Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nabaka shawarar daku ci gaba da zama da matar ka batula.

Tijjanj ya bude baki cikin kaduwa.
Batula fa kace? Matar da ka tsani zamana da ita Meyasa yanzu lokaci guda zakace dani haka?

Abdul ya muskuta yace Saboda akalla dai batula bata barazana ga rayuwar ka...... Amma ina tabbatar maka da cewa me yiwuwa idan ka auri wannan mata da kake magana akai da wahala in zaka kara shekara biyu aduniya.

Bansan abunda make nufi da haka ba.... Ni kam ka rudani Abdul duk me ya yi zafi kake irin wadannan maganganu.

Abdul ya dubi Tijjani da wani daddatan murmushin yake yace muryarsa a tausashe.
Ka gafarce ni Tijjani na dauka kai dan boko ne shin baka san irin yadda muguwar cutar nan ta kanjamau take yawo aduniya bane?

Tijjani ya girgiza kai cikin sauri.
Haba Abdul ai abun bai kai haka ba... Ni nasan yadda nadiya ta nuna tana kaunata bazata taba cewa zata aure ni ba in tasan tana da wannan muguwar cuta ta kanjamau ba.

Abdul ya yi shiru na tsawon lokaci yana kallon Tijjani can sai yace.
Dayawa daga cikin irin wadannan mata da suka sha sharholiyarsu basuda masaniyar suna dauke da wannan cuta ta kanjamau ba. Alhali kuma Dayawan su suna dauke da ita.

Tijjani ya muskuta cikin damuwa.
Toh wannan ai duk zato ne mukeyi Abdul bamuda tabbacin nadiya yar sharholiya ce ballantana har muyi mata zaton kanjamau.

Abdul ya tura kafarsa gaba har ya shure wani allo batareda ya sani ba.
Hakane gaskiya ne duk zato mukeyi amma ina son ka sani cewa riga kafi yafi magani ya danyi shiru sannan saiya matso kusa da Tijjani ya dafa hannunsa yace.
Duk duniya banida aminin da nake kauna kamar ka shiyasa kaga na damu da rayuwar ka zanyi matukar farin ciki idan nadiya ta kasance matar kirki shiryayyiya zan so kuma ka aure ta tunda dai ba laifi bane don ka aureta tunda tana da dukiya tabbas auren ta alheri ne to amma kafin ka aureta din dole ne mu tabbatar domin ni nagama tsorata da mutanen zamani.
Ya danyi shiru sannan yaci gaba jiya-jiyan nan wani tsohon kwamishina dayake zuwa gurina ina masa rokon Allah yake bani labarin wani abokinsa ya auro wata mace ko shekara basu yi ba aka gano tanada kanjamau zancen nan danake maka ayanzu ita watanta uku da mutuwa shi kuwa yau watan sa bakwai a asibiti yana can yana jiran MUTUWA.KISAN BOKO-19

Ko shekara basu yi ba aka gano tanada kanjamau zancen nan danake maka ayanzu ita watanta uku da mutuwa shi kuwa yau watan sa bakwai a asibiti yana can yana jiran MUTUWA.

Tijjani yayi mutuwar tsohuwa gumi na zuba yana kallon Abdul cikin tsananin kaduwa domin bayanin Abdul na karshe yayi matukar tsorata shi idan har akwai cutar dake tsorata Tijjani aduniya to kanjamau ce dan bai amince da batun a kididdige masa sauran numfashinsa aduniya ba. Abdul ya dubi fuskar Tijjani saiyaga tafara kyalli kamar waina akwai alamar tsoro karara a fuskarsa.
Toh... Yanzu me kake ganin yakamata nayi.... Na rabu da Nadiyar? Tijjani ya tambayi Abdul cikin karyayyiyar murya Abdul ya girgiza kai. Ni bance ka rabu da ita ba tunda dai kana kaunar ta amma zanso ace mun tabbatar da lafiyar ta kafin ka aureta domin idan mukayi la'akari da irin yarda mata suke da kunya abu ne mai wahala ace lafiya-lafiya daga haduwar ku kwana biyu kacal tace wai tana son ka aure ta. Abdul ya girgiza kai cikin damuwa.
Al'amarin akwai alamar tambaya a kansa dole ne a zargi wani abu.

Tijjani ya muskuta akan bakin buzun cikin tsananin damuwa lokaci guda kuma yasa hannun rigarsa ya share gumi sannan saiya dauki wani guntun kwali dake daf dashi yafara fifita.
Kace kada na rabu da ita ka kuma ce kada na aure ta to menene hakikanin abunda kake shawarta ta danayi? Abdul ya dubi Tijjani cikin murmushi yace.
Wani lokacin idan kana magana kamar ba dan boko ba yanzu kai duk bayanin danake maka baka fahimce ni ba? Tijjani ya gyada kai.
Lallai kam ni ban fahimce ka ba Abdul ya dauki alkalamin sa yafara susar kunne.
Abinda nake so dakai Tijjani indai zai yiwu ku tafi da matar nan a auna jinin ta domin a tabbatar ma da cewa batada wannan cuta ta zamani kuma ka tabbata a gabanka akayi gwajin. Tijjani ya katse Abdul.
Haba Abdul idan nayi mata haka ai na nuna mata cewa ban yarda da ita ba kuma zata dauka ina zargin ta da fasikanci duk dayake dai wannan cuta tanada hanyoyin dauka da yawa amma an fi zargin daukarta ta hanyar fasikanci.

To yanzu don kada tace kana zargin ta saika jefa kanka ga halaka? Inji Abdul. Tijjani ya dada share gumi jikinsa na rawa kwakwalwarsa a yamushe.
Abinda nake so dakai Abdul yaci gaba da cewa.
Idan kun sake haduwa ka sanar da ita ka amince zaka aure ta amma da sharadin sai an auna jinin ta an tabbatar da lafiyarta kada kaji fargabar komai fada mata gaskiyar abinda ke zuciyar ka nasan indai da gaske ne tana kaunarka zata amince da ayi hakan in kuma kana ganin kamar yin hakan bai zama adalci ba to kaima ka bada naka jinin sai a gwada baki daya kaga duk sai ku samu kwanciyar hankali gaba daya.

Tsawon lokaci kan Tijjani a sunkuye cikin damuwa ko kusa ko alama baya kaunar wannan shawara ta Abdul to amma dayake ya riga ya fadawa zuciyarsa cewa bazai sake kunyata babban amininsa ba sai Tijjani ya dago kai baki na rawa yace.
Kana ganin idan har an aunata an tabbatar min da lafiyar ta zan iya auren ta? Abdul ya dube shi da faffadan murmushi yace kwarai kuwa me zai hana ai indai lafiyar ta Ƙalau kuma mutumiyar kirki ce aurenta zai zamo alheri agareka.
Toh Ai Shikenan Tijjani yace cikin damuwa sannan ya Mike Tsaye zuciyarsa cike da zullumin hanyar da zai bi ya tunkari nadiya da wannan magana ta gwajin jini.

Abdul ya Mike tsaye mu tafi na raka ka ko?
Suka fice daga dakin lokacin da suka fara tafiya acikin kwararon Abdul ya lura da cewa ko kusa ko alama Tijjani baya cikin walwala amma duk da hakan saiya dube shi yace yanzu yaushe zaku sake haduwa da sabuwar mutumiyar taka?
Tijjani ya dago hannayensa sama yaja doguwar mika kana ya dubi Abdul.
Sati guda dai tace tabani wai nayi nazari akan al'amarin amma ina tunanin gobe zanyi kokarin samun ta domin na shaida mata shawarar dama bani.

Jin hakan shiyasa Abdul ya saki wani faffadan murmushi sannan ya dubi Tijjani cikin alfahari.
Dakyau Tijjani yanzu ne muka fara shiri da kai..... Fada mata komai kada kaji tsoron komai ko wai fargaba da iznin Allah zamu rike ma zuciyarta indai lafiyar ta Ƙalau babu abunda zai hana ka aureta.

***** ****** ***** ****** ******* ****** *******

Nadiya ta dubi yankwananniyar tsohuwar dake kwance guri guda bata ko motsi akan sangalin gadon ta girgiza kai sannan ta ciro ma'aunin numfashin dake sakale a wuyanta takara akan dan abunda ya rage na daga jikin tsohuwar sannan ta cusa majiyoyin abin awon numfashin cikin kunnuwanta tayi kasake tana sauraron bugun numfashin.
Haryanzu dai ashe tanada rai nadiya tace da kanta sa'ar data cire ma'aunin numfashin daga kirjin mara lafiyar dake kwance sannan tayi duba izuwa jerin gadajen dake cikin dogon dakin majinyata mata dake asibitin tayi ajiyar zuciya tabbas wannan itace mara lafiya ta karshe da zata duba aranar.KISAN BOKO-20
Tayi duba izuwa jerin gadajen dake cikin dogon dakin majinyata mata dake asibitin tayi ajiyar zuciya tabbas wannan itace mara lafiya ta karshe da zata duba aranar.

Dakin da Nadiya ke ciki dogo ne wanda ke dauke da gadajen majinyata goma wanda ko wanne gado akwai majinyaci daya a kwance sannan akusa da ita wasu yan siraran malaman asibitine mata tsaye suna jiran umarni.

Nadiya ta dubi majinyatan dake dakin cikin damuwa domin ta lura in ta dauke wata ramammiyar budurwa dake zaune kamar mutum mutumi akan gadon tana shan rabin lemon zaki duk sauran majinyatan a kwance suke suna numfarfashi sama-sama abin babu sauki kusan sati guda kenan ahaka su basu mutu ba su kuma basu yi rai ba. Nadiya ta tausayawa yan uwan majinyatan domin ta lura da yawa daga cikinsu duk na kiyasi ne da masu karamin karfi ne su kansu dakyar suke ciyar da kansu ballantana kuma su taimaki marasa lafiyar ta hanyar saya musu magani.

Akwai wani tunani a zuciyar nadiya dake yi mata nuni da cewa in har aka dada yan kwanaki ahaka cikin dakin babu mai samun sauki to da wuya in masu zaman jinyar suma basu fara kwantawa ba.
Yakamata ta taimakawa masu karamin karfin da dan abin sayen magani nadiya tace cikin zuciyarta wannan ba wani bakon abu bane agareta domin a yan shekarun datayi da fara aiki asibitin Allah ne kadai yasan iya yawan mutanen da ta taimakawa wannan yana daya daga cikin dalilanta na Aiki a asibitin amma ba wai dan dan abinda ake biyan ta ba domin wata sa'ar ma idan an biya ta agurin take rabar da kudin ga majinyata.

Nadiya ta dubi yan siraran malaman asibitin dake kusa da ita cikin murmushi sannan saita juya suka bi ta abaya cikin sauri kamar yadda suka saba kullum na al'ada.
Fitar su keda wuya sai nadiya taji gabanta yafadi sa'ar data nufi ofishin ta ba wani abu bane yasata Faduwar gaban ba daya wuce tunanin babban masoyin ta Tijjani kwata kwata ta mance dashi cikin yan mintuna da suke gabata me yiwuwa ganin marasa lafiyar dake kwance babu sauki ne ya dauke tunanin masoyin nata na dan wucin gadi ba mamaki kuma tunanin cewa ta bashi sati guda ne yaje yayi tunani akan maganar auren su ya mantar da ita.

Cikin sauri ta nufi ofishin ta sannan ba'a dade ba sai gata ta fito cikin sauri kanta a sunkuye akwai alamun farin ciki karara a fuskarta haka nan da wani zai lura da kyau da ba abunda zai hana shi ganin tattausan murmushin dake makale Agefen bakinta.

Ita kadai tasan abunda ke kai kawo aranta azuciyata tana kissima cewa nan da yan kwanaki Tijjani ne zai ke kawo ta asibitin kullum yana tukata tana zaune kusa dashi agidan gaba tana kallon kyakkyawar fuskarsa tanayi masa hira mai dadi wannan tunani shiyasa wani faffafan murmushi ya kubuce mata.

Ahaka ta nufi inda rantsatstsiyar motarta take cikin sauri domin so take ta isa gida tayi wanka sannan tasa riga marar nauyi tayi kwance akan gado tana lumshe idanunta tayi ta bijiro da hirar ta da Tijjani domin hakan shine kawai zai iya sata barci.

Adaidai lokacin ne data tura dan makullin motar zata bude motar saitaji ance.
NA..DIYA
Nadiya taji gabanta yafadi rass sa'ar da muryar da tafi kauna aduniya ta daki dodon kunnen ta ahankali jikinta na rawa ta juyo cikin tsananin mamaki ta dube shi.

Kiyi hakuri..... Ban fada miki zan zo ba ko?
Tijjani yace da ita yana dubanta ido da ido.

Nadiya tayi kokarin jifansa da murmushi amma saitaji fatar bakinta yaki amincewa da hakan domin kallo daya ta yiwa fuskar sa ta tabbatar akwai matsala.
Na shiga uku.... Zuwa yayi yace dani bazai aureni ba.
Nadiya tace cikin zuciyarta sannan cikin karfin hali sai tace dashi muryarta na rawa.
Tijjani kaine yau har asibiti Meyasa baka sameni a gida ba? Lokaci guda kuma saita sake juyawa ta bude kofar motar ta dada da cewa.
Zagaya ka shiga daga ciki ko? Kokuwa ofishina zamu koma?

Tijjani y girgiza kai kamar kadangare A'a cikin motar ma ta isa.Mutanen biyu sukayi shiru na dan lokaci zaune gaban motar kawunan su a sunkuye kowa zuciyarsa cike da zullumi daya na tunanin cewa ta riga ta rasa abunda tafi so fiyeda komai aduniya yayinda daya yake tunanin hanyar da zai bi ya bayyana mata abinda ke cikin zuciyarsa batareda ya kona mata rai ba sai da suka share kusan mintuna biyar kawunan su a sunkuye sannan nadiya ta dago kai ta dube shi tace cikin karyayyiyar murya.

Fadi mana Tijjani.... Kabarni ina jira.... Kada ka damu in ka yanke shawarar bazaka aureni ba Shikenan..... Yaya na iya da raina... Idanunta sukayi rau rau kamar zatayi kuka saidai bata bari Tijjani ya lura da hakan ba.

Ni bance bazan aure ki ba nadiya.....
Nadiya ta dube shi firgigit cikin mamaki to in bahaka bane menene na yin shirun wani abu ne ya same ka?

Tijjani ya girgiza kai.

Matar ka ce bata son ka aureni?

Tijjani ya girgiza kai

Mahaifan ka ne basa son ka aureni?

Tijjani ya girgiza kai.

Yau naga abinda ya isheni nadiya tace tana dubansa cikin damuwa.
To in duk ba wadannan abubuwan dana zana bane menene to?

Tsawon dakika talatin da doriya kansa a sunkuye can saiya dago kai ya dubeta yace....
DON ALLAH DON ANNABI NADIYA...KISAN BOKO-21

Tsawon dakika talatin da doriya kansa a sunkuye can saiya dago kai ya dubeta yace....

DON ALLAH DON ANNABI NADIYA idan abunda zan fada yanzu ya zama mai kona zuciya agareki to ki gafarce ni kada kuma ki dauka bana kaunar ki ne Wallahi ina kaunar ki har zuciyata.

Nadiya ta muskuta acikin motar sannan ta dube shi a rude.
Fadi abunda kake son ka fada Tijjani ko menene na yafema..... Kaji Tijjani Na!

Allah Sarki baiwar Allah Tijjani yafada cikin zuciyarsa sannan batareda ya yarda sun hada idanu ba sai yace.
Wani abu nake son muyi kafin azo ga maganar auren namu..... Maganar tasa ta yanke sakamakon wani kakkaifan kallo da nadiya tayi masa ya lura da hakan ne ta gefen idanunsa.

Kana nufin idan na yarda mukayi abinda kake nufi din zaka aure ni?

Tijjani ya gyada kai cikin sauri kwarai kuwa nadiya..... Domin na gama yanke shawara.

Nadiya tayi wata doguwar ajiyar zuciya gamida dafe goshi wanne abu kake son mu yi?
Awannan karon Tijjani ne ya sunkuyar da kai sannan ya rufe fuskar sa da tafukan hannayen sa biyu yace cikin wata murya dashi kansa bai iya ganeta amatsayin tasa ba.
Nadiya...... Zanso ace an auna jinin mu nida ke domin a tabbatar da lafiyar mu kafin muyi auren nan yana gama fadi saiya juya a fakaice ya dubi fuskar ta cikin fargaba. Nadiya bata yi ko gezau ba in ma maganar Da yayi tasa ta kaduwa to bata nuna hakan a zahiri ba maimakon ta hade fuska ma kokuma ta dafe kirji a razane saita juyo ta dubi Tijjani ido da ido da wani tattausan murmushi tace.
Shikenan Daman maganar taka.?

Tijjani ya gyada kai sannan yaci gaba da cewa cikin in'ina ki....yi hakuri don Allah ni ba nufina in......
Ta katse shi ta hanyar daga masa hannu kada ka damu Tijjani tunda ka amince zaka aure ni din ai Shikenan...... Don gwajin jini gobe ma in ka shirya saika zo ayi mana.

Abunda tace yayi matukar sashi nadamar abinda yace domin yasan tabbas abunda yace na nufin bai yarda da ita ba kenan amma maimakon tayi fushi sai taci gaba da dubansa tana murmushi.

Mu tafi na kaika gida ko? Har ma gaisa da matar ka nadiya tafada cikin murmushi.

Tijjani ya shafi hancinsa da yan yatsunsa biyu kana ya numfasa Ma...tata bata nan.

To ko bata nan ai ba laifi bane dan na mayar dakai gida ko?
Tijjani ya gyada kai a tsorace.

Saki jikin ka Tijjani nadiya tace dashi adaidai lokacin da ta sawa motar giya tafara tafiya da ita ahankali ko kusa kada kayi tsammanin abunda kace ya dami zuciyata ta girgiza kai gamida tabe baki sannan ta dada da cewa.

Ba gwajin jini ba ko cewa kayi kana son a farde maka cikina ka leka ka gani zan iya yarda indai har zaka aureni.

Tijjani dai yayi shiru kansa a sunkuye kamar ruwa ya cinye shi.
Ahakan suna tafiya tana hira Tijjani na gyada kai kamar jangwale-gwadan kadangare har dai suka karaso kofar gidan.
Nadiya ta tsayar da motar adaidai kofar gidan da Tijjani yace da ita ta tsaya.

Nan ne gidan naku? Tijjani ya gyada kai Nadiya tayiwa gidan kallon Allah Sarki rugurguzau sannan ta dawo da kallon ta izuwa fuskarsa.

Idan Allah ya kaimu gobe zan zo na dauke ka sai muje asibitinmu a gwada jinin namu ko?

Bama sai kin wahalar da kanki ba zanzo na same ki acan kamar karfe nawa yakamata nazo?

Nadiya ta muskuta kadan sannan ta dube shi kamar karfe goma yayi ma?

Bakomai Tijjani yace ko karfe nawa kike son nazo ni banida matsala... Daman ke nake ji.

Nadiya tayi murmushi kada ka damu dani akwai ranar da idan na tashi da asuba bana komawa barci tana gama fadin haka saita bude wata yar jaka fara dake ajiye agaban motar ta dauko wasu yan adadi na kudi ta mika masa.
Ga wannan nasan zaka bukacesu tunda dai yau matar ka bata nan..... Yau a gwauron ka kake tace gamida wata jaririyar dariya.

Tijjani ya dubi kudin ya girgiza kai gamida murmushin karfin hali. Kada ki damu ki barsu inada kudi sannan a zuciyarsa yana cewa Cab yau na cuci kaina.

Don Allah Tijjani ka karɓa kada kayi min haka.

Inada kudi Wallahi a zuciyarsa yana cewa Bandai yi karya ba tunda akwai naira arba'in a aljihuna.

Ai kyauta ce kada ka mayar da hannun kyauta baya indai ba so kake ka zama shaidan ba ta dan yi dariya.

Tijjani ya mika hannu galala ya karɓa yana yan waige-waige domin baya son daya daga cikin makwabtakansa ya hange shi yana karbar kudin don tuni labari ya watsu cewa wai wata MILONIYA ke son auren sa.

Yawwa ko kaifa wallahi har na ji dadi araina nadiya tace tana girgiza kafafunta.

Meyasa ki jin dadin? Tijjani ya tambaya yana dubanta da murmushinsa lamba daya jin haka shiyasa nadiya ta dan dauke kai gefe guda kana ta sa hannunta na dama akan giyar motar tace.
Saboda aduniya babu abunda nafi so irin ace na taimaka maka a rayuwa na kyautata ma na faranta ma na debe ma duk wata damuwa ta yadda zaka saki ranka ka amince dani ka kuma kaunace ni kamar yadda nake kaunar ka ayanzu tayi shiru kanta a sunkuye Saidai...........

ASHE DATA SAN ABUNDA ZAI BIYO BAYA DA BATA.......KISAN BOKO-22

Na debe ma duk wata damuwa ta yadda zaka saki ranka ka amince dani ka kuma kaunace ni kamar yadda nake kaunar ka ayanzu tayi shiru kanta a sunkuye.

Tijjani yayi ajiyar zuciya sannan ya bude kofar motar batareda ya dubeta ba sai yace Sai goben idan mun hadu. bai juyo ba ballantana ma yaga irin kallon da takeyi masa ba. ba don bayaso ba sai dan yana jin kunyar hada kwayar idanu da ita yanzun nan yagama cewa da ita bai yarda da ita ba bai amince da ita ba sai gashi yan mintuna kadan a tsakani tana jaddada kaunar ta gareshi ko da ya shige cikin gidan sai yayi shakkar anya kuwa goben zai iya zuwa asibitin gwajin jinin?

Sa'ar daya shige gidan sai nadiya tayi ajiyar zuciya kana ta tuka motar ta ta nufi gida cikin rashin tabbacin samun abunda take so to amma ta dada jaddadawa zuciyarta cewa indai har kudi suna magani babu abunda zai hanata auren Tijjani.

****** ****** ******* ******** ******* *********

Wannan zancen banza ne wulakanci da cin mutunci yake son yi miki in ba iskanci da rainin wayo ba ne ya dauke ki da zai ce wai sai an gwada jininki zai aure ki yar iska ko me? Amira ce ke ta wannan masifar babu ko kakkautawa azaune suke a lambun shakatawar gidansu nadiya suna kallon ramin wankan zamanin da Ruwan ke daukar idanu cikin dan abunda ya rage na hasken ranar wannan yammacin akwai teburi wanda ke dakon kayan ciye ciye da lashe lashe agaban su amira ta ajiye kofin dake hannunta akan teburin cikin fushi domin ko kurba daya batayi ba nadiya ta bata labarin yadda sukayi da Tijjani.

Don Allah amira...kada kice dashi komai ki kyale shi kawai a gwada jinin to menene ne idan an gwada din ba Shikenan ba hankalinsa ya kwanta.

Amira ta Harare ta hana nadiya ke fa wallahi bakya rabuwa da sakarci ya mutum zai dauke ki kamar wata yar iska.. Ai ni wallahi yabani mamaki da na dauke shi tamkar wani waliyi ashe KURA NE DA KAN RAGO nidai wallahi da zaki biye ta ni da kin hakura da zancen auren nan nasa.

Nadiya taji kamar an watsa mata wuta a fuska wannan shine mafi munin kalma data taba jin yafito saga bakin babbar kawar ta Amira. Ta rabu da Tijjani cab mafarki kenan Amma ba zahiri ba nadiya ta sunkuyar dakai tana duban fuskarta a Doron teburin dake gaban su.

Amira ta lura da sauyin yanayin dake kan fuskar nadiya don haka sai tayi sauri ta sassauta tsauraran kalamanta da cewa.
Amma idan kin ga kina son sa Shikenan....ya zanyi kuskure ne dai na riga nayi don ni wallahi na dauke shi mutumin kirki shiyasa ma na hada ki dashi.

Wani kyakkyawan malam bude min littafi ya taso ahankali kamar jirgi ya sauka akan cinyar nadiya. Sannu ahankali sai tasa yan yatsunta biyu ta dauke shi sannan ta nufi hancin ta dashi domin a tunanin ta fure ne adaidai lokacin ne to ta fahimci ashe kwaro ne mai launin shudi da rawaya hakan shiyasa ta furta abunda tayi niyya tun farko sannan ta dubi amira a tausashe.

Allah huci zuciyar ki ƙawata na fahimci kin dau zafi amma ina son kiyi COOLING DOWN domin Tijjani na nan a mutumin kirkinsa kamar yadda kika tsammace shi tun farko.

Amira ta dauke kai gefe guda tayi kamar bata ji abunda nadiya tace ba na fahimci kina bala'in kaunar sa ko?

Nadiya ta gyada kai tana wasa da kwaron malam bude mana littafin dake hannunta fiyeda komai aduniyar nan Amira.... Wallahi banajin akwai abinda zai hanani aurensa.

Koda kuturu ne? Amira ta tambaya cikin dariya.

Kwarai kuwa

Koda gurgu ne?

Kwarai kuwa

Koda makaho ne?

Eh koda baya ji baya gani kuma gurgu ne nidai wallahi ina son sa haka.

Amira ta fashe da wata daddattar dariya.
Oh yau na shiga uku da mace wai don Allah nadiya duk abin nan da kike fada da gaske kikeyi ko kuwa dai tsokana ta kikeyi?
Nadiya ta mike tsaye sannan tayi jifa da kwaron dake hannunta

Ba'a wasa da lamarin so amira idan nace dake inason abu to ina nufin hakane har zuciyata ke kan ki shaida ce tun muna makaranta kinsan haka nake.

Amira ta mike tsaye tana mai dogon duba izuwa kawar ta sannan tace a tausashe.
Kiyi hakuri to ki gafarce ni akan batancin dana fada AKANSA ban dauka kina kaunarsa haka ba.

Nadiya ta saki murmushi ta dafa kafadar kawar ta gamida gyada kai.
Kada ki damu ai nasan duk fadan da kikeyi saboda kaunata ne.
Amira ta gyada kai wannan gaskiya ne ta dan yi shiru yanzu yaushe ne zakuje gwajin jinin?

Gobe da safe.

A asibitin ku ne.?

Eh nadiya tace gamida yin mika a zuciyar ta tana tunanin me yiwuwa nan da sati guda duk wannan hayaniyar ta wuce an fara shirye shiryen aurensu.

Yaya sunan wanda zai gwada jinin naku?
Nadiya ta dubi amira cikin mamaki.
Sunansa IBRAHIM kwanan nan yafara aiki a asibitin... Me yasa kike son sanin sunansa?
Nadiya ta karashe kalaminta da tambaya cikin mamaki.

Amira ta dauke kai gefe guda tace daman so nake in gargade ki da cewa Allah sa dai yana da sirri.

Nadiya ta dada kallon ta cikin mamaki akaro na biyu wannan karon akwai alamun kaduwa a fuskarta.
Amira... Me kike nufi da SIRRI.?
Nidai nasan lafiya ta Ƙalau kuma na tabbata Tijjani ma lafiyarsa Ƙalau to me muke bukata kuma da sirri.?

Amira ta zunkuda kafada tace.
Oh hakane fa kinsan wallahi abun naku ne duk ya rudani cikin sauri ta dubi agogon dake jikin wayar tafi da gidan ka dake hannunta.
Kai! Kai!! Kai!!! Wallahi na makara munyi da mijina biyar zan koma gida kafin yadawo kinga yanzu har shida saura kadan.

Nadiya ta dubeta cikin murmushi.
Uhm su amira masu maza muje to na raka ki.

Amira ta girgiza kai cikin sauri A'a bari nayi sauri natafi bama sai na wahalar dake ba zan dauki taxi... Kafin nadiya ta kuma cewa wani abu amira ta nufi kofar lambun da zata kaita farfajiyar cikin sauri tana cewa Naji yadda kuka kare da mutumin naki goben.

Nadiya ta bita da kallo cikin mamaki a rude. Me ke damunta ne? Nadiya ta tambayi kanta sannan saita zunkuda kafada ta nufi cikin gida abinta azuciyata tana cewa in ma Tijjani ne bata son na aura to saidai ta mutu da wa ya ce ta hadani dashi?

******* ******* ******* ******* ******* ********

Shigarsa dakin keda wuya sai Tijjani yaji gabansa yafara faduwa domin baisan ta inda zai fara yiwa mahaifan nasa bayanin shawarar daya yanke ta sakin matarsa batula ba dakuma shirye shiryen dayake na auren NADIYA MILONIYAKISAN BOKO-23

Shigarsa dakin keda wuya sai Tijjani yaji gabansa yafara faduwa domin baisan ta inda zai fara yiwa mahaifan nasa bayanin shawarar daya yanke

Please Login or Register in order to submit comment