Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiransa Malam Shaihu ya ji labarinta. Domin kwadayi kawai ya kangarata, ko da ya ke yana da matansa hudu. Irin wannan mutum bai kamata ya zauna lafiya ba. Ba shi yiwuwa a gare ni in zauna cikin garin nan, in ji ya aure ta. Saboda haka ne na rasa abin da zan yi domin in fanshewa kaina takaici. Sai na shiga cikin duniya ina yawace-yawace har Allah ya kawo ni garin nan. Ina cikin tambaya har aka gaya mini babu wanda ya fi ka sanin magani cikin dukan kasar nan Saboda haka na zo gare ka, in ka yarda ka taimake ni in dauki fansa a kansu, raina ya huce."

Tausayinka-da-sauki ya ce, "To, madalla, ka kuwa kawo kuka inda za a share maka hawaye. Dukan abin nan da ya kawo ka kafin ka fadi na riga na san shi. Domin jiya bayan da muka rabu Doguwa ta zo ta bayyana mini dukan abin nan da ya ke tafe da kai. Amma yadda ka ke tsammani ba haka ba ne. Domin ba kwadayi kadai ne ya sa attajirin nan ya yi maka wannan abun ba. Dalili dai yana son ɗa ne, an kuwa gaya masa Idan ya auri yarinyan nan zai samu."

Sa'an nan Abubakar ya ce, "Ashe hakanan ne?" Yace, kwarai

Abubakar ya ce, "To, zai kuwa samu ?" Ya ce, "Lalle zai samu, domin wannan magana ba nufin mutum ba ce, ikon Allah ne."Sai Abubakar ya yi shiru, ya nutsa dikin zurfin tunani. Sa'an nan ya ce, "To, tun da ya ke kwadayin ɗa ne ya sa ya yi mini wannan abu, abu daya ne kadai zai faranta mini zuciya, shi ne albarkan nan da ya ke nema ta zama masa la'ana."

Sai Tausayinka-da-sauki ya yi shiru, sa'an nan ya ce, "Wannan abu zai yiwu, amma da wuya. Ka yarda in na yi maka dukan hakinsa yana kanka?"

Abubakar ya ce, Na yarda. abin da duk Allah ya so ya yi da ni a kan wannan abu na dauka ni dai bukatata ta biya." Ya sake cewa, "Idan ka yi mini wannan me zan biya?""

Tausayinka-da-sauki ya yi dariya, ya ce, "Ni ba zan karbi kome daga gare ka ba, domin dukan abu kai zakayi da kanka. Ka iya ka jure ka samo abin da zan gaya maka?"

Ya ce. "Da ikon Allah zan iya."

Tausayinka-da-sauki ya ce, "Ina so ka samo mini KARON
KALGO." Ya ce "A ina zan sami wannan? Ban taba ganin wanda ya same shi ba."

Ya ce, "Ba shi a kasar nan, amma zan gaya maka inda idan ka tafi, ka samu. Ka san ba a kasan nan aka haife ni ba, ni mutumin Yale ne. Na bar gida tun ina yaro, sabo da shedancin neman asiri. Na ji kuwa har yanzu ubana yana da rai, yana kuwa begen ganina kullum, domin ni ne babban dansa. Zan aike ka wurinsa shi zai gaya maka inda za ka samu, domin na tuna tun ina yaro na kan ji yana ba da labarinsa."

Abubakar ya ce, "Kaka zai yiwu? Ko na tafi ba zai san daga wurinka na fito ba, gama ka shi rabuwarka da gida shekaru da yawa ke nan."

Sai ya sa hannu cikin ratayensa, ya kwance wata laya, ya ce, "Ga wannan ka kai masa, da ganinta ya sani. In ka tafi ka gaya masa dukan labarinka ka ce ina gaishe shi ina kuwa da rai Ina kuwa so ya yafe mini dukan irin dangin abin da na yi masa. Idan ya huce ya aiko mini sa'ad da ka ke komowa, na koma gida. Idan ka cika abin nan da na umurce ka ka biya hakin dukan taimakon da zan yi maka ke nan.

Da gari ya waye, Abubakar ya danki hanya yana ta tafiya, kwana wannan gari, tashi kwana wancan. Wani wuri ya sami abinci, wani wuri kuwa sai ya yi bara sa'an nan ya samu da kyar. Da haka da haka bayan wata biyu ya kai garin da aka aike shi.

Da ya shiga Yale tun wajen azahar yana ta yawo yana ta tambayar gidan uban Tausayinka-da-sauki. Ko ina ya tafi sai a ce, "Ba mu taba jin mai suna haka ba, balle mu san ubansa." Da ya gaji da tambaya sai ya yi zaune a gindin wata itaciya. Can sai ga wani dattijo zai wuce, ya tashi ya tare shi, ya fadi ya gaishe shi, ya ce, "Tambaya na ke yi. Ni bako ne daga wani gari ana ce masa Zauna-da-shirinka, wani babban boka ne ya aiko ni wurin tsohonsa. Shi kuwa tun yana karami ya dora, yana can yanzu ya yi arziki. Ni kuwa domin ragon azancina da zam fito na manta in tambaye shi sunan ubansa. Shi kuma bai gaya mini ba. Ko Allah ya sa ka san shi?"

Dattijon ya tsaya shiru, ya sunkuyar da kai, ya dade bai yi magana ba. Sa'an nan Abubakar ya ce, "Me ya same ka? Domin na tambaye ka kawai, wannan ya isa ya ɓata maka zuciya?"

Dattijon ya ce, "I, wannan magana da ka fadi ta tuna mini da abin da ko da ya ke cikin raina." Abubakar ya ce, "Sannu baba, da na san wannan magana
za ta Bata maka rai da ban tambaye ka ba." Sai tsoho ya ce, Babu kome, Allah shi ne Sarki."

Sa'an nan da Abubakar ya ga dai hankalin tsoho bai kwanta ba ya ce, "Baba, don Allah ka fada mini abin da ya Bata ranka."

Tsoho ya ce, "Ka ji, dana, ina da wani ɗa kamar yadda ka fadi, yau shekaru da yawa ya dora, amma ya mutu. Shi ne abin da na ke tunawa kullum, da ka yi mini magana kuma ya sake fado mini a rai."

Abubakar ya ce, "Yaya ka tabbata ya mutu?" Tsoho ya ce, "Tun shekarun nan da ya fita gida ban ga wanda ya gan shi ba, ban kuwa ji labarinsa ba. Shi ne ya sa na tabbata."

Abubakar ya ce, "Yaya kamar danka?"

Sai tsoho ya sifanta masa shi, ya ce amma wannan tun yana yaro ne, ba wanda zai gane shi yanzu. Sa'annan ne Abubaka: yace, "Kada ranka ya Baci, watakila
Allah ya kawo ni nan domin ka sami labarin danka ne." Tsoho ya ce, "Wannan ba shi yiwuwa, abin da aka yi she- karu da yawa. Ko yana da rai ma yaya zan tabbatar"

Daga nan Abubakar ya sa hannu a aljihu yafito da laya, ya ce, "Duba wannan abu ka gani, ko ka san shi?" Sai dattijon ya karba ya duba da kyau, ya ce, "Daga ina ka sami wannan?"

Ya ce, "Shi ne mutumin da na gaya maka ya ba ni in kai wa ubansa domin shaida."

Dattijon ya ce, "A! Allah Sarki, shi ne mai aikata abin da ya ga dama. Babu kuwa abin da ba shi yiwuwa a gare shi. Babu shakka ZAKARI yana da rai." Daga nan ya ce, "Zo mu tafi gidana, na kosa in ji dukkan labarinsa."

Sai suka tafi gida, ya saukar da shi, aka ba shi abinci ya ci, ya huta, sa'ar nan ya gaya masa dukan labarin dansa. Dattijon ya ce, "Da ikon Allah sai na aika masa ya komo
gida."

Ya sake ce masa, "Kai kuwa menene gaminka da shi, har zai aiko ka tafiya mai nisa haka, da wahala, da rashin sanin wuri?"

NAZO NEMAN KARON KALGO NEJIKI MAGAYI-03

Abubakar ya ce, "Dalilin saduwata da danka, wani abin bakin ciki ne ya same ni a garimmu wanda na kasa daurewa, na yi fushi na fita gida neman sakayyar abin nan da aka yi mini Ina cikin yawace-yawacena har Allah ya kai ni garin da ya ke, aka gaya min shi kadai ne zai iya fashe min wannan takaicin. Dana, tafi na shaida masa, ya ce zai bani, amma sai na samo masa karon kalgo tukunna. Da ya fada mini haka, na ce masa bansan inda zan same shi ba. Shiyasa ya aiko ni gare ka, ya ce
domin sa'ar da ya ke yaro ya kan ji kana ba su labarin inda a ke samu."

Dattijon ya ce, "Wane abu aka yi maka da zafi haka har da za ka yarda ka sayar da ranka? Domin samun wannan abu sai wanda Allah ya nufe shi da ganinsa."

Ya ce, "Aure na nema a garimmu, wani attajiri ya kwace ta ba girma ba arziki, ni da azatona kwadayi ne kawai da alfarmar dukiya. Amma da na zo na gaya wa danka ya kauda ni cikin wannan jahilci, ya ce dalili dai sabo da an gaya masa sai ya aure ta, sa'an nan zai ga ƙwan sa shi kuwa bukatarsa ke nan gaba da kome cikin duniya, domin bai taba samun ɗa ba. Sa'an nan na nemi taimako wurin danka, abin nan da za'a haifa masa maimakon albarka ya zama kasaitaccen lalatacce a duniya wanda zai jawo masa ko wace irin masifa, ya zama ya gwammace ya mutu ba shi da ɗa. Ya ce zai bani, amma sai na kawo masa ƙaron kalgo."

Dattijon ya ce, "Samari, abin da ya fi kyau ka hakura, ka bar shi ga Allah ya saka maka, domin wannan abin da kake nema ba abin kirki ba ne. Bai kamata ka saka mugunta da mugunta ba, ka bari Allah shi ne mai hukunci tsakaninku."

Tsohon ya yi ta rarrashinsa. Da dai ya ga bai ciwo kansa ba; ya ce, "Wannan abu da ka gaya min ban ji dadinsa ba. Amma tun da yake dalilinka ne na sami labarin dana, lalle ba zan iya kin taimakonka ba, ko da ya ke abin da ka ke bukata ba mai kyau ba ne. Amma ka sani da wahala mai yawa a gabanka, ko rabin tafiyarka ma ba ka yi ba tukuna. Inda zaka samo abin nan, sai ka rabu da mutane, ka shiga can cikin Dawan rukuki, nan ne idan Allah ya yi maka katari, ya gajarta wahalarka, za ka samu, Amma fa, kai, samun abin nan sai namijin gaske! Idan ka ji maganar da na gaya maka, gwamma ka koma gida ka hakura, ka bar shi ga Allah."

Abubakar ya ce, "Komai wuya idan dai zan samu, ba ni komawa gida, na gwammace garin neman wannan abu in mutu da in koma gida in zauna ina ganin takaici kullum." Dattijon ya ga dai ya kwallafa ransa ga tafiyar ya ce "Ka
kwana biyu ka huta, sa'an nan inbaka guzuri ka tafi."

**************** *********** ******* ************

Ana nan Zainabu tana gidan mijinta suna zaman jin dadi da juna, ba ta fi wata biyu ko uku ba, sai ciki ya samu. Da lokaci ya yi ta haifi ɗa kyakkyawa. Aka gayawa Malam Shaihu matarsa ta haihu, sai ya yi farin ciki da murna mara iyaka, domin dama abin dayake nema kenan sama da komai a duniya.

Nan da nan aka fada wa sarkin Galma matar Malam Shaihu ta haihu. Sarkin Galma ya aiko da kaya da yawa, yana murna kwarai. Malam Shaihu ya sa aka aika ko ina a sanar da abokansa da yaransa matar sa ta haihu. Kowa kuwa sa'ar da yaji sai murna da farin ciki masoyinsa ya sami magaji.

Ranar rada suna aka yi babban taro, aka yanka shanu da raguna, aka yi gagarumin biki har ya fi na ranar da aka yi auren yarinyar. Aka sa wa yaron suna ABDULLAHI amma galibi suna kiransa KYAUTA. Aka yi kwanaki ana ta rigima. Manyan malamai da dattijai kowa ya yi masa addu'a, Allah ya rayashi ya zama yaron kirki cikin musulunci, ya rike su kamar yadda ubansa ya rike su.

Ana nan ana nan yaron ya yi girma, aka yi masa bante, aka sa shi a makaranta ya yi karatu, har ya kusan saukewa. Tun tasowarsa yaron kirki ne mai nagarta, abin so ga kowa. Kullum abin farin ciki ne ga ubansa, babu irin jin dadin da ba ya jiyar da shi. Kullum inda Kyauta ya raba baka raba shi da yara. Ubansa ya gina masa wani kyakkyawan daki a shamakinsa, nan ne ya ke kwana tare da sa'o'insa yara. Da shi da kowa a cikin gari sai ban girma da ladabi, baya raina kowa. Inda ya wuce duka sai sa masa albarka ake yi.

Amma Abubakar bayan ya kwana biyu Yaji ya huta, ran nan dattijon ya kawo doki wanda zai hau, ya kawo kudi da zai sayi abinci a hanya, ya kawo tufafin sawa da na rufa, ya ba shi, ya sa shi a hanya, ya ce masa, "In ka fita daga nan kada ka ratse ko ina sai ka kai wani gari da a ke ce masa SANGA. Daga nan idan ka huta ka tashi ka yi arewa tafiyar kwana kamar bakwai, kana ta tambayar Dawan Rukuki, in ka bi ga ka yi ta yawo, watakila Allah ya yi maka gamon katar. Ka san irin abin da za ka nema abu ne mai sihiri, ba shi da wuyar bacewa, har wani lokaci ya kan yi wa mutum kwari ya haukace ko ya mutu.

Ya ce, "Ban taba ganin irinsa da idona ba tun da na fito duniya."

Dattijon ya ce, "Idan Allah ya gwada maka shi, za ka ga wurin da ya ke ya dauki haske sai ka ce rana. Shi kuwa dan rankafen abu ne. Amma galibi idan ka je za ka dauka, ya kan Bace. Idan ka shiga Sanga ka sami batta, ka shafe ta da kitse, a ciki za ka saka in ka samu."

Suka yi sallama da juna, dattijon ya ce, "Allah yabaka sa'a, ya gajarta wahalarka!" Ya ce, "Amin."

Abubakar ya shirya 'yan kayansa ya daure, ya taka dokinsa ya hau. Ya yi ta tafiya cikin kungurmin daji. Tun da ya tashi bai gamu da kowa ba sai mutum guda kusa da Yale. Mutumin ya ce masa, kai kuwa Wannan mutum, ina za ka cikin wannan kungurmin daji kai kadai sai doki da wannan kaya haka a sarari? Ba ka tsoron hadari? Da alama dai kai bako ne, ba ka san hanyan nan ba."

Abubakar ya ce masa, "Za ni Sanga ne." "Sanga Amma wannan mutum da wargi ka ke, kodayake ban san irin shirinka ba. Je ka, Allah ya fisshe ka " Yace, "Amin."

Tun daga nan Abubakar ya soma jan Li'ilafi, yana ta tafiya har rana ta take: Yana dai ta yi, har shi da dokinsa suka tarke don yunwa da tsananin kishinwa.

Ya ciccije, suka isa wani babban rafi mai kwazazzabo da kyar. Da zuwansa sai ya sauka ya kowance wa dokinsa sirdi, ya debi 'yan kayansa ya kai inuwa, yaja dokin ya gangara da shi yasha ruwa ya yi wanka a rairayi.

Sa'an nan ya jawo shi tudu ya yi masa tarnaki, yana cin ciyawa a bakin ran. Shi kuwa ya gangara, ya tube ya yi wanka. Ya sa tufafinsa, ya debo ruwa, ya hayo ya zauna a inuwar da kayansa da dan guzurinsa yana ci. Babu zato Babu tsammani.....JIKI MAGAYI-04

Babu zato Babu tsammani ya duba bayansa sai ya hango mutum biyu suna zuwa, ko wanne da kwari cike da kibau, da baka da wata kibiya a zare, sun nufo shi. Shi dai a lokacin nan zaune ya ke kamar wanda ya mutu don tsoro. Da zuwansu sai daya ya yi sallama, Abubakar ya amsa "Kai, ina za ka?" da rawar jiki,
"Barawon ya ce, Ya ce, "Sanga."

"Kai bako ne ba ka taba bin wannan hanya ba ?"

Ya ce, "Tun da na ke ma ban taba zuwa kasar nan ba." Sai dayan ya ce da dan uwansa, "Kai wane irin mutumin banza ne, mun zo mu yi hira ne? Mu yi abin da ya kawo mu mana, mu tafi."

Ya ce. "Kai, da ranka da kayanka ka zabi na zaba"

Abubakar ya ce, "Na zabi raina."

Ya ce, "Tube riga da wandon da ke jikinka ka dora bisa kayan nan naka." Ya tube, ya dora, Sai dayan ya tafi garin ya kwanto doki. Da doki ya ga ba ubangijinsa ba ne, ya dinga harbe-harbe da cije-cije. Sai ya ce, "Zo mana, kana ganin dokinka zai cije ni!"

Sai Abubakar ya yanka a guje, ya kama doki, yasa masa linzami ya jawo, ya daura sirdi. Suka ce, "Je ka abinka!" Sai ya kama hanya tik sai turen bante. Da dai suka ga ya fara tafiya sai daya ya ce, "Tsaya nan!"
Abubakar ya tsaya cif, ko daga kafa bai yi ba, jiki duk na rawa. Da zuwan dam fashin sai ya kife shi da mari ya kife, ya zare wuka ya yanke masa rabin kunne, ya bar shi nan. Su kuwa suka tsere da kayan. Abubakar yana nan kwance sai kururuwa ya ke yi, ga zafin mari ga kunne yana ciwo, ga takaicin kayansa duk an kwace. Zuwa can sai ya farfado, ya ja jiki duk jini, ya kama hanya ya yi ta yi har la'asar, bai gamu da kowa ba, babu kuwa wanda ya cim masa. Sai da la'asar sannan ya ji maganar mutane suna zuwa a bayansa, tsammaninsa wadansu yan fashi ne, sai ya shige daji kadan, ya rabuke a jikin wata itaciya. Ashe masu jakuna ne su ke zuwa. Da ya ga haka,
sai ya fito ya tsuguna a hanya. Da suka zo suka ce, "Kai, me ya same ka?" Yace. "Daga Yale na fito za ni Sanga, 'yan fashi suka tare ni a hanya suka kwace min dukan abin da na ke da shi, suka bubbge ni, kun gani har kunnena ma sun datse don keta"

Da suka Ji dukan abin da ya gaya musu suka ce, "Lalle hakanan ne, gama jinin ga alama a hanya. Suka yi masa juyayi, wani daga cikinsu ya kawo 'yar taguwa ya ba shi. Suka dora shi a kan jaki, suka kai shi wani gari, suka wuce. Ranar dai kam ya rasa gidan sauka ya kwana da yunwa a kasuwa. Da gari ya waye babu abin karin kumallo, sai bara, wanda ya ga Allah ya ba shi sadaka. Kwana da kwanaki yana kwana a kasuwa. Ran nan sai wani mutum ya gan shi ya tambaye shi inda ya fito. Ya gaya masa dukan hadarin da ya same shi. Ya, ji tausayinsa ya karbe shi a cikin gidansa, har ya huta karfinsa ya komo. Da ya yi 'yan kwanaki ya huta sarai, ran nan sai ya ba shi guzuri, suka yi sallama, ya dauki hanya.

Kwanci tashi yana ta tafiya har ya kai wani gari ana ce masa RIMI da lisha. Ya nemi masauki, ko ina ya tafi sai a kore shi. Da dai ya ga babu wurin kwana, sai ya tafi kasuwar garin, ya nemi wata rumfa ya shiga ya kwanta. Ya yi barci kai daya sai ya ji ana cewa, "Barawo! Barawo!" Aka nufo kasuwa. Shi kuwa don ragon azanci, ga shi bako ba wanda ya san shi, sai ya fito ya tsaya a kofar rumfar. Sai wani mutum ya ga baki baki ya ce, "Gudummawa jama'a! Ai ga shi nan!" Nan da nan aka yi masa caa, aka rufe shi da duka, yana cewa, "Ku tsaya, ku tsaya, ni ba Barawo ba ne! Ni bako ne yau na sauka, na nemi wurin kwana ko ina a cikin gari ban samu ba, shi ya sa na komo kasuwa na kwanta. Gama kayana can a rumfa". Mutane suka ce, "Karya ya ke yi, lalle shi ne Barawon da aka
koro yanzu
Aka daure shi tam, sai gidan sarkin Rimi. Da gari ya waye aka kai shi gidan alkali, aka tambaye shi garin da ya fito, ya ce daga GALMA ne.

Suka ce, "Ba mu taba jin wani gari da suna haka ba. Lalle Karya ya ke yi, Barawo ne". Alkali ya ce a yi masa bulala, hamsin, a daure shi wata uku. Aka gwada masa azaba mai yawa.

Bayan ya gama wata uku aka kwance shi, aka kore shi daga garin. Ya kama hanya tasa. Duk wahalan nan da ya sha zuciyarsa ba ta girgiza ba, sai dada kekashewa ta yi, duk hankalinsa yana kan rama muguntar da aka yi masa.

Yana ta tafiya, kwance tashi har ya kai Sanga. Kullum a zuciyarsa ya kan ce, "Ba ni dai komawa gide komai wahala, sai na samo Karon kalgon nan, bisa ikon Allah

Da ya tuna da wuyar da ya sha a Rimi yana zuwa garin sai ya nu fi gidan sarki, ya ce shi bako ne zai wuce, amma yana neman masauki. Sarki ya tambaye shi daga inda ya fito, ya fada masa. Ya sa aka ka shi bakin kasuwa, aka saukad da shi a gidan wani mutum mai samu, ga shi kuma mutumin kirki. Yana nan zaune gidan da sarki ya saukar da shi, babu abin da ya rasa na wajen abinci.

Ran nan suna zance da mai gidansa sai ya ce masa, Zaman nan ba zai yi mini ba, ka ji ka ji abin da ya ke tafe da ni, an yi mini kwatanci ne da dajin can na Rukuki, an ce sai a can zan sami abunda na zo ne nema

Mutumin yace masa, "Lalle kuwa sai can, domin kuwa akwai daji, babu irin abin da ba za a samu a ciki ba. Amma ya kamata ka zauna kwana biyu ka huta sarai, gama ka gaji da wahala. Sa'ad da ka huta sa'an nan na ba ka dan guzuri ka tafi". Abubakar ya yarda da magana tasa, ya yi zamansa, yana dako yana samun 'yan kudinsa yana kullewa har ya tara guzuri.

Ran nan ya ce wa mai gidansa yana so zai tafi. Ya kawo guzuri mai yawa ya ba shi. Abubakar ya kintsa kayansa har ya sami battar da dattijon nan ya ce masa ya nema, inda zai jefa Karon kalgon idan ya samu. Sai ya mika, ya kwana wannan gari, ya tashi ya kwana wancan, har ya zo wani gari ya kwana, aka ce masa babu wani gari a gaba.

Ya tambayi labarin Dawan Rukuki, amma bai sami tartibi ba, domin kowa ya tambaya sai ya ce bai taba zuwa ba. Amma,. kowa ya sani mugun daji ne da gaske, ba su ma taba jin labarin wanda ya je ya komo ba. Ya zauna nan ya fara shiri don wahalar da ke gabansa. Da ya gama shiri sarai sai ya tashi ya kama hanya, har ya wuce karkara, tungana ganin kauyuka daya daya har ya komo kuma ba ya gani sai makiyaya. Bayan kwana da kwanaki su ma ya daina ganinsu. Bai dai fasa ba yana ta tafiya, har ya sami gidan wani maharbi can cikin kungurmin daji. Sai ya ratse gidansa, ya yi sallama, mai gida ya fito ya tambaye shi abin da ya kawo shi cikin wannan daji. Da ya gaya masa ya yi mamaki, ya ce, "Da za ka ji shawarata da sai ka koma tun kana da sauran sukuni, in ka ki tawa ka wuce, lalle ba za ka komo ba. Domin wannan ba karamin daji ba ne, ko ni da ya ke daji ne gidana, iyakata nan, na kan kuma yi wata uku ban ga wani mahaluki ba."

Abubakar ya ce, "Na ji na gode, amma tun da na rigaya na yi niyya babu abin da za ka gaya mini wanda zai kaushe ni daga nufina. In yi tafiya irin wannan mai dadewa, ga hadari da wahala, sa'an nan in koma hannun wofi ?"

Sai maharbi ya ce, "Kome hadari da wahala da ka sha kadan ne bisa ga wadanda za ka sha gaba nan." Daga nan ya shiga ba shi labarin abin da ya sani na dajin nan na wajen ban tsoro da mugunta da aljannu da ke ciki. Da ya ga dukan abin da ya gaya masa ba su razana shi ba, bai kuwa kauda shi daga nufinsa ba, sai ya kyale shi, ya ce, "Amma gobe zan raka ka har dutsen can, a nan zan nuna maka inda za ka nufa."

Da gari ya waye suka kama hanya da shi da maharbi har suka kai dutsen da ya fadi, suka hau. Daga can Abubakar ya duba, iyakacin ganinsa babu komai sai kungurmin daji baki kirin, gwanin ban tsoro. Sai maharbin ya ce, "Ka ga dutsen can dushi-dushi, ta nan za ka raba. In ka kai ka mike sosai, ina tsammani in ka yi ta tafiya kwana da kwanaki za ka fara shiga cikin dajin Inda abin da ka ke nema ya ke."

Abubakar ya yi masa godiya, sukayi sallama da juna, suka ce, "Allah ya sake gama fuskokin mu." Maharbin ya koma da baya, Abubakar ya wuce. Abubakar ya tafi kwana da kwanaki har ya shige dutsen. Ya yi ta tafiya har yatsammaci ya kai inda aka ce ya soma nema. Sai ya sami wani kogon dutse ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment