Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan busasshiyar
otal din da kake aiki a ciki, in sa a
rugujeta a sake gina ma ita, in ya
so sai ka zabi sunan da ka ga ya
dace ka sa mata." Aliya ta yi shiru
tana numfasawa, sannan sai ta
mike tsaye ta dubi Anas ta ce.
"Ka yarda zaka aure ta?" Anas ya
ji kamar katanga ta fado masa a
tsakiyar baya. Abu daya da ya
tabbatarwa kansa shi ne in duk
za a bashi duniyar nan domin ya
kaunaci wannan mummunar
gurguwa ba zai taba iyawa ba, to
amma da albashin naiura dubu
dari biyu a wata, da naira dubu
dari a sama da kuma kyautar
otal din da za a bashi, ya tabbatar
ko da Mabaruka kuturwa ce sai
ya aureta. Cak! Yau na zama
miloniya cikin sa'a guda... Ya ce
cikin zuciyarsa, koda ya tuna da
cewa lagwada otal za ta zama
tasa sai ya ji wani zazzafar gumi
na farin ciki ya zubo masa
tuntuni ya dade yana addu'ar
Allah ya bashi damar da zai rama
wulakancin da manajan otal din
ke yi musu, sai gashi a banza
yanzu dama ta samu a bagas.
Wani busasshen murmushin
mugunta ya subucewa Anas nan
da nan ya dauki alkawarin cewa
duk ranar da ya mallaki ota din
sai ya tikawa dan dukurkushin
manajan dundu a tsakiyar baya.
"Anas!" Aliya ta katse masa
tunani "Tunanin me kake... Baka
amince bane?" Anas ya girgiza
kai cikin sauri sannan ya ce.
"Kin ce cikin sati za a daura
auren ni ko yanzu naira dubu
takwas ce daidai a aljihuna ita
ma ta albashin da aka biyani ce
dazu da yamma."
Aliya ta yi murmushi sannan ta ce
"Tun da ka amince ina kai ina
fargabar kudi, nan gidansu ka
zo." Ta dan yi shiru sannan sai ta
ce.
"Kana jin naira miliyan goma zata
isheka fara shirye-shirye kafin
zuwa jibi". Anas ya ji yawun
bakinsa ya kafe ya dube ta a
rude.
"Miliyan goma kika ce ko kuwa
dubu goma."
Aliya ta fashe da dariya sannan
ta dubi yarta Mabaruka wacce ke
gefe ta yi tagumi tana
sauraronsu ta ce
"Miliyan goma na ce ko sun yi ma
kadan a kara ma?"****
Sidi mai jaka ya yi ajiyar zuciya
sannan ya dubi kwanon tubanin
dake gabansa cikin takaici duk
yawan tubanin nan ya hadiyesu
baki daya saura kwaya uku kacal
cikin kwanon.
"Nas ga labari ya dauko dadi
gashi kuma tubanina ya zo Gangara. Irin wannan abin shi yakansa wani lokacin na ji duk na
tsani bada labari domin tubanin
nan tamkar mota ce da man fetur
idan babu shi ka san ban cika
abin kirki ba".
Sidi mai jaka ya yi shiru yana
kallon cikin kwanon tubanin
sannan ya dubeni fuskarsa a
murtuke.
"Kamata ya yi ka karasa min
zuwa sallar Azuhur, idan na
koma gida sai na sa kakata ta
sake yi ma wani tubanin." Nan da
nan fuskar Sidi mai kaja ta
washe.
"shi yasa nake son ka NAS. Domin
daga na yi motsi sai ka gane abin
da nake nufi." ya dan yi shiru,
sannan sai ya ce, bari a gurguje
na kulla maka wani sabon zaren
labarin da wannan, domin naga
kamar lokacin sallah ya kusa."
Sidi Mai Jaka ya tsikari tubani na
ukun karshe ya jefa a baki
sannan ya dubeni.
Nas, ina son ka dauka cewa tuni
har an daura auren Anas da
Mabaruka gurguwa."
"Na dauka." Na ce da shi. Sidi mai
jaka ya dubeni, sannan ya ci
gaba.
Wato Nas, watanni biyun da suka
biyo bayan bikin Anas sun yi
matukar jefa Anas a cikin sabon
yanayi.
Lokacin da Anas ya bar gidan su
Mabaruka bai tsaya ko ina ba sai
wurin iyayensa, jikinsa na rawa
ya ce da su aure zai yi. Lokacin da
labarin auren nasa ya watsu a
cikin dangi sai aka yi ta zuwa ana
taya mahaifansa murna, domin
duk garin babu wanda bai san
ko wacece Mabaruka ba. Da yawa
daga cikin mahassada suka yi ta
zunde, tsegungumi da gulma,
suna cewa wai in ba lalacewa ba
ina kyakkyawa kamar Anas ina
auren gurguwa mummuna.
Wasu daga cikin masoyansa sun
taya shi murna, domin sun san
duk da dai bai yi dacen mata ba,
to amma ya yi bankwana da
talauci har abada, wannan a
gurinsu ya isa abin farin ciki,
domin a tunaninsu Anas ya gama
samin kwanciyar hankali da
nutsuwa.
To kamar yadda suke tunani NAS
hakanan ta kasance a cikin
watanni biyun da suka biyo
bayan bikinsu, domin Anas ya
sami hutun da bai taba tsammani
ba a iya tsawon rayuwarsa.
Da farko dai da yake daman shi
ba damuwa ya yi ba da wani
addini ba kullum kwanan duniya
Anas baya tashi daga barci sai
karfe goma sha daya na safe,
sannan ne zai tashi ya yi wanka,
sannan ya nufi wurin aiki.
Zamantakewarsa da Mabaruka ta
bashi mamaki, domin ya sami
Mabaruka macece mai iya dadin
magana, da tarairaya, duk kuwa
da cewa gurguwa ce, wani sa'in
sai su tafi bakin (Swimming pool)
su yi ta wasa da katuwar bal
marar nauyi, Mabaruka na zaune
akan kujerarta a bakin ramin
ruwan, shi ko yana ciki, idan ya
jefo mata, sai ta cafe ta jefa masa.
Wani sa'in kuwa sai Anas ya
dauketa a mota su yi ta yawo a
cikin gari suna bin guraren
shakatawa abinsu da yake Anas
gwanin ban dariya ne, sai ya yi ta
yi Mabaruka tana dariya. Wannan
ita tasa sau biyu ko uku kawai
Anas ke zuwa gurin aiki a sati.
"Kada ka dami kanka Anas da
yawan zuwa wurin aikin nan
kudi ne, muna dashi albashinka
kuma ko kaje ko baka je ba dole
ne a baka." Mabaruka ce ke cewa
Anas haka a wata safiya suna
karin kumallo.
"Anas, zamanka kusa dani ya fi
min zuwanka aiki, domin ni har
kullum idan na dubeka sai na ji
zuciyata ta yi fari tas, dan haka
ne bana son rabuwa da kai koda
dai dai da kankani...domin ..." Ta
dan yi shiru tana duban Anas.
Anas ya dube ta sa'ar da ya ji tayi
shiru.
"Domin muma me...?" Mabaruka
ta dube shi.
"Domin bana son wata mace ta
mallaki zuciyarka a duniya idan
bani ba, shi yasa ka ga na ce ma
sau biyu kawai za ka ke zuwa
aiki a sati."
Anas ya ji zuciyarsa ta harba, ko a
lokacin da yake yawon banzan
sa, babu abin da ya tsana a
rayuwarsa irin mace mai naci,
wacce zata makale masa kamar
cingam ta hanashi shan iska.
Sidi mai jaka ya dago kai ya
dubeni da murmushi sannan ya
ce "Nas, wata uku su Mabaruka
suka yi cikin farin ciki, daga
wannan kuma basu kara samun
koda dai dai da sa'a daya ba ta
farin ciki, domin a safiyar wata
rana ne Mabaruka ita da kanta ta
yi sanadiyar kawo karshen duk
wani farin ciki nasu!
Wata rana da safe aka yi sa'a
Anas ya farka tun da asussuba,
koda yake ba farkawar Allah da
Annabi bace. Anas na kwance
kawai sai ya ji idanunsa sun
bude. Abin ya ba shi mamaki dan
haka sai ya dubi agogo. Karfe
hudu na asuba agogon ya nuna.
Anas ya tashi zaune cikin
mamaki, ya dubi Mabaruka
gurguwa kwance a kusa da shi a
takure kamar kunkuru tana ta
barci abinta, mummunar fuskarta
a yatsune. Anas ya dauke kai
zuciyarsa na wasi-wasin dalilin
da ya sashi farkawa a wannan
lokaci. Tsawon lokaci yan zaune
akan gadon, sannan ne to
maganar Mabaruka ta fado masa.
"...bana son wata mace ta
mallakeka a duniya idan bani
ba..." Wani zazzafan gumi ya
barkowa Anas, sa'ar da ya tuno
da wannan kalami nan da nan ya
sake duban mummunar fuskar
Mabaruka. A zuciyarsa ya ce cab!
Ba zata yiwu ba duk kyawawan
matan dake duniyar nan na rasa
wacce zan kare rayuwata da ita
sai wannan! Anas ya share gumi
sannan ya dada kallon Mabaruka
tsigar jikinsa ta dauki rawa....TSOHON ALKAWARI-7
.
Sannan ya dada kallon Mabaruka,
tsigar jikinsa ta dauki rawa. Dole
ne na sami hanyar da zan rika
zagayawa gari ni kadai, ya ce
cikin zuciyarsa, wani abu da ya fi
baiwa Anas tsoro da al'amarin
Mabaruka shi ne ya fahimci tana
da bala'in Kishi.
Sau da yawa idan suna tafiya a
mota da taga ya dauke idanunsa
gefe guda ya kalli inda mata suke
sai ta kalleshi ta ce.
"Me kake kallo?" Anas ya kan ji
zuciyarsa kamar za ta fashe
saboda haushi.
Me take nufi ne da zata hana shi
kallon kyawawa bayan duk da
tarin miliyoyin kudin nan nata yar
karamar yarinyar dake talla a
gefen tituna ta fita fasali
Bayan da wannan kuma akwai
wata rana da yamma wata kawar
Mabaruka wai ita Amal ta ziyarci
Mabaruka Lokacin da ta samesu
zaune suke cikin tangamemen
lambun shakatawar gidan Anas
yana karantawa Mabaruka wani
littafi na hausa wai shi SIRRINSU.
Tun kafin Mabaruka ta gama
gaisawa da Amal ta kura masa
idanu. Anas ya lura da irin kallon
da take yi masa, dan haka sai ya
yi sauri ya sunkuyar da kansa
kamar yana kallon littafin da yake
karantawa duk kuwa da cewa a
fakaice kallon kyawawan
kafafunta yake yi ta kasan littafin.
"Tashi ka koma daga ciki kadan
bamu guri zamu gana, idan mun
gama zan sa a kirawoka."
Mabaruka ta ce dashi, Anas ya
mike tsaye simi-simi kamar
tunkiya ya wuce cikin gidan
zuciyarsa na kuna. Kalmar ta yi
matukar kona masa rai, to amma
tunda dai an saye shi ya yarda ya
amince babu abinda zai iya
domin kowa ya sayi rariya ai ya
san ta zub da ruwa. Idan har
akwai abu daya da Anas ya
tabbatarwa da zuciyarsa shi ne
ba zai taba yarda ya batawa
Mabaruka rai ba, domin ya san
hakan na nufin rabuwa da ita,
shi ko ya san a yanzu ya gama
sabo da jin dadi kum...
"Anas." Ya juyo firgigit sa'ar da
muryar Mabaruka dake kwance
kusa da shi ta katse tunaninsa.
Mabaruka ta dubi agogo, sannan
ta yi mika ta dubi Anas cikin
mamaki ta ce.
"Lafiya na ganka a zaune haka
tunda asussuba." Ta dan yi shiru
sannan sai ta miko siraran
hannunta ta shafi bayan Anas.
"Ko ba ka da lafiya ne?" Ta
rikoshi ta mike zaune,
nannadaddun kafafun da Anas
ya tsana fiye da komai a jikinta
suka fito fili. Anas ya girgiza kai.
"Kaina ne ya ke dan sara
min...amma na san nan da dan
lokaci zai bari daman lokaci-
lokaci yakan yi min haka."
Mabaruka ta dubeshi cikin
shakka da mamaki ta ce.
"Ina jin rashin yawan motsa jiki
ne..." Ta dan yi shiru, sannan sai
ta ce ya kamata na hada mana
wata hadaddiyar liyafa ta
shakatawa a gidan nan, ina
ganin haka zai sa ka dan
warware, kuma kamata ya yi
bayan liyafar mu tafi kasashen
turai hutu, domin tuntuni ya
kamata ace mun tafi mun yi
(honey moon) dinmu a can,
dadin da bana ji sosai ne ya
hana."
Ta dan yi shiru tana duban
fuskar Anas "Ko kuwa ya ka
gani." Anas ya ji wani dadi ya
lullubeshi domin tabbas ya san
irin liyafar miloniya me take nufi
ko shakka ba ya yi za a tara zuka-
zukan mata kyawawa, abin da
idanunsa suka fi kaunar gani fiye
da komai a duniya. Don haka sai
Anas ya dubeta cikin sauri ya ce.
"Kwarai kuwa haka za a yi liyafa
ba lallai kin zo da dabara." Suka
fashe da dariya, sannan
Mabaruka ta dora kanta bisa
cinyarsa ta rungumoshi fuskarsa
kusa da tata, abin da Anas ya yi
matukar tsana, ta ce.
"Anas wai don Allah me ka fi
kauna fiye da komai a duniya?"
Anas ya dubeta cikin mamaki
domin tambayar ta zo masa a
bazata, kadan ya rage ya ce da ita
kyawawan mata, to amma da
yake tsohon kwararre ne a sanin
tarkon mata ya fahimceta don
haka sai ya dubeta da tattausan
murmushin yaudara ya dada
rungumota a kirjinsa ya ce.
"Abin da na fi kauna a duniya ki
ke son ki sani?" Mabaruka ta
gyada kai cikin murmushi. Anas
ya dubeta a tausashe duk kuwa
da cewa zuciyarsa kamar ta
tsage saboda haushi ya ce.
"Ke na fi kauna fiye da komai a
duniya."
Mabaruka ta lumshe idanu cikin
tsananin farin ciki Tun da take a
duniya bata taba jin kalamin da
ya faranta mata rai kamar
wannan ba. Wani zazzafan
hawaye na farin ciki ya yi sartu
akan fuskarta.
***
Sidi mai jaka ya dauki dunkulallen
tubanin karshe ya jefa a bakinsa,
ya dubi kwanon cikin takaici,
sannan ya dubeni ya ce.
"Nas, ranar liyafa ta zo. Kamar
yadda Anas ya yi tsammanin tun
farko haka ta kasance domin duk
kusan kala-kala ta kyawu na
mata babu wadda ba a hada a
wurin ba. Liyafar ta sami halarta
mata kyawawa ashirin da uku,
maza goma kacal wadanda mafi
yawa ma daga cikinsu duk Anas
ya girmesu.
Aka yi ciye-ciye da shaye-shaye a
tangamemen lambun
shakatawar, aka saki kidan dujal
yan mata da samari masu
karancin kunya suka fara tikar
rawa.
A can gefe guda gindin wata
katuwar lema fara, Mabaruka
gurguwa ce da angonta Anas, ta
caba kwalliya ta gani ta fada, to
amma a wurin Anas kukun dake
rabon abinci ma a wurin tafi
Mabaruka kyawun fasali.
.
A daidai lokacin da liyafa ta yi
liyafa ne to zazzakar murya mai
kama da sarewa ta daki dodon
kunnen Anas Nan da nan ya ji
numfashin sa ya dauke ko
shakka ba ya yi ya san mai
muryar.
"Yaya Mabaruka ki yi hakuri don
Allah wallahi unguwa muka je
sai yanzu na sami damar
karasowa." Mai zazzakar muryar
ce ke magana sa'ar da ta matso
kusa da su cikin sauri.
Anas ya kura mata idanu cikin
tsananin shauki, zuciyarsa na
harbawa, rabonsa da ganinta tun
ranar da ya fara haduwa da ita.
In ba dan muryar ba da zai yi
wuya ma ya ganeta domin ta
dada tsayi kadan ta dan kara
kauri haka nan kyawunta ya
dada bayyana a fili har daukar
idanu fuskarta ta ke yi. Anas ya yi
mamakin ganinta matuka.
Budurwar mai zazzakar murya
ba wata bace da ta wuce Ummi,
budurwar da ta kirawo wa
Mabaruka Anas a ranar da suka
fara haduwa a wurin liyafar bikin
haihuwar Mabaruka.
Sidi Mai jaka ya dan yi shiru
sannan ya dubeni ya ce.
"Nas, ina fata ka tuna ta?" Na
gyada kai cikin kaguwa domin
na fahimci kamar ma yanzu ne
labarin tsohon zai fara dadi. Sidi
mai jaka ya ce "Yawwa Nas,
sannan ya ci gaba.
Mabaruka ta dubi budurwar cikin
farin ciki sannan ta ce.
"Ba ki da kirki Ummi kada ma ki
yi kokarin wani kare kanki, idan
yanzu kin zo a makare, to me ya
hana ki zuwa liyafar aurena?"
Ummi ta rufe fuska cikin dariya,
sannan a karo na farko sai ta
dubi Anas da tausasshen
murmushi ta matsa kusa da shi
ta durkusa ta ce.
"Yaya Anas ina wuni..." Anas ya ji
wani dadi marar misaltuwa ya
kwarara cikin zuciyarsa. Cikin
sauri ya tausasa murya ya ce.
"Lafiya lau...Ummi!" Idan ya yi
kuskurensa na farko kenan kiran
sunan nata da ya yi. Ummi ta
dubeshi cikin mamaki ta ce.
"Ashe ba ka manta suna na ba."
Murmushin Anas ya fadada.
"Ai...tun...tun ..." Ya yi shiru
sanda
ya lura Mabaruka ta sunkuyar da
kai ta mance dasu. Anas ya mike
tsaye jikinsa na rawa ya dubi
Mabaruka ya ce.
"Darling bari in dan zagaya na
barku ku gana." Nan da nan
fuskar Mabaruka ta washe domin
zamansa da Ummi shi take tsoro.
"Kwarai kuwa gara ka bamu
wurin domin muna son mu yi
sirrinmu na mata." Anas ya mike
ya nufi cikin farfajiyar lambu inda
samari da yan mata ke ta sheke
ayarsu, babu wanda ya kula
dashi, domin ba a sanshi ba
matar aka sani, sai yan tsirarun
da suka sami damar halartar
liyafar aurensa ne ke gane shi,
suma shekeke suke gayar dashi,
domin sun san shi ba kowan
kowa bane ya dillalin kashi.
Anas bai iya tsayawa cikin jama'a
ba, sai ya zagaya can bayan
lambun ya nemi karkashin wata
inuwa mai yawan bishiya ya
zauna. Bayansa jingine da
bishiyar, daga inda yake zaune
yana iya jiyo kida na tashi gami
da hayaniyar samari da yan mata.
Anas ya lumshe idanunsa,
sannan wutar kauna da bege ta
fara kona cikin zuciyarsa. Ko
shakka ba ya yi kaunar Ummi ta
fada zuciyarsa, tun sa'ar da ya
fara ganinta irin begenta ya
shuka kansa cikin zuciyarsa, a
yanzu irin ya girma ya fito fili.
Abin da ya fi damun Anas shi ne
bai san yadda za a yi ya girbi
bishiyar kaunar dake cikin
zuciyarsa ba. Mabaruka! Ya kira
sunanta a sanyaye, ita ce kadai
babbar katangar dake tsakaninsa
da Ummi haka nan...
"Anas." Zazzakar muryar ta katse
tunaninsa. Ya juyo firgigit, ya ce
bakinsa na rawa.
"Ummi." Ummi ta dubeshi da
murmushi ta ce.
"Ashe nan ka dawo Mabaruka na
can tana jiranka." Anas ya dubeta
ya sunkuyar da kai ya ce a
sanyaye.
"Har kun gama tattaunawar?"
Ummi ta gyada kai da murmushi
sannan sai ta sunkuyar da kai
tana wasa da siraran yan
yatsunta
Tsawon lokaci matasan biyu
suna nan tsaye suna duban juna
Wutar bege ta dada ruruwa cikin
zuciyar Anas musamman sa'ar da
iska ta buga kamshin turaren
dake jikinta zuwa hancinsa.
"Ummi." Anas ya kirawo sunanta
a sanyaye.
Ummi ta matsa kusa dashi
sannan ta dago kai ta dubeshi
ido da ido ta ce "Anas."
Anas ya yi sororo jiki na rawa ya
kasa cewa da ita komai akwai
wani irin kwarjini a jikinta da ya
karya zuciyar Anas duk kuwa da
kwarewarsa a harkar mata. To
amma duk da haka sai ya sake ta
yan maza ya ce.
"Ummi..wani abu ne ke damuna
wallahi na rasa yadda.." Ummi ta
katseshi ta hanyar dora hannu a
bakinta ta ce
"Ba sai ka fada ba, na san abin
dake damunka sai dai nan ba
wurin da ya dace a yi irin
wannan magana ba ce." Ta yi
shiru sannan sai ta mika masa
wata yar takarda ta ce.
Gashi nan sai mun hadu, ka yi
sauri ka koma tana can tana
jiranka ka santa da zargi." Tana
gama fadin haka sai ta juya da
sauri ta bar shi anan tsaye. Wani
zazzafan gumi ya kwararo tun
daga keyarsa har zuwa gadon
bayansa. Ya ji kamar ya bi
bayanta a guje domin ya tabbata
a yanzu bashi da wani sauran.TSOHON ALKAWARI-8
.
Wani zazzafan gumi ya kwararo
tun
daga keyarsa har zuwa gadon
bayansa. Ya ji kamar ya bi
bayanta a guje domin ya tabbata
a yanzu bashi da wani sauran
farin ciki a duniya da ya wuce
Ummi, to sai dai kuma wani
bangare na hadamammiyar
zuciyarsa na cewa "Uhum-uhm
Anas ka bi a hankali yanzu fa
zabinka biyu ne ya rage a
rayuwarka ta duniya, ko dai ka
zabi kudi da tashin hankali ka
bar Ummi, ko kuma ka zabi
Ummi ka bar kudi.
***
Karfe goma sha daya saura minti
uku na dare, Mabaruka da Anas
suka shiga dakin kwanansu.
Tun daga sa'ar da ya koma
wurin. Mabaruka a farfajiyar
lambun ya lura da cewa lallai yau
akwai masifa domin ta cika ta yi
fal har wani kumbura take yi.
"Ina ka tafi ka zauna ina ta
nemanka?"
Mabaruka ta tambayeshi a fusace
sa'ar da Anas ya dawo ya zauna
a kusanta. Bi a hankali dan
samari wata zuciya ta ce dashi.
"Ina can baya a zaune muna
gaisawa da bakin ki." Mabaruka
ta dubeshi a yatsine cikin
tsananin zargi sannan ta dauke
kai gefe guna.
Har bayan da suka gama sallamar
baki suka shiga dakin kwanan
nasu Mabaruka bata kara cewa
dashi uffan ba. Anas ya lura
saboda tsabar fushi bakinta har
wata kumfa-kumfa yake fitarwa,
haka nan duk illahirin jikinta
rawa yake yi kamar kamun
zazzabi.
Anas ya tura Mabaruka akan
kujerarta daf da jikin gadon
kamar yadda suka saba, sannan
ya yi yunkurin daukanta ya daura
akan gado. Ga mamakinsa sai ya
ji ta buge hannunsa a fusace.
"Ka da ka taba ni!...Na ce da kai
kada kabani munafuki...!" Anas ya
ja baya cikin kaduwa a tsorace.
"Me na yi miki?" Mabaruka ta kifa
fuskarta akan cinyarta, sannan
sai ta fashe da kuka mai karfi
jikinta sai rawa yake yi kamar
zata fado daga kan kujerar.
Tsohon lokaci sai ta dago kai ta
ce.
"Me ye...hadinka da Ummi?!" Anas
ya yi kokari ya sa alamun rudewa
akan fuskarsa ya ce.
"Ummi kuma...ba kawarki ba ce
ni ban ma taba ganinta ba sai
sau biyu kuma duk a dalilin ki."
Mabaruka ta ci gaba da
shisshikar kuka sannan ta nuna
shi da dan yatsa ta ce.
"Anas, ina son ka sani cewa na
aureka ne don ni kadai ba don
ka samar min kishiya ba. Na yi
maka abin da duk duniya babu
wanda ya isa ya yi ma haka ba
don komai ba sai don cikar farin
cikina." Ta dan yi shiru tana
mayar da numfashi.
"Tun farko sai da na ce sayenka
zan yi Anas ban fada maka ba?
Idan kuwa haka ne to kai nawa
ne ba na kowa ba, don haka
daga yau sai yau zan gargade ka,
babu kai babu Ummi, koda ta zo
gidan nan bana son ka kara ko
da kallonta ko gaisawa ban yarda
ku yi ba, kai ba ma Ummi ba duk
wata mace a duniya in ta wuce
kanwarka ta jini ko mahaifiyarka
ban yarda ku gaisa da ita ba,
kuma daga yau ka daina zuwa
wurin aiki, zan ci gaba da
biyanka albashinka na fi son
daga yanzu kullum kana tare
dani kana faranta min, duk inda
zaka daga yanzu tare zamu ke
tafiya, dare da rana safe da
yamma, ruwa da iska kai ko
bala'ine bai isa ya rabamu ba,
domin muna tare zan manne ma
kamar cingam domin sayenka na
yi."
Mabaruka ta yi ajiyar zuciya
sannan ta daga dan yatsa ta
nuna shi ta ce.
"Idan kuma kana ganin da
takura, to ina shawartarka da ka
rubuta min takardar sakina
yanzun nan, sai ka hada naka ya
naka ka bar min gidana, amma
ka tuna daga lokacin ka daina
karbar albashin naira dubu dari
biyu ka daina karbar kudin da
mahaifiyata ta ke baka duk wata
ka kuma daina hawa motocina
kai hatta kayan da ka saya da
kudin mahaifiyata sai ka ajiye
min kayana kuma sai ka yi
sallama da fita wata kasa a
duniya domin na san a rashin
zuciya da lalaci irin naka da
wahala in zaka yi arziki a duniya
mutumin da ko sallah baya iya
yi!"
Anas ya yi tsaye sororo cikin
tsananin kaduwar da bai taba
irinsa a duniya ba. Wani abu mai
kamar gare-gare ya fara yawo a
cikin kwakwalwarsa, nan da nan
ya ji cikinsa ya murda kamar zai
yi amai
Cikin sauri ya dubi Mabaruka baki
na rawa ya ce
"Ki yi hakuri Mabaruka abin duk
bai kai da zafin haka ba." Anas ya
dada dafe ciki sannan ya dubi
Mabaruka.
Mabaruka ta sake fashewa da
kuka. Anas ya ji ba zai iya
daurewa kukanta ba dan haka
sai ya ruga bandaki a guje yana
zuwa sai ya fara keta amai. Bayan
tsawon lokaci ya gama zubar da
abincin da ya ci a wurin liyafar.
Daga bandakin yana iya jiyo
shisshikar kukan Mabaruka
hakan shi ya tuna masa da
guntuwar takardar da Ummi ta
bashi cikin sauri ya laluba
aljihunsa ya dauko takardar
sannan sai ya warwareta ya fara
karantawa......
.
Anas Tun da nake a duniya ban taba
sanin mene ne so ba domin ni
ko zance ma bana fita wurin
samari
To amma tun ranar da na dora
idanuna a kanka sai na ji duk
duniya bani da abin so kamar ka.
Na yi matukar farin ciki sa'ar da
na dubi cikin kwayar idanunka,
sai na tabbata kai ma kana
kaunata. Haka nan na yi bakin
ciki da ya kasance wannan
gurguwa ta yi min shigar sauri ta
aureka.
Wannan shi ya sa na yi amfani da
damar wannan liyafa domin na
isar da sakon zuciyata zuwa
gareka Na gode, zan tsaya anan,
idan har abin da nake zargi
gaskiya ne, na san zaka so mu
hadu.
Ga adireshina nan a kasa, zan
jiraka gobe gida tun daga karfe
bakwai na dare har zuwa goma
na dare...sai na ganka mai...
Ummai.
Anas ya kankame takardar a
kirjinsa cikin farin ciki sannan
kuma cikin tsananin rudewa.
"Daga yanzu duk inda za ka
muna tare zan manne maka
kamar cingam!"
Ya tuna da kalaman Mabaruka.
"Ina jiranka gobe a gida..."
ya kuma tuna da kalaman Ummi
na karshe.
Anas ya lumshe idanunsa,
sannan ya kara takardar wasikar
akan hancinsa, ya shaki kamshin
turaren jikin Ummi dake jikin
wasikar, cikin jin dadi.
Daga can falo ya jiyo gurnanin
kukan Mabaruka. Anas ya yi sauri
ya toshe kunnensa domin baya
son kukan ya bata masa farin
cikin da yake, kai da zai yiwu ya
gwammace ya kwana cikin
bandakin rungume da wasikar
Ummi!
Sidi mai jaka ya yi shiru lokaci
guda. Na dubeshi cikin kaduwa
na ce bakina na rawa.
"To mana Baba Sidi...ci gaba
mana ya ka tsaya bayan labarin
ya gama daukar dadi."
Sidi mai Jaka ya dubi kwanon
tubanin dake gabansa cikin
takaici, sannan ya dubeni da
kyau ya ce.
"Kada ka bari dadin labari ya
dauke ka, saurara da kyau ka ji
kiran sallah ake yi. Tashi ka je ka
yi sallah idan an idar da sallar sai
mu sako wani sabon zaren
labarin." Yana gama fadin haka
sai ya mike tsaye ya dauki
tsohuwar butarsa ta karfe mai
kwarin tsiya ina tsammanin
butar tafi shekaru arba'in.
Na mike tsaye cikin sauri na ce.
"Baba Sidi dan Allah...da na gama
sallah fa zan dawo." Baba Sidi ya
dubeni da murmushi ya ce.
"Idan za ka dawo ka tabbata ka
dawo min da karin tubani, domin
idan babu shi, to babu labari Nas,
na riga na fada ma ni da tubani
tamkar tsohuwar mota ce da
man fetur.
Ya juya cikin sauri da butarsa a
hannu ya nufi waje zai yi alwala.
***
Ban sami damar dawowa wajen
Sidi mai jaka ba sai bayan sallar
La'asar sakamakon tsayawa da
na yi a sake dafa min sabon
tubani.
"Kai dan nema, bana son
shakiyancin banza, me kuma
zaka sake yi da tubani. Na dauka
dazu-dazun nan na yi ma cikin
kwano guda?" Kakata ce ke fadin
haka. Na dubeta da dariya.
"Kin ga in za ki dafa min ki dafa,
in kuma ba haka ba yanzun nan
in baki takardar saki akan
tubani." Ta fashe da dariya.
"Amma kuwa da ka yi abin kunya
wallahi ka saki matarka saboda
tubani?"
Daga karshe bayan mun sha
cacar baki kusan mintuna
bakwai, na shawo kanta da kyar,
ta sake cika min kwano da
tubani, a wannan karon har sun
fi wadancan girma domin ba a
son ranta ta yi su ba.
Na riski Baba Sidi mai jaka zaune
akan tsohuwar kujerar
katakonsa yana jan carbi, tun
kafin na gama yi masa sallama ya
dago kai ya dubi kwanon dake
hannuna cikin fara'a, kamar
karamin yaron da ya yi ido biyu
da alewa mai tsinke.
"Tsohon alkawari a karo na biyu,
lallai Nas ka kyauta min." Ya ce
sa'annan ya mika hannu ya karbe
kwanon daga hannuna tun ma
kafin na ajiye shi da kaina. Sidi
mai jaka bai jira komai ba, sai
kawai ya bude kwanon tubanin
ya fara juya tubanin da yan
yatsunsa bayan wani dan lokaci
ya tabbata da cewa sun juyu
yadda ya ke so don haka sai ya
can ku wani kato ya jefa cikin
bakinsa sannan ya dubeni.
"Nas, ina fatan dazu kana biye
dani a labarin da na fara baka."
Cikin sauri na gyada kaina.
"Kwarai kuwa ka tsaya inda Anas
ya shiga bandaki ya fara karanta
wasikar Ummi harma take cewa
dashi tana son ganinsa a daren
washe garin ranar
Sidi mai jaka ya gyada kai da
murmushi.
"Wani lokaci ina son mutum mai
saurin rike al'amura a cikin
kwakwalwa nan da nan ba tare
da mantuwa ba." Na dubeshi da
murmushi a karo na farko na ce.
"Ai kuwa in ka dauke labarai
babu abin da kwakwalwata ke
iya rikewa domin koda sunan
mutane in ba dadewa muka yi da
kai ba sai ka yi ta zuwa ina
kiranka da kai!" Sidi mai jaka ya
fashe da dariya sannan ya canko
wani katon tubani ya sha ya ji
jajur dashi ga girma kamar
dankali ya miko min.
"Ungo wannan Nas jefa a bakin
ka." Na yi saurin girgiza kai cikin
kaduwa.
"Allah kuwa karbi baka jiba
yadda tubanin nan ya yi dadi...TSOHON ALKAWARI-9
.
"Ungo wannan Nas jefa a bakin
ka." Na yi saurin girgiza kai cikin
kaduwa.
"Allah kuwa karbi baka jiba
yadda tubanin nan ya yi dadi har
ya fi na dazu." Na dada girgiza
kai. Sidi mai jaka ya zunkuda
kafada, "Ka cuci kanka Nas, ni
duk abincin duniya ban ga abin
da zai zo a na biyun tubani ba a
gare ni. Ya sake tsikaro guda ya
jefa a bakin salatinsa sannan ya
juya ya dubeni idanunsa na
zubar hawaye kamar kuturu.
"Nas, zaren labarin dana fara
baka labari dazu ya kare iyakarsa
kenan." Na dubi Sidi mai jaka
cikin kaduwa.
"Haba Baba Sidi, kai fa ka ce

Please Login or Register in order to submit comment