Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa ya isa ya ja da ikon Allah.tuni ta sauko kasa ta fara sujjada tana godewa allah tare da adduar zaman lfy.

Su salma da mimi tun da rahma ta fara haukar murnarta suka dakko waya suka mata video.da kyar ta lallabasu suka yarda baza su nunawa kowa ba.su kadai zasu dinga gani.ammafa sunsha daria yau.

Asmabaffa
[13:24, 1/29/2018] ‪+234 802 498 6436‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

145-150

By
Asma baffa.

Basu San rahma haka ke son ya ahmad ba sai yau,su husna ma taji komai wajen ammar ta taya kawarta murna,ai rahma bargo ta shige ta rufe kanta tana ta mutsu mutsun dadi,har mamakin kanta takeyi wai dama haka so yake ita Ashe hauka takeyi da take cewa baza tayi aureba da kuwa ta cuci kanta.

Su amrata ana can a kulle ana ta bincike kan case nata,duk da haka taci duka.jikinta du yayi lukuni,yau kowa ya watse daga biki baki na nesa ma duk sun tafi,ankai amarya mimi hadadden gidanta dake wuse zone11, ma'aikata sun gyara gidan fes komai ya dawo normal.yanzu rahma da ahmad ake shiryawa gidansu da zasu zauna gidan ahmad a maitama dady ya kera masa basu da nisa sosai.

Momi da dady ne suka kira ahmad zaune yake gabansu momi ce ta nisa tace lallai munyi kuskure na kin karbar yarinyar nan rahma,ana zaton wuta a makera sai aka jita a masaka,dady yace ni kunyar yarinyar ma nakeji.so nake a gama shirya gidan Ku tare nan da 2wks,momi ce ta umarci ilham da taje part din ahmad ta kira rahma,

A nutse tayi sallama gaban su dady ta zauna,ahmad kallonta yakeyi sosai rabon da ya ganta tun ranar daurin aure, nasiha suka musu sosai tare da neman gafarar rahma,

Haba momi ai dama ni banji komai ba Ku ai iyayenaa ne Ku daina ma bani hakuri dan Allah dan kun cancanci komai tunda kuka bar ya ahmad ya rikeni ai kamar kune cewar rahma.dadi kowa dake wajen yaji da maganganun rahma.momi ce tace rahma ki ebo kayanki ki koma part din su salma ki dinga kwana can kafin a kaiki garinku a sanar da yan uwanki.dadi rahma taji tare da cewar to momi insha'allah.kafin rahma ta rufe baki ahmad yayi tsalle ya dire wlh momi Sam bazai yiwu ba a part dina zata ci gaba da zama,me yasa tun farkon kawota bakuyi tunanin ba muharrama ta bace,bakuyi tunanin shedan ba idanku ya rufe akan zargi kuka barni daga ni sai ita a part daya sai yanzu da na aureta ta zama muharramata za kuce ta dawo nan nikam ban amimce ba.

Kunyace ta kama rahma harma da su momi,dady ne yayi murmushi yace hakane ahmad tabbas munyi kuskure babba kuje kuci gaba da zamanku nan da 2wks Ku koma gidanku.

Momi Jan hannun rahma tayi zo muje to room na baki sako,ahmad yace ke kiyi sauri ina jiranki,kai momi ta girgiza lallai ahmad bashi da kunya ko Kadan.wasu magun guna momi ta nunawa rahma tace kullumm tazo tana sha a dakinta,kuma ta biya me gyaran jiki kullum za azo ayi mata in ta dawo daga schl har lokacin tarewarta,godiya tayi sosai.momi huduba ta karawa rahma kan kar ta bawa ahmad kanta har sai sun tare.

Fitowa sukayi da momi rahma ana ta sunne kai,ita a dole kunya.yanzu kunyar ahmad da su momi takeyi sosai.taso ahmad ya barta part din salma da ta huta da kunyarsa,tashi yayi ta bi bayansa har part dinsa ahmad yana kallonta yanda take wani kunya.a hankali ta durkussa kasa tace yaya dan Allah ka barni na zauna a part din su salma...tsawa ya daka zan kwada miki mari stupid cinyeki zanyi dan kinga na aureki zaki fara rainani ko ance miki a son raina na aureki.inma wani abu kike tunani zan miki to ki cire,ban son ina magana kina canjamin am I clear kai ta daga hade da cewa yessssss sir .

A cikin fushi yake amma ta bashi daria sosai yanda rahma ke birgeshi comedian ce dole sai ta saka nishadi.mikewa tayi ta fara tafiya yace kin san fa baki bani abinci ba tun safe banci komai ba,ko so kike na dinga zuwa wajen momi haka akeyin mata da miji.daria ya bata yaya ai baka fada min ba,sai na koya miki ma abinda ya kamaceki.batayi magana ba ta wuce kitchen tana kai ya ahmad kwai fadan tsiya ni bana son fada da tashin hankali.

Miyar jajjage tayi tasha kifi da farar shinkafa,ta hada salat sai kunun aya da tayi yasha madara bata ganshi a palon kasa ba hakan ya tabbatar mata ya fita yin sallar isha tasan ya Ahmad akwai zuwa masallaci,part din ta kuma gyarawa fes ta fesa roomfreshna kala biyu ga turaren wuta na steamer ta kunna tiririn kamshi na tashi,zuge labilen ko ina tayi domin ya rufe ko ina ruf,sai da ta tabbatar ko ina ya kama kamshin sannan ta fesa wanka dan rahma ta ajiyewa kanta baza ta bari a kwace mata dan ahmad dinta ba,

Akwatuna ta bude so takeyi ta kure wanka fa,dama tuni take so ta dinga sa English wears amma ba dama sabo da ahmad ba muharraminta bane to yau ga rana ta samu sai shanya.bayan ta gama shafa lotion dinta.

Maganganunta take ita kadai tana duba kayan ai bazan ma fara sa ma tsinanu ba sai nan gaba zan gigita tunaninka ya ahmad.amma me tana gwadawa ta kasa sawa sabo da kunya,nan gaba zan sa ne ai cewar rahma,akwatin atamfa ta bude ta dakko wata Riga da skert rigar me tattara black ce sosai da zanen ganye green,tayi kyau atamfar inner wears tasa sannan ta sa kayanta,powder ta shafa sai kwalli da ta sa,girarta kuwa sabo da yawanta bata zanawa kawai da brush take dan gyarata,red JanBaki ta shafa sosai daurin dankwali ta tsantsara kamar zata party. Turare ta fesa kala 3 ta shafa humra me kamshin gaske wacce mimi ta ibar mata.

Fitowa tayi Palo baya nan abincin ta kwashe ta wuce turakar me gida lol kaji fa amarya da iyayi.

A yanzu amrata an yi bincike a gawar ALHAJI ba ita ta kasheshi ba zuciarsa ce ta buga,Ashe yana da ciwon zucia dan haka tayi karfi ba tare da ya sani ba zuciarsa ta buga lokaci daya.wa'iyazu billah alhajiji me zai cewa Allah, yana halin zina sai dai Allah. Ya masa rahma dama ita mutuwa bata jira,bata sallama shi yasa ake so har kullum ka kasance me aikata alheri dan baka San aya zata riskeka ba,Allah sa mu cika da imani.me Memakon amrata ta saduda ta koma ga Allah ina Sam tana komawa nijar da ta tabbatar ta warke daga raunikan da police suka ji mata, tajita dam taci ta koshi,ga lafiya a jikinta kamar ta rungumi zaki sai tace Sam sai tasan yanda tayi ko da tsafi ahmad sai ya aureta sannan tana shiga zata kawar da rahma daga doron kasa,har tawa wasu tsofafin mazan harkarta waya inda taci gaba da duniancinta, tare da bazama wajen bokaye.

Dama wani iya shegen du lafiya ce ke sa mutane yinsa .

Asmabaffa
[13:24, 1/29/2018] ‪+234 802 498 6436‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

150-155

BY
Asmabaffa


Wannan page din naku ne fa masu bibiyar littafin nan.godiya dubu gareku.


Shigowa Palo ahmad yayi wani arnen kamshi ne ya dakeshi ido ya lumshe ko ina sheki da kamshi yakeyi alhmdllh ya firta yasan wannan aiki sai rahmansa,ita kuwa amarya tana palon ahmad a sama ta shirya abinci,sannu da zuwa tace shi kuwa gogan naka kallo yake kare mata kyau kamar aljana ga iya kwalliya da dressing,sai da ta maimaita sannu da zuwa sannan ya dawo cikin hankalinsa,daya daga cikin kujerun ya zauna tare da kafe rahma da ido ta masa kyau,abinci ta shiga zuba masa shi kuwa santala santalan hannun Wanda suke dauke da zanen lalle yake ta kallo,

Mika masa tayi yaya gashi,abincin ya fara ci a nutse ita kuma ta juya kallonsa take tayi yanda yake motsa dan bakinsa komai nasa me kyaune,gajiya yayi da kallon yace lfy ba tare da ya kalleta ba kuma bai tsaya da cin abincin ba a daina kallona haka kamar yau kika taba ganina,fuskarta ta dauke gefe yace ko kefa yar fillo wannan irin kallo haka,mikewa tayi a kunyace zata tafi yace dawo ki zauna inda ta tashi ta koma ta zauna har ya gama cin abincinsa,sannan ya tallafe fuskarsa da hannu biyun ya matso da fuskar saitin fuskar rahma yace kiyi ta kallo sai kin gaji kar kice na tauye miki hakki,daria tayi tace ai na gaji ma tun dazu no sai kin koshi yau da kallonta,abinda rahma bata sani ba wayo ya mata dan yafi kallonta da yawa amma bata gane ba..kasa kallonsa tayi sabo da kwarjini yake mata tana jin wani iri a jikinta,idon Ahmad har ya fara canja kala,ganin in ya ci gaba zai iya zubar da mutuncinsa yasa ya janye fuskarsa ya wayance da kin kasa kallo to daga yau kar ki kara kallona a sace ki dinga fadamin zan kalleka sai na zauna ki tayi.

Murmushi rahma tayi ta cuno baki cike da shagwaba to ai kaima ka kalleni da tawa, dazu ma a gaban su momi ai ka kalleni,yace to ba kin rama ba ai shi yasa na baki ki rama,dalilin da yasa na kalleki gani nayi kinyi muni yau kwata kwata naga dan kyan da amare ke yi ke bakiyi ba Sam,kumbura baki tayi to yaya ai baka fada min ni zaka aura ba ko taya zanyi kyau din,daria ya gumtse ganin ta yarda da gaske,lallai yarinya ce tahma,to ke ai bakya so kiyi kyau ai da na koya miki da sauri tace ina so mana ,yace to daga yau a room dina zamuna kwana amma fa kwanciyar kai da kafa,kaina a sama naki a kasa,amma da sharadi ba me taba wani ko da yatsa ne,

Da farko rahma ta tsorata amma tunda taji yace bame taba wani yasa taji sanyi dan tana so tayi kyau,har ga Allah tasan in mata sukayi aure suna kara kyau da kiba Ashe idan ana kwancia bed daya da mijin akeyin kyau.ahmad ne ya katseta tunanin me kikeyi in bakya so kiyi kyau no need ki damu kanki kije da muninki ke za a tawa daria.kwancia rahma tayi a doguwar kujera tare da fadin yaya ai nafi kowa bukatar nayi kyau so nakefa na kara girma da kyau da wuri dan naje kauyenmu su me gari suga naci gaba.

Murmushi ahmad ya saki yace yasan rahma da son tayi kyau ga son a birge Wanda ake so,yace to kuwa ki dage dan nan da 1wk zamu je kauyen.zumbur ta mike yaya bacci yakeji ni bari na dawo.

Tana fita ahmad ya dinga daria lallai rahma yarinyace bata da wayo ko kadan gata ta girma amma ba wayo,ko da yake rashin muamula da frnds ne yasa,dan da tanayi da yanzu sun gama Wayar da ita.

Ita rahma kamar yanda tasan tana tare da ahmad ko hannu baya rike mata sai da dalili tofa har yanzu ma da ya aureta haka take daukansa dan ita ta manta ma ana wani abu a aure ita gani take ko anayi to fa banda ahmad dan bazaiyi da ita ba ko rungumeta bazai ba bare wani abu,dan haka wanka ta sakeyi tasa wata night gaunt dinta pink iya Rabin cinya da wata top ta sama ta Dora ta ko dankwali bata sa ba ta tufke gashinta har baya jelar na kwance tana baza kamshi ta fito dauke da hijab a hannunta hade da doguwar Riga domin sallah.

Bed room din ya ahmad ta shiga hade da sallama karar ruwa taji ta gane wanka yakeyi,bata jima ba ya fito daure da towel a kugu da karami yana goge jikinsa,nan rahma taga baiwar kyan fata,diri,da sura.dauke kanta tayi gefe kar ya ganta,burinta ma taji yayi hugging nata a wannan skin din nasa me kyau,a gabanta ya shirya wando short kawai yasa ba Riga,jikinsa yabi da turare rahma tana jinjina tsabtar ya ahmad,karasowa yayi gabanta yan mata lallai kina so kiyi kyau da wuri,farrrrrr tayi da ido Wanda ya bawa ahmad daria ita dole yan mata.hijab da doguwar rigar ya karfa ya ajiye mata a sip.

Cak ya dauketa ya cire mata rigar saman to fa rahma ido ya fara kawo ruwa jiki ya fara rawa kar kar,hankalinta bai kwanta ba sai da taga ya kwantar da ita kanta yana wajen kafarsa kwanciyar dai kai da kafa.dadi taji a ranta tana kuri haba ai ni nasan yaya na ba dan iska bane,me zaimin ma to ina karamata.

Addua yayi yawa rahma ma nanfa kowa yana sake sake a haka har rahma tayi bacci amma ahmad ya kasa bacci so yakeyi ko hugging rahma yayi don rage zafi,rahma kam bacci yayi bacci fa,ta gangara jikin kafar ahmad,hannu tasa ta rungume kafar a kirjinta, wani laushi ahmad yaji Wanda ya kara gigita tunaninsa.


MARAICIN RAHMA

155-160

BY
asmabaffa


Hankalin ahmad ya tashi sosai ya rasa me yasa tun farkon ganin sa da rahma a kauye yake shiga wani yanayi a jikinsa bare yanzu da suke ma'aurata kuma a gida daya bed daya,baccinta take sosai hankali kwance,a hankali ahmad ya zare kafafunsa ya sadada ya juyo da rahma ta dawo kwancia dai dai dashi ba wacce suke kai da kafa ba,

Hugging dinta yayi sosai zuciarsa na bugawa sai numfashi yake fitarwa ga fitinan nan kamshinta na fisgarsa,rahma bacci takeyi tukuru musamman da ta jita jikin ahmad ga dumi ga laushi da kamshi kara lafewa tayi luf tare da kara kanannadeshi ba tare da ta sani ba,

Dauriya kawai ahmad yake yana dana sanin hada gado da ita gashi ya shiga wani hali ba magani kuma,gashinta ya shiga shafawa a hankali gudun kar ta tashi ta tarfa shi,wuyanta ya gangaro yaji wani laushi kamar flour,cinyarta da tasa ya hade yana gogawa,wani haukacewa ya karayi bai San sanda ya zame hannun rigarta ba,ba bra na shanu sun bayyana ya kai hannu kai gaba daya ya FIta a tunaninsa,ya rude ya gigice,mutsu mitsu rahma ta fara zata farka,da sauri ya mayar mata da hannun rigar yanda suke a hankali ya kwanta luf kamar me bacci,farkawa tayi tace innalillahi wa inna ilayhirrajiun mikewa tayi zaune tana mamakin ganinta a jikin ya ahmad,kuma tabbas taji kamar ana shafata a mafarki,lekawa tayi taga ahmad baccinsa ma yake ita bata San na karya bane yana kallonta,daria ma yakeyi a boye,

Wayyo kar dai aljanune na shiga uku ta fada a fili,a hankali kamar rada ta fara yaya...yaya..ya ahma, muryar masu bacci yayi kamar ta mashayan giya lfy mene cikin dare zaki fara surutunki,kaga kamar a mafarki naji ana shafa min jiki,hamdala ahmad yayi rahma bata kamashi ba,a fili yace waye to ba kowa maybe shedanun dare ne ko mafarki kika fara yi kwanciarki kinji ba kowa fa,ai tsoro ne ya kara shigarta harfa wajenka na dawo kawai na ganni a jikinka.jinki kawai nayi kin fado kaina da karfi kashina har kara yayi cewar ahmad,rahma mamaki tayi ko tana da aljanu suna tashi in tayi bacci bata sani ba,dama ita rahma ba matsoraciya bace bata cika tsoro ba,

Ahmad ne ya nuna mata kan pillonsa dawo nan ki kwanta kar a sami matsala ko,kwancia sukayi a pilo daya,kowa na jin numfashin kowa,rahma jiki har rawa yake ga kunya gashi gabanta na faduwa,hugging dinta ahmad yayi wani zarrrrrrrr rahma taji kamar ta sume,shi kuwa gogan yama kasa tantance yanayin da yake.


Sosai yake mutsu mutsu da goge goge a jikin rahma dan ya rage zafi,sleep...baby okey...yana ta lallabata tare da shafeta da dawo,rahma kuwa kara narkewa tayi taji ta dawo jaririya ma kawai,sai shagwaba take zubawa tana zamewa yana manneta yana lallashi,ita a dunia tana so taga ana lallabata,ana ji da ita,ana lilitata,kuma a nuna an damu da ita ka nuna tana birgeka,to yanzu zata narkema tana zuba ma shagwaba.

Shi kuwa ango ahmad yana son shagwaba shi yasa yake kara rudewa kan rahmansa,suna haka har sai daya yi releasing ya rage zafinsa,hakan ya masa dadi,rahma kuwa taji yana shidewa amma bata je gano ba,

A ranta cewa ma takeyi ai na fada ahmad dina ba abinda zai min,shi ba irin mayun maza bane gashi ko tabani bayayi sai dai ya dinga lallabani ma,sai daya huta yaje toilet yayi wankan tsarki ya wanke wandonsa ya shanya,alwala ya dauro, gani yayi rahma batayi bacci ba ya umarceta da tayi alwala suyi nafila,tsaiwar dare sukayi sosai suka dinga zabga adduoi sannan suka kwanta, ya manne abarsa a jikinsa suka Lula bacci.

Da kyar sukayi sallar asuba suka sake komawa bacci sai 11am ahmad ya tashi ya shiga wanka, farkawa rahma tayi da sauri ta fice daga dakin kafin ya fito daga wanka,kitchen ta fada da rigar baccinta tana girki tana gyara part din haka ta gama gida ya dauki kamshin gyara Dana girki,sakkowar ahmad taji kafin yazo ta gudu room dinta dan karma yaganta batayi wanka ba ta makara a bacci,

Part din momi ya nufa sannan ta fito,sama ta hau ta gyara bangarensa ya day kamshin niima, dining ta shirya ta gyara kitchen sannan ta fada wanka,kwalliya tayi da wani hadadden Riga da skert na India red har karar karafuna yake in tayi motsi yau kyau kam ta shashi kamar a gudu da ita,

Ahmad na shigowa tana fitowa alhmdllh ya furta a hankali kullum ganinta yake kamar sabuwa kamar wankin inji,durkusawa tayi ina kwana yaya lfy alhmdllh haba ko kefa kinga yanda kika fara kyau iron na amarya, Allah yaya cike da murna, yace tab ai nan gaba ma ba a San ya zaki koma ba,sai ma gobe in kinje schl zakiji yanda frnds zasu fada miki,tun yauma su salma zasu fara in kinje, wow cewar rahma ana washe baki,kin San matar Frnd dina sabo da kar mijinta ya mata kishiya kuma kar tayi muni kin San me take mass?kai rahma ta kada alamar a'a,bude kunnenki kiji.👂🏻👂🏻


Asmabaffa
[17:54, 1/30/2018] ‪+234 802 498 6436‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

160-165

By
Asmabaffa


Masu addua da yabon wannan novel na gode sosai,ina ganin sakonku.


Ahmad yace ai kula sukeyi da mazajensu Abinci ma a baki suke bawa mijinsu kuma kullum a jikin mazajensu suke zama,kullum suna manne,daria rahma tayi ta fara gano me ahmad ke nufi, shi kuwa yayi ne don rahma ta saki jiki dashi su saba sosai dan yasan tana tsoronsa da kunyarsa,ita kuwa rahma a ranta cewa tayi af ka kwantar da hankalinka zan fara gudanar da duty na one by one,dan bana so ma wata ta dinga kawowa mijina hari,nafi so ko da ta Allah ta kasance ka kara aure to na zama nice on top,babu wani abu da nakeyi marar kyau da zaisa amin kishiya ko idan anmin ta zo ta fini wajen miji ehe.

A dining ahmad ya zauna ya kwashi girkin rahma me sashi santi yayin da rahma ke zaune a dining itama tana tsallake haba,yana gamawa ta dauko tissue ta mike tsaye ta tallafe keyar ya ahmad ta goge masa baki tana me cewa yaya gobe akwai schl fa kasani,kuma gashi ka maida baba driver wani gidan yana ma aiki wa zai kaini,

Tsananin daria da mamakin rahma ahmad yakkeyi yanda. Take masa abu kamar wani danta dan rainin hankali bata bashi abinci a baki ba tazo tana goge masa lips kuma in tana abu ko a jikinta tsakani da Allah takeyi ba wasa.

Kwace kansa yayi yace ki shirya mana goben ki gani zaki rasa me kaiki schl ko kin taba shiri kinga ba a kaiki ba,Allah kaimu tace ta kwashe kwanikan ta gyara wajen,kitchen taje ta wanke komai ta koma daki ta kara gyara fuska ta fito da mayafinta a hannu.


A Palo ta ganshi yaya zanje wurin su momi no...no ba inda zakije,pls yaya ta shagwabe masa kar ma ki fara wai ma me zaki je yi,yaya gaisar dasu zanje kuma zan karbi sako wurin mum,wanne sako ne haka tun jiya ake cewa sako sako sai kuma ki fito hannu ba komai,ban gane muku ba ke da momi,to nidai ka barni naje pls,how many minute zakiyi,minute fa kace yaya just a minutes wurin mum guda,

30minutes na baki ina nan ina jiranki kizo ki gyaran farce da wankin kafa,kai yaya kamar mace harda wankin kafa,ke kika sani je ki dawo da sauri,kina kara minute akan Wanda na baki baza ki kara zuwa ba try me kika gani.

Daria ta kyalkyale da ita rahma vadai son murmushi da daria ba bata fushi Sam,shi ko ahmad kamar ya samu TV sabo da daria na mata kyau.

Ficewa tayi sai da ta fita daga palon ta leko tace yaya sai 4pm zan dawo wooooo......na masa wayo,ta masa gwalo ta kulle kofar garam ta tafi,me ahmad zaiyi in ba daria ba.


Back to amrata tana can ta fada malaman tsibbu ta buga ta buga yaki cin ahmad,tawa rahma ma taga shuru,sai da ta hada malamai sunkai 20 lokaci daya, ita yawo kauyuka kauyuka,ta kurbe rubutun wannan,ta shanye na wancen,tayi turare,ta hadiye layoyi,ta karbe jikon kazamin wani bokan na kauye ta shanye,tana ta durawa cikinta ruwan kauyuka kala kala,na tabbata da za bude cikin amrata za a ganshi kayan cikinta sun rine sun koma baki sabo da shan rubutu.amma Sam aikinta yaki ci,kuma taki hakura Sam kara kaimi ma take tana ta binne binne hhhh amrata anji jiki.


Momi ta tarar a Palo tana kallo ammar na gefenta kirari ya fara mata sai amaryar yaya,amarya bakya laifi ko kin kashe ilham,fakar idon mum rahma tayi ta dagawa ammar babban yatsa ta jinjina, daria ammar keyi sosai,ya kara da mata a gidan ahmad me daya kwal daga ke ba kari,fakar idon mum ta kumayi ta masa alamar tafawa wai ta tafa masa,momi na kallonsu abin na rahma ya bata daria,ammar zai kara magana momi ta makeshi, rahma durkusawa tayi suka gaisa da momi,ta gaisar da ammar ma,salma da ilham ne suka shigo nan suka dasa hira,

Momi tace salma raka rahma room dina ki bata sakon nan,anjima kuma me gyaran jiki zata zo ki zama ready.. To tace tare da mikewa su shige room din momi ita da salma.kwankwade tsuminta tayi kala kala ta ebi na dare ta fito dasu,sai hira sukeyi da salma tana bata labarin irin yanda taga mimi suna zuba luv ita da angonta da ta kai musu ziyara murmushi rahma keyi tana kara daukan darasi.

tunani takeyi itama ya zatawa dan ahmad dinta,momi rahma na birgeta yanda take son dangin mijinta da fara'arta ba duhun kai,kuma bata kasa magana gaban mutane,tana murna ta sami suruka ta gari,dady rahma taje ta gaisar ya sa mata albarka,fitowa tayi zata koma part din su dan har ta kwashi 50mnt tasan ahmad sarai da fada,momi ce tace rahma zauna mana zaki koma da wuri haka me kikeyi ke kadai,momi ai bai fita ba yau cewa yayi 30 mtn zanyi nan wajen,hmm sai ki koma ai kar kiyi laifi naga ke tsoronsa kike kamar mala'ikan mutuwa ki dai dage sosai wajen karbar kanki kin San maza in suka ga kana tsoronsu ba sauki,momi ai wasu daban suke naga ya ahmad ba haka yake ba,momi gani tayi rahma ta dage tana yabon mijinta,daria momi tayi tare da jin dadi jeki to masu miji,a kunyace rahma ta fice bayan ta gama rashin kunyarta gaban momi.

A kwance ta ganshi ya mike a 3seater yana ta aiki a system,sallama tayi ta wuce dakinta da sauri kamar walkiya dan kar yaga tsumin data dauko roba biyu wajen momi,sai da ta boyesu,ta fito kitchen ta shiga ta dauko masa ruwa da juice har da dambun nama me dadi,Niko nace tofa kaga masu miji,bai Ce mata komai ba.ya kalli agogo ya kurbi lemonsa,ki hada ruwan wankin kafar ga nailcutter ki dauko a room dina kin San inda suke,

To tace tare da mikewa,ta shige room dinsa ta dauko nail

Please Login or Register in order to submit comment