Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sona ba,iya yadda kike nuna mini ko in kula ya isa na gane hakan".






Hannun ta Hafsat ta rik'e tace"yanzu sister gaya mini meye damuwar ki? ",shiru Ikhlas tayi tana zare idanu.





Murmushi hafsat tayi tace"kin gani ke kan ki baki san me yake damun ki ba,ko kina taya 'yar uwar ki murnar shigowar ta familyn mu ne?, yanzu ki tashi ki shirya mu tafi bauchi domin kuw Abba kabeeru ya kusa kashe Hafeez da matar shi".





Zaro idanu Ikhlas tayi tace"me?, da gaske dafatan dai be kashe shi ba? ",hafsat tace"kiyi shiru domin bamu sanar a gida ba,yanzu haka ma gwaggo bata sani ba".






Mikewa tayi jikin ta har rawa yake yi ta shirya,suna fitowa Maleek yayi ajiyar zuciya be san lokacin daya bud'e gidan gaba ba.




Ita kan ta shi take kallo, Bintu tace"yaya na kaje ka bude naka, ba dole sai ka wahalar da kan ka ba, tun yanzu kan muyi aure".






Juyawa yayi, tuno hakan yasa yayi murmushi yace"ai kinga gwara na fara kula dake saboda su Baffa su sani da wuri".






Cikin sauri Ikhlas ta bude motar saifullahi, Maleek yayi saurin cewa"ke madam anan zaki tafi".





Ba tare da ta kalle shi ba tace"ni yaya saifullahi zan bi",Maleek ya matso kusa da ita yace"bana son jayayya ki wuce muje".



Kallon shi tayi tace"nace bazan bika ba, sai kayi yadda zaka yi,banza mata-maza kawai", dariya yayi yace"au yau kuma zaki yi nadama ne wallahi ikhlas ina guje miki ranar da zaki k'arya ta kan ki, yanzu dai wuce muje".






Saifullahi yace"Lily ku tafi kawai da sadik ni ka bar ta mu tafi da ita a nan",ba tare da ya amsa ba ya d'aga ta cak, dukan da take mishi da masifar da take duk a banza.




Sai da ya saka ta a motar sannan ya kulle ya juya shima ya shiga,kallon Bintu yayi yace"Bintu kije motar lovely",bintu ta amsa da to sannan ta wuce.








Yana shiga ya tada motar ya fita, motar saifullahi na bin bayan shi.





"Wallahi Abba kabeeru yana bani mamaki, kamar wani mahaukci",sadik ya fad'a cike da takaici.





"Ka bari yanzu muna zuwa,police zamu sa su kamo shi, a hukunta shi",Saifullahi ya fad'a.




Hafsat tace"ai wallahi ni har mamaki yake bani, idan banda an tausa shi Ikhlas da yanzu jikin shi ya gaya mishi, kasan har yanzu bata san ya akayi umma ta bar bauchi ba? ".






"Ai gwara kada ta sani,Ikhlas rigima kenan,", dariya suka yi gaba d'aya,saifullahi yace"dama ai Lily shine dai-dai ita".





Dariya suka kuma yi, Hafsat ta kalli Bintu tace"wallahi ke kuma ki rage shige mishi dan kina daf da shan shak'a a wajen ta",dariya suka kuma yi.




"Hmm aunty Hafsat ai wallahi dazu wani kallo da tayi mini kad'an ya rage na gudu,ni yanzu ai na tabbatar yaya lily yafi k'arfi na ina ni ina kishi da ita, Allah wata rana sai dai a d'auko gawa ta",sosai ta basu dariya.






Sadeek yace"kada ki damu kinji, kiyi addu'a Allah zai baki nagari",Bintu tayi murmushi tace"ai yaya sadeek baba na ma ya riga da yayi mini miji a cikin yan uwan shi ni da aunty sadiya".





"Ita kuma shamsiyya fa? "Hafsat ta tambaya,Bintu cikin takaici tace"baki san meya faru ba aunty,ai aunty shamsiyya 'yar lesbian ce, shiyasa bata tab'a saurayi ba".




Zaro idanu suka yi,Bintu cikin takaici Ta cigaba"ranar da aka kamata ita da k'awar ta, abin bakin ciki ma kishiyar hajiya ta ganta".






"Wallahi babu kunya ba tsoron Allah ta tattara kayan ta tabi kawar ta ta,shine fa abban mu yace ya gaji aurar damu zai yi".






"Allah ya kyauta gaba, dan Allah bintu kuyi hakuri ku bi mahaifin ku, kinji", saifullahi ya fad'a.








"Ai yaya tuni ma,domin kuwa yana fad'a mana muka amince,Abinda ya hana hajiya zuwa bikin nan fa kenan".






"Allah ya kyauta gaba,yasa ta gane ta shiryu",duka suka amsa da ameen.







๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*




*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*

*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*






*written*
-by-
*Deeja one love*







*๐Ÿ†JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ†




*Dedicated*

-to-
*Maryam khamis*


*masoya na kun zama ginshik'i, ni danga ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*



*kuyi comments ni kar kuce dani kunyi fushi ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*




*zuciya ta ta dad'e tana neman masoyan asali๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*




*ASHE KUNE?? zaku zam cikon numfashi ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*


81-82



Maleek dake tuki yana kallon ta ta gefen ido,sosai ta d'aure fuska wanda hakan ya bashi dariya.





Hawaye ne ya fara zubo mata,a hankali take share hawayen,ita kanta baza tace ga dalilin kukan ba, sai dai duk haushin da take ji tana murna da basu taho tare da bintu ba.




Shi kuwa hawayen da take yi jin shi yake yi har ran shi daurewa kawai yake yi.




Kar'a volume yayi na qirar dake tashi a cikin motar,sosai suke gudu, kan lokacin da har ta fara barci.




Suna isa bauchi asibitin suka wuce kai tsaye,Islam har lokacin jikin ta rawa yake yi,Tana ganin su ta k'araso da gudu ta rungume yaya sadik.






Lallashin ta ya dinga yi sannan ya samu ta yi shiru,Saifullahi ya bada sanarwar duk inda aka ga Abba kabeeru to a kamo shi.







Yau kwanan su biyu a bauchi har lokacin kuma,Basu farfad'o ba gwaggo da Iman da Mummy duka suna kan hanyar zuwa.







Su beelert sun sha kuka har sun k'oshi,Islam na zaune taga Hafeez ya fara motsa hannu, sannan sai idanu.






Cikin matuk'ar murna ta fara ihu tana fad'in"wallahi ya fara motsi",da sauri brr bashir ya tafi kiran likita.





Su kuwa duka sun rud'e sai murna suke yi,kan wani lokaci har asibitin ya cika,mummy ce dai bata motsa ba.







Koda likitocin suka zo sun dudduba suka tabbatar da babu wata matsala.





Yanzu abinda suka maida hankali shine farkawar mummy, wanda hakan shi suke fata,su iman ma duka sun iso bauchin.






Babu wani internal injuries yanzu,sai dai fa har lokacin mummy bata farka ba,sosai hakan yake damun su.





Suna zaune suna fira,Maleek yace"ka san dai auren ka shine a gaba ko,to kayi sauri ka warke idan ba haka ba kuma to kaji anayi".






Harara ya galla mishi yace"kamar wani kai din ma ka shiga daga ciki ne, bayan auren naka suna ne".





"Kyale shi dai,Allah ne ya taimake shi fa muka taho bauchi da yanzu yana can gaban Baffa yana zare idanu kamar wanda yayi k'arya a gaban sarki"saifullahi ya fad'a.





Dariya suka yi sannan Maleek yace"ka san me?,ai ni yanzu idan Allah ya taimake ni, na sami matar aure", duka a tare suka kalle shi.





Ikhlas ta d'ago idanu cikin tsoro take kallon shi, shima ita yake kallo dan haka idanun su na had'uwa ya daure fuska.







Saukar da kai k'asa tayi tana jin zuciyar ta na mata zafi,sosai kirjin ta ke bugawa"aure lallai to dole ya sake ni kafin yayi auren dan wallahi ba zan zauna ana wulakanta ni ba", ta fad'a hakan a ranta.







Shi kuwa Maleek wani dad'i yaji saboda yadda ta kalle shi ya tabbatar da abinda ya fad'a ya b'ata mata rai sosai dama kuma saboda hakan ya fad'a.





Tunda suka zo tak'i kula shi kwata-kwata,yanzu taji maganar kishiya ai ta kalle shi.






A ranar aka sallame shi hakan yasa duk suka tafi gida, ya rage umma ce da gwaggo a wajen mummy.






Washe gari Mummy ta tafi da Iman kaduna,Hakan yasa Saifullahi shima fara shiri domin wucewa.





Washe gari suma zasu tafi, da dare suna zaune Hafsat tace"Ikhlas kin san dai ina son ki ko tunda ke 'yar uwa ta ce, kada ki bari Maleek ya kubuce miki zakiyi asarar masoyi mai daraja wanda da wuya ki maida kalan shi".




Ikhlas kamar zata yi kuka tace"Wai Hafsat bakiji maganar aure zai yi bane?,kuma ni wallahi na rasa yadda zanyi".






"Ki lallab'a shi Ikhlas domin kuwa dai shine mijin koma yaya ne?,sannan kuma ki dage da addu'o'i insha Allah komai zai zo da sauki".





"Insha Allah zanyi yadda kika ce,Dan Allah Hafsat kema ki taya ni dan wallahi yanzu nasan ina son shi, sai dai kamar lokaci ya k'ure".







"Lokaci be k'ure ba Ikhlas ki dage kada ki damu da maganar daya fad'a har yanzu Maleek yana son ki".






"Shikenan zan gwada na gani, na gode sosai Allah ya k'ara zumunci".





"Ameen, nan da zuwa jibi honey zai dawo,ni dai kam sai an kwana biyu,ko ina jin ma sai mun had'e a kaduna kawai".





"Idan da rabon na dawo ba, idan babu kuma sai kin haihu",Abin dariya yaso bawa Hafsat amma ta dake.





Daga haka suka mik'e suka fito, domin Ikhlas tana so ta raka ta.



Tunda suka fito ya zuba mata idanu, sosai k'irjin shi yake bugawa,ji yake kamar ya janyo ta ya had'a da jikin shi ko ya sami sassaucin abinda yake ji.






Ikhlas kuwa kallo d'aya tayi mishi ta dauke kai, ganin bintu tsaye kusa dashi,beelert kuwa kallon ikon Allah take kawai.






Sun tafi cike da kewar juna bama kalar Ikhlas,suna juyawa yayi saurin janyo ta ya had'a da jikin shi.





Da sauri ta kwace kan ta tace"wai meye haka ne, baka ganin mutane ne a wajen ka wani kama ka rungume ni,ko suma sai ka nuna musu a harkar iskanci ka k'ware".





Sosai maganar ta b'ata mishi rai dan haka kawai ya juya ya nufi cikin gidan ran shi na k'una.








Washe gari aka kamo Abba kabeeru acan bayan gari can wani gidan gona,an harbe shi a k'afa an kuma mishi dukan tsiya.





A ranar kuma mummy ta farka, sai dai fa tana farkawa babu dad'ewa ta fara jijjiga, sosai hankalin su ya tashi.





Duk sun bi sun zagaye ta, babu yadda likitocin basu ba, amma sun k'i barin d'akin,Islam da Hafeez sai kuka suke yi.





A haka aka shigo da Abba kabeeru,cikin fushi Hafeez yace da 'yan sandan"me kuka kawo shi nan yayi, yazo k'arasa mana mahaifiya ne?".





Islam cikin kuka tace"Abba ka cutar damu,ba zamu tab'a yafe maka ba",ta k'arasa tana kuka me ban tausayi.




Shi kan shi hawaye yake yi,kan shi na k'asa ya fara fad'in"Islam, Hafeez,Sadeek,Iman, Ikhlas,mata ta,Gwaggo dan Allah ku yafe mini wallahi nayi nadama".





Da k'arfi Islam tace"ba zamu yafe maka ba har abada ka tattara ka fice daga nan kafin na kashe ka da hannu na".





Ikhlas ta rik'o hannun ta sannan ta zaunar da ita tace"Islam ban sanki da rik'o da rashin yafiya ba, Tunda har ya nemi ki yafe mishi ki yafe mishi mana, Haba Islam mahaifi ne fa baki da wanda ya fishi".





Hannun ta ta kwace tana fad'in"Inada Ikhlas, Inada Gwaggo inada yaya Sadik, ina da ke haka iman da yaya Hafeez, dan haka bana buk'atar shi a rayuwa ta".






"Haba islam ya kike magana irin haka,mahaifin ki ne fa,kiyi hak'uri ki yafe mishi, ko Allah muna mishi laifi mu nemi tuba ya yafe mana balle mutum dan uwan mu", sadik da tun dazu beyi magana ba ya fad'a cikin sigar lallashi.






Da k'yar suka shawo kan ta ta furta ta yafe mishi,babu wani ja-in-ja sauran suma suka yafe mishi.





Yana kuka ya fara basu labarin meya faru,"bayan na bar gidan da kud'i masu yawa,gida na da yake wajen atap na nufa".





"Bana fita duk abinda nake so yara na su hazard ke siyo mini, a boye nake neman visa, ban san ya akayi ba kawai sai suka gane".






"Jiya da dare suka zo suka nemi su k'wace ragowar kud'in da nake dashi, ni kuma na hana ganin haka yasa suka mini dukan tsiya suka harbe ni a k'afa sannan suka kwashe komai suka gudu suka barni".





Kowa a wajen yayi shiru kafin Mummy ta fara kuka tana tari me k'arfi,Dandanan lokaci kad'an Allah ya amshi abin shi.





"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"dukkan me rai mamaci ne,hankalin su ya tashi sosai, Abba kabeeru kamar zai yi hauka hakan yasa police suka fice dashi.






Ko kan a dawo da ita gida har mutane sun taru, domin labarin mutuwa baya b'uya,wanka aka yi mata sannan aka shirya ta aka d'auke ta sai gidan ta na gaskiya.






Inda ni da kai da su da ku da mu duka zamu je,haka aka binneta daga ita sai halin ta,Allah kasa mu cika da imani!.







๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*




*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*

*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*






*written*
-by-
*Deeja one love*







*๐Ÿ†JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ†




*Dedicated*

-to-
*Maryam khamis*


*masoya na kun zama ginshik'i, ni danga ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*



*kuyi comments ni kar kuce dani kunyi fushi ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*




*zuciya ta ta dad'e tana neman masoyan asali๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*




*ASHE KUNE?? zaku zam cikon numfashi ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*

Ayi mini afuwa wallahi charger dina ce ta sami matsala, sai da na sami wata tukunna shiyasa kuka jini shiru.


Watakila ku k'ara samin koda one page ne kafin jibi na tafi kano, idan kuma baku samu ba ina baran addu'ar ku na Allah ya kaimu lafiya pls ku tayani da addu'a,to mu had'e a can kanon zan k'arasa muku kawai.



Dijensy am coming to your state, domin d'aukar amra a gidan brr kamal na had'ata da shettyn mummy.... Lols.




Wannan page d'in na baki kyauta kaka ta *fatima batula* ke da name sake na *khadija lipton*.



83-84



A lokacin idan kaga Islam sai ta baka tausayi domin irin ramar da tayi,Hafeez kuwa da dauriyar shi saboda kasancewar shi namiji.





Sai da akayi bakwai sannan suka fara had'a kayan su domin gida dai ba nasu bane yana cikin gadon Sadik.





Su gwaggo suna zaune,Ikhlas na wanke-wanke,Iman kuma na gaban murhu,gefe kuma Maleek ne da Sadik da alamu magana suke yi.





Ikhlas taja tsaki ganin duk lokacin da ta d'ago kai sai sun had'a idanu,wannan karan suna had'a idanu ta zabga mishi harara.





Murmushi yayi ya shafa gefen fuskar shi,sosai yanayin yadda idanun ta ya juya ya burge shi,wani iri yaji a jikin shi.





Mik'a yayi yana lumshe idanu,Sadik da yake kallon shi yayi murmushi yace"ya dai, ko ta bar wanke-wanken ne tazo? ".





Kallon Sadik d'in yayi yana fad'in"wallahi wannan da kake gani ko, ta fiye rigima, amma da zata zo ai dana rage zafi",dariya suka yi suka tafa.





Ikhlas ta kalle su ta tab'e baki,duk da bata jin abinda suke fad'a amma ta tsargi kan ta.





Shi kuwa Maleek ganin ta d'ago tana kallon shu yasa ya kashe mata ido d'aya.





Tashi tayi tsam ta bar wanke-wanken,Maleek ya b'ata fuska ya kalli Sadik yace"Haba yaya kaga ka hanani kallon ta,d'an rage zafin da nake daga nesa ka hana ma".




Bud'e baki yayi zai bashi amsa amma shigowar su Islam ya hana shi, duka mik'ewa suka yi suna tambayar" lafiya kuwa".




Hafeez yace"gashi, mun gode Allah ya saka da alkhairi,koba komai muna godiya da rik'emu da kuka yi kamar yan uwan juna",ya k'arasa yana mik'owa Sadik mukullin.






Da mamaki Sadik yake kallon su,gwaggo dake gefe tace"Amma wallahi Hafeez ka bani mamaki sosai,harda kema Islam, ashe zaku iya tafiya wani waje ku barmu? ".





K'asa suka yi da kai,Ita kuwa gwaggo fad'a take kamar wacce zata ari baki,Duk da dauriya irin ta Hafeez sai da hawaye ya zubo masa,Ballantana kuma Islam dake kuka sosai.






Ita kanta Ikhlas da hayaniyar su ta fito da ita hawaye take yi Iman ma haka,sadik kuwa zaka iya banbance yanayin da yake ciki ba,ya dai kafawa Hafeez ido ne.





Gwaggo ta warce keys cikin fushi tace"ku tafi Allah ya kiyaye hanya", Daga haka ta juya,Hafeez ya zube a k'asa yana hawaye me ban tausayi.




cikin kuka yace"gwaggo kiyi hak'uri ba zamu tafi bane domin wai abinda ya faru, zamu tafi ne domin gujewa magan-ganun mutane".




"Saboda zai fito muku a jiki ko? ",ta tambaya da alamun fad'a,k'asa yayi da kai,girgiza kai tayi tace"Hafeez ni a tunani na mun dad'e da zama d'aya, da ba dan su Sadik sun riga da sun kai mahaifin ku k'ara ba da duk hakan ba zata faru ba domin dama sai dana hanasu".






Hafeez yace"Kada kiga laifin su Gwaggo, ni da kaina na kawo shawarar a kai shi domin a hakunta shi".





Jinjina kai Gwaggo tayi tace"shine kuma abin zai dame ka,ka ajiye maganar mutane ka cigaba da rayuwar ka".






Hannun ta ya rik'e yace"shikenan gwaggo amma a gari nan waye zai auri k'anwata",murya a dakushe Sadik yace"brr bashir domin dama ya riga da yayi mini magana, ita ma kuma ta san dashi".






"Dauki jakar ki ki kai d'aki kinji, kai kuma ka cigaba da kneeling har fad'uwar rana",abinda Maleek ya fad'a yasa duka suka yi dariya.






Sadik yace"Dalla bar d'an rainin wayo mana, da kuwa na hana shi nabeelert naga ta tsiya",k'asa yayi da kai yana murmushi.







Haka yaya Hafeez ya d'auki jakar shi ya kai d'akin da yaya sadeek yake yana gwauro.




Su Ikhlas kuwa a ranar suke had'a kayan su domin wucewa Adamawa, duk da Maleek ba haka yaso ba amma gwara ya je can ayita ta k'are kawai.





Washe gari da wuri tayi wanka,murna take domin zata je wajen umman ta suyi firar su,wata dakakkiyar shadda blue ta saka.



D'aurin nan steps ta zauna ta nad'a gyale da takalmi duk farare ta saka hakama sark'a fasshion da bracelet sai agogo.




Tayi kyau sosai cikin doguwar riga gown, sallama tayi wa su Islam sannan ta fito,tare dasu yaya Hafeez ta same shi.




Tun da ta fito ya dena fahimtar abinda suke fad'i zuba mata idanu yayi yana jin wani magnet na furgar shi.




Gefe taja ta tsaya tana jan tsaki k'asa-k'asa,Maleek ya kalli su yaya Hafeez yace"kawai ku bari zamuyi waya",murmushi suka yi duka, shi kuma ya wuce.






K'ofar ya bud'e mata,d'an janye fuskar ta tayi, sannan ta juya idanun ta, tab'e baki sannan ta shiga.




Tsayawa yayi kawai a wajen domin yadda tayi ba k'aramin tafiya yayi dashi ba,Ikhlas ganin ya tsaya yasa ta kalle shi tace"muje mana".




Sai lokacin ya dawo hayyacin shi, ajiyar zuciya yayi sannan ya zagaya ya shiga yaja suka tafi.





Doguwar tafiya ce,ikhlas tafiya kad'an tayi mata barci inaga doguwa,ai tuni tabar naija๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ.




yana tuk'i yana kallon ta yana murmushi sosai tafiyar ke mishi dad'i,koda ya isa adamawa direct gidan shi ya wuce da ita.





Yana parking ya dube ta, a lokacin da alamu barcin ma dad'i yake k'ara yi mata, wayar shi ya ciro ya fara kashe mata poster.





Sai da ya gama sannan ya ciccib'e ta yayi cikin gidan da ita,a k'yayataccen bed d'in shi ya kwantar da ita.





Bathroom ya shiga yayi wanka,yana fitowa daga shi sai k'aramin towel a hannu yana goge ruwan kan shi.




Kallon ta yayi yadda ta kwanta ji yake kamar ya fad'a mata,murmushi yayi tuno drama da zasu yi idan ta farka.





Farar t shirt ya saka da wando three quater sannan ya koma kusa da ita ya kwanta,k'ank'ame ta yayi kamar wani zai k'wace mishi ita, a haka barci ya d'auke shi.






A hankali take bud'e idanu har ta sauke akan fuskar shi wacce suke facing juna,Ko ita ta san cewa Maleek miji ne na nunawa sa'a.




Hannu tasa ta shafo fuskar shi tana murmushi, caraf ya rik'e hannun yana murmushi.




Sannu a hankali ya bud'e idanun,winking ido d'aya yayi yace"haba Princess meye na satar kallo na?".






murgud'a baki tayi tace"ai nima naga ana satar kallon nawa",maleek yace"meye abin kallo a jikin naki? ".



Ba tare da wani tunani ba tace"abu da yawa mana",hannun shi ya d'ora saman kirjin ta yace"kamar nan ko", kasa bashi amsa tayi domin yadda tab'awar yayi tasiri a jikin ta.





Dama kwana biyu basu had'u ba,wai hakan ma da shamakin riga ina ga babu waya san kalar dad'in da zan ji? "Ikhlas ta fad'a cikin ranta.





Murmushin cin nasara yayi kafin had'e bakin su,Ikhlas kuwa wani dad'i take ji yana kaiwa har k'wak'walwar ta.





Sosai take taya shi wanda hakan yasa hankalin shi ya fara barin jikin shi,Cikin rawar jiki ya zuge zip din rigar ya cire ya wullar.





Dama babu bra a jikin ta hakan yasa ya kai musu damk'a,Ikhlas kuwa k'ara bank'aro k'irji take domin yadda take jin dad'in hakan.





Maleek kuwa sucking din su kawai yake mata,yayin da hannun shi ke zaga ko'ina na sassan jikin ta.




A wahalce ya fara zame pant dake jikin ta,magan ganun mummy suka fara dawowa kan ta, cikin sauri ta rike hannun.





Idanun shi yayi ja,da kyar yace cikin dashewar murya"pls Princess ki bani hak'k'ina wallahi ina cikin wani hali ki taimake ni".




Ita kan ta halin da take ciki tana buk'ata to amma kuma maganar da mummy ta gaya mata fa?.








Shi kuwa Maleek ganin tayi shiru yasa shi canza salo,Kissing din ta ya cigaba da yi yana romancing din ta wanda yafi wancan zafi.




Hakan yasa har yi take kamar zata shid'e,hawaye na gangarowa daga idanun ta,sai da ya tabbatar ya kashe duk dan ragowar karfin dake jikin ta sannan ya mik'e.






Cikin sauri ta riko hannun shi,cizar lip yayi yana murmushin mugun ta duk da shima a wahalce yake.






Kallo take bin shi dashi ta kasa cewa komai, domin babu bakin magana,A hankali ya kwace hannun shi ya juya ya shige bathroom.





Cikin bathtub ya shiga yayi shiru sosai yake son kasancewa da ita amma kuma tak'i bashi had'in kai.




Haka yayi wanka ya fito yadda ya bar ta haka ya dawo ya same ta,wucewa yayi ya canza kaya sannan ya dauki key.




Har ya juya zai fita sai kuma ya dawo,hannu yasa ya ciccib'e ta,Ikhlas kuwa ita kad'ai ta san halin da take ciki.





Jin ta rungume a k'irjin shi yasa ta k'ara lumshe ido, bata yi aune ba taji ta a cikin ruwa, wata irin ajiyar zuciya tayi sannan ta bude idanu.





Maleek duk da halin da yake ciki sai da ya kusa dariya, ganin kada ta gano shi ne yasa yayi saurin fita.




Sai da ya tsaya ya tik'i dariyar shi sannan ya fice, alhajr restaurant ya fara zuwa yayi musu take away sannan ya wuce modibbo suya spot ya siya musu kaza.



Haka ya siyo kayan tarkace su youghurt da su biscuits chocolates cookies etc.






Ikhlas kuwa sai da ta dad'e cikin ruwan kafin tayi k'arfin hali ta samu tayi wanka ta fito, tana d'aga rigar ta gaba d'aya tayi squeezing hakan yasa kamar tayi kuka.


Bud'e wardrobe din tayi, abin mamaki bangaren kayan mata daban yake,jinjina kai tayi sannan ta ciro wata doguwar riga brown and yellow.



Simple makeup tayi ta saka kayan, das suka zauna a jikin ta gashi sun yi mata kyau sosai abinka da farar mace *Alkyabbar mata*.






Wannan karon bata yi gigin tashi wai amsar kayan hannun shi ba,sai da ya zauna sannan ya kalle ta yace"Princess kin yi kyau".





Murmushi tayi kawai sannan ta d'auki ledar daya shigo da ita tayi kitchen, wa'inda zata saka a fridge ta saka wa'inda kuma zasu ci ta dauki plate ta saka a ciki.





Kan centre table ta ajiye sannan ta dauko ruwa shi dai Maleek da idanu yake bin ta, ita kuwa har lokacin ba gama dawowa dai-dai tayi ba.






Tare suka ci abincin ba tare da sunyiwa juna magana ba,sai dai satan kallon juna da suke yi.




Suna gama cin abincin Ikhlas ta kwashe kayan ta wuce dashi kitchen,tana fitowa ta tarar baya nan.




Kujera ta zauna tana kallon shirin da akeyi a arewa24,duk da rabi tunani take akan umman ta, dole ma yazo ya maida ta.




Maleek kuwa yana fita gida ya wuce,sun san dai ya dawo amma kuma basu san tare da Ikhlas yake ba.





Sai da yabi ya gaishe dasu sannan ya wuce ya koma,koda ya k'arasa tana zaune tana kallo.




Yanayin sallama ta kalle shi tace"dan Allah ka kaini gida",murmushi yayi yace"sai zuwa anjima", daga haka

Please Login or Register in order to submit comment