Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tana kallonsa har ya gama,dariar ta masa kyau,kasan kafarta ya kalla ai kuwa jini nata diga,dis dis daga kasan rahma,du tiles din ya baci,tana gani ta saki wani kukan,

Ahmad ne yace saurareni kiji rahma ke baki San period ba jinin haila da hukuncinsa wai? daga kai tayi tace nasan komai,yace to shine fa cutar taki,ai sai rahma ta fashe da daria tana ta tsalle tana murna,kamar an mata bushara da aljanna,ya ahmad kallon ikon Allah yake kawai,kafadunta ya rike ya turata toilet,pad ya Ciro ya bude ya mika mata tare da new pant,da ruwan zafi tayi wanka tasa pad dinta cike da murna,tana fitowa har cleaners sun shigo sun mopping room din tare da kara wanke toilet kamshin dadi ke tashi kawai,Riga da skert na atamfa tasa green and yellow dagwas da ita,ta fesa turare ta dane kan gadonta,ahmad ya gyara jakar kayan da kayan data cire,sallar isha yaje yayi ya dawo,tea ya hada musu da kansa yake bata tana ci shima haka,har suka koshi rahma sai murmushi takeyi kasa kasa,yana kallonta,ya rasa murnar da takeyi,itakam dadin ta fara period take,itama ta girma,ba shegen da zaice mata kwaila a schl,ga kuma dadin yanda ya Ahmad ke tattalinta,ji da ita,kuma ya daina daure mata fuska kamar da itakam wannan jinya ta mata dadi da haka ake jinya da taso a dinga kwantarta a hospital tana kallon Ahmad dinta kusa da ita kullum.

Dago fuskarta ahmad yayi yace lfy kike kuwa little sis sai daria kike,ko a kira doctor?kunya ce ta kamata,kara kyalkyalewa da daria tayi tare da boye fuskarta akan bed.

Asmabaffa
[12:40, 1/25/2018] ‪+234 806 420 6896‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

110-115

by
Asma baffa


Readers ina kara godiya sosai da karanta wannan novel,da yanda kuke binsa kullum ana Neman ci gaban kuna karamin karfin gwiwa,da masu yabon yanda yake dadi na gode kwarai.



Zazzabi yawa ahmad zafi a nade yake cikin bargo me taushi yana rawar sanyi,rahma kuwa tunda ta shigo ta hau gyaran part din nasu sai da ta gyara ko ina kal kal sai kamshi ke tashi da kyalli,room din ya ahmad ta nufa iya nan ne bata gyara ba kuma shima ai dole ta gyara ma,sallama tayi da nocking amma shuru,kawai turawa tayi tare da shigewa toilet nasa,dan ta hango ya ahmad kwance amma bata lura da yana rawar sanyi ba zatonta bacci yake sha kawai tunda tasan lfy suka dawo,

Toilet ta kalkale masa shima,sannan ta fito room din ta share da mopping din ko ina ta shirya komai inda ya dace,sai kyalli da kamshi haka ta gyara upstair ma shar bedsheet ne kawai bata canja masa ba coz yana bed din yana bacci,

Dai dai jikin bed din taje da ta karewa ya ahmad kallo ko taji sanyi a ranta,ko ba komai ta dinga tariyowa tana kallan zallar kyawunsa,

Tsayawa tayi gaban bed tayi tsuru,daga baya ta gano kamar fa vibrating yakeyi shi kadai kamar Wanda akewa shocking da wayar lantarki kaf kaf,lumfashi yake ja da kyar,ai da sauri rahma ta yaye bargon kadan,subhanallah tace tare da sakin kuka marar sauti,yau farin cikinta ba lfy,

Yayana?yaya?ya ahmad lfy me ya faru,da kyar ya mata nuni da ta dauko masa magani da ruwa,drowar da yayi pointing da yatsansa ta duba jiki na rawa ta kawo masa ya sha ya kwanta,zama tayi a gefen bed din tana jira taga yaji sauki,kin fita ko ina tayi du sallolin ma a room din tayi,tana idar da sallar la'asar taga ahmad ya yaye bargon daya rufa ya kara karfin ac,da ganin haka tasan zazzabi ya sauka,kitchen taje ta shirya masa paten dankalin turawa yaji hanta da kifi me ruwa ruwa,sai lemon tea data masa ta kawo masa,yaci ya sha yaji dadin girkin sosai,mikewa yayi ya Shiga toilet kafin ya fito rahma ta canza new bedsheet ta kwashe kwanikan daya ci abinci room ya kara share,wanka yayi ya shirya cikin jallabiya baka ya fara sallar da ake binsa,bayan ya idar Quran ya karanta sosai tare da addua dan yaji sanyi a ransa,kan bed ya koma ya zauna yana tasbihi ga wasu hawaye na fitowa da idaniyarsa,rahma ce ta shigo da wani glass cup hadadde kankana,apple,pineapple, ,inibi da banana tayi blending tasa fresh milk liquit ta kawo masa ko zaisha,ganin hawaye a tsadajjiyar fuskarsa yasa ta saurin karasawa ta a jiye cup din,

Yaya lfy,me ya sameka,shi kuwa da sauri ya goge kwallarsa kar ta gani amma ya makaro,yaya me ya bata ma rai?nothing kawai yace,yaya ko nice?ya kada mata tare da cewa no,ammar?a'a Mimi?no su salma? no office? A'a frnds?kada kai yayi alamar ba su ba,tace momi da dady?yeah yace mata a hankali,kamar wani dan yaro

Yaya case din a kainane ko? Yace ba naki bane,dadi taji tace eyya yayana am so sorry iyaye sai hakuri,dole a musu biyayya,ko me sukai maka ba a fushi dasu dole a bi su a hankali in dai har bai sabawa Allah ba,haka ta zauna ta dinga wa ahmad nasiha kan girma da darajar iyaye,yaji sauki aransa ya kuma samu nutsuwa a ransa,lallai rahma mace ce ta gari abar so,ga addini komai ta hada gashi ta taso tayi rayuwa ita daya,lallai Wanda allah ya shirya ko a INA yake ko a ya ya taso tofa shiryayyene ga Wanda suka taso ma cikin gata da iyaye basu kai ta hankali da addini ba,ga sanin ya kamata kai masha'allah rahma du a ransa ahmad ke wannan zancen a zuci,

Ita kuwa rahma tana zaune gefen bed din fruits din ta mika masa a cup ya shanye ko ba komai ya samu saukin zuciarsa,alwala ta dauro tace ya ahmad taso muyi sallah na tayaka addua,domin komai in zai zo Allah ya kawo mana agaji da sauki,

Allah yana son mutum me yawan addua sai kaga ya canja ma komai da mafi alkhairi abinda baka zata sai ya faru.mikewa yayi ta tsaya bayansa sukai ta lafila da yawa suna addua.

Abin mamaki sai kaga wasu matsala ta samesu sun kasa bacci amma sun gagara su mike da salloli da karatun alqurani da sauran aikin kwarai domin sukai kukansu wajen allah, kaga mutane da yawa musamman mata baza su Dage da addua ba ga matsala jingim,wasu ma sai dai kaga sun kwashi kafa an kaiwa bokaye malam tsibbu kuka ayi musu duba da aiki,ga Allah maji roko amma anki yin addua,aji tsoron Allah mu daina shirka jama'a wlh karyace a ciki gwara ka ki rungumi Allah da addua shine dai dai.to wasu ma sallar farilla bata damesu bare addua da nafila.

Asmabaffa
[12:41, 1/25/2018] ‪+234 806 420 6896‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

115-120

BY
asmabaffa

Bayan sun idar da sallolinsu addua sukayi sosai rahma bata San akan mene ba amma tayi masa wadda ta dace sosai,tuni ahmad ya samu jin dadi da sanyi ransa,direct dakinta rahma ta wuce,shi kuwa computer ya dauko ya fara aiki ciki,da safe kamar kullum baba driver ne ya dawo daga garinsu.ahmad ne bayan yaje wurin su dady ya fito ya tarar da drivern rahma ya dawo,wajensa yaje suka gaisa ya masa umarnin yaje ya huta for 3days sabo da gajiyar hanya, sai Monday yazo ya kai rahma yaji dadi sosai godiya yayi wa ahmad duk da haka ahmad sai daya mika masa kudaden kashewa gaskia baba driver najin dadin aiki da su ahmad da rahma,rahma CE ta fito da sauri tana duba baba cikin shirin schl,ahmad ya hakimce cikin wata sabuwar dalleliyar Benz tasa yana karewa rahma kallo yanda yaga ta girma sosai breast nata sun ciko sosai,ga hips nata ya fashe abin kallo da birgewa,fuskarta sai shining takeyi Dama gata jar fata fara da ita amma ahmad ya fita fari,du da dankwalin data daura gashinta ya fito ta gaban goshinta kwantacce da sajenta yabi ta gefen kunnenta zuwa keya,baki luf. Luf me sulbi

Hijab dinta ya kalla yaga da kadan ya wuce kirjinta,horn ya danna mata tare da sauke glass kasa,daria tayi ta daga masa hannu daga nesa,tace yaya baba driver nake jira ta kwala da karfi,da hannu ya yafitota, ta karasa wajensa dauke da murmushi harda tsallenta kadan, yaya banga baba driver ba kallonta ahmad yake sosai yawan fara'arta na birgeshi sai kallonta yake kamar ya lasheta dan me kyau ce rahma,

Gaban mota ya bude mata yace get in,shiga tayi ta zauna ya ja mota,suna hanya ya dauko wani karamin flask da cup karami ya mikawa rahma yace tsiyayo min abin,karba tayi ta tsiyayo sai taga cuffee ne hadadde ciki,tsiyayowa tayi ta rufe ragowar na flask din ta mayar bayan sit,tace gashi yaya taya zansha ina tuki rahma? Tana so taji ahmad yace mata rahma akwai dadi sai taji kamar aljanune suke fada dan dadi,

A baki ta dinga bashi yana tuki har tissue ce a hannunta kamar wani yaro take bawa,ya rage kadan ciki yace am OK, rike cup din tayi ta dinga goge masa baki da tissue,shi daria ma abin ya bashi kamar wani danta,murmushi yake sosai har ta gama,cup din ta daga da ragowar cuffee ta shanye sai lashe pink lips nata takeyi irin tasha ragowar ahmad abin sonta,ahmad na kallonta ta gefen ido yana kunshe dariarsa.

Juyawa baya tayi ta dauko flask din ta tsiyaye ragowar a cup gashi ahmad yayi parking a schl dinsu,mika masa cup tayi wai yaya sha wannan kaji yafi dadi wai ita dole wayo ta masa dan yasha ita kuma ta shanye ragowar tasa,

Ya ahmad ne yace nafa koshi rahma shagwabe masa tayi pls yaya ni Allah sai kasha,kadan ta bashi ya kurba ta janye cup din ta shanye sauran,tana ta murna ta bude motar ta fita,ya juya motar zai tafi ya tsaya ya mata horn ta dawo,tana zuwa ya zuge glass ta zira kanta ciki tambayarta yayi me kike son ci yau gashashen kifi da chips,kwadayayya ayi karatu sosai jeki class.ya ja mota ya tafi ita kuma ta wuce class cikin nishadi.

Tunda aka kai rahma schl wani malaminsu malam sagir ya nace shi sonta yakeyi da ya takurawa rahma,kullum sai ya kirata in an tashi daga boko kafin su shiga bangaren Arabic,

Ta tsaneshi bata masa magana ko taje wajensa haka zai kari surutu ta juya ta shige class,abin ya dameta,so take ta fadawa ya ahmad yaje Schl din ya mass warning amma tana gudin kar ta batawa yayanta rai shi yasa tayi shuru,

Kamar kullum sun tashi daga bangaren boko sunyi sallah sun fara dinner b4 su shiga islamiyya,malam sagir ya kira suna tsaye da sharbebiyar bulalarsa,yau zai Zane jikin rahma tunda taki karbar soyayyarsa,ga wulakanci tana masa dan haka yau sai yayi maganinta,

Tana tsugune gabansa yana zabgarta da bulala tana hawaye, ahmad kuma ya danno mota ciki yazo kawo. Mata kifi da chips da tace zatayi dinner dashi,itakam bata zata schl zai kawo ba ta zata a gida yake nufi tunda dinner yace ba lunch ba,shi kam surprise zai bata,shi yasa yace mata dinner,

Rahmansa ya hango wani gardi ya dame mata hijab yana labta,take idonsa yayi jajir sabo da bacin rai.
[17:49, 1/30/2018] ‪+234 802 498 6436‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

120-125

BY
asmabaffa


Wannan shafinku ne masu tambayar ci gaban wannan novel.


Ko gama daidaita motar baiyi ba ya fito cikin kana nan kayansa wando jean fari,sai Riga longslip yayi kyau kamar bature,kowa zuba masa ido yayi ana kallo cike da kasaita da isa cike da izza ya ke takawa ,yana zuwa wurin malan sagir ya shaki kwalarsa ya fesa masa maruka biyu a jere ya shake malam sagir,idonsa yayo waje kamar zai mutu da kyar teachers suka kwaci sagir a hannun ahmad,

Mutane yan kallo har yan waje sun shigo schl din ana bawa ido abinci,huci kawai ahmad keyi yana masifa,walli du Wanda ya kara taba min sis a schl din nan sai nayi kararsa cikin harshen turanci yake magana,da kyar principal ya lallaba ahmad yana bashi hakuri dan ahmad yace cire sis dinshi zaiyi daga schl dinsu,hakuri akayi ta bashi har ya hakura da kyar,tarzoma ta lafa an settling case da student,har sagir an masa last warning kan students.

Komawa yayi wajen rahmansa dake hawaye,tsaye ya mikar da ita ya dauketa cak kamar jaririya yan schl sai kallonsu akeyi sun birge wasu, wasu kuma sai kishi suke da rahma suna son ya ahmad,cikin mota a hankali ya zaunar da ita ta huta sannan ya shiga bata kifi da chips da kansa yana kora mata da lemo me sanyi,taci ta cika cikinta yace ya jikin?rahma sarkin daria murmushi tayi tace normal,

Je class har anyi nisa ana darasi dan 4pm tayi,masallacin schl din yaje yayi sallah ya koma mota kida ya kunna yana ji ya lumshe ido,kawai abunda yake tunowa shi ke bata masa rai yanda ya tuna malamin nan ya damewa rahmansa hijab kirjinta ya fito maza kowa na gani gashi a bainar jama'a ya kunyata masa ita yana dukanta cikin mutane.

Tsaki kawai yake ja,yana wannan tunanin har yaga students sun tashi yana duba agogo yaga 5pm,rahma da husna sai wasu gun gun student suka taho wai sai sun gaishe da yayan rahma,amma wasu dan sukare masa kallo suka zo,wasu kuma suna sonsa,rahma ce ta bude gaban mota tana wash yaya na gaji hade da jefa littafanta baya,husna ce tace yaya ina wuni ya amsa da sakin fuska tabi drivernta ta tafi gida,ita kuwa rahma kishi yasa ta daurewa sauran mata fuska sunzo kalle mata yayanta,dan tasan sonsa sukeyi da gulma,

Ahmad kuwa ko kallonsu baiyi ba bare yasan suna wajen,rahma da biyu taki rufe kofar su tafi ta kama yiwa ahmad shagwaba dan student suji haushi,yayana kalla yatsana yanda ya ke min zugi har nan ma ya shauda min bulala kalla ta nuna masa wuyanta tare da cire hijab,kamar zatayi kuka tana lankwashewa tana yarfe hannu,batasan ta iya shagwaba sai yau,ta gama kashewa ahmad jiki,biye mata yayi yace sorry little na yana duba wuyanta yana ta wani lallabata,ya kwantar mata da kujera huta my little,ta wani kwanta tana cewa yaya bazan iya rufe kofar ba,da Kansa ya rufe kofar,students munafukai na ganin haka suka watse kowa yayi hanyar gida.itakam dadi ya kamata tayi maganinsu shegu,

Suna isa gida yau ya gaji a gurguje yaje part din momi ya koma room wanka yayi ya kwanta yana hutawa,rahma ma hakan take.washe gari kuwa suna dawowa ya shirya ya fice,rahma taga ahmad yasha wanka da yamma lis ya fice,ta kasa zaune ta kasa tsaye karfa ko ahmad zance ya tafi wajen budurwa,kaji rahma da karfin hali ta gumi tayi har bayan sallar isha ta kasa cin abinci,tayi tagumi kishi ne cike a ranta.

Shi kuwa ahmad shopping ya fita daga nan ya wuce gidan su shahid.sai 9pm ya dawo ya iske rahma tayi tagumi,kaya ta gani Leda leda a hannunsa,sabo da kishi ko sannu da zuwa yau batace ba.

Kallonta yayi yace lfy?lfy tace kawai,zo yace mata kawai ya haye sama binsa tayi a baya,har palonsa na sama a kujera ya zauna taje gabansa ta zauna a kasa, naje wajen shahid yana gaisheki,dadi taji Ashe ba zance yaje ba,har ta saki rai fara'a ta fara sosai,ledojin duka ya mika mata,guda dayace tasa a ciki.wata ledar ya karba wajenta yace bari na hada mini wannan,wata dalleliyar waya CE ciki a kwalinta tecnoc9+ tuni rahma ta washe baki,kan kujerar 2seater wacce yake zaune ya nuna mata kusa dashi yace dawo nana ki gani,tana zaune kusa dashi ya hada komai ya nuna mata komai,rabi tana gani rabi kuma du halittarsa take karewa kallo tare da shakar kamshinsa tana lumshe ido kamar ta kwanta bacci jikinsa takeji,har wani gyangyadin dadi takeyi,numbarta yasa wayarsa ya kira tata wayar yayi saving da my rahma,yayi dialing number kiran ya shigo ya wayar ya mika mata yace tayi saving daga wayar dan kar ya ga me tayi saving da tasa masa my peace.su rahma an fada da yawa...

Ledojin yace ta kwashe in taje room ta duba,tana shiga ta baje kaya wasu new design arabian gaunt ne da cosmetics,sai kayan gyaran gashi su mayukan gashi,shampoo,hair steamer,hair spray ko wanne kala kala hair hand drier,hair straightener,sarkoki da bangles,agogo kala 4,ko wanne kala kala,komai shar,dan shi ahmad ji yake da rahma kamar yarsa dan komai a hannunsa yake dole ya kula da ita tunda su momi sunki yarda da ita,kuma sun kasa gane illar barinsa da ya mace kamar rahma ya ajiyeta kusa dashi ba muharammarsa ba ya jira yaga ko zasu gane hakan ba dai dai bane a musulunci amma Sam harkarsu sukeyi,kuma sun kawo wata zasu aura masa ai ganinsa gwara a bashi rahma ya aura duk da ba sonta yake ba zai riketa.




Asmabaffa
[17:50, 1/30/2018] ‪+234 802 498 6436‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

125-130

By
Asmabaffa.


Kamar kullum abubuwa nata ta fiya normal wurin rahma yayinda ahmad ke cike da kuncin aure yana matsowa daf,inda Mimi take ta gyaran jikinta da shirye shirye,amrata ana nijar tana nata dan ta matsu ta dandani zumar ahmad ta dalilin haka take ci gaba da fasikancinta abin nata yawa yakeyi dan tunda ta taso rayuwarta a bin maza ya kare,anyi fada da nasiha amma ina,tasan ko ta auri ahmad baza ta daina harkarta ta yau da kullum ba,duk abinda takeyi ahmad ya San komai yana bibiyarta ba tare da sanin kowaba,shi yasa kullum cike yake da takaici,

Amrat cikakiyar yar duniyace ta gagari iyayenta amma dady Sam baya ganewa momi kuwa tasan amrata ba matar auren ahmad bace danta baiyi dace ba ammma a ganinta da ya auri wata ko rahma gwara amrata,

Shi kam ahmad ya tabbata dady tsofaffin da ne masu karancin tunani ,abin na damunsa rashin hangen nesa na dady,ammar kuwa cewar sukai kauyece ke taba dady har yau,Mimi da salma sukace ragowar miyar kuka ce a kansa,momi kuwa sunce bin bayan mijinta take sabo da soyayya.dan sun tabbata tafi dady ganewa,

Bikin ahmad da Mimi saura 3wks Wanda har yau rahma bata da lbr,ga ahmad ya tafi Dubai hado lefe da kuma kayan Mimi,inda rahma tayi missing nasa sosai har Takai yanzu a bed dinsa take kwana.samun wuri su rahma kwana har dakin ahmad bai sani ba,saura 2wks biki Ahmad ya dawo gida,yana part din momi ya zube musu akwatuna guda 9,sun duba kaya yayi,sai na gida Nigeria aka zuba suma akwati sun zama 11.

Mimi kuwa a zamar da gidanta kamar a turai yanda aka shirya shi,su salma ba zama kullun rabon I.v da gyaran jiki,

Shahid ne ke ta rabon na ahmad,RAHMA baiwar Allah ana ss2 sai karatu taga gida dai sai shige da fice akeyi amma bata San mene ba,

Yau kwana biyu da dawowar Ahmad ko rahma bata San ya dawo ba yana can ya kama hotel yana hutawa kuma baya son momi ta dameshi da zancen bikinsa.

Amma yau ya yanke zai koma gida kodan yaga rahmansa dan kewarta yake sosai,karfe takwas na dare ya je wurin mum a gurguje ya tafi part dinsa,rahma ta gama gyara gidan kaf sai kamshi ke tashi,gashi tana ta girki a kitchen,sanye take cikin rigar atamfa 3quater da zani dai dai ita caras da ita,tana zaune tana kallo remote a hannunta yayin da take jiran girkinta ya karasa,

Sallamar ahmad taji ai da sauri ta jefar da remote ta daka tsalle tana murna oyoyo yaya...oyoyo yayana ,sannu da zuwa yaya tana wakar da yara keyi tana tsalle,dariyace ta kwacewa ahmad sosai,

Da gudu ta kwaso ta daneshi bai zata ba wani shock Ahmad yaji ai rigis suka fadi kasa,sai tumurmusa takeyi kamar dai yara kanana,

Da kyar ahmad ya kwace jikinsa,ya koma kujera.durkusawa tayi baki har kunne ya ahmad sannu da dawowa,kallonta kawai ahmad keyi,dan ta birgeshi ta sashi nishadi,Rabin da yayi daria tun kafin yayi tafiya,

Abincinta taje ta sauke ta shirya a dining kamar tasan zai dawo tayi pounded yam da miyar egusi tasha naman rago,ga farfesun kaji tayi,ga kankana ta yanka a plate,ta kawo ruwa da zobo me sanyi data hada, yasha kayan kamshi,

Riko hannun ahmad tayi sai murmushi yakeyi, zaunar dashi tayi ya dinga dura girki me dadi cikinsa,Rabon da ya ci abinci me yawan haka ya manta ranar.

Kwashe komai tayi ta gyara wajen har kitchen,ta fito taga ya ahmad ya fita,tana zaune taga baba driver na shigowa da new akwatuna masu kyan gaske,sai da ya shigo da guda 14 falon,

Ahmad ne ya shigo hannun rahma ya jawo ya zauna a kujera itama ta zauna kusa dashi,bude mata akwatuna yayi komai size dinta ne har dinkunan su atamfa,laces,shadda etc.yaya wannan fa kamar lefe ta tambaya zuciarta na bugawa karfa aure zaiyi,take ta dinga tuno yanda taga an kara gyaran gidan da shige da ficen da akeyi kullum,take jikinta yayi sanyi murnarta ta koma ciki.

Ahmad yace little sis,kallonsa tayi zuciarta na suya,aure dady zaimin da wata yar uwata a nijar,amrata sunanta,shine damuata bana sonta dady ya matsa min,ki tayani addua my little ina ji a jikina da kyar in auren zai yiwu.

Nan ya dai zayyanewa rahma komai,ta tausayawa kanta da kuma yayanta halin da yake ciki.

Ai ranar rahma kwana tayi tana kuka da addua,in tayi kukan sai addua,kamar mahaukacia haka takeyi,

Rahma har ta rame sosai ga biki saura 5days,tawagar amarya sun dira a gidan su ahmad ango,anan za ayi shagalin,suna part din mimi,
Ammar ne yaje wajen dady da momi kan su yafe musu su dingawa rahma magana,kuma a barta ayi shagalin biki da ita,sun yarda kuma sun amince, murna wajen su mimi ba a magana,ai da gudu suka shiga part din ahmad.jikin rahma suka fada kan kujera,ahmad na zaune gefe yana binsu da kallon mamaki,ammar ne ya fada masa su momi sun yarje musu,yaji dadi a ransa sosai,rahma ma taji dadin su momi sun rage tsanarta,nanfa aka baje koli ana labarin biki,yayinda labarin bayawa rahma dadi,haka ta daure sukai ta hira,ammar sai tsokanarta yakeyi,kusan yini sukayi a part din ahmad yau,

Biki saura 2days a fara tuni rahma ta saba da kawayen su mimi,tare akeyi da ita,momi ta fahimci rahma abar so ce kuma me hankali,bata da aibu,ga ladabi da biyayya,ga aiki da girki ba kyuya ba ganda,momi ma ta fara sabawa dan in rahma ta shiga part din komai da ita akeyi,

Dady ma ba laifi ya kuma gano rahma ta kirkice ga ladabin da take musu kamar su suka haifeta,ahmad najin dadin hakan da sauran family,bangaren amare amrata da frnds nata sun tsani rahma yanda suka ga ahmad shike kula da ita,sai zagi take sha da tsinuwa kullum,tun tana damua ta daina ma,

Salma da rahma sukaje saloon dinsu,sunyi kyau,zo kuga gashin rahma har tsakiyar bayanta,kowa kallonta yake suna inama nasu ne,

An kira me kunshi Ta zana musu wohoho momi kanta tana jinjina kyau irin na rahma,gyaran jiki suma an musu na 1wk,amare ne dai keta yi da yawa,amma rahma da salma na sati aka musu,me kula da amare wajen magungunan tsumi har rahma da salma take durawa maganin tsumi.

Abin masha Allah ahmad yini yake baiga rahma ba bacci ke kawota part dinsu,daga schl sai wajen su Mimi,ta gayyaci kawarta husna da wata rukayya kawai.




Asmabaffa
[17:51, 1/30/2018] ‪+234 802 498 6436‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

130-135

BY
asmabaffa


Haushi ya ahmad ke ji sosai na rashin zaman rahma a part dinsa,wai har tafi son su Mimi da ammar a kansa,shi za ayi bikinsa ma ko ta tayashi jaje amma ritin shagalin bikin take...ni kuwa nace dan ma ahmad baka ga gyaran da sukayi ba lol.abinda ahmad bai sani ba rahma kullum sai tayi kuka da dare za a kwace mata ahmad dinta,kawai daurewa takeyi, amarya kuwa anci attach tayi kyau kuwa,dama tana da dan kyau kadan dan dangin su ahmad kaf ba baki sai dai amrata kadan ta kwaso farin fatar.amma akwai wanka da iya kwalliya,shi yasa bariki ta amsheta,

Yau ta kama Thursday yaune kuma za aje dinner ta farko by 7pm,da kyar aka shawo kan ahmad shima sabo da mimi ya yarda zaije,amrata amarya ko kallo bata ishi ango ba ko magana bata hada su,yau angoma akwatuna Biyar ya hadawa kansa,dan yace bazai siya mata ba shi kuma ya zauna da Tsoho,ahmad lefe ya hadawa Kansa na akwatuna biyar na kayansa,Inda ya

Please Login or Register in order to submit comment