Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayanta abinda sonta,abin afaharinta mum and dad dinta wanda takejin zata iya sadaukar da ranta a kansa,ya shirya? Amma shuru ta tafi zata hau steps kenan domin yi masa magana kar tayi late dan 7am tayi,wani azababben kamshi ne ya daki hancinta Wanda take ya kara zuke mata jini,dan har kasala takeji dan dadin kamshinsa,

Sanye yake cikin wata tsadajjiyar suit fara kal dai dai jikinsa kamar a jikinsa tela ya dinka,abinka ga fari dama gashi kamar bature,ga gashin daya Tara sai sheki suke tare da dan sajensa da gemu kadan,abin sai Wanda ya gani dan sai ka yini kana kallonsa ba tare da ka gaji ba,

Da sauri ta durkusa yaya barka da asba,ka tashi lfy,kallonta yayi cikin kasaita da isa na Wanda yake ji da kansa,ilmi,kudi,kyau,ga Khan hali ba laifi,da kyar yace am fine kije parkingload ki jirani, I wl be there soon,ba ganewa tayi ba amma ta gane kije ta gane parking dan haka ta fahimci lalai taje ta jirashi a wajen da ake parking,murmushi tayi tace lallai nima Ashe kwaruwa ce,ina jin turanci,fitowa tayi taje wanjen cars din,

Tana tsaye nan taga ammar ya fito daria ya mata ya daga mata hannu ya shiga motarsa ya fita da alama aiki zaije shima,tana tsaye mimi da salma suka fito suma kowacce cikin shiri,murmushi suka mata mimi ta daga mata babban yatsa daya,dan ba ikon magana dady yayi baki,

Mumy da dady ne suka fito suma suka hau mota daya su kam ko kallonta basuyi ba,amma du da haka saida ta tsuguna ta gaishesu ko kulata basuyi ba,gwara mum ma ta kalleta,rahma ce take tunani to su kowa a gidan Neman kudi yake ba yaro ba babba amal ce kawai sai schl,bata fara ba,tana wannan tunanin ahmad ya fito da alama breakfast ya tsaya yi,wata luntsumemiyar mota ya hau baka,gaba rahma ta bude ta Shiga dan a birni taga haka akeyi in dai ba driver bane,7:30suka dauki hanya,7:40 sunje coz ba nisa,har ciki ya Shiga da ita ya hada ta da manyan schl din idan sunji kanwarsa na bukatar wani abu ko matsala a nemeshi,anga yar me kudi sai nan nan teachers suke da ita a staffroom,

Kudi ya Ciro 1000 ya bata na break,idan an tashi time din ya tashi daga office zaizo ya dauketa,idan da matsala ga number ta cati ya miko mata har 2 daya numbersa da address din office dinsa dayan kuma number sa da address din gidansu,ya nuna mata komai, ai kuwa ta Adana komai a bag,har ss1A aka rakata.

Du schl din kallonsa maza da mata keyi har ya fita,direct office ya wuce company da yake aiki, ita kuwa student mata da maza sai kallonta akeyi gata yar fulani me kyau ja ja fara fara,ba abinda ke basu daria irin hausarta da bata fita saboda tafi jin fulatanci,haka take hada haukan turancinta tayi har daria ake mata amma ita ko a jikinta, kuma baza ta taba shuru ba domin tace in tayi shuru ta zama jaka ta karshe dole tayi magana tafi iya komai da wuri kar a rainata.ga yan ss3 sunga ahmad yayan new student wasu da yawa suna sonsa,dan haka suka dinga kula rahma dan ta musu hanya ko zasu sami shiga,haushin su ma takeji har wani epizi take tana sharesu dan sun bata mata rai dan me zasu so yayanta.amrata ta nijar tana can tana ta kiran dady on phone tana kama kafa akan aurenta da ahmad dan ta matsu dady yayi maganar,Wanda uban gayyar ahmad bai San komai akai ba.dady da momi kuwa kara kaunar amrata sukeyi tare da kwantar mata da hankali cewa in dai za ayi bikin mimi nan da 8mnths da na amrata da ahmad za a hada,murna wajen amrata ba a magana.

Asma baffa
[14:57, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMA

80-85


Rahma dama an saba zuwa kiwo tun safe sai magrib dan haka yau gashi shine na farko da ta zauna a schl tun 8am sai 5pm aka tashesu ko gajiya bata ji tayi ba dan dama ta saba,wajen gate take so itama ta fita inda taga student na fita dan so take ta jira yayanta ahmad yazo daukanta,ta taho hanyar waje kenan taga an wangale gate din schl din motar ahmad ta hango ya cinno hancinta cikin schl din,mutane caaa akayi ana kallo waye wannan daukan student bazai parking a waje ba sai ya shigo ciki,

Da fara'arta ta karasa wajen motar ta bude ta shiga wani sanyi da kamshi ya daketa,har lumshe ido takeyi,barka da yamma yaya ya aiki,lfy kawai yace yaja bakinsa yayi duf,suna zuwa gida ta wuce part dinsa yayi bangaren su mum,yana zuwa jikin mum ya kwanta yana wash na gaji,momi ce ta tabe baki tace ba dole ka gaji ba ka dorawa kanka wahala daukan nauyin mutum azamanin nan kuma marar asali ma,bata rai yayi tare da ficewa daga palon cikin fushi dan ko abincin ma bazai ci ba,dakin dady ya nufa,da ammar suka ci karo zai shiga palon gaisawa sukayi suka danyi hira a tsaye,bro ina zaka naga yanzu ka shigo cewar ammar,ahmad yace kasan su mum wlh na rasa me yarinyar nan ta musu ni tausayinta ma nake,ammar ne yayi murmushi tare da jinjina kai sai hakuri bro,kaci gaba aikin lada kakeyi sosai kar ka gajiya,bari naje wurin dady cewar ahmad,ammar ne yace ai dady baya nan ka manta zai Cairo za a masa medical check up,ahmad yace na manta ne nan da 3wks zai dawo ai,part din su mimi ya shiga ya duba su ko sun dawo aikuwa du suna Palo zama yayi cikinsu duk da shi bame surutu bane na 30mnt ya mike ya wuce part dinsa,momi kuwa ammar na shiga ta tareshi tace my son kalli bro dinka ya susuce ya zama banza sai wahala yake da yarinya,ba a isa a fada masa gaskia ba sai yayi fushi ya fita ko abincin bai ci ba,Allah shirye shi ya ganar dashi dan sai addua,ammar shi mum ma daria suke bashi wlh amma haka ya dingaawa momi dabara da wayo har hankalinta ya kwanta,tace to shikenan ai sai yayi ta yi,dan na daina masa ma zancenta sakaran banza,a ranta kuwa tace ana aura masa amrata zata kori yarinyar daga gidan,dan tasan amrata baza ta bar rahma gidan ahmad ba.

Bangaren rahma kuwa tana shiga part din uniform dinta ta cire ta wanke su kal sannan tayi wanka,ta shirya cikin wata shadda dark pupple ba wata kwalliya tayi ba powder tasa da Jan baki ja kadan,dakin ahmad ta shiga yau domin ta gyara masa gaskia ya hadu dan ta kusa suman tsaye dan kyan room din,gaba daya kamshi ne ke tashi komai Fes amma haka ta kara kalkale saman ahmad din du,komai kamshi yake da sheki,sallar magrib tayi ta fada kitchen,littafin koyon girkinta ta dakko dan tun a kauye tana da abinta wata da take zuwa birni ce ta ke siyarwa mata dan haka itama ta siya guda biyu daya na abinci daya na juice,

Miyar kwai tayi tasha naman rago da pounded yam,sai tayi farfesun kifin gona ta hada fruit salad,sunyi dadi sosai,komai kadan tayi dan ahmad baya cin nata,dama rahma akwai son a iya abubuwan birni musamman girki da kwalliya burinta kenan shi yasa take cikin farin ciki tare da godewa Allah da kuma yiwa ahmad addua kullum,jera komai tayi a dining dan tace itama ta zama yar gayu yanzu. Sallar isha tayi ta fito wurin dining zata ci abincinta,ya ahmad ta hango zaune a palon kasa yana latsa waya abin mamaki bata ga yayi wanka ba, har wajensa tazo ta tsuguna tace yaya ga abinci ka dandana kaji na iya Allah, shi yanda take kwantar da Kaine ke bashi ma daria,ya gaji da tayin girkin da take masa bai taba ci ba,gashi yau dama baici abincin mum ba,yunwa yakeji gwara yaci na rahman yau dan bazai iya fita restaurant ba,danshi sai dole yake cin abinci waje sabo da kyankyami.

Asmabaffa
[14:57, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMA

85-90

BY
asma baffa


Umarni ya mata da ta zubo masa ta kawo a gajiye yake bazai je dining ba,cike da murna da zumudi ta zubo komai daban daban,fruit salad kuwa zuba nata tayi a cup ta kawo masa jug din gaba daya,jiki na rawa yau ya ahmad dinta zai ci girkinta dan bata da burin da ya wuce ta faranta masa tare da birgeshi,kadan ya fara ci yaji wani azababban dadin dan rabon da yaci girki yaji dadi haka bazai iya tunawa ba,zagewa yayi ya Lodi abincinsa,fruit salad kuwa sai da ya shanye shi tas ya masa dadi,yayi mamaki yarinya 15yrs da iya girki haka,sama yahau yasha mamakin gyaran dakin dan yasan rahma ce tayi,cikin nishadi ya salla wanka yayi nafila ya zura kayan bacci ya haye bed sai bacci,rahma kam wanke kwanukan tayi ta gyara wurin da kitchen,ta shige daki,wanka ta sake itama tasa rigar bacci ta dauko littatafanta tayi karatu,inda bata gane ba ta barshi da safe ta tambayi ya ahmad,

Bacci ta kwanta amma bacci yaki zuwa mata sai tunanin ya ahmad take tana daria ita kadai,a haka har bacci ya saceta,washe gari 7am ta shirya tana jiran ahmad dan yana part din mum kamar kullum,a wajen ajiye motoci ta jirashi,yau bai Dade ba ya fito sun Riga kowa na gidan fita da wuri,suna isa schl kafin ta fita ta Ciro liffan inda bata gane ba tace yaya dan gaya min nan ni ban iya ba,wata uwar harara ya balla mata yace u r very stupid rahma muna gida daya same part ki kasa daukowa na koya miki sai now,sai ki jira Saturday Sunday me miki lesson tazo ki tambayeta ko wata ta koya miki a schl,sha sha sha wallahi kinji na rantse baki isa kisa nayi asarar kudi ba,dole ki iya kisan me kike dole ki kawo min good result,in ba haka ba wlh garinku zan maidaki ko na aura miki wani na huta,aure zan miki kawai kuma gate man zan aura miki,dakikiya fice min a mota,idon rahma ya cika tab da hawaye kallonsa tayi rau rau zatayi magana yace get lost,tsawa ya buga mata out.da sauri ta fita tana share hawaye,yaji tausayinta bai san dalili ba baya son kukanta,amma dole ya tsoratar da ita,

Yau rahma kawai dai tayi karatune amma hawaye take ta yi,ita ba fadan ne ya sa ta kuka ba ta batawa yayanta rai,ita me son sashi farin ciki ta sashi Bacin rai dole ta faran ta masa,wata student ce husna tana son rahma,gata nutsatsiya ta gari,wajen rahma tazo tace sister lfy?ita dai rahma cewa tayi umh umh yayana ne yake fushi dan ban iya aikin jiya ba,murmushi husna tayi tace wannan baturen,me kyau?banza rahma ta mata dan me za a yabi yayanta ai ita ya dace ta yabi abinta. to fa kaji su ramata,husna yar gidan wani senator ce me ci akwai kudi amma suna da tarbiya su uku iyayansu suka Haifa,aiman,husna,nusaiba.

Husna ce ta koyawa rahma komai ta iya sosai,har abubuwan turanci take ta koya mata dan ta iya,ta kuma yi mata alkawarin koya mata English sosai,ai a ranar suka kulla kawance da husna,ko ina suna tare,husna ta bawa rahma lbrn gidansu,amma rahma kawai lbrn gidan su ahmad ta bata kuma tace ita daga kauye suka daukota ita yar uwarsu ahmad ce,amma ahmad yafi ji da ita .

Suna zaune a class rahma tanajin sauran yan class mata suna ta lbrn period wato jinin haila,kowacce na fadan kalar nata,can wasu sukace ai in bakayi baza ka taba haihuwa ba,take rahma ta shiga firgici,da tunani domin gashi ta girmi wasu yan class din amma sunce suna period ita kuwa batayi,bata taba ba,take ta shiga bacin rai,ita shikenan baza ta haifu ba bata yin period,tabbas ita ba lafiyaya bace,

Ana haka aka kada tashi tare suka fito da husna,tuni ya ahmad ya ruga zuwa daukanta,dan kawai ya barta tana kuka, yasa dole ya taho daukaanta da wuri dan yaga halin da take ci,alhmdllh ya hangota normal,da Sauri ta karaso,husna ce ta gaidashi,ya amsa da kyar ba laifi,shiga rahma tayi a sanyaye ta zauna.

Asmabaffa
[23:12, 1/24/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

90-95

BY
Asmabaffa

Amin afwa banyi posting da wuri ba kun San typing da wuya,ba time kuma.na gode


Kanta a sunkuye dan tsoron ya ahmad takeji ta masa laifi,da kyar ta iya cewa sannu yaya ya aiki,yau radau taji yace alhmdllh,ta danyi mamaki,kallonta yayi yaga hijab dinta ya karkace bari daya,hannu yasa ya gyara mata,rahma sai murna take a ranta yayanta ya daina fushi da ita,a hanya ya tsaya ya musu take away na shawarma,hambugga da kaji,suna isa gida ya bata kayan yace kici iya yanda zaki iya ci ba sai kinyi girki ba,Dama a gajiye take taji dadi,part din mum ya wuce can yaci abinci suka taba yar hira ya kira dady a waya shima,daga nan part dinsa ya wuce,wanka yayi yasa jallabiya fara kal ta masa kyau,saukowa yayi kasa,rahma ya gani kwance a kujera tana bacci hankali kwance,tayi wanka sanye take da doguwar Riga yar kanti marar nauyi,yarinyar na birgeshi wajen tsabta da kula da kai,agogo ya duba yaga 6pm ta kusa,baya son tashinta dan ta gaji yaga alama,sallah ya fita yi ya dan tsaya wajen ma'aikatan gidan ya musu kyautar kudi,dama ahmad akwai kyauta,yayi sallar magrib,a hanya sukayi waya da frnd dinsa shahid zai zo wajensa yaga yarsa kanwarsa rahma dan ya fada masa komai,

Bacci ya sameta tana tayi bata tashi ba,gashi har sunyi sallah tashinta ya fara yi ya dan bigi kafarta,a hankali ta bude sexy eye dinta Wanda yayi ja sabo da bacci,da sauri ta mike yace hey hey relax. Je kiyi sallah to kawai tace ta wuce daki,sallah tayi ta sake wanka dan jikinta weak takejinsa shi yasa ma tayi wankan,manta ta shafa,sai powder ta shafa Vaseline a lips enta ta dauko wani dan hijab dinta me kyau kalar rigar ta sa,ga a cuci anyi sai tayi kyau,Jakarta ta schl ta dauka Arabic da boko ta koma wurin ahmad,

Tana fita taga shahid sai hira suke suna daria,a nutse ta karasa dinining ta ajiye bag en,ta karasa wajensu rusunawa tayi ta gaida shahid cikin nutsuwa,shahid sai kallonta yake dan yaga baiwar kyau ga hankali da nutsuwa,kitchen ta wuce kamar matar gidan ta hado masa drinks da ruwa,shi kanshi ahmad yaji dadin abinda tayi,shahid ne yace kanwar ahmad ya schl murmushi tayi tace lfy lau,ya abokina amma baya zaneki ko daria kawai tayi,shahid sai janta yake da surutu har sai da ta saki jiki dashi ta fara bashi lbrn schl da kawarta husna,shi hausarta ce ma ke bashi daria dan fulatanci tafi iyawa,

Tace kaga kawata fa daya,yace why daya jal,to ai ya ahmad ya hana yin kawaye fa,kuma ma su bana sonsu,zaro ido shahid yayi yace sabo dame?ai sune suna damuna sai na hadasu da yaya,kaga yan ss3 du sunce sonsa sukeyi fa,ni bana musu magana ma,tunda suke hirar ahmad ya kafeta da ido a ransa yace wannan daga ji mijinta zai sha kishi,shahid kam ya fuskanci tabbaas rahma na son ahmd ko ba da yawa ba ta kamu,tabbas ahmad zai iya sonta nan gaba,yayi fatan haka ta faru dan yarinyar na da hankali,

Shahid ne yace ta kawo books nata suyi karatu,ya koya mata abubuwa da ma,kuma ya fuskanci tana da kwakwalwa,shima ahmad yafi kowa mamakin iron basirar rahma,gata a kauye amma tasan abubuwa da yawa,musamman Arabic, yaji dadi kam.haka har shahid ya wuce kowa ya wuce room nasa bacci.

Rayuwa ta ja rahma yanzu tana ss2 first term,tana kokari sosai dan tana zuwa 3,4,ko ta 5 a class ensu,gashi yanzu english ba laifi ta iya alhmdllh,sosai ahmad ke jin dadi baiyi asara kudi,lafiya da time daya bata kanta ba,islamiyya kuwa hmm ba a magana tayi zarra a bangaren ta 1 takeyi,ga wani fari data karayi skin dinta ta murje,har yar kiba tayi kadan,yayin da hips suka kara budewa tare da cukowar na shanu,samari kuwa sunyo caaa amma ko kallonsu batayi dan son ya ahmad ne dankare a zuciyarta,kullum a tunaninsa take,tayi addua amma ina kullum karuwa yake,su rahma an waye,tayi fresh,daga kallonta kasan tana hutawa kuma ana mata abinda takeso,husna kam tuni ta gano rahma son yaya ahmad take,daga yanda take nuna kishi karara bata so wata ta kallar mata shi,shi kuwa ahmad tuni ya samowa rahma driver shi ke kaita da dakkota dan shi busy yake yanzu,shakuwa sosai sukayi da ahmad,sai abinda take so ake mata,hakan bai hanata masa tsananin biyaya ba dan ahmad baya wasa da ita ko kadan bare ta rainashi,Kawancensu yayi nisa da husna amma tana tsoron yayanta ta hana husna tazo mata visiting gidansu itama taki tambayar ya ahmad,bangaren su mum kuwa har yau dady bai sauko daga fushi da rahma ba,amma dai ya rage dan yana amsa gaisuwarta,momi ta rage sosai ta kula yarinyar me nutsuwa ce har murmushi tana mata yanzu in zata amsa gaisuwar,ba karamin dadi rahma da ahmad keji ba,haka su ammar ma,

Dady yaje nijar sunyi maganar auren ahmad da amrata,Mimi ma wani lawyer zata aura usman matashi me kyau ga hankali ga kudi,dan haka dady ya yanke bikin Mimi za a hada da na ahmad nan da 3mnths,ahmad kamar ya hadiyi zucia sabo da bacin rai,amma dole yayi biyayya,rahma bata San zancen auren ba,amma tana yawan ganin ya ahmad dinta cikin damuwa,tunani take taya zata tambayeshi meke faruwa amma ba hanya,shahid friend din ahmad kam yana zuwa sosai sun saba da rahma,me wa rahma lesson meena tuni rahma ta koreta akan in yayanta ahmad ya zo wucewa tana Kallar mata shi,shi yasa tace ita ta iya komai a sallami me lesson lol ,har yau rahma ta gaji da jin lbrn period a schl ita kam batayi,ta matsu tayi amma shuru abin na damunta,

Kamar kullum yau drivern rahma ya fadawa oga bazai zo ba zaije garinsu ganin iyalinsa ba lfy bai San ranar dawowarsa ba amma zaiyi waya,kudi ahmad ya bashi da yawa tare da kayan abinci,rahma kuma ta kwaso kayanta da taga zata iya badawa ta bashi ya kai gida ko da masu so,yayi Murna kwarai da gaske,

Cikin shirin makaranta take tana jiran yayanta a palon kasa,sakkowa yayi cikin wani danyen boyel fari kal hula baka da takalmi baki,yayi matukar kyau,anan ta lakace tana kallonsa har ya zo daf da ita bata kula ba sai kamshi taji,let's go yace da ita kawai,firgit ta dawo tare da saita kanta suka fita kowa ya gansu yasan sun dace,

Tunda suke hanya ya ahmad ya kula sai cije lips takeyi tana dan rike ciki,ke are u okey?kai ta daga tace yea,yace good rashin jini ya motsa kenan,cike da shagwaba tace a'a yaya,haka kawai take jinta in tana gaban ahmad kamar jaririya,shi yasa bata San sanda take tabara ba,

Yana kallonta bai ce komai ba har yayi parking a schl en yace make sure in da Matsala kinkirani a wayar wani teacher na baki kudi ki siya recharge card kisa,ban amince kiyi waya da kudin kowa ba,zan siya mini taki very soon sai time yayi dan ban son shashanci shi yasa na hanaki phone,kai kawai ta kada sai class,

Tunda ta shiga class mararta ta rike,kuka take sosai,an kaita chemist din schl din amma a banza,dole ta bada number da kudin kati wani teacher ya kira ahmad ya fada masa,1pm yayi sallar juma'a kenan kasancewar Friday ce,da sauri ya bar masallacin, ya taho schl din,sai kuka take tana wash yayana,marata yaya,salati kawai take tana kiran yayanta,daukanta kawai yayi cak ya sabata a kafada,motarsa yasa ta sai wani private hospital me tsadar gaske,iya haduwa ya hadu,gado suka bata suka dukufa aiki kanta,shi kam gogan ya shiga tashin hankali me tsanani,ya rasa inda zaisa ransa babynsa ba lfy,can wani likita ya fito ya sameshi,yace ka kwantar da hankalinka, ba wani ciwo bane,period zata fara,maybe yazo mata yau,gobe amma yanzu munyi abinda ya dace ta samu sauki bacci take,amma bazan sallameku yau ba sai nan da 1wk ko 5days,dan in ta koma gida da matsala,kaje ka shirya jiyya yanlabai,

Wani ajiyar zuciya ya sauke sannan ya koma gida ya ciko mata karamar trolley da kayan amfani dai na me jinya,

Bacci take sha,kara fita yayi ya cika room din da aka ajiyeta da juice kala kala,milk,kayan tea,fruits,nama gashashe,da abinci laafiyayye,gida ya koma yayi wanna,sallah ya huta, wajen magrib yawa Momi da dady karyar sun tafi kauyen su rahma zai kaita ganin danginta,da yake su gidansu akwai freedom ba Wanda yace komai sai adawo lfy.dady ne kadai yace son amma flight zaku bi,in kaje ka duba aikin nan ka gani ba Matsala,insha'Allah yace tare da jefa jakarsa a wata azababbiyar motarsa tafi 12millions kudinta.


Asmabaffa
[23:12, 1/24/2018] ‪+234 806 858 0203‬: 💢💢💢

MARAICIN RAHMA

95-100

BY
asmabaffa

Su momi sun yarda ya tafi kauyen su rahma sun San ahmad baya magana biyu,gashi yace flight zai bi sai addua suka masa,yana fita direct hospital ya nufa da jibgegiyar motarsa,ahmad kwai zurfin ciki ko shahid bai fadawa ba,a hanya ya tsaya ya siyi carton din always pad me kyau sai kace wacce ta haihu haka ya lodar mata pad,tare da new panties masu kyau da tsada,dakin ya shiga ya tarar bacci take har yau bata tashi ba,wata nurse ce ta shigo tace sir a kula da ita zata iya farkawa ko yaushe daga yanzu,magun gungunan ta ajiye tare da cewa anjima zan dawo bata medecine Nata,ok kawai yace,

Bata Dade da fita ba ta farka bude idonta ke da wuya ta ga ahmad zaune gefen gado,hawaye ne suka gangaro mata kawai ta tausayawa kanta bata da kowa me sonta sai ahmad,kusa da ita ya kara matsawa tare da shafa fuskarta,gwiwoyinsa ya sauke kasa daga gadon yana share mata hawaye dan ya gane me takewa kuka,so sorry my little sis,me kike so?waya tabamin ramata ta,hannunsa ya Dora kan mararta tare da cewa ke Mara ki daina wahalar min da baby ramata ta ki rasa wa zaki sa kuka sai daughter na,to bata San sanda ta kama daria ba,kamar a film,tana mamaki wai dama yasan sunanta na kauye,amma kamar baya ji,shi yanda yake lallashin nata ne ma kamar wata jaririya,ai take ta kara shagwabe masa dama me kuka ne aka jefeshi da kashin awaki sai yi,shi ko sai fama yake da ita yana aikin lallashi.

Tashi kiyi wanka baby ramata make kafada tayi ni wlh yaya bana son ramata,yace inye yar gayu me kikeso to,ni little rahma nake so,murmushi yayi yace OK,yau kadai ahmad yawa rahma wasa,kuma dukkansu sunyi nishadi,

Little sis oya muje kiyi wanka kici abinci,kar yazo,yaya waye zaizo?Sam ya manta bata San meke damunta ba,sharewa yayi yace kafin doctor yazo dubaki I mean,tace yaya wai me yasa meni?yace kawai wai kinci abun da bai karbi cikinki ba that's why,ohhh tace tare da shigewa toilet,

Ai tana shiga ba jimawa ta tsala ihu tare da fitowa da gudu daga toilet,da kyar ma ta dauki towel ta dauro tayo waje,jikin ahmad ta fada tare da hugging nasa sosai a rude take,jikinta sai rawa yake shi kam gaba daya ji yayi duniyar ta kife dashi ta masa daurin butar malam,dan rungumenshin da tayi ya jefa shi wani halin,ya rasa dalili duk mata masu kyau da gayu gasunan yana ganinsu amma ko a jikinsa,amma duk sanda ya kalli surar da allah yawa rahma sai ya girgiza,sai yasan shi namijine,bare gashi ta kai ga cukwikuyeshi,da kyar ya banbareta a jikinsa,lfy yace da kyar tace wlh ina tsugunawa nayo fitsarin jini,wlh yaya fitsarin jini,shike nan kayan cikina sun narke,hanta ta,ko kidney waya sani ta karasa tare da rushewa da kuka,

Shi kam ahmad bai San sanda ya kwashe da daria ba,tsayawa

Please Login or Register in order to submit comment