Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abuja yace"shikenan yaya hakan kawai za'a yi",daddy kuwa be ce komai ba sai dai kallon saifullahi da yake yi.


Haka shima saifullahin da maleek mahaifin nasu suka zubawa idanu,daddyn adamawa yaja hannun daddy suka fice.




Baffa ne ya riko saifullahi ya zaunar dashi yace"kuyi hakuri ku bi iyayen ku, kada ku bujirewa umarnin su".



Jiki a sanyaye suka daga kai,tashi suka yi, maleek ya rike hannun saifullahi gam domin gani yake kamar faduwa yake shirin yi.




A falon daneji suka same su, umma da mummy da hajiya rabi sai danejin duka suna zaune a hakan baza ka ce wai mummy suruka bace sai ka dauka duka yayan danejin ne saboda rashin nuna banbanci.




Mumny ganin yadda suka shigo, kowa fuska dauke da damuwa yasa gaban ta ya fadi, da sauri ta mike ta rike hannun su.


Ba tare da tace komai ba ya wuce dasu bedroom din daneji jikin ta har rawa yake yi,zaunar da kowannen su tayi gefen ta duka ta hada ta rungume su tana tambayar "lafiya meya same ku".




A tare suka yi ajiyar zuciya,saifullahi yace"mummy yau na batawa daddy rai",sakin shi tayi tana tambayar "me kayi mishi".




Maleek ya bata labarin abinda ya faru duka, ita kan ta jikin ta yayi sanyi, lallashin su ta cigaba da yi tace"na san mahaifin ku beyi fushi ba,ku bari zan same shi na bashi hakuri".



Daga kai suka yi suna murmushi, itama murmushin tayi tana shafa kan su,wato tun suna kanana haka suke idan daya yayi laifi to ji suke kamar dukan su suka yi.




Sai da suka ware suka cigaba da harkokin su, duk da saifullahi daurewa yake yi amma ji yake kamar za'a raba shi da wani bangare na jikin shi.




Cikin natsuwa ta tura kofar dakin, a tsaye ta tarar dashi yana kallon hannun shi, juyowa yayi ganin itace yasa ya cigaba da kallon hannun.



waje ta samu ta zauna kan tayi magana taji yace"aisha yau na mari saifullahi, da wannan hannun nawa daya daga cikin abu biyu masu mahimmanci a rayuwa ta".




Mummy ta matso kusa dashi cikin tausayawa domin ita kan ta sheda ce na irin son da yake yiwa yaran shi.




Dafashi tayi tace"daddyn maleek ya kamata ace ka gane cewa sayrin yanke hukunci cikin fushi bashi da amfani, amma tun da hakan ya faru ka dena damun kan ka akan hakan domin idan har sauran mutane da yan uwan ka suka ji zasu yiwa abin wata fassara, sannan sukan su yaran suna can sun damu sun ce na baka hakuri".




Kallon ta yayi idanun shi sun yi ja yace"kin gani ko mummyn maleek taya zan kwantar da hankali na bayan na san suna cikin damuwa,kada ki manta duk duniya su kadai nake gani hankali na yake kwanciya, muje na basu hakuri๐Ÿ™Š".




Da mamaki mummy tace"ka basu hakuri fa kace, gaskiya hakan ba zai yiwu ba, zan dai je nace musu ka yafe musu kawai amma wane kalar basu hakuri".



Tana fadin hakan ta juya ta fice, kamar yadda ta bar su haka ta dawo ta same su,suna ganin ta suka mike.



Suna tambayar ta"mummy yace ya hakura kuwa? ",murmushi tayi tace"eh ya hakura amma yace kada hakan ya kuma faruwa".



Ajiyar zuciya suka sauke a tare, sannan suka yi dariya suka rungume ta, umma da ta shigo tayi dariya tace"aunty wannan irin soyayya haka? ".




Shafa kai maleek yayi domin shi dai nauyin ta yake ji, a hankali ya zame ya fice daga dakin, mummy dake ankare dashi tayi murmushi kawai.



Dole saifullahi ya sauke damuwar shi domin farin cikin iyayen shi,sai dai fa idan ya zauna shi kadai yake shiga damuwa.




Maleek yace"ni dai a gani na ka gaya mata kawai, so that ta hakura kada fa taji a wajen wani".



"Hakane gaskiya zan kira ta a waya, ko kuma kai pls ka kira ka gaya mata, ko kaje kanon da kan ka gobe".



Tabe baki yayi yace"ka dai bani number din ta sai na kira na gaya mata",murmushi yayi sannan ya bashi.




Ikhlas na zaune gefe amarya hafsat ce wacce ta gama amsa wayar mahaifiyar ta dake ta faman yi mata fada akan me yasa taje kano ta zauna gashi daddyn ta gobe dashi da yan uwan ta na adamawa zasu taho.




Hakuri dai ta bata, bayan sun gama ne tace da ikhlas ita fa tare take so su tafi.


Ikhlas tayi murmushi tace"hafsat dole kiyi hakuri ki tafi ke daya domin kuwa mu tare zamu taho da beelert".



Da kyar tayi confessing din ta ta yarda akan zata tafi washe gari, su kuma sai su taho next week.





Ana haka wayar ta tayi kara, duba me kiran tayi, kamar baza ta daga ba ganin number din ko na waye.




Sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka,shiru tayi shima jin taki magana yayi shiru.




Ganin baza ta ce komai bane yasa yace"assalamu alaykum".




"Wa'alaykumus salam", ta bashi amsa,cikin sanyin jiki yace"kin gane mai magana".





"A'a waye ne?" ta maze domin bata so ya gane cewa tana da number din shi.




"Kanin saifullahi ne, maleek na kira ne domin na gaya miki cewa nan da two weeks bikin shi, sannan shi yace ba zai iya kiran ki ba saboda baya so ki kara neman lalata shi, and kada ki damu komai zai zo da sauki, ki taimaka ki bi wani mai tsautsayin amma yaya na yafi karfin ki, kada ki damu kome ake zan dinga turo miki events din da ake yi".



Daga haka yayi murmushi mai sauti, cikin dakewa tace"oh babu matsala ai allah ya sanya alkahiri, sannan bin wani kuma ai ya kare,ka sani ko a gobe naso kulla maka sharri zan yi, domin baby kai kadai ya sani a matsayin daddyn shi,kaga idan na bukaci wulakanta ka zan kawo shi har inda kake".




"Babu bukatar sai kayi wani dogon bayani,da kan shi idan ya kira ka da daddy za'a yarda dan ka ne,and kada ka damu zan turo maka da number ta da nake whatsapp da ita domin saukake maka wajen turo mini events din, wallahi ka sani tsane ka kamar yadda ka tsane ni, banza mata-maza".




Murmushin mugun ta yayi yace"zaki gane kin yi babban kuskure ranar da kika zo hannu na sai na tabbatar miki da ni cikakken namiji ne".



"Kada ka damu yayan ka ya riga da ya tabbatar mini da hakan, kasan yayan naka akwai jarumta, idan ya sami mace baya raga mata, especially irina da ta iya kula da namiji akan gado".




Ji yayi wani abu ya caki zuciyar shi, da sauri ya katse wayar yana maida numfashi"tabbas abinda ta fada gaskiya ne, idan akayi la'akari da yanayin yadda lovely ke shiga gidan ta babu excuse, ga itin kayan da take sakawa kuma hakan baya damun su".



"Ya ilahi! Yaya why? Me yasa ka fada rayuwar da bata kamace ka ba? ".


(To daman idan baki yasan me zai furta ai be san mai za'a maido mishi ba, maleek gashi an gaya maka abinda zai dame ka).




"Yanzu ya zanyi, idan ya zama karya ne ba, kai bazan iya tarar lovely da wannan maganar ba".



Gaban shi ne ya fadi tunawa da yayi da baby,kada dai ace dan lovely ne? Kai bazai taba yiwuwa ba, wata zuciyar tace mishi"baka ganin yadda yake kula da ita, da yaron baya gajiyawa".




Maleek kenan yake wannan magan-ganun shi kadai kamar mahaukaci sabon kamu.



Bangaren ikhlas kuwa tana kashe wayar ta fashe da kuka, tabbas dama bata saka a ranta wai saifullahi zai aure ta ba, kuma tana da tabbacin cewa abinda maleek ya fada ba haka saifullahi yace ba.




"Umma ina kike ne, kika barni ana faman yi mini kazafi", ta fada hawaye na zubo mata.





Daga cikin office din aka bata izinin shiga, tura kofar tayi ta shiga,kallon ta yayi yace"ya akayi ne nabeelert? ".




Mika mishi file din tayi tace"gashi wannan ne kayan da aka fitar dashi, shine na kawo kayi signing".




Amsa yayi yana signing din yana murmushi yayin da ita kuma gaban ta yake faduwa,yana gamawa ya miko mata.



Boyayyiyar ajiyar zuciya tayi sannan ta amsa,har ta mike zata tafi yasa hannu ya finko ta ya hada ta da jikin bango.




Gashin kan ta ya fizgo yana fadin"ina take?",tsabar shakar da tasha yasa ta kasa magana.





Cikin daka tsawa yace"ina munafikar da ta baki wa'innan takardun take, ina IKHLAS take, zakiyi magana ko sai na kaahe ki".






-to masu karatu shin nabeelert tana gayan inda ikhlas take ko kuwa bata fada?




-maleek yana tambayar saifullahi dan shi ne baby?




-taya umma ke haduwa da ikhlas?





-taya ikhlas ke kwatar nabeelert daga hannun abba kabeeru, sannan yaya documents din?.




-shin hafeez yana auren nabeelert ko kuwa dama ba son gaskiya yake mata ba?




*duk ku biyo ni domin jin amsoshin wa'innan tambayoyin*.





*gashi nan nayi muku typing biyu yau domin dai gobe da jibi kamar yadda kuka sani babu updates na gode*






*babyn abdul, haka kuma maman farouk da ilham insha allah, love you oll๐Ÿ˜˜*









๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

โœโœโœโœโœโœโœ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
โœโœโœโœโœโœโœ


*~โ„We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


*written*
-by-
*Deeja one love*




*๐Ÿ†JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ†




*Dedicated*

-to-
*Maryam khamis*





53-54






Wani abu kamar frame ya danna, kofa ta bude, duk da wahalar da beelert take sha be hanata jinjina da santin falo din ba,wulla ta ciki yayi sannan ya mai da kofar ya rufe.




Bubbugawa take iya karfin ta,komawa tayi ta zauna, tunawa da tayi da maganar da ikhlas ta gaya mata.




*FLASH BACK*


"To cat eyes shi meye amfanin wannan din", feenert ta tambaya.




"Kada ki damu, wannan agogon duk abinda ke faruwa zan dinga ganin ki, wannan kuma tracker ne,banda tabbacin inda zai kai ki, ta wannan ne zan gane inda ya kai ki".




Zaro idanu tayi tace"kina nufin zai gane kuma zai kama ni",murmushi ikhlas tayi tace"eh mana me kika maida abba kabeerun? Ya fi karfin tunanin ki, zai kama ki abinda nake so ya fahimta shine akwai takardun a hannuna kada ya sakankan ce akan cewa takardun iya na hannun shi ne".




Dafata tayi tace"kada ki damu, kwana uku kawai zaki yi a wajen shi, za'a fitar dake, sai dai ki tabbatar lokacin da zaki fita kin ajiye agogon da band din nan dakin".




Tuno hakan yasa ta jingina da jikin kofar tana ajiyar zuciya.



A kano kuwa, sai faman shirye-shiryen bikin hafsat,ikhlas kam da feenert duk sun gama abinda zasu yi, jira kawai suke nabeelert ta dawo domin su tafi.






Adamawa ma daddyn adamawa shi ya rike ango yace"babu inda zaka je, duk wani abokan ka dan uwan ka ya sanar musu da daurin auren".




Kamar be so ba haka ya amsa,tun lokacin be samu damar yin magana da ikhlas ba saboda hidimar da yake ciki.




Ita kuma ikhlas hidimar bikin hafsat yasa bata samu lokacin kira ba.




Abba kabeeru ne sai safa da marwa yake yi a cikin falon shi, tabbas idan yayi wasa hakin daya raina zai tsole mishi idanu.




Huci yayi yace"dama kenan ba original copy din bane yake hannu na? ".




Wayar shi ya danna sannan ya kara a kunne, cikin sauri yace"barr bashir ka shigo bauchi ina da bukatar ganin ka".





"Okay, idan allah ya kai mu gobe zan shigo,amma sai zuwa yamma domin ina da wasu ayyuka da zan yi".




"Babu matsala allah ya kaimu, ka tabbatar dai babu wanda ya san da zuwan ka".




Daga haka ya ajiye waya, hafeez yayi sallama ya shigo, cikin farin ciki abba kabeeru yace"son ya dai da wannan murna haka ko ta samu ne? ".




Hafeez ya shafa kai yace"wallahi eh dama abinda yasa nazo shine ina so naje zamfara zuwa gobe".



Dafa shi yayi yace"babu matsala allah ya kai mu, amma me yasa ka fiye son zuwa zamfara ne? ".




"Babu komai abba kawai ina da aboki ne a can din".




Murmushi uban yayi mishi, shima ya maida mishi daga haka ya fice.




Abba kabeeru ya kira hazard a waya yace"ina so ku saka mini ido akan hafeez gobe zai je zamfara ku tabbatar kuna biye dashi".








Washe gari, brr bashir ya sauka a garin bauchi, kiran abba kabeeru yayi yace"gani a star life hotel, kazo da wuri".




"Ka bani minti talatin domin kuwa yanzu haka ina da meeting da wani company".



"Ok babu matsala amma kayi sauri", daga haka suka ajiye wayar.




Ikhlas da dama tun jiya suka iso bauchi ta kalli feenert tace"muyi sauri feenerh yana star life hotel",cikin sauri suka fice.



Tana parking da motar, feenerh ta fito shigar da tayi da yanayin tafiyar ta sai ka tabbatar da cewa karuwa ce, a haka ta shiga reception din.





Ta kalli receptionist din tace"hello, dan Allah wane room brr bashir ya kama?.



Kallon up and down tayi mata tace"ke wacece? ",feenerh tace"his chick,yace nazo na same shi anan, na manta be fada mini room ba kuma na manta phone dina a gida".




"Ki koma ki dauko, domin bama bada details na customers din mu har sai idan shi yayi confessing, dan haka out"ta fada tana nuna mata kofa.



Har ta juya sai gashi ya fito, ta gane shine saboda ikhlas ta riga da ta nuna musu pic din su.




Tana fita ta dan tsaya a gefe,shi kuwa fitowa yayi domin shiga cikin gari,"hi"ta furta tana lumshe idanu.



Brr bashir idanu akan mata, take yaji wani abu ya ziyarce shi,da kyar ya iya daga mata hannu.




Dan sunkuyawa tayi wanda gaba daya kirjin ta yayo sama,mukut kaji ya hadiye yawu,ciin daburcewa yace"ya akayi ne yan mata?".





A hankali ta dan bankare tace"wallahi nazo wajen wani friend dina ne to kuma ban san room number din shi ba kuma wayar shi taki shiga".



Murmushin samun nasara yayi a zuciyar shi yace"tsuntsu daga sama gasashshe",hannu ya dora akan fuskar ta yace"mu shiga daga ciki kawai".





Hannun ta ya rike suka shige tare,ikhlas da take kallon komai tayi saurin kiran asp abdallah,suna gama waya text ya shigo.



Dubawa tayi *room 146* murmushi tayi tace"dan akuya kawai, dama duk yadda jaki yake sai yaci kara".




Asp abdallah yana isowa suka shiga tare,id card din shi ya nuna ma'aikatan wajen suka barshi ya shiga.



Dai dai kofar suka kwankwasa, yana kwance a couch idanun shi biyu amma babu damar magana.




Da sauri ikhlas ta dau waya tace"kana son budurwar ka kada ta mutu to kayi sauri kaje ka fitar da ita daga office din mahaifin ka".




Bana jin maganar na can bangaren, ita ta kuma cewa"ka tambayi kanwar ka islam ta zata baka wata takarda code kuma shine *19051886*".




Tana ajiye wayar ta kalli asp abdallah ganin fuskar shi a daure yasa ta tabe baki ta juya, shi kam asp sai da ya daure barr sosai sannan ya dauko wata allurar yayi mishi.




Brr bashir bakin shi yana budewa yace"ku sake ni mana,ikhlas dama kina da rai? ",kallon shi tayi tace"eh mana ina da rai".




Ajiyar zuciya yayi yace"kiyi hakuri da abinda ya faru, wallahi babu sa hannu na a ciki abban kabeeru shi yake aiwatar wa".



Mika mishi takardu tayi tace"yi signing anan",kallon takardun yayi yace"alhamdulillah lokaci yayi da zan sauke wani nauyi daya rataya akai na",amsa yayi babu gardama yayi signing din.



Ya kuma cewa"ikhlas ni zan iya taimaka miki wajen tura abban ku a court",ikhlas tace"hakane amma kada ka manta tare kuke aiki dashi".



"A'a wallahi, tun lokacin da abubuwan dake faruwa suka fara faruwa dama bana bayan shi,yanzu dai akwai magan-ganun da zamu tattauna ki bari zuwa gobe,kinga yanzu alhaji kabeeru ya kusa isowa".



Da sauri duka suka mike, ikhlas tace"to barr idan kun gama zuwa gobe zan kira ka sai na gaya maka inda zamu hadu".




Daga haka suka fice, ko a mota babu wanda yayi magana, ikhlas ta kuma kallon asp abdallah dariya ta kufce mata.



Steering ya daka yace"amma abinda kike yi ikhlas ya sabawa addinin musulunci ya za'a yi ki bari ta saka wannan kayan taje gaban wannan katon, da yayi mata fyade fa".




Murmushi tayi tace"asp kenan,ba gori ba ni lokacin da naje wajen kabeer a haka baka yi tunanin zai mini fyade ba, me yasa ka fiye son kan ka da yawa ne? ".





"Kuma da kake maganar na bar ta, idan ban bar ta ba waye zai je, ni dai ya riga da ya san ni, beelert kuma bata nan har yanzu".



Feenerh tace"wai ina mamaki,ya akayi kika samu takardun nan da brr yayi signing bayan kin riga da kin ba beelert su? ".



Kallon juna suka yi ita da asp suka yi murmushi, asp yace"my love kenan, ya za'ayi mu bashi original din, ai na san zai yi tunanin original sune a hannun shi, har sai mun shiga court sannan zamu fito da wa'innan".



Feenerh tace"wallahi kai da ita akwai baiwa da ace zakuyi aure ku haihu da ban san wane kalar yara zaku haifa ba".



Asp yace"rufa mini asiri wannan ai tafi karfi na, kece dai dai ni, a gama hidimar bikin hafsat a zo ayi tamu kawai".




Dariya suka yi gaba daya.










๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

โœโœโœโœโœโœโœ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
โœโœโœโœโœโœโœ


*~โ„We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


*written*
-by-
*Deeja one love*




*๐Ÿ†JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ†




*Dedicated*

-to-
*Maryam khamis*





55-56



Kan shi tsaye ya tura kofar ya shiga,abba kabeeru da yake hada takardu ya kalle shi yace"ka iso kenan? ".



"Eh na dawo, abba ina zuwa haka naga sai sauri kake yi ne? ".



"Eh akwai wanda zamu hadu dashi ne yanzu, amma bazan dade ba zan dawo", jinjina kai hafeez yayi sannan ya nemi kujera ya zauna yana fadin "to Allah ya kiyaye hanya".




Yana amsawa da ameen yana fita,hafeez na ganin ya fice yayi sauri ya mike,takardar da islam ta bashi ya dauko, zanen office din mahaifin shi ne, sai inda aka yi arrow.



Dai dai wajen ya duba, ganin karamin frame yasa ya matsa kusa ya danna, kamar da wasa kofa ta fito, ganin akwai code yasa ya tuna *19051886* yana danna wa kofar ta bude.



Falo hadadde yaci karo dashi,da sauri ya kalli cikin wajen, can bayan kujera ya hango ta da alamu ma abba kabeeru ya mata duka domin yadda jikin ta yayi shatin bulala.




Ga hannuwan ta da kafafun ta a daure, da sauri ya karasa kusa da ita ya kwance ta,sannan yace"am sorry dear wallahi ban san kina nan ba da tuni na fitar da ke".



Cike da wahala tace"babu komai ai",hannun ta ya rike sannan yace"muje,jikin curtain ta ga ya ja wani zare,glass din wajen ya bude.




Wata hanya ce yar karama ya ja ta suka bi, tafiya mai dan tsayi suka yi kafin suka iso wata karamar lifter, bude mata yayi ta shiga sannan shima ya shiga.



Suna sauka ya bude kofar wajen sai gasu a waje ta bayan company din, jinjina kai beelert tayi tana mamakin irin wannan wato dai alamun rashin gaskiya kenan.





Kallon ta yayi yace"abba ya kusa dawowa kuma nasan ta wannan hanyar zasu biyo dan haka ina so kiyi sauri ki fice,idan kika mike hanyar nan zaki fita bakin titi daga nan sai ki wuce wajen ikhlas".




Kallon shi tayi tace"na gode sosai,",murmushi yayi sannan ya juya ya koma ta hanyar.



Ganin ya bace mata yasa ta juya tabi hanyar, gudu take sosai, tana daf da fita bakin titi wata mota tasha gaban ta.



Jikin ta har rawa yake yi,glass din motar tinted ne dan haka bata ganin na ciki,bude baya aka yi aka sa hannu aka jata ciki sannan motar ta bar wajen da gudun tsiya.




Bangaren maleek kuwa duk wani abu daya kamata ace yayi ya aikata, bangaren gayyata da duk wani events da za'ayi idan an kawo amarya, sannan ya juya ya koma adamawa.




Bangaren amarya hafsat ma yau suka wuce adamawar domin dai aure ya kusa ya kankama,duk wani abu daya kama ta ayi to sai da tayi shi kan ta tafi adamawar.





Tun da taje take faman kiran su ikhlas, amma kodayaushe ce mata suke suna nan zuwa,yau ma tana zaune a falo ta kira ta.




"Dan allah ku taho haka mana, haba cat eyes so kike nayi ta zaman jiran ku ne",.



"Wallahi hafsat bawai naki zuwa bane,beelert muke ta jira har yanzu bata dawo ba, kuma hafeez ya riga da ya fito da ita".




"To ni dai dan allah da kun gama ku taho",insha Allah zaki ganmu as early as possible".






Umma tayi murmushi tace"amarya sai faman kira kike a waya, da alamu suna da mahimmanci ne? ".




"Wallahi hakane umma suna da mahimmanci sosai da sosai, amma nasan zasu zo ne, tun da har sun amsa".




Mikewa tayi tace"umma bari naje bangaren daneji na dawo", daga haka ta fice.




Maleek da saifullahi dake zaune saman mota suka hango ta,tun daga nesa saifullahi ya zuba mata idanu.



"Lallai hafsat ta girma sosai, ji yadda ta zama",maleek ya dube ta yace"lovely gwara kai kasan wacece matar ka nifa an barni sai bulayi nake yi".



Dai dai lokacin ta karaso kusa dasu, tace"sannun ku da hutawa", murmushi saifullahi yayi yace"yauwa sannu da fitowa,ke baki zumanci ko? ".




"Wallahi ba haka bane, kasan ayyuka sun yi yawa, kuma nima dai na dade banga kazo gidan mu ba".




"Oh tunda bama zuwa kema ba zaki zo ba kenan? ",maleek ya bata amsa.



"Haba lily ya zaka ce haka, ai ba ina nufin hakan bane",ta fada tana dariya.


"To yanzu dai ina auntyn tamu zata je",kallon hanyar tayi tace"bangaren daneji".




"Lovely taso mu kai ta dan mu baza mu yarda ki tafi ke daya ba", saifullahi ya mike.




Suna tafe suna fira, hakan ba karamin dadi yayiwa iyayen ba, kasancewar sukan wuce su, daidai balcony hajiya rabi ce ke tsaye gefen ta sadiya da bintu.




Da idanu suka bisu kafin hajiya rabi taja tsaki tace"wannan karuwan ci har ina daga zuwa an kama mannewa juna, waya sani ko tuni dama ana lekawa".



Babu wanda ya tanka mata, suka wuce hafsat tace"ni kuwa lily naji ance an baka mata".



Dariya suka yi gaba daya kafin yace"haka nima naji ana cewa",firar su suka cigaba hankali kwance.





Zaune ikhlas take gefen ta asp abdallah ne tare da feenerh,hafeez da kuma islam suma suna zaune a wajen, sallama brr bashir yayi musu sannan ya zauna.



Bayan sun gaisa yace"jiya kamar yadda na gaya muku,alhaji kabeeru yazo kuma nayi signing akan takardun hannun shi".




"Kada ka damu, ba original bane wa'innan, yanzu dai gaya mini abinda kake so ka gaya mini".




"Da farko dai,lokacin da alhaji sadik adam zai rasu ko ince za'a kashe shi,a daren yazo ya same ni,yake gaya mini yana ganin ana bibiyar shi may be kashe shi ake son yi dan haka ga amanar yara na nan ya bani, in inganta rayuwar su".




Ina kuka na amshi wannan amanar, a lokacin da

Please Login or Register in order to submit comment