Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jijjiga shi ta dauke kai gefe guda.

A farfajiyar wani tsohon gida ake wannan diramar tsakanin ma'aurata guda biyu irin wannan rikici ba shine karo na farko ba bashine karo na biyu ba ga dukkan alamu kuma bashine sai zamo na karshe ba domin......KISAN BOKO-05

A farfajiyar wani tsohon gida ake wannan diramar tsakanin ma'aurata guda biyu irin wannan rikici ba shine karo na farko ba bashine karo na biyu ba ga dukkan alamu kuma bashine sai zamo na karshe ba domin acikin wata hudu da suka yi na rayuwar aure kusan kullum sai sunyi fada kamar kaji. A watan daya gabata watarana da daddare Tijjani yana kwance a falo sa'ar da matar ta rufe dakin taki budewa yayi kokarin lissafta iya adadin manyan manyan fadan da sukayi cikin zuciyarsa ba karamar kaduwa yayi ba sa'ar daya kididdige adadin fadan yaga har sun kai kimanin sabanin da hudu duk kuwa da cewa baiyi lissafin da yan kananan fadace fadace ba irin su dauko min ruwan zafi ita kuma tace bazan dauko ba kokuma ni zan tafi gurin aiki ita kuma ta murguda baki tace to ina ruwana kuma ko a bayana zaka? Wata sa'ar kuwa sai ta wuni tana wake wake tana zaginsa a fakaice kokuwa ta dubi tsohon gidan da suke zaune aciki tayi ta aibanta shi tana cewa wai Allah raba mutum da auren matsiyacin miji marar zuciyar neman arziki.

Sake ni na tafi batula kinga zan makara kuma yan makullayan shago ahannu na suke sai naje za'a bude. Batula ta turo baki gaba kamar tsuntsuwa sannan ta dada damke kwalar rigarsa tace
Baiwa yaro ya kai musu dan mukullinsu daga yau ka Daina wannan tsinannen aikin in bazaka nemi aikin kirki ba gara ka zauna ahaka idan yunwa ta ishe ni in tafi gidan mu na barka ka karata.

Yanzu kina ganin kinyi min adalci Kenan batula? Tijjani yace da ita a sanyaye duk kuwa da cewa zuciyarsa sai zabalbala take kamar rude.

Kwarai kuwa nayi maka adalci tunda nake kokarin raba ka da aiki a karkashin wannan tsohuwar karuwar Tijjani ya dubeta sannan ya bude baki cikin kaduwa.

Kai batula wallahi bakida kirki yanzu ashe har kina da bakin da zaki kira uwar dakina da ta bani aikin yi da karuwa? Batula tayi tsalle ta dire tace.
Karuwa ce mana wane ne duk fadin unguwar nan baisan amira ba matar da tun muna yara kanana suka yi yan matan cin su saida ta gaji da karuwancinta ta tsofe a titi sannan tayi aure.

Tijjani yaji zuciyarsa ta kara harzuka tabbas yau zan bata mamaki yace cikin zuciyarsa.
Menene amfanin zargi batula? Don me zaki yi mata kazafin karuwanci bayan bakida tabbas?

Kaima ai munafuki ne waya sani ma koda can kafin ka aureni kai take nema taga dan yaro kanin kaninta shiyasa ai ka nace da wani tsinannen dinkin da bazaka taba arziki dashi ba dubi tsakar gidan nan ko sumunti babu kamar filin yaki dubi dakunan dakuka zo kuka cusani aciki kamar dakin tattabaru dubi jikina da fara kal nake ina sheki amma wata hudu kawai har nafara jemewa kamar fata.... To in ba karuwar ka bace Meyasa bazaka rabu da shagon dinkin ba
Kaje ka nemi aiki da takardun karatun ka na dauka tun kafin ka aureni kayi difloma?
Kiji tsoron Allah batula ki......KISAN BOKO-06

Kaje ka nemi aiki da takardun karatun ka na dauka tun kafin ka aureni kayi difloma?

Kiji tsoron Allah batula ki dawo hankalinki ki nutsu kikuma godewa Allah dayasa na iya dinkin nan domin ina tabbatar miki da cewa abinda nake samu da dinkin nan acikin wata guda ko mai digiri idan ba dacen aikin yayi ba bazaifini samu ba to balle kuma difloma Haba batula yanzu ashe duk kokarin da nake yi akanki bakya godiya sai kin butulce min batula?

Yeh Yeh batula ta kwarara shewa cikin izgilanci kuji ni da dan mutumin nan kai yanzu ko kunyar fada bakayi wane kokari kake yi min? Me ka taba yi min tunda ka auro ni? Shinkafa da taliyar kullum? Ko kuwa dan kifin da kake kawowa kullum kamar wata mage kokuwa so kake ka goranta min dan dinkin kala biyar dakayi min atamfofin dako hada kudin Dinkinsu bazasu sayi atamfar kirki ba oh yau na shiga uku kishiya mayya miji ɓarawo!

Tijjani ya girgiza kai cikin takaici wani zazzafan gumi ya fara sartu akan kyakkyawar fuskarsa tuni har numfashinsa yafara daukewa sakamakon muguwar shakar datayi masa. Duk abin nan da akeyi hannayensa cikin aljihu suke domin wannan bashi ne karo na farko data shaki kwalarsa ba kuma aduk lokutan baya Tijjani ya koyawa kansa cewa da zarar taci kwalarsa ya zura hannayensa cikin aljihu don gudun kada shaidan ma ya tunzura shi ya dake ta. To amma ayanzu akaro na farko saiya zaro hannayen sa biyu daga aljihu ya dubi batula yace a sanyaye

Sake ni batula

Bazan sake ka din ba kayi abunda Zakayi

Tijjani ya sake cewa akaro na biyu
Sake ni batula.

Bazan sake.... Kafin ta karasa Tijjani ya kife ta da mari Tasss batula ta kwalla ihu ta sake shi a rude domin bata taba tsammanin Tijjani zai doke ta ba.

Ni ka doka Tijjani ni ka doka? kauce daga gabana ko na kara miki shegiya mara kunya yana gama fadar haka sai ya hankade ta gefe guda sannan yanufi kofa cikin sauri wuyan farar rigar dake jikinsa duk ta kudundune dukun-dukun kamar an kwato shi daga bakin saniya koda yakai kofar Gidan sai batula tace dashi cikin karaji tana sheshshekar kuka

Saboda na hana ka aikin wannan tsohuwar karuwar ka doke ni Tijjani?

Tijjani ya juyo ahankali ya dubi fuskar matarsa tana zubar da hawaye sharaf-sharaf matar da A yan watanni kadan da suka shude yake kauna fiyeda komai aduniya koda ya kalleta ayanzu sai yayi mamakin shin wai da can me ya gani ne a jikinta da har yake kaunar ta?

Wannan matar da ki ke kira karuwa Wallahi yanzu tafi ki agurina tunda tabani aikin yi kuma bata taba zagin iyayena ba yana gama fadin haka saiya juya cikin sauri ya fice yabar ta tana ta jefo bala'i

******** ******* ***** ******* ******* ********

BABI NA BIYU
Jibgegiyar motar jeep bakakirin tana sheki acikin hasken rana ta nufi kofar daya daga cikin sheguna takwas din da sukayi jerin sahu akasan katon farin benen dake fuskantar babbar kasuwa daga arewa yaku-bayi sama da mutum talatin da doriya suka zubawa motar idanu sa'ar data ja birki ahankali ta tsaya a kofar sanannen shagon Madinkan na yan kwalisa sannan tun kafin kofar motar ta gama budewa wasu rukunin kolawa sukayi caaa zuwa gindin motar kowa da kwanon sa ahannu

Kaga kalatattun almajiran nan har sun fara yanyame motar nan daga zuwanta ko?
Daya daga cikin yaku-bayin nan yace da abokin sa.
Wallahi su suke bada talakawa agurin masu kudi abokin da ake baiwa labari ya girgiza kai idanunsa akan motar yace kada ka ga laifin su rabe samu sukeyi shiyasa kaga sun yanyame ta yanzu in dan ta mu ne sai yunwa ta kashe su tunda dai sai su wuni suna suntiri agurin nan basu sami koda loma daya na abinci ba
Kai kanka ina tsammanin rabon da kayi sadaka koda ta naira biyar ce an fi shekara

Rabe ya fashe da dariya ya dubi abokinsa yace. Nima da zan samu sadakar karɓa zanyi domin garin nan ya dau zafi Billahillazi dau-dau.

Kofar motar ta bude ahankali matan guda biyu suka fito ta kofofi daban daban yayinda kuma jikinsu yabasu cewa duk kusan gurin su ake kallo wannan ba wani bakon al'amari bane ga duk mazauna wannan guri domin akalla ba akasara ba aduk kwanan duniya sukan yi tozali da kyawawan motoci da matan dake ciki sama da dari da ashirin wadanda ke zuwa karbar dinki kokuma su kawo dinkin kantin YAN KWALISA TAILORING SERVICES.

Wani Ustaz dake jan sallah agurin ya taba cewa da Abokansa in Allah ya yarda zai rage zama agurin domin yace bazai iya jurewa kallon kyawawan matan da ba nasa ba alhali shaidan nata kai kawo a tsakani wannan ita tasa a duk loakcin da Ustaz din yazo gurin idan irin wannan kyawawan matan masu zuwa a manya manyan motocin alfarma suka kawo dinki saikaga duk sun dauke kawunan su gefe guda don gudun kada yagani yayi musu wa'azi amma a zahiri basa barin kallon kyawawan ya wuce su koda ta wutsiyar ido ne sai sunyi dan tozali hakan ita tasa dayawa daga cikin mazajen kan taru agurin da yamma ba sana'a ke kawo su ba sai lallace kallace narasa amfani.

Don haka ayanzu da matan biyu suka fito daga cikin motar sai wnai dogon saurayi wankan tarwada yaja wani dogon tsaki ya dauke kai gefe guda yace da Abokansa
AIKIN BANZA NI NA DAUKA MA WASU YARAN CIKU NE ASHE MA DUK CUSSS NE.

Ba kyau muzanta dan adam wani daga cikin samarin yace dashi.
Kaga su basu san ma da zaman ka ba amma har ka dauki hakkin su saurayin ya hada fuska sannan ya dubi saurayin yace
Kaga malam ni bance kayi min wa'azi ba.

Matan biyu suka nufi kofar shagon na dinkin cikin mamaki domin sunga kofar a rufe.

A'a me yafaru haka haryanzu ba'a bude shagon ba? Amira tace cikin damuwa

Me yiwuwa ko makara sukayi nadiya tace muryarta na dan rawa domin duk dokin ganin saurayin da Amira tace zata nuna mata ya Sakata cikin rudewa.

Toh Ai abin ne da.....KISAN BOKO-07

Me yiwuwa ko makara sukayi nadiya tace muryarta na dan rawa domin duk dokin ganin saurayin da Amira tace zata nuna mata ya Sakata cikin rudewa.

Toh Ai abin ne yabani mamaki dubi fa sha biyu saura basu taba kaiwa kamar yanzu basu bude ba matan biyun suka yi cirko cirko na yan dakiku agaban shagon amira tana yan dube dube ko zata hango daya daga cikin Madinkan ya bullo.

Ahannun wa dan makullin gurin yake ne?
Nadiya ta tambaya sa'ar dataji kamar shirun tayi yawa dajin haka sai amira ta saki wani murmushi tace.
Agurin mu.... Bata karasa ba sa'ar data hango shi ya nufo inda suke cikin sauri tun daga nesa amira ta lura da cewa ransa a bace yake wani farin ciki ya lullube zuciyarta sa'ar data hangi kwalar rigar sa tayi dukun dukun tabbas tasan kwanan zancen

Ga shi nan ma yazo amira tace da nadiya sa'ar da kyakkyawan saurayin ya karaso inda suke cikin sauri.

Hajiya ina kwanan ku? Yace dasu
Lafiya lau Tijjani.
Kuyi hakuri don Allah hajiya inafatan dai baku dade kuna jira ba Wallahi wata matsala ce ta dan rike ni agida shiyasa na makara.

Lah.. Babu komai Tijjani bude shagon mu shiga lokaci guda kuma sai ta dubi Nadiya ta kifta mata idanu nadiya ta fahimci abinda take nufi kuma tun ma kafin ta kifta mata idanu jikinta yafada mata hakan. haka nan kuma tun ma kafin jikin nata yabata sa'ar data hango saurayin ya nufo inda suke saita sami kanta tana me addu'ar inama ace wannan shine Tijjanin da Amira ke bata labari. Ba karamar harbawa zuciyar ta tayi ba Sa'ar dataji amira ta ambaci sunan saurayin da TIJJANI.

Cikin sauri Tijjani ya bude kofar shagon sannan ya dageta sama yayinda nadiya ta kurawa bayansa idanu bata ko kifitawa azuciyarta tana cewa Allah kai ka hadani da wannan kyakkyawa Allah ka iya min zuciyata ta shiga rudani.

Ita ko amira tana satar kallon nadiya a fakaice domin ta lura lokaci guda Tijjani yayi tasiri agurin Nadiya.

Cikin sauri Tijjani ya janye musu gilashin suka shiga shagon wanda tuni har ya haskake da farin kwan lantarki yayinda na'urar sanyaya dakin da Tijjani ya kunna tafara fifita su. Tuni daman har sun fara gumi sakamakon dan jiran da sukayi awaje sabanin yanayin cikin motar Nadiya ma'abociyar raba kamar damina.

Nadiya ta zubawa dogon shagon idanu hakika amira tayi kokari domin ta tsara shagon daidai da zamanin da ake ciki haka nan ta lura kekunan dinkin guda bakwai ne kamar yadda tafada uku na surfani ne hudu kuma na hadi.

Daga can bangon arewa na shagon tangamemen hoton amira ne wanda ganin hoton ya tunawa da nadiya rayuwar su ta jami'a domin hoton tun amira na da sauran kurciya ta dauke shi.

Kawayen biyu suka samu biyu daga cikin kujeru masu dan wadatar laushi suka zauna duk kuwa da cewa kujerun tamkar dutse suke dan tauri in har za'a kwatanta su da kujerun dakin shakatawar nadiya.

Saurayi Tijjani ya nufi kan keken dinki cikin gaggawa don fara aiki.
Tijjani amira ta kira sunansa. Saurayin yayi turus sannan yadawo inda suke hannunsa dauke da almakashi.

Na'am Gani hajiya. Amira ta dube shi da murmushin tace
Ku dada gaisawa da wannan ta nuna nadiya kawata ce tare mukayi karatu da ita a jami'a cikin sauri Tijjani ya dubi nadiya.

Ranki ya dade ina kwana.... Da Allah kiyi hakuri ai ni da farko dana ganku tare na dauka sabuwar kwastoma ce aka kawo mana shiyasa ban gaishe ki gaisuwa ta musamman ba nadiya ta haske shi da murmushi lamba daya wanda ta sha ribartar samarin da batada lokacin su tun tana yar shekara sha takwas ta dube shi a nutse tace.
Raina ya dade tare da naka T.J suka fashe da dariya shuru na dan lokaci.

Tijjani na tsaye agaban su yanayi kallon wannan mata ma'abociyar faffadan murmushi ba wata kyakkyawa bace sosai yace cikin zuciyarsa amma akwai wani abu dayasa zuciyarsa fari lokacin datayi kalaman farko a gare shi nadiya ko ta dan sunkuyar da kai tana satar kallon shi a fakaice.

Yanzu idan nace ka dinka min babbar riga irin ta mata zaka iya dinka min? Tijjani ya fashe dariya yace
Ranki ya dade wacce iri ce kuma babbar riga ta mata? Nadiya ta kada masa idanu ta tsuke baki ta dauke kai gefe guda tace
Nima na sani.... So dai nake yau ka kirkiro min ita amatsayin ka na kwararren tela gaba daya suka fashe da dariya suka sake yin shiru na dan lokaci Tijjani ya lura da irin leshin Dake jikin wannan mata zuciyarsa ta harba domin ko acikin matan masu hannu da shuni da kan kawo musu dinki bakowace mace bace ke iya dinka irin wannan leshi ba.
Alokacin ne wata alamar tambaya ta darsu cikin zuciyarsa shin wannan katuwar jeep din baka daya gani a kofar shagon ta matar ce?

In kuma baka iya dinkin babbar rigar mata ba to ka dinka min rawanin mata kaga na zama limamiyar mata kenan.. Tijjani ya sake fashewa da dariya yace.
Ranki ya dade kwarewa ta a dinki bata kai ni ga iya dinkin rawanin mata ba saidai ko in so kike dai kice na yi miki dankwali a fakaice nadiya tayi murmushi tace toh nidai yau bazan bar gurin nan ba sai kayi alkawarin yi min dinki. Tijjani ya dubeta cikin mamaki da murmushi yace.
Dinkin kam in kina so ne zai hana ayi miki to amma sai dai ki fadi irin wanda bai zarce kwarewa ta ba Nadiya ta lumshe idanu tana karkada kafa.

To ko so kake na baka zabi ka dinka min duk abunda kaga yafi dacewa dani? Tijjani ya danyi Jim A rude.
KO kuwa dai na dauko miki littafin hotunan Kala kalar dinkunan ki zaba Nadiya ta girgiza kai. A'a ban yarda ba kaje na baka zabi duk abinda kaga ya dace dani ka dinka min kawai ta danyi shiru sannan sai tace.
Yanzu idan na kawo yaushe zan samu? Tijjani ya dubi amira wacce ke zaune shiru tana ta nazarin hirar tasu cikin mamaki yace muryarsa na dan rawa.

Bari na duba littafin tsare tsaren dinkin mu naga ranar da za'a baki. Cikin sauri nadiya ta zazzaro idanu gamida bude baki da tafi na rudu tace.
Oh! Daman ai gwada ka nayi wato ina bakuwar taka ma sai ka bani wani lokaci? To kaga dana kawo dinkina zan dawo washegari na karɓa ni bana son delay ta mike tsaye tana duban Tijjani cikin murmushi.

In kuma bazaka dinka min ba kafada min Tijjani ya girgiza kai yace
Ban isa ba wane Ni nidin banza.... Yanzu yaushe zaki kawo? Nadiya ta juya ta dan kare Tijjani da bayanta sannan saita kifitawa amira idanu tace.
Da Kai zamu tafi gidan mu yanzu nan ka karbo kayan ko kafara dinkawa da wuri don gobe dana dawo daga aiki zan biyo da yamma na karɓa.

Tijjani ya dubi uwargidansa Amira a rude ga mamakinsa saiyaga tayi masa murmushin karfafa gwiwa.
Babu komai kabi ta ka karbo sai kayi sauri ka dawo domin akwai lissafin danake so muyi da kai kafin na bar gurin nan sannan sai amira ta dubi Nadiya tace.

Sai yaushe zamu hadu dake? Nadiya ta dan yi jim sannan sai tace...KISAN BOKO-08

Sai yaushe zamu hadu dake? Nadiya ta dan yi jim sannan sai tace.

Kizo yau da daddare mana saina rubuta miki abin nan in yaso gobe Monday saiki yi Withdraw

Toh nagode amira tace gamida mikewa tsaye muje na raka ki nadiya ta dubi Tijjani wanda ke Tsaye kikam kamar zane tace
Toh ajiye almakashin mana sarkin madinka ko da almakashin zaka bini? Tijjani yayi dariya ya girgiza kai.

Duk abinda kikace haka za'a yi ranki ya dade

Ka same mu awaje amira tace dashi sa'ar da suka nufi kofar fita daga shagon.
A kofar shagon a gindin motar kawayen biyu suka dubi juna suka kiftawa juna idanu a gulmace.
Yaya kika ganshi? Amira tace muryarta kasa-kasa

Beautiful! Nadiya tace cikin harshen turanci wallahi ya ma wuce yadda nake tsammanin sa tun farko.

Yanzu Idan kun tafi me kuma.... Maganar amira ta katse sa'ar data hango Tijjani yanufo su cikin sauri.

Kada ki damu kyaji labari idan kinzo da daddare nadiya tace cikin rada idan har ba'a kusa da ita mutum yake ba saika rantse da Allah fatar bakinta bata motsa ba sannan saita daga murya tace zagaya ta can ka shiga mu tafi ko ka dawo da wuri jikinsa na rawa Tijjani ya zagaya ya bude ya zauna akan rantsatstsun kujerun motar ahankali a tsorace kamar mai zama akan kwai. Wani lallausan kamshi ya bugi hancin sa adaidai lokacin ne nadiya tayi sallama da Amira tashigo motar ta kame sannan ta kunna na'urar sanyi nan da nan raba ta fara busowa ajikin Tijjani.

Saki jikinka sosai Tijjani naga ka takura guri guda nadiya tace dashi sa'ar data lura taga ya zauna cakeke duk a mimmike kamar ya hau jaki wanan shine karo na farko daya taba shiga jeep arayuwarsa nadiya ta gyara zama sannan ta yi wa motar key ta tuka suka hau titi ahankali sulululu kamar suna tafiya akan gajimare nadiya taji warin ranar da jikin Tijjani keyi ya bugi hancinta. Me yiwuwa akasa yazo tun daga gida Allah Sarki bawan Allah nadiya tace cikin zuciyarta sannan ganin Tijjani shiru saita dube shi tace.

Me ya samu kwalar rigar ka naga duk ta kudundune?

Tijjani yaji kamar ta soke shi da mashi a zuciya domin tun sa'ar daya baro gida cikin matsanancin bacin rai bai kara tunawa da matarsa batula ba sai yanzu wannan mata mai iya raha da saukin kai duk ta gusar da bakin cikinsa ta mantar dashi duk bala'in da sukayi da matar sa saiga shi yanzu da kanta tana tuno masa da bakin cikin dake damunsa duk dayake nadiya bata juyo ta kalle shi ba ta lura da sauyin yanayin daya bayyana akan fuskarsa ta cikin Mudubi.

Tijjani ya dubeta da murmushin yake muryarsa na rawa yace
Wani kazamin yaro ne ya kama min wuyan riga dazu....da....safe inayi masa wasa

Tun kafin ya karasa bayanin nadiya tasan karya yakeyi domin amira ta rada mata cewa meyiwuwa fada sukayi da masifaffiyar matarsa kafin ya taho.

Don haka sai nadiya ta dube shi da faffadan murmushi tace.
Allah Sarki Tijjani ashe kaima kamar ni kake kana son wasa da yara.

***** ****** ***** ***** ***** ***** ***** ******

A kofar tangamemen gidan su nadiya sa'ar da suka zo kofar gidan dogon maigadin mai tankwararriyar hula kamar makani ya sheko aguje har hularsa tana kokarin faduwa ya bude musu kofa suka wuce zuwa cikin farfajiyar gidan maigadin ya janyo kofar mai tafiya akan taya ya rufe sannan ya dubi abokinsa IDI mai sigari yace......KISAN BOKO-09

Maigadin ya janyo kofar mai tafiya akan taya ya rufe sannan ya dubi abokinsa IDI mai sigari yace
Dan kunna mana mu busa. idi mai taba ya dubi maigadin cikin mamaki yace
Wai kai kullum bakada aiki ne saidai a kunna ma ka busa tunda muke dakai baka taba sayen tabar nan ba shin ko baka san kullum nayi mana kunni jarina muke busawa sama ba? Maigadin ya dan hade fuska sannan ya tsartar da yawu yace.
Bar ganin wannan gingimemen gidan da nake gadi bar ganin wadannan zunduma-zunduman motocin idan nafada maka abunda suke biyana awata sai kayi mamaki domin duk watan duniya sai naci bashi kuma kaga wannan matar data wuce ciki yanzu duk kusan dukiyar gidan nan ahannun ta suke amma shegiyar rowa ce da ita... Yayi karyar gamida yin shiru.

Idi mai gadi ya dube shi yace ashe dai kace huhun ma'ahu ne ana ma ganin kitsen rogo maigadin ya fashe da dariya sannan ya nuna kofar gidan da baki yayi kasa-kasa da muryarsa yace.
Ga Huhun ma'ahu can ta wuce
Wa kenan? Idi mai gadi ya tambaya
Uwargijiyata mana duk fa girman nan nata batada aure.

Kai kabari don Allah idi yace cikin kaduwa
Alkur'an da gaske nake gata da shegen girman kai kamar iblishiya tunda maigadin nan ya kwanta dama taga ta samu gado mai yawa sai kawai ta mike kafarta.. Kaga yanzu ma har tafara shigowa da maza dubi wancan da suka wuce tare mai dogon hanci kamar Karas koda yake ma dai naga ya dan fita kyan fasali kuma naga kamar ma ta girme shi nesa ba kusa ba.

IDI mai taba ya zaro taba guda ya cinna mata wuta ya zuki hayaƙi yakarawa sama hazo sannan ya mikawa maigadin tabar yace
Ga dukkan alamu KISAN BOKO ce ko ?

Maigadin ya dubi idi mai taba a rude yace menene kuma kisan boko? Idi mai taba ya dada huro sauran hayaƙi daya rage a bakinsa ta hanci kana yace
Haka Naji ana fadawa irin wannan matan da suka tsufa basu yi aure ba suna boko kasan shekara ta goma ina aikin lebura a jami'a anan Naji sannan saiya fase da dariya yace.
Allah ya kyauta Allah baiwa kisan boko mazan aure ya danyi shiru sannan yace
Amma ina shakka in har Uwargijiyata zata sami mijin aure dan muguwar marowaciya ce idi mai taba ya girgiza kai yace
Uhm Uhm rabu da irin wadannan matan idan suna son abu zasu iya yin komai domin su mallake shi.

Adaidai lokacin da duk wannan ke faruwa ne nadiya ta shiga da Tijjani cikin rantsatsatsen dakin shakatawarta wanda ke fuskantar lambun shakatawar gidan.

Zauna mana tace da Tijjani sa'ar data ga ya tsaya yana ta waige-waige kamar Wanda yayiwa sarki karya me yiwuwa kayan alatun dake shirye a dakin ne suke tsorata shi domin ko a mafarki bai taba yin kyakkyawan mafarki da irin wadannan dandasheshshen daki ba.

Koda Tijjani ya nufi kujerar zai zauna saiya juyo ya dubi nadiya yace muryarsa na rawa.
Anan zan zauna? Nadiya ta gimtse dariya domin taga kyakkyawan saurayi yagama rudewa nadiya ta gyada masa kai da faffadan murmushi zauna mana ka saki jikinka nan ai kamar gidanku ne.
Eh... Ah..... Tunda dai kuna tare da kawata Amira ai gudanmu gidan ku ne.

Tijjani ya zauna ahankali saiyaji kamar kujerar kamar tana kokarin zuke shi zuwa cikin sosonta saboda taushi cikin sauri Tijjani ya daddafe kujerar da hannunsa domin ji yake kamar lumewa zaiyi aciki.

Nadiya ta lura da hakan amma saita dauke kai gefe guda tayi kamar bata ganshi ba.

Ina zuwa tace dashi sannan saita wuce zuwa wani dan karamin daki dake fuskantar dakin shakatawar kofar dakin ta gilashi ce amma baka isa kaga abunda ke cikin dakin ba koda ka leka saidai kaga hoton kanka Timeme yakara girma wannan shiyasa nadiya take son a sauya mata kofar gilashin a karshen wannan watan.

Tijjani yayi shiru yana ta Kalle-Kalle kamar sauna dakyar yake motsi haka nan numfashi dakyar yakeyi wai don kada yayi wani kwakkwaran motsi ace yayi kauyanci haka nan kuma duk a tsorace yake a zuciyarsa yana cewa wannan mata da neman janyowa mutum jafa'i take yanzu idan mijinta ya dawo ya same ni ni kadai anan tareda matarsa me zan ce dashi? Nazo karbar dinki kokuwa nazo kwartanci? Tunanin matarsa batula yafado masa adaidai lokacin da idanunsa suka kai ga dan karamin tekun gilashin nan da kifayen bogi ke wasa aciki cikin sauri ya kawar da tunanin matarsa daga ransa domin bashi bukatar bacin rai Awannan lokacin.

Kofar gilashin ta bude ahankali nadiya ta shigo dakin dauke da wata farar jakar leda katuwa haka nan ahannun ta na hagu littafin hotuna ne sannu ahankali ta matso

Please Login or Register in order to submit comment