Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Compiled By Umar Dalha Funtua.

Copied By Zulyheart Rano

[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

```Wannan page din sadaukarwa ne ga MARYAMERHABDUL (KWAISEH), fatan Alhairi na ke maki a dukkan rayuwar ki, Ubangiji ya kareki daga sharrin makiya da masu yi maki hassada, Wallahi Allah ina kaunarki har cikin raina, Allah ya kara maki basira da kafin k'wak'walwa.

Ina yinki sosai marubuciyar DUHUN DIMINA```😍😍


_*MY BESTY KHADIJAH S MUHAMMAD, HMMMM BA SAI NA FADA MAKI IRIN SON DA NAKE MAKI BA, DON KE DIN SHAIDA CE*_💞

*27*

Wani sansanyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe ido ya buɗe su fes a inda yake, sosai ya ke jin dadi na kewaya duk ilahirin jikinsa a fili ya furta

"Alhamdulillah! Na sauka a kasar haihuwata Nigeria kasar mu ta gado."

Duba ya kai ga agogon da ke manne a hannunsa, in da ya nuna masa karfe biyar harda mintina, sanye yake cikin kananun kaya wanda suka amshi jikinsa, ya yi kyau a ɗan zaman da ya yi na kwanaki bakwai a can, ji ya ke kamar ya yi tsuntsu ya gansa gabanta, babu abin da yake buk'ata a wannan lokaci sai ganin kyakkyawar fuskarta da daddaɗar muryarta, murmushi ya sauke ma kyau a fili ya ce

*I LOVE YOU AMEESHA*

Muryar direban su ne ya sa shi dawowa da hankalinsa sa kan shi, murmushi ya saki tare da fadin

"Har ka iso?"

"Eh! Yallaɓai."

"Madallah! Mu je kawai."

Shigo ya yi cikin motar, sannan direban ya ja, mintina ƙalilan suka isa gidan, a parking space direba ya faka motar sannan ya fita, da sallama ya shiga falon

"Assalamu Alaikum!"

Mummy da ke kai komo tsakanin falo da kicin ta amsa masa

"Wa'alaikumus salam! Barka da isowa NAJEEB."

Murmushi ya saki yana ci gaba da takawa har inda Mummy take, ya ce

"Yawwa Mummy na, *I miss you* ."

" *I miss you too my son*" Mummy ta faɗa cikin jin daɗi.

Zama ya yi akan kujera ya soma gaidata, da kulawa ta amsa tana tambayarsa yadda ya baro garin

"Ka ga kar ka zauna surutu, ga dukkan alamu akwai yunwa a tattare da kai, don haka tashi ka yi wanka sai ka zauna cin abincin."

"Wallahi kamar kinsan na yi missing ɗin abincin ki mai daɗi, bari na fito wanka sai na zauna." Ya yi maganar yana soma tafiya.

"Najeeb! Mummy ta kira sunan sa.

Dawowa ya yi yana faɗin " gani mum."

"Ka bar wankan nan, bari na hada maka kawai ka je da shi gidan ka, tunda yau kwana biyu kenan da aka kai maka amarya kuma ba ka nan."

Kallon Mummy ya yi mamaki kwance a fuskarsa ya ce

"Mummy Ameesha ta tare ne?"

Girgizar kai ta yi ta ce ya zauna, zama ya yi duk jikinsa ya yi sanyi, nusiha Mummy ta fara yi mu mai tsuma jiki

"Kana ji ko Najeeb! Ina so ka yadda da komai na duniya sai da Allah ya tsara shi, ka yadda wani ba zai taɓa auran matar wani ba, haka duk inda ka kai ga son abu matukar ba Alhairi ba ne bazaka taba samunsa ba, ka yadda Ameesha ba matarka ba ce, Rufaida ce matarka ina son ka yi hakuri da canjin da ka samu." Mummy ta dakata tana kallon wani yanayi Najeeb ya shiga, sai ta ga ya saki murmushi ya ce

"Mummy na fahimci inda nusihar ki ta dosa, wallahi na yadda da kaddara kuma insha Allahu ba zan bijirewa ikon Allah ba."

"Yawwa ɗan albarka, Allah ya yi maka albashi ya baka zuri'a dayyaba."

"Amin." Ya amsa cikin ɗan dariya, duk da zuciyarsa tana kuna da rashin Ameesha, sai dai hakan ba zai hana shi kula da Rufaida ba domin kuwa ita ce farkon masoyiyar sa.

"Mummy haɗa min in tafi." Najeeb ya yi maganar yana mik'ewa tsaye.

Tashi Mummy ta yi tare da nufa kicin ɗin, sai da ta haɗa masa komai sannan ta kawo masa, tana faɗin ƙasa Rufaida ta ci abinci da yawa, domin na kulla bata son cin abinci." Da yake tunda aka kai Rufaida kullum sai Mummy ta aika mata da abincin.

"Insha Allahu Mummy zan sanyata."

"Yawwa to ka gaidata, idan ka huta ko zuwa jibi ne sai ka kawo min ita." Don lokaci ɗaya Mummy ta ji son Rufaida, domin dai Allah ya yita da nutsuwa ga kunya.


******

Dr yana fita gida ya nufa, lokacin da ya shiga falon babu kowa, don haka bedroom ɗinsa ya shiga, shirin wanka ya yi cikin sauri sauri, bai wani jima da shiga ba ya fito, shiryawa ya soma yi cikin wasu kananan kaya wanda suka karbi jikinsa, sosai kayan sun yi masa kyau jikinsa yana fitar da wani sansanyar kamshi mai sanya nutsuwa a jikin dan Adam.

Rigar kalar ja ce an yi mata rubutu da kalar golden *Special one* sunan dake manne a jikin rigar kenan, ya yin da wandon kuma baƙi ne, wayoyinsa ya kwasa tare da key ya yi waje, har ga Allah ya manta da wata Aneesa, don burinsa kawai ya yi arba da Ameesha farin cikinsa, motsin da ya ji shi yasa shi saurin waigawa

Gabansa ya yi mummunan faduwa ganin yadda fuskar Aneesa ya kumbura, cikin sassarfa ya k'arasa inda take yana faɗin

"Anee lafiya?" Ya yi maganar yana kai hannu jikinta.

Harara ta watsa masa tare da kaucewa don bata son hannunsa ya sauka jikinta, juyar da kai gefe ta yi ranta yana tafarfasa ji take kamar zuciyarta zata faso waje muryarsa ta kuma shiga kunnenta

"Tambayar ki fa nake yi, ni yanzu bani da yancin taɓa jikinki kenan?"

Da masifa ta kalleshi ta ja tsaki tare da tabe baki ta ce

"Ina ruwan ka da lafiyata, maganar taɓa jiki kuma ai ina ga ka yi sabuwa sai ka je ka ci gaba da taɓa nata na bar mata, yanzun ma wajenta ka nufa ko? Wai don Allah Hamma dama haka kake ko kuwa dai zumudin amarya yasa haka?" Cikin kunar rai ta k'arasa maganar.

Murmushi ya saki ya ce

"Bari na dawo zan baki amsa, amma Please ki daure ki bar kuka haka, ki dubi yadda kika koma fa?

"Ina ruwanka da yadda na koma? Duk yadda na zama ai ina ga ba matsalar ka ba ce ko?"

"To ki daure ki ci abinci, kar ulsa ta kamaki."

"Ba ulsa ce zata kamani ba typoid zaka ce, kaga Hamma bana son *kankamba cirani ba miji a tafi ba ciki a dawo da goyon* ba zan ci ɗinba." A fusace ta dire maganar.

Girgiza kai ya yi cikin takaici da halin Anee, karin maganar ta ta karshe ce ta bashi dariya, har ya kusa yin dariyar sai ya yi saurin kumshe dariyar don kar ya kuma kular da ita sai kawai ya fita, tana ganin ya nufi fita ta ruga ɗaki da gudu bedroom ɗinta tare da sakin wani kukan.

Shi kuma yana fita motarsa ya shiga tare da bata wuta cikin gwaninta da kwarewa yake juya kan motar, har ya isa unguwar su Ameesha, farin ciki ke kwarara zuciyarsa har ya ɗan gana da get din yana hon maigadi ya buɗe masa, shi kuma ya cusa hancin motar cikin gidan yana gaida maigadin.

A parking space ya faka motar ya fito, jingina ya yi tare da harde hannunsa a kirjinsa yana tasbihi ga Allah, a hankali ya zame hannunsa ya zaro wayarsa ya yi dailling Number ɗin ta,

Lokacin wayar tana hannun Meena don ita ke amfani da shi, ganin Number din babu suna sai ta yi kamar kar ta ɗauka, har tana daf da katsewa sannan ta dauka

"Hello."

"Assalamu Alaikum! Dr ya faɗa yana gyara tsayuwa.

Amsawa Meena ta yi tana dan zaro ido jin muryar kamar ta Dr. Maganar sa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta faɗa. "Meena Dr ne gani a cikin gida, ki yi min iso a wajen Ummi."

"To." Meena ta amsa tana nufa bangaren Ummi, a falo ta samu Ummi Ameesha ta yi filo da cinyar Ummi ɗin, zama ta yi kusa da Ummi sannan ta ce

"Ummi Dr ne fa yazo!

Murmushi ta saki tare da shafa kan Ameesha ta ce

"Barkan shi da zuwa, a kawo shi nan bari in koma bedroom ɗina." Ta Kai karshen maganar tana mik'ewa.

Meena ma hannun Meesha ta ja tana fadin

"Mu je ki shirya tarbar Dr ga shi can a harabar gida." Tana maganar ne suna tafiya, suna shiga bedroom din Ameesha, Meena ta fara gyara mata kwalliyar fuskarta, domin bata wani dade da yin wanka ba, ko kayan jikinta bata canza ba domin dai doguwar riga ce baka, wacce ta sha adon duwatsu, sosai rigar ta yi mata kyau dankwalin rigar kuma aka yi mata rolling ɗinsa akanta sosai ta yi kyau.

Turaruka masu sanyin kamshi Meena ta feshe mata jiki da shi, kai masha Allah gaskiya Ameesha ta haɗu iya haɗawa, takalmi ta dauko mata shima baƙi, Meesha sai murmushi take yi don ita kanta tasan ta haɗu balle kuma shi ogan ya ganta. Sosai Meena ke kula da lamarin Meesha, duk wani abu da tasan Meesha tana yi a lokacin da take cikin tunanin ta, shi take mata. (Allah ka hadamu da kawaye na kwarai ameen).

Rike mata hannu ta yi har suka shiga falon, tunda Dr ya daura idonsa kan Ameesha ya kasa saukewa, domin ba karamin kyau ta masa ba, sai yaga kamar yau ce ranar da ya soma ganinta.

Ita ma Ameesha ganin yadda ya kafeta da ido fuskarsa da murmushi i it din ma ta sakar masa, kallon su Meena ta tsaya yi domin sun bala'in burgeta, Meesha tana isa inda Dr yake sai ko ta faɗa jikin sa tana faɗin

*"SWEETY ASMAD?"* Domin ta rike yadda ya ce mata rannan, sai dai ita da sigar tambaya take maganar.


_Nafee Ankerh korafi_☹

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username *ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_*Wannan page din sadaukarwa ne ga NAFEESA ANKERH (mr korafi) na sadaukar maki da shi ki yi yadda zaki yi dashi idan ma kika ce kar kowa ya karanta wannan ikon ki ne, ni dai kawai a barnin in inke yin typing a time da na samu dama hhhhhhhhh!, Fatan Alhairi a gareki Zulayheart Rano tana yinki sosai*_ 😍😍

*28*

Daddaɗar muryarta ne ya ratsa kunnuwansa, musamman yadda ta faɗin sunan sai ya ji ta saukar masa da kasala, dadingushi kuma yadda ta lafe a jikinsa, sai wani feeling wanda tunda yake da Meesha duk fadawa jikinsa da ta keyi, bai taɓa jin irin saba, gyara mata zama ya yi a maimakon da da yake zameta daga jikinsa ya ce

"My Meesha ya ki ke?"

Bata ce komai ba sai lumshe ido da ta yi, fuskarta har yanzu da murmushi, Meena kam tsayawa ta yi tana kare masu kallo don yadda Dr ya yi ko wanda bai san SO bane ya gansu to zai iya shaida su ɗin masoyan junane, murmushin farin ciki ta yi a ranta tana faɗin

"Alhamdulillah! Ashe Dr ma yana son Meesha Amma wannan abu ya min daɗi."

Ganin hankalin Dr yana ga Ameesha bai masan da wata Meena ba sai ta ɗan gyaran murya ta ce

"Dr ina wuni! An daura aure lafiya?"

Wata kunya ce ta kamashi, don da farko yaga lokacin da suka shigo tare da Meena ɗin, amma tunda Meesha ta matsa inda yake sai ya manta da komai ya maida hankalinsa kan Ameesha.

"Lafiya lau Meena ya kuke?"

"Duk muna lafiya." Ta bashi amsa tana tafiya.

Meena tana wucewa ya maida hankali kan Meesha da ke ta daddana wayar Dr ɗin. Ya ce

"My Meesha zaki bini gidanmu?"

Da sauri ta daga kai alamar "eh!"

Murmushi ya yi ya ce "to bari Abba ya dawo, sai na kaiki wajen Nenne ku gaisa." Ya ida maganar dai dai da zuwan Meena, abin motsa baki ta shiryo masa.

"Thanks Meena sannu da k'ok'ari."

"Your are welcome!" Ta faɗa tana tafiya. Shi Dr tunda Ameesha ta wanzu kusa da shi sai ya nemi yunwa ya rasa, don kasancewarta kusa da shi ba karamin farin ciki ne a gare shi ba.

Kallon ta ya yi tana ci gaba da danna wayarsa, cikin zuciyarsa fadi yake

"Ina ma ace Ameesha tana cikin tunanin ta aka daura masu aure! Lallai yasan da ace tana tunanin ta, to yau da abin ya fi masa jin dadi, amma a haka ma yana farin ciki, yana godiya ga Allah."

Dr ya manta da komai ya dauki lokacin da kacokan ya dankawa Ameesha, sam ya manta a gidan surukai yake, soyayya kawai yake nuna mata irin mai tsayawa arai dinnan, ya yin da ita kuma ta wani lafe a jikinsa kamar wani ya ce zai raba su, bai tashi farga ba sai da ya ji kiran sallar magriba, ɗago da ita ya yi yana faɗin

"Meesha time for prayer, zan je masallaci."

Da kallo take binsa don bata fahimci inda maganar sa ta dosa ba, ganin zata bata masa lokaci har ya rasa jam'i yasa ya kira Meena yana sanar mata to zo ta tafi da Meesha, babu bata lokaci sai gata, da wayau Dr ya samu ya guje mata.

****

Aneesa kam tana shiga dakin wani sabon kuka ta fashe da shi, zuciyarta tana wani irin zafi tana jin kishin Dr fiye da komai, zata iya yin komai don ta hana Dr zama da amaryar sa, yadda take kukan Ni kaina sai da na tausaya mata, don *kishiya ko ta kashin dankali ne babu daɗi* balle wacce aka auro don ku zauna a karkashin inuwar mutum ɗaya.

Ganin kukan ba shi ne solution ba sai ta jawo wayarta tare da dannawa Rukky kira, bugu biyu kuwa Rukky ta amsa

"Hello k'awata!" Rukky ta faɗa tana gyara wayar a kunnenta.

Shiru Aneesa ta yi har sai da Rukky ta yi magana sau uku kana ta iya sauke nannauyan ajiyar zuciya ta ce

"K'awata babu lafiya fa!"

Zaro ido Rukky ta yi kamar Aneesa tana kallonta baki har yana rawa ta ce

"Mai ya faru? Da ga jin muryar ki nasan babu lafiya faɗa min mai ya sameki?"

"Dr ya yi aure." Ta yi maganar cikin rawan murya.

"Aure! Kan uban... Rukky ta mulmulo wani katon ashar, ke Aneesa anya kuwa kin san me kika faɗa min?"

"Ce maki na yi Dr ya yi aure." Wannan karon tare da hawaye maganar ta k'arasa fitowa.

"Amma kuwa an yi mara mutunci, yanzu don Allah duk son da kike masa shi ne zai saka maki da kishiya? Lallai na yarda da ake cewa *namiji dan kunama* to ke yanzu wane mataki kika ɗauka?"

"Hmmmm! Wane mataki zan ɗauka kuwa, Nenne ce fa da bakinta ta sanar min da maganar, abin takaici ma wai har yau kwana biyu da ɗaurin auren fa, saboda ranin hankali wai bai san an yi masa auren ba, ki ji fa kamar shi ɗin yaro ne da za'a masa dole."

Mtsss Rukky ta ja tsaki ta ce

"Kina nufin haka zaki zuba masa ido?"

"To ya zan yi Rukky? Kuka kawai nake yi, amma mutumin nan haka ya tsallakeni ya yi tafiyar sa wajen ta."

"Allah ke Aneesa wani time gaki kamar wayayya ashe ba haka ba ne. To bari ki ji wallahi da Ni ce ke sam bazan damu da lamarin sa ba, balle har in damu da lamarin aurensa, domin kuwa kamar wata dama na samu in yi yadda na ga dama da rayuwata." Rukky ta yi shiru don jin me Aneesa zata faɗa.

"In fita harkar Asmad hmmmm! Gaskiya wannan ne da kamar wuya gurguwa da auren nesa, kince na samu dama ban gane nufin ki ba? Wacce irin dama kenan?" Aneesa ta yi tambayar cike da rashin fahimta.

"Dallah ke wallahi kina da matsala fa."

"Gidan haya ce Ni." Aneesa ta bata amsa cikin jin haushi da maganar Rukky din.

"Ki bari zan shigo Kano rana ita yau, wannan maganar tafi gaban yinta a waya, fatan kina ci gaba da shan mugungun nan?"

"Suna nan ina sha, duk da dai zubar da ciki bai min rana ba, ina gudun na tsufa da wuri, sai gashi tun ba aje ko ina ba an samu matsala."

"Karki damu fa komai zai warware, matuk'ar dai muka bishiyoyi a sannu, ki tattara lamarinsa ki watsar nan da sati biyu, zaki ga canji ita ɗin banza."

"Kai wallahi Rukky bana jin zan iya barin ma wata Hamma, domin shi ɗin ba fa irin sauran mazan da kika sani bane, bazan iya barin Hamma."

"To na ji karki rabu da shi amma ki ɗauki shawarata ki rika tada masa hankali sam karki raga masa sam."

"Tabbas haka zan yi ko dan na kwatowa kaina yanci, zan nuna masa ainahin Aneesa." ta bata amsa cikin tabbatar mata da zata iya aika abin da ya fi haka.

```(Allah ka shirya mu Ubangiji kasa mufi karfin zukatanmu, Allah ka rabamu da aikin danasani, Aneesa kin yi asara tunda dai ke har kullum idan kika samu matsala kawa kike fara sanarwa, duk shawarar da ta baki shi kike dauka wata rana da idonki zaki yi hawaye. Allah ya tsaremu ya tsare mana imanin mu.)```

Karfe takwas da mintina Dr ya koma gida, domin sai da ya biya wajen Hafiz a falo ya samu Aneesa zaune ko sallamar da ya yi kin amsawa ta yi sai hararar da ta rika zabga masa, murmushi kawai ya yi ya wuce bedroom ɗinsa ya canza kaya sannan ya kuma dawowa falon harlau dai tana zaune wajenta ya nufa ya zauna tare da faɗin.

"Sannu da gida kanwata." Cikin tsokana ya yi maganar.

Turo baki ta yi ta juyar da kai gefe, don haushi yake bata

"Allah sarki kanwata fushin ne har yanzu Allah dai ya huci zuciyarki!"

Shiru ta masa har lokacin, ko juyo da kai taki yi

"Ina dai kara bada hak'uri adaure ayi min koda magana ne kila ko baki sanyi." Cikin sigar lallashi yake maganar.

"To ina ruwan biri da gada! Nifa wallahi bana son sanabe kai Hamma kana tunanin akwai sauran abin da zaka faɗa min!" A fusace ta dire maganar.

"Yi hakuri yanzu dai kawo karshen ci abinci?"

"Bana jin yunwa?" Ta bashi amsa a takaice.

"Ban gane mai kike nufi ba, rabon ki fa da abici tun safe baki tsoron wani ciwon ya kamaki?"

"Eh! Ta bashi amsa kai tsaye.

Gyada kai ya yi ya ce "da da kyau gashi kuma nima ɗin yunwa nake ji ya za'ayi da ni?" Ya yi tambayar yana kashe mata ido ɗaya.


Karamin tsaki taja ta ce "kai da ka je gidan amarya kuma mai zai sa kazo kana tambayata abinci?" Cike da tsiwa ta ƙarashe tambayarsa.

Mik'ewa ya yi sannan ya saki Murmushi mai birgewa ya ce
"Saboda naki na saba ci, amma wallahi yammata kin haɗu fa, aikinki yana kyau ina son irin wannan tsiwar, ya yi maganar yana kai hannu kan bakinta.

Kuka Aneesa ta fashe da shi cikin kunar rai da maganar shi, don a nata tunanin ya maidata wata mara lissafi ne, bai san irin mugun kishin sa da take ji bane shi yasa. Amma a fili sai ta ce

"Hamma dama don ka riƙa walak'antani ka yi aure? Tun kafin amaryar ta tare har ka soma faɗa min magana, har ka fara nuna baka damu da damuwa ta ba?" Ta yi maganar tana mik'ewa tare da soma tafiya.

Cikin zafin nama ya rikota ta faɗa jikinsa gam ya riketa, hannu saya tare da ɗago fuskarta ya ce

"Sam ba shi ne dalilin aurena ba Aneesa ki yi hakuri kar kisa wannan a ranki har ya zame Mali matsala, insha Allahu ni ASMAD na dauki maki alk'awari ba zan taɓa walak'antaki ba." Cikin sanyin murya wacce a ke kwantarwa da mutum hankali ya ke maganar.

Sun ɓuro baki Aneesa ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Mu je in haɗa maki te...






_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:08 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*


*29*

"Mu je in haɗa maki tea please don bani son ki kwana da yunwa."

"A'a bana sha nifa." Cike da shagwaɓa ta k'arasa maganar.

"Haba dai My Anee ki dai daure kishi, ko kina son in shiga damuwa ce?"

Dan juya kai ta yi alamar a'a. "Ok zauna bani five minutes bana son ki wahalar min da kanki." Ya ida maganar yana zaunarta a kan kujera kamar wata kwai. Har ya kama hanya sai ya dawo ya sa hannunsa cikin nata ya marairaice fuska ya ce

"My Anee wai har yanzu ban baki ajiya bane?"

"Wane ajiyar?" Ta tambaya tana binsa da kallon rashin fahimta.

"To menene na zaro ido kuma? Nufi na fa shi ne har yanzu baki dauke da cikina?"

Wani irin faduwar gaba ta ji da jin da tambayar da Dr ya mata, ba karamin firgita ta yi ba, amma sai ta dake ta ce

"A'a Hamman har yanzu bani da komai." A tsorace ta bashi amsa.

Murmushi ya

Please Login or Register in order to submit comment