Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sakin matarsa batula ba dakuma shirye shiryen dayake na auren NADIYA MILONIYA har sa'ar da ya durkusa gaban mahaifan nasa ya gaishesu zuciyar sa na ta wasi wasin ta inda zai fara domin abubuwa dayawa sun faru cikin sa'o'i takwas din da suka gabata.

Tun karfe uku na dare yaji idanunsa sun bude sannan sai fargaba da taraddadi suka cafki zuciyar sa kamar yadda shaho kan cafki bainu domin baisan irin sakamakon da gwajin jinin zaizo dashi ba wannan duk zargine da tone tonen magana irin na Abdul Tijjani yace da kansa cikin talaitainin daren tabbas nadiya lafiyar ta garau babu wata cuta dake damunta bayan ga fuskarta nan garau jikinta da kuzari yaya Abdul zaiyi zargin tana dauke da kwayar cutar kanjamau in ba neman magana ba ko shakka babu dan kawai Abdul bai taba ganin nadiya a fili bane shiyasa yake wannan zargin amma shi kam ya tabbata nadiya lafiyar ta Ƙalau saidai kuma duk wannan kabli da ba'adin dake kai kawo basu iya tausasa tsananin fargabar dake kai kawo cikin zuciyarsa ba shin yanzu idan sakamakon gwajin jinin ya nuna nadiya na dauke da cutar kanjamau zan iya auren ta kuwa? Tijjani ya tambayi kansa sannan cikin gaggawa ya kawar da wannan tunanin daga faifan zuciyarsa.

Ahaka yana ta haure haure da juye juye kamar kifi a koma har aka fara kiran sallar farko na asuba.
Tun karfe shida da rabi yayi wanka sannan karfe goma saura minti uku yana farfajiyar asibitin anan ya sami nadiya zaune cikin motar ta agurin fakin din motoci tana jiran sa wannan shi ya tabbatar masa da cewa ko ofishin ta bata shiga ba.

Muje ko? tace dashi da dan murmushi sa'ar data fito daga cikin motar ta rufe yabi ta abaya zugum zugum kamar tunkiya har suka shiga dakin gwajin.

Sannun ku da zuwa ranki ya dade wani dogon saurayi baki siriri mai yawan fara'a da kyakkyawar fuska yace dasu.

Nadiya ta dube shi a gaggauce tace.
Mun zo ne akan maganar dana fada maka jiya awaya. Jinin mu za'a gwada tana fadin haka saita juyo ta dubi Tijjani wanda ke gefe kusan duk a tsorace tunda yake ba'a taba daukar jininsa ba.
Saki jikin ka jarumin maza ba yanka ka za'ayi ba gaba dayansu suka fashe da dariya.

Anfada miki tsoro nakeji?

Bawani tsoro kakeji mana ba gashi nan har kafara gumin goshi ba.

Tunda tace tsoro kakeji bari na fara ta kan ka Ibrahim yace cikin dariya.

Ba'a dauki sama da mintuna goma ba aka dauki jinin.

Yaushe zamu samu sakamakon Tijjani ya tambaya sa'ar da suka fito farfajiyar asibitin.
Nan da kwana uku nadiya tace a tausashe akwai wani boyayyen murmushi na farin cikin kasancewa tareda shi sukayi shiru na dan lokaci cirko cirko suna duban juna.

Zamu bari sai mun sami sakamakon ko kuwa muna iya zuwa fara shirye shiryen bikin gobe?

Tijjani ya zura hannayensa cikin aljihu kansa a sunkuye akwai alamun tunani karara akan fuskarsa.
Da dan tani ne muna iya fara shiri yanzu ma yafada yana dubanta ido da ido da tattausan murmushi. Hakan shiyasa nadiya taji kunya ta dan kamata cikin sauri ta sunkuyar dakai tana murmushi.

To amma kinga ai maganar aure bata yiwuwa har sai an fara sanar da mahaifa ko?

Nadiya ta dago kai cikin gaggawa ta dube shi au Daman basu ma taba sanin da zamana ba? Ai ni na dauka tuntuni kafada musu LABARINA.

Kada ki damu yau din nan zan sanar dasu in Allah ya so.
Ahaka hirar tasu ta kare a farfajiyar asibitin kafin su rabu saida nadiya tayi kokarin rage masa hanya.
Kedai bakya rabuwa da dorawa kai wahala nan da gurin aikin ma sai kin kaini...me yasa kike son shagwabani ne?

Saboda banida wani abun shagwabawa aduniya saikai.

Da haka suka rabu bai zame ko ina ba sai gidan surukansa karfe sha daya saura kwata na rana ya isa kofar gidan abayan dan acaba.

Kai wannan layi da yawan kaji yake saikace gidan sarkin ruga dan acabar ne ke fadi adaidai lokacin da Tijjani ke kokarin mika masa takardar naira hamsin.

Anyi sa'a ma da yake ba agwagwi bane da sai ranka ya baci saboda kazantar su Tijjani tace Adaidai lokacin da wani ramammen zakara me gwagwiyayiyar kai kamar kan ungulu ya kawowa wani kuda dake kan kafarsa cafka kudan ya tashi zakaran ta caki kafar Tijjani cikin sauri ya janye kafarsa dan acabar ya fashe da dariya.

Ka godewa Allah dayasa zakara bai kai girman mutum ba amma ina tabbatar maka da cewa da ya kai girman mutum hadiyeka zaiyi dan masu kiwon su ba basu abinci suke ba....KISAN BOKO-24

Na yarda dakai dan samari Tijjani yace da dan acabar gamida ajiyar zuciya sannan ya dubi inda zakaran ya cake shi fatar har ta daga.

To Allah kyauta dan acabar yace sannan ya fizgi mashin din aguje kamar zai tashi sama kajin dake tsakiyar layin suka watse aguje amma duk da hakan bai hana dan acabar Takewa wata bushashshiyar kaza kafa ba.

Tijjani ya nufi kofar gidan surukansa hannayensa cikin aljihu yana zuwa sai yayi sallama ba'a dade ba sai ga wani yaro mai dogon kai kamar shantu yafito aguje.
Yaya Tijjani wai ance kashigo Tijjani yabi yaron da boyayyen murmushi baiyi mamakin gane muryarsa da akayi cikin gaggawa ba wannan shi ya dada tabbatar masa da cewa an dade ana sa ran zai biyo bayan matar sa Batula
Sannu ahankali ya durkusa agaban HAJIYA HABI. mahaifiyar batula ya gaishe ta cikin ladabi.

Alhajin baya nan ne? Tijjani ya tambaya ganin cewa tun bayan da suka gama gaisawar mahaifiyar batula bata kuma cewa dashi kala ba sai ma hararar sa da takeyi.

Me Zakayi masa idan yana nan iye? Dan wulakanci ko yanzun ma biyo ta kayi har gida ka jibge ta ka jibgi mahaifanta. Toh karya kake Matsiyaci kurwarta kurrr naci na sha ba domin ka ba Wallahi karya kake.

Kan Tijjani a sunkuye bai dago ba balle ma ya kalli masifaffiyar fuskar ta saida ya bari tagama sai ya dago kai ahankali yace a tausashe.
Allah huci zuciyar ki mama ni banzo da niyyar ci muku mutunci ko wulakanci ba.... Idan da hali so nake na gana da ita.

Dawa zaka gana? Da yarinyar da ka kusan kashewa... To bari kaji wallahi bazata kara komawa wannan kangon daka jefa ta aciki ba.

Tijjani yaji zuciyarsa kamar zata fashe kirjinsa ya fado tsakar dakin gidan amma duk da hakan saiya hadiye.
Adaidai lokacin ne Tijjani ya daga kai kansa ga mamakinsa saiya hango batula akofaar dakin dake fuskantar sa idanunta cike da hawaye tana kallonsa bata ko kiftawa.

Kiyi hakuri mama ki kwantar da hankalinki ba zuwa nayi na tafi da ita ba so dai nake na gana da MATATA.

Matar ta Harare shi Anji matar ka ce amma kasan ni na tsugunna na haifeta ko? To bazata koma cikin bakar wahala ba ta mike tsaye kana ta nuna shi da dan yatsa tace.
Gata nan a daki shiga ku gana amma ita da kofar gidan ka koda hanya.
Tana gama fadin haka saita zari buta cikin sauri ta nufi bandaki.

Tijjani ya Mike tsaye ahankali jiki na rawa kamar mazari ya nufi dakin da ya hangi batula tsaye yana shiga dakin saita fashe da kuka.

Don Allah Tijjani kayi hakuri.... Nasan laifina ne duk ni na janyo maka wannan cin mutuncin....
Muryarta ta shake taci gaba da kuka.

Tijjani yayi sororo yana kallon ta cikin mamaki domin ya dauka da ya shiga itama zata hau shi da sabuwar masifar kamar yadda ta saba.

Tsawon lokaci yana tsaye tana kuka yana nazarinta hannayensa cikin aljihu.

Wannan itace matar da ke kuntatawa rayuwarsa.

Wannan itace matar da kullum Saita muzanta shi.

Ta raina masa arziki.

Wannan itace matar dake da karfin zuciyar da har zata hada kayansa ta ƙone su kurmus.

Wannan itace matar dake da tsabar rashin kunyar da zata buda baki ta zagi mahaifansa.

Tijjani ya girgiza kai sannan saiya dube ta a tausashe yace.

Batula Daman zuwa nayi mu gana akan wani babban batu.

Batula ta share hawaye ta dube shi
Wace magana ce... Kayi hakuri don Allah tace cikin shishshikar kuka.

Daman zuwa nayi na sanar dake cewar
ZAN SAKE AURE.!!

Idanun batula suka firfito waje cikin tsananin Kaduwa.
KADA KAYI MIN HAKA TIJJANI tace cikin kuka.

Me nayi miki? Keda kikace kin tsane ni kin tsani sama dani?

Ya lalubi aljihunsa ya zaro wata farar takarda ya jefa mata sannan yace.
Idan an buga katin gayyata zan aiko miki amma kafin nan zan so ki karanta wannan takardar.... Na SAKE KI SAKI DAYA.

Cikin sauri ya fice daga dakin sannan ya fice daga gidan.KISAN BOKO-25

Cikin sauri ya fice daga dakin sannan ya fice daga gidan.

Har zuwa wannan lokacin da Tijjani ke gaban mahaifansa yana basu labarin dalilin sakin matarsa Tijjani na iya jin sautin kururuwar batula sa'ar daya fice daga gidan.

Tsawon mintuna mahaifansa na dubansa cikin kaduwa da jin wannan labari mahaifinsa ne yafara magana
To Daman ai saida na fadama ka rabu da yarinyar nan yar mace ce sai abunda mahaifiyarta tace shi ake yi agidan.... Amma taurin kanku na yaran zamani ka kafe ka turje kace sai kayi to yanzu menene amfanin irin wannan anyi auren ko cikakkiyar shekara ba'a yi ba har an rabu?

Tijjani dai bai ce komai ba kansa a sunkuye. Bayan wasu yan dakiku sai mahaifin nasa ya dago kai yace.
To yanzu ita wannan din da ka jajibo baka ganin kamar tafi karfin arzikin mu?

Tijjani ya muskuta eh toh nima duk sai da nayi mata wannan bayanin amma tace taji ta gani tana kaunata.

Kai Tijjani kada ka debo ruwan dafa kanka ni wannan mata bata kwanta min Arai ba cewar mahaifiyarsa.

Uhm Uhm ai ba laifi bane don mutum ya auri mace mai tarin dukiya in har dai suna kaunar juna kuma za'a zauna lafiya kinsan sau dayawa abunda kake fargabar kamar bazai yiwu ba shi yake faruwa.

Hakane mahaifiyarsa tace.

Allah ya taimaka Allah yayi maka albarka dukkan wani bala'i dake tattare da wannan al'amari Allah ya kare ka daga shi tashi ka tafi Allah ya tsare mana kai ya rufa ma asiri.

Koda Tijjani yafito daga gidan mahaifansa saiyaji shi ya zama tamkar sarki haka nan saiyaji kamar an dauke masa wani kaya ne mai shegen nauyi daga kan doron bayansa domin yasan ayanzu baya bukatar ya sake damun kansa da tunanin batula abun kawai dake gabansa shine shirye shiryen aurensa da Nadiya.

Lokacin da dan achaba ya dauke shi saiyaji kamar ya sauka ya ruga da gudu akasa ko ya isa gida da wuri domin Allah Allah yake yakoma gida ya dan watsa ruwa a jikinsa sannan ya tafi Gidansu Nadiya da albishir din cewa to fa daga yanzu babu wani abu daya isa ya hana auren su..

****** ***** ****** ****** ***** ******* *********

Yau ne cikar rana ta uku yau ce ranar da zasuje karbar sakamakon gwajin jinin amma ga wanda baisan me ake ciki ba idan ya dube su sa'ar da suka shigo cikin farfajiyar asibitin sai ya rantse da Allah wata rantsatstsiyar liyafa sukazo tun daga nesa zaka hangi fuskokinsu na kyalli

Tijjani kamar YARIMA nadiya kamar SARAUNIYA ayadda suke tafiya cikin nishadi da farin ciki suna taku dai dai babu abunda zai hana su kama hannun juna da sunada aure to amma duk da hakan adab suke da juna ji suke yi kamar ma an daura aure domin cikin kwanaki ukun da suka gabata tuni an sami musayar kalamai na alkhairi tsakanin magabatansu har an tsayar da maganar aure cikin gaggawa nan da wata guda za'a daura auren.

Da farko saida abun yasa Tijjani kaduwa Haba nadiya a ina kike tsammanin zan sami kudin aurenki cikin wata guda ai ko zata zanyi Nabi ahankali domin na sato mai dan nauyi amna........

Nadiya ta katse shi
Kada wannan ya Dame ka ai sai da nayi maka alkawari tun farkon haduwar mu so nake kawai ka amince zaka aure ni nikuwa duk abunda kake so aduniya zan baka bari ma ka ga ni ta mike cikin sauri ta nufi wani daki dake fuskantar dankareren dakin shakatawar da suke ciki ba'a jima ba ta dawo dauke da.........KISAN BOKO-26

Bari ma ka gani ta mike cikin sauri ta nufi wani daki dake fuskantar dankareren dakin shakatawar da suke ciki ba'a jima ba ta dawo dauke da littafin fitar da kudi na banki cikin sauri ta tayi Rubutu aciki sannan ta yago takardar cikin gamsuwa sannan saita lankwashe takardar ta zura ta cikin jakar wasika ta like sannan ta mika masa tana dariya.

Don Allah kada ka bude saika je gida.

Menene aciki? Tijjani ya tambaya cikin zargi yana kallon ta da murmushi Nadiya ta kada harshen ta tsakanin fatar bakinta ta Harare shi.
Idan kaje gida ai ka gani.

Lokacin da Tijjani ya isa gida ko kayan dake jikinsa bai iya cirewa ba sai da ya farke takardar ya nufi kan gado zai zauna saikuma ya tuna da cewa ashe fa auren su da batula ya mutu don haka sai yaga bazai iya zama akan gadon ta ba cikin sauri yadawo dan akurkin falon ya zauna a kasa sannan yau janyo fitilar kwai dake ta faman bulbular da hayaƙi kamar salansar jirgin kasa bai damu da hayakinta ba musamman ma sa'ar da ya farke takardar yafara karanta cek din kudin da farko ya dauka dubu daya ne da ya dada dubawa sai yaga kamar dubu goma can kuma sai ya dada dubawa domin tun farko ya fahimci abin dake rubuce ajiki amma ya kasa yarda da haka don a tunanin sa kuskure ne tayi toh saidai kuma ai gashi baro baro a rubuce ko makaho ya laluba zai iya ji kalma ta nuna hakan lamba ma ta nuna naira miliyan daya ce a rubuce 1,000,000
Saida Tijjani yayi mintuna talatin rungume da takardar cek din yana jijjigata a kirjinsa kamar wani jariri bai taba mafarkin zai iya samun koda dubu dari a dunkule ba.

Bazata yiwu ba Tijjani yace da ita a washegarin ranar a kofar gidansa.

Menene bazai yiwu ba? Nadiya ta tambaya cikin dariya.

Haba nadiya ai kema kinsan wannan kudi ai sunyi yawa haka.

Nadiya ta dube shi na takaitaccen lokaci tana girgiza kai sannan sai ta ce a tausashe
Ai kudin ma sunyi kadan Daman wannan kudin dana baka so nake ka dinka wa kanka sutura sauran ka zuba a aljihun ka saboda harkokin biki ni bana bukatar ka saiya min ko da allura domin nawa sun ishe ni har sunyi min yawa inada kayan da zanyi ta sawa kullum har sau uku na tsawon shekara guda ta danyi shiru tana girgiza dan makullin motarta sadaki kawai nake bukata agurinka shi kuwa wannan ko nawa ka bani Allah ya amfana ya isheni Awannan karon Tijjani ne yayi galala yana dubanta cikin kaduwa.

Don haka a ayanzu da suka jera suna tafiya cikin farfajiyar asibitin cikin annashuwa da begen juna sai nadiya ta dubi Tijjani da wani
MURMUSHIN ALKAWARI tace yaya... Ka tsara shirye shiryen bikin.? Kafin Tijjani ya bata amsa sai wani masinjan asibitin ya nufo inda suke cikin sauri
Ranki ya dade Barka da zuwa
dattijon yace bakinsa har kunne domin jifa jifa idan nadiya taga dama takan jefe shi da nannadaddiyar naira ashirin ko hamsin.

Yauwa TARKATAU... Inafatan dai lafiya?
Lafiya lau ranki ya dade saidai fa anayi mana garin nan.

Adaidai lokacin ne mici micin idanunsa da suka ga jiya kuma suka ga yau suka kai kan Tijjani
Ranki ya dade wannan kanin ki ne naga kunyi kama sosai.
Nadiya ta dubi Tijjani sannan ta dubi tsohon sai taji kamar ta fashe da dariya domin ta riga tasan in banda son tsurku babu ta inda tayi kama da Tijjani Kamata yayi ma maganar ta bashi haushi amma dayake yau cike take da farin ciki saita dubi dattijon da faffaadan murmushi tace.

Wannan ba kanina bane MIJINA ne idanun dattijon suka firfito yace iko sai Allah hajiya Daman kinada miji? Nadiya ta sake dubansa wannan karon a fusace tace kwarai kuwa.
Ahaka suka bar shi durkushe yana kallon su cikin mamaki har suka shige cikin gine ginen asibitin.

Dogon malamin asibitin mai kyan fuska da yawan son dariya ya tare su da faffaadan murmushi sa'ar da shiga dakin gwajin jinin.

Sannun ku da zuwa yace idanunsa akan fuskar nadiya baya ko kiftawa bai taba gajiya da kallon ta ba akwai sa'ar da har lekenta yake ta cikin taga idan tana sunturi a farfajiyar asibitin.

Yawwa sannu dai Ibrahim yaya aiki?

Alhamdulillahi.. Ranki ya dade

Yace sannan ya dada hasketa da wani murmushin fara'ar dake fuskarsa ita tasa Tijjani yayi ajiyar zuciya cikin tsananin farin ciki domin duk dayake yayi imani da cewa nadiya lafiyar ta Ƙalau garas take babu wata cuta dake damunta hakan bai hana zuciyarsa taraddadin karbar wannan sakamakon ba domin ji yake kamar za'a ce nadiya na dauke da cutar.

Tabbas murmushin dake fuskar Ibrahim ya goge duk wata fargaba dake zuciyarsa dan haka ma sai ya dubi Ibrahim cikin murmushi.
Toh yaya akayi malam Ibrahim ina sakamakon?

Dogon malamin asibitin ya cire gilashin sa ya goge kana ya mayar da shi fuskar sa sannan ahankali ya dauko wani koren fayil daga kan teburin sa ya bude shi ya danyi nazarinsa sannan saiya dauko takardun guda biyu ya dubi Nadiya yace.

Ina taya ki murna lafiyar ki Ƙalau nadiya ta karɓa gamida tsaki irin alamun dake nuni da cewa ai daman nasan haka zaka gani.

Shi fa ba ka bashi tasa ba tace tana kallon Tijjani.

Dogon malamin asibitin ya dada gyara tabaronsa kana ya dauko ragowar takardar dayan ya dubi Tijjani yace a tausashe.

Uhm malam... Ina son ka kwantar da hankalin ka ka dauka cewa wannan kaddarace tana iya fadawa akan kowa kuma wannan bashi ne zai zama karshen rayuwar ka ba.....

Nadiya ta rike numfashi a firgice....
Me....me kake nufi.? Ta tambayi Ibrahim akwai alamun razana a muryar ta.

Ibrahim yayi ajiyar zuciya kana ya dubi Tijjani.
Abinda nake so nace shine wannan dan uwan Naki yana dauke da cutar KANJAMAU gwaji ya tabbatar da hakan.

Nadiya ta kwalla kara a razane karya kake yi ba daidai bane

Ibrahim ya dubeta a tausashe yace
Idan baki yarda ba gwada da kanki ina tabbatar miki da cewa haka zaki gani don wannan aikina ne....KISAN BOKO-27

BABI NA BIYAR
Tun tana karamar budurwa sa'ar da take makarantar gaba da sakandire babu abunda ta tsana irin ayi ta tari akusa da ita haka nan kuma ko acikin film taga muutum yana amai to aranar wuni zatayi bata ci abinci ba wannan ce ma tasa bata son cin naman kaza domin wai ta sha ganin idan kaza bata da lafiya tana fto da wani abu daga bakinta mai kamar amai.

NA SHIGA UKU TACE A FUSACE SA'AR DATA JUYO dattijon yana kakarin tari daga cikin dakin shakatawar.

A kwance Take akan gado sanye da doguwar riga fara Kal mai shara shara kanta babu dankwali amma gashin kanta daure yake tsaf adoron keyarta yana sheki
Mujalla ce ahannunta na turanci tana kallon Rubutun domin zuciyarta cike tak da dimbin tunane tunane tana ta sakawa taba warwarewa kamar yadda ta saba.

Lokaci yayi da ya kamata ta gudanar da mataki na biyu acikin babban shirinta adaidai lokacin da zuciyarta ke ta fama da alkaluman lissafin shirinta ne to ta janyo dattijon yana tari. Cikin sauri ta jefar da mujallar dake hannunta ta nufi dakin shakatawar a fusace

Azaune ta same shi kamar yadda ya saba yi a dakinsa yana ta tari kufur kufur akwai sa'in da sautin tarinsa ke tuna mata da karar tashin tsohon mashin ko data duba gefe kadan sai ta ga duk ya tofe bangon dakin da yawu. Cikin kunar rai ta kura masa idanu ba ta ko kiftawa tana tunanin ta inda zata fara kullo sharrin don Daman wannan itace damar da take jira tun da garin Allah ya waye koda taci gaba da kallon sa saita tambayi kanta dalilin dayasa ta auri wannan dattijon.

Mutumin dake zaune Yana kakarin tari dattijo ne me yiwuwa dan shekara hamsin ne zuwa sittin amma fuskarsa ta nuna saba'in dan gajere ne baki mai manyan idanu jajaye yana da dogon baki wanda hakan ya sa shi kama da cilakowa yanada faffadan kai sal sal babu gashi kamar koko haka nan akwai wani dan farin gashi da yayiwa kansa hanya ta tsakanin habarsa kamar jelar tsuntsu sau da yawa yara kanso suyi wasa da gashin idan yana yi musu wasa idan yayi dariya kananan yara marasa wayo kan fashe da kuka domin hakoransa uku na gaba babu su ya baro su awani gidan giya acan Ikko tun zamanin kuruciyarsa wani kato mai karfi kamar talauci ne ya naushi hakoran har kuma zuwa wannan lokaci bai damu daya sa na roba ba sunan mutumin ALHAJI MAI JAYE-JAYE Amma yataba cewa da matar tasa wai sunansa na gaskiya SANI.

Menene kika zura min idanu kamar wata mayya!!
Mutumin yace da ita kalmomin na rawa tsakanin harshen sa matar ta lura da cewa ashe kwalbar giya ce rike akan cinyarsa.

Dani mayya ce ma babu abunda zanyi da gwano kamar ka.
Mutumin ya barke da wata dariya mai kama da haushi.
AMIRA kenan da baki san ni gwano bane kika aure ni? Amira ta dube shi cikin takaici tana mai kara tambayar kanta wai shin me yasa ta aure shi ma tun farko?
So ne? Kokuma ta aure shi ne dan kudinsa?

Haka dai ta fadawa babbar kawarta nadiya amma a hakikanin gaskiya al'amarin bashi da arzikin da zaisa ta aure shi da mahaifiyar ta bata takura akan ta aure shi ba da'ace tasan dan giya ne kazami da'ace tasan zata hadu da kyakkyawan saurayin nan tun farko da babu abinda zaisa ta aure shi to amma yanzu tayi kai tabbas idan shirinta ya tabbata babu abunda zai hanata auren babban abun kaunar ta fasihi kyakkyawa Amma kafin nan ya zama dole na rabu da wannan Jangwam din ta fadawa kanta.

Ai kai ka sani Wallahi in ba dan kusancin yan uwanta ka dake tsakanin ka da mahaifiyata ba babu abinda zaisa na aure ka.

Karya kike Munafuka. yace sannan ya fashe da wata dariya mai bada sauti dum dum kamar harbin bindiga.

Wallahi karya kikeyi Daman Badon Allah kike bin maganar mahaifiyar ki ba kika aureni. tari ya shake shi idanunsa suka zazzaro kamar idanun kwado.

Keda mahaifiyar taki ai duk barayi ne kun dauka wata uwa duniya na tara na mutu kici gado... To banida komai sai wannan gidan Dan kudin danake samu ma dana baki kwabona gara in sha giya mota guda yakara fashewa da dariya.

Amira ta dube shi cikin kunan rai sannan saita tuno da muryar mahaifiyar ta
Don ubanki in baki aure shi din ba kinada wani zabi ne?
Shegiya kinfi so kiyi ta yawo a gari wai ke yar boko fanko babu miji shekara sama da talatin babu aure to so kike ki tsofe ahaka?

Ni... Ni dai wallahi bazan auri tsoho ba amira tace cikin kuka.

To don ubanki ba sai ki auri jariri ba tunda bazaki Auri tsoho ba.

Kwana Uku Tsakani Ashe........KISAN BOKO-28

Shegiya kinfi so kiyi ta yawo a gari wai ke yar boko fanko babu miji shekara sama da talatin babu aure to so kike ki tsofe ahaka?

Ni... Ni dai wallahi bazan auri tsoho ba amira tace cikin kuka.

To don ubanki ba sai ki auri jariri ba tunda bazaki Auri tsoho ba.

Kwana Uku sukayi suna cacar baki kasancewar mahaifinta mijin Hajiya ne sai ya zuba musu idanu baice dasu ta tafasa ba ballanta ma ta ƙone ran nan da yamma sai mahaifiyarta ta same ta cikin lalama tace.
Ke shashasha ce bakya ganin abunda nake nuna miki mutumin nan yanada yan kudi kuma kin ga sai abunda kikace shi zai yi.

To amma mama ance fa mutumin nan tsohon dan duniya ne sai da ya gama yawon sa aduniya yadawo Gida kiji fa shekarun sa kusan hamsin amma ko aure bai taba yi ba.
Wa ya fada a miki? Yataba aure tun muna yara matar ce ta mutu shiyasa ya kasa aure kece baki san shi ba amma ai dan uwa ne ma agurin mu kuma in banda abun ki ma ni abin kunya da zagin mutane nake guje miki kin girma babu miji to me zai hana ki aure shin in kinga bazaki iya zama dashi ba ai sai ki dawo da zaman babbar budurwa dai gara na karamar bazawara.

Amira ta aure shin kuma ayanzu da take tsaye tana kallonsa cikin takaici sai taga lokaci yayi da ya kamata ta rabu dashi bakuma wai don maganar mahaifiyar ta ba sai don alkawarinta da kyakkyawan saurayin kaico! Tace aranta inama ace tun farko dashi nafara haduwa da babu abinda zai sa na auri wannan lalataccen mutumin dake gabana.

To na ji ka gama zagina da mahaifiyata saika sallame ni lalatacce domin banga amfanin zama dakai ba ta matsa kusa dashi tana zazzare idanu kamar zata hau

Please Login or Register in order to submit comment