Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanar min?"
Yaji saukar muryarta kamar daga sama.
Cikin mamaki yabita da kallo inda tai gefe da kanta kamar ba ita tai maganar ba.
"Babu komai daman hannun nawa ke ciwo amman nasa akawomin magani".
Yabata amsa atakaice.
"Ba wannan ba, kana addu,a dai ko,ina son ka ƙara wata akan wadda kake kaji ko?".
Sunkuyar da kansa yay sosai.
Sannan yace.
"Naji maamah insha ALLAHU zan ƙara".
"Alhamdulillahi ina son kaje kauye wajan Malam ka ƙara basa kudi yay maka addu,a sannan akuma sauke maka alkur,ani da ni zanima amman gudun kada na tafi kuma haihuwar sakina tazo yasa banje ba tunda ita antynku abubuwa sun mata yawa".
Cikin mamaki yabita da kallo yanzu sakina matar imran harta samu cikin daya isa haihuwa amman bai kulaba kuma babu wanda ya gaya masa sabida ya lura yanzu ba,a son gaya masa maganar haihuwar wani kamar ana gudun kada ya shiga damuwa, aishi ya yarda da ALLAH yasan babu mai bayarwa seshi kuma babu mai hanawa seshi.
Amman bai maganaba ya sada kansa kawai yana cije bakinsa.
Sannan yace.
"Insha ALLAH dana samu lokaci zanje ".
Kallonsa tai sosai batare data cire idanunta akansa ba se asannan naga kamanninsu ya kuma fita sosai.
"Ka gayamin ɗayan maganar".
Yaji saukar muryarta a dodon kunnensa.
Ɗago kansa yay da mamaki
"Maamah mekenan"
Yafadi maganar a rarrabe.
"Tun jiya jikina ya bani akwai abinda ya sameka wanda ya taɓaka bayan wannan harbin wanda har cikin baccina najishi wanda ya hanani na rintsa idanuna ajiyan ka daure ka sanar dani meke faruwa dakai hakika banida ilimin sanin gaibu amman jikina ya bani akwai ƁOYAYYEN SIRRI atare dakai".
Takai maganar idanunta ƙyam akansa.
Daburcewa yay sosai alamun rashin dauriya suka bayyanar masa lallai ya yarda idan aka ce maka mahaifi kat!! kenan.
Ɗago kansa yay a raunane.
Tare da ɗaga hanif ajikinsa wanda ya soma barci.
Ajesa yay akan tumtum ya kwantar sannan yaja kafafunsa daga zaunen ya isa gabanta.
Ya saka hannunsa guda biyun ya riko nata.
Awannan karon ya kasa daurewa.
"Maamah tun jiya ina cikin wani irin hali marar misaltuwa, amman kafin na furta komai nafara duba kai nane shin ko akwai wani laifi danai ne wanda har ALLAH ya jarabceni da shiga wannan masifar, na duba amman iya hangena na kasa tunawa amman nina san ni ɗan adam ne har abada bazan taɓa fita daga siraɗin jarrabawar mahaliccina ba wadda harse na koma garesane zan dena amsa,shiyasa a kullum nake addu,ar ALLAH ya sadani da farar ƙaddara ya rabani da mummuna".
Ɗan numfasawa yay kaɗan ayayin da falon maamah ya kuma ɗaukar tsit se karar na'urar sanyaya ɗaki kaɗai ke fita.
Sannan ya cigaba.
"Maamah kitayani addu,a ina buƙatar ƙarinta daga bakinki mai kaifi mai kuma falala daga gareni ma'ana bakin mahaifiya, maamah nafaɗa cikin masifa amman wallahi maamah wannan ba halin ANWARR ɗinki bane kafin ki dauki mataki akaina inason ki fara duba tarbiyar da kuka ginamu akanta wadda har muma muka ɗora wasu akanta wallahi! tallahi!! na rantse da ALLAH maamah sharrin shaiɗanne........tiryan tiryan".
Yagama bata labarin abinda ya faru jiya shida nafisa idanunsa yayi wani irin kaɗawa.
Hawaye ke ɗiga daga saman kamilalliyar fuskar maamah wadda ta cika da kamala da haiba gami da tsantsar addini wanda hatta saman goshinta ya rine da baƙin tabon sallah.
"Alhamdulillahi Rabbil'Alamin".
Maamah ta furta a bayyane kana ta sunkuyar da kanta a ƙasa harna tsahon lokaci.
Sannan ta kuma furta kalmar.
"Astagfirullaha wa'atubu ilaikh".
Kana ta ɗago idanunta ta zuba masa.
"Ka kyauta ALLAH ya shirya mun kai yakuma shirya dukkan musulmi baki ɗaya,kakuma kyautawa ɗiyar mutane wadda ta saida rayuwarta akanka, ya ilahi ina zanga wannan yarinya?" ta faɗa tana kuma zubar da hawayen tausayin nafisa akan fuskarta.
"Maamah" tai saurin ɗaga hannunta alamun dakatar dashi.
"Bazan goyi bayan zalunci ba, sabida ka zalunci ɗiyar mutane,amman kuma zan yarda da ƙaddarar data sameka wanda nasan wannan ƙaddarace wallahi nasan wana haifa tabbas wannan wani alamarine daga ALLAH fatana ALLAH yasa hakan yazama alkairi gareka ALLAH kuma ya sassauta maka wannan lamari ya mayar dashi sanyi, amman tabbas ina son kanemi wannan yarinya danta yafe maka wannan hakkin nata daka ɗauka idan san samu nema ka kawomin ita".
"ALLAH ya yafe maka tare damu baki ɗaya seka dage da addu,a tare da kuma tunkarar mulkinka da gaskiya da amana dan wannama kaɗai wata ishararce ta sauka gareka wadda ALLAH ya nuna maka ita ALLAH ya rufa asiri zanta addu,a Har ALLAH ya kawo mana mafita acikin wannan lamari, wanda nakeson na horeka da ko matarka kada ka yarda taji hakan muyita addu,a dagani harkai muga mai ALLAH zeyi".
Tafaɗa tana share hawayenta.
"Nagode maamah kuma insha ALLAH zanyi dukkan abinda kika ce ALLAH ya yafe mana baki ɗaya".
Ya faɗa bayan ya miƙe yana mata sallama.
Tunda yake baita ɓa zama sunyi magana kamar wannan da itaba sabida bata yarda.
Cikin tausayi ta dubesa.
"Kajirani"
Tashi tai ta nufi cikin ɗakinta.
Minti kaɗan ta dawo da wani ƙaton galan a hannunta ta mika masa.
"Kadinga sha kafin kaci komai safe da dare, ruwan tofine jiya na zauna nai maka ALLAH ya ƙara tsarewa".
Tafaɗa cikin alkunya.
Godiya yay mata sannan ya saka hannu ya amsa yay hanyar fita.
Da kallon tausayi ta bisa sannan ta koma ta zauna ta rafka tagumi.
Shikam hanyar bangarensa yay hannunsa guda dauke da galan ɗin.......!!!!


ƊAN MAJALISA IS NOT FOR FREE BOOK PAY.
200naira to 0078174806 starling bank... evidance08142105218.or mtn airtel crd.
34 - 35


Seda ya aje galan ɗin akan wani ɗan top sannan ya saka ɗayan hannunsa,mai lafiya ya murɗa handle ɗin Ƙofar dazata sadaka da babban falon ɓangaren nasa na ƙasa.
Ɗaukar galan, ɗin yay tare da shiga cikin falon wanda kamshi da wani irin sassanyan ƙamshi ke tashi acikinsa, babu kowa afalon dan haka kansa tsaye ya nufi kwanar data karya wadda corridow ya rabata da falon.
Wata ƴar kwana ya shiga kaɗan wadda wani irin azababben step ɗin bene mai ɗan karan kyau, yabi har hanyar saman direct.
Da ƙyar yake taka step ɗin cike da gajiya haka ya ƙarasa hawa saman benen inda ya shiga cikin wani falon wanda yafi na ƙasan tsaruwa da haɗuwa gami da kayan more rayuwa.
Nufar gaban wani ɗan lungu yay wanda ya raba wasu ƙofofin bedroom guda biyu, wadda tafi sheƙin naga ya tura tare da shigar da jikinsa cikin wani haɗaɗɗen bedroom mai mugun kyau wanda yaji kayan saitin gadon royal komai fari tass, babu wani tarkace a ɗakin daga, gadon se ƙatuwar wadrov se babban dressing mirrow, gefe guda wani table ne wanda yake manne da farar sopa.
Se gaba kaɗan wani ma dai dai cin table ɗinne wanda aka aje tarkancen system akai.
Gefe guda ya aje galan ɗin tare da faɗawa kan sopa ya kwanta yana lumshe idanunsa alamun gajiya.
Sannan kuma yaɗan ɗago hannunsa mai ciwon, yafara warware farar audugar da aka naɗe masa dashi.
Ɗan rintse idanunsa yay da alamun hannun nasa nai masa zafine sannan naga ya miƙe ya nufi gaban wadrov ɗin,tare da buɗe wata ƴar loka ya ɗauko wani ɗan akwati, tare da komawa kan sopar ya zauna.
Yana kici-kicin budewa hidaya ta turo ƙofar ɗakin ta shigo.
Hannunta riƙe da wani ɗan madai-daicin kwando, cikin nutsuwa ta ƙaraso gabansa bayan ta aje kwandon ta tsugunna agabansa.
"Ranka ya daɗe barka da shigowa yaya jikin naka ALLAH ya kiyaye gaba".
Tafaɗa face ɗinta yay kalar tausayi.
Cikin mamakin hali irin nata yake dubanta ta ƙasan, idanunsa.
"Bakiyi fushiba madam?"
Ya jefa mata tambayar sam ita bata san wani abu waishi fushi ko hayaniya ba, wannan dalilin yasa yake sara mata yadda batai tunani ba.
"Haba yallaɓai akan mi zanyi fushi da mijina dan kawai kace na zauna agida sena hau fushi dan dai fushin bashida wahala".
Takai maganar tana sinne kanta a ƙasa.
Murmushi yayi cikin jin daɗi gami da godewa ALLAH akan kyautar daya basa na mace kamar hidaya wadda ta tara abubuwan burgewa na bam mamaki.
Sannan ya saka hannunsa mai lafiyar, cike da soyayyarta, ya ɗagota zuwa jikinsa yanajin raguwar damuwar dayake ciki ta ragu fiye da yadda ya shigo da ita.
Agefensa yay mata masauki tare da ɗan zame mata kallabin kanta yana shafa kanta da tafin hannunshi.
"Kabari kaga ba lafiya garekaba, kawo na taimaka maka".
Tafaɗa tana ɗan zamewa daga jikinsa, tana kokarin karɓar ɗan akwatin dake gaban nasa.
Karɓa tai tare da budesa ta ɗauko auduga wadda taketa ɗaukar idanu dan haske.
Tafara goge masa ɗan jinin daya tsatstsafo,daga ciwon nasa kana ta naɗe masa.
Cikin nutsuwa ta sauka daga kan jikin nasa tare da adana,akwatin a inda yake sannan ta kuma zuwa ta janyo kwandon gabanta.
Ɗan madai-daicin tea flaks ta ɗauko daga cikin kwandon sannan, ta bude ta zuba ruwan coffee ɗin dayace ta haɗa, masa acikin wani ɗan cup mai kyau, sannan ta saka teaspoon tare da miƙa masa.
Da hannunta ya hade yana kokarin tallafo ƙwanƙwasonta, cikin sauri ta zille tare da mikewa.
"Bara naje na duba girki kada ya kone".
Tafaɗa tana dariya.
Ɗan tura baki yay kamar wani ƙaramin yaro sannan ya kauda kansa gefe kamar wanda yay fushi.
Cikin salo ta kawo kanta dai dai saitin face ɗinsa, ta tallafo face ɗinsa da hannunta tare da fito da harshenta taɗan lashi bakinsa kaɗan taja gemunsa sannan ta ruga aguje tana dariya.
Wata irin miƙa yay tare da komawa kan sopa ya lumshe yana jinsa awani irin mood kana ya tallafi kansa da hannunsa ya faɗa duniyar tunani, batare daya kula cup ɗin coffeen daya aje agefensa ba.
*********************

Cikin ɗan jin zafi kaɗan ta tube rigar jikinta tai saura daga ita se pant, ahaka tai gaban siff ɗin ummah sahura ta kaya, ta dauki zani ta daura sannan ta fito tsakar gidan sanin ummah sahura na dakin baba mijinta yasa ta karasa kicin.
Ruwa mai ɗumi ta ɗiba tare da dauka tai cikin bayi.
Sosai tai kamar yadda ummah tai mata jiya, ma,ana ta gasa kanta dai dai yadda zata iya.
Tanayi tana cije bakinta sabida zafin da gaban nata ke mata harta kammala ta ɗauro alwala tai ɗaki.
Tana yin sallah ta haye gado ta kwanta da dabara saboda karta fama hannunta da bayanta.
Babu jimawa bacci mai nauyi yay awon gaba, da ita.
Koda ummah sahura tazo ganin tai bacci yasa,ta aje mata tsiren da baba ya siyo yace ta kawo mata.
Sannan ta ƙarasa ta rufe mata jikinta da bargo kana ta kashe mata ƙwan ɗakin tafita.
Bacci sosai nafeesah ta samu wanda bata farkaba se asubahi.
Koda ta miƙe ruwan ta kuma ɗiba ta kuma gasa kanta😛( su nafi anji maza ).
Sannan ta ɗauro alwala ta fito waje tare da nufar ɗaki.
Sallah ta tayar bayan ta idar tai azkar, sannan ta fita zuwa ɗakin baba.
Tsugunnawa tai agabansa ta gaisar dashi cikin nutsuwa sanna, ta ɗan zauna seda ta bari umma sahura ta idar da tata sallar sannan suka gaisa.
Tana koƙarin fita baba mijin ummah sahura ya kirawota.
"Nafisah zonan kinji".
Yafaɗa cikin tausasa murya.
Komawa tai gabansa ta zauna tana ɗan matse jikinta kaɗan jin yadda jikin nata yake mata zafi.
Gyaran murya yay sannan ya dubeta cikin tausayi.
"Haƙiƙa nafisa babu wani mumuni daze zauna a haka batare da ALLAH ya jarabce shiba,kiyi haƙuri ki ɗauki dukkan abinda ya sameki a matsayin ƙaddararki, kada ki sakawa kanki damuwa mu, masu tawakkaline ga ALLAH kuma musan komai ya faru daga shine,dan haka nakeson dana horeki akan da ki boye wannan magana kada ki bari su kaka, suji wannan kaddara data sameki,muma zamuyi kokarin ganin bamu bayyanawa kowa itaba, sannan abun da nakeson nagaya miki kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki anan har hutunku ya kare ni da kaina zanwa gida waya akan ninace ki zauna anan din idan ankoma zamu mayar dake makaranta da kammu".
Yakai maganar yana kallonta cikin tausayi.
Share hawayenta tai sannan ta dubi baba.
"Nagode baba ALLAH ya saka muku da gidan aljannah hakika naji babu dadi da wannan kaddara ta faɗamin amman zan zauna anan naita istigifari neman yafiyar ALLAH akan ya yafemin laifin danai na aikata zin.....".
Bata kaiba umma sahura ta kamota ta rungumeta tana share mata hawayenta.
"Karki damu nafisa ALLAH gafurur rahim ne fatana dai wannan yazama izina gareki kodan gaba babu ke babu wani ɗa namiji matukar ba miji ALLAH ya kawo maki ba".
"Ummah nikam kidaina min maganar aure dan waye ze aureni alhalin....." takasa karasa maganar sabida kukan daya ƙwace mata.
Shafa kanta umma sahura take tana rarrashinta
"Sha ALLAHU zaki aure harma kiga ƴaƴanki ƙaddararki daban lamarin aurenki daban kinji ɗiyata ALLAH dai ya jikan yaya kabiru" takai maganar tana kuka!
Ganin zata karya mata zuciyane yasa tai wuff tabar dakin.
Ɗakin ummah sahura daya zama nata a ayanzu ta nufa ta faɗa gado.
Afili take bayyana maganar tata.
"Wama ze aureni yanzu bayan wanda nakeso, yagama dani ya karbi abinda yake mutuncina shikam nama fidda raina daga garesa tunda aka kai war haka banji sanarwar nemana agidan redioba" ( ji wauta 😝 ).
Wani wawan kuka ne ya kuma ƙwace mata.
"Anwarr har abada bazan manta dakai ba, kuma har abada bazan dena fegenkaba, sedai koda zan mutu bazan kuma gigin nuna soyayyarka agabankaba".
Takai maganar kamar yana gabanta.
Rungume pillow tai akan kirjinta nan da nan bacci mai dadi ya kwasheta.
Bata farkaba seda ummah tazo ta tayar da ita.
Brush tai sannan ta koma daki ta dauko kayan karin da umma takai mata ta zauna. tsiren jiya ta fara ci duk bakinta babu daɗi sannan ta ɗauki kofi ta xuba ruwan shayi taɗan sha kaɗan, cikin haka walida tai sallama itada hajiya mamarta.
Sosai ummah ta taresu anan suka zauna ana kuma jajantawa juna sannan hajiya tai sallama ta wuce itakam walida anan ta zauna bata tafi ba se magariba.
Akofar gida suka tsaya bayan ta rakata.
"Nafeesah jiyafa naji maganar mai girma shugaban ƙasa yanawa mutumin jajen abinda ya samesa agidan redion ɗawisu, wallahi bakiji yadda jama,ar gari suke shiga suna masa jajeba"..
Hade ranta tai tamau sannan tace.
"Wanine hakan kuma naji kinata faman zuba kamar kin samu redion kema?"
Cikin mamaki walida ta dubeta.
"Mutumin kifa f.k mai girma mas!"
Sake hade ranta tai sannan tace.
"walllahi ni tsiyata dake walida shirme wanine kuma hakan, pls idan ina tare dake kada ki kuma min maganar wani wallahi akan kina sakomin hirar sa zamu iya ɓatawa dake".
Tana kaiwa nan ta juya fuwwwwww!
Tai gida tabar walida a dashe.
Ko sallama batai ba ta faɗa ɗaki ta zauna tanajin zuciyarta na mata zafi a fili ta bayyana.
"Ɗan iska yana can yana shagalinsa tunda yagama da rayuwata" cikin tsananin jin zafinsa ta furta hakan sannan kuma tai waje tayo alwala tazo ta tayar da sallah.
Koda ta idar bata fita waje ba Alkur'ani mai girma ta dauko na umma sahura ta soma karatu cikin daddaɗar muryarta.
Har zuwa wani lokaci kana ta kammala ta aje waje guda sannan ta fita taiwa ummah sahura seda safe wadda take zaune a tsakar gida tana jin redio.
Dakin ta koma ta haye gado ta kwanta bayan tai addu,a atake bacci mai dadi ya kwasheta.
*************-


Ɓangarensa....!
36 - 37


Aɓangarensa.


Anasa ɓangaren kuwa tunda yay wannan kwanciyar a saman sopa bai miƙeba seda yaji ansoma kiran sallah.
Tube kayan jikinsa yay tare da ɗaura farin tawul a ƙugunsa ya nufi cikin bathroom ɗin dake cikin ɗakin nasa.
Ruwa mai zafin gaske ya haɗa acikin ƙaton bathtube ɗin dake cikin bathroom ɗin, sannan ya shiga yay zamansa yana jin yadda ƙashin jikinsa ke karɓar ruwan.
Yakai fiye da mintuna 20 acikin ruwan seda yaji dukkan wata gajiya da wata, nuƙurƙusa da jikinsa ke yimasa ya ragu sannan ya, fito daga ciki.
Bath rube, ya ɗauko ya saka ajikinsa sannan ya tsugunna agaban famfo ya ɗaura alwala, ya fito waje.
Agurguje ya shirya kansa cikin farin jeans da baƙar t.shirt mai dogon hannu, sannan ya ɗauko wata farar p.cap wadda a jikinta aka rubuta, STAR da jan rubutu, ya ɗora akansa wadda tai matukar yi masa kyau, sannan ya karasa gaban dressing mirrow yay ɓarin turare masu sanyin ƙamshi ajikinsa, ya dauki key ɗin motarsa ya bar ɗakin.
A tsakiyar falo yaga hidaya tana kokarin nufar gaban daining hannunta dauke da katon faranti wanda yake shaƙe da kayan abinci akansa.
Da sauri ya isa gareta ya taimaka mata suka aje kayan akan daining sannan ya dubeta.
"Madam zanje sallah daga nan zan je wajan dr safiyan na karɓo magani tunda na kira osk bai ɗaukaba, sena biya wajan shugaban jam'iya zamuyi magana dashi".
Sakin baki tai tana kallonsa.
"Amman kasan dai dankai na zauna nai wannan girkin ko? amman shine zakace zaka fita".
Tafaɗi maganar cikin fushi.
Da kallo ya bita sannan ya ɗan basar da abinda ta gaya masa.
"Zanje na dawo ay ba jimawa zanyi ba".
Yakai maganar yana tafiya.
Cike dajin haushi hidaya tai ɗakinta tana jin zafin abinda yay mata cikin zuciyarta.
Shikam mamakin rashin uzurinta na wataran yake, zamafa yay tare da mata bayanin abinda ze futa yay wanda duk mai amfani ne agabansa amman sam taki tai masa uxuri.
Masallacin gidan yaje yay jam,i bayan sun idar nanfa mutane sukai masa caa kowa yana kokarin yay masa yaya jiki.
Tare da addu,ar ALLAH ya tsare gaba, sannan ya saci jikinsa yabar wajan sabida ganin yadda wajan ya soma amsa yawan jama,a sakamakon daman indai yana gida, tofa mutane basa tsayawa haka zakaita ganin suna shigowa kamar babu gobe.
Damma a iya farkon gate suke tsayawa, wajan masallaci.
Tunda daga wajan masallacin zuwa cikin gidanma akwai tazarar gate har uku.
Wata farar mota mai tin ya nufa ya budeta tare da shiga ciki ya xauna.
Yakai minti biyar awajan bai tashi motar ba harseda ta gama saituwa sannan yay revars tare da nufar main gate.
Horn ya danna masu gadi suka rugo suka bude masa suna ɗaga masa hannu haka yabar gidan cikin tuƙinsa na nutsuwa.
Anguwar rafi ya soma nufa, cikin wata area mai kyawun gaske, abakin wani ƙaton gida ya tsaya yay parking sannan ya ciro wayarsa ya fara neman wata number dan baya son fita waje wani ya gansa sabida tsaro.
Bugu ɗaya aka daga anan ya sanarwa dana cikin wayar cewar gaya nan a ƙofar,gida.
Mintuna kusan goma sega wani bakin mutum nan kakkaura ya fito daga gidan jikinsa cikin manyan kaya wanda daga gani ya girme masa sosai.
Karasowa yay gaban motar tare da bude emty side ya shigo ya zauna.
Cikin mutuntaka suka gaisa anan na gane wannan mutumin shine shugaban jam'iyar tasu.
Cikin mutuntaka mai girma mas! ya dubi mutumin bayan ya gama karɓar jajan daya masa, sannan yace masa.
"Ranka shi daɗe wallahi kaga ban samu zuwa wajan meating bafa sabida wannan matsalar data faru, amman zan kira uban jam'iya muji mi suka tattauna".
Ɗan murmushi shugaban jam'iya yay sannan yace.
"Ai babu wani taro da akai muhammad sabida matsalar data faru dakai, wallahi bakaramin girgizamu taiba, dan adaran fa mai girma shugaban ƙasa ya kira taron gaggawa, akan dole a tsawaita bincike akan suwaye sukai maka wannan gadar zaren, sannan yace a kuma kai maka securty's sosai cikin gidan naka".
Ɗan shafa kwantacciyar sumar dake gefen fuskarsa yay kana yace.
"Nikam bana bukatar wasu masu tsaro sannan wannan abinda ya faru tuni ma nariga dana san suwaye sukaimin hakan fatana dai kawai shine ALLAH yasa na gama wannan mulkin lafiya".
Da kallo shugaban jamiya ya bisa sannan yace masa.
"Aikam nima na gano waɗanda sukai wannan abun wallahi ba kowa ze kokarin ganin bayanka ba illah mai DARBEJIYA,sabida daman tun lokacin da akai maku primary election dayaga kai kaci shikenan ya fara neman fitina acikin jam'iya shine mai girama shugaban ƙasa yace, a basa sallama nasan daganan yafara shirye shiryen yadda zega bayanka, wanda wallahi nasan harda ƴan kwamatinka waɗan da suka zama kamar fuska biyu a wurinka".
Yakai maganar yana kallonsa, kasancewarsa mutuminsa na amana sosai suke mutunta juna kuma suke zaman amana, tunba yauba shugaban jam'iya yake kamar yaya awajansa sabida ALLAH yay mutumin da amana tare da ganin mutuncin anwar.
"Nasani shugaba wallahi ina ganin kowane, kawai da ido amman tuni ƙwaƙwalwata take aiki akan dukkan wanda naga badan ALLAH yake biye daniba, habawa sekace wani karamin yaro, wannan dalilin yasa yanzu bana cika yawo dawasu na cikin tawagata sabida na gane ƴan leƙen asirine".
Yakai maganar cikin serious.
Murmushi shugaban jam'iya yay tare da jinjina ƙwaƙwalwa irinta anwar kasancewar sa irin mutanan nan ne masu tunani sam baya aiki da ka komai yana yinsane cike da basira, sedai ahaka idan kaga yana ruwan kyauta seka rantse bai san miyake ba

"Nasani muhammad ai kai ɗinnan bakaramin baiwa mukai ba da ALLAH yasa kazo acikin jam'iyarmu sabida zuwanka ya kawo mana cigaba sosai da sosai, yanzu fa duba duk yawanci waɗan nan kujerun fa acikin jam'iyarmu suke, illah acire gwamna shine kaɗai yake a Waccan jam'iyar, amman daga kanku har mai girma shugaban ƙasa dukfa muna cikin wannan jam'iya mai albarka, ALLAH dai yasa next eclection kazama shugaban ƙasarmu mai albarka ta AZURFA"
shugaban jam'iya yakai maganar yana dariya.
Zaro idanu yay cikin dariya kaɗan yace.
"Wai ina laifin dai ɗan majalisar taraiyar danake amman mulkin ƙasar nan tamu ta azurfa ai akwai wahala fa".
( zakuji na kirki sunayen unguwanni jaha da kuma ƙasar kanta, wannan ba wani abu bane illah kasantuwar ,labarina nina ƙirƙiri abina yasa komai na cikinsa na ƙirƙireshi saboda tsaro banyisa dan cin zarafin kowa ba na yisane bisa ra,ayina da kuma baiwata da ALLAH ya bani dan na isar da sakona da kuma nishaɗantar da mosayana wanda yaga wannan labari yayi dai dai dana sa kowani abun nasa, tofa akasi aka samu domin ban yisa dan cin zarafin wani ko wata ba dan haka ƙasar azurfa ɗawisu da sauransu duk cikin basirata nai creative ɗinsu kudai kubiyo alkalamina 👊 )

Sosai a wannan karon ya baiwa shugaban jam'iya dariya, wanda yay ta harya godewa ALLAH sannan ya dubesa.
"Haba jarumi! aini kam jikina yana bani tabbas da yuwuwar kazama shugaban kasar nan tamu, sabida samun gwarzo kamarka se an tona a wannan lokacin jibafa kaga yadda ka mayar mana da ɗawisu tamkar wani ƙasa ta turawa, wallahi ba yabon kaiba adai yanzu samun kamar ka se antona ALLAH dai ya baka kaima abinda kake nema".
Yakai maganar yana kallonsa.
Ɗanjan numfashi yay kaɗan sannan ya kalli shugaban jam'iya kana yace.
"Masha ALLAH kasan girman ubangiji tunda na karɓi wannan kujera bana kwanciya cikin daɗin rai, a kullum ina kwanciyane da tunanin wani tallafi da kuma cigaba zan kawowa jama,ata, ni na kwanta akan gadona na miliyoyin kuɗi na tashi naci mai kyau nasha mai kyau bantaɓa kwanciya cikin sauro ko duhu,ba haka zalika bantaɓa kwana ɗaya batare dana kai nama bakina ba, shin su jama,ata ayaya suke? shin wanima yana da muhallin daze kwanta ko yaya? wanima seya shekara baici naman ba? wanima agidansa baya kwana da wutar kullum yana cikin azabar duhu da saurone.........,
Wallahi idan na tuna da haka se jikina yay sanyi komai ya fita akaina, amman me ni kaɗai bazan iyaba dole ina bukatar magoya, baya waɗanda zamu haɗa hannu wajan kawo gyara acikin ƙasarmu jahohinmu da sauransu,amman me aikin bana mutum guda bane ba akwai yiwuwar da mucire son zuciya acikin aiyukanmu wannan shine ze kawo mana cigaba da gyara acikin wannan tafiyar tamu......,
Wannan dalilin yasa na shirya taro anan cikin ɗawisu square wanda insha ALLAH anan zamu tattauna da wasu daga cikin talakawanmu domun muji menene a yanzu yafi addabarsu wanda mukuma zamuyi iya kokarin Da ALLAH ya bamu wajan gyara wasu daga cikin matsalar wadda mu bamu isa mun maganceta duka ba sabida ALLAH dayay mu shikaɗai ya isa ya magance mana dukkan matsalarmu.....,
Wallahi shugaba ina cikin jawabi kawai naji saukar wannan bulet ɗin a hannuna, bada ban wannan baiwar ALLAN data kawon dauki ba da tabbas zan iya rasa raina, dubafa kaga".
Ya ƙarasa maganar yana nunawa shugaba hannun nasa wanda aka nade da farar auduga.
Ɗan numfasa shugaban yay sannan ya dubesa.
"Tabbas dukkan maganganunka haka suke, amman ina son idan har ALLAH ya baka dama da a zaɓe na gama mu zamu tsayar dakai amatsayin shugaban ƙasa a jam'iyarmu, idan har ALLAH ya baka wannan kujera zaka iya amfani da ita wajan gyara wasu daga cikin waɗan nan matsalolin da yardar ubangiji".
Murmushi yayi kana ya dubi shugaba sannan yace.
"Komai tsarin ALLAH ne amman bana tunanin daga wannan kujerar zan kuma neman wata sabida yanzu kuma zanyi kokarin mayar da hankalina ne akan wasu daga cikin abinda ya shafeni bayan mun sauka daga wannan matsayi".
Yakai maganar yana dan dafe kansa alamun maganar tafara isarsa kasancewarsa mutum marar son hayaniya.
"Nasani muhammad akwai abubuwa masu tarin yawa agabanka wanda koba a iya siyasaba kaiɗin shugabane ga AHALINKA dan haka kadai daure ka kuma tunani kafin lokacin yazo dan muna da sauran shekaru,ALLAH dai ya baka wanda ze maka hakan kaima fatana a kullum yadda kake tallafawa marasa shi kaima ALLAH ya maka kyautar ɗan kanka wanda zaka gani kaji sanyi acikin zuciyarka".
Kafinma shugan jam'iya ya ƙarasa haryay saurin amsawa cikin jin dadi wanda yafi ko yaushe.
Ahaka suka gama maganganunsu sannan sukai sallama bayan yaywa shugaba

Please Login or Register in order to submit comment