Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya wuce ne ya kai 59 zuwa da 60 yana da Tarin gemi baki Mai Kyali kyalin Furfura kadan Shi ai Dan Malam ne kuma Duk wanda yasansa Tun Farin yasan sa da Gemu ne shiyasa wasu Mutanen da suka sansa a baya suke mai lakabi da SA'IDU MAI GEMU..!
cikin Lokaci ta kare mai kallo Kafin tace"Wlh Aba baka fara tsufa ba..Gemun ka fa baki ne bai yi fari ba irin na Baba malam..!
Tafada Har Fararan Hakoranta suka Bayyana Kauda kai yayi yana Danne yanayinsa kafin yace"Tashi kije..Kuyi shirin makaranta kada,ku makara..!
Da Sauri ta Mike tana Fadin"To Aba..!
Daga haka ta fice ya Bita da kallo Acikin Ransa yana Fatan kada watarana Amina ta zame mai Zakka da gaskem da bazai iya Da Jidalinta ba.
Ba wanda yamata mgana ta Dauki Tsintsiya ta Share gidan ta Fito da wanke wanke Lokacin da Hamida ta Fito ita da Hanne,bayan sun je sun gaida Aba da yaya suka zo suna Tayata Har suka gama suna gamawa Hamida ta Shiga Tiolet din Dakinsu sukayi wanka,Amina a Dakin Mamanmu tayi wanka ita da Hanne Yau Ya Zeenatu da Rigima tatashi Mgana Kdan sai ta fara Harara da Fada Amina tayi Dariya aranta tace"Su ya Zeena kwana nawa ne..!
Domin adokar Malam in aka Aurar dasu ya Zulahat suma za"a bama Manemansu Daman neman su Domin Daman akwai su Baba Malam da Aba sun sansu kune bazaku sani ba sai Lokaci yayi.
Su ya zulaihat wata Biyar da suka gabata aka bama Manemansu izinin fara ganawa dasu kuma Tunda Hanne tace mata taji ana mgana auran ya tashi..Ba adau Lokaci ba sukaji Baba Malam yace Rana kaza Daurin auran Da yinin Biki Daman komai na Bukata an Tanadar dashi
Bikin Amare Hudu ne za"ayi Ya Zulaihat Daga gidan Ya Sadiya yar wajen Anty Amarya Ya Aishan Hajiya Babba Ikram din Anty Uwa sune za"a Aurar dasu wannan shekarar kuma Dukkansu suna matakin Shekarar karshe ne a makaranta Dama wannan kowa ya sani Tundaga kan Iyalan gidanmu har Gidan Malam maza ne ke Karatu mai zurfi mace kuwa iya Secondary sai Karatun addini har matakin Sauka da Hadda za"a Aurar Dake in mijinki ya amince adakin ki sai ki Cigaba ammh agidan Mallam da Gidan Baba Sa"idu ba wacce ta wuce wannan Matakin.
Sama sama suka karya da Dankali da kwai da tea susan in suka bata Lokaci ya shamsu zai ce atafi a barsu makaranta bata da nisa dasu sosai ammh gabadaya yara da manya a School Bus ake kaisu.
Amina ce karshen shigowa Motar Hijabinta yasha Tattara saboda Rashin Guga Daman a Kujerar tsakiya suke zama su uku ita da Hanne da Hamida
Sanda ta Shigo sai da ya Shamsu dake Bakin Kofa ya rankwasheta yana Fadin"koda yaushe kece abaya..!
Aranta sai da tayi Allah ya isa tana ganin Akilu da Zubairu na Dariya bama wani fa Girmansu sukayi ba Kwafa tayi aranta tana Fatan samun wata Dama.
Tana ganin Sa"adatu na Hararanta itana ta maida mata kafin taje ta Zauna kusa da Hanne tana gyara zaman Jakarta wanda Qur"ani ke Ciki da Taujud sai Sauran Littafin Islamiya.
sabeeha ce ta ga tana kallomta Lokacin da Motar ta Fita Daga Haraban gidan Baba Malam Hararanta tayi kafin tace"Qurwata Kur..Wlh Aniyar kowa sai ta bisa..Amina dai nan bari wh badai Mutum ba sai Allah..!
Ya Zeenatu ce ta dago daga gaba Tana kallon Amina kafin tayi mgana Ya Umaimatu wacce bata da Cikakkiyar lafiya tana Fama da mtsalan junnu don ma ana Tsaye akanta saboda haka Tayi Deliying karatu Ashekaru ma ta Girme su ya Zeena kamata yayi tana Cikin su ya Aisha ammh Saboda Lalurarta yasa komai ya koma baya Bata zuwa makarantar Boko iyakarta jss3 Mallam yace ta daina zuwa.
Cikin Sanyinta tace"Amina ki bar mgana haka kina cikamin kunni..!
Tafada tana yamutsa Fuska Amina tamele baki tace ahankali.."Kaji Sauran Iska..!
Hanne kadai ta jita Ya Abida Tsaki taja Zatayi mgana Shamsu ya Juyo Daga gidan Gaba yana Fadin"Kun Damemu da surutu..In bazaku Duba Littafanku ba kada na sake jin bakin kowa anan..!
Duk da ya Aisha da ya Zulaihat suna gaba dashi ammh suna girmama juna..ya Ikram na gefe tana jinsuTak batace ba tana ta Duba Qur"aninta Ballatana ya Sadiya datayi kamar bata amotar....!

******
*A RANAR..!*
10:50am.

Madina na gaji na Fara Sarewa acikin wannan Tafiyar tamu..Haba abu Daya yaki ci yaki cinyewa..Shekera wajen goma sha muna abu Daya babu Riba na kasa samun abunda nake so nake kowani Lokaci kina Fadamin wannan karon zamu dace To yaushe..?gobe ko jibi..?ba Rana Madina kowani Lokaci aikin baya Tafiya Daidai na Fara Tunanin ko dai bani da Sa"a ne. ?ko kuma ban zo Duniya da sa"a ba ko kuma kila bani da kashin arziki ne..!

Bansan me ake cewa Dagachan bangaran ba Sannan ita kanta me wayar ba ganin Fuskarta nake yi ba ta riga ta juya ba waya ce rike a Hannunta tana mgana cikin Zafi da kuna..!

"Kullum sai kice na kara Hakuri..?Har zuwa tsawon wani Lokaci zan cigaba da Dauriya da Nade wannan Bakinciki na shekara da shekaru dake Cikin Raina..?Nagaji fa Madina na Fada miki..nayi babbn aiki kan Na samu abunda nake muradi aka Kuskure a karon Farko Madina..JAFAR naso ya zama Haka JAFAR naso Madina..Ba AMINA ba..Meyasa shi aikin ya kuskure kansa sai ya koma kanta .?kinsani bata Cikin Lissafina Domin ita karamar alhaki ce..Sai gashi Sakacinki da yarda Dake da nayi yasa Aikina ya Lalace Komai ya kare ban samu komai ba sai Wahala da Bakinciki Madina to me yayi min Saura..!?
Shuru ya kara Biyo baya kafin ta Daga hannu Cikin kaifin Murya tace"Kul..Dayyaba batasan Ja da baya ba..Madina yanzu aka fara wasan..Yadda nayi alwashin ta rasa komai sai ta rasa madina...Tun ashekarun baya nake fama da Kunar wannan Kaunar wannan Soyayyar dani ke gani acikin Idanuwana SA"IDU ji nake kamar na kashe shi na Wuta..Madina ki Dora aikinmu..Ba gudu ba ja da baya..!
Mu keda Nasara....Nasara tamu ce..
Hahahaaa..!!!!
Lokaci Daya tana Sakin Wata Dariya kafin Shuu kamar Walkiya tayi Saurin barin wajen batare datayi waige ba..!







*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo(Besty)Alherin Allah yakai miki a dukkan inda kike*

*Intelligent writer's asso*


*🅿️04*



Har cikin Haraban Makarantar Idi Direba ya kaisu,Mai Dauke da Babbar Haraba da jerin ginin Azuzuwa Sama da kasa makarantar bata fi shekara goma da samar da ita ba Sannan Filin na Baba Malam ne sannan Kungiyar izala reshen Jahar Gumel din suka bada kwangilan Ginata,
Ta samu kafuwa sosai da Jajircewan Baba Malam yawancin Malaman makarantar Dalibansa ne sannan Ana Biyansu albashi da Kudin makarantar da yaran ke biya ammh ana karawa Tunda ba Duka bane zai isa abiya kowa da kowa Nauyin makarantar da komai yana Wuyan Baba Mallam ne..!
Sannan akwai matakin Ajin yara akwai matakin Manya Tundaga aji Daya Har zuwa aji na Shidda Sannan akwai matakin Jss1 har zuwa 3 sannan akwai ajin Matan aure su kuma Daga 9am zuwa 12pm Na rana ajin da Su Ya Jafar suke koyawar shi da Ya Nasir in basu da wani aiki Alokacin.
Tun zuwansu kowa ya Nufi ajinsa Hamida da Hanne da Amina da Sa"adatu suna aji Daya ne,Sannan Ya Aisha da ya Zulaihat da Ya Sadiya da Ya ikram da Ya Shamsu suna Matakin karshe ne Wato Jss3 yayinda Ya Zeenatu da Ya Umaimatu da ya Abida suna Jss2 ne Akilu da Zubairu ke Jss1 sai Jawaad Da Sabeeha Dake aji Hudu a matakin Shashen primary.
Kamar yadda kowa ya sani ne Ranar asabar ake karban Haddan Qur"ani da Tajwid,Sai Washegari Ranar Lahadi ake karin karatu To aranar ma Amina bata kawo Hadda ba kame kame ta fara tama manta inda take.
Malam Amadu Shine Malaminsu na Qur"ani Mahaddaci ne sannan ya Taba cin gasan Qur"ani na Duniya Gabadaya,Sosai yake da Ilimi da Sanin ya kamata
Yana zaune Daga gaban ajin da basu wuce su Ashirin ba Mazan da matan Sanye yake da Jallabiya Fara da Hula tabani kaji Hadisi Jallabiyar da kadan ta wuce gwiwansa sannan Gemunsa zai kai kamu Biyu da Rabi baki Silif yasha gyara.
Ya kalli Amina Dake gabansa kan wani Benci inda duk wani Malami kema indai zai bada Karatunsa.
Cikin Tsausayinta Domin ta koma Abun Tsausayi yayi Dukan Har yagaji Amina bata Sauya ba.
Cikin Natsuwarsa yace"Amina Sa"idu kinsan Satin ki nawa baki kawo Hadda ba..?
Amina ta Dago Daradaran Idanuwansa ta kallesa Kafin tace"Kamar sati na Biyar kenan ko..?
Tafada kai Tsaye mamaki Daya take basa Bata jin kunyar kallon Mutum Cikin Idonsa sannan abunda ke Daure ma kowa kai in akazo Jarabawa itace Take doke kowa acikin ajin,Abun mamaki kuma ko wajen Jarabawar Haddar baki itace Overoll acikin Ajinsu Tiryan tiryan zata yi karatunta Cikin kwarewa da Tajwid din Da sukansu Malamai suna mamaki yaushe ta koya yaushe ta iya..?Ahalin har aka gama Team bata Fahimci komai ba Kullun sai an Fito da ita bata bada Haddanta ba Wlh su kansu suna mamakin Amina sun kuma yardan ma kansu Kirarinta na badai Mutum ba sai ta Allah.
Sauran Dalibai kuwa sai suyi ta cewa an yi Cucene ammh Amina me ta sani banda Rashin kunya da Rashin Muttumci.
Kai kawai ya Kada Kafin yace"Fita kofar aji kisa gwiwanki a kasa..!
Amina ta mike kai Tsaye ta Fice Tana Dariya Daman Wlh ta gaji da zaman Waje Daya tana Fita kamar abun arziki ta saka gwiwanta akasa agaban ajinsu sai Sauran azuzuwan Dake kusa dasu Hankalin Daliban ya Dawo kanta Kaf Daliban Makaranta Umar Ibn Khallad waye baisan Amina Sa"idu ba bama Dalibai ba,Hatta malamai Sun san dazamanta Musamman Malam Datti Wanda ke Rike da Mukamin Shugaban makarantar.
Har Wajen karfe Daya Lokacin da za"a Tashi Sallah kana Malam Amadu ya Fito ya samu Rigima Amina ta Hada wata yar aji Biyar ta Leko to tana mata Dariya Amina ta nuna kanta tace"Ni kike ma Dariya..?lalle bakisan wacece Amina ba..Ammh yau zaki sani..!
Dutse ta Dauka ta yi Saita sai a saman Goshinta ta window ajin sai kuwa goshin ya Fashe sai jini ta Fara kuka sai da Malam Lawali Dake ajinsu ya Fito yana ma Amina mgana ta Karkace baki tace"Dariya tamin..Ni kuma nayi mganinta..!
Ransa ya baci yayi mata Bulala goma ta Kakkabe hijabinta irin ko ajikinta Din nan ga yarinyar nata kuka sai da aka kaita Chemis aka mata Dinki Domin wajen yayi zurfi mgana Har gaban Malam Datti Shugaba me zai ce.. ?Daman ai Amina ce kadai mganarta ke zuwa yana Dawowa Jikar Malam ce yana jin Nauyi ya Koreta ko kuma yace zai Dauki mataki Lokacin da aka kaita Office din Malam Lawali yana bayani yana nuna goshin Adawiya Daya sha Plasta yace"Shugaba kalli yadda ta ji mata Ciwo..?infa baka Dauki mataki ba yarinyar sai ta fara aikata wasu abubuwan da watarana zai zo yafi karfi mu..!
Malam Datti na kallon Amina yana Nazarinta kwata kwata ba tsoro ko Karaya acikin Idanuwanta kyam Take kare ma kowa Dake Babban Ofishin Shugaban makarantar kallo.
Sai da ya gama karantar ta kafin yace"Amina Sa"idu meyasa kika Fasama Adawiya Bala goshinta..?
Sai da ta kallesa Ido na Cikin Ido kafin Tace"Yauwa Shugaba kai kadai kayi mgana mai kyau na Hankali..!
Malam lawali ya Rankwasheta asaman kanta yana Fadin"Au ni na marasa Hankali nayi ko..!
Tana sosa kanta tana kunkuni tace"Alqur"an ban yafe ba..Wuta balbal..!
Yana kallon bakinta yace"Me kikace..?badai zagina kike yi ba ko..?
Tana Juya Idanuwanta tace"Nifa cewa nayi kana da Hankali kama fi kowa ahankali a makarantar nan..!
Ta Karishe fada tana Sauke ido Daga gani Ba har ranta ta Fada ba Malam Datti sai da ya Murmusa kafin ya kalli Malam Lawali yana Fadin"Mallan kyaleta tayi mgana..!
Amina ina jinki..?kina sane da sai da Aka yima Adawiya Dinki a inda kika Buga mata Dutse..!
Amina tace"Kai don Allah..?naji Dadin haka gobe ai bazata kara ma Amina Dariya ba..Shugaba Daga malan Amadu yace na fito kofar aji na saka Gwiwiyona a kasa ta Fara lekoni tana mim Dariya batan Uba ke ni zaki ma Dariya..Humm baki sanni bane ni ko Jawaad Yamin Dariya Barar dashi nake yi ballatan Ke da babu Dangin iya bare na Baba..Na Rantse da Sarkin dake Busamin Numfashi da awaje ne tamin Dariyan nan sai na mata Dukan Mutuwa sai na Lahira yafita jin Dadi Shugaba..!
Ta Fada tana Hararan Adawiya dake kukan Wuya da Sauri tace"Karya take yi malam..!
Amina ta Zaburo tana Fadin"Ke wake karya..!Alqur"an ki kiyayeni..Bar ganin gaban Shugaba bamai hanani Sama da Fadi dake na fiki Jidali wlh..!
Shugaba ya Dakatar da ita yana Fadin"Ke Amina natsu..Ke Adawiya Fadi gaskiya kin mata Dariya ko A.a..?
Adawiya kanta na kasa ta Daga kai alamun Hakane nan Shugaba ya fara mata Fada yace ta bama Amina Hakuri Data bata Hakurin Hanci ta Daga tana Fadin"Na Hakura Tunda ko banza za"a je gida da goshi Ham..!
Tafada Tana Dariya sai da Shugaba ya Tsawarta mata sannan yasa itama ta bama Adawiya hakuri sannan ya Sallamesusu
Suna Fitowa bakin Office din Amina ta Bangaje Adawiya tana Fadin"Ke karki Dauka har zuciyata na baki Hakuri ne..Amina bata Nadaman kan abunda ta aikata kuma bazan taba Nadama ba..!
Tafada Tana Kada mata ido kafin ta wuce Damam an tashi Sallah zuwa inda suke sallah sannan tasan su Hanne nachan na Jiranta Adawiya dai bata tanka ba Daman ai tasan Amina tasu ne bata taba Hadosu ba sai yau.
Wani kebabbam Waje ne aka Maida inda ake sallah na Maza na gaba barayin mata na Baya koda Amina taje su Hanne duk sun yi Sallah suna Wata Baranda inda ake cin Abinci kowani Dalibi ana kawo mai abinci Suma Daga gidan Baba Malan Idi ke kawo musu nasu Kula Uku Daya nasu Ya Aisha Daya nasu su da su ya Zeenatu sai Daya nasu ya Shamsu ne.
Saida taje ta fara Sallar kana ta zo Inda suke cin Abincin Tana zuwa ba wanda ya Fara mata mgana sai itace ta Rike Haba tana Fadin"Naga yan Ubanci Hanne da Hamida ko ku Jirani nazo muci tare..!
Ta Fada tana Leka Filet din gabansu Jallop din Shinkafa ce taji Kifi Sosai,Hanne ce tana kai Loma tace"Wazai tsaya miki .?jidalin ke sai ke Amina..!
Su Ya Aisha suna chan gefe barayin manya su ya Zeena ne ke kusa dasu Tana Shirin zama Sa"adatu Dake gefe tama cin nata ita da Sabeeha tayi Tsaki kafin tace"Allah ya rabamu da Alfahari da jidali..!
Amina tasan da ita take Ranta ya baci Hanne ta Rikota ganin tana Shirin Tace Cikin Lallashi tace"Ki kyaleta Neman Rigima take..!
Amina ta Fizge Jikinta Tana Fadin"Neman Rigima..?to ai gidan Tatarar Dillah Sakeni naci Uban yarinyar nan..!
Da Karfi ta kwace Hannunta ta Mike Sa"adatu bata sani ba sai gani Tayi Anina ta Chakumota ta Mikar da ita Lokaci Daya tayi Wurgi da Filet din Abincin ya bare a wajen Cikin Zare ido Tace"Maimaita abunda kikace in ba Tsoro ba..!.?
Ayadda Aminan ke Huci Sa"adatu tasan bazata iya da ita ba Su Ya Zeenati Dake gefe ne suka taso dasu Hamida Cikin Fada ya Zeenatu tace"Miye haka Amina Sakar mata Hijabi..!
Ya Abida tace'Ko sai an saka miki Duka ne..!
Amina tace"Ta maimaita abunda ta Fada..In ba tsoro ba da yau Filin makarantar nan ta mana Kadan in na Fara Dukanki sai kinyi kanin Mutuwa..!
Sa"adatu ganin maceta sun zagayesu yasa ta Kwace Hijabinta tana Huci tace"Wake tsoronki..?Allah ya kyauta..Kuma sai kin Biyani abincina..!
Amina tace"In naki fa..?
Kai Tsaye Sa"adatu tace"Sai me kuwa..?yar bakin ciki..Dadin abun dai arziki ake ci..Abincim ma badaga gidanku akazo dashi ba..Sannan makarantar ai bata gidan Uban Mutum bace duk Tsiya dai Ta Gidanmu ce Jinin Bazanga..!
Tafada Cikin Isa da Gadara da kowa sai da ya tsaya yana kallonta Ya Abida ta Daka ma Sa"adatu Tsawa tana Fadin"bazaku bari ba ko..?bari na Kira shamsu shi ai kuna jin tsoronshi..!
Amina bata ma jisu ba Kirjin Sa"adatu ta Daka kafin tace"Abincin banza..Kashi kema kinsan bamu Rasa Abun da zamu ci ba..Sannan da kike mganar ta gidanku ce karatun ma na Gidanku ne..?aida na Gidanku ne da baki zo nan ba sai ki zauna agida chan a Koya miki..Bari kiji na Fada miki ni bana Alfahari da Kowani Gida kada Kice da Gidanku nake alfahari Har yau har gobe bana jin kunyar Nuna BABA SA"IDU amatsayin Ubana kuma Har Gaban Abada Amina Sa"idu Gusai Dashi nake ado..!
Sa"adatu tace"Hmmm..Naga dai ko shi Baban naku karkashin Baba Malan yake gidan Gonar da kike takama Dashi na Uba..!
Bata karisa ba Amina ta kai mata Duka a kanta tana Fadin"Kada ki kuskura kice zaki zagi Ubana..Domin zan yi Kaca kaca Dake..Duk jidalina ina Martaba Aba..Ina Daraja Aba ina Mutumtatasa..Ni bazan zagi Baba Malam ba kuma bazan taba bari Azagesa ba..Bambamci na Dake kenan nasan Darajan Manyana..Sakaryawa kawai..!
Tana gama Fadin haka ta Tureta sai da ta Fadi ta wuce Fuu sai hanyar ajinsu Su Hanne suka Bita da Kallo ya Abida tayi kafci kafin tace"Sa"adatu Duka abunda kika aikata....A kunnen Baba Malam..Kowa ya koma yaci abincinsa..!
Abincin da Amina bataci ba kenan Har ajin Hanne ta koma tana Rokon Amina tazo taci abimci tace bataci Sai da Hamida ta saka baki ne Amina ta Kalleta tana Fadin"In Hanne bata Damu ba bazan yi mamaki ba..Ammh ke Hamida baki da zuciya..Ai ko abincin yakai Cikin ki kya amayosa Domin ki nuna mata ba yunwa ke Damun mu ba..Ammh sai gashi ko ajikinki..!
Tunda ta Fadi haka susan ta Harzuka Shiyasa suka kyaleta har aka Dawo aji Malamin Tajwid ya shigo Malam ilaysu alokacin Amina tana Bencin su Zainab ce sai tatashi zata koma Wajen zamanta ita da Hanne da Hamida Inda Taga Mariya Muhammad ta zauna..!
Tana zuwa kai Tsaye tace tatashi ita kuma ta balla mata Harara tana Fadin"Bazan tashi ba..ai bamai kujera Tunda bada gidanku kikazo dashi ba..!
Amina tace"Haka kikace..?
Ta Daga kai Batayi mgana ba Domin itama tana da Tsiwa Hanne ta Juya tana Fadin"Mariya ki tashi don Allah..Amina ta fara zama anan da Safe..Bana son jidalinta..!
Mariya ta Bude baki Zatayi mgana kawai taji ta akasa Amina ta Zauna Daga chan Farko ta Dage iya karfinta ta Turo Kujeran sai da Mariya Dake Farko ta Fadi hannunta ya Bugu da kasan simintin ajin Dayasa ta saki Ihun zafi gabadaya Hankali ya koma kanta Harda Malam Iliyasu.
Da Sauri ya mike ya kariso yana Fadin"Subhanallah me ya sameta..?ku kamata..!
Su Hanne suka mike suka kama Mariya Dake kukan Hannunta zuwa Kujeran gabansu suka zaunar da ita Amina ko ajikinta Cikin Mamaki yace"Garin yaya ta fadi..?
Da Sauri Sa'adatu tace"Amina Sa"idu ce ta Turota Daga kan kujera..!
Tafada Tana Hararan Amina da ko kallo bata isheta ba.
Mallam iliyasu ya kalli Amina a Harzuke yace"Ke zo ki fita. bana son Rigima kina jina ko..?
Amina batayi gaddama ba ta mike Harda Daukan jakanta ta fice Tana wani Hura Hanci ya Bita da kallo kafin ya Kada kai afili ya Furta"Allah ya shirya. !
Da sauri Hamida da Hanne suka amsa da Ameen Domin su kadai ne In Amina ta Dibo Jidalinta yake karewa akansu Saboda sunfi kowa kusa da ita.
Bata kuma koma ajin ba sai dai ta tari Islamiya kafin shima atashi sai da sukayi Tsiya da Samira tana Rubutu Daga ta mata mgana ta Dauki Littafin ta yaga suka Fara Fada da Chachar baki sai da aka kai su waje Dagachan da akaji abunda ya Faru Amina ce ba gaskiya aka sakata wankin Bayi batayi ba tadai je ta watsa ruwa ta kusa Rabin Bayin da Ruwa Dayake Inda Ruwan ke wucewa ya Lalace ya toshe Tana ganin haka ta Dinga kai ruwa sai da tayi Rabi Dashi ba Domim ma ta gaji ba ga yunwa taso ne ta Cika Tiolet din da Ruwa gobe ma su kara Sata aiki.
Aranar da suka koma Gida Hamida ta bama Mamanmu Labarin Fadan Amina da Sa"adatu mamanmu ta rike baki Tana fadin"Lalle yarinyar nan bata da kunya..Kuma kalaman ba nata bane na Uwarta ne..Kin Burgeni Diyata gwara da kika fadamata haka..!
Yaya na jinsu batace kala ba Tana Kofar Dakinta Lokacin bayan Sallar mangariba ne suna baranda Dukansu saboda Zafi ba wuta sannan kuma ba"a Riga an kunna inji ba.
Ya Zulaihat nadaga gefe tace"Mamanmu kada fa kiga Laifin Sa"a..Amina ce mai laifi koma Meya faru ita tajawo..!
Mamanmu ta Harareta Kafin tace"rufemana baki me kika Sani..?Uwar Sa"adatu yadda take kishi Damu ai bazai Fadu ba..Bata da yadda zatayi da Aba dinku ne Tare da Malam ammh da Tuni ta rabasu..Bari Aba Dinku ya dawo zan Fadamai bazan Dauka ba..Bazan Dauki arika Cin Zarafin Diyata ba..In ta kama Malam Din yaji sai ayi mana iyaka da ita da ya"yanta Tunda bata da Mutumci..!
Ba wanda ya kara mgana Sanin Halin Mamanmu in ta fara Fadan kan Amina bataji bata gani,Aminar batace komai ba abincinta take ci yunwa take ji Sosai,Jidalinta yafi Tashi ne inTaci ta koshi
Hanne tatafi gida Domin Laifin Sa"adatu ya Shafeta Tana Ma Amina Mgana tayi kamar bata jita ba Abida ita ta Fadama Hajiya Abunda yafaru Ran Hajiya ya baci ana Falon Malam ana cin abinci Tace Abida ta maimaita abunda ya Faru yau a makaranta Ran Baba Malam ya baci matuka Anty Amarya ta Bude baki zatayi mgana ya Daka mata Tsawa.
Nan take yasa Shamsu yayi ma Sa"adatu Bulala goma lafiyayyu da Jan kunnen in aka kara jin mgana makamancin wannan abakinta sai ta gane kuranta awajen Baba Malam ya kalli Matansa Cikin Kaushin Murya yace"In ma acikin ku akwai wacce take Kitsa ma ya"yanta Sa'idu bakomai bane a wajena Tayi kuskure..Sa"idu D"a na ne..Shine Babban yarona sai da na Sameshi na Samu UMAR..!
Sannan nan gidan da Gidan Sa"idu Duka abu Dayane ya"yansa Jikokina ne..Har Abada..Kamar yadda ku da ya"yanku kuke da iko da Gidan nan da Dukiyata da ni kaina kuke alfahari dani Haka Sa"idu da yayansa zasu yi Na Rantse da Allah in na kara jin wata mgana mai kama da wannan Dukkanku Daga ku har ya"yanku sai naci Mutumcinku..!
Ku tashi ku bani waje mutanen banza Ke Sa"adatu ban gama Dake ba..Ki Taka kije har gida ki bama Mamana Hakuri in ba Haka ba Wlh sai na maidake Kauye nayi miki aure kinji ma na Rantse tashi ki bani Waje..!
Ya karishe Fada Ransa na kuna da wani kunya da Nadama yaya zai ji in Sa"idu yaji wannan mganar Tun bayan Haduwarsa da Sa"idu bai Taba ganin Daraja da kima kamar yadda Sa"idu ke ganin kimarsa ba ko Umar baya masa Biyayya irin yadda Sa"idu yamai dashi komai nashi ba..Shekaru nawa ya kwashe yana gina Iylansa Domin su zama abu Daya ammh ya Fahimci akwai babban baraka barakan in da ta barke baza tayi masa Dadi ba ya zama Dole yayima Abun Tufkar Hanci Ransa yayi Mummunar bacin da ko matansa sun Dade basu gansa Cikin wannan yanayin ba.

Sa"adatu kuka ta saka ma Anty Amarya Tana Fadin"Anty ki bama Baba Hakuri kada yakaini Kauye..!
Anty Amarya Farar mace alkyabban Mata itace kadai mai kananan Shekaru acikin Matan Baba Malam faman Zagaye take a Tsakiyar Falonta Ranta ya baci meyasa komai sai Sa"idu da Ahalinssa ta tabbata ko Yayan Daya Haifa da Cikinsa Mallam bai musu soyayya kwatankwancin yadda yake kaunar Sa'idu da Iyalansa .!

SA'IDU....SA"IDU..SA"IDU..!


Halitta kwara Daya da Tun Shigowarta Rayuwar Malam ya Hanata Rawan gaban Hantsi komai na Mallam din kafin ya"yansa suzo agaba Sa"idu ne kan gaba meyasa haka..?Tasan itama ta fito Daga gidan Manyan Mutane kakanta Shehin Malami ne kafin Rasuwarsa Malam kamar Dalibi yake garesa Duk garin Dutse ba wanda baisan Malam Armaya"u ba Shine ya Haifi Mahaifiyarta,sannan shi ya Daura mata Aure da Malam lokaci Rayuwarsa Duk da itama Tana ganin Baba Malam din a Talabijin yayi mata Duk da ya kasance ya Manyanta ammh bata Damu ba azatonta zatazo Tayi Mulki sai kuma taga akasin Haka Bamai iya Mulki agidan Baba Malam Suna Biyu ne ke yawo Daga na SA"IDU sai na HAJIYA BABBA..!
Suna da matukar Tasiri a Rayuwar Baba Malam din..

Sa"adatu ce ta kara kallonta yadda tayi Zurfi wajen Tunani Kafarta ta taba Tana Fadin"Anty baki ce komai..?
Dayake Tun zuwanta gidan Anty Amarya ake cema yasa bayan ta Haihu Sunan yabita har bakin ya"yanta.
Anty Amarya ta Sauke ajiyar rai kafin ta koma kan Kujera ta zauna Kusa da Sadiya Dake kallonsu kala batace ba Daman ai bata da Hayaniya.
Sabeeha na gefe itama ta Damu da ganin Sa"adatu na kuka.
Kanta ta Dafe kafin ta Dago Tana Fadin"Mafita dayace..Kiyi abunda yace..!
Sa"adatu tace"Naje na bama Amina Hakuri Anty..?
Kai ta gyada mata kafin tace"Eh haka nce..Kinsan Waye babanku..Tunda ya Rantse bazai Sauya mgana ba..kuma bazai Fara kaffara Saboda ke ba Sa"adatu..!
Sa"adatu zata sake mgana ta Daga mata Hannu lokaci Daya tana Fadin"Kiyi abunda yace..Koma meya Faru ke kikaja..?Amina..Amina wannan Shegiyar yarinya kinsan yadda Babanku ke Somta baya ganin Laifinta me yasa kika Biye mata..?kin ja An Tozartani gaban Kishiyoyi Kin

Please Login or Register in order to submit comment