Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

inda takeba.

Hanan tadawo inda yake tazauna tana kallonshi tace"yaya Rafeeq kayi haquri bazan sake aikata irin hakaba,kuma nayi maka alqawarin zan fadima su Abba gsky akan qazafin da nayima Zuhra,duk abinda kaga inayi *A DALILIN KANE*,ina sonka sosae kuma banason abinda zaesa ciwonka yatashi............

*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*

*110-115*

Hanan tagoge hawayen da suka zubo mata taci gaba da cewa"yaya Rafeeq dan Allah yaushe ne zaka soni?yaya Rafeeq katemaka min,katina lokacin da nadauka ina dakon soyayyarka,amma ae........."

Mami ce tashiga tare da sallama,tare suka ansa..

Mami tace"Rafeeq taso dector yazo dubaka,tayuwa wurin Hanan tace kije kici abinci kinji,banason kina zama da yunwa wani ciwon sae yakama ki"

Hanan tayi murmushi tace,tou Mami"

Rafeeq yatashi yabi Mami.

Bayan yan gwaje2 da dector yyi yana samun sauki sosae,kuma yaqara jaddadama su Abba cewa ba'ason ranshi yana yawan 6aci,tare da yawan tinani,sannan yaqara bada magunguwa,yyi sallama da su Abba yatafi.

Yaya Rafeeq yatashi yatafi part dinshi sbd jiyake Hanan nayawan damunshi da surutu.

Abba da Mami suna zaune porlour Hanan tashigo tare da sallama,bayan sun ansa tayimasu sannu da hutawa.

Cikin jin dadi suka ansa kamar kullun dan jinta suke kamar yar su.

Mami tace"Hanan kindae ci abinci ko?"

Hanan tayi qasa da fuska tace"eh Mami naci"

Mami tace"kaga Alh. tinda Rafeeq yafara rashin lafiyar nan Hanan batacin abinci,gaba dayansu sunfita hayyacin su"

Abba yace"haba Hanan aeke yakamata kiriqa kwatanta mashi,bawae kutaru kuzama daya ba,kiyi haquri kinji insha Allah yayanki zai samu lfy sosae fiye da can baya"

Hanan tagoge hawayen da suka zubo mata tace"Allah yasa Abba"

Suka ansa da ameen ya rabbi.

Hanan tace"dama Abba wata magana ce nakeson fada maku"

Abba yyi murmushi yace"munajin ki yar Abba"

Hanan tace"dama maganar da nafada maku akan Zuhra ba gaskiya bane,amma dan Allah kuyafe min,wlhy son yaya Rafeeq ne yasani aikata hakan"

Taci gaba da kuka.

Abba yace"wacece Zuhra kuma?"

Hanan tace"itace wadda yaya Rafeeq yakeso"

Mami tace"Hanan kina nufin qazafi kika yima yarinyar mutane har aka koreta daga makaranta?"

Hanan tace"eh Mami,amma wlhy natuba Abba bazan sakeba"

Mami tayi salati tace"amma Hanan baki kyauta ba gsky"

Abba yace"ban fahinci abinda take nufi ba"

Mami tayima Abba bayanin duk abinda yafaru.

Abba yace"gsky Hanan baki kyauta ba,amma Alhmdllh da kika gane kuskurenki awannan lokacin"

Abba da Mami sukayi mata nasiha sosae sannan kuma zasuje suba iyayen Zuhra hakuri akan abinda aka aikata mata.

Bayan kwana biyu,Abba da Mami zaune a porlour suna cikin firarsu.

Abba yace"dama akwae maganar da nakeso muyi dake amma ina tinanin yiyuwar abin"

Mami tace"ina jinka Alh."

Abba yace"akan maganar yarinyar da Rafeeq yakeso ina tinanin munema mashi aurenta sae ayi bikin tare,amma kuma ina tinanin hada mashi mata biyu kada suje suriqa sakashi cikin damuwa,kinsa mata basason dama da kishiya"

Mami tace"Alhmdllh,dama maganar da nakeso kayimin kenan Alh.,ai idan kuma bai aureta ba kumafa bazai dena tinaninta ba,sbd itafa yashiga cikin wannan yanayin"

Abba yace"kumafa hakane,Maryam kinkawo shawara mai kyau,amma bari inkira wayarshi yazo yanzu"

Abba yakira layin Rafeeq yace mashi yana nemanshi yanzu.

Bayan 5mins yashigo tare da sallama,cikin jin dadin ganinshi kuka ansa.

Yagaishe da su cikin girmamawa,suka ansa tare da tambayarshi ya kkejin jikin naka yanzu.

Yaya Rafeeq yace"ina samun sauki sosae"

Abba yace"Alhmdllh,dama maganar yarinyar nan Zuhra,munyanke shawara zamuje munema maka aurenta tare da ba iyayenta haquri akan qazafin da akayimata"

Yaya Rafeeq da sauri yadago kyawawan idanuwanshi yana kallon Abba,ji yake kamar mafarki yake.

Mami tayi murmushi tace"kana mamaki ko Rafeeq?,tou ashirye muke da musakaka cikin farin ciki kamar yadda yake sakamu Rafeeq,muna alfahari da kae,kuma muna sonka sosae"

Yaya Rafeeq yace"hakika nayi dacen iyaye nagari,Allah nagode maka daka hadani da iyayena masuson farin cikina kuma suka bani tarbiya tare da kyakykyawar kulawa,Abba,Mami nagode sosae"

Abba yace"haba Rafeeq kaifa dammu ne,miye abin godia aciki,sbd kada 6ata mamu kashiga cikin wannan halin fa,dan haka bayan ansaka lokacin bikinku zamu tafi Egypt domin aqara duba lfyrka,idan muka dawo lfy sae ayi bikin,amma fa ina nufin zaka auresu su biyu"

Mami tace"sae ayita haquri kuma kayi masu adalci"

Yaya Rafeeq yyi godia sosae,amma shi haryanzu baijin son Hanan acikin zuciyarshi,saedae bbu yadda zaeyi dole ya aureta,amma yazai qare da Zuhra itada batace tana sonshi ba.

Koda Abba yasanar da daddy maganar zuwa wajen iyayen yarinya,daddy yyi farin ciki sosae.

Mami ce tasanar da Islam zuwansu Abba gidansu Zuhra,Islam tayi masu qwatancen gidan tare da unguwar.

Mami tasanar da Abba,washe gari wajen karfe 10am suka shirya suka tafi.

Azziqi na Allah,an qara gyara gidansu Zuhra har mota Baba yasaya kirar HONDA CIVIC amma 2 door ce,bake motar tayi kyau sosae,dahar Baba yafara maganar tafiyarta karatu a BUK.

Zuhra na zaune tagama break kenan Islam takirata,suka gaisa nan take fada mata su Abba yasuzo wajen Baba,Zuhra tayita fama da Islam tafada mata abinda ke faruwa amma taqiya haka sukayi sallama.

Zuhra tasanar da Mama zuwansu Abba amma batasan komi yasuyiba,Allah yasa lokacin Baba bae fitaba,Mama tasanar da shi,yyi mamakin zuwansu,haka yazauna bae fitaba,Mama tayi masu abinci tare da coconut juice wanda yaji madarar ruwa.

Koda su Abba sukazo Baba yyi masu tarba mai kyau sbd Baba mutunne mai kirki,sukaba Baba haquri akan abinda yafaru,Baba yace haka Allah yakawo,bbu komae.

Bayan sundan jima suka gabatar da buqatarsu taneman auren Zuhra,Baba yace ae Rafeeq bbu abinda zai nema yarasa agurinshi,dan haka yabashi,nan aka tsaida magana wata biyu suka bada sadaki 300k,Baba yace sunyi yawa amma sukaqi ragewa haka suka gama magana cikin jin dadi suka tafi.

Baba yashigo gida yyima Mama bayanin yadda akayi,taji dadi sosae sbd itadae tarbiyar yaron tayi mata,Baba yace gobe zaije kauye yasanar da qaninshi abinda ke faruwa tare da bashi haquri.

Koda Mama tasanar da Zuhra halin da ake ciki,Zuhra batace komaeba banda turo baki da tayi tatashi tanufi dakinta,Mama tabita da kallo tace tou Allah yasa kigane.

Rafeeq yaji dadin labarin da Abba yasanar da shi sosae,su Islam sunji dadi sosae sbd sudai sunason Zuhra.

Koda labari yajema Hanan akan subiyu Rafeeq zae aura tayi kuka kamar ranta zai fita bbu yadda ta iya dole tadangana,tare da lallashin Mummy.

Bayan sati hudu da saka ranar bikinsu,suka fara shirye2 tafiya Egypt tare da Mami da Abba za'a tafi saeshi uwar gayyar Dr. Rafeeq.

Ana gobe zasu tafi,yashirya tsaf cikin shigar manyan kaya yafadima Mami zaiye yyi sallama da su Baba,tace adawo lfy kagaishe min da su.

Motarshi qirar ANACONDA 2017 fara sul yashiga bbu inda yaci burki sae kofar gidansu Zuhra..................

*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIA TION🤝*

*115-120*

Wani farin ciki yakeji wanda baya musaltuwa,yadan jima acikin motar kafin yashigo.

Yana fitowa yasamu yaro ya'aikashi cikin gidan yace kace Rafeeq ne yazo,yaron yashiga bayan mintina kadan yadawo yace ance kashigo,Dr. Rafeeq yabashi kyautar dari biyar sannan yatafi.

Shiga yyi cikin gidan sannan yashiga porlour tare da sallama,Mama ce kadai acikin gidan Baba bayanan Zuhra kuma tana islamiya.

Mama ta umarceshi da yazauna cikin kulawa,yaya Rafeeq yashiga gaishe da ita cikin girmamawa.

Mama ta'ansa cikin jin dadi,yaya Rafeeq sae wani jin kunya yakeyi irinna sirinkai.

Nafef ce tasauketa qofar gida sanye take cikin uniform ruwan toka,sunyi mata kyau sosae tasaka very long hijab dinta.

Tinda taga danqareriyar mota akofar gidansu zuciyarta keyi mata sake2,tana tambayar kanta kodai yaya Rafeeq ne yazo?,dasauri taba kanta ansa tace Allah yasa shine.

Cikin sallama tashiga porlour kamshin ni'imtaccen turarenshi yadokar mata zuciya daqer tasamu tayi sallama.

Mama da yaya Rafeeq suka ansa.

Kanta aqasa tagaishe da shi sannan tanufi room dinta.

Yaya Rafeeq yace"Mama dama zuwa nayi infada maku gobe ne zamu tafi,kuma nayi maku sallama"

Mama tace"ashe tafiyar tazo Rafeeq,tou Allah yasa ayi nasara,Allah yatemaka"

Yaya Rafeeq cikin jin dadin addu'ar ya'ansa da ameen.

Mama tace"saedai kuma Malam bayanan amma insha Allah zan sanar da shi zuwanka"

Yace"tou shikenan Mama nagode"

Mama tatashi tanufi room din Zuhra,Mama tatarar da Zuhra tana cire uniform da niyyar shiga wanka.

Mama tace"kije yana jiranki,kuma tinda sae nace kikai mashi ruwa tou nace yanzu sai kikai mashi,akwai fruit salad danayi yana cikin freedge sae kikai mashi tare da abinci"

Zuhra tace"tou Mama"bata tsaya wani bata lokaciba sbd tasan halin mama sarai.

Mama tana fita Zuhra taturo baki cikin zuciyarta tace wannan mutumin yadameni da yawa.

(Ni missj nace wai Zuhra me kike nufi ne🤔)

Tasaka wata doguwar riga sannan tazubula dogon hijab dinta tafita.

Cikin sallama tashiga porlour hannunta dauke da tray.

Yaya Rafeeq yadago kyakykyawar fuskarshi tare da ansa sallamarta,baisan lokacin da yyi murmushi ba,Zuhra tasukuyar da fuskarta tayi mashi sannu da zuwa.

Zuhra tatashi zata fita da niyyar dauko coolers din abinci.

Yaya Rafeeq yace"dawo ki zauna plz"

Zuhra tace"zanje nadauko abinci ne"

Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"ae ganinki da nayi yaqosar dani Zuhra,na dade banganki ba"

Zuhra dae batace komae ba.

Yaya Rafeeq yace"kinbarni inata magana ni daya Zuhra"

Zuhra tace"tou ni me zance yaya Rafeeq?"

Yaya Rafeeq yadaure fuska yace"tambayana ma kike?,tou shikenan ni zantafi,amma idan bazaki damuba inaso kimin rakiya wurin motana"yatashi tsaye yafita.

Zuhra tabi bayanshi,harsuka fita waje,motarshi yabude yafiddo wata leda sannan yafito yamiqa mata.

Yace"akwai waya aciki nakine"

Zuhra duk sae bataji dadin maganar da tafadi mashiba tace"yaya Rafeeq naga kamar ranka yabaci?"

Yaya Rafeeq yace"ba dole raena yabaciba Zuhra,yaune ranar dana fara fita sbd ke,amma bakida abinda zaki fadamin"

Zuhra tamarairaice murya tace"dan Allah yaya Rafeeq kayi haquri"

Yyi murmushi yace"bbu komae Zuhra ni zantafi kiyimin addu'a"

Zuhra tace"Allah yabada sa'a,Allah yadawo mana da kae lfy"

Ya'ansa da ameen sannan yashiga mota tare da sae munyi waya.

Washe gari da safe jirginsu yatashi zuwa Egypt.

Bayan sati ukku da tafiyarsu aka gama binkice tare da shanye magungunan da aka qayyade mashi.

Abinciken da likitoci sukayi naqarshe sungano Rafeeq yasamu sauki sosae bbu wani abu dake damunshi.

Ana saura sati daya biki suka dawo gida Nigeria,sae shirye2 biki ake tare da murnar dawowar ango,agidansu suka tarar da Hanan tazo tarar angonta,su Islam da Iman sundawo gida.

Dukda takaicin dake damun Hanan na hadata da Dr. Rafeeq yyi da Zuhra bai hana Hanan yin events din bikinsu ba,tin ranar wednesday ake event har ranar walima,bbu event dinta da yahalarta sbd yace bbu abinda za'ayi wanda baza ayishi da Zuhra ba,ita kuma tace bazatayi da Zuhra ba.

Saedae wanda Fans dinshi suka hada da wanda family dinsu suka hada,sune yahalarta kuma suma hada Zuhra.

Ankashe kudi kamar ba'aso haka aka daura aure daurin auren da yahaqa manyan yan siyasa da yan boko tare da masu hannu da shuni.

Haka akai amare dakinsu gidane babba me dauke da 3 parts kowace da part dinta sae kuma na oga.

Duk hidimarnan da ake Islam da Iman suna kusada Zuhra,sune qawayen amarya.

Part din Zuhra yyi kyau sosae ankashe mata kudi abin mamaki dama hausawa sunce fadama mai zuciya biki ba me kudi,komae na part dinta coffee da milk yyi kyau sosae,mutane sae santin part dinta da abinda yake ciki suke.

Haka kowa yawatse part din Zuhra sae Islam da Iman.

Sune suka qara gyara mata ko ina,suka feshe part da room freshner tare da na'urar dake zuba turarukan wuta.

Iman tace"Islam taso mutafi kada yaya Rafeeq yashigo yatarar da mu"

Islam tace"ae munanan sae munga shigowar ango"

Zuhra tamarairaice fuska tace"dan Allah ku kwana anan"

Islam taware ido tare da daukar jakarta tace"kinsama natashi tafiya yanxu,Iman taso mutafi"

Zuhra tayi saurin dauke mayafin Iman tace"ni kuma bazan bayarba,sae kun kwana agidan nan"

Iman tace"haba Aunty Zuhra ae saekin gaji da ganinmu agidannan amma dae yau gaki ga yaya"

Zuhra tace"hmm tou zo ki'anshi mayafinki"da niyyar idan Iman taxo tariqeta ae kuma da hanzaro suka fita sbd sungano logic dinta... ..........

*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*

*120-125*

Suka fita suna zolayarta,Zuhra kamar zatayi kuka haka suka tafi suka barta ita daya.

A6angaren Hanan,zaune take gaban dressing mirror ansha make-up tayi kyau sosae,sae faman qara gyara fuska take,tadaura kallabi takwance,itadae babban gurinta tafaranta ma mijinta rae.

Gsky ankashema Hanan kudi kamar ba'aso part dinta yyi kyau matuqa,dakagani kasan muhallin yar gata kuma masu da shi.

Bayan taga nada kallabin tafeshe jikinta da turaruka masu dadin kamshi tare da humra,takoma bisa lafiyayyen bed dinta tazauna tana jiran angonta dan ita tamance da wata Zuhra da yahadasu ya'auro.

Har 11pm bbu ango bbu labarinsa ita Zuhra har tamance da tayi bacci,dama tadade batayi bacci ba.

Hanan tin tana zaune harta dan kishingida har tazo takwanta,amma duk tana jiranshi.

Baishigoba sae 11:30pm yyi parking din motarshi a harabar gidan sannan yafito dauke da ledoji ukku a hannunshi.

Cikin bacci taji alamar abude tama bedroom anshigo,daqer tasamu tabude idanuwanta batare da tayi motsiba sbd tsoro,cikin arashin sa'a tana bude idanuwanta taga duhu ankashe wutar room din.

Tini jibi yafara sauko mata,dama atsorace takwanta,addu'a kawae take ji take kamar tanutse cikin kasa.

Akazo bakin gadonta aka tsaya,ae tini tafara zubar da hawaye dan tana tinanin ko 6arayi ne.

Ae tini tafara kurma ihu sakamokon lalubarta da taji amfara.

Da sauri yace"Zuhra nine mijinki"

Amma dukda haka Zuhra batayi shiru ba,yatashi yakunna wuta tini dakin yagauraye da haske.

Can yahangota qarshe gado tamakure tabi ta qudundune,fuskarta tayi sharkaf da hawaye tsabar tsorata.

Baesan lokacin da dariya taqwace mashi ba,bai taba ganin mai tsoro kamar Zuhra ba.

Zuhra tabishi da kallon mamaki sbd bata ta6a tinanin ya'iya dariya kamar haka ba.

Ahankali yatako inda kusa bed din shima yahau bisa yazauna kusa da ita yana kallonta.

Murya qasa2 yace"kin kusa taramin jama'a,ashe haka kike da tsoro"

Zuhra cikin zuciyarta tace kakusa samin hawan jini amma afili sae tashagwa6e fuska taci gaba da kuka.

Tini yarude yafara tambayarta,Zuhra lfy?,me ke damunki ne?,nine ko toyi haquri.

Yafara qoqarin goge mata hawayenta,ji sukayi ambanko qofa da sauri,gaba dayansu hankalinsu yakoma gurinta.

Hanan ce,atsaye fuskarta bbu alamar fara'a sae cika take tana batsewa.

Yaya Rafeeq yasauko daga bisa gado yataka har inda take tsaye.

Yace"lfy dae kika shigo mana bbu ko sallama?"

Hanan tace"yaya Rafeeq me kike anan?"

Ranshine yaqara 6aci yayi mata tsawa yace"ina tambayarki kina tambayana?,tou wurin matata nazo ko kinmanta da ita matata ce?"

Hanan tini hawaye suka fara zubo mata tace"ni kuma awane matsayi nake awurinka kenan?"

Yace"wannan kuma ansar na wurinki"

Hanan tayi murmushin takaici tace"tou shikenan nagode"tajuya tafita.

Zuhra bataji dadin abinda yyi ba dukda itama tanada laifi miye nashigo mani bedroom bbu ko sallama bare neman izini.

Zuhra tasauko daga bisa gadon takoma porlour tazauna,batare da tayi mashi magana ba.

Yaya Rafeeq yabita porlour yazauna kusa da ita yana fuskantar fuskarta yace"me kuma yafaru ne?"

Zuhra sanyaya tace"yaya Rafeeq abinda kayi bai daceba,dole Aunty Hanan zataji bbu ddi, amma dan Allah kayi haquri idan ranka ya6aci"

Yaya Rafeeq yace"kamar ya kenan?"

Zuhra tace"bawae ina nufin wani abu ba,amma yaya Rafeeq yakamata itama kaje part dinta kaduba halin da take ciki"

Yaya Rafeeq yatsaya yana kallonta,yarinya qarama amma tasan abinda yadace.

Yyi murmushi yace"ina jinki my wife"

Zuhra tace"kuma kaga itace babba part dinta yakamata kaje yau,dan Allah kaje kaga halin da take ciki yanzu naga ranta a6ace yake"

Yaya Rafeeq yace"tou shikenan,insha Allahu zanje yanzu,kuma inaso ciki abinci"yamiqa mata daya daga cikin lodojin ya'ajiye bisa centre table.

Yasa hannu yasha fuskarta sannan yyi mata murmushi sukayi sallama da juna,Zuhra tabishi tarufe part dinta.

Koda yashiga part dinta bata porlour yanufi bedroom dinta kwance take bisa gado kamar meyin bacci.

Yashiga tare da sallama,amma bata ansa ba.

Hanan tatashi zaune ranta a6ace dajin muryarta tasha kuka tagaji bakinta har rawa yake.

Tace"mi yakawoka part dina?,kafita banason ganinka Dr. Rafeeq kakoma wurin wadda kafiso,sae yanzu nagane nayi babban kuskuren aurenka wlhy"

Mamaki yabayyana afuskarshi yace"Hanan ni kike fadima irin wa'annan maganganun?,tou wlhy bazan dauka ba kuma kinsan waye Rafeeq zan kamaki ahannuna Hanan,saekin raina kanki"

Hanan batace komae sbd tsabar takaici.

Yace"abincinki na porlour idan kinga dama sae kici"

Kamar jira take yagama magana tace"banaci kakai mata tahada"

Yace"kina iya zubarwa"yafita ranshi abace.

Part dinshi yatafi sbd bayason yahana Zuhra bacci yau yasan agajiye take,zuciyarshi cike da takaicin magamnganun da Hanan tafadi mashi,amma zataji kuka da idanuwanta akan wannan maganar.

Hanan itama takasa bacci tasan yau da ita yaya Rafeeq zai kwanta,Allah yasa dae kada nazamo sanadiyyar tashin ciwonshi.

Wayarta talalubo da niyyar kiran aminiyarta Khubra domin tabata shawara,sae wata zuciyar tace kiyi haqurin gari yawaye mana.

Bbu yadda ta'iya dole tahaqura amma fa batayi bacci ba sbd tinanin yaya Rafeeq tanason shi tana kaunarshi kuma batason bata mashi rae,amma zancen gsky bazata juri wulaqancin shiba.

Hanan bata iyacin abincin ba hasalima bata buda taga mike cikin ledarba.tasaka cikin freedge sannan tatafi daniyyar takwanta,amma takasa bacci tarasa mike damunta,toilet tashiga tadauro alwala tafara nafilfili har aka fara kiran sallar asalati.................

*125-130*

Haka gari yawaye zuciyar cike da tinanin laifin data aikata ma Dr. Rafeeq,dukda itama bae yi mata dai2 ba.

Da asuba yaya Rafeeq yashigo da niyyar yatada Zuhra,yayi switch on din light,kwance take bisa lafiyayyen gadonta baccinta take cikin kwanciyar hankali.

Ahankali yake tafiya harya'isa bakin gadon,yaje saitin fuskarta sannan yadurqusa,kalllon kyakykyawar fuskarta yakeyi tare da murmushi.

Cikin zuciyarshi yake fadin Zuhra banaso natakura maki,ina sonki sosae,kamar yarda yakeson kaina.

Hannunshi yadaura bisa kyakykyawar fuskarta mai santsi kamar fatar jariri,har yakai cikin gashin kanta mai tsawo da taushi ga kamshi yaji gyara.

Shafa gashin yake harya soma fita hayyacinshi.

Da sauri tabude idanuwanta fuskarta cike da tsoro,sbd al'amarin yafara bata tsoro.

Suna hada ido yyi murmushi yace"sarkin tsoro nine mijinki"

Zuhra tace"yaya Rafeeq harkatashi,ya Aunty Hanan?"

Yadan yamutsa fuska yace"eh nazo kuma natada ke,lokacin sallah yyi"

Yamiqe tsaye yana fadin kitashi fa kada nadawo natarar da ke kina bacci.

Tashi tayi tare da dauro alwala tafara gabatar da sallah tare da nafilfili.

9am Zuhra tagama shiri cikin wani tsadadden material pink colour tayi kyau sosae,make-up tayi wadda taqara fitar mata d madarar kyanta.

Zaune take porlour tana kallo komae neat sae kamshi ke tashi tako'ina.

Yaya Rafeeq ne yashigo cikin shigar qananan kaya,riga blue da jeans black fuskarshi dauke da fara'a sakamakon ganin kyakykyawar matarshi da yyi.

Gashin kanshi yaji qara yanata shining ga kuma qamshi,yaqara wani kyau mai daukar hankalin duk wata mace.

Yaqaraso har bisa kujerar da take zaune shima ya zauna,yana kallonta.

Kafin tayi magana yace"my wife kinyimin kyau sosae fa,gsky nayi dacen mata"

Zuhra tayi murmushi tace"yayana katashi lfy?"

Yadan nisa yace"lfy amma ba lau ba"

Zuhra taware ido tace"lfy dae yaya Rafeeq me ke faruwa?"

Yaya Rafeeq yace"tinaninki ne yahanani bacci da kamar nadawo sae nayi tinanin kada natakura maki"

Zuhra tace"tinanina kuwa yaya Rafeeq kana tare da Aunty hanan,kadae kawae kana zolayana"

Bayason sanar da ita abinda yafaru dole yacanja maganar.

Hannunta yariqe yahada da nashi yana kallon cikin idanuwanta yace"Zuhra da gaske ne,kwana nayi ina tinaninki"

Zuhra tayi murmushi tace"nima haka yaya Rafeeq"

Kallonta yake cikin mamaki yace"Zuhra da gaske kindamu da ni?"

Qarar qaraurawa sukaji,da alama sunada baqo.

Zuhra tace"bari naje naga waye"tare da tashi tanufi bakin kofa.

Tana budewa taga wata mata hannunta dauke da basket tare da wata leda ahannunta,wacce bazata wuce shekara arba'in da wani abu ba,Zuhra tagaishe da ita tare da bata umarni tashigo.

Yaya Rafeeq yana ganinta yasaki fuska,bayan sungaisa tace gashi inji Mami tace akawo maku.

Haka yaya Rafeeq yyi mata kyautar kudi yasallameta tayi masu addu'a tare da fatan zama lfy sannan tatafi.

Zuhra tace"wae yaya Rafeeq yaushe su Iman zasuzo ne wlhy nati tinanin sune shiyasa nayi saurin bude gida,jiya bbu yadda banyiba sukwana anan amma suka gudu"

Yaya Rafeeq yadan harareta cikin wasa yace"a ina zasu kwana?"

Zuhra tace"anan mana yayana"

Yace"mijinki na gidan zakice wasu suzo sukwana"

Zuhra tashagwabe fuska tace"abinda tafiya kayi kabarni kuma kasan inajin tsoro"

Yyi murmushi yace"tou yau zantayaki kwana tinda tsoro kikeji"

Zuhra taware ido tace"a'ah rufamin asiri,Aunty Hanan nagidan,yanzu kayima Aunty hanan magana sae muje part dinta muyi breakfast"

Yace"muje part dina sae tazo muhadu acan"

Yaya Rafeeq yadauki kwando daya Zuhra tadauki leda suka tafi part dinshi,saeda Zuhra jera masu komae bisa dinningtable sannan ya'umarceta da takira Hanan.

Bbu yadda ta'iya dukda tsoron da takeji haka tabi umarninsa tatafi gabanta nafaduwa.

Yyi alqawarin kozain qara zuwa part din Hanan sae idan laluri amma hakanan bazae shigaba.

Zuhra tashiga part din Hanan,bbu kowa aporlour sae plasma dake manne da bango da keta fatan aiki.

Zuhra tafara sallama cikin zazzaqar muryarta,bayan kamar 7mins Hanan ce tafito cikin shigar qananan kaya batako ansa sallamarba,fuskarta cike da bala'i...................

*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*

*130-135*

Zuhra tasanyaya murya tace"Aunty hanan kintashi lfy?"

Hanan tawatsa mata harara tace"da bantashi ba zaki ganni ne?,me yakawo ki part dina munafika?"

Zuhra bata nuna mata ranta ya6aciba tace"yaya Rafeeq ne yace kizo muyi breakfast"

Hanan tace"bazan zoba,kinje kinyima

Please Login or Register in order to submit comment