Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kowa,sannan suka koma hirar duniya inda Mimi ke bada lbrn birni ramata na bata na kauye har sukayi bacci a dan sakarKarin gadon ramata na kara da katifar yayi,sosai ramata ta kwantawa mimi,ga tsabta,hankali da nutsuwa,ba gida danci kamar sauran mutanen kauyen,komi na gidan a wanke a share,a tsaftace wannan kenan.

Ahmad cikin dare ya kasa bacci Sam shi kauyen bai masa ba ga yunwa dan baici komai ba,sai juyi yake yana tsaki,gashi Mimi ta tafi da jakar kayan abincinsu da mum ta basu,gashi dady ya bada komai na abincinsu a kaiwa Mimi gidan ramata su zasu dinga dafa musu abinci kullum,dan haka ahmad ya kasance cikin tsananin bakin ciki tare da tsinewa noma gaba daya,shi kuwa ammar kallon american film yake a computer sa tunda yaga kauyen har wutar nepa ce dasu,duk da ana daukewa amma ba laifi suna samu, ammar shi gari ya birgeshi bashi da Matsala.shi kam uban tafiyar dady dama ya saba yana can suna hira da me gari har sun saba sosai abinka da manya.

Washe gari tun asuba da su Mimi sukayi sallah suka koma bacci har 9am basu tashi ba,ahmad ya kasa bacci dan baisa ba da zama da yunwa ba gashi yana da ulcer,cikin sa har ciwo yake sabo da yunwa,dan haka da kyar ya iya kaiwa 8am yaje ya dami dad shi yunwa yakeji,me gari yace shi gidansa koko da kosai ne sai dumamen tuwo,shi kuma ahmad baya cinsu,haka dady ya dinga masa fada akan ya dameshi,suje yaro ya rakasu gidan da Mimi take ta musu girki,da sauri ya kira dan me gari karami suka tafi Inda Mimi take har ammar Dama su ko a gida da wuri suke Brkfast,har gidan ramata yaro ya rakasu ya koma gida,su kuma suka Shiga da sallama,ahmad da ammar gidan ya birgesu dan gwadas dashi gashi a tsaftace,ahmad cewa yayi dama su aka sauka a gidan tsabar tsaftar gidan kamar drawing, ammar har pics yayi a gidan ya dinga selfie, gashi dai na kara ne na kauye amma yayi kyau,gajiya sukayi da sallama suka leka dakin,ahmad kamar ya hadiyi zuciya ganin su bacci ma suke, da kyar ammar ya dinga kwala ma Mimi kira suka tashi,ramata kunya ta kamata har wani sunne kai take,cinyayyen brush ta dauko zata fita,mimice ta tsayar da ita tare da dauko Sabin brush a jaka ta bata,kar kuso kuga murna wajen ramata,da toothpaste din mimi ta matsa mata me tsada,har ga Allah ramata ta manta da su ammar suna waje tana fitowa da brush a bakinta,ga wani dadi da sanyi dake ratsata tayi sabon brush ga weather yau ta mata dadi,bata San sanda ta daga hannaye sama tare da gantsarewa akayi mika,ta mikar da hannunta tace uhmmmmm tare da murmushi,ai ammar bai sanda ya kwashe da daria gashi ya tuno lbrn da lawwali ya bashi akan ramata,gashi yan brst kamar karamin lemo,amma abinda tayi sai ya mata kyau,ga dimple dinta,abin sha'awa,ahmad ne ya harareshi,tare da masa gargadi da ido,amma ko shi ya firgita da kyanta.kuma yayi mamakin lbrn su lawwali, dan sai yanzu ya mata kallon tsab,ita kam ta zata gulmarta suke dan haka ta balla musu Harara ta murguda musu baki ta wuce bayi abinta.

Asma baffa
[14:00, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMA

25-30

By

Asma baffa


Dan danan Ahmad ya kara daure fuska,fitowa mimi tayi dauke da brush da katon carpet din da suka zo dasu saga birni,ta shinfida musu a gindin bishiya,suka zauna ahmad in banda hararar mimi ba abinda yake,ramata na fitowa mimi ma ta shiga tayi brush ta fito,fitowa rahma tayi su ammar na satar kallonta ta Dora ruwa a wata yar tukunya babba,sannan tace musu ina kwana,ammar ne yauma ya amsa kawai,Ahmad latsa waya yake a ranta cewa tayi wannan dan rainin hankali ne ,na tsaneshi ma,bayan ruwa ya tafasa ta juyewa mimi ta shiga wanka,sannan ta kara tafasa wani sannan ta koma wajen su Ahmad tace a cikinku akwai me yin wanka,mamaki su ammar sukai yau ga mace me acting din maza,ita kuwa rahma ko a jikinta dan ta sawa ranta ba so take kowa ya aureta ba dan haka ba wani noke noke uban kowa ma ya tsaneta bata da damuwa,Ahmad cikin tsananin fushi ya Daka mata tsawa akwai sa'anki anan eh,tsorata rahma tayi ta sulale ta koma daki,a ranta tana me cewa daga abin arziki ya zama tsiya,dan ma na karramasu,lallai yan birni basu San mutunci da kara ba,tana haka har mimi ta fito,a tsorace rahma ta sake fitowa taje wajen shanunta da wani sabon kokonta me kyau,ta fara tatsan non on cikin kwarewa,sai kallonta suke har ta gama ta sauke ruwan gefe ta kara gyara wutarta ta dauko wata tunkunyar ta kara wanketa,ta Dora madarar ta tafasa ta,yanda suka ga tana aikin sun yaba kwarai sabo da tsaftarta,tuni mimi ta ebo cups din da suka zo dash guda 4 duk kowa an zuba masa madarar,ta ebo kaayan tea dinsu,namansu,da snacks ta Jere a gaban brothers dinta,ramata ko India suke bata kalla ba,mimi CE rahma kawo ki hada tea mana kar ya huce,tana son sha amma kunya takeji dan haka ita fresh milk kawai take sha da safe sai indomie watarana,

Dama tana da indomie ta guda 3 suma a kasuwa ta siyo ranar juma'a dan haka ta dauko daya,ta dauko attarihu da albasa,taje wajen da kajinta me kwana ta dauko kwai guda biyu tazo tayi hadaddiyar indomie ta cikin kwarewa da tsafta,dan malam hassan da ke zuwa daga birni koya musu karatune ya koya mata dafa indomie kala kala,sabo da yana dafawa yaci in yazo,shi yasa ta iya,suna kallonta tayi lafiyayyar indomieta da dafaffan kwai a ciki,

Tuni yawun Ahmad ya tsinke,Barin ma ammar mayen indomie,tsam mimi ta mike ta koma wajen rahma tace tab ai wlh baki is a ba sai naci,daria rahma tayi tace kinga ungo wannan kije wajensu Ku ci,in wata zan dafa dama taku ce wannnan,

Mimi ce ta dauka ta kai musu nanfa suka rufarwa indomie sai da suka ga bayanta,rahma ksm bason ci take ba dama amma haka ta kara dafa wata tacinye abarta a gindin murhun sai murna take yau cikakun yan birni sunci girkinta sun yaba,tattara komai tayi ta wanke,ta gyara gidanta fes,harda kunna turaren wuta na tsinke,gida sai kamshi,ta cika gidan da ruwa ko ina,sannan taje ta salla wanka,tasa a yar powder ja da kwalli ta shafa Vaseline a lips enta,sai gata ras,ta dauko wata yar tsohuwar doguwar rigarta yer kanti wankarkiya,amma a gani ta tsufa sosai, wata hula tasa,sannan ta kunce shanunta tazo India su mimi suke suna hir脿,tace mimi zanje kiwo sai yamma,in zaki amfani da koma meye gasu nan kiyi kawai,na tafi,juyawa tayi tare da kada kan shanunta da sanda sai kiwo.

Asma baffa
[14:04, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMA

30-35

By
Asma baffa


Fitar rahma kiwo ke da wuya Ahmad ya sauke wani gauron numfashi,yaya a dafa muku ruwa kuyi wanka anan gidan muje wurin dad kasan yau za a fara aikin fa cewar mimi,da Sauri Ahmad ya amince dan har ga Allah yafi jin dadin zaman gidan ramata,kunna risho mimi tayi duk tare suka zo da abinsu ta daura musu ruwan wankan,kowa yayi wanka cikin dakin ramata suka shirya sukayi komai sai kamshin turaren Ahmad yake gidan haka suka dunguma sai wajen dadi,suna zuwa suka tarar dady ya sha manyan kaya,gaishesa sukayi sannan mimi ta mika masa soyayyen namansu kadan yaci da lemo suka wuce gonar gaba dayansu,yayin da suka tarar da ma'aikatan dadi tuni sun fara aikin,Ahmad sun zage suna ta tsare tsare a wajen ba yanda suka iya dole suyi ko dadi yaci ubansu,

Bangaren ramata kuwa ta rasa dalili tunda taje kiwo ta kasa hasala komai sai tunanin Ahmad,ta rasa me yasa yake birgeta,kuma in ta ganshi gabanta yana faduwa,ga tsoronsa da takeyi,tunda ta fito kawai so take ta koma ta sake kalonsa hmmm,

Da kyar ta iya kaiwa karfe biyu ta jawo shanunta suka dauko hanyar gida,Ahmad kuwa ya kai kololuwar gajiya a wajen ga rana kawai bacci yake so yayi,ruwa faro a dauka yana sha,ya sha malt,sannan yace mimi tazo suje a dafa musu abinci yayi hakan ne dan ya gudu,dadi ya ganeshi kawai ya kyaleshi,suna zuwa Ahmad ya shige dakin ramata kamar nasa ya haye mata bed ya kwanta sai bacci,mimice ta kunna risho ta fara musu girki,har zuwa tayi ta siyo naman rago ta musu. Jullof rice tasha nama,ta musu farfesun kifi Wanda shima a garin ta siyoshi ana kamowa a rafi,lemo da ruwa ta ebo ta shirya komai a dakin ramata,sannan tayi wanka tasa wata atamfa super Riga da skert tayi kyau sai kamshi takeyi,sallah tayi sannan ta tashi Ahmad dan 5pm ta kusa,yana tashi yayi wanka ya sa wani 3qwtr da Riga armless farare kal yasa p cap yayi matukar kyau kamar bature,sallah yayi yaci abincinsa ya koshi ya koma bed ya kwanta,ammar ne ya shigo yaci shima sannan yayi wanka da sallah ya kwashi na dad ya tafi kai masa,

Mimi ma gyara gidan tayi ta koma gonar da ake aiki ahmad kawai aka bari yana baccinsa hankali kwance,ana haka ramata ta dawo gidan da shanunta,tun daga kofar gida take jin wani asirtaccen kamsh,dakinta ta shiga ba karamin firgita tayi ba da taga mutum na bacci sai da ta kalla sosai ta gane waye,hakura tayi da shiga dakin ta koma cikin rumfa ta zauna tana jira ya tashi ya fito,

Har wurin magrib ta gaji da jira ta Shiga dakin da sallama amma shuru gajiya tayi ta turo baki tana kunkuni cike da shagwaba ta sa hannu ta buga kafarsa kadan,a hankali ya bude idonsa,yana ganin itace ya kara tamke fuska gashi ta turo masa baki yace lallai ma wannan village girl din,ai tana jin yayi turanci bata San sanda tace to city boy in ka tashi na dawo dakina kuma wanka zanyi,tsananin mamaki ya kama ahmad gashi wai har tana gane turanci,kuma wai wanka zatayi ya fita me take nufi kenan kar yaganta,lallai ma yarinyar nan to me zai gani a jikinta yan Matan kirki ma na birni basa gabansa bare wannan kwailan,harara ya watsa mata tare da ficewa daga gidan baki daya,

Kaf garin su ramata ya dauka cewar ramata ta zama karuwa,ta Tara mazan birni a gidanta,kuma me gari ya yarje mata sabo da tana bashi cin hanci,sai gulma ake zance ya cika kauyen Cewar ramata ta zama karuwa da yan birni take harka,ko ina kallonsu ake ana ga yan iskaan ramata nan,ko INA suka wuce yaran gari tsokanarsu suna cewa karuwai ne,wasu suce yan iskane,yau kwanan su mimi uku a garin amma su ko ajikinsu dan sun San kauyenci ke damun yan garin,ramata kuwa ta saba da mimi sosai sun zama kawaye,ammar ma da yake me fara'a ne da tsokana sun saba da ramata,Suna hira,da wasa sosai,Ahmad kuwa Hutu ke kawoshi da cin abinci gidan,ko hira suke baya kulasu,ya matsu ma su tafi gida,kamar a kaya yake haka yake jinsa,

Ramata ta kaiwa baffajo shanunta yaci gaba da yimata kiwonsu,dan yanzu bata iya fita kiwo sabo da tsokanar da ake mata a gari,yanzu an kara tsanarta a gari a dalilin yan birni,gashi nan da 2days su baffajo da inno zasu tafi kiwo wani dajin me nisa,sabo da yankinsu yanzu ba abincin dabbobi da yawa,dole su zama fulanin tashi,kayan abinci da kudi ya bawa rahma ya mata nasiha kan tsoron Allah da aure yace da asuba zasu bar gari ba lallai su hadu ba,tasha kuka sosai,tasan yanzu bata da wani sauran gata a duniya, gashi kowa ya tsaneta gashi yan birnin ma nan da 11days zasu tafi,ba Wanda zata gani taji dadi,Kiwon ma ta bawa su baffajo su tafi dasu kiwo dan garin yanzu ba ciyawa dabbobi wahala suke, tunani take idan yan birni sun tafi ya zatayi,

Dady kuwa ramata ta birgeshi,kuma ya yaba mata yanda take kula da yaransa, gata me hankali, shima ya samu kiran gaggawa a wani company sa dake lagos har ya koma lagos ya Dora su Ahmad su kula da aikin dan bazai dawo garin ba,yace tunda sunga kan aikin sai Dora har zuwa nan da 11days sannan su tafi gida,abin baiwa Ahmad dadi ba Sam, yaso shi aka tura lagos.

Asma baffa
[14:40, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMA

35-40

by
Asma baffa

Ina godiya masu karanta novel din nan,da masu yaba min ta inbox da kirana a waya na gode sosai Allah bar kauna.


Kamar kullum sun gaida me gari sun tafi aikinsu,Ahmad yana inuwa yana waya da frnd dinsa doctor najib suna ta daria,mimice tare da ramata suka karaso dauke da abinci,tun daga nesa rahma ke karewa Ahmad kallo yanda yake daria tare da rangada turanci me dadi,a ranta cewa take jiba komi NASA me kyau ne,ji yanda daria dama yana daria haka lallai,sai kuma ta tabe baki tace to ina ruwana dashi ma,

Mimi ce ta dan daketa a baya tana daria tace me kike tunani kawas,daria tayi tare da aika mata da harara tace dama ai akwai sa ido mimi,ammar ne ya taho yana daria yace rahma yan mata ko kin San daria na miki kyau,harararsa rahma tayi tace Allah ya ammar ko tam,cike da shagwaba ta fadi maganar kwashe mata sukayi da daria,kunkuni ta kama tana dira diran kafafu,duk abinda suke AHMAD na kallonsu,shi dama baya shiga harkar wani kuma yana da kunya,dan shi Su sukeyi shi yakejin kunya ma,mimice tace ya Ahmad abincinka yace sai anjima ki ajiye min,da kyar yake magana,sukam fara ci sukayi ramata ta ebi nata ta juya musu baya dan kar aga lomarta,ammar ne ke lallabawa yana zagawa yana kallonta sai yace wooo tab wannan katuwar lomar fa na gani,daria rahma take sosai ga kunya,ta rufe idonta da tafin hannunta,can ammar ya kuma lallabawa ya dauke ruwanta tana kallonsa yana sa hannu ta rike hannun kokawa suka fara da hannun rahma Dana ammar,har haki rahma take,gajiya tayi ta sakar masa ruwan,mikewa tayi ta dauko abincinsa ta ebi miya a cokali ta shafa masa a fuska,daria suke sosai,tsawa suka ji daga sama an daka musu,ba kowa bane face ya Ahmad,yace ammar da girmanka wannan wanne hauka ne sai wasa kukewa mutane da abinci,aikin banza,in haukarku zakuyi kar kuyi mana da abinci,kazamai kawai,wlh wlh na kara ganin kana haka sai ka San me zan muku,

Zaku tsiri iskancin banza dan bakusan darajar abinci ba,ko da kudinku a ciki,masifa yaci gaba da yi ba ji ba gani,mimi duka mamaki sukai dan basu taba jin yayi wannan bala'in ba,shuru sukayi ammar yace am so sorry ya,mimi ma tace pls we r sorry,tsaki yayi ya juya tare da cewa sorry for ur self,rahma kuwa bata saba da fada ba har idonta ya ciko da hawaye,ammar ne ya fara sorry beauty yasa handkerchief yana share mata hawaye,Ahmad ne daga nesa yace ammar u r very stupid kaji ko wai bakayi islamiyya bane,ko kulashi ammar beba sai da yama goge mata ya tashi tsaye yace beauty zo muje gidanki ki huta,sosai Ahmad ya kulu,rahma kuwa bata so ya rakota ba ko dan yan gari zasu kara tabbatarwa karuwace,kuma ga Ahmad najin haushinta dama ya tsaneta,kuma bata so ya kara tsanarta,ammar ne ya dinga kwantar mata da hankali har sukazo gida sannan ya juya ya koma wajen aikin,yan gari kuwa ko ina zancensu akeyi.

Yan kauyen sunga ramata ta kara kyau da fari,ta kuma dan gogewa,ta yi yer kiba tsabar cin me kyau,ai kuwa yanzu duk sun zuba ido cewar ramata ciki ne da ita shi yasa tayi kiba ta kuma haskakawa,yanzu ranar da kowa zaiga ciki ya girma ake jira,a taru a koreta daga garin tare da mata Allah wadai da tofin Allah tsine,yanzu mutan gari da dattawan gari tun suna zuga me gari baya dauka shima yanzu ya yarda,dan yaga ammar da Ahmad kwana kadai ke kawosu gidan,gashi dan alherin da suke masa na kudi sun rage bashi,yanzu haushinsu yakeji tare da tsinewa ramata da ta jaja masa asara,dan yana jin tsoron su Ahmad ne sabo da suna da kudi yana sa rai kullum da kyauta da suke masa baya da haka da tuni ya koresu daga gidansa,suje su sa amusu na kara da yayi suma,amma kudi masu gidan rana masu fada aji baza su bari ko kallon banza ya musu ba.haka yake kyautata musu ala dole,suna tafiya zai huce kan ramata to fa.

4:30pm ahmad yayi sallama a fusace dakin rahma dan yana jin haushin abinda suka masa ita da ammar, ita dan ta rainashi taki CE masa ko sorry ma,bude ido tayi yace ke tashi ki fita zanyi bacci,haushinsa taji ta turo baki ta fice fuuuuu,tana ta kunkuni,kai ya girgiza tare da yin da kwafa,kwanciya yayi sai bacci.


Asma baffa
[14:40, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMA

40-45

BY
asma baffa

Tunda ya koreta ta hakura a ranta tace ai baki ne sun kusa ma tafiya,tabarma ta shinfida a gindin bishiya ta kwanta tana ta tunanin iyayenta,baffajo,da idan yan birni sun tafi ya zata kasance a garin,rahma sun shaku sosai da su mimi da ammar,yayinda Ahmad ko shiga harkarsu baya yi,yau ta kama gobe su mimi zasu tafi abj,mimi kayan sawanta kaf ta kwashe ta bawa ramata da kayan abincinsu da duk wani kayan amfaninsu,wankin boxers da singlet ammar yayi ya wankewa Ahmad ma nasa ya shanya a gidan rahma,lallabawa rahma tayi ta saci singlet daya da boxers na Ahmad,sabo da in sun tafi ta dinga shakar kamshinsa,tana jin dadi,yau da safe duk Suna cikin motarsu driver zaija su wuce,ramata na kuka mimi ma na hawaye,ammar na tsokanarsu,sannan ammar ya ebo kudi ya bawa rahma yace tayi amfani dasu kin karba rahma tayi sai da Ahmad ya daka mata tsawa yace dallah malama karbi mu wuce kina waisting mana time,hannu na rawa ta karba suka ja mota suka wuce,komawa gida tayi ta kwanta tana tunani,

Kwanan su Ahmad uku da tafiya me gari ya kira ramata,yace ya yanke mata nan da 3mnths ta kawo miji ko ya bayar da ita sadaka,idan taki kuma to tabbas zai koreta daga kasarsa,kuka take tana bashi hakuri amma inaa,rufemin baki munafukar banza fasika,tashi ki ban waje,tana kuka ta tashi,ta tafi,haka rahma ta dage da addua ba dare ba rana akan Allah ya kawo mata agaji,kullum da singlet din Ahmad take bacci da boxers dinsa tana jin dadi tare da tunawa dash.

Ramata yanzu ba Sana'a ga kudin da take dasu tuni sun kare,kayan abinci ya kare,bata da komai,sai ta kwana bats ci ba,har bara sai da ta fara,ganin irin wulakancin da ake mata a kauyen ne yasa ta daina zuwa barar,ta koma sana'ar daka da surfe tana samun goma da ashirin na shan koko da sauransu,yanzu goge baki ma da gawayi da aswaki take amfani,fatarta kuwa ko Vaseline ta Dade rabon da ta shafa,tayi duhu,ta dan rame,dan ma tana da hakuri da tawakali,gajiya tayi ta tafi wajen dangin baffanta akan su riketa ta sauna wajensu kafin baffajo da inno su dawo ammaa fir suka ki saima zagin tsamar nama da suka mata,yunwa da wahala suka kara kwasarta ta tafi dangin mamanta nan ma suka mata kaca kaca,suka ce bada su ba zama da karuwa,haka ta dawo taxi gaba da karbar wahalarta.

Tun ramata tana jurewa har ta kai ga ta kasa sai kuka,yau ta kama ranar kasuwa ko wanka babu haka ta tafi kasuwa dan ta roki wasu masu siyen furarta ko rance su bata,sai addua take,ta isa wajen baba tsoho ta fada masa,ya tausaya mata da kyar ta samu 200 wajensa,ta koma gun me saida wake shi kam hakuri ya bata haka ta karaci zagayenta da kyar wani matashi me sonta wato isa ya bata dari ta hada Dari uku,taci abincin hamsin ta dawo gida,haka kudin suka kare,

Rayuwa taja yau kwanakin da me gari ya yanke wa ramata sun cika,kofar gidansa ya cika dam da mutane yayin da ramata me tsakiya tana sharbar kuka,

A bangaren su mimi kuwa tunda suka koma mimi kullum zancen rahma takewa mum,dan mum ta tausaya mata,kuma taji dadin yanda ta kula da yaranta,yau Ahmad tun 8am ya bar gida ya dau hanyar garin su rahma,dan yace kwana daya zaiyi ya dawo,so yake yaje da wuri ya gama komai gobe da safe ya juyo,run 12pm yana garin yana shiryawa ma'aikata aikinsu sai daya gama komai ya taho domin gaida me gari,daga nan zai bawa rahma sakon mimi data rokeshi ya tafi dashi.

Tun daga nesa ya hango jama'a damkam a kofar gidan me gari wasu na jifa wasu na zage zage da sauri ya karasa yaga meke faruwa hakane.

Asma baffa
[14:40, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMA

45-50
By
Asma baffa

Karasawa Ahmad yayi cikin mutanen wajen nan ya tambayi mutane uku me ya faru ai kuwa gulma na cinsu da sauri suka kwashe lbr suka bashi tun farkon rayuwar ramata har zuwan yan birni,da kuma abinda me gari yace suka ce ai munji dadi barin irin wannan yarinyar guba ne a rayuwarmu data yaranmu,take ran Ahmad ya baci,wato duk a Kansu ne ake mata haka a grain Allah sarki,ji yayi wani tausayinta ya shigeshi

Me gari ne ya daka mata tsawa yace to tunda haka ne in dai baki yarda da zabi na ba sai dai ki bar kasata,tana kuka tace dan Allah kayi hakuri,me gari ne ya daga hannu ya shara mata mari tsinaniya INA magana kina yi tambadadiya asararriya,take fuskarta tayi ja dauke da yatsun me gari,su kuwa yan garin dadi kawai sukeji suna ihu jira kawai suke suji na annabin da za a daura dashi,sai cewa suke jira kawai Muke a daura da Muhammad,domin su duk namiji sunansa muhammadu,suka CE wa zai auri wannan ai sai marar gata hhhh,can wani yace aradu da na sa kudina abani wannan tsohuwar karuwar gwara nayi sana'ar gwanjo ko naira ishiri in siyar,

Mai gari ne cikin karaji yace munafukar banza na aura miki zabina ko zaki bar kasar,shuru rahma tayi,haushi ne ya kwashi me gari ya sake daga hannu da niyyar marinta karo na biyu,cikin zafin nama Ahmad ya rike hannun tare da cin kwalar me gari,yana huci,idonsa ya kada yayi ja sabo da Bacin rai,da kyar ya saki me gari yace tsohon banza,Jan hannun rahma yayi ta mike hannu yasa ya share mata hawaye,ya riketa har mota ya sata ciki,tsananin mamaki ne ya kama yan kauyen Wanda ya haddasa musu mutuwar tsaye,yau ga wani ya shake me gari guda,lallai yan birni ba kunya,me gari ne ya nisa yace kowa ta tafi gida a mata addua a ja mata tsinuwa cikin carbi dai dai,tsinaniya kanjamauce ajalinta,me gaari yaji hauci ya kulu akan be huce haushinsa kanta ba lallai Ashe bariki ma Nada rana,an rabasu da kaya,wannan shedaniyace cewar mutanen yankin.

Tunda Ahmad ke sharara gudu ba Wanda yayi magana cikinsu bai tsaya ko ina ba sai wani makeken hotel dake cikin garin kebbi city,tun a hanya rahma ke kalle kalle yau taga birni,ba ta kara shan mamaki ba sai da suka shiga cikin hotel en,daki Ahmad ya kama guda biyu rahma daya shi daya,duk abin nan ba Wanda ke wa wani magana,room dinta ya rakata ya nuna mata yanda zatayi amfani da toilet fuskarsa kamar an aiko masa da mala'ikan daukan rai tsabar tamkewa,fita yayi yace saura ki fita kallo wlh ranki sai yafi na saniyar da ake noma da ita baci,dariya ya bata kan abinda yace kallonsa tayi tana murmushi,yana fita tace jarababbe na gode dai tunda ka taimaka min,wanka tayi da sallah,jikinta har rawa yake

Please Login or Register in order to submit comment