Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun lura da cewa lallai yau Tijjani baya cikin walwala domin mutum kamar Tijjani mai yawan son hira da ban dariya yau yayi shiru baya son Magana da kowa to amma Abokan aikin sa basu damu da su tambaye shi dalilin shirun nasa ba don duk kusan wanda ke gurin nada masaniyar cewa Tijjani baiyi sa'ar mata ba. Wannan ita tasa sau dayawa koda wani abu ne na daban ya batawa Tijjani rai sai Abokan aikin nasa su alakanta hakan da matarsa.

Tijjani yau sake duban kofar gilashin akaro na Kusan arba'in sa'ar da wata bakar marsandi tayi fakin tabbas itace Tijjani yace cikin zuciyarsa Kwatsam wai wata siririyar mata fara tafito daga cikin motar sannan ta nufo shagon dauke da yar jaka ahannunta Tijjani yayi tsaki ya dauke kansa gefe guda.

Lokaci-lokaci Tijjani yakan dubi rigar dake jikinsa cikin damuwa don duk a cukwikwiye take babu guga domin sa'ar daya tashi da safe har karfe goma batula bata bude kofar dakin ba yayi iya kokarinsa da magiya akan ta bude dakin ya daki dutsen gugarsa amma taki wannan ita ta takura shi ya sanya kayan haka nan a cukwikwiye yafito da wuri dan kawai ya karasawa nadiya dinkunan ta kafin tazo. Koda yasake kallon rigar dake jikinsa saiya fara nadamar inama ace rigar daya sa jiya ita ya dada sakowa can kuma sai yayi tsaki sannan yace da kansa to menene ma amfanin damuwa shi yanzu wa zai yiwa wata kwalliya.. Nadiya dai kawar uwargidansa amira ce ina ruwansa da ita.

Bai dade da gama wannan tunanin ba sai wani almajiri ya yashigo shagon yace
Wai ana kiran Tijjani a waje sauran madinkan suka dubi Tijjani shikuma ya dubi almajirin yace wanene mai kiran Tijjanin?
Almajirin ya kifa kwanon sa aka sannan yafara tauna hannun rigarsa
Wata... Matace acikin mota wai tace kayi sauri
Tijjani na jin haka sai jikinsa ya bashi cikin sauri ya yi zumbur ya dauki ledar daya zuba dinkunan kayan sannan yabi almajirin abaya zuciyarsa na harbawa.

Awannan karon acikin wata falleliyar Honda hala tazo fara sol da ita sai sheki takeyi kamar Mudubi tun kafin ya karasa inda take nadiya ta bude kofar motar ta zuro kafar ta waje kana ta haskake shi da murmushi kyawawan hakoranta masu kyau gani jere farare sol kamar takardu suka bayyana afili.
Daman kasan ni ce ko ka ga zuwana ne?

Tijjani jikinsa na rawa ya mika mata murmushin da tayi masa a tsorace yake.
Jikina ne yabani cewa ke ce kika zo.. Tun...Tun dazun nake jiran ki nadiya ta lura da cewa duk a rude yake Don haka saita boye murmushin tace.
Harka gama min dinkin? Tijjani ya gyada kai cikin sauri ya mikawa nadiya jakar Duba ki gani sunyi? Nadiya ta girgiza kai cikin murmushi Bama sai na duba ba ai na yarda dakai nasan ma sunyi. Ta jefa jakar a kujerar baya ta motar sannan ta sunkuyar da kai gamida tausasa murya tace.
Idan bazaka damu ba zan so mu tafi gidanmu tare dakai yanzu Tijjani yaji zuciyarsa ta harba tsakanin hakarkarinsa bai taba tsammanin zai sake jefa kodaddiyar kafarsa acikin wannan kyakkyawan Gida ba.

Yanzu.... Yanzu kokuwa idan an jima nadiya ta girgiza kai tace
Nidai yanzu nake son mu tafi ta danyi shiru tana dubansa ta kuma lura da rigarsa duk a cukwikwiye tace oh nashiga Uku yau kuma ko kokowa sukayi da matar tasa? Tace cikin ranta sannan ganin Tijjani ya rasa ta cewa sai tace.
Kada ka damu nima nasan aiki yayi maka yawa amma ba dadewa Zakayi ba yanzun nan zaka dawo so nake ku gaisa da Mahaifiyata.

****** ***** ***** ***** ****** ****** *********

Tijjani na bin ta abaya zugum zugum kamar tunkiya suka ratsa ta cikin wani katon dakin shakatawa wanda yafi wancan Daya shiga ajiya kyau da kawa duk inda Tijjani ya taka saiyaji kafar sa kamar zata lume acikin tattausan kilishin daya mamaye ko ina haka nan duk dakin shakatawar da suka gifta saiyaji wani ni'imtaccen kamshi mai sanyaya rai ya bugi hancinsa sannan ahankali suna tafiya har suka wuce dakunan shakatawa shida sannan ne to nadiya ta tsaya awata kofa mai kyaun gaske launin sararin samaniya anyi mata ado da ruwan gwal. Akaro na farko tun sa'ar da suka shigo gidan sai nadiya ta dubeshi da murmushi tace.

Mun Karaso Tijjani saika saki jikinka ku gaisa sosai da mamana dan ita babu ruwanta... Tana da fara'a Tijjani ya gyada kai kamar kadangare domin bashida abun cewa.

Nadiya ta bude kofar ahankali suka shiga dan madaidaicin dakin shigar su keda wuya sai Tijjani yayi ido biyu da wata dattijuwar mace fara doguwa sanye da doguwar riga fara tana tsaye a tsakiyar dakin rike da tasbaha shudiya kanta lullube da Katon mayafi matar ta dubi Tijjani da busashshen murmushi sannan tace
Sannu da zuwa Tijjani tun dazun ai nake sa ran zuwana.

Cikin sauri Tijjani ya durkusa har kasa ya gaisheta matar ta amsa cikin fara'a sannan tace.
Nagode Tijjani ka kyauta Ai da kazo muka gaisa.. Allah yabar ku tare Yakuma nuna mana alherinsa Ameen.

Tijjani yayi sororo dashi kai kace zantukan dayake ji baisan me ake nufi dasu ba.

Nadiya ta dubi Tijjani da murmushi sannan tace.
Mama zan koma na mayar dashi gurin aikin sa dan sauri yakeyi dattijuwar matar ta dube su da murmushi tace.
Wannan ma zuwan daya yi ai mun gode Allah yabar ku tare Tijjani ya Mike tsaye gwiwowinsa na rawa kamar bazasu iya daukarsa ba.

Toh zan koma.... Mama nagode sai anjima.

ASHE DAI...KISAN BOKO-15

To Tijjani Allah kiyaye da haka sai nadiya ta juya da murmushi. Tijjani yabita abaya kwakwalwarsa dauke da tambayoyi sama da goma sha biyu duk babu amsoshin su saukin al'amarin yayi yawan yace a zuciyar sa.

Tijjani yaci gaba da binta abaya batareda yasan inda zasu ba lokacin lokaci ta kan dan waigo fa jefe shi da murmushi ahaka dai har suka kawo kofar wani daki nadiya ta dauko wani dan makulli ruwan gwal ta bude kofar ga mamakin Tijjani saiya ji sassanyar iska ta bugi hancinsa gamida kamshin furanni kofar bata daki bace lambu take kallo kai tsaye akwai matattakala ta farin dutse wacce ke gangarawa har zuwa cikin lambun nadiya ta gangara zuwa cikin lambun ta matattakalar ta farin dutse.

Tijjani na biye da ita abaya sannu ahankali har suka zo bakin ramin wankan nan dake cikin lambun fararen kujeru guda biyu da suka zauna ita da Amira akai adaren jiya na nan ba'a dauke su ba haka nan teburin nan na gilashin mai kafafu uku shima yana nan amma dauke yake da kayan shaye shaye iri iri.

Zauna mana. Nadiya tace da Tijjani cikin murmushi Tijjani ya zauna itama ta zauna sannan suka fuskanci juna.

Kikace ba dadewa zanyi ba. Nadiya bata dube shi ba saita ci gaba da tsiyaya masa abin sha acikin kofin tangaran lokacin guda tace kada ka damu yanzun ma ba dadewa Zakayi ba...
Tijjani ko har ka gaji da gidan namu?

Tijjani ya girgiza kai sa'ar dayaji kamshin furanni da sassanyar iska sun fara yi masa wanka.

Ni na isa nace gidanku ya isheni.

To menene na gaggawar tafiya?
Tijjani ya gyara zama yace saboda aiki yayi mana yawa kinga babbar sallah ta karato.

Nadiya ta dube shi da murmushi sannan ta mika masa kofin zuwan zaki mai sanyi.
Ga wannan kasha na fuskanci in ba baka nake da hannuna ba sai ka ki sha dan jiya ma da kyar ka sha rabi.

Cikin murmushi Tijjani ya karɓa ya dan kurbi sassanyar ruwan lemon sannan ya ajiye kofin ahankali.

Karfe nawa kuke tashi daga gurin dinkin ne? Tijjani ya dan sunkuyar dakai sa'ar da iskar tafara huro kamshin turaren dake jikinta zuwa hancinsa.

Karfe goma na safe muke budewa sannan mu rufe karfe goma na dare zuwa sha daya nadiya ta girgiza kai gamida zazzaro idanu.
Awa goma sha biyu kenan fa kai yayi yawa wannan ai sai mutum yayi mutuwar tsaye gaskiya yakamata ka sami Sauyin aiki ba Kanada DIPLOMA ba?

Tijjani ya fashe da dariya yace hajiya nadiya kenan in banda abin ki mai digiri ma yaya yayi da kansa wajen neman aiki ballanta me diploma. Nadiya ta dube shi gamida murmushi tace gaskiyar ka Tijjani.

Ta danyi shiru sannan saita sauya zancen.
Ina matar ka tana lafiya? Tijjani yaji wani abu ya soki kirjin sa yanzu haka ma tana can kaca kaca ko shara batayi ba yace cikin zuciyarsa.

Tana....nan lafiya Tijjani yace da ita bakinsa na rawa.
Gaskiya matar ka tayi sa'a Tijjani... Data sami miji kamar ka Tijjani yaji abinda tace amma bai ce komai ba sai kawai yayi murmushin yake.

Nadiya ta tsinko wani kyakkyawan fure fari daga jikin yar dukurkusar bishiyar fulawa dake daf dasu tafara juyashi ahannu.

Yanzu kuwa Tijjani kana tunanin sake aure?
Tijjani ya sunkuyar dakai tsawon lokaci kansa a sunkuye ga mamakin nadiya sai taga Tijjani ya dauki kofin lemo ya tsiyaya lemo acikin sannan yasa a bakinsa ya zuke lokaci guda ya ajje kofin kwasss da karfi akan teburin me kafa uku kana ya dubeta ido da ido. A zuciyarsa yana tunanin kalaman Amira.

Meyasa kikayi min wannan tambayar nadiya? Nadiya ta sunkuyar da kai kasa domin ba zata iya hada ido dashi ba.
Wani abu ne acikin zuciyata.
Sai tafara dariya saita rufe fuska sannan cikin sauri saita gyara zama kai kace wata yar karamar budurwa ce.
Wani sirri ne boye cikin zuciyata..... Sirrin da bazan iya fadama da bakina ba. Tana gama fadin haka saita miko masa wata farar ambulan sannan ta mike tsaye tace.
Idan kaje gida kayi kokari ka karanta sakon dake cikin nan ta jefe shi da murmushi Tijjani ya karbi ambulan din cikin tsananin mamaki da dokin sanin abunda ke ciki.

Toh Ai... Nadiya ta katse shi ta hanyar daga masa hannu tana murmushi tace.
Don Allah....kayi shiru nasan Kanada tambayoyi da yawa a bakin ka ina son ka sani cewa duk amsoshinsu yana cikin ambulan din nan Tijjani ya Mike tsaye gamida juya ambulan din ahannunsa kamar wanda ke dauke da mushe.

Zo muje na mayar dakai nadiya tace dashi zugum zugum farar ambulan din ahannunsa yabita abaya Koda suka fara fita daga cikin lambun sai nadiya tace.
Kada ka manta idan kaje gida ka gaisar da matar ka.

****** ****** ****** ******** ******* **********
Karfe goma sha daya na dare ya isa gidan tun kafin ya karasa kofar gidan yaji gabansa yafadi baisan dalilin Faduwar gaban ba amma me yiwuwa hakan na da nasaba ne da kofar gidan daya gani Wangam-Gam abude wannan bakon al'amari ne a gare shi domin ya riga yasan batula tanada matukar tsoro idan dare yayi bata iya barin kofar gidan a bude wata sa'ar ma idan ya dawo saita bude masa saigashi yanzu karfe goma sha daya na dare kofar a bude.
Zuciyarsa na harbawa ya shiga gidan.....KISAN BOKO-16

Zuciyarsa na harbawa ya shiga gidan tun daga zaure yau hangi tsakar gidan a haskake tabbas akwai wuta to saidai kuma kauri-kaurin daya bugi hancinsa shi ya hana shi murna da hasken wutar Lantarkin. Jikinsa na rawa yau shiga tsakar gidan lokaci guda kuma idanunsa suka kai ga tarin jujin dake tsakar gidan domin daga nan hayaƙin marar dadin shakar yake tasowa jikinsa na rawa ya karasa inda jujin yaje sannan ne to ya hangi wuyan sabuwar rigar sa ta shudiyar shadda bata gama cinyewa da wuta ba Koda Tijjani ya dubi tarin tokar dake gurin saiyaji kamar zuciyarsa zata fado saboda bakin ciki ko shakka bayayi suturar sa ne agurin aka kona jikinsa na rawa zuciyarsa na tafarfasa ya nufi cikin dakin.

Batula! Ya kirata cikin karaji abunda bai taba yi mata ba tunda suke da shi. Shiru ta gaishe da kunnuwan sa.
Batula ya kuma kwalla mata kira shiru. Dayake dakunan duk a haske suke da kwayayen lantarki sai Tijjani ya wuce kai tsaye zuwa dakin da suke kwana baiyi mamaki ba sa'ar daya ga duk dakin a yamutse kamar filin yaki komai a birkice zanen gadon an jefar dashi a tsakar dakin haka nan jakar dayake ajiye suturansa na sawa babu komai aciki sai wata tsohuwar safarsa mai kamar hanji.

Sannan kuma daya akwatin da batula ke zuba nata kaya aciki babu ita tabi iska.
Jikinsa na rawa Tijjani ya zauna akan gadon jagwaf domin ji yake kamar zai sume daga tsaye yana zama saiyaji kansa yafara sarawa kamar zai tsage Gida biyu saboda ciwo yasa hannayen sa biyu ya matse kansa ji yake kamar ya cilla ihu duk duniyar tayi masa zafi.

Yanzu ashe matar danake kauna nake muradin zama da ita har abada nake kiranta RUHINA itace zata ƙone min suturana?
Tijjani ya tambayi kansa.

Sannan ne to tunanin farar ambulan din da Nadiya ta bashi ya fado masa hannunsa na rawa kamar mazari ya zaro ambulan din ya budeta sannan ya gyara zama duk kuwa da cewa dakyar idanunsa suke iya gane Rubutun yafara karantawa.

BA wata doguwar wasika bace kamar yadda ya tsammata bayan sun rabu da nadiya wannan wasikar dake hannunsa layi goma ne kacal wasikar tace.

DAGA MAI MAFARKIN ZAMA MATAR KA.
me yiwuwa ka dauke ni mahaukaciya kokuma shashasha. Me yiwuwa kayi min dariya kokuma kayi min tsaki to koma dai me Zakayi min Tijjani ina son ka sani cewa acikin awa ashirin da hudu dana yi da ganin ka sainaji duk duniya babu wanda nake kauna nake Fatan ya zama miji gareni sai kai Tijjani.

Nasan nayi araha dayawa na karya darajata a matsayina na mace amma babu yadda na iya da raina ne domin shi SO sartse ne bakasan lokacin da zai shige ka ba tambayar danake son yi agare ka shine.
Shin zaka aure ni? Kada kayi tunanin talaucinka Tijjani domin ina da arzikin da har iya rayuwar mu bazamu iya cinye shi ba ni da kai koda bama aikin idan kuma kana tunanin rashin sabo ne to ina son ka sani cewa ni ayanzu ji nakeyi kamar nayi shekara ashirin da sanin ka Tijjani nabaka sati guda kayi tunani nagode sai anjima.
NICE NADIYA... MAI MAFARKIN KAUNA.

Nashiga Uku Tijjani yace cikin zuciyarsa lallai amira ta fadi gaskiya wannan matar mahaukaciya ce indai tana son abu yace a ransa wani zazzafan gumi yafara wanke masa fuska kamar ruwa cikin karfin hali ya mike tsaye yabaro dakin zuwa cikin dan kankanin falon mai kamar akurki wanda girmansa baikai ko rabi rabin dakin maigadin gidansu nadiya ba jikinsa na rawa ya zauna akan kujerar sai yaji rumumus ya zauna akan wani abu mai kamar leda haka nan shiyasa shi ya dada mikewa zumbur kamar wanda yayi ido biyu da maciji koda Tijjani ya dubi ledar da kyau sai yaga ashe ledar nan ce daya kawo leshin da nadiya ta bashi acki baiyi mamaki ba sa'ar daya ga sai ledar ita kadai babu leshin acikin wannan shiyasa wani zazzafan gumi ya karyo masa numfashinsa ya dauke sannan ya zargi kansa da wauta da tsaban sakaci dazu da safe da zai tafi gurin aiki ya cire Wandon dake jikinsa ya sakale wani acikin aljihun Wandon daya cire akwai naira dubu goman da nadiya ta bashi saboda rashin rabo maimakon ya dauke kudin saiya bar su cikin aljihun Wandon sannan ya dora ledar leshin akai yabar su akan kujerar.

Ayanzu da yayi tsaye sororo gumi na zuba kamar ruwa sai ya hangi Wandon akan kujerar hannunsa na rawa ya dauki Wandon duk kuwa da cewa ya sani ko shakka ba yayi bazai samu dubu goman aciki ba Tijjani ya zura hannunsa acikin aljihun Wandon ga mamakin sa saiyaji wani abu kamar takarda yana zarowa saiyaga ashe takardar naira dari biyar ce da wata yar guntuwar takarda mai dauke da guntun sako. Tijjani yafara karantawa kamar haka.
.........Natafi Nabar maka gidanka matsiyaci ga naira dari biyar nan na tausaya na bar maka nasan ta ishe ka kari ko?

BABI NA HUDU
Ranar Laraba da misalin karfe tara da yan mintuna na safe Tijjani ya shiga wani dan.....KISAN BOKO-17

BABI NA HUDU
Ranar Laraba da misalin karfe tara da yan mintuna na safe Tijjani ya shiga wani tsukakken layi mai yawan jama'a da kuma tarin kwatoci da tarin shara tsibi tsibi ko ina Tijjani yaci gaba da tafiya cikin layin lokaci-lokaci yakan dan tsaya domin yabar kananan yaran dake giftawa ta gabansa su wuce da yawa daga cikin yaran wasa sukeyi da gare-gare da tayoyi wasu kuma suna ta kokarin tafiya makarantar safe a makare.

Tijjani yayi mamakin dalilin dayasa haryanzu mutanen wannan kwararo basa son yin shara.
Rabon Tijjani da shigowa wannan layi tun kafin aurensa da batula. Ada can baya iya yin sati guda sai ya ziyarci babban abokinsa Abdul amma bayan da akayi dan cece-ku-ce akan maganar auren batula sai dangantakar tasu tayi tsami wannan shi ya yanke musu zumunci kowa ya daina ziyartar kowa saidai Idan an hadu ahanya su Gaisa.

Al'amarin yayi matukar batawa Abdul domin shi a tunaninsa tijjani ya raina shi yaki daukar shawararsa saboda yana ganin shi bashida ilmin zamani domin shi babansa babban malami ne makarancin alkur'ani mai tsarki.

Wannan ita tasa sa'ar da Tijjani ya nufi gidan sai yaji gabansa yana faduwa domin baisan irin karbar da Abdul zaiyi masa ba gashi kuma ya sami kansa acikin matsalar da duk duniya babu wanda yake tunanin zai iya shawarta sai babban abokinsa Abdul.

Tun daga nesa Tijjani ya hangi katuwar rumfar dake kofar gidansu Abdul makil da almajirai sunata karatu yayin da wasun su kuma ke ta faman wankin allo wasu ko suna Rubutu kasancewar yau Laraba ce ranar wankin Allo.

Tijjani ya isa kofar gidan jikinsa a sanyaye yana waige-waige sai ya hangi MALAM TANIMU mahaifin Abdul zaune a tsakiyar almajirai da bulala a hannu. Tijjani ya matsa kusa yacire takalminsa ya ratsa ta tsakanin almajiran ya isa ga malam TANIMU ya durkusa a gabansa ya gaishe shi cikin girmamawa.

Tijjani....kwana biyu ko tafiya kayi? Tijjani yayi murmushi
Ina nan wallahi baba al'amuran rayuwa ne kawai malam ya gyada kai yace.
Toh Allah rufa asiri.. Ai Abdul din yana cikin shagon zaure yana Rubutu Tijjani ya Mike tsaye.

Bari to naje na same shi ya sake ratsawa tsakanin kolawa da gardawan ya shiga zauren gidan sannan kai tsaye ya shiga katon shagon gamida sallama.
Abdul zaune shi kadai acikin shagon akan farin buzu wani fankadedden allo irin na gardawa ahannunsa yana ta Rubutu karkar-karkar baya ko kuskure kamar yana bugawa da keken Rubutu Abdul ya dago kai ya dubi Tijjani cikin tsananin mamaki.

Yau wa nake gani haka? Tijjani ya dube shi da murmushi sannan ya zauna akan wani bakin buzu dake kusa da Abdul.
Tijjani ne kake gani cikin murmushi Abdul ya jingine allon jikin bango kana ya rufe kurtun tawadar ya dora alkalamin akai ya tura sa gefe guda sannan ya dubi Tijjani yace.

Ina fatan dai lafiya? Tijjani ya gyara zama kana ya dubi katon dakin mai tagogi guda biyu daya yana kallon waje dayar kuma tana kallon tsakar gidan daga ina Abdul yake zaune yana iya hangen kan tabaryar da matan gidansu ke daka haka nan akwai alluna sama da guda dubu acikin shagon duk a jere wani akan wani ajikin bangon daga saman allunan kuma gafakaken alkur'ani ne duk a rataye saman dakin Ruffin azara ne wanda ke lullube da yanar gizo-gizo ko ina duk wannan Tijjani ya lura dasu ne daga cikin kallo daya Tijjani ya dada gyara zama yace.

To lafiyar kenan ya sunkuyar dakai yana wasa da alkalamin akan buzun baisan ta inda zai farawa Abdul zancen ba Abdul ya dubi Tijjani cikin damuwa yace.
Batula ce ko? Tijjani ya dago kai ya dubeshi kana ya gyada kai.

Daman nasan zaka dawo gareni nasan ko ba dade ko ba jima saika dawo gareni domin ni nasan wannan matar taka kyawun dan maciji gare ta ya dan yi shiru yana kokarin kankare bakin tawadar daga kan karfensa.

Ina fatan dai ba fada kukayi ba? Tijjani ya rufe bakinsa sa'ar da wata doguwar Hamma ta kufce masa domin bai karya ba yafito saboda bacin rai.

Abin ma yafi da haka Abdul har kona min kaya tayi.. Takum sace min kudi naira dubu goma da leshi... Kodayake leshin din ita akace na baiwa Abdul ya rike baki cikin kaduwa.
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN ta kona maka kaya ta sace ma kudi da leshi?

Tijjani ya gyada kai tabbas kamar yadda nafada ma tun farko kafin ka aure ta wannan ba matar kirki bace domin duk matar da zata bude baki ta zagi iyayen ka tayi maka barna to rabuwa da ita yafi alkhairi.

Tijjani ya share gumi daga fuskarsa.
Wannan shine dalilin dayasa nazo gurinka domin na baka hakuri na kuma fada ma cewa zanyi mata saki uku sannan kuma nafada ma cewa HAR NA SAMU MATAR AURE.

Abdul ya zabura cikin mamaki yana duban Tijjani kamar tababbe.
Ka sami matar aure a ina kuma Tijjani ya gyara zama sannan saiya fara bashi labarin haduwar sa da Nadiya.

Tsawon mintuna arba'in suka kwashe Tijjani yana baiwa Abdul labarin Nadiya Abdul yayi ajiyar zuciya Sa'ar dayaji Tijjani yagama bashi labarin kana ya dube shi cikin kaduwa yace.
Haryanzu Tijjani bakada hankali yanzu ashe duk abunda yafaru a kanka na batula bai isheka darasi ba? Ya danyi shiru yana mayar da numfashi.
Haba Tijjani yaya daga haduwar ja da mace kwana uku kawai har zaka fara tunanin auren ta?

NADIYA ABDUL YAFARA LALATA MIKI SHIRI FAKISAN BOKO-18

Haba Tijjani yaya daga haduwar ka da mace kwana uku kawai har zaka fara tunanin auren ta?

Bani nace zan aure ta ba itace tace zata aureni... Kuma wallahi tafi batula kirki nesa ba kusa ba domin ita tana sona Tijjani yace yana kallonsa.

Abdul ya girgiza kai yace.
Kai Tijjani wannan labarin naka yafi kama da tatsuniyoyi da wasanni matar nan kace tanada tarin dukiya kace ta girme ka kace kuma likita ce... Kai ni wannan matar bata kwanta min Arai ba ni ji nakeyi kamar irin matan nan ne yan damfara kokuma lalatattun karuwan nan na zamani.

Tijjani ya muskuta cikin damuwa ya rigaya dama yasan sai sun kai ruwa rana da Abdul shi ko acikin dogon tunanin dayayi jiya ya rigaya ya ya yanke cewa indai har nadiya da gaske take yi babu abunda ya kamace shi sai kawai ya aure ta don ya rama wulakancin da batula tayi masa Yakuma kona mata zuciya domin duk da yasan ba wani kaunar sa takeyi ba hakan bazai hanata kishin sa ba.
To saidai kuma abunda yafi damunsa ayanzu shine in har Abdul bai goyi bayansa ba dole ne duk irin son aurensa da Nadiya ya hakura domin bazai taba kaunar irin rashin fahimtar daya faru akan batula yasake faruwa ba domin haka yanzu saiya yanke shawarar kawai ya lallabi Abdul ahankali domin acan gefe guda yasan zai iya batawa Amira rai idan yaki auren Nadiya.

Abdul kaine fa lokacin da za'ayi aurena da batula bata sona.. Amma ita wannan nadiyar ta nuna tana matukar kaunata wallahi bakaga yadda take tarairayata ba Abdul ya shafi kansa sannan sai ya dubi Tijjani da wnai busashshen murmushi yace.
Dole ne ta tarairayeka tunda so take ta cuce ka to bari kaji in fada maka wani sirri dake tattare da irin wannan mata wanda kai baka sani ba duk kuwa da cewa kai ma dan boko ne kamar ta to amma zan iya cewa anan din nan danake zaune ina hulda da yan boko fiyeda kai albarkacin almajiranci.

Abul ya danyi shiru adaidai lokacin da wani dan gajeren yaro mai katon kai a aske kamar molo yashigo dakin.
Koma... Idan anjima ka dawo Abdul yace da almajirin tun kafin ma yaron yace wani abu bayan yaron ya fice sai Abdul yadawo da hankalin sa kan Tijjani sannan yace.
Saurara dakyau Tijjani domin na fayyace maka cikin sa da baya na irin wayannan mata. Kamar yadda kace shekarun ta kusan talatin da biyar toh duk ire iren su haka suke da gangan suke kin aure saboda zuciyoyinsu sun bushe sun shagala d rayuwar duniya abinda ke gaban su kawai shine sharholiya da mazajen duniya shagalallu sannan ahankali suna cikin wannan hali bazasu yi aune ba sai su ga shekaru sun taru a kansu don haka sai su fara lalubar yara masu danyen jini irin ku suna son su aura inafatan kana fahimtata?

Tijjani ya gyada kai sannan yace bakisan na rawa Abdul ban tari numfashinka ba amma ina ganin yakamata mu yiwa nadiya kyakkyawan zato tunda akalla dai aure ta neme ni dashi ba wani abu ba Abdul ya girgiza kai yace cikin damuwa.

Na yarda dakai Tijjani gaskiya Kamata yayi muyi mata kyakkyawan zato tunda dai ba duka aka Taru aka zama daya ba amma duk da haka bazan iya shawarartar da ka auri wannan mata kai tsaye ba domin rayuwar ka tana cikin matukar hatsari ayanzu don zaka yi mamaki idan nace dakai dana baka shawarar ka auri wannan mata kai tsaye gara

Please Login or Register in order to submit comment