Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi da duka.

Dakata.... Ya isa haka ba sai kin hauni da duka ba nasan karfin tsiya ne dake kamar talauci yanzu me kike so nayi miki?
SO nake ka sakeni ta fada cikin ƙaraji domin a tunanin ta idan batayi masa hauka hauka ba bazai sake ta ba amma ga mamakinta saita ga yayi ajiyar zuciya sannan ya ajiye kwalbar giyar akan teburin gilashin dake tsakar dakin ya dubeta yace.

Kin taimaka min wallahi ni kaina kin ishe ni domin banga amfanin zama da waccce bata kaunata ba ya daga kwalbar giyar ya dubeta gamida yi mata murmushi kai kace rai ne da ita kina ji MY DARLING Wai so....so.....so take yi na sake ta yaya kika gani? Ya tambayi kwalbar giyar.

Bakin ciki ya turnuke amira cikin sauri ta damki kwalarsa ta warce kwalbar daga hannunsa.
Idan baka sake ni ba Wallahi zan fashe ma kai da kwalbar nan ni za kayiwa mayen banza?

Idanun gajeren mutumin suka firfito waje ya dubeta a tsorace akwai wani abu a yanayin fuskarta da ya tabbatar masa da cewa tana iya aikata abunda tace haka nan kuma ya riga yasan ba karamin aikin ta bane ta doke shi domin ta taba jefa masa faranti dauke da abinci mai zafi afuskar sa sa'ar da ta nemi yabata kudi zata bude shagon dinkin yaki kadan ya rage ta makanta shi tun daga lokacin yake tsoranta wannan shiyasa ko zata kai sha biyun dare bata zo gida ba bai isa ya nuna mata bacin ransa ba duk kuwa da cewa yana zargin ta da mu'amala da maza a awaje musamman ma wani saurayi daya taba ganin hotonsa a karkashin matashin kanta.

Sakar ni.... Don Allah ajje kwalbar.... Da kin bi ahankali ma sakin ki zanyi don Nima kin isheni maganar sa ta katse sa'ar da tarin sa yadawo Amira ta yi tsalle gefe guda ta ya tsine fuska cikin kyankyami tsawon lokaci yana tarin sannan saiya dago kai ya dubeta idanunsa na zubar da hawaye kamar kuturu.
JEKI JARABABBIYA NA SAKE KI SAKI UKU 3

Amira tayi ajiyar zuciya tafi nono fari yau Allah ya rabani da dakai tsohon jaraba cikin sauri ta shiga dakinta ta yafo gyale sannan ta dauko jakankunan ta biyu wadanda tun sa'ar da tayi niyyar kashe auren tagama zuba duk suturunta aciki ba'a dade ba sai gata tafito zuwa cikin falon.
Adaidai lokacin ne to ta tuna tayi mantuwa cikin gaggawa ta koma cikin dakin sannan ta dawo dauke da katin hoton da akullum ke boye a karkashin matashin kanta duk abunda take mutumin na kallon ta har sai da yaga zata fita dauke da hoton saiya duheta da wani busashshen murmushi yace

Gurinsa zaki?
Amira ta Harare shi shima zan aura idan mutuwa Zakayi saidai ka mutu ta juya cikin sauri rabe rabe da jakankunan ta biyu dakyar take jansu akasa ta fice.

Mutumin ya fashe da mahaukaciyar dariyar sa sannan saiya dubi kwalbar giyar dake hannunsa yace.
Oh yau Allah ya rabani da bakar jaraba wani zai dauka arashin sani baisan tsumma bace makunshin cuta ya rungume kwalbar giyarsa a kirji sa'ar da Amira ta buga kofar falon da karfi mutumin daya kankame kwalbar giyar kana saiya lumshe idanu yace da kwalbar daga Ni sai ke my Darling Ba'a dade ba yafara Munshaari kamar Rago.

******** ******* ******* ***** ****** ******* *****
Ta bude idanunta ahankali amma bata iya fahimtar komai ba sai dishi dishi taje gani ahankali sai dishi dishin yafara yayewa sannan ne to ta hangi fankar dake wanawa a saman kanta ta muskuta cikin mamaki shin me ya kawo ta nan? Ta tambayi kanta.
Nadiya kin tashi? NADIYA Tajiyo muryar......KISAN BOKO-29

******** ******* ******* ***** ****** ********
Ta bude idanunta ahankali amma bata iya fahimtar komai ba sai dishi dishi take gani ahankali sai dishi dishin yafara yayewa sannan ne to ta hangi fankar dake wanawa a saman kanta ta muskuta cikin mamaki shin me ya kawo ta nan? Ta tambayi kanta.

Nadiya kin tashi? NADIYA Tajiyo muryar mahaifiyar ta a raunane kamar zatayi kuka ta daki dodon kunnenta hakan shi yasa ta dago kai ahankali sannan ne to tayi ido biyu da mutane kusan su shida duk a tsaye akanta daya daga cikinsa kanin mahaifinta ne ALHAJI ABDU saikuma yayar mahaifiyarta ASMA'U akwai kuma dan kanin mahaifinsu SAMIR sauran mutanen kuwa bata san su ba kuma duk mata ne idanunsa cike da kwalla.

Nadiya ta dada mikewa zaune akan gadonta tana kallon su daya bayan daya tana mamakin abinda yakawo ta gadon asibiti idanunta suka kai kan Samir sai gabanta yafadi domin tsayuwar karan hancinsa daya yake dana masoyin ta Tijjani nan da nan sai abubuwan da suka faru suka barko aguje zuwa cikin kwakwalwarta cikin sauri ta koma ta kwanta sannan ta lumshe idanu ta cije baki ji take kamar zata yi ihu kamar kuma ta fashe da kuka kokuwa dariya zatayi ba gaskiya bane ta fadawa kanta don haka saita dada lumshe idanunta tana mai addu'ar Allah yasa kawai ta farka taga duk abubuwan dake zuwa zuciyarta wani mummunan mafarki ne kawai kwarai kuwa ta dada tabbatarwa da kanta mafarki nakeyi.

Nadiya..... Bude idanun ki don Allah kada ki mutu ki bar ni muryar mahaifiyarta ta dada dukan dodon kunnenta na shiga uku... Na shiga uku tace cikin zuciyarta. Ba mafarki ba nake yi gaskiya ne tabbas gaskiya ne mutumin dana fi kauna fiyeda komai a doron kasa na dauke da muguwar cutar nan ta KANJAMAU nan da nan sai wani zazzafan hawaye ya subuce yafara zuba akan fuskarta ta mike zaune ta dubi jama'ar daga zagaye da gadon asibitin cikin sauri mahaifiyarta ta matso ta zauna kusa da ita ta dafa kafadarta tace.

Nadiya kin daina jin ciwon komai?
Hawaye ya dada kwarara akan fuskarta ta dubi mahaifiyarta bakinta na rawa tace.
INA TIJJANI?

Mutanen dake dakin suka dubi juna cikin gaggawa musamman ma wadanda suka san tsakanin ta da Tijjani yanzu ne suka fara fahimtar dalilin Faduwar ta a sume abunda suka sani kawai shine ta shigo gida aguje tana kuka sannan ta fadi a shide ta sume idan ka dauke wannan babu wanda yasan dalilin suman sai ita nadiyar dake zaune ayanzu faifan majigin zuciyarta na kokarin yi mata tariyar baya na abubuwan da suka faru.

Karya kake Wallahi Ibrahim bazai yiwu ba ace Yana dauke da cutar kanjamau kaidai kawai kace baka san....aikin ka ba malam.

Ibrahim ya gyara tabaronsa batareda ya dube ta ba yace.
Saidai hakuri ranki ya dade kuma bai kyautu ki tayar da hankalin ki ba ke kanki likita ce bai kyautu ki tayar da hankalin ki ba sanin kanki ne don mutum ya kamu da wannan cuta ba wai yazo karshen rayuwarsa ba kenan... Kuma... Ta katse shi ta hanyar daga masa hannu sannan ta dubi Tijjani wanda ke Tsaye yayi mutuwar tsohuwa goshin sa sai tsatstsafo gumi yake tunda likitan yafadi sakamakon bai iya hada idanu da shi ba.

Wannan mutumin da kake gani nadiya tace tana duban Tijjani cikin hawaye shine mijin da zan aura to wane irin kwantar da hankalin ki kake so nayi iye?
Ta sake fashewa da kuka sannan ne to Tijjani yayi abinda yasa ta kaduwa ga mamakinta sai taga Tijjani yayi ajiyar zuciya sannan saiya dubeta yace bakinsa na rawa.

Kiyi hakuri nadiya... Kaddara ta raba aurena dake yana gama fadin haka sai ya warce takardar sakamakon daga hannun likitan ya keta ta guda takwas ya watsar sannan ya fice daga ofishin cikin sauri.

Tijjani nadiya ta kirashi cikin kaduwa bai ko juya ba balle ya kalleta.
Ibrahim da nadiya suka dubi juna dakin yayi wani irin tsit na wucin gadi sannan sai nadiya ta dago kai ta dube shi fuskarta sharaf sharaf da hawaye tace a tausashe.
Kayi hakuri... Da maganar dana fada wallahi tsananin kaduwa ce Ibrahim ya gyada mata kai cikin fahimta nadiya ta fice aguje daga dakin tana kuka tariga tasan duk asibitin basuda kwararren mai gwajin jini kamar Ibrahim tunda yake bai taba aiki yazo da kuskure ba.

Nadiya batasan yadda akayi ta iso gida lafiya ba ita dai kawai abunda zata iya tunawa shine ta shigo dakin shakatawar ta sami mahaifiyar ta zaune da wasu yan uwanta daga nan bata kara ganin komai ba sai duhu da wasu kananan taurari da suka yanyame kwakwalwarta.

Don haka ganinta a asibiti shiyasa ta fara tunanin me yiwuwa sumewa tayi wannan duk wani abu ne daya wuce ta fadawa kanta sa'ar da ta share hawaye amma ayanzu abunda yafi damunta shine awane hali Tijjani yake ciki?

Ina Tijjani? ta sake tambayar mahaifiyar ta a razane domin gani take kamar za'a ce da ita cutar har ta kashe Tijjani.

Koma kan gadon ki zauna kada ki fadi kanin mahaifinta ALHAJI ABDU yace sa'ar dayaga ta sauko daga kan gadon tana kokarin fita daga dakin.

Wai wane Tijjani ne take tambaya? Wata mace daga cikin matan ta tambaya tana duban mahaifiyarta.

Wanda take son aura ne.

Ni don Allah ku bar ni na fita gurinsa zani.....
Nadiya tace cikin kuka mahaifiyarta dake zaune akan gadon ta kamo hannunta ta zaunar da ita a bakin gadon tace cikin rarraunar murya..

Kwantar da hankalin ki yanzu zamu koma gida tunda kin farfado bari likita yazo ta danyi shiru tana duban fuskar yarta abar da tafi kauna fiyeda komai aduniya hannayen ta akan kafadarta.

Nadiya ta girgiza kai cikin sauri
Babu abinda ke damuna mama ta sake fashewa da kuka mutanen dake dakin suka sake kallon juna akaro na biyu cikin mamaki.....

******* ****** ******* ****** ****** ***** *******

Assalamu Alaikum. Sassanyar muryar ta daki dodon kunnensa Tijjani ya zabura arude kadan ya rage ya buge kai ajikin tsohuwar kofar dakin.
Ga irinta nan Ai daman saida na fada miki dan me zaki zo har gida? Tijjani yace yana duban daya matar dake gabansa a gigice.

Salamun Alaikum Tijjani muryar ta sake fadi.
Matar dake tsaye agaban Tijjani ya rike numfashinta a tsorace domin jin muryar mai sallamar adaf da kofar dakin adaidai lokacin ne wata basira fado mata cikin sauri gudu gudu sai ta fada dakin dake fuskantar dan kankanin falon zuciyar sa na bugawa Tijjani ya janyo kofar dakin ya rufe ta aciki sannan cikin hanzari sai ya shake murya yace.
Amin Wa'Alaikumussalam baya bukatar tambayar ko wanene mai sallamar domin ya riga yasan muryar Daman kuma ya tsammaci haka tun farkoKISAN BOKO-30

Salamun Alaikum Tijjani muryar ta sake fadi.
Matar dake tsaye agaban Tijjani ya rike numfashinta a tsorace domin jin muryar mai sallamar adaf da kofar dakin adaidai lokacin ne wata basira fado mata cikin sauri gudu gudu sai ta fada dakin dake fuskantar dan kankanin falon zuciyar sa na bugawa Tijjani ya janyo kofar dakin ya rufe ta aciki sannan cikin hanzari sai ya shake murya yace.

Amin Wa'Alaikumussalam baya bukatar tambayar ko wanene mai sallamar domin ya riga yasan muryar Daman kuma ya tsammaci haka tun farko

Jikinsa na rawa kamar mazari yafita zuwa farfajiyar gidan fitar sa keda wuya suka yi ido biyu da ita tsaye tana duban kofar dakin hawaye na zuba akan kumatun ta sanye take da riga da siket launin rawaya da dishi dishin wani dan siririn gyale kafi babu mai kamar rawani shara shara yana iya hangen gashin kanta ta cikin gyalen akafadarta akwai jaka baka kafarta sanye cikin wani takalmi mai tsayi da tsinin baki kamar na tsereren kankara hakanan Tijjani ya lura idanunta sun kukkumbura sunyi luhu luhu da alama taci uban kuka dakuma rashin barci isashshe sukayi Carko Carko suna duban juna kamar zakaru wani abu yafado masa a zuciya nan da nan ya matso hawaye daga cikin idanunsa hawayen yayi sartu akan kumatunsa.

Tijjani takira sunansa cikin karyayyiyar murya.
Nadiya.... Sannu da zuwa nadiya ta dubi tarkacen tsakar gidan nan dan lokaci sannan ta dawo da dubanta izuwa kan fuskar Tijjani.

Kiyi hakuri nadiya kinga yadda....
Kada ka bani hakuri wannan abu na iya fadawa akan kowa ta danyi shiru sannan sai tace cikin wata murya mai dauke da kakkarfan amo.

Daman zuwa nayi nafada ma cewa haryanzu ina nan akan bakana Tijjani ya dubeta a rude.
Ban fahimci abunda kike nufi ba nadiya ta gyara tsayuwa kana ta goge hawaye ta dube shi ido da ido tace.

Ina nufin zan iya aurenka duk kuwa da cewa kana dauke da cutar kanjamau ajikinkaKISAN BOKO-31

Daman zuwa nayi nafada ma cewa haryanzu ina nan akan bakana Tijjani ya dubeta a rude.
Ban fahimci abunda kike nufi ba nadiya ta gyara tsayuwa kana ta goge hawaye ta dube shi ido da ido tace.

Ina nufin zan iya aurenka duk kuwa da cewa kana dauke da cutar kanjamau ajikinka.

Har ga Allah maganarta ta sa shi tsananin kaduwa ashe haka take kaunata ya tambayi kansa a zuciyarsa tabbas ayanzu ya tabbatar matar Dake tsaye agaban sa mai kaunar sa ce ta gaskiya abin ya narka masa zuciya.

Bazai yiwu ba Tijjani yace da ita yana girgiza kai.
Ki hakura dani ki bar ni da cutata bazan iya aurenki ba na dora miki wahala tun da ke lafiyar ki Ƙalau.

Nadiya ta girgiza kai cikin kuka
Gara cutar dake jikin ka ta kashe ni da ace rashin ka ya kashe ni hawaye yafara sartu babu kakkautawa.

Tijjani yaji kwakwalwarsa tafara hargitsewa al'amarin yafara wuce tunanin sa ya dubi kofar dakin a tsorace sannan ya dubeta yace a tausashe.
Nadiya inason ki bani zuwa gobe zanyi tunani sanin kanki ne nayi nufin auren ki to amma tsananin kaunar danake miki bazai bari na aure ki ba alhali ina dauke da wannan cutar.

Nadiya ta sake fashewa da kuka zan baka zuwa gobe kayi tunani nidai wallahi da begen ka ya kashe ni gara cutar Tayi ajalina.

Tijjani bai iya hada idanu da ita ba sai ya nufi kofar gidan ganin haka sai nadiya ta bishi abaya sa'ar sauya lallabata ta shige cikin motarta sai ta dube shi tace.

Zan zo goben Tijjani ya girgiza kai cikin sauri A'a ki bari zan zo na same ki har gida.

Nadiya ta dube shi cikin tausayi sannan ta dafa hannunsa babu inda ke ma ciwo? Tijjani ya girgiza kai yace Haba dai tun yanzu ai ko zan mutu zan dauki shekaru kafin na mutu.

Yauwwa Tijjanina haka nake son ji kana fada da haka suka rabu.

Cikin rauni Tijjani yadawo farfajiyar gidan ya wuce kai tsaye zuwa cikin tsukakken falon sannan saiya kwankwasa kofar yace cikin dariya.
Fito ta tafi.

Kofar dakin ta bude ahankali sannan ta fito itama tana dariya.
Kai Tijjani wallahi na dade banga kwararren makaryaci kamar ka ba

Au ashe kina jin mu?
Inajin ku mana ai kunnena na kara ajikin kofar inajin muryar ka kama zaka fashe da kuka.

Tijjani ya fashe da dariya har da buga kafa akasa kai lallai shashasha ce kamar kamar yadda kika fada min tun farko kiji fa wai ta amince zata aureni da cutar.

Ai daman nafada maka idan tana son abu shashasha ce tana iya yin komai. Ta danyi shiru tana dubansa sannan saita hade fuska tace
Saida kuma tayi abanza dan babu mai aure min kai Tijjani.

Tijjani yayi ajiyar zuciya ya dubeta cikin damuwa yace
ZAUNA MUYI ZANCE A NUTSE AMIRA.

***** ******* ****** ******* ******* ****** *******

Tijjani ya kurawa amira idanu yana mai mamakin kwakwalwa irin nata tuni har naira miliyan guda tashigo hannunsu duk saboda kwakwalwarta kuma Allah ne kawai yasan nawa zasu karɓa daga hannun shashashar matar da farko Sa'ar data fara zuwa masa da dabarar yayi zaton mahaukaciya ce.

Haba amira yaya kike magana kamar karamar yarinya wannan zance ne irin na littattafan hausa.

Amira ta dube shi da murmushi tace.
Kai kake ganin haka ai ko labarin litattafan hausan nake baka ya kyatu ka saurare ni domin suna faruwa da gaske balle ma wannan a zahiri ne zaka gani kaidai kawai so nake ka amince din idan zaka aure ta...KISAN BOKO-32

Amira ta dube shi da murmushi tace.
Kai kake ganin haka ai ko labarin litattafan hausan nake baka ya kyatu ka saurare ni domin suna faruwa da gaske balle ma wannan a zahiri ne zaka gani kaidai kawai so nake ka amince din idan zaka aure ta.

Tabbas yafara ganin abun da take nufi domin gashi har naira miliyan daya tafara shigowa wannan al'amari ya kara masa karfi duk kuwa da cewa tuni amira ta karbe miliyan dayan daga hannunsa.

Wannan mata mai dimbin tunanin samun sulalla daga zaune agabansa bazai taba mantawa da ranar da suka fara haduwa acikin dan akurkin dayake aikin tela ba.

Kai nake son na gani tace dashi kai tsaye kuma a tausashe sa'ar data shigo dan dakin kafadarta rataye da shudiyar jaka Tijjani ya dubi matar dake tsaye a kansa cikin mamaki domin tace shi take son gani kuma shi bai ga alamu alamun tana dauke da wani yadi ko atamfa ba ballantana yace ko dinki ta kawo.

Inafatan dai lafiya?

Sumul tace dashi cikin murmushi na hakika Tijjani yaji haka kawai ransa yayi fari akaro na farko tun da garin Allah ya waye domin a washegarin wannan ranar kwana sukayi suna fada da matarsa Batula
Suka fita kofar mitsitsin shagon sannan suka fuskanci juna cikin murmushi bakuwar matar ta dube shi tace.
Sunana Amira.

Toh... Sannu da zuwa Tijjani yace yana dubanta cikin mamaki.

Ku nawa ne kuke aiki anan? Tijjani ya nuna shagon da hannu
Mu biyu ne dani da mai shagon amma baya nan yayi tafiya.

Kuna samun dinkuna kuwa sosai anan? Tijjani ya dada dubanta cikin mamaki sannan ya kadai kai.
Eh mu kan dan samu jifa jifa amma idan zamu sami kari daga gurin ki ba zamu ki kari ba.

Amira ta gyara tsauwa kana tace
Wani abu Nazo maka dashi me kama da haka.
To saidai kuma ba aiki na kawo ba so nake idan ka amince kadawo shagona dana bude kana iya dinkin acan muna da manyan kwastomomi acikinsu harda matan masu mulki da sarakuna kuma abunda zaka samu a sati guda acan yafi na wata guda anan musamman ma dayake kai kwararrene don na Samu labarin ka ta saki wata kankanuwar dariya amma sai kana da ra'ayi idan baka so kana iya zaman ka anan.

Dayake tuni Daman Tijjani yagama gajiya da gorin arziki da matarsa batula keyi masa kullum kamar karatu ba'a fi sati guda ba suka fara aiki a shagon dinkin amira daga shi har uban gidan nasa.

Tun daga ranar tafara bauta masa takuma fara kaunar sa domin tafi jin dadin hira dashi fiyeda mijinta dan giya wanda bashida aiki sai shegen tari da zubar da yawu wannan ita tasa dayawa saita daidaici lokacin tashin su daga rumfar yayi sai amira tazo ta hilace shi suyi ta hira sai su raba dare Tijjani bai taba sanin tanada aure ba domin bai taba ganinta da mijinta ba haka nan batada kamun kai bakuma ta yin lullubi akwai sa'ar da zata sako riga da wando ta yafo dan gyale abunta kai ka dauka wata yar karamar budurwa ce itama marar tarbiyya sannu ahankali sai amira tafara shiga ransa ba don komai ba sai don abu uku.

Na Farko dai itace cin sa itace shan sa kai har kyautar shaddodi take bashi ya dinkawa kansa gata da iya hira da kwarkwasa ta taba cewa dashi watarana suna hira.
Rufe idanunka yana rufewa saiya ji cu cu.

Tun kafin ya bude idanunsa yaji kamshin turare ya bugi hancinsa.
Nafi son kayi ta yin kamshi my love tace tana jujjuya idanu.

Irin wadannan dabi'u su suke burge shi gashi dai ta girmewa matarsa batula nesa ga kusa ba amma saboda tsabar masifar matarsa saiyaji zuciyar sa ta karkata ga kaunar amira sannu ahankali har amira ta gama shanye zuciyarsa ta hanyar kyauta tarairaya kissa da kuma bin malaman tsibbu.
Wani malami yabata cewa da ita Tijjani bazai taba iya Rabuwa da ita ba koda kuwa ya hadu da wacce tafita komai da komai.

Ana cikin haka ne to ran nan da magariba sai ga amira cikin sauri ta shigo shagon.

Idan kun tashi ka jirani zan dawo... Ina son Magana dakai amira tace dashi cikin rada sannan saita faki idanun sauran Madinkan ta watsa masa alewar Cakulat kwaya biyar akan cinyarsa ta fice abunta abin da bata sani ba shine a shagon babu wanda baisan akwai kullin boye tsakanita da Tijjani ba.

Suka dubi juna sa'ar data dawo su kadai ne a shagon duk sauran Madinkan sun tafi gida Tijjani ya lura da cewa amira ta sauya kayan dake jikinta kuma ta sake kwalliya sai kamshin turare ne ke tashi daga jikinta ya tuna da matar sa wacce ke gida kaca kaca cikin kazanta sai masifa.

Tijjani kasan dai ina masifar kaunarka ko?
Tijjani ya gyada kai cikin mamaki.

Kuma nasan kaima kana kaunata ko? Tijjani ya dada gyada mata kai cikin sauri yana dubanta.
To amma kasan abunda yasa ban taba neman ka aure ni ba.? Tijjani ya girgiza kai
Abubuwa biyu ne suka hanani Tijjani ya muskuta cikin damuwa yace da ita.

Wadanne abubuwa ne? Amira ta sunkuyar dakai tana wasa da wani zoben daham dake dan yatsanta.

Bazan fada maka ba sai in har ka fada min da bakin ka cewa zaka aure ni.....KISAN BOKO-33

Wadanne abubuwa ne? Amira ta sunkuyar dakai tana wasa da wani zoben daham dake dan yatsanta.

Bazan fada maka ba sai in har ka fada min da bakin ka cewa zaka aure ni.

Haba amira Tijjani yace cikin damuwa ke kin sani ko ban fada ba alamu sun nuna zan iya auren ki indai har zaki amince... Kece farin cikina amira don matata ta bata da aiki sai masifa sai nazo nan kike faranta min amira ta gyada kai cikin gamsuwa kana ta dube shi tace.

Matar ka itace abu na farko data hanani neman ka aure ni.. Nasan kai kanka ta isheka..... Zaka iya sakin ta ka aure ni?

Tijjani ya sunkuyar da kai cikin damuwa.
Nasan abunda kake tunani masifarta kake tsoro ko?
To bari kaji da zaka zage rana guda idan tayi ma kaima kayi mata in da hali ka sharara mata mari babu abunda zai hana tayi yaji tunda bazata tsammaci duka daga gareka ba tana yin haka saika bi ta da takardar saki.... Zaka iya yin hakan?

Tijjani ya yi ajiyar zuciya sannan ya gyada kai yace zan gwada.

Amira ta danyi shiru sannan ta dago kai.
Abu na biyu danake tsoro idan na aure ka shine TALAUCI kai kanka ka isa shaida kaji kamshin irin turaren danake fesawa kana kuma jin kamshin irin maye mayen danake shafawa ka dubi sarkar dake wuyana ka kuma kiyasta tsadar takalmin dake kafata haka nan zanso ka nazarci irin suturun da nake sawa zaka san lallai hatsari ne na aure ka cikin talauci.

Tijjani ya daga hannu cikin kaduwa sannan ya dawo da hannayen ahankali ya ajiye su abisa cinyar sa ya dubeta.
Ya to na iya da raina... Haka Allah ya yi ni talaka.

Amira ta kalli fuskarsa da wani busahshen murmushi ta lura da cewa a tsorace yake don ya dauka bazata aure shi ba tabbas malamin nan yafadi gaskiya ta fadawa kanta sannan sai tace dashi.
Kada ka damu akwai mafita in har zaka amince ka auri babbar ƙawata wai ita NADIYA.

Asannan ne to Tijjani yace da ita cikin kaduwa bazai yiwu ba.
Me zai hana? Amira ta tambaye shi.
Abun kawai danake bukata shine kace zaka aureta miloniya ce kuma shashasha ce marar wayo idan tana son abu zata iya kashe ko nawa ne a kansa nasan halin ta tun muna makaranta.

Tijjani ya dubeta a rude Ni kam haryanzu ban fahimce ki ba amira kina nufin wai na aureku ku biyu?

Amira ta girgiza kai cikin sauri
Ita kadai zaka aura duk abinda kace kana so zatayi ma ayanzu haka tanada milyoyin naira a banki wanda ta gada daga wurin mahaifinta batasan me zatayi dasu ba mun sha yin zancen da ita ta dan yi shiru tana nazarin fuskarsa na dan lokaci.
Shashasha ce daka aure ta zata mika komai da komai ahannunka zan barku ka zauna da ita na shekara guda duk kuwa da cewa hakan shi na fi tsana fiyeda komai aduniya to amma nasan a shekara daya ka kwashi rabon ka daga nan kana iya sakinta kadawo gareni muyi zaman mu cikin nutsuwa ina fatan ka fahimce ni.

Tijjani ya gyada kai babu musu can kuma sai yace kince matar aminiyar ki ce kuma kin ce na sake ta zaki aure ni kina jin zaki iya hakan?
Amira ta fashe da dariya Tijjani kenan ai ba'ayi namiji dan mace daya ba ni dai kawai abinda nake son kace shine zaka aure ta?

Sauran bayanin kuma saika aureta zan shirya yadda za'a yi. ta matso daf da shi tana huci a fuskar sa kamshin jikinta na dukan hancin sa Tijjani ya dubeta a kidime cikin rashin tabbas yace na Amince.

Amira ta jefe shi da wani tattausan murmushi sannan tace daga yau bazamu sake haduwa da juna afili ba sai a sirri haka nan kuma inason kayi duk abinda Zakayi ta amince dakai

Please Login or Register in order to submit comment