Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinsa yay garau kuma baya son yay sallah ba,a cikin jam'i ba.
Sabida tsananin tunanin daya faɗa bai tsaya tashin oska ba kuma bai ma tuna da shiɗinba seda ya kai bakin masallacin sannnan ya tuna ganin rashin dacewar hakan yay shiyasa ya sauya akalarsa ya dawo da baya yabi ta cikin ɗakunan marasa lafiya domin ya isa dakin da aka kwantar da shi ɗin ya taso oska suje suyi sallar a tare.
Umma sahura tana bayi da alama wanka take daman aladar tace idan zatai sallar asubahi setai sabon wanka.
Cike da wani irin yanayi nafisa tafara fesar da wani irin nishi jin baki ɗaya yanayinta ya sauya.
Tsigar jikinta ta miƙe hatta ga nipple ɗinta ya mike kamar an jawosa daga kasanta kuma tanajin tai wani irin linking kamar wadda akai sex da ita.
Mafarkin dataine ya soma dawo mata akanta.
Wai yana rungume da ita yana sha mata.....bata kai ga tunawa kuka ya kufce mata.
"Bawan ALLAH ka bar rayuwata haka kaimin illa afili shine a mafarkina ma kakeson yimin haka" takai maganar a fili tana jan kuka.
Jin kamar umma zata jitane yasa ta ɗingisa kaɗan ta bude kofa tai waje.
Bude kofar tai ta fita tana dafe bango kana tana cigaba da kukan nata.
Kifa kanta tai da bango tana cigaba da kuka tare da dafe saitin zuciyarta jin wata mahaukaciyar faduwar gaba ta risketa kafin ta soma bude idanunta tana kallon abunda ya ɗaga mata hankali.....!!
26 - 27

Tsanin dukan da zuciyarta keyi shiya baiwa kirjinta damar dokawa da mugun ƙarfi kamar ze fito waje, hannunta guda ta saka ta dafe kirjin nata kana ta tsugunna a wajan tare da cusa ɗayan hannun nata a bakinta ta toshe shi.
Sa,annan ta sunkuyar da kanta a ƙasa ta saka tafin hannunta ta kare fuskarta sosai dashi ta yadda babu mai ganeta.
Tunda taga tawowarsa take faman addu,a akan ubangiji ya kawo mata ɗauki kada ya ganeta.   tun kafin yama karaso wajan da take kamshin mayen turarensa wanda ya cika wajan ya gama mamaye wurin baki ɗaya.
Sanye yake cikin baƙar jallabiya mai yankakken hannu se ɗayan hannun nasa, wanda ke ɗaure da farar auduga, yana tafiyane cikin sauri kamar wanda yay mantuwa.
Cike da tsabar mamaki take binsa ta cikin tsakiyar yatsun hannayenta da kallo tare da furta "miya kawosa nan asibitin kuma a dai dai wannan lokacin?" sanin babu wanda ze bata amsar hakan ne yasa ta kuma sada kanta a ƙasa sabida yazo gaf da ita ze gifta.
Wata mahaukaciyar wawiyar faɗuwar gaba mai sifurin ce ta zo mata wadda inda wani na kusa da ita dafa tabbas, ze iya jin fitar sautin ta.
Lokacin dayake karasowa dai dai saitin bayanta tafiyar sa da kuma ƙarar sautin takalminsa sun cika mata kunne cike da juriya ta kuma ƙamƙame jikinta tana kuma ambaton sunan ubangijinta.
Wata wawiyar bahaguwar ajiyar zuciya ta saki a yayin dataga ya gifta daga ganima bai kula da tsugunnon mutum a wajan ba.
Cike da kuzari ta mike tare da saurin sunkuyawa ta dafe kafafunta jin kamar zasu tsinke.
Ɗan rintse idanunta tai kana ta cigaba da tafiya cikin ɗingishi.
Adai dai lungun ɗakin da aka kwantar da ita wanda yake a jere da sauran ɗakunan word ɗin, ta ɗan ƙara dafa bango kana ta ɗago ƙwayar idanunta ta kuma kallonsa a yayin daya ke kokarin shiga word ɗin da aka kwantar dashi.
Kamar ance ya waigo yaɗan sosa sumar kansa as usal,  tare da ɗan jiyowa kaɗan sabida yadda yaji yanayinsa ya sauya ma,ana gabansa ya ɗan faɗi kaɗan wanda ya rasa dalilin jin haka atare dashi.
Rintse idanunsa yay yana ambaton sunan ubangijinsa kana ya kuma saisaita nutsuwarsa.
Tare da sosa idanunsa kaɗan jin kamar sun nuna masa ba dai-dai ba.
Wannan yarinyar ta jiya yagani dafe da bango a tsaye tana kallonsa daga ganinta tana jin jikine duba da yadda idanuwanta ya sauya kala.
Cike da ɗumbin mamaki akan kyakykyawar kamilalliyar fuskarsa ya furta.
"Hasbinallahu wani'imal wakil"
Kafin ya kuma saita nutsuwarsa sa,annan ya nufeta gadan gadan cike da ishirwar buƙatar ganinta dama.
Itakuwa nafisa tana ganin ya nufota yasa tai wani irin tsallan albarka sam ta manta da ɗinkita haka tai cikin ɓangarensu aguje.
Aƙarƙashin wani ɗan step ta boye tana faman zare idanu.
Tana hango sanda ya nufo wajan yana faman waige waige kamar wanda ke neman wani abu.
Sannan taga ya leƙa kofar wani ɗaki ganin baiji koda motsinta ba taga ya saka hannu ya kaiwa iska naushi kamar wani ɗan ƙwallo kana taga ya juya a fusace kamar kububuwa.
Yabarwa wajan mugun mayen ƙamshin turarensa.
Seda ta bari kamar da minti goma da barinsa wajan kana ta fito daga maɓoyarta tare da sakin wata ajiyar zuciya kana ta furta.
"ALLAH nagode maka"
Cike da rawar jiki ta nufi dakin nasu wanda yay dai dai da fitowar umma sahura daga banɗaki.
Cikin yanayin tuhuma tabi nafisa da kallo kana tace.
"Yanaga jikinki yana rawa hala dai lafiya ko?"
Bata jira mima nafisan zata faɗi ba ta kuma cewa.
"Daga ina kike shinma danni kam banga alamun kina ɗakinnan ba".
Lumshe idanunta tai wanda ya cika da hawaye tare da cewa.
"Naje wajan likitane sabida mu nemi sallama".
Tai wannan ƙaryar sabida kawar da zargin ummah sahura.
Cike da mamaki umma sahura ta dubeta.
"Kina haukane zakice mu koma gida daga kawoki jiya ta inama raunikan naki suka warke bare kice a koma gidan".
Ummah sahura ta faɗi maganar bayan ta shimfiɗa sallaya a tsakar ɗakin tana kokarin data sallah.
Tura baki nafisa tai gaba tare da ɗingisawa kaɗan itama tai cikin bayin.
Alwala tai da ƙyar tare da fitowa itama ta niyata gayin sallar.
Tana idarwa ta saka kanta cikin cinyarta tana kuka!
Salati umma sahura tai a bayyane kana ta dubeta.
"Shin mai akai maki ne na wannan kukan ko ciwon naki,ke maki zafi?".
Girgiza kanta tai bayan ta saka bayan hannunta ta share hawayen sa,annan tace.
"Ummah dan girman ALLAH mubar asibitin nan jikina yana bani kaka zata iya aiko wani ya dubani acan gidan naki, kuma kinga daganan zasu iya jin komai a yayin dasuka zo suka tadda bama gidan".
Cike da gamsuwa tare da sanin halin masifa da bin ƙwaƙwaf irin na kaka dama sauran ƴan uwansu umma sahura taɗan nisa kaɗan gami da cewa.
"Duka naji bayaninki nafisa kuma tabbas biri ze kama da mutum, amman abin dubawar anan shine yaya zamuyi da raunin jikinki a yayin da muka koma gida kinga baki gama warkeba?".
Jimm tai kaɗan kana tace.
"Nidai ummah muje subamu sallama tunda dai asibitin kyautane idan yaso sena dinga zuwa ana duba min nasan bazasu ƙiba sabida kinga na ƙwarara jikina ban langwaɓeba".
Cike da mamaki umma take duban nafisa bata taɓa tunanin tana doguwar magana kamar haka ba amman seta share. tare da furta.
"To mubari anjima, babanki yazo semuji mizece".
"Ahh nidai umma bazan iya zama anan ba dan ALLAH kizo muje wannan likitan mai kirki shine naga ya shigo tun ɗazu".
Jimma tai kaɗan kana ta mike sukai waje zuwa office ɗin likitan.
Bayani umma sahura ta zauna tai masa cike da nutsuwa wanda ze gamsu.
Rubuce-rubuce yay akan farar takadda tare da sunan nafisa ya aje guda ɗaya gudar kuma ya mikowa ummah tare da kallon nafisa wadda ta hade rai kamar zata saka kuka!.
"Ki daure kina zuwa ana duba wajan har zuwa sati biyu insha ALLAH komai ze normal".
Se a sannan ta ɗan saki fuskarta kana tai masa godiya sannan sukai dakin da aka kwantar da ita ɗin.
Dan tsabar rigima irin tata babu yadda ummah sahura batace mata akan data zauna a dakin ta fita ta samo masu abin hawa ba amman fafur taki haka ta biyo ummah sahura tana cije baki. da dafe bango harsuka fita daga asibitin anan ta sauke ajiyar zuciya kana suka tari mota sukai gida.
Seda sukai nisa umma taɗan ja tsaki kaɗan cike da tuhuma nafisa ta dubeta, "ummah lafiya?".
"Abin takaici ban bari munyi bankwana da wannan likitar data dubaki jiyaba, yarinya mai mutunc,kiga jiya har abinci ta kawon".
Ɗan murmushi ta saki kafin tace.
"ALLAH bai nufaba umma amman nima naso na ganta duk da jiyama na ganta tanada kirki ai".
Daɗa faɗaɗa far,a umma tai tare da cewa.
"Aisu kirkinsu ba,a ƙasa suka ɗaukaba, kokinsa ƙanwar babar ɗan majalisarmu ne".
Wata irin ƙwarewa feenah tai kana ta waro ido tana duban umma bakinta ya gaza furta komai.
"Aikinsan wannan asibitin na mahaifiyarsa ne".
Muryar umma ta kuma sauka cikin kunnenta.
Awannan karon tsananin mamakinta ya gaza buya, waro idanunta tai waɗanda take suka kawo ruwa tuna ƙaddarar tada samesu.
Amman seta basar tare da sakin hamdala a zuciyarta tana ayyana ai ita da wannan asibiti har abada.
Ahaka suka karasa gida harkuma sukaje bata kuma gigin maganaba tasan koda kuwa tai maganar kukane ze biyo baya.
Da baba suka haɗu yana kokarin kullo gidan wanda a wannan lokacin karfe bakwan safiya.
Bakaramin mamaki yay ba ganin umma da nafisa amman bai maganaba ya biya mai motar kudinsa sannan suka rankaya cikin gidan.
Seda suka nutsa suka huta kana umma tai masa bayanin komai.
Dayake shi mutum ne mai tsananin hakuri shiyasa bai wani yi musuba haka nafisa taja jikinta tai daki jin ɗinkin da aka mata yana yimata ɗan zafi kaɗan da alama ko gudun datai dazune yadan taɓa mata ɗinkin.
******************************
Aɓangarensa.......!!
ƊM.

28 - 29

Is not for free book.....!


Aɓangarensa kuwa.
Yana tafe yana faman waige tamkar wani zautacce kuma ba wani abunne ya sakasa hakan ba illah mamaki da yadda tai masa ɓatan dabon yanzu ya saka yake faman wannan waigen haka.
Harya ƙarasa cikin dakin da aka kwantar dashi jikinsa bai dawo normal kamar ɗazuba.
Da ƙyar ya iya tasar oska daga bacci sannan ya kuma fita a karo na biyu jin har antayar da sallah.
Koda ya idarma da sallar wuff yay ya kuma fitowa tare da komawa wannan lungun daya ganta yana faman dube dube ko ALLAH yasa ya ganta a karo na biyu.
Har wani ɗaki ya tura yana kare face ɗinsa da hannunsa dan baya son wasu su shaidasa.
Ganin haske ya farayi yasa,yabar wajan ya nufi ɗakin da aka ware masa.
Agaggauce yay azkar tare da komawa ya kwanta ya saka hannu ya dafe kansa wanda tsananin damuwa ke sakasa kamar ze rabe biyu.
Sallamar oska ita ta saka ya ɗago rinannun idanunsa ya zuba masa batare daya cewa oskan komai ba sedai a kasan zuciyarsa ya amsa sallamar. amman a baki baxata yiwuba sabida damuwar data haddasa wa bakinsa kasa furta kalmar komai.
"Mai gida barka da asuba, yaya kuma ƙarfin jikin naka?".
oska ya faɗi hakan yana ɗan zama a bakin emty bed ɗin dake gefe.
Cikin ƙasan maƙoshinsa ya furta.
"Alhamdulillahi".
Tare da fesar da wata zazzafar iska mai fitar sauti sa,annan ya dubi oska.
"Osk ya kamata katafi gida hakan nan fa kodan iyalanka,nima anjima zan wuce dan banson zaman nan am not comfatable".
Yakai maganar yana ƙyafe bakinsa gefe kamar ze amai.
Cike da kulawa oska ya dubesa.
"Mai gida nikam ina tare da kai anan ɗin sabida masu kawo maka hari kaga zamanmu mu biyun zefi".
Wata uwar harara ya makawa oska kana ya dubesa.
"Ni ALLAH shike gadina ba wani ba am pls live me kaje babu komai nima zan taho soon insha ALLAH".
Sanin halinsa yasa oska mika masa key na mota tare da yi masa sallama.
Cike da kulawa ya kirawo sunan oska sannan ya miƙa masa key ɗin "kaje da motar ni babu damuwa i will call imiran yazo yay dropping ɗina" yakai maganar tare da komawa ya kwanta.
Mamakin halin karrama ɗan adam irin na Anwarr shiya kama oska amman sanin ba yau ya saba masu haka ba yasa yabar wajan yana faman zabga godiya.
Bai cewa oska komaiba illa ma jan pillowa dayay ya matse a kirjinsa yana faman lumshe idanunsa kamar mai bacci.
Special phone nasa ta soma ringing wadda ta tayar dashi cike da kalasa ya saka hannu yay picking call ɗin ganin number Hidaya.
Cikin kulawa take gaidashi sannan tace meyake buƙata zatazo ta kawo masa dan su anty ma orredy sun taho ita ta tsaya arrangement ɗin break fast ɗinsa ne shiyasa bata tahoba.
Ɗan lumshe idanunsa yay tare da warasu kaɗan sa,annan yace.
"No kibari madam nima ina nan bisa hanya kidai hadamin black coffee shima is ok" tura baki tai gaba kamar yana gabanta.
"Yanzu bazan zoba kenan?"
"Eh".
ya bata amsa direct sabida yadda take kokarin ɓata masa mood.
Kafinma tace wani abu yay rejecting call ɗin tare da komawa ya kwanta kamar wani maraya.
"Oh my GOD mata kenan ita bata ma tunanin yaya nake ita kawai ta break takemin sekace wani.jaki".
Yafaɗi maganar a bayyane tare da rintse idanunsa cike da ƙwarin gwiwa ya furta.
"ALLAH ka kawomun mafita".
Sekuma ya miƙe yay bathroom 10 Mnt yay aciki sannan ya fito kansa jike da ruwa sannan ya kuma kowama bakin gado ya zauna yanajin sa a takure sabida shiba ma,abocin zaman wuri ɗaya bane.
Shiyasa dik wannan zaman ya ishesa.

Cike da sauri anty aisha ta fito daga mota, hannunta dauke da two basket masu tsananin kyau.
Seda ta kulle motar sannan ta dauki sauran kayan tai ciki.
Worda ɗinsu......

KAI KUYI HAKURI WALLAHI NAKASA DARE YAYMIN GASHI INA JIN BACCI😢😢😢😢😢
30 - 31


ƊAN MAJALISA NA KUƊINE.....




Ta ɗauki hanyar ward ɗin da aka kwantar dasu nafisah sosai take sauri gami da duba agogon dake manne a hannunta kana ta ɗan ja ƙafarta sabida kayan sunyi mata nauyi sotake tai maza ta mikawa su ummah nasu sannan ta nufi inda aka kwantar da Anwarr.
Da mamaki akan fuskarta take laluba cikin ɗakin babu kowa babu kuma alamun cewar akwai mutum acikinsa har bayi ta tura kotana tunanin da mutum aciki.
Amman babu kowa ganin tana ɓata lokacin tane yasa tai maza tabar room ɗin tare da nufar office ɗin dr.Harɗo wanda ya kasance yaya a gareta ƙani kuma ga maamah.
Cikin harshensu na fulatanci take sallama cikin office ɗin kana tace.
"Hammah awalijo'm"
Daga nasa ɓangaren ya ɗago da kansa daga jikin farar takardar dake gabansa kana yace.
"Jamm sago" nan sukaci gaba da zuba fillancinsu kamar babu gobe.
Cikin ɗan jimami Aisha ta dubi doctor hardo kana ta soma zuba masa tambaya.
"Hammanah nikam banga patient ɗinmu ta jiyaba wadda aka kawota emergrncy".
Ɗan jimm yay tare da caka biron ajikin papper dake gabansa sa,annan ya dubeta.
"Eh amm ɗazu mahaifiyanta tazo akan..blah....blah....blah...."
Yagama mata bayanin yadda sukai da ummah sahura tas sannan ya sunkuya ya cigaba da aikin dake gabansa.
Babu yadda nurse Aisha tai sabida koba a aikiba Harɗo yayanta ne shiyasa cikin sanyin jiki ta dauki basket's ɗinta tabar office bayan tai masa sallama.
Cikin sanyin jiki ta nufi ward ɗin da aka kwantar dashi.
Tana kokarin murɗa handle ɗin ƙofar room ɗin nasa segasu anty nan tare da imiran mai bin Mas! se shaheedah ƙanwarsu, sabida maamah tace itakam tana masa fatan alkairi amman baxatazo ba.
Dakatawa tai har suka ƙaraso sannan shaheedah ta amshi ɗayan kwandon hannun nurse aisha kana suka shiga cikin ɗakin dukkansu.
Zaune suka tadda shi a bakin gado ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya ya kurawa plasma ɗin dake manne a ɗakin idanu wanda ake watso labarai a tashar CNN.
Itakam aisha nurse aje kayan hannunta tai ta koma bakin emty bed ta zauna kamar wata marar lafiya.
Imiran da shaheedah su suka gaidashi bayan nan anty ta koma gabans tana tambayarsa jikin nasa.
Babu walwala akan fuskarsa haka ya amsa masu gwarama anty ta samu arzikin tambayar ina zuby yarta kenan sukuma ƴar auta a wajansu.
Shikam imiran gaban anty aisha yaje yana faman tsokanarta daman dukkansu.
Sun mayar da ita kamar kakarsu.
Ganin bata kulasa ba yasa ya koma serious yana mata tambaya "yau dai antynmu kodai baban beby ne yay maki albishir na kishiya naga kinyi mana banza?"
Pillow ta dauko ta wurga masa kana tace.
"Sedai kaiwa sakina matarka amman nikam daga kaina babu kari".
Baki ɗaya ɗakin aka saka dariya har anty wadda take tsaye gabansa tana haɗa masa tea a cup.
Shikam ko murmushi bai ba sema kara hade rai dayay tamau.
Seda ta kammala tare da saka tea spoon aciki ta miƙa masa sannan ta koma ta zauna.
Ɗan kallon Imiran yay sannan yace.
"Bros jeka daukomin kaya agida nikam bazan koma da wannan ba"
Yafada cikin bada umarni.
Cikin ladabi imran ya mike tare da kama hanyar waje zeje ya dauko masan.
Itama shaheeda bin bayansa tai sabida duk tajita a takure shidaman yaya anwarr ɗinnan ba,a zama agabansa duk yabi yawani hade rai.
Cike da tsoro tacewa imran.
"Abban hanif zan bika nima gidan".
Dayake imran akwai tsokana juyowa yay ya kalleta.
"To maza taso autar maamah mai tsoron yaya kada ya kawo maka".
Cike da sauri tabi bayansa bayan taiwa su anty sallama.
Bayan futarsu imran anty ta dubi aisha nurse kana tace.
"Waini kam yau yana ganki haka anya kuwa maganar imran ba haka take ba?" itama takai hakan tana dariya wadda daman sun saba ƴar hakan da aisha.
Tsaki aisha taɗan ja kana ta dubi anty.
"Wallahi Anty ba haka bane ni kaɗai nasan asarar danai yau".
"Asara kamar yaya?" anty ta jefeta da tambaya.
"Wallahi wani taimako nasoyi amman ALLAH baiba"
Bata tsaya jin ta bakin anty ba ta dora da cewa.
"Wani emergency case jiya aka kawo mana wata yarinya ce".
Kafin takai wayarta ta dauki ƙara dalilin haka yasa ta dakata da maganar tare da ɗaga wayar.
Shikam tsitt yay tare da tsayar da cup ɗin a dai dai kasan bakinsa shi bai kai bakiba kuma bai ajeba.
Yana son jin mike faruwa amman ko a fuska bazaka alamun ma yana sauraransu ba.
Harta gama wayar da mijinta idanunsa na lumshe batare daya bude ba harta dora da cewa....
"Wallahi aka kawota kamar gawa bakiganta ba anty rauni taji ajikinta wanda yay alamun kamar bindiga harfa bayanta, ni wallahi dan dai mamarta tace hatsari tai ne amman dasenaga kamar case ɗinta yay dai dai da yarinyar datazo tare Muhammad jiya,.
Amman abinda yasa ban gasgata ita ɗin bane sabida, wannan itafa har fyaɗe aka mata......"
Cikin tsoro anty ta furta "fyaɗe fa Aisha".
Wadda sautin maganar ya kusan sakawa mai girma mas! ya diro daga kan gadon dayake sabida tsabar yadda maganar ta dokesa.dan dai kawai shiɗin namijin zakine ba,a gane inda ya dosa.
Rintse idanunsa yay yana sauraran muryar aisha nurse.
"Wallahi anty jikinta duk tabon harbi ga kuma fyade seda nagama cire mata ragowar karfan daya makale sannan na lura da yarinyar tana zubar da jini, wallahi abin baxe faduba anty harfa ɗinki huɗu nai mata".
Tafaɗa muryarta na shakking.
"Wallahi anty dan dai kawai wannan sunce accident ne amman danace wadda zata baiwa muhd kariyane jiya wasu ɓata garin suka far mata bayan sunga bata motsi may be".
Wata irin ƙwarewa ce tazo masa wadda ta firgita kowa da gudu anty taje ɗan karamin furjin dake dakin ta dauko ruwa ta basa yadan kurɓa sannan sukai masa sannu ya koma kan gadon ya kwanta idanunsa na kallon sama.
Seda sukaga ya koma normal sannan aisha ta cigaba.
"Kuma anty yarinyar fa marainiyace wannan matar data kawota jiya kanwar mahaifintace wallahi daga gani basu da wani gatan kirkima, yau wai nazo da shirin kawo masu abinci na tarar da an basu sallama".......
"What!!! sukaji saukar muryarsa kamar ba shiya gama tarin ƙwarewa ba.
"Wayace abata sallama dama haka akeyi?"
Ya kai maganar cikin tuhuma jikinsa har yana rawa.
Duk yadda sukai da doctor hardo aisha ta zauna ta gaya masa sannan ta ɗora da cewa ita daman taso idan yarinyar ta warke seta haɗashi da ita tasan ze shige gaba wajan ƙwatowa yarinyar ƴancinta.
"Amman kuma naga yarinyar tanada ɗan taurin kai wallahi tun jiya mukai mukai da ita akan ta faɗi wanda yay matan amman tace baxata gane ba".
"Ya salam" ya furta akasan labban sa tare da ayyana tabbas itace.......!!!
"Ina zanganki baiwar ALLAH inne mi yafiyarki inkuma hukuntaki da abinda kika mun ba halina bane ba hakan ya salam keki ka jefamu acikin wannan ƘADDARAR"
Yakai maganar cikin ransa kafin kuma kace me idanunsa har sun kaɗa Baikuma bin takansu anty ba ya faɗa duniyar tunanin mafita.
Tabbas seya nemota adik inda take wallahi baze barta haka ba.
Sallamar imran ita ta katse masu hirar su shikuma ya karbi kayan ya wuce bathroom anan ya shirya cikin ƙananun kayan da aka kawo masan kana ya ɗan ja p/capɗ ɗin kaɗan ta yadda mutane basa ganesaba kana yay hanyar waje.
Anty aisha nurse haka ta kwashi kayanta tai waje itama anty tabi bayansu ita tai office anty kuma tai can inda imran yay parking.
Shikam harma ya bude motar ya shiga kallo guda zaka masa kasan yana cikin tentsion amman tsabar miskilanci yahana ya nuna halin dayake ciki ɗin.
Anty na shiga imran yaja motar yabar clinic ɗin cikin tukin nutsuwa suka dauki hanyar gida....

32 - 33


Sunkuyar da kansa yay ƙasa yana kallon screen ɗin tafkekiyar wayar dake hannunsa mai uban kyau da tsada,wadda ta kasance iya mutanan dake kusa dashi ne sosai suka san layin dake kanta.
Number Abokinsa dr safiyan yake dialing wanda sukai karatu tare wanda yake a matsayin babban likita a babban asibitinsa na can cikin garin ɗawisu.
Kira ɗaya daga ɓangaren safiyan aka ɗaga wayan.
Sallama dr safiyan yay masa bayan sun ɗan gaisa sannan anwarr yay masa bayanin drugs ɗin dayake bukata a kawo masa sabida yadda hannunsa ke masa wani irin zafi na azaba.
Bayan sun kammala wayar ya komar da kansa baya ya kwantar yana lumshe idanunsa yana jin jikinsa fayau.
Tafiya mai ɗan tsaho sukai zuwa cikin ɗawisu g.r.a cikin nutsuwa imran ya saita hancin motar har zuwa bakin tafkeken gate ɗin gidan nasu.
Da gudu masu gadi suka taho tare da wangale masa gate ɗin,suna masa barka da shigowa.
Seda ya gyara revers ɗinsa sannan ya buɗe motar ya fito yana kokarin zagayawa baya ya budewa mai girma mas!.
Anty ce ta bude nata side ɗin ta fito shima bai jiraba ya saka ɗayan hannun nasa mai lafiya yaja marufin motar tare da ziro da kyakykyawar farar ƙafarsa guda sannan ya fito da sauran jikin..nasa ya fito baki ɗaya.
Da sauri masu tsaron gidan sukayo wajansa cikin mamaki suka zube suna masa barka da shigowa.
Kowa yana kokarin ya nuna masa yadda yake jajanta masa halin daya faɗa ajiyan na ƴan adawar da suka kai masa farmaki wajan taron jiyan.
Cike da rashin son hayaniya yake ɗaga masu hannun yana mai wucewa cikin gidan.
Bayan ya kirawo sarkin gida ya umarcesa akan yau kada ya sake ya budewa kowa gate indai ba oska dazezo anjima ya kawo masa magunguna ba..
Sabida bayason hayaniya kuma yasan muddin jama,a suka farga daya dawo gida tofa yanzu zasu damesa musamman yan jarida wanda hakan yasa tun jiya da sukai magana da shugaban jam'iyarsu ya kashe wayarsa bai kunnata ba har yanzu.
Cikin bin umarni sarkin gida ya rissuna kana ya amsawa uban gidan nasu batare dayay musuba.
Jan ƙafafunsa yay ya nufi part ɗin maama bayan sun rabu da imran wanda yay part ɗinsa itama anty part ɗinta tai domin ta samu taɗan huta.
Cikin kamala da kamewa yake sallama acikin haɗaɗɗan falon mahaifiyar tasa wanda yaci kayan more rayuwa kamar babu gobe.
Babu abinda ke tashi acikin falon se ƙamshi turaran wuta tare da sautin karatun alkur'ani mai girma cikin muryar shaik sudais wanda yake karanta suratul baƙara, ummi mai aikin mamah wadda take tsakiyar falon tana faman gyara fulallukan dasuka faɗo ita ta ɗago ta amsa masa sallamar cikin ladabi kana ta cigaba da aikin gabanta.
Cikin dakakkiyar muryarsa ta jaruman maza ya furta.
"Ke ina maamah?"
Jikin ummi mai aikin maamah wadda mahaifiyarta ita kewa mamah girki ita kuma ummin ke gyare gyaren ɗakunan maamah mahaifinta kuma shine sarkin gida ƴan kauyene suke zaune agidan can cikin b.q kuma sun jima suna tare dasu maamah dan tun Alhaji sameer yana raye suke tare shiyasa suka saba sosai da mamah ita ta kalli anwar kana tace.
"Tana sama tare da anty sakina"
Bai tankata ba yaja kafafunsa yay hanyar step ɗin cikin sauri.
Tun daga bakin kofar glass ɗin dake saman yafara zame takalman kafafunsa sannan ya saka hannu ya bude ƙofar bakinsa dauke da sallama.
Sautin muryar sakina matar imran kaninsa ke tashi da alamun hira suke da mamah amman inda hidayace mama bazata zauna da itaba.
Da gudu hanif ya taho wajansa yana gwaranci.
"oyoyo daddy" dayake haka hanif ɗin ke ce masa.
Wara hannayensa yay tare da sakin murmushi kana yace.
"Oyoyo my boy i miss you yaron daddy" yafada yana rungume yaron sam yama manta da ciwon hannunsa.
Muryar sakina yaji tana magana.
"Wallahi hanif kada dai ka famawa dadyn naka ciwonsa kaji ko".
Shikam karasowa yay tsakiyar falon yana shafa kan hanif wanda ya lafe ajikinsa sannan ya zauna a saman kujera mai fuskantar maamah.
Ganin haka yasa sakina kama gabanta bayan ta gaishesa tai masa yaya jiki.
Tana fita yaɗan zame hanif sannan ya zube a ƙasa yana gaida maamah wadda tai kamar bataga shigowarsa ba.
Cikin alkunya ta amsa masa kamar wani na gabansu.
Sannan ta aro jarumtar yi masa yaya jikin kana taja bakinta tai gum.
Kamar ze kuka haka ya zuba mata idanu yana kallonta batare daya ce mata komai ba shima.
"Mike damunka naga jikinka yay sanyi akwai abunda yake damunka ina son ka

Please Login or Register in order to submit comment