Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiye kayansa. Idan almuru tayi ya shiga nema, ba ya komowa sai gari ya waye. Haka ya yi wata da watanni, har guzurinsa ya kare. Sai ya shiga cin 'ya'yan itace da saiwoyi da kwari. Dukan lokacin nan bai ga kome ba, har ya soma fid da zuciya.

Sai ya tashi ya fara gaba yana ta nema. Da rana ya sami kogon dutse ko na itace ya shiga ya yi barci. Da haka da haka har ya manta da lissafin shekarun da ya yi..

Ana nan ana nan wata rana yana yawo cikin daji sai ya hango wani abu yana kalkali kamar rana a jikin wani kalgo, duk murna ta kama shi, jikinsa ya dauki rawa, ya katsa a guje don ya ciro. Cikin gudu sai ya ci karo da wani kututture ya fadi, hakoransa suka fita. Da ya tashi bai ga kome ba, wuri ya yi dudum kamar da. Ya yi ta duba ko ina, duk ya tattake kewayensa, yana dubawa har gari ya waye. Sa'an nan zafin hakora ya tashi, ya rasa abin da ya ke masa dadi nan duniya. Ya zauna, nan ya ke yini da kwana, amma bai sake ganin kome ba. Ya cika da bakin ciki. Sai ya tashi daga wurin, ya yi ta nema. Ya dade da gaske bai sake gani ba.

Wata rana sai babban hadari ya taso, aka tsunke da ruwa. Amma a wannan lokacin ba ya kula da zafin rana ko ruwa kome tsananinsu, sai ya yi ta yawo yana nema. Yana cikin tafiya sai aka yi babbar walkiya da tsawa gaba daya, idonsa ya dushe, bayan haka sai dudum, ba motsi. Can sai ya daga kai ya hango haske kal. Bai yi wata-wata ba sai ya yanka a guje ya nufi can, sai ga kalgo shirim a gabansa kamar zai ci karo da shi, abin na walwal a jikinsa. Ya yi tsalle zai ciro. Kwaram sai aradu ta fada wa itacen ta tsaga shi biyu, ya fadi kasa tija! Tuni an yi jifa da Abubakar, yana can kwance bai san abin da aka yi ba. Bai farka ba sai can gari ya yi sha. Ya ga itacen ya bushe, babu alamar abin da ya gani da dare. Ya tashi jikinsa na nauyi, ya yi kwanaki kafin ya murmure ya iya yawo.

Ba'a dade ba da yawa ya sake ganinsa, gani na uku,, Ya kwana yana yawo ya gaji, sai ya juya zuwa mahutarsa, gari ya kusan wayewa. Ya duba gabansa, sai ya ga haske kamar hudowar alfijir, ya ce, "Ashe gari ya waye." Ya waiwaya, ashe abin da ya ke nema ne, haskensa kuwa ya fi dukan na sauran da ya gani. Nan da nan ya manta da gajiya, sai ya sheka a guje da bakin karfinsa don kada ya sake bace masa, kafin ya kai. Da ya mika hannu har ya taba shi sai ga katon kumurci ya tashi tsakaninsa da gindin itacen bakikirin, kaurinsa kamar cinya, bai ga iyakar tsawonsa ba. Sai ya fadi da baya, kumurcin ya fasa kai yana dubansa, idanunsa kamar garwashin wuta, yana fitar da harshe jawur kamar tartsatsi. Abubakar ya rufe idonsa ya ba da rai ga mutuwa.

Sai ya ji tsawa ana cewa, "Kai mutum, wane karambani ne ya kawo ka nan? Hadarin da ka shiga sau biyu ba su ishe ka ba

Cikin tsoro ya ce, "Wane ne?"
"Ni ne wanda sarkin aljanu ya mallaka mini dukan Karon kalgo. Babu kuwa wata halitta da za ta iya kwace shi daga hannuna sai wanda na ga dama in ba shi. Kai kuwa yau shishshiginka ya kawo ka ga halaka.

Abubakar ya ce, "Ranka ya dade, wallahi ban sani ba. Ba shisshigi ne ya kawo ni ba." Ya fada masa dukan dalilin abin da ya kawo shi.

Sai ya ji ya kyalkyace da dariya, ya ce, "Samari, ko da mu ba domin alheri a ke neman mu ba sai don mugunta. Da ka zo gare ni tun da fari da dukan wannan wahala ba ta same ka ba. Dukan muguntar da ka ke so na taimake ka da ita, amma ban da alheri, domin mugunta ita ce halina, wanda kuma ya yi nufin yinta shi ne abokina."

Daga nan ya suma, bai san komai ba. Da ya bude ido sai ya ga rana ta fito, shi kuwa yana kwance a gindin kalgo daidai inda ya fadi. Ya dubi nan ya dubi can, bai ga kumurcin ba, sai ya tsammaci ya yi mafarki ne. Sai ya duba ya ga battarsa, ashe ya yar da ita sa'ad da ya fadi. Ya mifa hannu ya dauka, sai ya ji wani abu yana rawa, ya bude sai ya ga haske kal, ko da ya ke da rana. Ya yi maza ya rufe, ya yi hamdala. Ya kunshe a jikinsa, ya tashi ya tafi, bai san abin da ya ke ciki ba, duk ya rude saboda murna da farin ciki. Sai ya kama hanya ya tasam ma wajen mutane. Ya yi ta tafiya yau da gobe, har ya fita daji ya shiga karkara, da haka da haka har ya kai SANGA.

SAIDAI FA KASH.....JIKI MAGAYI-05

ABUBAKAR ya yi kwanaki a Sanga ya sami abokan tafiya sa'an nan ya shiga cikin ayari, ga su nan ga su nan sai Yale. Da shigarsa bai zame ko ina ba sai gidan dattijon nan, uban Tausayinka-da-saufi. Da ya tafi tsohon ya gan shi bai gane shi ba. Ya ce shi ne Abubakar. "Tsohon ya ce, "Wane Abubakar ?" Ya ce wanda aka aiko shi daga Zauna-da-shirinka.

Tsoho ya ce, "Karya ka ke yi. Domin ka ji labarin wani yaro sunansa Abubakar ya zo nan na yi masa goma sha biyu na arziki, shi ya sa kai kuma ka zo."
Abubakar ya ce, "Wallahi, ni ne." Tsoho ya ce, "Ni ban yarda ba. Abubakar wanda ya zo daga Zauna-da-shirinka kyakkyawan yaro ba inda ya ragu, ga shi kai kuwa mummuna, baki, babu hakora, sai gizo kamar Barawo. Abubakar ya ce, "Abin da ya sa ka ga na fita kamata yunwa
ce, da wahalar tafiya. Ka ga tabban nan na jikina, bulala ne hamsin da aka yi mini a wani gari. Kunnen nan da ka gani an datse min 'yan fashi ne suka yi mini. Hakora kuma da ka ga babu, acikin jeji ne nabar su. Amma in har yanzu ba ka yarda ba, ga shaidata!" Sai ya mika masa battar.
Da ya buda sai ya ga haske kau ya haskaka dakin. Ya ce,
"Ashe gaskiya ne ! Ba wata shakka kai ne. Sannu, Abubakar." Sa'an nan tsoho ya ce, "Du wahalan nan da ka sha zuciyarka ba ta yi taushi ba, ka yafe wa abokin adawarka ba ?"

Ya ce, "Mutum ya sha wahala kamar haka sa'an nan zuciyarsa ta yi taushi? Dukan alhakin wahalan nan da na sha, zan dauki fansarsa ga wanda ya cuce ni, har da ta muguntar da ya yi mini da fari."
Abubakar ya kwana biyu ya huta. Rannan ya ce wa tsoho yana so ya koma gida. Tsohon ya yi masa goma sha biyu na arziki, ya hada shi da kanen Tausayinka-da-sauki domin ya je ya ga wuri. Suka yi sallama da juna, ya yi musu rakiya, suka mika suka yi ta yi, kwance tashi har suka kai Zauna-da-shirinka. Da Abubakar ya iso ya tafi gidan Tausayinka-da-sauki,
yaransa duk ba wanda ya gane shi. Ya ce, "Na zo wurin mai gida ne." Aka shiga aka shaidamasa ya yi baki. Da ya fito suka shiga, bayan da suka yi gaisuwa ya tambaye su daga inda suka fito. Abubakar ya ce, "Mai gida, ka manta da ni ne ?"

Ya ce, "I, na manta da kai, sai ka sanar dani," Ya ce, "Ni ne Abubakar mutumin Galma da ka ce in tafi in nemo karon kalgo."

Ya ce, "Abubakar! Wallahi ban gane ka ba, na ga duk ka fita kamarka ne, alama ka yi ciwo ne ?"

Abubakar ya ce, "Mai gida, ai ba don Allah ya sa ni mai yawan rai ba ne, da na mutu. Wahala duka ta duniya babu wadda ban sha ba. Saura na gode wa Allah da ya biya mini bukata. Abin nan da ka ce in nemo na samu. Ga shi. Wannan yaro kuwa da mu ke tafe tare da shi kanenka ne, tsoho ya hado mu da shi domin ya zo ya gan ka, ya ga inda ka ke zaune."

Tausayinka-da-sauki ya yi murna kwarai da gaske da ganin kanensa, da kuma jin ubansa na da rai. Ya ce wa Abubakar, "Tafi dakinka ka sauka, sai gobe in ka huta ma yi magana." Abubakar ya tashi ya tafi dakinsa ya sauka, aka kawo masa abinci ya ci, ya huta. Ya bar Tausayinka-da-sauki tare da kanensa yana tambayarsa labarin gida.
Da gari ya waye Abubakar ya zo ya ce wa Tausayinka-da- sauki, "Ga shi, abin da ka ce in nemo na samu. Ina so ka hada mini in koma gida, gama yau shekarata wajen goma sha ke nan rabuwata da gida, ina tsammani ma ba a zaci ina da rai ba."

Tausayinka-da-sauki ya ce, "Daidai ne." Ya hada magani ya ba shi, ya ce, "Ga wannan, idan ka tafi ran da za ka ga yaron ka wanke hannunka da shi, kada ka tabi kome sai yaron. Ga wannan kuma, sa'ad da ka gan shi ka yi kokari ka yanki gashin kansa, ka hada da wannan ka tafi ka sami sabon kabari ka tona ka binne a ciki, dukan bukatarka ta biya."

Abubakar ya sa hannu ya karba da murna da farin ciki da godiya mai yawa. Sa'an nan ya ce, "Amma ina da magana yadda zan sami damar shafa jikinsa, da kuma yadda zan samu gashin kansa, watakila shi ya ke da wuya."

Tausayinka-da-sauki ya ce. "Wannan ma ba shi da wuya, wanda ya tafi ya nemo abin da a ke tsammani ba shi samuwa, balle wannan? Amma ga wannan laya ka rike ta, kada ka yarda nan duniya wani abu ya raba ka da ita." Abubakar ya sake godiya da yawa."

Ran nan bai kwana a garin ba, ya tashi, kwanci tashi sai gashi a kofar Galma, kowa ya gamu de shi babu wanda ya ganeshi, har ya isa gida. Da ya isa gida bai tsaya ba sai ya kutsa kai a ciki. Uwar sa tana zaune a waje da la'asar, sai ta ga mutum ya shigo mata gida, ta ce, "Wane irin mutum ke nan ya ke shigowa gida bai
yi sallama ba ?" Abubakar dai bai ce komai ba.
Ta ce, "Idan ba ka fita ba na yi maka kururuwar Barawo." Sa'an nan ya ce, "Iya!"
Sai ta runtumo a guje ta rungume shi, ta ce, "Abubakar! Ya ce, "Ga ni dai, Allah ya nufa za mu sake ganawa."

Sai ta fashe da kuka. Makwabta suka ji, suka sheko a guje suna cewa, "Mene ne, mene ne?"

Ta ce, "Dana ne ya komo." Duk gida ya cika da murna da farin ciki.

Uwar ta ce, "Allah na gode maka tun da ka komo mini da dana lafiya." Nan da nan ta tashi ta kawo masa abinci ya ci, ya huta. Labari ya watsu ko ina Abubakar ya komo. Can kanensa yana kasuwa ya ji wansa ya komo, sai ya bar kayansa, ya yanko a guje ya nufo gida. Da ya zo ya iske shi da uwa tasu zaune, ya ce, "Iya, ina yaya?" Ta ce, "Ba ga shi nan ba a zaune?"

Ya ce, "Yaya! Barka da zuwa."

Ya ce, "Yawwa!"

Sa'an nan kanensa ya ce, "Wallahi da dai za mu hadu da yaya a hanya ashe da sai ya wuce in wuce, ba zan san shi ba, sai dai shi idan ya yi magana da ni. Domin na ga duk kama tasa ta sake."

Suka zauna suna ta tadi, mutane suna zuwa ana yi masa barka kwana da, kwanaki.

Ran nan suna zaune sai ya tambayi kanensa, "Ina labarin Zainabu ?"

Ya ce, "Ai Zainabu da fitarka ba ta jima ba sai ta haifi danta namiji kyakkyawa, yaron kirki, mai karatu, mai ganin girman kowa. Hanyar da ya kan wuce zuwa makaranta ke nan, zan nuna maka shi. Yaro ya girma kwarai." Suna zaune da azahar sai ga KYAUTA ya debo yara za su tafi kasuwar ranar Jumma'a. Kanensa ya ce, "To, ga shi can a tsakiya
mai kyakkyawar rigan nan."

Abubakar ya ce, "Ashe yaron ya yi girma, masha ruwa ba shi wuyar girma." Ya ce, "Haba yaya, kai kuwa ba ka dubi shekarun nan da ka yi ba!"

Ya ce, "Ai kuwa gaskiyarka." Abubakar ya ce, "Yanzu kuwa ai ba ya kwana cikin gida."

Kanensa ya ce, "Haba, wannan yaro ya fi karfin ya kwana cikin gida! Na ji ubansa ya gina masa wani babban soro daga cikin shamakinsa, ya sa masa kayayyaki masu ban sha'awa a ciki, nan ya ke kwana tare da yaran ubansa."

Abubakar ya ce, "A cikin gida kuma wane daki uwarsa take?" Ya ce, "Na ji daga wajen tsofaffi ya gina mata wani babban daki mai ciki uku, nan ta ke."

Ran nan da dare kafa duk ta dauke, sai Abubakar ya tashi. ya wanke hannunsa da maganin nan da Tausayinka-da sauki ya ba shi, ya fita sai gidan Malam Shaihu, ya shiga shamaki ya ga dakin da Kyauta ya ke. Ya shiga, ya iske duk suna barci. Sai ya kware jikinsa, 'ya shafe shi da hannunsa. Ya Lalubo almakashi daga ratayensa, ya datsi gashin kansa, ya fita abinsa

Ya sake shiga cikin gida kuma, ya tafi dakin Zainabu ya iske ta tana sharar barci, ya kira sunanta, "Zainabu !""

Sai ta juya cikin magagin barci, ta ce, "Wane ne ?" Ya ce, "Ni ne Abubakar wanda kika ci amanata. Kin sani sabo da ke ne na bar garin nan, na shiga duniya, na sha kowace irin azaba. Amma na komo in shaida miki ranar sakayya ta zo. Ki ji abin da zan gaya miki, don ki sani ba wanda zai ci fuskata ya zauna lafiya. Ɗanki da kika haifa zai zama lalatace. Don albarka kuka same shi, amma zai zama la'ana, zai jawo muku abin kunya da bacin rai, har wata rana zai zama sanadin kisan ubansa !" Sai ya juya a kan sawunsa ya fita abinsa.

Da asuba, Zainabu ta farka, tana zulumi a ranta tana cewa"Yau na yi mafarki mai ban tsoro, lalle muryar Abubakar ce na ji cikin magagin barci, kamar yana cikin dakina yana magana da ni, wannan magana kuwa ta ba ni tsoro !" Sai ta tashi a firgice, ta je ta dubo yaron, ta je har shamaki ta leka ta gan shi yana nan kwance yana barci. Sai ta komo dakinta, ranta ya kwanta kadan, ta ce, "Ashe mafarki ne kurum." Ta rike wannan a ranta, ba ta gaya wa kowa kome ba.
Da Abubakar ya fito, ya hada maganin nan, cikin dare ya tafi makabarta; ya sami wani sabon kabari ya tona, ya jefa ya maida kasa, ya rufe, ya komo gida ya yi kwanciyarsa.

Da gari ya waye Kyauta ya tashi. Bayan ya wanke ido ya yi salla ya shiga ya gaida ubansa da uwa tasa, ta ba shi karin kumallo, ya ce za shi makaranta. Ya fita sai dakin ubanda, ye iske kudi a zube a buzu, uban kuwa ya fita kofar gida, Sai ya sa hannu ya debi sule biyu ya fita abinsa. Maimakon ya tafi makaranta sai ya guje wa abokan zuwansa, ya shigh gari, ya kashe kudinsa.

Da uban ya shigo gida ya kirga kudi ya ga babu sule biyu. Saiya kira uwargidansa yace. Wa kika ga ya shiga dakin nan?" Ta ce. "Tun fitarka dai ban ga wani ya shiga ba sai Kyauta. Me ya faru ?" Ya ce, "Babu kome.

Ya yi mamaki a ransa ya ce, Na tabbata dana ba ya sata. Wannan. dabarar mata ce don su gama ni da yaron nan." Don ya sani ko da suna kishinsa. Amma in shi ne sa'ad da ya komo na tambaye shi, lalle ya gaya mini."

Shiru shiru bai ga Kyauta ya komo ba. Sai ya aiki wani daga cikin yaransa a je a gani Kyauta lafiya, bai ga ya komo gida ba. Malam ya aiko a fada masa shi ma da yana da niyyar zuwa da kansa ya gani ko lafiya, domin bai ganshi ya zo makaranta yau ba....JIKI MAGAYI-06

Sai ya aiki wani daga cikin yaransa a je a gani Kyauta lafiya, bai ga ya komo gida ba. Malam ya aiko a fada masa shi ma da yana da niyyar zuwa da kansa ya gani ko lafiya, don yau bai ganshi ya zo makaranta yau ba.

Da yaro ya komo ya gaya masa, ya kara mamaki domin bai taba fashin zuwa makaranta ba. Sai ya aika a neme shi. Aka yi ta nema ba a same shi ba, sai da la'asar ya komo gida. Sa'anan ubansa ya tambaye shi, "Ina ka tafi ka dade haken ?"

Ya ce, "Na tafi makaranta ne, na tsaya garin rubutu, ban gama da sauri ba."
Uban ya yi shiru, ransa ya baci, ya sani tun da ya ke wata karya ba ta taba fitowa bakinsa game da shi ba.
Ubansa ya ce, "Da safe da ka shigo dakina ka ga kudi a buzu? Domin na bar wadansu akai, ban ga sule biyu ba. Ko ka san wanda zai dauka?"

Sai Kyauta ya ce, "Ina ruwana, ka ba ni tsaronsa ne?" Sai Malam Shaihu ya tafi wurin Zainabu, ya ce mata, "Me ya şami yaron nan yau? Gama ban taba ji ya yi mini magara irin wadda ya yi mini yanzu ba."

Sai jikinta ya yi sanyi, ta tuna da mafarkin da ta yi. Ta ce, "Me ya gaya maka?"

Ya ce, "Tambayarsa kawai na yi ko ya ga wani abu nawa da ya Bace mini, sai ya taso mini da bakar magata, ga shi kuma ya yi mini karya ya tafi makaranta ashe kuwa bai tafi ba." Ta ce, "Sai ka kyale shi, ni zan tambaye shi, watakila akwai wani dalili."

Da uban ya fita sai ta tashi, ta shirya masa abinci mai kyau. ya shigo yana ci na tambaye shi, lalle ya gaya mini ko menene ke damunsa, gama bai taba Boye mini kome ba Da abinci ya yi ta aika a kirawo shi ya ci, sai ya yi zamansa
bai kula ba. Sai zuwa can abinci duk ya huce, sa'an nan ya shigo
ya ce, "Ina abincin ?" Ta kawo masa. Da ya bude ya ce, "Abincin kenan da sanyi haka, sai ka ce na kare?" Sai ya shure da kafa, abincin ya zube, ya tashi zai fita.
Sai tace, "Tsaya, ina so in yi magana da kai. Me ya same ka?"

Sai ya ce, "Ni fa kun ishe ni da tambaya." Sai ya fita abinsa, ya bar ta ranta a Bace, tana ta kuka. Shi kuwa ran nan bai kwana a gida ba. Ya tafi inda a ke molo, nan ya kwana.

KWANCI tashi aka ga halin yaro yana dada lalacewa, sai yawan fade-fade da yara a cikin gari, kullum a kawo kara tasa yaki zuwa, makaranta, sai yawace-yawace barkatai, ba ya kwana a gida. Idan ya shiga gida kome ya gani na ubansa, ko na uwar, sai ya sace. Gari duk aka tsargu da shi, ana ta mamaki, ana cewa, "Me ya faru? Yaron kirki kamar wannan wanda ba ya iya gaida mutum a tsaye, ba a taba jin ya yi fada da kowa ba, ga shi yanzu ya lalace sai sace-sace kamar Bera." Ya zama dai Malam Shaihu ba shi da sukuni, balle uwar yaro. Kome ya hada su da kishiyoyinta sai su rika mata gorin cewa, "Tafi can! Da ana dokin an sami ɗa, ga shi nan ya zama gafiya." Ta yi ta kuka babu magani. Ita ta buga, uba ya buga.. Kayya! Bakin alkalami ya riga ya bushe.

Sai Zainabu ta tunawa da abin nan da ta ji cikin magagin barci, ta ce ashe kuwa gaskiya ne. Allah ya isa mana da wanda ya yi wannan aiki. Amma galibin zaton mutane a cikin gari kishiyoyinta ne suka yi wa dan magani, sabo da kishinsu basu da shi.

Rannan sai Malam Shaihu ya kirawo uwar yaro, ya ce mata, Abin da ya su na yi kiranki ina so mu yi shawara, ni fa al'amarin yaron na ya ishe ni. Ga shi yanzu ni wanda na ke kamar shugaba cikin wannan gari yau na zama kamar bera, sabo da kunyar wannan yaro. Ga shi yaki zuwa makaranta, sai yawace-yawacen banza a gari, kina gani wani lokaci na kan kwana bakwai bansa shi a ido ba, sai na aika a nemo shi tukuna. Idan ya dore da wannan hali. lalle zuwa gaba ban san irin abin kunyar da zai jawo mini ba. Ina shawara ?"

Ta ce. Mai gida. mace tana da wata shawara? Ai wannan abu ya fi karfin magana. Me zan ce? Amma sai ka yi hakuri. zai wuce da ikon Allah"

Ya ce. "Ba za mu iya zama da shi haka ba, zan aika da shi wurin malaminsu ya daure shi a mari, a hana shi fita har lokacin da ya sauka."

Sai ta fashe da kuka.

Yana shirin in gari ya waye ya aika a kirawo Malam Sambo ya hada su. Da asalatun fari sai Kyauta ya gudu daga gida ya tafi nasa yawo. Da ya ga idan ya zauna cikin gari za'ayi ta nemansa har a same shi, sai ya tuna akwai wata kasuwa kamar mil biyar daga Galma inda a ke taro, sai ya nufi can. Ya sani kuma akwai wani yaron ubansa can yana sayadr da hajjoji.
Da ya je sai ya ce wa yaron ubansa anyi musu hutun fitar makaranta ne, domin Salla ta kusa, ya tambayı ubansa ya zo wurinsu a kasuwa. Yaron ya ce, "Kai Kyauta, watakila karya ka ke yi. ba ka taba zuwa nan ba, ko dai ka gudo 'ne ?"

Ya ce, "Wallahi ban gudo ba, idan kana tsammani karya na ke yi ka aika a tambayo."
Ya cc, "To, Zauna."
Rumfar kuwa ta cika da baki masu Sayayyar kayan Salla. A cikin bakin nan kuwa akwai wani wanda ya ke da kudinsa a jaka, ya sa a cikin kayan da ya saya, ya ta da kafa da shi. Kyauta kuwa ya lura sa'ad da ya kwance, ya biya wani kallabi da ya saya, ya mayar ya ajiye. Can an jima sai ya tashi zai fita ya yi bawali ya debi kayan da ya saya, ya dora bisa kudin ya fita. Da ya gama bawali, sai ya ga wata riga, ya saya yana ciniki. Kyauta kuwa ya tashi, ya faki idon mutane ya dauke kudi ya fita abinsa. Bai yi wa kowa sallama ba. Da bako ya gama cinikin riga dillali ya biyo shi rumfa ya karbi kudi. Da ya zo ya hankada ya duba kudi, sai suka ce daukarmu inda ka ajiye mu. Nan da nan sai ciri ya tashi a rumfar, kowa ya yi tsaye, aka bincike masa kaya ba a ga kudi be. Aka nemi Kyauta aka rasa.Kica kica sai rumfar alkali. Aka tafi aka maida jawabi, alkali ya sa aka sake zuwa aka yi cajín rumfar kaf, ba a ga kudi ba. Sai daya daga cikin wadanda su ke zaune a rumfar ya ce, "Allah ya gafarta malam, wani yaro fa ya zo rumfar, ni kuwa da ganinsa ban yarda da shi ba. Da aka zo kuwa ana ceton kudi muka neme shi muka rasa."

Alkali ya tambayi mai rumfar, Wane yaro ne?" Ya ce, "Gafarta malam, ai Kyauta ne dan mai gidammu Malam Shaihu."

Alkali ya ce, "Barawon yaron nan ! Babu shakka shi ya debe kudin." Ya sa aka yi ta cigiyar yaron ba a gan shi ba, sai da kayar aka samo shi.

Da aka kawo shi gaban alkali ya tambaye shi, "Kai ka shiga rumfar wancan yau Ya ce, "Ni dai ban shiga rumfarsa ba, ni ma yanzu na zo
kasuwa Alkali ya ce, "Kai dai fada mini gaskiya, ai ba da wata magana a ke nemanka ba." Da kyar da wayo ya ce ya shiga. Alkali ya ce, "Ka fada mini gaskiya, sa'ad da ka shiga rumfar ba ka ga mutumin nan da kudi ba?" Ya ce, Allah ya gafarta malam, ban lura ba. Wanda bai je
sayen kome ba ya kula da kudin mutane ?"

Alkali ya ce, "Ka ga lokacin da ya tashi ?" yace eh Na gani."

"Me ya sa a lokacin da ya tashi kai kuma ka fice daga rumfar, bakayi sallama da kowa ba

Ya yi shiru.

Alkali ya ce, "Ina kudinda ka dauka nasa" Alkali ya ce, "Ida ka fada mini gaskiya, baka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment