Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa dashi ta zauna da murmushi sannan saita Mika masa littafin hotunan tace.
Ga wannan kayi kallo kafin ka tafi ko?

Hannunsa na rawa ta karbi album din zuciyarsa yana Allah Allah ta sallame shi kada mijinta yadawo ya same su.

Nadiya ta janyo wani dan karamin teburi na gilashi gabansa sannan ta mike ta nufi wani dan dukurkushin firji ta dauko wasu kofunan tangaran masu ruwan garai dauke da tataccen ruwan lemo kore shar ta ajiye akan teburin sannan tace da Tijjani.

Idan ka gama kallon sai ka sha wannan ko? kayi hakuri abin ba yawa Tijjani ya dago kai daga kan littafin hotunan yace.
Nagode Wallahi bakomai.

LA! Tijjani harda su godiya abin nawa yake dan lemon kawai dana kawo ma ai nice da godiya da ka biyo ni har gida zan saka aiki tunanin matarsa batula yafado masa yaga tunda ya aure ta yake wahala da ita amna bata taba gode masa ba.

Tsawon lokaci Tijjani yana kallon kyawawan hotunan wanda mafi yawa daga cikinsu duk na biki ne yayinda ita ko nadiya tayi amfani da wannan damar ta kare masa kallo a zuciyarta tana cewa lallai kam komai zai faru bazan taba bari wannan damar ta wuce ni ba ga mamakin nadiya sai ta ji Awannan lokacin datasa saurayi Tijjani agaba tana kallo saita ji bata ma damu da cewa saiya so ta tsakaninsa da Allah ba.

Ayanzu kam koda ta hanyar amfani da dukiyar ta ne saita aure shi menene to amfanin kudin? Baka sami abunda kake so ba aduk lokacin da kayi niyya ba? Ta tambayi kanta.

NI ZAN TAFI ina kayan suke? Tijjani yace da ita sa'ar daya gama kallon hotunan.

Nadiya ta Harare shi cikin wasa.
Haba Tijjani daga zuwanka kamar wanda ake kora dubi fa ko lemon ma baka sha ba.

Tijjani ya dauki lemon ya dan kurba sannan yace. Gashi na sha ni zan tafi kya gaishe min da maigidan ki.

Nadiya ta fashe da dariya tace
Au Daman don haka kake tunanin guduwa? Ka dauka inada aure ne?

Tijjani ya dubeta cikin tsananin mamaki yace.
Kina nufin kice bakida aure?

Nadiya ta gyada kai lokaci guda kuma ta dauke kafafun ta sama ta mayar dasu kan kujerar tace.
Kasan yan boko mukan dade bamuyi aure ba shekarata kusan takwas har da yajin aiki ina karatun likita a jami'a.

Tijjani ya gyara zama ya dubeta cikin girmamawa. Kina nufin kice ke likita ce?

Nadiya ta gyada kai Tijjani yace cikin murmushi Angaishe ki mace da kamar maza.

Nadiya ta fase dariya sukayi shiru na dan lokaci sannan sai suka dago kai suka dubi juna idanun nadiya dauke da wani sako. sakon da babu mai iya fassara shi sai kwararren masanin al'amuran mataKISAN BOKO-10

Nadiya ta gyada kai Tijjani yace cikin murmushi Angaishe ki mace da kamar maza.

Nadiya ta fase dariya sukayi shiru na dan lokaci sannan sai suka dago kai suka dubi juna idanun nadiya dauke da wani sako. sakon da babu mai iya fassara shi sai kwararren masanin al'amuran mata

Kaifa Tijjani Kanada aure? Nadiya ta tambaye shi duk kuwa da cewa tasan yanada shi din Tijjani yaji kamar kada yafada mata domin yasan auren sa kafi babu ne.

Ina...dashi yace bakinsa na rawa.
Matan ka nawa? Nadiya ta tambaya
Matana ashirin suka fashe da dariya.

Don Allah kafada min matan ka nawa iye
Tijjani?

Tijjani ya dago kai ya dubeta yace.
Matata daya.

Nadiya ta sunkuyar da kai sannan saita sanyaya murya tace.
Kunji dadin ku masu aure kullum kuna tare kuyi hirar ku mai dadi kuci abinci tare ku sha tare ku baiwa juna labarin duniya cikin nishadi da soyayya.... Mu ma Allah bamu masu son mu... Nadiya tace kamar zatayi kuka Tijjani yaji tausayin ta Yakamashi lokaci guda kuma yana mai mamakin shin me zaisa miji yayiwa wannan mace mai tarin arziki wahala.?

Allah zai baki... Insha Allahu...

Nagode Tijjani. Nadiya tace muryarta akarye sannan saita miko masa katuwar jakar ledar tace.
Gasu nan leshina ne guda uku ka zabi dinkin da kaga ya dace dani kayi min gobe zanzo da yamma Tijjani ya karbi jakar gamida mikewa tsaye.

Sai yaushe kenan Tijjani?

Bazaki zo karbar dinkin ki gobe ba?

Nadiya ta mike tsaye tace.
Toh sai nazo goben kenan nagode Tijjani nagode sosai.

Suka nufi kofar fita daga falon.
Ki tsaya ma anan sai gobe nadiya ta girgiza kai tace
A'a bari na raka ma ma mana kamata yayi ma na mayar dakai har can.

Tijjani ya girgiza kai yace Haba ranki ya dade ni na isa ki koma kawai daga nan nadiya ta sunkuyar dakai tana wasa da yan yatsunta.

Toh nagode.... Kuma dan Allah ranki ya dade din nan ta fita daga bakinka sunana NADIYA. Okay?

Tijjani ya gyada kai da murmushi.

Nadiya ma ta dube shi da murmushi sannan tace.
Uhm... Idan ka duba cikin ledar zaka ga Leshinan guda hudu ne... Ka baiwa matar ka daya daga cikin shudayen leshin guda biyu tana gama fadi saita juya tabar shi agurin tsaye baki bude.

Nagode Allah ya saka miki.

Nadiya ta dan tsaya amma bata juyo ba.

Ka gaishe min da ita sosai kace nace da ita tana daya daga cikin mata masu sa'a aduniya.

Har sa'ar da Tijjani yakai ga farfajiyar gidan bai lura da zankala-zankalan jiminonin ba saboda tsabar sake-saken zuci.

KASHI NA UKU.........KISAN BOKO-11

Har sa'ar da Tijjani yakai ga farfajiyar gidan bai lura da zankala-zankalan jiminonin ba saboda tsabar sake-saken zuci.

****** ****** ****** ****** ******* ****** *****

KASHI NA UKU

Ga al'adar su basa rufe shagon dinkin sai karfe goma sha daya na dare amma Awannan ranar tun karfe tara suka rufe shagon kowa ya kama gabansa.

Karfe tara da minti goma kacal Tijjani ya isa gida sakamakon dan kabu-kabun daya hau da ace tafiyar kasa ce kamar yadda ya saba sai ya shafe mintuna Kusan arba'in baije gida ba.

Tun kafin ya shiga gidan yaji zuciyarsa tana ta harbawa domin ko shakka ba yayi yasan yau sai sun debo tsamiyar miyagu shi da batula. To a abanza ma suna masifa ballantana ya mare ta.

Aduk tsawon wannan rana babu wani abu dake zuciyar Tijjani sai tunanin nadiya tunanin mutuncin ta, karramawarta, kulawarta, dakuma iya hirar ta abinda ke bashi mamaki shine gata dai ita ba yarinya budurwa ba domin yasan ta girme masa nesa ba kusa ba amma dan zama da sukayi da ita saiyaji bai taba samun wani farin ciki makamancin wannan ba aduk iya tsawon watanni hudu da suka yi tare da matarsa yar shekara goma sha takwas kacal ba.

Tijjani ya cika da mamaki sa'ar daya dawo shagon dinkin domin buda ledar data bashi keda wuya zai fito da lesunan sai kudi suka zubo daga ciki Naira dubu goma ne daidai.

Ga wannan.... Inajin kudin dinkin ne ta hado dasu aciki Tijjani yace gamida mikawa uwargidansa amira kudin.

Amira ta girgiza kai cikin murmushi.
Haba Tijjani ai ko kai kayi min fada idan na karbi kudin dinkinta bani fa da wata kawa da ta fita aduniya.

Tijjani ya juya kudin ahannunsa yana mai al'ajabi.

Toh wannan kudin menene? Murmushin amira ya fadada.

Naka ne kai ta baiwa. Tijjani ya girgiza kai idan nawa ne kamata yayi tun daga can ta bani da hannunta.

Kai baka san nadiya bane ai haka take idan tayi niyyar yiwa mutum kyauta tun da nake ban taba ganin mace mai sakin hannun nadiya ba ta danyi shiru.

Ka rike kawai Tijjani na fada ma wallahi kai ta baiwa rashin sa'a ma kayi da saidai ka ga mota zugudum ta fado daga cikin jakar.
Gaba daya shagon madinkan aka bushe da dariya.

Don haka a yanzu da Tijjani yanufi kofar gidansa gabansa na faduwa saboda tsoron masifa. Dauke yake da shudin leshin da nadiya tace ya baiwa matarsa aljihunsa kuwa dauke da naira dubu gomansa cif cif yaso ya biya ya sayo musu kayan lashe lashe to amma ayanda suka rabu da batula yau cikin masifa yasan duk abinda yakawo saita jefe shi da shi hatta leshin dake gurinsa ayanzu yana shakkar in zaice da ita nata ne aka bata. yadai danganta da irin halin daya sameta aciki.

Cikin sanda jiki na bari ya shiga cikin gidan.
Salamu Alaikum. Yayi sallama kamar yadda ya saba duk kuwa da yanada masaniyar cewa sau biyu kawai ta taba amsa masa sallama wannan kuwa tun kwanaki biyun daren amarcinsu ne na farko.

Duk da yake babu wuta a lokacin daya shiga gidan hakan bai hanashi ganin tarin kwanuka ba tsibi-tsibi ko ina a tsakar gidan duk babu wanki haka nan Agefe Guda daga jikin katangar tarin shara ne tsibi guda kuma wani abin karin bakin ciki igiyar daya shanya fararen kayansa guda uku ta tsinke ta fado kan juji batula bata damu da ta dauke masa su ba Allah ne yasan tun sa'ar da kayan suka fado yace a ransa Tijjani yashiga dan falon nasu mai kamar akurki a tsorace yana shiga saiya iske fitilar kwai a tsakar dakin a kunne hakan nan duk dayake sabuwa ce kasan ta ya bude kalanzir sai naso yakeyi akan ledar tsakar dakin haka nan a kwance akan yar doguwar kujerar mai kama da makara kanta babu dan kwali gashin kanta bucucu kamar gonar rogo batula ce tayi rigingine idanunta sharkaf da hawaye taci uban kuka har ta gaji.

Tijjani ya ajiye jakar ledar Agefe Guda sannan ya matsa kusa da ita zuciyarsa na harbawa yace. Batula...

Bata motsa ba ballantana ma ta kalle shi Tijjani ya tsammaci haka tun farko don haka sai yau zauna agafen kujerar tun kafin yagama gyara zama batula ta zabura ta janye jikinta gefe guda ta takure tana zazzare idanu.
Kada ka tabani kaji ko? Matsa daga kusa dani

Tijjani bai dubeta ba ya dada gyara zama.
Bataba ki zanyi ba...

Me kazo yi to? sake dukana?

Tijjani ya girgiza kai.
BA wannan bane nufina abunda nake so batula shine mu kafa sabon harsashin zaman lafiya nida ke Awannan daren.

Batula ta zabura kamar wacce aka soka da kibiya tace.
Zaman lafiya? Dakai? Kana matsiyacinka mai hannun dukan mata za'ayi zaman lafiyar? Cab sabon salo wai kaza taji shikar dare. Ta dauke kai gefe guda

Tashi ki dauko min abinci.

Banyi da kai ba don haka ka kyale ni kawai malam Nasha iska.

Tijjani yaji zuciyarsa tayi kuna tana tafasa. Adaidai lokacin ne wani katon bera baki ya surnano aguje daga cikin dakin dake kallon falon yayi waje abin sa batula tabi shi da kallo sannan ta tabe baki tace.

Uhm bera ma kenan zafi ya ishe shi acikin wannan akurkin to ina kuma ga mutum....kai Allah ya raba ni da wannan gidan kurkukun zafi ya dafa ka kuma a doke ka ta tsartar ta yawu ajikin bango ta dada takurewa guri guda Tijjani ya dubeta cikin takaici gata dai kyakkyawa amma mugun Halinta yafi bakin gawayi muni.

Alokacin daya fara ganin batula yarinya kyakkyawa mai yawan son dariya Tijjani ya dauka idan ya aure ta yafi kowane namiji sa'a aduniya ayanzu kam ya tabbata yayi kuskure.
Tabbas zabin Allah shine zabi ba zabin mutum ba.

KA RABU DA YARINYAR NAN TIJJANI SANIN KANKA NE IDAN HAR MACE TA NUNA CEWA BATAYI DA KAI TO KA KYALE TA KAWAI SHI YAFI.
Maganar babban amininsa ABDUL ta fado masa a lokacin dayake ta faman gwagwarmayar neman auren batula ita kuma tana ta juya shi kamar WAINA.KISAN BOKO-12

KA RABU DA YARINYAR NAN TIJJANI SANIN KANKA NE IDAN HAR MACE TA NUNA CEWA BATAYI DA KAI TO KA KYALE TA KAWAI SHI YAFI.

Maganar babban amininsa ABDUL ta fado masa a lokacin dayake ta faman gwagwarmayar neman auren batula ita kuma tana ta juya shi kamar WAINA.

Bazan iya Rabuwa da batula ba Abdul sonta ya riga ya mamayi zuciyata batula tamkar wani bangare ce a ruhina gata mai yawan fara'a gata kyakkyawa kallon ta kawai kan yaye min bakin ciki.

Abdul ya girgiza kai yace.
Ai duk kyawunta da fara'arta shirme ne agareka in har batula ba kaunar ka takeyi ba...nidai da zakabi ta tawa da ka rabu da ita kawai.

Kayi hakuri Abdul bantaba bijirewa shawarar ka ba amma Awannan karon ina mai fargabar cewa bazan iya bin abunda kake muradi ba wato rabuwa da muradina abar sona ruhina BATULA.

Wannan duk wata hira ce data gabata tsakanin Tijjani da amininsa Abdul aduk lokacin baifi watanni bakwai ba kafin a daura masa aure da batula
Ayanzu da Tijjani yasa batula agaba yana kallo cikin matsanancin takaici sai mamakin kansa da kansa ya kama shi shin wai wannan masifaffiyar matar dake zaune agaban sa itace kuwa yake kauna itace yake muradin zama da ita har abada itace yake tsammanin daya kalle ta bakin cikinsa zai yaye??

Tabbas nayi Kuskure ya fadawa kansa akaro na farko saiya fara nadama ina ma ace yabi shawarar Abdul tun farko.

Kasani agaba sai kallo kake yi kamar wani naman daji kaga ni bana son yawan kallo kurwa ta kurrr!
In daki zaka shiga ka shiga in kuwa anan falo zaka zauna ni in shiga daga ciki batula ce ke maganar tana ciccije baki.

Tijjani ya dubeta cikin karfin hali yana ta tausar zuciyarsa domin ji yake kamar ya hau ta da duka.
Dauko min ruwa mai dan sanyi to na sha idan bazaki bani abinci ba. Tijjani yace cikin karyayyyiyar murya.

Batula ta Harare shi tace.
Uhm samun guri ka doke ni na dauko ma ruwa cab tayi tsalle ta diro daga kan kujerar ta mike tsaye ta tsaya a kansa kamar zata hau shi da duka.

Bazaki dauko min Ruwan ba?

Eh bazan dauko ba in ba zaka tashi ka dauko da kanka ba ka dauki azumin dare! Tana gama fadin haka sai ta juya da sauri ta shige dakin barcin su ta mako kofar dakin da karfi ta sa Sakata.

Tijjani ya jingina bayansa ajikin kujerar zuciyarsa na kuna yan sa'o'i kadan da suka shude matar da ba tasa ba tasa shi gaba tanayi masa magiya tana rokonsa daya sha ruwan tataccen lemo mai sanyi sai gashi ayanzu ruwan zartsi ma ya gagare shi samu agurin matarsa ballantana abinci koda ya lumshe idanunsa saiyaji wata sassanyar iska mai dadi tafara hurowa daga farfajiyar tsohon gidan zuwa cikin falon. Jin haka keda wuya sai Tijjani ya tube rigar sa sannan ya bude jakar ledar dayazo da ita dauko shudin leshin da nadiya tabashi yakara shi akan fuskarsa kamshin turarenta ya bugi hancinsa ga mamakinsa saiyaji sassanyar iskar dake hurowa gamida daddadan kamshin turaren sun hadu sun narkar da bakin cikin dake zuciyarsa sannan suka dauke tunaninsa cak suka jefa shi zuwa ga tunano daddadan kalaman Nadiya.
Da wannan tunanin sai Tijjani ya karkace akan doguwar kujerar mai kamar makara ya dauko shudin leshin ya ajiye shi adaidai inda zaisa kansa sannan saiya kwanta ya lumshe idanunsa yana godiya ga Allah daya huro masa sassanyar iskar mai dadada zuciya ba'a dade ba sai ya dan bude idanunsa ya kalli kofar dakin dake fuskantarsa yayi mamakin abinda batula takeyi aciki sannan sai wani daddatan murmushi ya subuce daga bakinsa ya dada duban kofar yace
ZAFI MA YA ISHE KI MASIFAFFIYA.

***** ****** ***** ******* ****** ***** *********

ACIKIN dai wannan ranar Lahadin da isha'i misalin karfe takwas na dare amira takoma gidansu nadiya tana mai dokin jin yadda ta kaya.

Kawayen biyu zaune suke acikin ni'imtaccen lambun shakatawar gidan wanda ke fuskantar katon ramin wanka na zamani. Fitilu sai ci suke yi kamar rana acikin lambun ga iska mai sanyi sai busawa takeyi gamida kamshin furanni jifa jifa kuma sukan ji kukan tsuntsaye duk kuwa da cewa suma lokacin barcin su yayi.

Amira ta muskuta kadan akan farar kujerar roba kana ta dauki kofi daya daga cikin kofunan Dake kan dan karamin teburin mai kafafu uku kamar aljani ta kurbi sassanyar ruwan dake cikin kofin wani tattausan kamshi ya bugi hancin ta kana taji bakinta ya game da zaki kamar ta sha zuma sannu ahankali ta ajiye kofin kyangyaran! Akan teburin ta mika hannu ta tsinko fure daga cikin wata yar dukurkusar bishiyar fulawar dake daf dasu ta kara a hancin ta kana ta dubi nadiya wacce ke zaune daf da ita tana kallon mujjala acikin hasken kwayayen lantarkin da suka mamaye gurin.

Toh ya akayi.. Ba ni labari kin bar ni cikin zakuwa amira tace.
Nadiya ta ajiye mujallar dake hannunta sannan ta dauko wata dankwaleliyar alewa cakulan ta jefa a baki tace.
Labari ya rage namu.... Ko kuma in ce ya rage nawa amira.

To kamar yaya kenan? Nadiya ta saki wani tattausan murmushi
Wato amira... Wallahi abin ne ya zame min kamar wani asiri kinga tunda na dora idanuna akan yaron nan Wallahi na kasa samun sukuni azuciyata dana rufe idanuna saina fara ganinsa dana bude sai na ganshi zaune agabana yana murmushi. Amira ta fashe da dariya.

Kina nufin dai kice dani kin kamu kenan?

Nadiya ta lumshe idanu tace..
Eh toh kamuwar kenan koma in ce abin ya wuce da haka domin ayanzu yadda nakeji ban ma damu dana jira wai sai ya soni ba.... Kota yaya indai har kudi suna amfani saina aure shi.
Nadiya ta danyi shiru kana ta kurbi ruwa amma bata hadiye gaba daya ba saita fesa sauran acikin furanni.
AM....REALLY IN LOVE AMIRA!"

Amira tace oh matan zamani dai wallahi mun ji kunya wai mu muke neman maza....

Nadiya ta kai mata duka da bayan hannu.

Karkiyi min iskanci amira in kika ga mace bata Lallabi namiji ba to bataga wanda take so bane...
Hakane..... Amma duk da haka dai.....KISAN BOKO-13

Nadiya ta kai mata duka da bayan hannu.

Karkiyi min iskanci amira in kika ga mace bata Lallabi namiji ba to bataga wanda take so bane...

Hakane..... Amma duk da haka dai mu ya kamata su nema bamu mu neme su ba. Amira tace.

Gaskiyar ki amira amma inason ki gane cewa mata halitta-halitta ce wata ko zata mutu da ciwon son da namiji bai isa ta neme shi ba saidai in shi ya zo gareta nadiya ta danyi shiru sannan saita ci gaba.
Nikam bazan iya ba Allah ya hadani da wanda nake kauna a sanadiyar ki...dole ne na yi duk iya kokarina naga na mallake shi.

Yanzu kenan babu zancen mu jira lokacin da zai kauna ce ki saboda Allah Badon dukiyar ki ba ko? Inji Amira.

Amira kenan nadiya tace da murmushi.
Wannan ai duk tsohon zance ne kuma koda ya aureni din ma ai ba haramun bane dan ina da tarin dukiya ahakan ma idan Allah yaso saiki ga ya cusa masa kaunata ta danyi shiru.
Kuma ai in ma me nake son yi na riga na makara shin bai nuna miki abunda na bashi bane? Amira yayi murmushi.

Ya nuna min shudin leshin da dubu goma ko?

Nadiya ta gyada kai tsoro ma nayi kada na bashi da yawa ya tsorata wallahi ayadda yaron nan ya burgeni so nayi na bashi (Hundred Thousands) Dubu dari amira ta fashe da dariya.

Kai nadiya lallai ya rudaki amma kudin zancen ai yayi yawa dubu dari fa. dubu goman ma wallahi DAKYAR nasa shi ya karɓa nadiya ta dada kaiwa amira duka abaya.

Bafa Nason iskancin banza amira wato na zama abin tsokanar ki ko? Wato don wulakanci ma shine zaki ce Ina bashi kudin zance?

Allah yabaki hakuri amira tace cikin dariya yanzu meye abin yi? Nadiya ta dan janyo kujerar ta gaba kadan ta dubi amira sannan tayi kasa kasa da muryarta tace. Na riga na sami mijin aure don haka saidai mu fara shirye shiryen biki kawai Amira ta dubeta cikin kaduwa baki bude tace.
Ke zakin mazallako wai da daga ciki yana rokon uba kwabo daga fara soyayya awa goma din har kin fara zancen aure... Tun ma baki san matsayin ki agurin shi ba nadiya ta girgiza kai tace.
Amira jikina yabani cewa babu abunda zai hana shi aurena domin dan zaman da muka yi dazun da rana na lura da cewa kasancewa tare dani ya kwantar masa da hankali ya jefa shi cikin annashuwa sabanin yadda ya taho daga gidansa cikin bacin rai.

Amira taji wani zazzafan gumi yafara ketowa daga goshinta duk kuwa da tsabtatacciyar iskar mai Lema dake busowa daga cikin tsirrai.
Amma dai agaskiya nadiya ina ganin ai yayi wuri a fara zancen aure... Ina laifin ma kici gaba da tarairayarsa nan da tsawon wata biyu.
Nadiya tayi sauri ta girgiza kai.
Bazan iya jira mai tsayin haka ba amira don ke bani bace don ke bake kike jin abunda ni nakeji bane shiyasa kike fadin haka Wallahi dazun da na sa shi agaba ina kallo sainaji kamar karda na bar shi ya tafi domin hankalina yagama kwanciya dashi tuni nafara daukar sa amatsayin mijina.

Amira ta bude baki zatace wani abu amma sai ta sunkuyar da kanta kasa tana mai mamakin irin yadda yanayi kan sauya mutum cikin dan kankani lokaci domin ko kusa ko alama wannan matar dake zaune kusa da ita tana sambatun auren saurayin da ko cikakkiyar awa goma sha biyu batayi da sanin sa ba batayi kama da nadiya data sani a yammacin ba to amma abun ya faranta mata rai.

Shi aure ai nufin Allah ne nadiya taci gaba da fadi batareda ta dubi amira ba dadewa ana soyayya bai sawa ayi aure haka nan rashin dadewa da sanin junan bai hana aure idan Allah yakawo domin shi aure kamar mutuwa yake yawan cuta bai kawo mutuwa haka nan zaman ka lafiya bai hana ma mutuwa idan Allah yasa gobe ma sai kiji an daura mana aure da Tijjani amira ta dago kai tana kallon Nadiya irin kallon da za kayiwa mutumin da kake tsammanin ya tabu tace muryar ta na rawa.

Yanzu... To wane mataki kuma zaki dauka nan gaba?

Nadiya ta dubi amira da murmushi
Shin bakisan dazu har na fadawa mahaifiyata cewa na sami mijin aure ba?

Idanun amira suka zazzaro kamar zasu fado kasa saboda tsabar kaduwa.

Bakida hankali nadiya ya zaki sanar da mahaifiyar ki abunda bashida tabbas nadiya ta hade fuska tace.

Agurin ki ne babu tabbas amma ina tabbatar miki da cewa gobe war haka Tijjani suna tareda mahaifiyata suna gaisawa amira ta mike tsaye cikin kaduwa domin ji takeyi kamar almara.

TUNDA nake ban taba ganin zakin mazallako irin wannan ba nadiya ta mike gamida mika tace kadan ma kika gani indai nice ai idan ina son abu bana hutawa raina saina same shi.

Kawayen biyu suka fara tafiya sannu ahankali cikin lambu. Can sai amira tace.

Nadiya kina tsammanin Tijjani zai aure ki?

Nadiya ta dubeta cikin mamaki tace
Meyasa kikace haka?

Saboda naga ko kwana daya bakuyi da sanin juna ba nadiya ta zunkuda kafada.

Anyi ma auren da ba'a taba ganin juna ba ballantana mu da muka ga juna na kusan sa'a guda amira ta danyi shiru adaidai lokacin da suka kawo wata yar siririyar kwana ma'abociyar yawan shuke shuke.
Na fada miki yanada mata kina jin ko da auren naku ya tabbata zaki iya zama da kishiya?

Nadiya ta tsaya turus ta kalli amira gamida girgiza kai tace
Babu abunda na tsana aduniya irin kishiya.

To yaya zakiyi da matar sa?

Nadiya ta yi shiru na yan dakiku kanta a sunkuye tana kallon ruwan ramin wankan dake dab dasu yana daukar idanu acikin hasken lantarkin daya haskake duk ilahirin lambun. Sannan saita dago kai tayi ajiyar zuciya tace.
Amira dazun dana kalli Tijjani Naji irin yadda ya kwanta min Arai saina sami kaina ina mai addu'ar inama ace matarsa ta mutu tabar min shi ni kadai....Wallahi bana son hadashi da kowa domin tjjani nawa ne ni kadai

Ke shashasha kada bege ya saka ki hauka tun ma baki aure shi ga har ya zama Naki?
Amira tace cikin alamar kaduwa adaidai lokacin da katuwar jiminar nan ta shawo yar siririyar Kwanar ta tsaya agaban su kikam.

Amira tayi sauri ta rike Nadiya a tsorace tace.
Nashiga Uku me zan gani?

Nadiya ta fashe da dariya tace.
Ai laifin ki ne ke kika janyo ta nan ji ta yi kamar bakya son aurena da Tijjani.

******* ***** ******* ****** ******* **** *******

WASHEGARI Litinin tun karfe biyar na yamma Tijjani yafara tsammanin zuwan ta. Daga inda yake zaune cikin shagon dinkin yana iya hango farfajiyar kofar shagon kai tsaye ta cikin kofar gilashin tun karfe biyu na azahar gabansa ke faduwa domin da wata mota mai dan fasali ta tsaya a kofar shagon sai zuciyarsa ta harba a tsammaninsa ko nadiya ce tazo.

Sannu ahankali wannan mota tazo wannan ta wuce har dai zuwa yanzu babu motsin nadiya.
Meyake damuna ne?
Tijjani ya tambayi kansa sa'ar da ya fahimci yayi matukar matsuwa da nadiya tazo duk kusan sa'a guda sai ya dauko dinkunan da yayi mata ya jujjuya su yana kokarin hango nakasu domin yayi gyara.

NIMA jikan sidi mai jaka INA CIGIYA IDAN AN SAMU KAMAR NADIYA A SHIRYE NAKE ARADUKISAN BOKO-14

Tijjani ya tambayi kansa sa'ar da ya fahimci yayi matukar matsuwa da nadiya tazo duk kusan sa'a guda sai ya dauko dinkunan da yayi mata ya jujjuya su yana kokarin hango nakasu domin yayi gyara.

Abunda yake ta faman addu'a duk tsawon rana shine Allah yasa dinkin ya burge ta dayawa daga cikin Abokan aikin Tijjani

Please Login or Register in order to submit comment