Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[11/25, 3:54 PM] Rano2: Sanadin
              Labarina
                   Free Page (1)

©®Hafsat Rano

****Gudu take a cikin ruwan da ake tsugawa kamar da bakin kwarya, kokari take ta kai gidan kafin duhun magriba ya sakko, duk da shekarun ta ba zasu wuce sha hudu zuwa sha biyar ba, amma haka ake aikenta har gaba da  in da taje a yanzu,ba yau ne karo na farko da ruwa ya fara tare ta ya zane ba, ba kuma shine zai zama na karshe ba, duk da haka har yau ta kasa sabawa da dukan ruwan, duk sanda ya tabata toh fa sai ta kwanta rashin lafiya amma hakan ba zai hana idan wani hadarin ya sake hadowa a sake aiken nata ba. Daidai wajen wani shago tazo wasu manyan mutane da suka fake a wajen suka ce tazo ta fake, kallon su tayi kawai ta cigaba da gudu a cikin ruwan dan idan har ta yarda ta fake din toh bayan dukan ruwan za'a kara mata ne da dukan gaske, shiyasa ta gwammace ruwan ya dake ta akan dukan Iya Lami wanda a duk sanda ta dake ta sai ta sha matukar wahala, bayanta duk shatin dukan ta ne da kafafun ta, shiyasa take matukar tsoron abinda zai hado su da ita.
   Tana cikin gudun takalmin ta ya tsinke, ta durkusa ta cire su dukka ta rike a hannu ta cigaba da falfala gudu. A zauren gidan nasu ta tarar da iya Lami tana hura wuta, wani kallo tayi mata wanda ya saka hantar cikin ta kadawa, tayi saurin cewa

"Wallahi ita ta tsaida ni, sai da aka samo chanji kafin nan kuma har an fara ruwa."

Ta fada tana rawar sanyi hakoranta na hadewa waje guda.

"Bani." Tace tana mikowa hannu, hannun na rawa ta mika mata ta warta tana hararar ta

"Shegiya me zubin mayu, wuce kije ki cire kayan nan kizo nan,kin tsare ni da shegun idanuwan ki kamar na kura."

Da sauri ta shige ciki tabi gefe ta shiga dakin ta, ta cire kayan ta shanya su akan kofar langa-langar dake dakin sannan ta saka wasu, har cikin kashin ta take jin wani irin masifaffen sanyi, amma haka ta sake fitowa ta koma zauren, ta samu gefe ta durkusa ta hau tankad'e, tana yi tana gyara wuta, ta gama ta rud'a sannan ta koma gefe ta hade kanta da guiwarta zazzabi na neman rufeta.
   Ji tayi an duma mata dundu, ta dago da sauri tana kallon Iya Lami akanta

"Dan ubanki shine zaki yi min talgi ruwa ruwa, ki hade kai da guiwa kina ji har ya soma zubewa dan rashin mutunci kiyi kamar baki sani ba?."

Da sauri ta kalli wajen tukunyar, ta mike da sauri ta hau gyarawa tana rage wutar baya, kwafa tayi ta sake ficewa lokacin ruwan ya tsagaita sai dan yayyafi da ake yi, a gaban wutar ta zauna dirshan har ta gama tuwon ta kwashe, ta maida ruwa akan tukunyar da zata gasawa baffanta kafarsa.
   Tana zaune ruwan yayi ta kwashe kwanukan tuwon ta shigar dasu dakin iya Lamin sannan ta samo baho ta juye ruwan ta dauka ta shiga dakin Baffan da sallamar ta, yana kwance akan yar katifar sa, ransa babu dadi tunda aka fara ruwan yake ta tunanin ta, ganin ta yanzu ya sakashi sauke ajiyar zuciya

"Bongel..."

"Na'am Baffa "

"Kin dawo ashe, ruwa ya taba ki ko?"

Girgiza kai tayi

"A ah yayyafi ne kawai."

"Alhamdulillah, ina ta tunanin ki tunda naga an soma ruwan nan, kiyi hakuri kinji?"

Shiru tayi kawai, ta jawo tsumman da take gasa masa kafar ta soma danna masa kamar yadda iliya ya koya mata. Ta gama ta fitar da ruwan sannan ta dawo ta zauna a gefen sa, cikin tsananin tausayinsa, tun bayan da akayi masa aiki a kafar ya zamana duk damuna kafar na tashi har ta hanashi takawa kwata-kwata, ita take kula da fiye da rabin dawainiyar sa Iya Lami babu abinda take sai yi masa fada da masifa kullum ita ta gaji da dawainiya dashi da yar sa, baya tanka mata dan yana tsoron tace zata tafi, abubuwan zasuyi musu yawa shi da yar sa, shiyasa yake lallabawa baya taba mata musu ko yayi jayayya da ita.
   Shigowa tayi dakin dauke da kwanukan tuwo da miya, da sauri ta tashi ta karbe ta, ta ajiye a gefen baffan sannan ta raba ta fice daga dakin, ta nufi dakin ta, ta kwanta akan tsohuwar katifar ta, ta lulluba da wani zanin mahaifiyarta, duk da haka bata daina jin sanyin ba, amma babu yadda ta iya, haka ta cigaba da rawar sanyin har dare ya soma yi sosai, kafin ta samu bacci me nauyi ya dauke ta.
     Da safe ta tashi da ciwon kai, duk da haka sai da tayi duk ayyuka kanta, ta koma dakin bayan ta gama ta kwanta kenan Iya Lami ta leko tace ta tashi, tazo ta debo ruwa, ba musu ta saka wani tsohon Hijab dinta, ta fito ta dauki bokitin ta fita. Dakin da baffan yake ciki Iya Lami ta leka, ya kalle ta yace

"Lami nace a daina saka yarinyar nan dibar ruwa dan Allah."

"Idan bata debo ruwa ba kai ne zaka debo? Eh?"

Shiru yayi ganin ta harzuko masa

"Da me zan ji? Da wahalar ka ko tata? Ko ni kake so na debo ruwan da kaina ne!?" Ta cigaba da fadan tana fita tsakar gidan

Be amsa mata ba, ta dinga sababi har sai da yaji dana sanin yin magana, haka yana ji yana gani sai da ta cika gidan tas sannan Lamin ta kyale ta, ta sake komawa dakin ta kuma kwanciya kanta na sake matsa mata sosai, ga wata mura da tazo ta chunkushe mata hanci da makoshin ta.
Har wajen azahar Jiddan na kwance bata fito ba, tasan dukan ruwan ne ya sakata zazzabi amma tayi biris kamar bata sani ba,ta cigaba da sabgar ta bata damu da halin da zata shiga ba, ko dubo ta batayi ba har sai da Saude ta shigo dauke da kanin ta Muhusin a kafardar ta, ta gaida Iya Lamin sannan tace

"Inna ce dama tace muzo muji ko lafiya Jidda bata leko yau ba?"

"Jeki dakin ta ki dubo."

Tace tana yin gaba ta cigaba da sabgarta, dakin ta shiga ta sameta a kanannade ta chure waje daya, ta lulluba da tsuman zanin ta.

"Jidda, jidda?" Tace tana janye rufar.

"Sanyi nake ji Saude, rufe ni."

Maida mata rufar tayi, ta zaunar da Muhsin a gefenta sannan ta fita, taje ta sanarwa da Babar tasu sai gasu sun dawo tare, a zaure Iya Lami ta tsaida su.

"Lafiya Asabe?"

"Lafiya lou, Jidda nazo dubawa Saude tace min tana kwance bata da lafiya."

"Me zaki mata toh? Ko tsabar kinibibin da kika saba ne, salon a cigaba da zagi na a gari ace bana kula da ita."

"Kina kula da ita din ne? Kiji tsoron Allah wallahi Lami, Allah kuma sai ya tambaye ki wallahi,

"Abinda naga dama shi zanyi a cikin gidan nan, kamar yadda babu shegn da ya saka miki ido akan gidanki haka nima babu shegen da zai zo min da iyayin banza da wofi."

"Kinsan mutumin da be haihu ba, ba lallai yasan daraja da zafin d'a ba,kuma dole naje naga halin da yarinyar mutane take ciki dan ke bakar azzaluma ce baki san rayuwa ba."

Magaanar tayi mugun yi mata zafi, tayi kokarin warto rigarta da nufin su daku amma ta goce tayi shigewarta dakin da Jiddan ke ciki, ta taimaka mata ta mike tsaye, ta riketa suka fito, bayan su ta biyo tana huci kamar zakanya tana zage-zage amma tayi mata banza sai da suke fice daga gidan.
Gidan ta, ta kaita ta dora ruwa ta sakata tayi wanka, ta bata kayan Saude ta saka sannan ta bata abinci da paracetamol ta sha, ta kwanta lamo abin tausayi, duk wanda ya rasa uwa yayi kuka dan tabbas yayi babban rashi a rayuwa.
Yamma likis zazzabin ya sake rufe ta, ta saka aka samo machine a chan hayi yazo ya dauke su tare, ya kai su chemist din cikin garin,akayi mata allura aka bata magunguna sannan suka dawo, ko da suka dawo bata barta ta koma ba,tace tayi kwanciyar ta anan har sai ta samu sauki, ta aika Saude ta fada wa baffan zata kwana a gidan su, yayi godiya dan hakan yafi masa sauki kuma hankalin sa yafi kwanciya.



Cikin dare ya kasa rintsawa, tunanin irin rayuwar da yar sa take ciki ya dame shi, be san ya zai yi ya samar mata ingantacciyar rayuwa ba a halin da yake ciki, irin rayuwar da mahaifiyarta tayi mata shaawa, duk da haka ba zai zauna ya zuba ido Lami ta lalata masa rayuwar ta ba. Ya dade yana sakawa da warwarewa ya rasa mafita haka ya hakura ya kwanta har bacci yazo yayi awon gaba dashi.
Da safe ta tashi da dan kwarin jikin ta, har ta taya Saude yan aikace-aikacen gidan duk da ba masu yawa bane, bayan sun karya suna zaune yar karamar wayar Innan tayi kara alamun shigowar kira, da sauri ta shigo dakin tana fatan ya kasance wadda take jiran kiran ta ne. Ita din ce kuwa, jiya tayi mata flashing bata biyo ba, sai yanzu da safe dama tayi tunanin bata gani ba, waje ta fita zuwa dakin baffan su Saude ta turo kofar saboda bata so suje magaanar da zasuyi.
Sallama sukayi wa juna sannan suka gaisa da tambayar bayan rabuwa, sai kuma ta dora da

"Dama kiran da nayi miki akaan magaanar Hauwa'u ne, ina ganin lokaci yayi da zaki tuntubi B weaffanta da magaanar nan da mukayi kwanaki, a wannan gabar ba lallai ya hanaki ba, dan magaanar da nake miki ma yanzu haka a gidan nan ta kwana, bata da lafiya amma ko a jikin tsinanniyar matar chan, gwara kawai kizo yayi hakuri ki tafi da ita."

Shiru tayi, alamun maganpma take itama daga dayan bangaren, tana dai ta amsawa da eh, sai kuma tace

"Hakuri zai, idan da rai da lafiya watarana da kanta zata zo har in da yake."

"Yawwa kin gani, kizo dan Allah ko zuwa gobe ne, zan barta anan din har zuwa goben idan kin tabbatar da zuwan naki sai ki sanar min, akwai abubuwan da zan bata ta tafi dasu."

"Toh shikenan a gaida yaran da Maigidan."

Soke wayar tayi a zanin ta bayan sun gama, ta fito zuciyar ta fes, tana kuma fatan idan Innajon tazo ta samu tafiya da ita chan in da take aure, a kalla zata huta da wahala rayuwar ta zata sauya, ko da sanadin labarinta ne, idan mutane suka ji zasu tausaya mata.

***Wunin da tayi a gidan su Sauda ya sa ta kusan mance rayuwar da take a cikin gidan mahaifin ta, har tana dariya da hira tamkar ba ita ba, gabannin magriba aka sake kiran Innan ta amsa cike da jin dadi, bayan sun gama wayar ta dinga murna tana fatan hakan su ya cimma ruwa, da daddare bayan sun gama cin tuwo ta dauko wata yar karamar jaka, me dauke da sarkar kafa da ta wuya, jikin su dauke da tambarin zuciya da wani abu kamar ganyen bishiya, mika mata tayi tace

"Wannan shine abinda mahaifiyar ki ya bar miki Jiddah, ki adana su watarana zasu miki amfani."

Karba tayi tana dubawa kafin tayi murmushi kawai, bata ce komai ba ta damke su a hannun ta, tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa.


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS  4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[11/25, 3:54 PM] Rano2: Sanadin
               Labarina

              Free Page (2)

©®Hafsat Rano

***Rayuwar ta tun bayan da ta bude ido ta ganta a gaban baffan ta, bata san wani abu daya danganci mahaifiyarta ba, bata san wacce irin rayuwa mahaifiyar ta tayi ba har zuwa ranar da ta koma ga mahaliccin ta, ranar da ta zama silar zuwan ta duniya itace ranar da tayi silar mutuwar ta.
A duk lokacin da ta bukaci sanin wani abu na daga sashe na rayuwar ta sai Baffa yace mata ba yanzu ba, sai ta girma ta mallaki hankalin kanta. Ta kan yawan tuna mahaifiyar ta duk da iyakar sanin hoto kawai tayi mata,amma ta gaza manta zanen fuskarta a cikin zuciya da kwakwalwarta. A yau da ta samu wani abu da ya danganci mahaifiyarta sai taji tamkar ta san wani sashe na labarin ta, wani sashe me matukar muhimmanci a kundin rayuwar ta. Sake damke su tayi da kyau, ta samu kasan kayan ta, tayi musu boyo me kyau, irin boyon da zaka yiwa duk wani abu me matukar muhimmanci a gareka.
Gidan su ta shiga kanta tsaye cike da karsashin ganin ta, tayi saurin fadawa kanta cike da murna da dokin ganin ta, rungumeta tayi a jikin ta tsam zuwa wani lokaci kafin ta saketa tana dariya

"Jidda."

"Na'am..." Ta amsa cike da zumudi sannan ta zauna a gefen ta,

"Ya jikin naki?"

"Da sauki."

"Sannu. Allah ya kara sauki."

"Amin." Ta amsa sai ta mike, taje ta kawo mata ruwa sannan ta fita zuwa dakin ta, ta tura kofar ta shiga ta soma harhada kayanta waje daya, zuciyar ta cika fal da farin ciki. Kasancewar kayan ba masu yawa bane yasa ta gama hade su kaf, ta fito zata koma taji suna magana da Baffa sai ta fasa ta samu waje ta zauna har sai chan da aka kwala mata Kira, ta tashi da sauri taje, Baffa yace ta dauko kayanta tazo.

Zama tayi a gaban baffan ta tankwashe yar kafarta, kayan ta dake cikin yar karamar ghana most go ta sake rik'ewa gam tana sauraron maganganun dake gudanuwa tsakanin Baffan da Innajo.

"Jidda amana ce a wajenki Innajo babu yadda zan yi ne amma da babu yadda za'a yi na rabu da ita, sai dai tana bukatar kulawar uwa a halin yanzu, dan haka na baki amanarta, idan kika ci amanarta ba zan yafe miki ba, ita din marainiya ce, bata san mahaifiyar ta ballantana wani dangi na kusa, ni kadai ne gatanta, sai ke yanzu da na damka miki amanarta a hannunki."

"In sha Allahu zan rike amana, nagode nagode da karamcin ka gareni, in sha Allah Jiddah ba zatayi kuka ba, kuma nayi alkawari duk sanda akayi hutu zan kawo maka ita nan, nayi wannan alkawarin."

"Shikenan,ubangiji Allah ya baki ikon rike amanar da kika dauka."

"Ayi dai mu gani idan iska zata hura wuta."

Lami tace tana daga kan kofar dakin ta, kallon ta Baffa yayi ya girgiza kai kawai, itace ummul'aba isin da yasa zai bawa kanwar tasa Jidda, ba dan haka ba babu yadda zai ya rabu da ita dan ganin ta kadai yake rage masa kewar marigayiya, amma babu yadda ya iya, hakan shine maslaha akan irin kuntacacciyar rayuwar da Jiddan take fuskanta a cikin gidan mahaifin nata a gaban idon sa bashi da ikon hanawa ko tsawatarwa saboda lalurar da ta sameshi ta ciwon kafa.

"Ku tashi ku tafi kar kuyi dare a hanya, Allah ubangiji ya kaiku lafiya."

"Amin Baffa." Tace cikin yar siririyar muryarta da take nuna tsantsar yarintar ta

"Allah ya kiyaye kinji? Ki rike abinda na fada miki kar kiyi wasa dashi, in sha Allah ba zaki yi kuka ba."

Da kai ta amsa masa, ta mike Innajon ta mika mata hannu ta karbi kayan, sannan tace

"Zamu tafi Lami, sai ki zuba ruwa a kasa kisha, kuma in sha Allah sai mugun nufin ki ya koma kanki."

Abun ka da me jiran kiris sai gata a tsakiyar tsakar gidan tana huci tayi kan ta

"Ke har kin isa ki fadan magana? Waye be san rayuwar wahalar da kike a gidan miji ba, bora wadda bata da maraba da yar aikin gidan."

Wani kallo Innajo tayi mata, maganar tayi mata mugun ciwo amma sam sai taki nunawa, ta rike hannun Jiddah ta soma tafiya

"Yaya mun tafi, Allah ya kara lafiya."

"Amin, Allah ya tsare, ki kirani da zarar kun sauka dan Allah."

"In sha Allah."

Cikin daga kafa suke fice daga gidan, ya saka hannu ya share guntun hawayen da suka zubo masa, kansa a kasa yana sauraren maganganun da Lamin take ta farfad'a cikin daga murya dan Innajon ta jiyo ta. Sai da taji tashin motar su sannan ta shiga daki tana cigaba da sababi.

***Mota ce irin golf din nan Alhaji yayi mata shatar ta, su biyu ne a bayan motar lokaci zuwa lokaci sai ta kalli fuskar Jiddah tayi mata murmushi, maganganun Lami sun yi matukar tasiri a zuciyar ta, bata da maraba da bora kamar yadda ta fada amma ya zatayi? Ta ta kaddarar kenan, zata jira zuwa lokacin da Allah zai kawo mata dauki ko ta samu sauki a zuciyar ta. Tafiya ce ta kimanin awa daya da rabi sannan suka iso, daf da magriba me motar ya sauke su a kofar gidan, idanun Jidda suka fito waje tana kallon in da suka zo din, gida ne matsakaici me bakin gate, tura yar karamar kofar dake jikin gate din tayi hannun ta daya na rike da kayan Jiddan daya kuma hannun Jidda ne. Abu ce ta fara ganin su, ta taho da sauri ta karbi kayan hannun ta sannan tace

"Sannu da hanya Anty "

"Yawwa sannu Abu."

Ta amsa sannan ta cigaba da tafiya zuwa wata kofa dake kallon gabas, irin kofar nan me hannu biyu,da glass me kauri a tsakankanin kowanne waje, duhun magriba ya mamaye babban falon nasu Amma duk da haka kana iya ganin mutane a zazzaune, sallama tayi yaran suka amsa, dama kuma su din ne zasu amsa uwar gayyaar ko kallo bata ishe ta ba, tana hakimce a saman kujera cikin yanayin rashin jin dadin ganin su.

"Anty sannu da zuwa."

Yaran suka shiga jera mata sannu, Usman da Muhammad suka taso da gudun su, suka rungume ta, ta daga su sama daya bayan daya tana dariya.

"Anty wace wannan?"

Amira ta tambaya tana leken fuskar Jidda da ta rakube a bayan Antyn.

"Ina ruwan ki Amira? Bana son shishigi fa."

Hajjajun dake hakimce ta tsawatar mata tana jan tsaki, murmushi Antyn tayi kawai ta girgiza kai sannan tace

"Yar uwa kuma kawa na kawo muku Amira, gata nan sunan ta Jidda."

Shiru Amiran bata ce komai ba tana tsoron sake magana tasan halin Mama sarai zata iya bugunta akn haka.

"Muje Jidda, naji ma an soma kiran magriba." .
Suka wuce su zuwa wani dogon corridor da zai sada su da bangaren Antyn, daidai lokacin aka kawo wuta, Abu ta ajiye kayan Saudan sannan tace

"An gama tuwon Anty, na fadawa Mama dai a zato na ko har na tafi baki dawo ba."

"Sannu da aiki, kin yi saurin gamawa ma."

"Wallahi, gani nayi garin damina, gwara kayi da wuri kafin ruwa ya sakko."

"Gaskia kam."

"Akwai abinda zaa yi ne kuma?"

"Umm, babu gaskia,zaki tafi ko?"

"Eh idan ba abinda za'a yi ba."

"Babu, bari na diba miki yar tsarabar kauye ba dai yawa."

"Aikuwa nagode Anty."

"Zo Jiddah." ..

Ta yafito ta da hannu, suka shiga daya daga cikin dakuna ukun dake dan madaidacin falon Antyn.

"Ga dakinki kinji, zauna bari na sallami Abu nazo sai na nuna miki yadda komai yake, ki saki jikinki kinji?"

Da kai ta amsa tana kallon dakin, fita tayi taje ta sallami Abun sannan ta dawo tace tayi alwala, itama taje dakin ta, tayi alwala sukayi sallar a tare, sannan ta kunna mata kallo tace tana zuwa.
Part din Maigidan ta nufa bayan ta dora ruwa a saman gas din dake kitchen din bangaren nata, ta gyara masa dakin duk da kafin ta tafi ma sai da ta gyara amma tasan da gayya Maman zata bata musamman toilet, haka ko yaushe take sake gyarawa idan zata shiga ta bata sau dubu bata kuma taba tanka mata ba, yau din ma sai da ta sake gyarawa ta kunna turare sannan ta fito, ta dawo ta samu ruwan ya tafasa ta cika flask sannan tayi masa tuwon alkama wanda zai ci yanzu da kuma safe, ta zubawa Saudah a ciki ta kirawo ta kitchen din duk dan ta sake da ita, ta karba ta fita, Usman da ya gama zaman falon ya shigo ya haye kafar Jidda yana mata magana

"Kece Yayarmu da Anty tace zata kawo mana ke?"

Gid'a masa kai Jidda tayi, sannan tayi masa murmushi

"Zaka ci tuwo?" Tace masa tana kallon plate din dake gabanta.

"Naci tare da Muhammad, amma zan kara naki."

"Toh muci."

Ta tankwashe kafarta shima sai yayi yadda tayi, suka shiga cin tuwon a tare, har suka gama Anty na ta kaiwa da komowa a tsakankanin bangaren Maigidan da nata, sai da ta gama hada masa komai sannan ta nutsu ta zauna taci abincin ta watsa ruwa dan a gajiye take jin ta sosai dan ba wani zama tayi ba tunda suka shigo. Wajen takwas da arba'in Baban ya dawo, sun idar da Isha Usman yayi bacci, Antyn tace itama Jiddan taje ta kwanta, ta rakata har daki ta nuna mata duk abinda zata bukata ta kawo mata ruwa saboda dare sannan ta dauko Usman ta dawo dashi dakin tayi musu addua sannan ta kashe musu wutar dakin ta nufi bangaren Baba.

***A zaune ta samesu da Mama, ta bararraje tamkar kwananta ne ranar, ta bude masa abincin har ya soma ci

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment