Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dokawa kamar ze ɓallo waje.
"Feenah ga gwarzonki fa ya ƙaraso tashi ki bude idanunki kiga kyautar da ALLAH ze baki nan gaba kaɗan".
Lumshe idanuwanta tayi tare da sakko dawata zazzafar ƙwallah fafur taƙi ɗagowa sema kuka data saka tare da mayar da kanta kan cinyar walida.
Gigicewa walida tayi tana faman tayar da ita.
"Haba nafisah yaya kike hakane yau fa ranace guda ta farin ciki garemu dan ALLAH kidaina wannan kukan hakan nan mana".
Cikin can ƙasa da murya ta fara magana.
"Walida jinake zuciyata zata fashe walida kice masa yabar wajan nan wallahi zan mutu"
Takai maganar tana gunjin kuka.
Daƙyar walida ta samu ta miƙar da ita sannan ta dinga gaya mata maganganu masu daɗi.
Bisimillah! tayi tare da ɗago ƙwayar idanunta ta zubasu akansa.
Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda ƴar gaske mai kalar dark blue wadda taci wani irin aiki mai kamar na ƴan sarauta, wani irin ɗinki akai masa wanda yaɗan matsesa kaɗan irin na matasa, se hula dake manne akansa mai kalar shaddar jikin nasa, bata samu damar kallonsa dukaba sabida yadda idanunta ke faman kawo ruwa.
Jitake kamar taje ta fincikosa ta faɗa kirjinsa yaji yadda zuciyarta ke faman tsalle tana bugu kamar zata fashe.
Bayani yake cikin harshan turanci amman baki ɗaya ta rasa gane mai ma yake faɗi sabida yadda ta tafi wata duniyar ta daban.
Har sanda manyan mutane suka fara zuwa suna gaisawa dashi kafin waje ya ɗauki sautin shuru.
Se ƙarar sautin speaker da akeji tana fitar da amon sautin daddaɗar muryarsa wadda ya koma bayani da harshan hausa yana magana akan cigaban da aka samu na aiyukan da kujerarsa ta gabatar da sauransu.
Lumshe idanunta tayi tana sauraran kamilalliyar muryarsa wadda tafi zuma daɗi agareta.
Idonta ta kuma ɗagowa ta waresu akansa.
Karaf taga abinda ya ɗaga mata hankali.
Zumbur ta miƙe kamar mahaukaciya ta fara ƙoƙarin fita daga wajan.
Damƙe hannunta walida tayi,
"Feenah ina zakine?"
Bata tsaya bawa walida amsaba ta fincike hannunta kamar wadda zata hau iska tabar wajan aguje.
Zuwa wannan lokacin hankalin mutane yafara yowa kanta sabida yadda ƙarar sautin takalmanta ke fita.
Tsaye walida ta mike tana kokarin binta amman ganin hanyar datayi yasa walida ta tsaya cak cike da mamaki.
Ƙarasowarta kan step ɗin yayi dai dai da lokacin da tsinin harsashin da aka saito ta can wani ɗan waje da aka ɓula ta inda yake tsaye, yake kokarin ɓullowa.
Wanda daga gani seda aka shirya abun da tunani kafin a aiwatar da shirin, wanda iya ita kadai kuma nake tunanin ALLAH ya nunawa wajan itama kuma ba komai yasa hakan ba illah tsananin yadda ta ƙura masa idanune yasa ta hango wannan rikitaccen al,amarin.
Cikin azama wani jami'in tsaro yayo gabanta yana kokarin tareta ganin tayi wajan mai girma mas! aguje.
Wanda hakan ya jawo hankalin mutanan wajan dama sauran jami'an tsaron dake yaɓe a wajan.
Wani ƙarfine yazo mata kamar mahaukaciya ta bangajeshi aguje tai wajan mai girma mas! ta kifa bayanta adai dai saitin kirjinsa ta fuskancin wajen da abin ke fitowa sam bakinta ya rufe ruff dan tsabar tashin hankali tama kasa furta komai.
Ƙarar!! saukar wasu irin kibiyoyin harsashi har guda uku shine ya karade wajan tare da bawa kowa mamaki tare da alajabi dan ganin ba,aga gilmawar kowaba seta waɗannan harsashen.
Waɗanda basu dira a ko inaba se a saitin bayan feenah ɗaya kuma a kafaɗarta ɗayan kuma a gefen hannunsa.
Cikin zafin nama jami'an tsaro dama jama,ar wajan suka fara mikewa cike da tsoro kowa yana son ya bada tasa gudun mawar.
Al'amarin dayasa tawagar su oska tayo kansa gadan gadan suka kamasa hannunsa na ɗigar da jini sukai hanyar fita dashi bayan sun zagayeshi gaba da baya cike da bada kariya.
Dafe saitin bayanta tayi wanda nan da nan jini ya soma ambaliya cikin gushewar hankali ta gangara tai baya ta sami wani ɗan lungu ta ɓuya ganin yadda jami'an tsaron ke faman nemanta wanda saƙon daga shi yake.
Gabaki ɗaya tagama galabaita amman duk da haka hankalinta na garesa baki ɗaya jinta take kamar ta mutu cikin zafin nama da aro dauriya tabi ta ɗayan hanyar ta sha gaban motocin dayake ciki tahau mashin tare da cewa ya bisu, duk yadda takejin dishi dishi a tare da ita amman haka ta daure suka bi bayansu burinta ta ga halin dayake ciki.
Can cikin square kuwa hankalin jama,a atashe yake baki ɗaya jami'an tsaro sun gama zagaye wajan ana faman duba ko ina gefe guda kuma ana neman wannan yarinyar mai kama da aljanu domin neman duniya anyi ba,a gantaba
Gashi babu wanda yaga fuskarta sabida ta bada baya, ƴan jarida har sun fara baza labarin wanda ya cika garin baki ɗaya cikin lokaci kaɗan.
Hankalin walida atashe babu abinda take se kuka!
Ita kadai ta gane feenah ce wadda tai wannan aikin sabida tare sukazo amman hatta ya nura baze shaidaba sabida yadda ta bada baya.
Haka waje ya rincaɓe da hayaniyar wannan lamari wanda babu waɗanda aka zarga se ƴan adawa maƙiyansa masu son ganin bayansa.
*************************
Jini ke zuba ajikinta baki ɗaya ta gama galabaita har zuwa sanda mashin ɗin ya tsaya adai dai gefen wata ƴar unguwa mai cike da tarin bishiyu.
Ganin halin datake ciki yasa mai mashin ɗin yaki tsayawa sauraranta bare ya nemi ta basa kudi ya burga mashin ɗinsa yabar wajan.
Da ƙyar take taka ƙafafunta har zuwa bakin wani ƙaton gida mai kyawun gaske wanda taga mota ɗaya jal daga cikin motocin dayazo ta nufi gidan wanda take tunanin shine aciki andakatar da ragowar kenan.
Cije baki take tana takawa har ALLAH ya bata sa,ar danna kanta ciki wanda gidan yake tsitt se wannan bakar motar data shiga kaɗai a harabar gidan.
Bayan wasu fulawowi ta raɓe tana saka ɗankwalinta a bayanta ta matse wajan dayake fitar da jini tana tunanin yadda harsashin yabi tsokar jikinta ya maƙale amman ita bata ta wannan fatan ta kawai ta gansa taga halin dayake ciki shine muradinta.

Gabaki ɗaya ya kashe wayoyinsa sabida baya son kira ya dakatar da duk wasu securty's ɗinsa tun acan ya umarci oska daya kawosa wannan gidan nasa wanda ya kasance na sirri idanba oskaba baya tunanin da wanda yasan yanada Wannan gida sabida ya kasance na sirrinsane.
Ganin yadda kowa ze damesa ne yasa yay wannan tunani akan ya taho nan ɗin tunda shiba wani ciwo yajiba.

Cikin wani ƙaton bedroom oksa yadan taimaka masa ya zauna a bakin gado yana cije lip's ɗinsa alamun ciwon yana masa zafi.

Kallon oska yay da rinannu idanunsa da suka koma jajur.

"Kaɗauki mota kaje ka zomin da Anty and please ka ganomin yaya hidaya take".
Numfasawa yay yana kallon oska.

"Duk yadda zakuyi kunemomin ita yanzu haka ina son ganinta ina son naji sabidame ta sadaukar da rayuwarta akaina, banajin zan yafewa kaina idan ta rasu adalilina".
Yakai maganar cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa.

"Angama mai gida"
Oksa ya faɗa cike da ladabi gami da barin ɗakin.

Oska na fita ya miƙe cikin jarumta ya tube rigarsa tare da zare singlet ɗin cikin jikinsa, ya daure hannunsa wanda akai sa,a harsashin baya jiki ya fita tun acan tare da zama a bakin gado ya dafe kansa wanda yake barazanar rabewa biyu.

Ganin wani mutumi ƙato baki ya nufo motar nan yasa ta kuma raɓewa ta ɓuya sosai yadda baze gantaba.
Har zuwa sanda ya shiga motar ya figa yabar cikin gidan.

Cikin yanayin jiri ta fito tanajin zuciyarta na tsuma ta nufi hanyar dataga mutumin ya fito.
Falo tsit ba kowa yasa ta nufi wajan wata ƙofa mai kalar golden.
Ta murɗa handle ɗin ta shiga ciki wani azababben kamshine yakaiwa hancinta cafka.
Da sassarfa ta nufi gaban sa wanda yake zaune gefen gado hannunsa dafe akan kuncinsa da alama baima san da shigowarta ba.
Agabansa ta tsugunna tare da miƙa hannunta wanda yake karkarwa ta ɗora akan hannunsa wanda yake naɗe da farar singlet ɗinsa wadda ta jiƙe da jini.
"Haka sukai maka, mai yasa wannan ɗinma bai sauka ajikinaba banyiwa kaina adalciba dana bari jinin nan ke fita ajikinka"
Yaji sautin fitar amon daddaɗar muryarta ya cika masa kunne.
Cike da mamaki ya ɗago jajayen idanunsa ya ɗora akan ƴar yarinyar dake tsugunne a gabansa tana faman kuka.
Wadda sam takasa ɓuya acikin idanun nasa.
Lumshe idanun sa ya ƙarayi tare da waresu akanta cikin dakewa.
Kallon second guda yay mata ya shaidata, tabbas itace.
Cikin jarumta ya ɗagota tare da ɗorawa a gefen gadon dayake shikuma ya tsugunna a gabanta tare da tsirata da idanunsa yana kallonta.
"Sabida me kikai hakan?"
Taji saukar muryarsa a dake acikin kunnenta.
Kallonsa tai sau ɗaya ta kawar da kanta gefe saboda ba itaba kowa ma baya ido biyu dashi sabida kwarjinin da ALLAH ya basa.
"Sabida ALLAH da kuma soyayyarka a zuciyata".
Tafaɗa a dake batare datai shakkaba.
Tsira mata idanu yay yana kallonta yanajin wani irin yanayi ajikinsa.
Cike da basar da abin ya fara ƙoƙarin ganin raunin bayanta.
Domin yafison lafiyarta ta tsira kafin wata magana ta fita abakinsa.
Saukar tattausan hanunsa a gadon bayanta yasa taɗan rintse idanunta kaɗan tanajin wani irin mugun zafi mai wuyar gaske.
Saukar da ita yay ƙasan tiles ɗin yana kokarin ƙara mayar da hannunsa gadon bayan nata domin ya zare harsashin dake ciki wanda harya fara kore alamun ze mata illah.
Cikin hikima ya kwantar da ita a lafiyayyan kirjinsa tare da fara kokarin zare mata cike da dubara.
Wata iriyar ƙara! ta saka a yayin dataji ya zare harsashin bayan nata kafin ta kai hannunta ta kuma damƙesa tsam.
Baki ɗaya ta zuba masa nauyin jikinta duk ta cakumesa tana sakin wani irin kuka mai shiga zuciya.
Wani azababben feeling ke fisgarsa tare da wani irin mutuwar jiki, wanda tunda yake aduniya bai taɓa jin makamancin irinshiba.
Duk yadda hannunshi ke masa zafi bai hana shi jin wata fitinanniyar sha,awa ta kamasaba.
Dafe mararsa yay wadda take barazanar fashewa.
Tare da ɗan tureta ajikinsa yana neman tsarin ALLAH daga sharrin, shaiɗan.
Sake komawa tai jikinsa tana sakin wani kukan sabida azabar datakeji.
Baki ɗaya ta zuba masa breast ɗinta ajikinsa tana goga masa su wanda ita zafin da bayanta ke mata yasaka take wannan birgimar ajikinsa shikam jiyake kamar da gayya take hakan kamar kuma tana sake kaɗa masa wata gangar sha,awar tata take.
Kamota yay sosai zuwa jikinsa ya lumshe idanunsa yana jin wani irin mutuwar jiki.
Ya ɗora bakinsa akan nata yaƙi bata damar yin koda motsi.
Ya fara kissing ɗinta cike da ƙwarewar gaske.
Baki ɗaya ya fita daga hayyacinsa babu abinda yake se ruɗa mata jiki da salonsa.
Har sanda ya kwanatar da ita akan ƙasan tiles ɗin yabi ruwan cikinta ya kwanta yana romancing ɗinta.
Kuka kawai feenah take tana neman ɗauki wanda ko fitar sautinsa ba,aji azaba biyu ta haɗar mata.
Lokacin da hannunsa yakai kan breast ɗinta wani azababben kuka ta kuma kecewa dashi ga azabar bayanta ga azabar yadda yake jamata su kasancewar bata saba da hakanba.
Duk yadda yake bidirinsa bata hayyacinta har sanda ya sami damar rabata da martabarta da kuma, mutuncinta
Wata ƙara! tasaki kafin ta koma luuuuu ta sume.
Jinsa yake kamar wani shaho asama sabida wani irin ni'ima dayake kwasa ajikinta itaɗin zumace madara ce baya cikin hayyacinsa ko nutsuwarsa ko tunaninsa.
Har seda ya kawo sau uku ajikinta sannan ya murgina gefenta yana mayar da numfashi kamar wanda ya sami ƴar hanu daman can.
Wani azababben zazzaɓine ya rufesa ruff haryana haɗa haƙoransa wanda tuni ya saka ya gigice ya fita ahayyacinsa da ƙyar ya mayar da wandonsa tare da komawa gefenta yana mayar da numfashi sama sama.

Takai kusan minti 30 ahaka kafin ta soma ɗaga hannunta cikin azaba da neman ɗauki.
Harta soma bude idanunta waɗanda suka koma kamar wuta dan ja!
Tare da nauyi, ta diresu akansa wanda ke yashe agefenta yana fitar da numfashi cikin azabar zazzaɓin daya rufeshi ayanzu.
Wata irin nadama da tausayin kanta nan take taji ya dirar mata, da jan ciki taja jikinta ta nufi hanyar falo.
Duk jini yana bin ƙafarta tana jin yadda ƙasanta ke faman azaba kamar ana barbaɗa mata barkono.
Harta samu ta fita daga falon baki ɗaya...
Cike da tsananin azaba take jan ƙafarta bayan ta dafa bango ta miƙe ta nufi hanyar bakin gate domin fita daga gidan.
Tana cigaba da kuka mai cin zuciya.....!!

Innalillahi'wainnah ilaihirraju'un......!!


INA ƳAN AMANAR AUTAR MANYA MASU BIBIYAR LITTATTAFANTA?

KU MATSO KUSA WANNAN SALON NASA DABAN YAKE AKWAI SOYAYYA MAI ZAFIN GASKE AKWAI RIKITATTUN AL'AMURA ACIKIN WANNAN TAFIYA.

*SHIN INA FEENAH ZATA? WACE RAYUWA ZATA FUSKANTA? WANI ƘALUBALE ZATA SHIGA*?
*GA HARGITSIN GIDANSU GA AURAN DAZA,AI MATA DA HABU GA WANNAN ƘADDARA DATA FAƊAWA MARAINIYAR ALLAH*?
*SHIN TA INAMA ZATA FARA FUSKANTAR WANI DA WANNAN LAMARIN MAI SARƘAƘIYA DAYA KUTSO MATA*?

*YAYA ZATA KASANCE DA MAI GIRMA MAS! A YAYIN DAYA FARFAƊO DAGA GIGITAR ZAZZAFAN ZAZZAƁIN DAYA RISKESHI*?
*INA ZE GANTA YAYA ZEYI WANI HALI ZE SHIGA? WANNAN ABUN ZESAKA YA SOTA KO ZE SAKA YA ƘITA NE HAR HAKAN YASA YAJI YA TSANETA DOMIN TAI SANADIN JEFASHI ACIKIN ƊABI'AR DAYA TSANA FIYE DA KOMAI WATAKAN ZINA.....?*

AGASKIYA BAZAN IYA TSAYAWA JERO MUKU ABUBUWAN DA WANNAN LITTAFI YA ƘUNSABA SEDAI KUƊINKI YA GAYA MAKI A YAYIN DA KIKA BIYA KIKA TSUNDUMA CIKIN PAID GROUP ANAN ZAKI SAN KOYAYA WANNAN TAFIYAR ZATA KASANCE.


*WANNAN SHINE ƘARSHAN FREE PAGE GAMAI BUƘATAR SAYA SEYAY MAZA YA NEMENI TA HANYAR BAYANIN DAZEZO A ƘASA* 👇




*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
*ƊMS*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_


14 - 15


Cike da tsananin azabar da tunda take acikin duniya bata jin koda makamanciyarta ba take taka ƙafafunta tare da cije bakinta da ƙarfin tsiya jitake kamar ta mutu ta koma ga mahaliccinta ta huta, ahaka harta samu ta buɗe gate ɗin da hannunta wanda yake faman karkarwa.
Buɗewatai ta fita daga gidan baki ɗaya adaddafe tayi bakin titi bayan tasha tafiya mai ɗan tazara kaɗan daga gidan zuwa bakin titi.
Ganin idanunta na faman lumshewa kamar wadda zata mutu yasa ta nemi gu ta zauna abakin titin tare da ɗagawa kowace mota dazo wucewa hannu.
Har ALLAH ya taimaketa ta sami mai napep wanda yake shiɗaya.
Cike da tausayi yaja ya tsaya a gabanta yana faman yi mata magana cikin gushewar tunani take masa bayanin inda ze kaita da ƙyar ta samu ta lallaɓa ta shiga cikij napep ɗin wanda tsohon dayake tuƙa napep ɗin yay kamar ze mata kuka.
Haka yaja yatafi cikin nutsuwa Dayake gidan umma abakin titi yake shiyasa bai wani sha walahaba ya gane ƙofar gidan ya tsaya ya sauketa tare da mata fatan alkairi.
Kuma fafur yaƙi tsayawa karɓar kuɗinta sabida yarinyar ta basa tausayi kuma daga gani acikin wani tashin hankalin take.
Itakuwa nafeesah cike da ragowar ƙarfin daya rage mata take lallaɓa jikinta harta samu ta ƙarasa bakin ƙofar gidan umma sahura.
Da dubara ta samu ta shigar da jikinta cikin gidan tanajin wata iriyar faluwar gaba wadda tazo mata baka tatam.
Atsakar gida taci karo da umma sahura da baba mijinta duk sunyi tsaye gefensu walida tsugunne tana kuka kamar ranta ze futa.
Atare suka ɗago idanunsu sukabita dashi suna kallonta cikin mamaki daga baya kuma suka rugo aguje harda mijin umma sahuran sukayo kanta.
Rumgumeta umma sahura tai tare da fashewa da wani matsanancin kuka!
"Nafisah yau kin ɗagamin hankali ina kika shiga?" inda kin mutu da yaya kikeso naida raina" takai maganar tana rungumeta ajikinta.
Ganin tana faman lumshe idanu kamar bata hayyacinta yasa mijin umma ya fita aguje ya taro napep aka cicciɓeta zuwa ɗan ƙaramin asibitin dake bakin unguwar.
Wanda zuwa wannan lokacin ita tuni tama suma bata cikin hayyacinta.
Umma kuka kawai take tana neman ɗaukin ubangiji har suka isa clinic ɗin cikin mintuna goma leburorin clinic ɗin suka zo da ɗan gadon ɗaukar marasa lafiya akai ciki da ita.
Akabarsu umma cirko cirko suna zaman jiran tsammani.
Shikuwa mijin umma sahura wajan biyan kuɗi da lissafi ya nufa domin yay booking kafin azo garesu.
Itakam umma da walida anma rasa waze baiwa wani haƙuri kowa kuka yake musamman umma datake fatan ALLAH yasa kada maganar tajewa su kaka.
Sosai likita dawata nurse suka duƙƙufa akanta abinda yasama basu nemi akira policeba sabida Mas! ya riga ya cire mata bulet ɗin amman da inda dashi dole se hukuma ta shiga sabida criminal case ne ba,a duba irin waɗannan masu mugun raunin batare da hukumaba.
Sun ɗauki manyan lokuta suna mata ɗinki tare da taimawa wajan da harsashin ya shiga wajan wankewa da liƙewa sannan nurse ɗin ta fito ta bawa baba takardar biyan kuɗi tare da rufesu da faɗan akan kada sukuma wannan gangancin na kawo marar lafiya bayan ya jigata.
Hakuri suka bata sannan baba yay hanyar pharmacy ita kuma umma ta tsaya tare da walida awajan.
Seda aka gama mata komai tsaf sannan nurseɗin ta lulluɓeta da farin mayafi na asibiti tana kokarin fita taga jini na biyo ƙafafunta......!!!
*ƊMS*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_


_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_

                  *16 - 17*

Cikin tsananin tsoro da kiɗima nurse ɗin tabi ƙafafunta da kallo tare da saka hannunta ta yaye mayafin rufar da akai mata,.
Cikin azama ta ɗan ɗaga rigar jikinta wadda ta kasance doguwace tare da ɗan zameta kaɗan.
"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un"!
Nurse ɗin ta faɗa ta ƙarfin gaske tare da saurin mayar mata da rigar ta koma baya tana share hawayen tausayinta dasuka soma mata gudu akan kuncinta.
Akiɗeme ta fita daga room ɗin tare da zuwa wajansu ummah.
Ɗan tsayawa tai agaban umma tana binta da kallon tuhuma bayan ta share hawayenta.
"Baiwar ALLAH kece mahaifiyar wannan mai raunin ko?"
Nurse ɗin ta furta hakan cikin aro dauriya.
Cikin rawar jiki ummah sahura tace.
"Eh nice ƴar nan ALLAH yasa dai ba mutuwa nafeesah tayiba"
Tafaɗa tana zubo da sabbin hawaye.
"Bata mutuba amman da ALLAH kiɗan biyoni ɗakin yanzu am pls ke ɗayafa kada kizo da wannan yarinyar".
Tanuna walida wadda ke tsaye tana zare idanu.
Ummah sahura hartana tuntube tabi bayan nurse ɗin izuwa ɗakin da aka kwantar da nafeesah.
Tana kwance samɓal tamkar gawa dan babu alamun motsi a tare da ita.
Da hannu nurse ɗin ta nunawa ummah sahura nafeesah tare da umartarta akan data ɗaga rigar ta tagani.
Jikin ummah sahura na karkarwa ta nufi gadon tasaka hannunta ta yaye rigarta abinda tagani shiyasata jada baya aguje tana runtse idanunta.
"Innalillahi wainna ilaihirraju'un"
Umma ta faɗa tana saka kuka.
"Waya maki fyaɗe nafisah waya maki haka wani marar tsoron ubangijin ne yay maki haka nashiga uku ancuci marainiyar ALLAH"!
Takai maganar tana kuka.
Ɗan matsota tayi nurse ɗin cike da tsantsar tausayawa tace mata.
"Kiyi hakuri ummah wannan maganar bata fitarwa bace ba yanzu kiɗan bamu waje zanyi kokarin yimata ɗinki sabida gaskiya anbuɗata da yawa, sannan ki rufe bakinki kada ki gayawa kowa harta samu sauki muga yaya za,ai".
Likitan takai maganar cike da rarrashin umma sahura.
Cikin mutuwar jiki umma tabar ɗakin tana jin matsanancin tausayin nafeesah aranta.
Abakin ɗakin ta zauna ragwajab ta saka kuka kamar zata shiɗe.
Cikin sauri baba mijinta dake tafe da kayan magunguna a leda a hannunsa ya karaso gabanta ya tsugunna cikin tashin hankali yake tambayarta meke faruwa?.
Abokin kuka ba,a boye masa mutuwa atake ta zayyane masa komai inda shima nan ya rashe agabanta yasaka kukan tausayin nafeesah.
Sun ɗan dade suna koka lamarin kafin ya rarrasheta su mike su karasa wajan walida wadda ta kafesu da ido dan itakam bama tada bakin magana tunda taga ƙawarta a halin rai ko mutuwa.
Cike da tsantsar tashin hankali a kan fuskar walida ta dubi umma cikin kiɗima kana tace,.
"Ummah tun ɗazu naga kin zauna kina kuka! ƙafata ta gaza ɗaukata zuwa gareki shin lafiya dai ko,koko wani abunne ya faru da nafeesah?".
Takai maganar cikin tuhuma.
Goge hawayen daya zubo mata tayi kana ta dubi walida sa,annan tace.
"Koɗaya walida kedai mutaya yarinyar da addu,a ALLAH ya tasheta lafiya".
"Ameen ummah".
Walida ta faɗa tana ƙara share hawayenta.
Cikin ɗakin kuwa sosai nurse ɗin ta haɗo kayan dazatayi amfani dasu wurin ɗinkin nafisah wadda take jin tausayinta na ratsa mata jikinta tare kuma da la,antar wanda yay ma wannan jaririyar yarinyar wannan cin kacar.
Duƙƙufa tai sosai akanta tafara yi mata ɗinki wanda a wannan lokacin ko yatsan nafisa baya motsi sabida manyan alluran da akai mata masu saka bacci da kashe jiki.
Ta ɗauki kusan awa biyu akan tana ɗinketa wanda seda akai mata ɗinkuna har huɗu kana aka kammala cikin tausayi nurse ɗin ta lulluɓeta bayan ta zare handclov ɗin dake hannunta.
Fitowa tai daga ɗakin tare da nufar office ɗin doctor bayani tai masa tare da aje masa kayan aikinta tai wajansu umma.
Cike da hikima ta jawo umma gefe sannan tai mata bayanin komai tare da shaida mata cewar anbasu gado dole zasu ɗan kwana biyu sabida ɗinki da akai mata tare kuma da raunin dataji wanda yake son abasa kulawa harya warke.
Sallama sukai ita tai nata waje ita kuma umma ta koma taiwa baba bayani amman batai gigin faɗin zancan ɗinkiba sabida walida.
Cike da rawar jiki walida ta dubi ummah sahura sannan tace.
"Umma zanje gida yanzu na shaidawa hajiyarmu idan yaso semuzo da kayan abinci da wasu abubuwan tunda ke kina nan".
Ɗan numfasawa ta kumayi kana tace.
"Amman ummah kada kiyi saurin faɗin cewar ga dalilin dayasa feenah ta sami wannan raunin sabida kinga shi babban mutum ne mubi abin a sannu harta warke kafin asan matsaya, mudai kawai mubari akan cewar motace ta daketa a titi".
Walida takai maganar tana kallon ummah sahura.
Cikin gamsuwa baba mijin ummah sahura dama ita umma sahuran sukai na,am da maganar walida sabida basusan mita hango acikin lamarinba.
Sallama tai musu ta wuce tare da shaida musu cewar seta dawo ɗin.
Shima baba kallon umma yayi tare da ce mata bara yaje kasuwarsu ya ɗan samo kuɗi sabida koda za,a nemi wani abun.
Da kallo tabisa bayan tai masa fatan alkairi ya wuce itama ta wuce can bakin ɗakin ta zauna akan wani ɗan tudu tare da zaman jiran tsammani.
**********************

Hannunshi yake ɗagowa.......!!!
*ƊMS*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_


18 - 19


Hanunshi yake ɗagowa wanda yake masa tsananin zafi sakamakon harbin daya shigesa aɗazu.
Cike da tsananin jarumta wadda tazame masa ɗabi,a tabi jininsa ta mamaye ya gama ɗago hannun nashi tare da saka ɗayan ya dafe ƙasan tiles ɗin sannan ya tallafi jikinsa ya mike baki ɗaya.
Tan ƙwashe ƙafafunshi yayi bayan ya zauna ɗin tare da saka tafukan hannayenshi ya dafe kansa wanda yake barazanar tarwaste masa.
Yakai kusan minti goma a haka yana fama da kansa yana jin yana sake ɗaukar wani matsanancin zafi sassan jikinsa na kama wani irin zazzafan zazzaɓi wanda har rawa rawa jikinsa keyi.
Ɗago idanunsa yay waɗanda kallo guda zaka masu ka kawar da kanka sabida yadda sukai wani irin sauya kala zuwa jawur harwani ruwa ke kwanciya acikinsu dan tsananin jan dasuka ɗauka.
Kallon dai

Please Login or Register in order to submit comment