Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels













ENJOY READING.

MARAICIN RAHMAH

1-5

By
Asma baffa

Jinjina da dubun godiya ga masoya makaranta novel dinnan馃檵鈥嶁檧馃憤

Bismillah

Kebbi state,na wuce gari,kauyuka da dama,Wani daji na cinna tafiya nake katsam sai ga asma a wata rigar fulani Wanda babu komai face yan gidaje Wanda akayi su da ainihin karan dawa da yayi irin dai gidaje na asalin fulanin daji,babu komai a dajin sai korayen bishiyu,ruwa da gonaki da mutanen yankin suke noma,gidajene daya can daya can,tsalli tsalli,sai wata yar kasuwa,garin ALLAH ya albarkacesu da niima kala kala,wannan ne yasa na tsaya kallo, can wata yarinya na hango kyakyawar gaske,yar doguwa fara fara ja ja,gashinta har gadon baya amma shi ba baki ba kuma ba ja ba kalar na fulani dai,hancinta me tsayi amma ba can ba me kyau,idonta dara dara,ga eyelashes baki,bakinta hakora kana na lips pink dan cut dashi,kai karshe dai tayi,sanye take da wasu yagagun kaya, wata kodadiyar atamfa ta jeme,takalminta duk ta daure da Leda,amma daga ka ganta kaga me tsafta dan komi Fes take,sai dai kana gani Kasan tana wahala.

Yarinyar baza ta wuce yar 15yrs ba sanda ce a hannunta tana kada yan shanunta Wanda gaba daya shanun guda uku ne kacal,saniya,sa,da dan maraki wato dan saniyar,binta nayi ina dauko muku rahoto,tiryan tiryan naga dai dai wajen magariba ta nufi wata yar bukka wacce take zagaye da katangar kara,sai toilet guda shima na kara da yayi ne,harda rumfar girki da yan watsatsun tukwane da sauransu a wanke fes a gyare.

Jira nake naga wani ko wata ta fito amma shuru,yarinyar naga ta daure shanunta a wani bangare na gidan ta cire kayanta ta daura wani jememen zani ta ebi ruwa ta shige bayi da dan kwandon soson buhu da wani koren sabulun wanki,ta dan jima ta fito Ashe wanka ta sillo,dan Vaseline ta shafa da kwalli,ta dauko wata t.shirt ja ta saka ta daura wani zani Wanda shi na fulani ne,kayan data cire da zanen wanka ta hada ta wanke da koren sabulunta,ta shanyasu,wata sandarariyar shinkafa da manja ko yaji babu tacinye ta bude randarta tasha ruwa,wata futilar kwai ta kunna a cikin yar bukkarta ta dakko wata tsohuwar jaka,wasu littaatafai ta dakko,

Abin mamaki teach your self na hango da brighter grammar,sai littatafan koyon rubutu da karatu na Hausa,da bironta sai littafin rubutu guda 2 ciki Wanda a su take rubutunta,sai da ta gama karatunta kuma ba laifi ta iya sai ta kuma dauko Qurani tayi ta karatu cikin dadan murya,tabbas da gani ba jahila bace ko daga yanda tayi sallah ma komai dai dai,da azkhar du ta dan iya ba laifi,bayan ta gama karatunta ne naga tayi sallar isha tayi adduoi,amma tana zub da ruwan hawaye tare da kuka me tsuma zuciyar me sauraro,bayan ta gama ne ta kwanta,sai bacci,washe gari da asuba tayi sallah da azkhar,bayan rana ta fito ne ta kwanta bacci sai wurin Tara ta tashi,tana tashi naga ta dauko wata Leda ta Ciro toothpaste da brush duk da brush din tsohone tukub,da gani yaci duniya,amma tayi kokari,ta goge bakinta tas,sannan ta shige rumfar girkinta wuta ta hada ta dauko tukunya ta zuba madarar shanu 1 cup,ta dafa ta bayan ta huce ta sha abarta ta koshi,sannan ta wanke kwanikan da omo,wani botikin karfe ta dauka Wanda yama gama bulewa ta ko ina ,ta fita,Garin mutane sun fito jefi jefi,wani dattijo me kamala ya tareta cikin hausarsu da batafita yace a,a RAMATA da sauri ta durkusa baffajo ina yini,yace lfy ramata maza ki tafi kiwo,zan aiko,miki da geron hura yau kanji yata,murmushin dadi tayi tare da zuba godiya,gidanta ta cika da ruwa,sannan, ta share ko ina fes,tayi wanka ta tatsi madara a saniyarta ta rufe a daki,ta kada su sai kiwo,da alama haka takeyi kullum.yau ma kamar kullum haka tayi,bayan kwana uku ranar ta kama ranar juma,a ramata bataje kiwo ba, ciyawa da ruwa taba shanunta,fura naga tayi me yawa da lafiyayyan nonon kirdirmo,ta shirya komi a sabuwar kwaryarta da faifai,du komi sabo me kyau,har kokunan dama furar ta,ta sa kayanta me kyau da wani takalmin roba shima ba laifi,sai kasuwa.tana karasawa kasuwa tun a hanya ake ga ramata fillo nan,wasu na ga ramata,wasu fillo,ba wanda ta kula ta nemi waje ta zauna,kafin kace me har ta kusa saida furarta,mata masu talla sai gulma da jin haushin ramata suke. ko ya asalin wannan yarinya take oho Ku biyoni.

Asmah baffa
[13:59, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMAH

5-10

By
Asma baffa

Cikin murna da jindadi ramata ta siyar da furar ta, tattara komai tayi ta shiga kasuwar ta siyo kayan abinci dan dai dai ta boye ragowar canjin sai gida,a hanya ta tsaya cikin gona tayi ciyawa ta tafi da ita dan bawa shanunta,da kyar ta kai kanta gida sabo da nauyin kaya ga ciyawa,tana komawa ta bawa shanunta ciyawar ta Adana kayan abincinta,wanka tayi,ta fito sai gidan baffajo,sallama ta rangada,inno matar baffajo Ce ta amsa cike da murna tana ah ramata yan mata malam yace ga itacen ki nan a baro ki tura ki kai gidanki,godiya tayi sosai irin taimakon da baffajo ke bata,ta tabbata ko baffanta abinda zai mata kenan,ba ita ta bar gidan ba sai da taci tuwon dare tayi sallah sannan taja kurar itacenta ta kai gida,sosai inno da baffajo ke birgeta dan ba karamin taimaka mata suke ba bata da kamarsu duk fadin rugar su..

Wace ramata

Ramata asalin sunanta rahmah abubakar amma da yake fulani ne usul suke ce mata ramata, Abubakar Wanda aka fi sani da bukar shi kadai ne wajen iyayensa Wanda sun jima da rasuwa sai danginsa,malam bukar mutum ne me tsatsan addini dan kaf garin ba mai illimin addini kamar sa,mutumin kwarai dattijon arziki,da matarsa mero dattijuwar arziki me hakuri ita kadai bukar ya aura,har suka haifi rahmata,Kaf mutan rugar ba Wanda ya kaai bukar arziki,gonaki da dabbobi,a sanadiyar haka yan uwansa suka tsaneshi babu me sonsa,daga shi sai matarsa da yarsu rahmah tunda iyayensa sun rasu,haka rahma ta taso cikin gata da kulawa,ya sata a makarantar islamiyya da boko,dan har wani malam hassan wanda a lokacin yake zuwa daga birni,ya dauka yana biyansa kudi yana koyawa rahma karatu extra lesson kenan duk wani dan turanci a wajen malam hassan ta koya kafin a masa transfer,

Haka mero ta koyawa shatu tarbiya da girki da sauran Ayyuka tun tana karama ta saba,suna cikin jin dadi da koshin lfy,rahma na 13yrs kwatsam wata ranar asabar da dare wasu arna yan fashi suka shigo gari satar dabbobi basu hari ko INA ba sai gidan bukar,motsi malam bukar yaji ya fito yana fitowa suka harbeshi har wuri uku,wannan Harbin ne ya farkar da rahma da mero Inda suka rugo da gudu,yan fashi na ganin zasu Tara musu mutane suka dorawa mero bullet a goshi ko shurawa batayi ba tace ga garinku nan,haka cikin Sauri suka kwashe dabbobin duka yanda suke sauri ne yasa suka bar shanu guda biyu, sa da saniya,sai wata akuya daya sai kaji biyu su kadai rahma taa gada sai gidan da take ciki,ranar mutan gari sunsha kuka,da bakin cikin babban rashi da akayi,sai kuma tausayin rahma kowa da yakeji, wacce sai kuka kawai take ko magana ta kasa,suma kuwa ta suma yafi a irga,da kyar aka shawo kanta,

Amma rashin imanin fulani watarana in ya motsa,ba Wanda ya yace a bashi ita ya rike,sai baffajo da yake mutumin kirkine shi da matarsa,kuma abokin malam bukar na amana,shi kadai take kula da rahma,dan shi ya dauketa tana 14yrs tace ita sai ta koma gidanta da zama,ba yanda ba ayi ba taki ji,yan uwan bukar da mero kuwa ko kulata basa yi,in ta gaishesu ma da kyar suke amsawa,tun tana zuwa har ta dainaa ma,rahma ita kadai take fadi tashi a wannan gida,don Allah yasa me gari ya kafa doka duk Wanda aka kama da mace zaiyi fasikanci hukuncin kisa ne,kuma haka ake zartarwa ko dan uban waye shikenan zaawarawa da yan mata da masu zaman Kansu irin su rahma suke zaaune lfy,

Itakam rahma zuciyarta ta gama bushewa bata tsoro gwara taa dinga tuna iyayenta,baza ta zauna wani wajee ba sai gidan baffanta tana tunawa dasu tana musu addua,dan ta kudirce ko aure baza ta taba yi ba,haka zata kare rayuwarta tana wa iyayenta addua,dan burin rahma kenan,shi yasa bata kula kowa a maza,dan su baffajo sunyi har sun gaji,dan yanzu tana 15 kuma suna aurar da maata suna 12 13 11ma itakam rahma ai kowa kallon tsohuwa yake mata,wai ta tsufa ga kyau ba aure,har tsokanarta suke a gari tsohuwa me Kyan banza,ita kam ko a jikinta,wannan kenan,rahma dai wahala ita ta kara dorawa kanta,dan tana da su baffajo ta zabi zama ita daya tana wahala,ko innce kuruci dangin hauka,ace mace ta kudirce ba ita ba aure maji ma gani, Ku biyoni

Asmah baffa
[13:59, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMAH

10-15

By
Asma baffa

Haka rahma take kullum yau da dadi ba dadi,gobe taci me kyau jibi ta kwana da yinwa,gata Allah yayota me kara da kunya da kawaici,akan ta roki wani abu awajen wani koda baffajo ne gwara ta kwana da yinwa,gata da hakuri da juriya amma ba aure a tsarinta,baffajo da inno abun na damunsu har me gari sun rasa ya za suyi da ita,gashi duk danginta basa kula lamarinta bare a samu a daura mata aure da wani ko da dan uwanta ne,abinda basu sani ba rahma ta sawa ranta in akace za a aura mata wani to tabbas guduwa zatayi ta bar garin.


Birnin tarayya abuja wani gangamemen gida na hango na alfarma dake cikin unguwar maitama gidane wanda ya amsa sunansa ko a abuja sai an yi da gaske a samu kamar gidan,wasu zaratan sojojine a kofar gidan su 5 suna zagawa da bindigogi,gidane na gaske wajen tsaruwa da kyau Wanda yafi gaban kwatance masu karatu,cikin gidan aljannar duniyane,flowers masu kyau,garden tare da grass carpet,swimming pool har 2 kowanne design daban,ban garden motoci kuwa ba karama,dalla Dalla ne na gaske birjik,part uku ne a gidan part din mom and dad komai golden color ne,sai part din sauran yaran gidan dark brown and golden,sai na babban yaya komai white color ne,gidan ya tsaru komai na akfarma ne,duk yanda zan fada bazai fadu ba,abin ya wuce a iya fada sai Wanda ya gani,

Wani handsome guy na hango yana sakkowa daga saman steps da alama wurin dad take dan a part din yake,wata dattijuwace ta biyosa tana my boy wait tsayawa yayi yana murmushi,turare ta fesa masa me dadin kamshi,yace tnx mum I luv u,kai ta dungure masa tace ammar kenan,wai Ina sauran yara na ne kuma yau banga Ahmad ba,gashi rana har rana tayi,ammar yace mum kin San yaa A.A fa mum shi halinsa daban ne,bari na nemo miki su Mimi suna part dinmu.

Numfashi mum taja tace kafin ka fita ka kira min Ahmad da duka yaran kace ina nemansu kuma karma ka manta yau dady na Neman kowa a dare tunda yau Sunday babu me fita bare ace an gaji,yace yes mum daria sukayi duka ya wuce ta koma wurin dad.

Dare wurin 9 duk yaran dad sun hallara su bakwai maza uku many a mata 4,dady ke bayani kan gidan gonar da zai Gina a wani kauye dake kebbi state,tare da yin gagarumin noma a yankin,yace Ahmad Kaine babba dole da kai a tafiyar this time around,sabo da sadiq ke zuwa irin wannan wurare dan haka yau ba sadiq a tafiyar kuma ka sani dani da kai da ammar da kuma Mimi za a tafi kuma sai munyi 2wks munga komai na tafiya sannan mu dawo,muna da masauki a kauyen da yarana masu kula da harkar,amma dole a fara a idonmu,tunda dad ya fara magana Ahmad ya bats fuska dan baya son doguwar tafiya,kuma baya son nesa da gida,gashi kuma wait kauye zasu zauna har 2wks shikam ya tsani Noman nan da dad ke so,shi began wani alfanu a harkar gona ba,shi an takura masa,amma dole ya bisu ya ya iya,dan a 1 day ma ai zasu iya zuwa a dawo amma ace har 2wks haba,
Shi kuwa ammar da Mimi murna kawai suke,dady yana kula da ahmad ya share shi kawai,suna fitowa daga dakin dad kowa ya baje a palo mum ce ta fito,autarsu amal ce ta fada jikin mum tana momi nima zanje pls mum,mum ce ta shafa gashinta tace amal sai watarana zamuje,da sauri amal ta mike tana kuka ta fice,ita kam salma tabe baki tayi taci gaba da game a wayarta,sadiq kam mum yawa sai da safe ya wuce,ahmad kuwa da magana ma wuya take masa chanel kawai ya canja yana kallon news har suka fara magaba da mum sama sama,mimi kuwa ta cika mum da lbr,haka kuwa akayi kwana biyu tsakani suka hau daya daga dalleliyar motarsu babba,me tsadar gaske,driver na jansu sai kebbi.

Su waye ahmad

By asma baffa
[13:59, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMAH

15-20
By
Asma baffa


Alh. Abdullah shehu shine dady Baban su Ahmad,dan asalin nijar ne iyayensu wanda sun dade da rasuwa su uku suka haifa,abdullahi,sani sai autarsu hauwa,sani shima yana da arzikinsa ba laifi sabo da shi doctor ne yayi boko,kuma a nijar yake da zama,tare da matarsa fati da yaransa 4,dattijo me dattako kenan,sai hauwa wacce take auren wani ambasador ita tana nijar,dady ne babba kuma shine baiyi boko ba iyakacinsa secondary,kuma shine yafi kowa arziki a family su,kasancewar yana da zafin nema,kuma da san,ar noma ya fara har yayi karfi,noma ne ya kawoshi nigeria kuma ta karbeshi shi yasa yayi zamansa,inda ya samu matar kirki me addini wato aisha mum kenan,abdullah ya mallaki dukiya me tarin yawa da kadarori,ga kamfanonuwa da dama,ga gidajen mai da sauransu,matarsa aisha mum fara tas yar fulanin kebbi ce,a nan suka hadu ya aurota itama ba laifi tayi boko a bangaren agriculture take aiki har yau,suna da yara kyawawa 7 Wanda kowa yana da haske sosai ga kyau kamar Arabs,amma Ahmad duk yafi su kyau ga farinsa shi kamar kusan na bature yake dan ya sirka da ja ma Kadan, ahmad shine babba 32yrs,sai sadiq 29yrs,ammar 26yrs,mimi wato zainab 21,salma17yrs,sai auta amal 10yrs duk family suna zaune lfy,kuma suna ziyartar yan uwansu dake kebbi da nijar,dady na matukar taimakawa marasa karfi,dattijon kirki ne bashi da wani hali marar kyau sai abu daya wato bai cikaa yadda da kaddara ba in tazo ta fannin asara ne sai da gaske yake iya hakuri,kuma shi Sam baya wasa da yaransa kuma bai cika sakar musu fuska ba amma sunayin yar hira har ayi nishadi,shi yasa kowa ke tsoronsa fiye da mum,

Yaransu sun taso cikin jin dadi,tarbiya ga ilmin addini Dana zamani,dan Ahmad da saddiq sun sauke,kuma sunyi littatafa da dama sadiq a egift yayi karatu,Ahmad a england ya karanci harkar business both degree da masters,sadiq degree ne dashi yace ya gaji,ammar kuwa yace bazai iya nisa da mum ba ko umrah baya son zuwa in ba mum,yanzu haka yana final year a wata private schl dake abuja,sai Mimi yar level 1,salma ss3,amal js1.

Kowa harkar gabansa yake a gidan kumaa suna mugun son junansu,shi dady yace ba mace ba namiji a Neman kudi,kowa ya nema,dan haka yakke tasa yaransa gaba yana koya musu komi,suke kula da komi NASA na dukiya kawai guiding dinsu yake,dan yasan illar maraici,mum da dad suna matukar son Ahmad.

Ahmad fari kyakyawan gaske shi ba dogo ba ba kuma gajere ba normal yake,shi ba kiba kuma ba rama ba,idonsa masu matukar kyau,gashin nan ya tarashi luf luf,da wani dan saje kadan,hanci dogo,ga shi giant,a mazanma ya amsa sunansa,gashi da tsananin tsabta da daukan wanka,miskili ne na gaske,mata basa gabansa,nutsatse ne sai rashin daria da faraa,ga son harkar birni,da son class etc,yana da abokai amma bai cika kula kowa ba sai shahid dan gidan wani minister ne kuma yana da nutsuwa ga hankali,ba ruwansa ga fara'a da wasa tare sukayi PRI,sec,wannan kenan.

Cigaban labarin

Tafiya suke sosai a motarsu har Allah ya kawosu garin kebbi lfy tsayawa sukayi sukayi sallah suka ci abinci a wani resturant, sukayi take away suka kara daukan hanyar kauyen,Ahmad sai tsaki yake yana fushi,Inda ammar ke tsokanarsa,Mimi ta gaji dan tayi matashi da cinyar ya Ahmad sai bacci take abinta,yau juma,a yau kasuwar garin ke ci,sai Dana duba sai naga ai rugar su ramata suka zo ma tofa,basu suka karasa ba sai yamma lis,wani suka tambaya gidan me gari,aka kaisu,kowa sai kallonsu ake kamar a cinyesu,wasu matasan kuwa sha'awa suke inama sune haka,

An musu saukar girma,madara,zabi soyayye,da sauransu,haka me gari ya bawa dady daki shi kadai ba laifi komi yana da dan kyau,ga tsafta, shi yasa ma suka yarda da zama gidan,Ahmad da ammar ma an basu dan akurkin daki daya,driver da dan me gari dakinsu daya,Mimi CE kadai bata da masauki ko ina an rasa waje,sai maigari yayi umarni da a nemo masa ramata yanzu tazo,
Ramata najin kira gabanta ya fadi,dama dawowarta kenan daga kasuwa,wanka ta fito,tana tunanin lfy,ko wani laifi tayi,haka dai ta shirya cikin Sabin kaayanta na yan fulani da inno matar baffajo ta siyo mata,da sabon takalmin robarta hard a dan turarenta body spray me dadin kamshi dan Dari da hamsin ta fesa fito Fes,dole za a fadar sarki kar a ganta a yamutse馃榾馃榾tun daga nesa ta hango mota kamar jirgi,zo kuga idon ramata,kamar zai fado.


A dinga afwa da typing error readers.

Asma baffa.
[14:00, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMA

20-25

By
Asma baffa


Tunda ramata taga mota ta tsaya tana shafata tana kallonta,ta rasa inda zata sa kanta,tana can kallon mota ,shi kuwa lawwali dan me gari ya karkace yana ta bawa ammar labarin ramata yayinda Ahmad ke jinsu dan shi abin ma haushi ya bashi yanda suke gulmar wata banza,lawwali ya gyara zama yace aai in fada ma da me gari yace in aureta naki yarda hauka nake,yarinya ta tsufa a gida,ta girma har ta gaji da duniya,shi kam ammar daria yake kwasa yana ta zungurar lawwali,can lawwali yace ai su ramata anyi asara ga kyau sai ya tashi a banza shekara da shekaru ba miji,kawai dan iyayenka sun mutu, sai da me gari ya harareshi sannan yayi shuru,

Hakan yayi dai dai da sallamar ramata cikin nutsuwa da zakin murya,har kasa ta gaida me gari da alhajin birni baban su ammar cike da ladabi,ta gaida ammar da Ahmad,ba karamin mamaki ammar yayi ba shi da ya ganta me kyau haka,ga ta yarinya,dan shi ya zata takai 35 a yanda lawwali ke basu lbr,shi kam Ahmad ko kallon Inda take beba,bare yasan ya take,itakam ta zata ma bakin turawa ne,dan da a hanya ta gansu cewa zatayi aljanune,wani tsoro ma suke bata tsabar kyau da murjewar fata.

Me gari ne ya fada mata bukatarsa kan ta tafi da Mimi gidan su zauna zuwa 2wks,ba tare da jin komi ba ta amince,shi kam dady tunda yaji ita daya take kwana yace bai yadda ba sai dai ammar ko Ahmad ya bisu gidan da kyar aka kwantar masa da hankali cewar ba matsala,haka Mimi ta dauki Jakarta tabi ramata suka tafi,shuru duka sukayi suna tafiya,Mimi Ce ta gaji tace ya sunanki?ramata cewa tayi na karyar ko na gaskia,daria Mimi tayi tace all,take ramata ta wani kara gyara murya na gaskia rahma abubakar na karyar ramata,Mimi ta danyi mamaki da taga ramata ta gane mene ALL,murnace ta kama ramata tayi turanci sai dadi takeji,a ranta cewa tayi bari in dinga yara mata turanci ko ba komai na karu,can ramata tacewa Mimi and you,zainab ana CE min Mimi,tabbas Mimi tasha mamaki ko ba komai taga kokarin rahma a English,suna haka har suka je gidan,rahma dafawa Mimi ruwa tayi tayo wanka,sannan ta tafasa musu madara da sugar,sannan itama tayi wanka,kafin ta fito Mimi ta dakko bournvita ta hada tea lafiyaye da wannan madarar ta shanu da ramata ta dafa,bude Jakarta tayi ta dauko musu soyayyen naman kaza da snacks suka ci,ramata har godiya ga Allah tayi taci abinda ko a mafarki bata taba gani ba,itakam Mimi har ga Allah rahma ta kwanta mata har ji take dama dady ya dauke ta koma birni gidansu,haka suka kwanta suna hira,yayin da rahma ta kwashe tarihinta kaf ta fadawa Mimi,tausayata Mimi tayi matuka,itama ta bata lbrn gidansu

Please Login or Register in order to submit comment