Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kada ka sake ta gane cewa ba kaunarta kake yi ba sai ka shirya gobe zata zo.

Fara haduwar su keda wuya sai Tijjani ya fahimci ashe nadiya har tafi amira iya hira toh saidai kuma bata iya kisisina irin na Amira ba.
Tijjani yaje neman shawara gurin babban amininsa Abdul Badon yana son yayi amfani da shawarar ba sai don kada abokin nasa yaji Kwatsam ya yi aure gashi kuma Daman sun sha takun saka akan auren batula da'ace Tijjani ya tsammaci Abdul zai ce suje awon jinin da bai je gurinsa neman shawara ba.

Dakyau na sami mafita wallahi na sami mafita kuje a gwada jinin amira tace dashi cikin murna sa'ar da Tijjani yakawo mata shawarar da abokinsa Abdul yabashi ya dubeta arude.Me kike nufi da muje a gwada jinin?

Haka na nufin bama sai ka aureta ba kenan
Abinda kawai da nake son sakamakon gwanin jinin ya nuna shine kana dauke da cutar kanjamau.

Tijjani ya zabura cikin kaduwa bakinsa na rawa yace wani lokacin fa bakida hankali wayace dake ina dauke da cutar kanjamau?

Amira ta fashe da dariya sannan ta bata rai tace likitan nake so ya bayar da sakamakon ahaka wahalar kawai nasamu sunan likitan zan iya sayen sa.

Menene to hikimar hakan? Tijjani ya tambaya yauwa abinda nake son ka tambayeni kenan to hikimar yin hakan shine na riga na fada ma shashasha ce indai kabi ahankali har kaunar ka ta shiga zuciyar ta duk abinda ka tambaya yi ma zata yi indai ta sami labarin kana dauke da cutar da zaka ce kana son miliyan uku ma tana iya baka ya danganta da irin kaunar daka dasa mata acikin zuciyarta.

Ke amira wannan shiri naki kuwa anya zaiyi aiki?
Mu gwada mu gani ai motsi yafi labewa kace ni nafada ma ka da kuma fa ka manta ƙawata ce kusan kullum sai mun hadu duk abinda zaka tambaya zan zuga ta iya zuga naga ta baka.

Wannan duk wani zance ne daya wuce ayanzu da Tijjani yasa amira agaba cikin tunani gamida yabawa da kwakwalwarta ya riga yagama imani da duk abunda tace domin tuni har naira miliyan guda na hannun su.

Yanzu menene abin yi? Tijjani ya tambayi amira wacce ke kallon tarkacen dake cikin dan tsukakken dakin.
Batace ta baka zuwa gobe ba? Tijjani ya gyada kai.

Yawwa to Abunda nake so da zarar ka kadaice kai da ita saika fashe da kuka agabanta nasan zata gigice hankalinta zai tashi za kuma ta tambaye ka dalilin kukan saikace da ita ka riga ka fadawa mahaifanka halin da ake ciki ka nuna mata cewa mahaifin ka ya hana auren domin wai akwai cutarwa aciki amira ta danyi shiru tana dubansa akwai alamun tunani mai zurfi akan fuskarta.

Nasan tabbas daga karshe zata nemi ta taimaka ma idan tayi hakan wanda kuma na tabbata zata yi din saika sake fashewa da kuka ka nuna mata cewa mahaifin ka yace kabar garin nan ka koma wajen kaninsa dake KADUNA acan zaka ke shan magani.
Amira ta sake yin shiru sannan sai ta matso kusa dashi ta dafa kafadarsa tace...KISAN BOKO-34

Amira ta sake yin shiru sannan sai ta matso kusa dashi ta dafa kafadarsa tace idan kayi haka sai kayi shiru abinka ni zan zugata ta baka dunkulallun kudi akwai wani kerarren gidanta a kaduna zansa ta hada ma har da shi me yiwuwa kuma idan mun dage mu fitar da akalla miliyan hudu adaidai lokacin ne yar mitsitsiyar wayar tafi da gidan ka dake cikin jakarta ta dauki ruri amira ta dauko wayar cikin damuwa.

Hello..
Amira ce?
Eh nice wake magana?
Ibrahim ne
Oh Ibrahim yaya akayi?

Kudin nan da kika bani agaskiya yayi min kadan dubu dari biyar yayi kadan ya sayi sakamakon karyar dana bayar.

Wani zazzafan gumi yafara tsatstsafowa daga kan goshinta Tijjani ya lura da haka kuma yasan lallai akwai matsala shi daman tun farko bai gama amincewa da dogon likitan mai yawan dariya ba to amma tunda amira tace zata iya dashi dole ya amince.

Toh.... Yanzu nawa kake so na kara maka? Amira ta tambaya a tsorace domin tasan likitan shine ran duk wani shirin da take.

Gaskiya ya wuce dan dadi dan inason ki kara kamar yadda kik bani tun farko kinga miliyan daya kenan ahaka nasan ko nine kabarai uban surutu dole nayi shiru da bakina.

Haba... Ibrahim yaya Zakayi min haka bayan mun gama magana da kai ina laifin ma na dada ma dubu dari.

Idan kin amince da abunda nace Shikenan idan kuwa baki amince ba to gara mu daina bata lokacin mu kizo kawai ki karbi kudin ki in yaso daga nan ma sai ki raka ni mu kaiwa kawar ki nadiya sakamakon na gaskiya nasan hakan zai iya kwantar da hankalin ta sai ta nutsu ina fatan kin fahimce ni.

Na fahimce ka... Ka jirani yanzun nan zan kawo ma cikon dubu dari biyar din.

Yawwa yar gari yanzu kika fara zance mai dadi yana gama fadin haka sai ya kashe wayar.

Amira ta kalli gawar wayar dake hannunta jikinta na rawa sannan ta dubi Tijjani a fusace tace.
Kaji ni da tsinannen mutum wai dubu dari biyar yake son mu dada masa shegen kamar yasan Daman miliyan daya ce daidai agurin mu.

Tijjani ya dubeta a tsorace yace yanzu bashi din zakiyi? Amira ta saki wani busashshen murmushi sannan tace a tausashe.
Dole ne mu bashi in har muna so mu rufe bakinsa....amma kada ka damu (my love) zamu farke ne akanta dole ne mu yi kokarin karbar miliyan biyar maimakon hudu.

******* ******* ******* ******* ****** ***********

Kiran yazo mata ne karfe goma sha biyu na dare sabanin yadda tayi tsammani tun farko.
Amira tayi tsammanin tun karfe hudu na yammaci nadiya zata neme ta shiru shiru har bayan goma bata kira ba to amma wannan duk bai damu amira sosai ba domin labarin da Tijjani yazo mata dashi yayi matukar sa ta farin cikin da bata taba shiga Irinsa ba.

Babu wahala ina fashewa da kuka agabanta sai duk ta bi ta kidime toh saidai kuma abunda yabani mamaki banga alamun ta damu sosai ba sai sa'ar danace da ita mahaifina ya hanani na aureta amma tace gobe na koma zata bani abunda har na mutu bazan taba shiga talauci ba domin ta hakane kawai zata ta tabbatar min da irin tsantsar kaunar da takeyi min.

Naira nawa tace zata baka?
Eh to bata fadi hakikanin abunda tace zata bayar ba amma Naji tana cewa ko MILIYAN ASHIRIN TA BANI YA ISHE NI.

Amira ta rike numfashi cikin kaduwa...
Miliyan ashirin Tijjani? Anya kuwa kaji daidai..?

Kwarai kuwa me yiwuwa ma sai yafi haka.
KAI GASKIYA NADIYA TANA KAUNATA.

Amira ta Harare shi tace TAFI NI KAUNAR KA NE?
Kada ka sake fada min haka ta dan yi shiru yanzu yaushe tace ka koma? Tijjani ya dubeta da murmushi yace.
Tace dani nan da sati biyu zata yanke shawarar abunda zata bani takuma ce zata shawarce ki tunda kece dalilin haduwarta dani.

Sati biyu? Tijjani ya gyada kai amma Naji tace wai yau zata neme ki.KISAN BOKO-35

Don haka sa'ar da wayarta ta dauki ruri cikin dare saita dauko sannan ta kashe murya tace
Hello... Nadiya haryansu bakiyi barci ba ina fatan dai lafiya?

Don Allah Amira idan da hali inason ganinki yanzun nan.

Amira ta rike numfashi sannan ta dubi agogon dake makale ajikin bangon tsohon dakin da aka bata agidan su.

Nadiya.... Karfe goma sha biyu n dare fa yanzu.!

Eh na sani wallahi wani abu ne ke damun kwakwalwata ya hanani barci shiyasa nake son ganin ki yanzun nan zan iya turo miki mota don Allah ki lallami mai gidanki nasan bazai hanaki ba tunda dai na fahimci kamar kece mai gidan.
Nadiya tayi dariya sa'ar data fadi hakan.

Banason iskanci... Kin ga ni yanzu ina gida ma mun rabu da mijina.

Nadiya ta rike numfashi acan daya bangaren.. Oh to.... Allah sauwake ashe bazaki sami damar zuwan ba yanzu kenan ko?

Me zai hana shi baba ai ba ruwansa da duk abunda nakeyi mama ce ita kuwa yanzu tayi barci zan iya sulalewa ki turo motar kawai idan yazo saiya danna Hamm.

Mintuna ashirin bayan hakan sai ga amira zaune agaban nadiya cikin hawaye sharaf sharaf tana nuna tausayawar ta ga cutar da ya sami babban masoyin kawarta.

Duk abunda kikayi masa baki fadi ba nadiya.
Amira tace cikin kuka kuma Naji dadi da kika shawarce ni domin yaron nan yana matukar kaunar ki kullum a zancen ki yake akwai lokacin dana ji telolin shagon dinkina na cewa a rana ya kan ambaci sunan ki akalla sau saba'in saikace mai yin salati to amma ko ni bazan baki shawarar ki aure shi ba tunda dai yana dauke da cuta. Don yin hakan kamar kisan kai ne amma Alheri komai yawan sa kina iya yi masa domin ta haka ne zaki iya saka masa kaunar da yayi miki tunda Allah bai kaddara auren ku ba. Amira ta share hawaye.

To ai shi kenan Daman don haka nayi kiranki domin nan da sati biyu zan sallame shi inason aranar ki kasance kina nan tare dani domin ki zama shaida.
Don kece dalilin haduwata dashi. Nadiya ta dan tsagaita sannan saita dubi Amira ido da ido tace.

Yace Kaduna zai koma da zama kina ganin idan na bashi wannan gidan nawa na can da cek din kudi naira miliyan ashirin yayi?

Kadan ya rage amira ta buga tsalle don murna amma maimakon hakan saita fashe da kuka harda majina tana cewa Allah yasaka miki da alkhairi nadiya.
Wallahi da haka ake samun attajirai masu imani kamar ki da talaka bai sha wahala aduniya ba.

Babu komai Nadiya tace a sanyaye AI KIMAR TIJJANI TAFI NAIRA MILIYAN DARI MA AGURINA.

****** ******* ******** ******* ***** ************

ARANAR da za'a karbi cakin din kudin amira ce tafara isa gidan sannan Tijjani yabi ta abaya..KISAN BOKO-36

Babu komai Nadiya tace a sanyaye AI KIMAR TIJJANI TAFI NAIRA MILIYAN DARI MA AGURINA.

****** ******* ******** ******* ***** ************

ARANAR da za'a karbi cakin din kudin amira ce tafara isa gidan sannan Tijjani yabi ta abaya..

Sati biyun da suka gabata. Amira ta kasance ne cikin uzuri domin tuni har tayi cinikin motocin hawa guda biyu takuma shiga kantin kwari ta tambayo kudaden leshi leshi da yadudduka na alfarma masu tsadar gaske duk ta rubuta a takarda bata iya barcin sama da sa'a uku a kowane dare saboda tsabar lissafi da kwakwalwarta keyi kamar kwamfuyuta tana tunanin yadda zasu kashe naira miliyan ashirin idan ta auri Tijjani daga karshe dai ta yanke shawarar da an daura auren su da Tijjani zasu bar Kasar bazasu dawo ba sai sun nutsu.

To saidai kuma ayayinda take fama da lissafe lissafe shi kuwa Tijjani kusan kullun suna tare da Nadiya suna ci gaba d soyayyar su abun su amma cikin damuwa.

Wallahi Tijjani ni nakeyi haryanzu kamar aurenka zanyi tace dashi ran nan da yamma.

Yaya za'a yi saidai hakuri Tijjani yace da ita a tausashe.

Da haka ranar karbar kudin ta riske su. tun karfe goma na safe amira ta isa gidansu nadiya.
Bayan sun gaisa sai amira tace da babbar kawar tata
Haryanzu bai karaso bane? Nadiya ta dubi agogo cikin damuwa.

Nasan yanzu yana kan hanya kinsan har yanzu tunanin masifaffiya cutar nan ne ke damunsa.

Sukayi shiru suna kallon wasan tseren dawakai da akeyi acikin allon fankadediyar talabijin din dake can kusurwar dakin shakatawar.

Karfe goma sha daya daidai saura kwata Tijjani ya karaso gidan sanye da wata kyakkyawar riga ta shadda shudiya wadda yasa ta a karkashin umarnin Amira.

Kazo mata a shiga mai kyau kasan attajiran yanzu sukan kimanta kyautar da zasuyi maka ne da irin kyan kayan dake jikinka kada kuma ka manta da cewa an fa baka naira miliyan daya yakamata taga sauyi ajikinka kada zargi ya darsu azuciyarta amira ce ke cewa da shi haka.

Don haka ayanzu da Tijjani yashigo sai Tijjani ya dubi amira cikin mamaki alamun wai baiyi tsammanin ma zai ganta agurin ba.

Sannu da zuwa Tijjani tun dazun kai muke jira Nadiya tace dashi cikin murmushi

Wallahi kinsan yadda cinkoson motoci yake don ma a mashin nazo Tijjani yace cikin murmushi.

Kai ai maza kuna kokari ma ni Wallahi bazan iya hawa mashin ba ai sai na fado. Gaba dayansu suka fashe da dariya.

Akayi shiru na dan takin lokaci.
Amira bata yarda sun hada idanu da Tijjani ba.

Nadiya ta janyo wata yar karamar jaka fara mai siffar kalangu ta dauko wata takarda mai tsawo da kauri ta daga sama ta kalli takardar kana saita dauko alkalami daga cikin jakar tafara Rubutu ajiki tana gamawa saita Mike tsaye ta nufi inda Tijjani yake ta mika masa takardar cikin murmushi tace.
Kamar yadda nayi ma alkawari ga cakin kudin nan naira miliyan ashirin ne ba yawa kayi hakuri.

Amira taji kirjinta ya harba wani farin ciki mara misaltuwa ya mamayeta kadan ya rage ta taso aguje ta rungume Tijjani don murna amma maimakon hakan saita dago ta dubi nadiya tace.
Allah saka miki da alkhairi.

Ah ba komai wallahi nawa abin yake?

Adaidai lokacin ne to amira ta fahimci lallai wani abu na tafiya b daidai ba domin fuskar Tijjani ya yamutse haka nan cek din naira miliyan ashirin din dake hannunsa bai jefa shi cikin farin ciki ko da daidai da kwayar zarra ba.

Tijjani ya dubi takardar dake hannunsa sannan ya dubi nadiya bakinsa na rawa yace....KISAN BOKO-37

ƘARSHE.....

Tijjani ya dubi takardar dake hannunsa sannan ya dubi nadiya bakinsa na rawa yace....
Ina ganin kamar kinyi kuskure wannan ai katin daurin aure ne kika bani ba cek ba amira taji hanjin cikinta ya yamutse.

Nadiya ta dube shi da tattausan murmushi sannan tace kawo mu gani ta sake tasowa ta karbe katin daga hannunsa ta kalla sannan sai tace.
Kaine dai baka gani sosai gashi nan an rubuta ASHIRIN ajiki ta jefa masa katin akan cinyarsa sannan ta komo ta zauna a binta.

Hannunsa na rawa Yakuma daukar katin ya kalla.
Nadiya wannan katin daurin aure ne da za'a yi ran ashirin ga wata naga kamar sunan ki ne ma ajiki.

Nadiya ta mike tsaye sannan ta dubi amira da wani fatalwan murmushi tace ƙawata amira kiji wani abun mamaki wai mutum dan boko kamar Tijjani yasaka gane cakin kudi na naira miliyan ashirin kacal tana gama fadin haka sai ta karbe katin daga hannun Tijjani ta mikawa Amira.
Duba ki gani amira don Allah ba cek din naira miliyan ashirin bane?

Jikinta na rawa amira ta girgiza kai bata bukatar ta karɓa domin tasan ko kusa ko alama takardar bata yi kama da cekin kudi ba. Nadiya ta dubi amira cikin mamaki.

Au ke ma bazaki iya karantawa ba? Ta rike baki kai amma duk kun bani mamaki wallahi da Alama kunyi asarar kudin Taran ku na makaranta tunda dai bazaku iya karanta cek din naira miliyan ashirin ba ta danyi shiru tana dubansu da murmushi.

Bari to na kirawo angona ya karanta muku tunda kun kasa sannan nadiya saita daga murya tace.
ANGONA fito ka karantawa dakikan nan cek din kudi.

Kofar dakin ta bude sannan yafito dauke da wata katuwar jaka sanye da doguwar riga tazarce tana sheki Awannan karon harda hula to amma farin tabaronsa na nan daraf a saman hancinsa yana fitowa saiya dube su da faffadan murmushi kamar yadda ya saba yace.
Sannun ku da zuwa bayin Allah.
Nadiya ta dube su sannan ta dube shi tace.
Wannan shine mijin da zan aura IBRAHIM

Ibrahim ya gyara tabaronsa sannan ya ajiye jakar agabansa yace da Nadiya.
Ga kudin ki nan da suka karɓa nadawo miki dasu.

Amira taji zuciyarta ta cunkushe wani bakin ciki ya turnuketa nan da nan ta mike tsaye ta dubi Ibrahim tace..
Allah ya isa tsakanina da kai maci amana.

Nadiya ta fashe da dariya tace.
Ai duk cin amanar sa baikai ki ba sannan saita dubi Tijjani tace.

Kaine ka bani mamaki na dauka zaka iya talaucin ka irin ku ne ke hanawa a janyo talaka daga cikin rana.

Tijjani bai iya dago kai ba balle ma ta kalleta.
Nagode wa Allah daya karbi addu'a ta yabani mijin dake kaunata tsakani da Allah wanda kunya ta hana shi ya sanar dani tuntuni har saida tayi dalili.
Wanda ya hakurewa kudi har naira miliyan guda ya kuma ki yarda a hada kai dashi a cuce ni duk saboda kaunata kai Wallahi nayi dace. Tace cikin murmushi.
Sannan taci gaba.
Amira kun dauke ni shashasha ko? baki san cewa ke kin fi ni shashanci ba kin dauka wannan kukan da nake agabanki da gaske nake to bari kiji tun ranar da kika same shi yafada min duk shirin ki ta nuna Ibrahim da hannu.

A daida lokacin ne sukaji motsi abayan su gaba dayansu suka juya.
Don me zaki ajiye mana wayannan maciya amanar haryanzu acikin gida? Mahaifiyar nadiya ce ke maganar ta dubi Tijjani ta girgiza kai
Dube shi lokacin da ya zo gaishe ni kamar waliyi tashi ka fice mana daga gida ka cuci kanka ka yi asara.

Amira ce tafara mikewa ta fice simi simi kamar tunkiya tabar Tijjani anan ya kasa motsi mahaifiyar nadiya ta dubi Ibrahim tace.
Kaci gaba da rike gaskiya Ibrahim kaga aikin ku na likitanci aikine na taimakon al'umma kada ka sake shaidan ya rude ka kayi amfani da aikin ka ka cutar da al'umma abunda kayi ka kyauta Allah saka ma da alkhairi tana gama fadin haka saita juyo ta dubi Tijjani tace
Tashi nace ka fice kar ka kara bata min rai.

Tijjani ya Mike tsaye jiki babu kwari bai kalli kowa ba a dakin sai nadiya bakinsa na rawa yace da ita.
Nasan bazaki yarda da duk wani abu da zan fada ba amma ina son ki sani cewa duk abin nan danayi ba'a son raina bane fin karfina tayi..... Amma ina son don Allah idan zaki iya yafe min koda bayan na tafi ne ya juya ahankali yatafi kamar Kazar da kwai ya fashewa aciki ya fice daga dakin.

Nadiya taji wani zazzafan hawaye ya kwararo akan kumatunta sa'ar da ta ga namijin da tafi kauna fiyeda komai aduniya ya fice daga cikin kundun rayuwar ta.

Ta riga ta sani har yanzun nan tafi kaunarsa akan Ibrahim to saidai kuma tayi imani dacewa Ibrahim yafi kaunarta tsakani da Allah sannan ne to ta tambayi kanta tambaya mai tsada

Shin danayi aure tun ina da kananan shekaru?

Shin da'ace ban zauna ruwan ido ba?

Shin da'ace na auri wancan wanda ke matukar kaunata tun inada kurciyata wannan zata faru gareni?

Shin Zan auri mijin da bana so sai shi yake kaunata?

Ta fadawa kanta cikin kunan rai zazzafan hawayen ya sake kwararowa akan fuskarta.

Sa'ar da ta daga kai sai saita fahimci ashe tuni mahaifiyarta ta fice daga dakin tabar su daga ita sai Ibrahim.

Kukan me kikeyi? Ibrahim ya tambaye yana kallon ta cikin mamaki nadiya ta share hawayen sannan sai ta haske shi da murmushin alkawari tace.

KUKAN FARIN CIKIN NAN DA KWANA ASHIRIN ZAKA ZAMA ANGONA NAKEYI.....

ƘARSHE..............
Nazir Adam Salih.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment