďauka, watarana har ya katse ma ba a samunki", tace "Ammah wayan ne tana hannunsu Nawwal basa barina dashi, yanxu ma ita ta kawo min a guje", Ammah tace "toh yanxu duk bama wannan ba, turaruka nakeso ki siya ki turomin da English Golds, Diamonds, Inner wears, vanity sets sai English wears, sai perfumes, shoes, da nighties sai bags" da sauri Aunty Amna tace "Ammah ba dai auren Sadiq bane ya tashi ban sani ba, yaushe za ayi, wace ma matar", ta tambaya with so much excitement sounding vry surprised, Ammah tace "A'ah ba shi bane", Aunty Amna tace "toh waye za a siyawa kayan nan haka da naji kaman lefe", ta faďa excitement ďinta na komawa ciki jin ba Sadiq ne zaiyi aure ba, cewa Ammah tayi "Aliyu ne zai k'ara aure", da mamaki Aunty Amna tace "aure kuma Ammah, yaushe yyi aure har yake son kara wani, wace matar da zai aura ďin, kardai Abu ya zama mai son aure aure fa", cewa Ammah tayi "Amna auren Aliyu na farko ba amfani ne dashi ba", tas Ammah ta gama gayawa Aunty Amna yadda auren Abutturab ďin na farko yake da dalilin da yasa take son ya k'ara auren, jiki a sanyaye jin abunda Ammah ta faďa mata tace "Ammah ni inace ma ni kaďai ya share baya nema, ashe har gidan ma hakane, toh Allah ya rufa asiri, wacece matar da xae auran yanxu", Ammah tace "Batuul", da sauri Aunty Amna ta karb'e tace "Batuul dai, Batuul ďaya da na sani?", Ammah tace "k'warai kuwa ita", guďa Aunty Amna ta sa tace "Ammah dama yarinyar nan nada hankali, sosai nakeson yarinyar tana birgeni, Toh Allah ya tabbatar da alheri, yaushe ne bikin, idan yara na hutu sai muzo kawai gaba daya" Ammah tace "ai next week kenan ďaurin auren, biki ko daga baya ne sai ayi", da mamaki Aunty Amna tace "Laah Amma, everything so fast, toh shikenan, zan duba sauran, amma Ammah perfumes ďin bazai yiwu su biyo plane ba, kuma in za ayi shipping zasuyi taking time, so akwai wani abokin Babansu Nawal yana da perfume shop a Aminu Kano crescent, yayi sabon order recently, so kawai zan mishi magana ya kawo har gida, inma container zaki duba, that will be better sai ku zab'a mata, amma sauran yanxu zan shiga in dudduba", Ammah tace "toh shikenan Amnah, zan turo miki kuďin sai kiyi siyayyan, yanxu zansa Farida ta turo miki sizes da details ďinta tunda k'awartace tasan komai", da haka sukayi sallama, suna gamawa ta shiga k'iran mai gold ďinta dake Dubai, yana ďagawa shima ta bashi order ďin Gold har na wajen 50 mil zai turo mata samples in ta zab'i waďanda take so sai a sakosu a jirgi a turo, shima da haka suka rabu, Farida ganin Ammah dagaske take kuma tasan kayan da k'awatar tafi so tace "Ammah a saka mata abaya a ciki, tana sonsu sosai", Ammah tace sai ki dubo mata suma online shima ki mata ordering ko set 30 ne", sai da ta tabbata ta gama order komai har atampopi daga London tasa aka turo mata su sai laces da lappayu daga switzerland, sai da tabbata ta gama tukunna ta tashi taje tayi sallah.







Har ta gama aman bai saketa ba yana nan rik'e da ita duk ta wanke su gaba daya, murya can kasa yace " Srry!" Kkrin sauka ta shiga yi yaki sakinta, a hka wata nurse ta shigo ta samesu, da sauri ta karaso bakin gadon tana cewa "Wat happened?" Sae a snn Abuturrab ya sake ta, nurse din ta shiga yi mata sannu, shi kam unbutton din shirt din jikinsa ya shiga yi ya nufi toilet, nurse din ta shiga cire mata rigar jikinta ganin tana da vest a ciki, da sauri ta rike rigar taki barin ta cire mata, nurse din tace "Haba! you've messed the blouse, ki cire sae in baki wani abun ki lulluba da shi kafin a kawo maki kaya" bbu ynda Batuul ta iya hka nurse din ta taimaka mata ta cire rigar jikinta, ta sakko daga kan gadon, nurse din tace bari ta kawo mata wani abu ta rufe jikinta, Cleaners ta fara kira su je su gyara wajen su canxa bedsheet, Batuul na tsaye duk ta kagu nurse din ta dawo ta rufe jikinta kafin ya fito, ae ko sae gashi ya fito da singlet rike da shirt dinsa da ya wanke, suna hada ido ta juya masa baya da sauri ta ji kmr ta nutse wajen, dai dai nn nurse din ta dawo rike da hijab cleaners biyu na biye da ita, daya rike da xanin gado daya kuma na rike da bucket da mopper sae Freshner, da sauri ta karasa ta karbe hijab din tasa, ficewa yyi daga ward din bayan ya dauki makullin motarsa da wayarsa, ko minti biyar bae yi da fita ba Anty ta shigo rike da kayan Batuul a leda.

Ammah ta bi sa da kallo bayan ta amsa gaisuwarsa ganin ya nufi stairs tace "Meye hkn Abuu?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Amai tayi min" daga hka ya haura sama, farida ta saka dariya sanin ynda Amai ke bala'in irritating yayan nata sae gashi an masa a jiki, Ammah tace "Allah sarki, Allah dae ya bata lfya". Da daddare yana kwance kiran Ajiddeh ya shigo wayarsa, ya dde yana kallon wayar kafin ya d'aga ganin ya kusa katsewa.
💖💝BATUUL💖💝






36






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Yana ďaukan wayan ya hau ta da bala'i, "wai ba nace miki zaki iya tafiyar ki bane, wat are yhu still waiting for, in kuma ke da amaryar za a kai sai inji", kashe murya tayi cikin salo tace mishi "Babe na wuce fa tun ranan da kace min in koma, naga ko sau ďaya baka nemeni ba shiyasa na k'iraka yanxu tunda ni ina sonka ya na iya da halinka", kallon screen din wayar yyi, sae a snn ya lura da international Number ma ta kirasa, jin yayi shiru bai ce mata komai bane yasa taci gaba da cewa "Babe am missing you, wai yaushe zaka dawo ne, am so lonely without you here", d'an ajiyar xuciya ya sauke yace "soon, i gat things to do over hear, i will be back immediately when am done dear", ssae taji ddin abinda yace mata, cikin muryar shagwaba tace "Aii baby, i will be waiting, take care of yourself, i will also do that for you, bari in barka ka huta", da haka ta katse k'iran tayi wani murmushi a ranta tace zaka shigo hannu ne vry soon, baza ma ka samu k'afar zuwa Nigeria bama nan gaba bare har kaje kaqi dawowa har ka mance ni na kwanaki, wani irin dariya ta saki da ta tuna irin tanadin da takeyi a kanshi, shi kam lumshe ido yayi bayan sun gama wayan, aman da Batuul tayi mishi ne ďazu scene ďin ke dawo mishi kamar yanxu abin ke faruwa da yadda yaji jikinta yayi zafi lokacin da ya rik'eta, buďe idanunshi yayi ya mik'e ya nufi toilet yin alwalan sallar Isha don bai ma jin yau zai iya fita masallaci, yana fitowa daga toilet ďin Farida ta turo k'ofar ďakin, harara ya watsa mata yace "sallama ne baki iya ba ko knocking da zaki shigo min ďaki kai tsaye", dariyan dake cikinta ta mayar dan tun lokacin da taji Batuul tayi mishi amai da ta tuna take k'yalk'yalar dariya, tasan halinshi na k'in amai, maida dariyar tayi da sauri ganin yana k'ok'arin tada sallah tayi maza tace "Yaa Abu", bai amsa bama bare ya juyo ya dubeta, sake k'iran sunanshi tayi tace "Yaa Abu", tayi shiru ba tare da tace mishi wani abun kuma ba, wani mugun kallo ya jefeta dashi yace mata "fita min a ďaki", da sauri ta juya zata fita, ta tsaya daga wajen k'ofa ta lek'o kanta tace "Ammah ke nemanka fa", tana kaiwa nan ta fice da sauri tana dariya, sai da ya idar da sallah tukunna ya fito, a ďakinta ya tarar da ita Farida na daga gefenta, harara ya sakar mata ganin ta kafa mishi ido, daga gefe ya zauna yace "Ammah gani", dubanshi tayi tace "sae yanxu kayi niyyan zuwa kenan, toh abinci zaka kaiwa Batuul a asibiti, maza kuje tun ďazu aka gama na tura a k'ira ka baka ga daman xuwa ba", ido ya rintse tun da yaji inda zashi har sai da yaji tayi shiru tukunna ya buďe yana kallonta yace "Ammah ba driver na nn ba, wllh kai na sarawa yakeyi, ko Sadiq sai ya kaita in ma drivern bae nn kinji Ammah na", Ammah tace "bakaji inda nace zaka bane, in kaje kace su baka magani a can ďin, tashi kaje kar ku b'ata lokaci", mik'ewa yayi jiki a sanyaye ya koma ďauko key ďin mota, shi baisan mesa Ammah ke yi masa hka kan yarinyar nan ba, k'wafa yayi tunawa da yayi da aman da ta mishi daxu ya ďau key ya fito, a wajen parking ya tarar da Farida da masu aikinsu su biyu rik'e da basket ďin abinci, daga jikin makullin ya buďe musu k'ofa suka saka kayan daga baya shi kuma ya shige gaba hka ma Farida, sai harararta yake, itadai bata ce mishi komai ba har suka fita gidan, k'ira'ar Shuraim kadae ke tashi a motar.






Bayan nurse da cleaners ďin sun fita Aunty ta taimaka mata tayi wanka ta saka kayanta mara nauyi da ta kawo mata, tea Aunty ta haďa mata tasha ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa, gyara mata kwanciyanta Aunty tayi ta gyara mata bargon sannan ta jawo kujera ta zauna gaban gadon ta zubawa y'ar tata ido tana tausayin halin da zata shiga, turo k'ofar ďakin akayi, Yayya ta shigo Ahmad a bayanta, ganin waďanda suka shigo ďakin yasa Aunty ta ďauke dubanta daga kallon k'ofar, k'arasawa cikin ďakin sukayi, daga gefen Batuul Ahmad ya tsaya zuciyarshi fal da tausayin y'ar uwarshi, rashin lafiyan kwana ďaya har ta rame, Aunty ya duba yace "Aunty yaushe sukace zasuyi discharging ďinta?", ya faďa yana ďan tab'a goshinta yaji temperature ta, Aunty tace "Yanxu doctor ya shigo ya duba ta, ta samu tayi amai, amma baice min yaushe zai sallametan ba", da jimami Ahmad ya sake cewa Aunty "Aunty wai mey ke damunta, meye doctor yace muku na damunta all of a sudden", caraf Yayya dake tsaye bakin window tana k'ok'arin ďaga labule kamar an sata ta karb'e maganan da cewa "mey ko zai sameta, daga na ce mata za a haďa aurenta da yaron nan yaron kirki Abutturab shine fa ta tada hankalinta har da rashin lafiya, ko xuga ta uwar tayi oho", jin abunda Yayya ke faďi ya dubi Aunty da mamaki yace "Aunty aure kuma, wai hakane dagaske?", "Au k'arya zanyi maka, toh tambayi uwar taka da bata k'arya sai ta faďa maka gaskiyan zancen, kuma ko nayi rantsuwa baxan yi kaffara va, ita ke daďa ingiza ta har aka kwantar da ita asibiti", Ahmad da ranshi ya fara b'aci jin tana aibata Aunty yace "Keh Yayya nifa bake na tambaya ba", "ehh ai nima ďin nasan ba ni ka tambaya ba, amsa ce na baka don nasan ba baka xa suyi ba", Aunty dae ko kallon inda suke bata yi ba dan ita tunaninta daban takeyi, Ahmad yyi tsaki yace "kinga zo mu koma, dama Baba cewa yayi in kawoki ki ganta mu koma, toh tunda ba ma dubatan zakiyi ba kizo mu wuce, dan ni in na tafi sai dai ki nemi mai dawo dake", masifa ta shiga yi ganin yayi hanyan k'ofa yana cewa Aunty zai tafi, Allah ya bawa Batuul lafiya, binshi tayi a baya tana ta zazzaga mishi ruwan bala'i har tana cewa sai tasa an karb'e motar ya dena tuk'awa tunda wulak'anci ne abun, suna fita Aunty ta tashi ta gyara windown da Yayya ta buďe, wayan Batuul da ta taho mata dashi ďazu ne ya fara ringing, mik'ewa tayi ta ďauki wayan, ganin mai k'iran yasa ta maida ta ajiye.






Sai dare Batuul ta tashi lokacin har an idar da sallah magrib, da taimakon Aunty taje tayi alwala tayi Sallah, Ce mata Aunty tayi bari in shiga office ďin doctor, tun ďazu yake nemana kina bacci shiyasa ban fita ba, Aunty na fita wayanta dake ajiye gefenta yayi ringing, da kamar baza ta ďaga ba ganin mai k'iran yasa ta ďauka lokacin har ya kusa katsewa, a hankali murya can k'asa tace "Hello", wani irin ajiyar zuciya ya saki jin muryanta, shima murya kaman ta mai damuwa yace "Habibty dont do this to me again kinji, i was so worried abt you, tun jiya nake k'ira you werent picking, do you know how this affected me", shiru tayi tana saurarenshi idonta ya cicciko da hawaye tana tuna abinda Yayya ta faďa mata jiya, jin tayi shiru ta kasa magana yasa yace mata "you there", kasa mishi magana tayi sai kukan da ta fashe mishi da, har cikin ranshi yake jin kukan nata, kiďimewa yayi ya shiga tambayanta "Fatima mey ke damunki, ki daina kuka and tell me whats wrong with you, you are making me distressed, kina inane i will come right away...", da k'yar ta samu ta saita kukan nata tace mishi "Na'am", cikin shesheka, with so much concern yace mata "Its okay stop crying and tell me whats wrong with you kinji", har muryanshi na rawa, murya can k'asa tace mishi "I was sick", mik'ewa yayi tsaye daga zaunen da yake yayi hanyan ďakin Mummynshi, tambayanta ya shiga yi "mey ke damunki Fatima, kuma kina inane", a hankali tace mishi " Nima ban san mey ke damuna ba, I was admitted a asibiti tun jiya", ce mata yayi "Its okay, you will get better soon kinji, i will b on my way right away, take care of yourself", har ya katse wayan sai ya tuna ashe baima tambayeta wane asibiti bane, sake kira yayi ta faďa mishi asibitin da aka kwantar da ita, da haka ya katse k'iran ya karasa ďakin Mummy, zaune ya tarar da ita akan abin Sallah, zama yayi daga bakin gadonta yana jira ta gama azkar ďinta tukunna ta juyo ta dubeshi tace "Babana dama kana gida baka fita ba, ya akayi naga duk ka zama wani iri, what is it", ce mata yayi "Mummy Batuul, i mean Fatima ba lafiya, yanxu haka tana asibiti a kwance, Mum ki shirya muje mu duba ta kinji Mum", kallonshi take yadda ya rikice yana mata magana, bata tab'a ganinshi ya damu akan wata mace kamar haka ba, kanshi ta shafa tace "jeka canja kaya ka ďauko key kazo mu tafi", da hanzari ya mik'e ya fita, girgiza kai tayi tana addu'an Allah yasa son Batuul ya zame mishi alheri ta cire Rigar sallah dake jikinta ta shirya tafiya asibitin da ďanta.





Batuul na gama waya zata ajiye taga an turo k'ofar ďakin, a zatonta Aunty ce ta shigo, Farida ta gani bakin kofar rik'e da Basket a hannunta, Murmushi ta saki tana kallonta, ba shiri murmushin dake fuskanta ya bace ganin wanda ke tsaye bayan Farida, sunkuyar da kai tayi da sauri, farida ta karaso ta xauna gefenta murmushi dauke fuskarta har lkcn tace "Waow Besty, I can see yhu are getting much beta ynxu, ga abinci na kawo maki, ur favourite!" Batuul tayi murmushi sae dae bata ce komae ba don ita ko kadan bata ji ddin dawowan Abuturrab ba, karasowa cikin ward din yyi ya ja kujera ya xauna fuskarsa a daure, farida ta sauka daga gadon ta nufi basket din abincin don dibar mata farfesun da tayi mata, Batuul ta kalleta tace "Don't wrry dear, am okay ynxu, bn dde da cin abinci ba, ltr sae in ci, hope yhu are spending d nyt here?" Farida ta wara ido tace "Y not love, ae da shirin kwana dama na xo" wani harara Abuturrab ya watsa mata yace "Ki gama abinda xa kiyi mu tafi, dnt waste my tym" Bata fuska farida tayi tace "but Ya Abuu Ammah fa ce tace in kwana wllh" mikewa yyi kmr xae maketa yace "Tafi mota ki jira ni" kuka ta saki, ganin ya yo kanta ta fice da sauri daga dakin, juyawa yyi yana kallon Batuul ya galla mata harara yace "C'mon sense din ki bae baki cewar hakurin filthy abinda kika min a jiki daxu ya kamata ki ban ba" ganin taki kallon inda yake bare ya sa ran amsa yasa ya karasa inda take yana mata wani irin kallo, bude kofar dakin aka yi Anty ta shigo, da sauri ya koma baya, Anty ta karaso cikin dakin ya juya kai a kasa ya gaisheta, amsawa tayi d'aga hka ta nufi inda wayarta yake ajiye ta dauka ta fita, Batuul ta dauki wayar ta da ya soma ring a gefenta ta dauka ganin me kiranta, "Hello love gani a hospital din ban san ward din da ku ke ba" satan kallon Abuturrab tayi ta ga idonsa kyar a kanta, ta sunkuyar da kai tare da dauke kai, a hnkli ta gaya masa ward nmbrn da take, snn ta katse wayar ta ajiye, shi kam har lkcn bae bar kallonta ba xuciyarsa na tafasa ganin ynda ta ki ko da kallon inda yake, Anty ce ta kuma dawowa dakin da mamaki take kallonsa tace "ga kujera Abuturrab, ya da tsayuwa" murmushi ya kirkira yace "Tafiya xan yi Anty" Batuul ta kalli Anty a hnkli tace "Anty Abubakar ya xo wae yana waje, na gaya masa ward nmbr" kallonta Anty tayi xata yi magana aka tura kofar dakin, kansa a k'asa ya shigo da sallama mum dinsa na biye da shi a baya, da fara'a Anty tace "A'ah sannun ku da xuwa" Kallon Abubakar kawae Abuturrab ke yi ko kiftawa bae yi, Anty ta ajiye ma mum dinsa kujera ta xauna tana kallon Batuul tace "Sannu Fateema, ashe baki ji ddi ba" Batuul da kanta ke k'asa ta dan yi murmushi cike da jin kunya tace "Ina yini Mama" Matar ta fa'da'da murmushin fuskarta tace "Lfya lau Batuul ya jikin?" A hnkli tace "Da sauki" tace "Allah ya sauwake" har k'asa Abubakar ya kai ya gaida Anty ta amsa murmushi dauke fuskarta tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh Mumy" mikewa yyi yana kallon Abuturrab dake kallonsa har lkcn ya mika masa hannu, Abuturrab ya sunkuyar da kai suka yi musabaha, snn Abubakar ya juya yana kallon Batuul sae dae taki kallon inda yake, sae a snn Abuturrab ya ga daman gaida Mahaifiyar Abubakar ta amsa da fara'a, Mikewa Mumy tayi daga karshe ta nufi gun Batuul ta ajiye mata ledan hannunta tace "Toh fateema Allah ya kara lfya kin ji" Batuul tace "Ameen ngd Mumy" Mumyn ta kalli Anty tace " Hajiya ni xan koma Allah ya sauwake" Anty tayi mata gdya ssae, Abubakar yace "Momy ki jira ni gani fitowa ynxu" dariya Mahaifiyar tasa tayi tace "Dama ae xan jira ka" d'aga hka Anty ta rakata suka fita ward din, Batuul ta sace kallon Abuturrab ta ga kallonta yake, ga Abubakar da duk ya kagu ya fita ya basu waje da Habibtyn sa.
💖💝BATUUL💖💝

25

By Phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*


Tsayawa yayi ya zubawa fuskanta lumshashen idonshi, babu komai fuskanta daga dogon hanci sai lashes ďinta da suka kwanto a fuskan da ďan k'aramin baki, ya kai minti biyu yana kallon fuskanta ya ma rasa me yake kallo a fuskar, daga k'arshe ya dan ja tsaki ya tada motar sukayi gida, Batuul kam tunda ta kwantar da kanta bata ďago ba, parking yayi da suka isa gida ya kashe motar, jin an tsaida motan ya sata buďe idonta a hankali ta dubi side ďin da yake, maza tayi ta ďauke idonta don kallonta yake, buďe k'ofa tayi zata fita yace mata "wa zai ďaukar miki maganin", bata kulashi ba ta dawo ta ďauki ledan magani tayi gaba abinta, ďakin Ammah ta nufa, a hankali ta tura k'ofan ďakin tasa kai, babu kowa a ďakin sai k'anshi dake tasowa ta kowane angle, shiga tayi ta zauna kan gado tare da jinginar da kanta a jikin gado ta lumshe idonta, numfashi take sauk'ewa kamar wacce tayi wani babban aikin, buďe k'ofan ďakin yayi shima ya shigo, babu kowa sai Batuul jingine a gado, k'irjinta na heaving, a zuciyanshi yace "she is lazy, kamar wacce ta ďauko gari" tabe baki yyi yaja k'ofan ya rufe, falon sama ya tsaya zai k'ira Sadiq ya tambaye shi inda Ammah take, yana ciro wayan ya hango Ammah ita da ďaya daga cikin masu aikin gidan ďauke da babban tray suna hawowa sama, sai da suka hawo tukunna ya k'arasa wajen ta yace "Ammah mun dawo", ba tare da kalleshi ba tace "mey suka duba sukace ya sameta", ta faďa tare da tura k'ofar ďakin, sam shi baya jin daďin yadda Ammah ke yi mishi akan yarinyar nn, binta yayi shima jiki a sanyaye ya shiga ďakin, trayn hannunta yarinyar ta ajiye ta juya ta fita, sai da ta fita tukunna ya zauna ďan nesa da Ammah yace "pneumonia ne sukace yana son kamata, sunce ta guji anything cold sai ta rage yawan wasa da ruwa da shan abun sanyu", katseshi tayi da "wane irin ta rage wasa da ruwa, ai dama ba yi takeyi ba, kuma da k'yar aka samu ta rabu da wannan pneumonia tun tana k'arama yake wahalar da ita, sai da aka samu yarinya ta huta zaka sa ya dawo mata, ai da baka sata shiga ruwa ba da babu abinda zai sameta", a hankali yace "Ammah nace kiyi hak'uri fa, bazai sake faruwa in sha Allah, kiyi hak'uri", tana kwance bata buďe ido ba tana jiyo duk abinda yake faďa, wani ďan k'aramin murmushi tayi dan taji daďin yadda yake yiwa Ammah, ashe akwai waďanda yake jin maganarsu, "ai dama aikin kenan , da kayi abu ka fara bani hak'uri, k'arfe nawa zakuje gaisuwan iyayen?", sakin murmushi yayi dan ya gano cewa ta hak'ura tunda ta fara wani zancen, ce mata yayi "bayan azahar zamu je, sai dare kuma aje a ďaukota", "Allah ya kaimu , Su Aunty Amna sai suje su ďaukota, ba sai kun shiga gidan naka ba ai tunda kwana huďu kawai zakuyi ku wuce, tayi zamanta kawai a nan a side ďinka, kar a bata mata gida, duk ranan da kuka tashi dawowa gidanku ya zamana sabo", yace "hakan ma yayi Ammah, inaso inci abinci" ya faďa mata kamar wani k'aramin yaro, tray ďin ta nuna mishi tace "dama Batuul na sa akawowa, amma yana da yawa zaka iya ci a ciki, Ammah ce ta mik'e ta isa inda Batuul take ta tasheta taci abinci, har kan gadon ta bita da abincin, ta ansa, kasa cin abincin tayi da hankalinta sam yaki kwanciya, shiko ko kallon inda take ma bai yi ba sai abincin shi yake ci suna ta hira da Ammah, a hankali ta ďan tsatsakuri abincin

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

11 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment