Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyauta mai tsoka tajin daɗin addu,ar daya masa sannan ya dauki hanyar asibiti.
Lokacin duhun magariba ya soma kawo kai.
Yana kaiwa cikin asibitin ana kiran sallar magariba cikin sauri ya gama parkinga sannan ya fito.bayan ya kare fuskarsa da p.cap haka ya karasa cikin office ɗin DR SAFIYAN.

Zaune ya tarar dashi yana aikin rubuce-rubuce dan haka kansa tsaye shiga cikin toilet ɗin dake manne a office ɗin yay tare da ɗauro alwala sannan ya fito ya shinfiɗa carpet ya soma sallah, batare daya kula dr safiyan ba wanda tun shigowarsa yake masa tsiya irin ta abokai.
Bayan ya idar yay azkar sannan ya mike ya nufi gaban,sa.
"Malam kadai tashi kai sallah wanna duk shurmen banza ne".
Yakai maganar bayan yaja kujera ya zauna.
Aje rubutun yay tare da nufar bayin shima ya dauro alwala yazo ya tada sallah, seda ya idar sannan ya karaso.
"Dan haka nake sonka ya ustaz"
Yafaɗa cikin shaƙiyanci.
Shikam bai kulasa ba sanin halin safiyan na tsokana sema fito da wayarsa da yay ya turawa hidaya message akan tai hakuri yana nan cikin office ɗin dr safiyan amman yanzu ze taho.
Seda message ɗin ya tafi sannan ya ɗago ya dubi dr safiyan ɗin.
"Malam dafatan dai ka haɗamin magungunan nawa dan bana tsayawa jin shirmenka ina da abinyi".
Ɗauko masa ledar maganin dr safiyan yay gami da jefa masa.
"Kaidai halinka sekai. kai ɗaya wani zubin kaita kuncin rai kamar hidaya ta hanaka abinci"
Yafaɗa cikin dariya.
Shikam mikewa yay shima yana dariyar sabida safiyan idan yay wani abun kobakai niyar dariyar ba sekayi.
"Ni ai banyi kama da wanda mace zata raina ba, illah dai abin da nasani namiji ya zauna yanawa mace kurari da zagi ko duka ko wani abu marar dadi duk wawancine, bayan ka gama zage girmanka agabanta ƙila ma lokacin da kuna sex kuka kake mata amman, kazo daga baya kana wani kurarin banza bayan duk abinda kake boyewar ta gama sarrafa maka shi, ni aganina zaman mutunci da mutunta juna shiyafi komai daɗi azaman aure".
Yana kaiwa bai tsaya jiran dr safiyan ba yabar office ɗin cikin sauri bayan ya kare fuskarsa da hannunsa gudun kada wani ya shaida sa.
Daganan office ɗin dr harɗo yaje can clinic ɗin da aka kwantar dashi.
Statement ɗin nafeesah ya nemi dr harɗo daya basa bayan yay masa bayanin cewar ze nemeta ne yabata tallafi akan raunukan dataji. sabida jiyan aisha tazo masa da maganar wadda yaji tausayin yarinyar.
Murmushi dr harɗo yay sannan yace.
"Aikam naji daɗin yadda zaka taimaka masu ɗin, sabida yarinyar daga gani bamai wadataccen gata bace, danni kam jiya ina zargin rashin wadata yasaka suka karɓi sallama tunda jikinta bai warkeba kuma ciwukan dataji suna da yawa".
Bai kula dr ba illah ƙurawa, ɗan hoton ta dake jikin file ɗin ido dayay tare da nazarin sunan daya gani jikin file ɗin.
"Nafeesah kabeer kawai ya gani seda ga can ƙasa yaga an rubuta shekarun ta 17yrs, babu sunan anguwa babu lambar waya babu wata shaida wadda zata bayyana ainihin inda take.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un"!
Yafaɗa a bayyane wanda yasa dr hardo kanin mahaifiyarsa ɗagowa yana dubansa.

Cikin jan ido ya ɗago yana kallon dr harɗon wanda shima a lokacin kallon nasa yakeyi.

"Baffa harɗo yaya babu wata shedan daza,a ganeta illah hotonta babu phone number babu next of kind nata wannan ai babu wani evidance daze kawo ganinta nan kusa?".

Caka biron dr harɗo yay akan table tare da zare glass ɗin idanunsa.

"Wallahi muhammad na manta da duk wannan abun sabida yadda muka gigice da yanayin da aka kawo yarinyar amman wannan ba damuwa bane, tunda munyi da mamarta zata kawota dress na wajan, duk da yauma munyi zata zo amman har yanzu shuru wanda bamu san what happen da ƙin zuwan nata ba".

Yakai maganar yana duba tarin takardun gabansa.

Ƙilama ta mutu ya furta cikin wani irin yanayi, sannan ya mike tare da zira hannayensa cikin wandon jean na jikinsa sannan ya dubi dr harɗo.

"Zanje duk abinda yake faruwa baffa ka sanar dani idan tazo ɗin" yafaɗi hakan bayan yay kokarin mayar da damuwar sa cikin ransa gudun kada baffan nasa yay saurin gano wani abun.

Cikin busy na aiki dr hardo ya amsa masa sannan sukai sallama ya fita.

Yajima cikin mota yana tunani aransa kafin ya tada motar yabar wajan duk jikinsa a sanyaye.

Yau idan yarinyar nan ta mutu nima tabbas inada kamasho wallahi yazama tilas ba baza jama,ata a nemo min halin datake ciki.

Yafaɗa tare da kallon ɗan hoton nata daya yago a file ɗin .

"she is young girl" yafaɗa cikin tausayi ashe daman yarinya cema amman na zuba mata girmana na kusan shekara arba'in sosai yaji tausayinta ya kamasa tabbas yakusan haifar kamarta ma inda ALLAH ya basa haihuwa.

Bai koma gida ba se bayan isha dan seda yay sallah ma sannan ya shiga.

Sosai sukasha artabu da hidaya dan ta kulu dashi, sannan sukai dinner suka nufi master bedroom

Asuba tagari.


Abangaren nafisa kuwa.....!!
38 - 39

Ɓangarenta.


Ɓangaren nafisa kuwa baki ɗaya ta koma wata irin shuru-shuru fiyema da,da. bata fita ko ina daga tsakar gida se ɗaki tana karatun alkur'ani tare da zikirin ubangiji wannan lamarin daya faru da ita bakaramin firgita ta, yay ba sam bata doguwar magana idan ka dubeta da kyau kusan kullum bakinta motsi yake na alamun zikirin data duƙufayi tare da neman saukin ALLAH akan ciwon soyayyar anwar wanda babu laifi yanzu taɗan soma sakin jiki tafara mantawa dashi.
Sosai ta gane wautar datai na zuwa gidansa.
Wanda bata ko son tuna wannan mummunar ranar agareta.
Kwanci tashi kuma babu wuya a wajan ALLAH yanzun haka hutunsu ma ya kusan ƙarewa.
Kuma har yanzu bataje gidan kaka ba sannan kuma bata koma asibitin ba agida take zaune tana gyara jikinta yadda ya kamata kuma ALLAH ya taimaketa bata da ƙan jiki sosai wajan ya samu warkewa tafiyarta ta koma normal jikinta ma kuma haka.
Yau sun wuni da walida har dare sannan ya nura yazo ya dauki walida suka nufi gida.
Da mamakin nafisa walida ta kwan aranta ganin fafur taki yarda ay mata hiran mai girma MAS!.
Itakam nafisa walida na tafiya taja tsaki tare da komawa ɗaki ta kwanta tana jan numfashi sam bata ko son a faɗi sunansa agabanta sabida, yadda takejin wani irin soyayyansa gami da haushinsa sun cika mata zuciyanta.
Yauma da daddare ummah sahura na zaune a tsakar gida, tana sauraran redio itakam nafisa tana gefe ɗaya tana jin yadda gefen maranta yake yimata ciwo.
Ta fuskanci wannan watan bataga al'adanta ba amman bata damu ba sabida a farkon wata takeyinsa kuma gashi yanzun har wannan watan yazo tsakiya.
Amman shuru bataga komi ba, sema tsabar wani uban ciwon mara daya sakota agaba wanda baya tashi se cikin dare.
Umma sahura ke mata magana, amman sam batama jitaba.
muryan ummah sahura ne ya ƙara fita.
"Nace nafisa ko ina zamuga aisha likita oho yarinya mai mutunci, saurari kiji yadda wannan yaron arzikin yakaiwa gidan marayu tallafi, tace ɗan yayarta ne ai".
Basarwa tayi ta nuna kamar bataji mai umma take faɗi ba tare da ɗan kallonta kaɗan domin ta ɓatar da maganar.
"Umma yaufa sauran sati ɗaya mu koma makaranta, kuma naga har yanzu kaka batazo cigiyata ba kodai haushi taji".
Ɗan numfasawa umma sahura tai kana ta ce.
"A,a nikam bana tunanin haka sedai ko da malam yaje ( mijinta ) yay bata bayanin tanan zaki koma makaranta inaga shine yasa bata nemekiba, gobema nakeson kije can cikin babbar kasuwa kisiyo kayan abincinki amman inaga sema kinje babban super market ɗin dake sabon garin ɗawisu sabida kayansu sunfi kyau".
Tafaɗa tana kallon nafisa.
"Tom ALLAH ya kaimu bara naje na kwanta umma bacci nakeji".
Da kallo ta bita sannan tace.
"Nafisa zonan," komowa nafisan tai ta kara zama.
Da kallo umma sahura ta bita.
"Meyene naga kina cije baki bakijin dadine?"
Tafaɗa mata hakan cikin kulawa.
"Wallahi ni narasa miyasa mara takemin ciwo watarana har daurewa take kuma se dare yayi takemin haka".
Tafadi hakan kamar xata saka kuka.
"Yaushe zaki fara al'ada, naga rabonki dayi tun wancan watan ai?".
Ta jefa mata tambayar.
"Eh daman yana min haka se ƙarshen watan nan inaga tunda baizo a farko ba".
Tafaɗawa ummah sahura hakan cike da gamsuwa.
"Daman yana maki haka?"
"Eh mana sosai ma ko kin manta bashine wata shekara dana taɓa zuwar miki hutuba yay min haka".
"Eh kam hakane tashi kije seda safan".
Tagaya mata hakan tare da gamsuwa da abinda ta gaya matan.
Daman kuma wasu matan yanayin jininsu yana masu haka, yana ɗan rikita daga kwanakinsa.
Tana shiga ɗaki ta hau gado ta kwanta.
Ananfa ciwo yace salamu alaikum. kuka sosai take tana dafe mararta.
Ta lura sam yanzu bata wani baccin kirki sabida wannan ciwon daya sakata agaba.
Yau kimanin wata ɗaya da faruwar abinda ya sameta kuma batafi kwana biyar da dawowa daga asibitiba wannan ciwon ya sakota agaba wanda tagaza gayawa kowa illa taci kukanta da daddare da safe kuma kaga idanunta yay fam.
Da ƙyar tai sallar asubahi sannan ta koma bacci ta dunkule wuri guda tana huci sabida zazzafan zazzaɓin daya rufeta ruff.
Har wajan karfe tara tana kwance,seda ummah sahura ta gaji sannan ta shigo ɗakin ganinta a kwance yasa ta karasa gabanta ta janye mayafin data rufa dashi.
"Ke nafisa yaya kiketa baccine hala kina lafiya yau kuwa?".
Ko motsi batai ba ganin haka yasa ta barta tare da kara gyara mata mayafin ita kuma ta futa waje tacigaba da aikinta na gida.
Bata farkaba se wajan la,asar, aguje ta mike ganin lokacin sallah ya wuce, fita tsakar gidan tai ta zubda miyon daya taru abakinta sannan ta dibi ruwa tai alwala.
Takoma daka tai sallah.
Sannan ta fito.
Kicin taje ta dauki kofi ta zubo ruwan shayi tare da lemon tsami ta zauna akan turmi, tana sha hartana lumshe idanunta.
Ahaka umma tazo ta isketa wadda itama sallah tai a daki.
Tsugunnawa tai har kasa ta gaisar da ita sannan ta cigaba da shan shayin nata.
"Nafisa ga abincinki can akan tebur kiɗibi yaji yana cikin tasa ni zan fita idan kin gama ki dauki kuɗin aiken akan madubi seki rufe gidan natafi da makullin".
"To adawo lafiya".
Tafaɗa cikin kasa da murya.
Ɗan dakatawa umma tai tana kallonta.
"Waini yanaga jikinki yay sanyine ko bakya jin dadine? ɗazuma naje na tadda kinata bacci bakima san nazoba, idan wani abunne ki gayamin bana son wannan yawan shurun naki?".
Ɗan rausayar da kanta tai tare da furta.
"Wallahi babu komai umma kawai bacci na tarane ɗazu kuma na rama".
Dawowa tai gabanta ta kalleta.
"Wani irin ramuwar bacci kuma bakya baccine?".
Tajefa mata tambayar.
"Eh wallahi ni kusan kullum da ciwon mara nake kwana shiyasa ban fiye yin bacciba".
Cikin tausayi umma sahura ta bita da kallo sannan tace.
"Sannu bara malam ya dawo se yay maki rubutu".
Sunkuyar da kanta tai tare da yiwa umma sahura godiya sannan, umma tasaka kai tabar gidan.
Itakam tana gama shan shayin ta wanke kofin sannan ta ɗan ɗebo shinkafar ta zauna anan tanaci vatare data zuba yajin ba sabida bakinta kamar ya ɗaɗe da ƙuraje.
Lomar farko takai tana yatsina fuskarta ata biyu, kuwa aguje tai bakin rariya seda ta amayar da ita tass sannan taja ta kwanta a gefe tana mayar da numfashi.
Ta dade awajan ahaka kafin ta ɗauraye wajan ta mayar da kwanan kicin tare da daukar lemon tsami ta saka abakinta, jin kamar miyon ze dawo mata.
Agurguje ta shirya kanta cikin riga da skirt na atamfa sannan ta dauki mayafi baki mai ɗan shara-shara ta yafa akan atamfar ko kwalli bata saka ba haka, ta kammala shirin nata sannan ta shiga dakin umma ta dauki kuɗin naira dubu biyar ta saka acikin ƴar ƙaramar jaka, baka.
Sannan ta zira ta kalminta marar tsini ta nufi hanyar zaure.
Seda ta karanta addu,ar fita daga gida sannan taja kofar ta fita bakin titi.
Kusan mintuna goma tana faman jiran abin hawa kafin ALLAH ya kawo mai mashin, ta tara tahau bayan ta gaya masa inda zataje.
Tafiyar kusan mintuna 20 sukai sannan ta sauka abakin kasuwa, bayan ta basa kuɗinsa ta shiga cikin kasuwar.
Kwaki ta fara saya da sauran kayan ƴan makarantar kwana sannan ta fito hannunta da kaya niki niki.
Abin hawa ta kuma tara tare da gaya masa, Ɗawisu super market,babu musu ya yarda ta hau suka wuce.
Nanma abakin katon super market ɗin yaja ya tsaya bayan ta basa kudinsa taja kayanta tana mayar da numfashi ta nufi wajan.
Abakin gate din ta tsaya ganin masu tsaron wajan suna kaiwa da komowa daman ita ba wani abunne ya kawota ba illa siyan su madara da sauransu saboda wajan yana da sauki duk da, kasancewar wajan na manyane amman kayan wajan sunfi na ko ina sauki da rahusa tare da kyau da inganci, dan ance turawane ma ke bada kayan wajan.
Ganin tana faman baza idanu kamar marar gaskiya, yasa wani daga cikin securty's ɗin wajan ya ƙaraso gabanta.
"Ƴammatah yaya naga kina tsaye anan kamar kin yada wani abun?".
Ɗan tsaki taja kaɗan tana masa kallon sama da ƙasa, batare data tankasaba.
"Hellow!!" yakuma gaya mata akaro na biyu.
Awannan karon ta ɗago manyan idanunta waɗanda sukai wani irin haske gami da girma kaɗan ta dubesa dasu, kana ta furta.
"Nazo yin provision na school ne kuma senaga kamar ba,a barin shiga wajan".
Takai maganar tana aje,ledar kwakin hannunta cike da gajiya.
Kallon tausayi ya bita dashi sannan yace.
"Eh gaskiya kam bama barin shiga wajan ne sabida tsaron mai gida, daya zo shida families ɗinsa suna shopping dan da baki ɗayama zamu fitar da mutanan, ciki amman sabida tausayi irin nasa yace mubarsu shine, muka bar na ciki amman bama barin kowa ya shiga".
Yakai maganar yana kallonta.
Ɗan jimm tai sannan ta dubesa.
"Tom nagode bara na koma na siya a anguwarmu".
Ganin da ragowar zafin rana agari gashi kuma yarinyar da alamun tana da hankali yasa yaji tabasa tausayi seya dubeta.
"Kawo kayan naki semu jera ciki nai kamar tare muke sekije ki saya ko?".
Ɗan jimm ta kumayi akaro na biyu seda tai tunani ganin sunan wajan da kuma jami,an dake zagaye da wajan yasa ta amince masa tabi bayansa bayan, ƙara gyara mayafinta sosai.
Shikam ledar kayan tarkacen kwakinta da sauran kayan data siyo ya dauka, bayan ya sakale ƴar bindigarsa a gefe suka jera kamar sun san juna, yana janta da hira itakuwa jikinta banda tsuma babu abinda yake, sakamakon yadda taga securty's ɗin wurin suna zagaye tare da bindiga suna faman zare jajayen idanunsu zat rashin mutunci.
Baƙaramin mamaki bane ya kamata, ganin yadda taga wasu mahaukatan manyan tsala tsalan motoci fake acan gefen wajan , waɗanda idan ba idanunta kemata gizoba tabbas, wasu ƙartin guards tagani suna zagaye wajan motocin.
Sake jin gabanta tai yay wata irin faɗuwa wanda batama ji me wannan securtyn ke gaya mataba.
"Ƴammata idan kin fito ki sameni anan, ki amshi kayan ki, tacan kofar zakibi".
Amsa masa tai sannan tai masa godiya kana tabi ta inda yace mata ɗin.
Bakaramun kauyanci tai ba awajan dan seda ta tsayama tana karewa wasu turawa kallo waɗanda suke kan wasu kujeru suna buga game.
Sannan ta isa gaban kofar ta danna wajan, kana ta kutsa kanta babban wajan wanda seda tai danasanin shigowa sabida tasan batada kuɗin siyayya awajan.
Anyama kuwa nan umma ta gaya mata gaskiya ba nan bane dan wancan ance bashida wani girma sedai ko maybe mistake na suna tayi.
Jin wani irin sanyin ac ya ratsata yasa ta saki kofar wadda ta koma ta rufe ruff sannan ta shiga ciki tana faman baza idanunta a waje.
Gaban saitin wasu mayuka ta nufa tare da kura masu idanu, tundaga nan ta soma raina kanta sabida baki ɗayama kayan wajan babu na kuɗinta, saboda ita abinda ya rage a jakarta 3500 ne baki ɗaya.
Tsiru tai da idanunta tana neman ta faki idanunta tabar wajan ta samu ta fita tin kafin kunya ta kasheta.
Tafe take kanta ƙasa tana faman danne ƴar jakarta sam bata san tai karo da mutum ba seda ta ɗago kanta.
Sannan tai maza ta sunkuya ta tayata kwasar kayan da suka zube na cikin kwandon.
Seda suka kwashe tass.
Sannan ta ɗago ta dubi matar datake gaban nata wadda ta bigewa kayan hannun nata.
Farace ƴar gayu mai kyau.
Cikin karkarwa tace.
"Anty dan ALLAH kiyi hakuri ban kula ba".
Da kallo wadda aka kira antyn ta bita batare datace mata komai ba ta juya tana kokarin barin wajan bayan ta ɗan jefeta da kallon raini kaɗan.
Da mamaki nafisa ta juya baya zata bar wajan tana mamakin wannan lamari watakan wasu mutanan ma da kallo kaɗai suke hukunta mutum koda basuyi magana ba.
Ganin wata yar farar budurwa wadda taci kwalliya tare da ƙaton mayafi ajikinta tana nufo wannan wadda ta buge ɗin yasa nafisa ta bata waje tare da kokarin tama bar wajan baki ɗaya ganin wannan budurwar, tana son ta bigeta bata saniba.
Saukar muryar budurwar nafisa taji cikin kunnenta.
"Anty Hidaya kizo ga cream ɗin da kike nema canfa".
Ɗan waigawa nafisa tai ashe wannan wadda taɗan buge ɗin itace anty hidayan, kafin ma taja kofar tabar cikin wajan saboda hartaje kofa taji saukar muryar wannan matar.
"Are you serious shaheedah" bata tsaya jin mai budurwar zata faɗa ba ALLAH ya taimaketa tabar wajan bayan tasha gwagwarmayar danna abun bude kofar da ƙyar.
Ganin kamar kofar data biyo akwai yawan masu tsaro yasa tabi tawani dogon hanya wanda yabi ya mike yay samɓal.
Babu yawan mutane wajan illah yalwar bishuyu gami, da tsirarun securty's waɗanda suke kaiwa da komowa,.
Cikin tsoro tare da fargaba take tafiya gakuma ilahirin jikinta yana tsuma, gefe guda wata mahaukaciyar faduwar gabace ta rusketa.
Jan kafarta kawai take tana ALLAH ALLAH tabar wajanma baki ɗaya.
Adai dai saitin wasu manyan bishuyu taja ta tsaya tana kallon wajan tana kuma danasanin bin hanyar sabida tama manta inda zataga wannan na ɗaxun ta karbi kwakinta da ragowar ƴan kayanta.
Wata ƙwallace ta zo mata bayan ta saka mayafi ta share sannan tacigaba dabin hanyar.
Tunda ta biyo ta bakin wata ƙofa mai ƴar raga taji gabanta ya cigaba da faduwar fiye dana baya.
Kirjinta har wani dokawa yake kamar ze fito.
Ambaton sunan ubangiji ta somayi cikin zuciyarta.
Adai dai wani katon fili wanda zakabi ta bayan wata baƙar mota ka fita hanyar taji wani mahaukacin mugun daddaɗan ƙamshin mayen turare wanda ya saka seda ta dakata ta shaƙi ƙamshin sosai sannan tafara cigaba da tafiyar nata.
Jan burki tai ganin wani mutum tsaye a saitin kofar hannunsa wanda ya cika da gargasa rike da waya mai uban tsada yana faman magana wadda bazakaji miyake fadiba.
Sosai gabanta ya fadi tana tuna inda tasan wannan kamshin.
Tare kuma da kurawa bayan nasa idanu wanda yake sanye cikin wani mayen bakin boyel mai uban sheki kwantacce wanda daga kallo guda zakasan anci uwar nera a siyansa.

Raɓewa tai kaɗan tana kokarin kare kanta daga kallonsa tana son tabar wajan.
Adai dai saitin kofar karaf kamar ance ta waiga sukai idanu huɗu dashi.
"Wayyo ummah sahura" tafaɗa bayan ta tattare skirt ɗin jikinta tana kokarin guduwa.
Bakaramin tsoro firgici gami da tsantsar kyau yay mataba.
Ganinshi tai tamkar jinin larabawa sabida tsantsar kyawun sura dana xati da ALLAH yay masa.


Shikam kamar star ya tsaya yana bin yarinyar dake ɗan gabansa da kallo wadda ko a ina ya ganta baze gaza ganetaba.
Bakinsa ya gasa furta komai illah nunin dayake mata da hannunsa wanda yaji uban manyan zobunan azurfa masu uban sheki da kyau.
Jan ƙafafunshi yake yana kuma kokarin saita tsinin mashin kaifin idanunsa acikin nata wadda ita kuma jikinta yake faman karkarwa yana rawa kamar mazari wadda take kokarin sakin fitsari.
Yana zuwa gab da ita yay saurin saka hannunsa ya damƙi tsintsiyar hannunta da ƙarfi wanda seda hannun nata ya amsa dan tsabar yadda ya damƙar mata shi.
Itakuwa tsugunnawa tai awajan daɓar tana sakin numfashi, tare da sakin kuka!.
Tsintar muryarta yay mai kama data yara dan tsabar sirarantar ta.
"Malam ka sakeni kona maka ihun kwarto"!!!
Tsananin mamakin furucinta, yasa ya sakar mata hannun nata gami da biyota kasan shima ya tsugunna agabanta irin tsaiwar yan ƙwallon ƙafar nan.
Yana tsirata da kaifafan idanunsa yana binta dasu yakuma gaza furta kalmar komai agareta.
Cikin dabara take kara tattare skirt ɗinta tana kuma ja baya batare data bari ya ankara da hakan ba.
Allah kuma ya bata sa,a tai wata irin hantsilawa wadda tai matukar basa mamaki..
Cikin zafin nama tai tsalle ta fice daga kofar.
Shikam cikin tsananin tashin hankali yay wani irin juyi, yabita yana faman yiwa guards ɗinsa magana alamun su bita.
Yarinya kamar aljana, kafin suyi wani yunkuri nafisa harta sami nasarar barin wajan baki ɗaya.
Ganin kamar hankali ya fara yowa kanta yasa tabi bayan wani ɗan tudu ta boye tana share hawayenta tana, kuma saita nutsuwarta jin kirjinta yana dokawa kamar ze ɓallo.
Sunkuyawa yay ya dauki bakar ƙaramar jakar dake gabansa.
Wadda yake tunanin ta,tace.
Cikin alamun ɓoye damuwarsa yake kallon ɗaya daga cikin securtyn waɗanda su suke tunanin kamar sata tayine awajan.
"Mai gida wannan yarinyarfa inaga ta ƙware a satar nan dan wallahi har waje mun duba, bamu gantaba,".
Yana kaiwa nan yay kasa da kansa cikin ladabi yana kallonsa.
Sega wanda ta bawa ajiyar kwakinta ya karaso yana huci.
Cikin ladabi ya dubi, na kusa dashi.
"Oga yarinyar nan kukace barauniya ce aini na shigo da ita, dan ga kayanta can ma ta bani ajiya garin kwaki ne da ƴan tarkacan sabulai, amman batai kama da ɓarauniya ba sabida naga nutsuwanta".
Jin zasu ɓata masa rai yasa yabar wajan batare daya tankawa kowansu ba.
Cikin motar gabansa ya nufa nan da nan guard ɗinshi ya bude masa ita ya shiga ya zauna.
Dafe kansa yay yanajin ninkin tausayin yarinyar ya kamasa.
Acikin zuciyarsa yake jimamin yadda ta saka gudu a yayin datai idanu biyu dasu, wanda da alamun kamar bata son ganin sanne ma baki ɗaya.
"Malam kasakarmun hannuna ko nai maka ihun kwarto"!
Yake nanata maganar tata cikin ranshi, tare da bude yar jakar dake gabansa.
Kirjinsane ya buga.
Ganin ƴan ɗari biyar-biyar na dubu uku da dari biyar acikinta.
Se ƴar guntuwar takarda an saka.
_Kwaki da madara da sabulu da omo da carbin da comflaks da milo da pad_ da dai sauran tarkacen kayan masurufi acikin takardar.
Nan da nan wani mugun tausayi ya kamasa tabbas tana bukatar taimako.
"Ina zan ganki?"
Kalmar daya furta kenan tare da maida kansa saman seat ɗin kujerar dayake kai, yana jin zuciyarsa na zafi akan furucin da akai mata.
"Ɓarauniya ce" wanda tsabar takaici ya hanasa tanka masu komai.
Yafi gaban mintuna goma haka yana takaicin sakacin dayay na barinta ta kufce masa.
Har hidaya ta shigo motar oska ya riko mata siyayyar tata haka suka motocinsu suka bar wajan.
Kumashi tunda ya kifa kansa bai ɗagoba har suka isa gida.


Aɓangaren nafisa.

Tana ganin waɗan nan guards ɗin sun gama dube-dubensu sun koma ciki taja jikinta cike da tashin hankali tabar wajan.
Saboda tsabar kiɗima batama san ta yada jakartaba seda sukai nisa akan mashin ɗin sannan ta lura.
Kukane ya kufce mata.
Kifa kanta tai tana kuka, ahaka tai masa kwatancen gidansu walida.
Abakin gate ta dakatar da mai mashin ɗin ta shiga gidan, a tsakar gida ta tarar da hajiya maman walida tana bawa masu aikin gidan umarni.
Adaddafe suka gaisa sannan hajiya ta ɗaga murya ta kira walidan.
Bata tsaya jan hiraba ta amshi kudin mai mashin ɗin takai masa sannan suka shiga cikin katafaren dakin walida wanda yaji kayan alatun rayuwa kala kala.
Sosai ta saka walida agaba tana mata kuka.
"Walida wannan mutumun kasheni zeyi".
Cikin kidima walida ta furta "waye hakan nan kawata?"
"Ɗan majalissarku walida anan ta zayyanewa walida komai amman ta saya mata rike mata hannun dayay tadai nuna mata cewar ita ganinsa datai yasaka ta gigita harta yada poss ɗinta.
Dariya walida tai.
"Hmm da har kina cewa bakya sonsa, kintaba ganin daman wanda yace so ya dawo yace ƙi? sedai a ɓacin rai, ahaka kike kinsa haryasa kika gigita kika kasa siyayya har kika yada kudi, ALLAH yasoki yarinya yaya nura daman jiya ya bani kudi yace na baki, seki mike na tambayi hajiya muje muyi siyayyar".
Godiya tahau yi mata bayan sun fita sunwa hajiya sallama.
Seda suka futa zuwa waccan super market ɗin sannan nafisa ta gane, cewar ashe mistake tai ba ɗayar zatajeba wannan umma take gaya mata.
Sosai sukai siyayyar sannan suka fito dan harma kudin yay ragowa.
Mai napep suka tara ya sauke walida agida ita kuma ya nufi gida da ita.....!


*AUTAR MANYA*
40 - 41


Bata shiga gida, ba se goshin magariba, seda ta shigar da dukkan siyayyar datayi cikin zaure, sannan ta koma ta miƙawa mai napep ɗin kuɗinsa sannan ta soma shigar da kayan da ƙyar.
Abakin rijiya ta tarar da umma tana kokarin zira guga zata ɗebo ruwa, seda ta kammala jera kayan a tsakar ɗakin sannan ta fito waje, ta ƙarasa gaban umma wadda tama dibi ruwan tana alwala, sannu da zuwan fitar datayi tai mata sannan itama ta ɗibi ruwan tai alwala tabi umman ɗaki.
Atare suka tada sallah, bayan sun idar umma sahura ta dubeta.
"Nafisa amman kin zauna kodai lafiya?" ɗan muskutawa tai sannan ta dubi umma sahura "wallahi umma wajan ne akwai

Please Login or Register in order to submit comment