Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana masifar dacewa da kai musamman ma idan ka dora farin tabaranka.

Dakta Ali ya yiwa kansa murmushi jikin madubin sannan ya dubi agogo. Tabbas yasan yanzu Aziza na nan tana jiransa. Da farko ya so ya yi mata waya domin ya sanar da ita cewa ga shi nan zuwa, to amma sai yaga gara ya bata mamaki, sai dai kawai taji an ce mata gashi nan ya zo.

Cikin sauri Dakta Aliyu ya dauki jakunkuna guda biyu wadanda ke cike da kyauttuka na musamman domin babbar masoyiyarsa a duniya Aziza. A yammacin da ya gabata ya shafe sama da sa'o'i biyu a cikin kantin (WELL CARE) yana ta yiwa Aziza siyayya, duk abin da ya gani na mace idan yaga ya dace da Aziza sai ya saya, bai fito daga kantin ba har sai da ya batar da kudi sama da dubu sittin da uku. Dakta Aliyu ya zuba sayayyar da ya yi abayan motarsa sannan ya shige ciki ya tuka ya nufi gidan su Aziza.

Karfe tara da 'yan mintuna Dakta Aliyu ya isa layin gidan su Aziza. Dakta Aliyu ya yi mamaki, sa'ar da ya hango taron mutane jingin a kofar gidan su Aziza, duk a zazzaune akan tabarma an kafa musu rumfa, gashi kuma layin cike da motoci tun daga farkonsa har zuwa karshensa, wanan shi ya sa Dakta Aliyu ya yi fakin da motarsa tun daga farkon layin.

Cikin mamaki Dakta Aliyu ya fito daga cikin motarsa ba tare da ya dauko jakunkunan da yazo da su ba. Dakta Ali ya fara tafiya ya nufi kofar gidan a kasa, abu na farko da ya fara zuwa zuciyarsa shine daurin aure ake yi. Yayi mamakin dalilin da yasa Aziza bata fada masa sa'ar da ya yi mata waya a yammacin jiya Ko da Dakta Ali ya fara kusantor inda rumfunan suke sai
yaji gabansa ya fadi ras, domin ya lura duk kusan mutanen dake gurin a zazzaune suke hakanan babu alamar walwala a fuskarsu, babu kuma alamar maroka, hakanan kuma jama'a da dama sai daura alwala suke ta faman yi. Dakta Ali yaji bayan Kwat dinsa ta fara jikewa da gumi, yanzu kam ya tababta a yau dai bashi da damar ganin Aziza, abu na farko da ya fara zuwa zuciyarsa shi ne mahaifinta ne ya rasu Dakta Ali ya dada matsawa gaba yana dube-dube a cikin jama'a yana tunanin wanda ya kamata ya tambaya a dai-dai wanan lokaci ne ya hango wani mutum acan gefe guda zaune akan wani farin vespa. Dakta Ali ya matsa kusa da shi yace.

"Assalamu Alaikum. Mutumin ya amsa sallamar ya juyo ya dubi Dakta Ali. mutumen ya jike sharkaf da hawaye. "Sai dai hakuri, Allah jikansa ya gafarta masa": Dakta Ali yace da shi Mutumin ya juyo ya dubi Dakta Ali ido-da-ido yace.

"Ai ba namiji hane mace ce ta mutu..." Dakta Ali yaji gabansa ya yi muguwar faduwa. Mahaifiyar Aziza ce ta rasu? Allah jikanta yace a ransa, ya tuno da irin mutuncin da ta 'nuna masa a zamanin da yake zuwa gurin Aziza, nan da nan sai yaji hawaye ya cika masa idanu

"Dan... uwanta ne kai". Dakta Ali ya tambayi mutumin. Ga mamakinsa sai yaji mutumin ya fara shsshekar kuka da karfi har jikinsa yana girgiza.

"Masoyiyata ce Wallahi... jiya-jiyan nan nazo tun daga Bauchi saboda ita, sai ma da muka yi hirar yamma da ita muka yi alkawarin zamu hadu yau da safe ina zuwa sai naji ashe Allah ya yi ikonsa.." mutumin ya sake fashewa da kuka. ALLAH YA JIKAN KI AZIZA!" koda jin haka sai Dakta Ali yaji kamar zuciyarsa ta tsage gida biyu, kwakwalwarsa ta fara zagayawa, sannan sai ya sulale a gurin ya sume.

A dai lokacin da jama'a suka yi kan Dakta Ali suna ruwa ruwa sai wata bakar mota baki kirin kirar fijo ta shigo layin. Mutane suka bi motar da kallo domin motar 'yan sanda ce. Alhaji Ibrahim da ke zaune cikin taron jama'a ya ga zuwan motar hakanan shima kamar sauran jama'ar da ke gurin ya yi mamakin ganinta, shi dai a iya tunaninsa bashi da wani aboki dansanda ballantana ace ta'aziya aka zo masa. Bakar motar ta tsaya a gaban rumfunan da jama'a ke zazzaune a ciki. Alhaji Ibrahim ya mike tsaye kana ya nufo inda 'yan sandan suke, tun kafin ya Karaso 'yansanda biyar suka fito daga cikin motar dauke da bindigogi. Alhaji Ibrahim ya matsa kusa da su yace.

"Sannunku da zuwa ince dai ko lafiya?" Wani Insifecta daga cikin 'yan sandan ya dube shi yace.

"Waye me wannan gidan?" Duk jama'a aka yi tsit ana sauraro, wadanda ke alwala ma suka yi tsit suna kallon ikon Allah, Alhaji ya dubesu ya ce. 'Nine maigidan, akwai wani abu ne?" "Yan sandan suka dubi juna kana sai Insifectan ya hade fuska yace.
"Zuwa muka yi mu tafi da 'yarka Aziza, domin ta amsa wasu 'yan tambayoyi, muna zarginta da kashe mai gidanta ta hanyar turoshi daga kan bene hawa uku".

Jama'ar dake zagaye dasu suka rike numfashi cikin kaduwa. Alhaji Ibrahim yaji kamar hakarkarinsa zai tsage, daman tun jiya da aka sanar dashi mutuwar yarsa kwallin kwal a duniya, ya fara jin kamar ana rura masa wuta, dan haka wannan labari da 'yan sandan suka zo da shi, ya gama dauke masa numfashi, tuni ya fara tunanin dama mutuwa ya yi shima ya huta.

"Ko baka ji abin da muka ce bane" dansandan ya bugawa Alhaji Ibrahim tsawa sa'ar da yaga yayi shiru. Alhaji Ibrahim ya dubeshi a fusace yace.

"SAI KU JIRA AYI MATA WANKA A KUMA SATA A LIKKAFANI. IDAN YA SO SAI KU TAFI DA ITA!

ƘARSHE

ALHAMDULILLAHI

ALHAMDULILLAHI

ALHAMDULILLAHI

NAZIR ADAM SALIH (NAS)
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

4 days ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

2 days ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment