Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ware masa nasa sannan ya zuba musu ƴan aiki da duk abinda ake buqata na jindadin rayuwa.

Wanda kuma yanzun haka su imran kaninsa su suke jagorantar kaddarorin da mahaifinsu ya bari,shikuma yake jagorantar dukkan wani abu daya shafi gidansu dama sauran ƴan uwansu nacan ƙauye dana cikin garin ɗawisu cikin gidan kakansu mai carbi inda a yanxu haka kakarsa wadda ta haifi mahaifinshi take cikinsa da sauran ƴan uwan mahaifin nashi.


DAWOWA LABARI.



*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*NA*
AUTAR MANYA🌹


🅿️ *7*


Cikin tafiyarshi ta zafin nama irinta lafiyayyan namiji mai jini ajikinshi yake taka ƙafafunshi tare da barin ɓangaren antynshi.
Harabar gidan ya nufa inda ya hangi ma'aikatan gidan maza sunata alwala a bakin famfuna domin nufar masallacin dake tsakiyar gidan wanda ake ƙoƙarin tayar da sallah.
Cikin sauri yake tattare hannun rigarshi tare da nufar wani famfo wanda yake gab da bakin masallacin ya kunnasa aikuwa nan da nan ruwa yafara gudana, batare daya ɓata lokacinshi ba ya tsugunna ya soma alwala cikin azama da himma.
Tube takalmansa yay tare da fito da ƙafafunshi masu kama dana jarirai jajur tabarakallah.
Yafara zuba masu ruwa yana wankesu yana kammalawa ya ɗan ɗebi ruwa acikin tafukan hannunshi ya shafe sumar kansa dashi sabida zafin da ake agari danya ji sanyi kasancewarsa mutum mai tsananin jin zufa.
Yakashe famfon yay saurin shiga cikin masallacin harda haɗawa da gudu! sabida jin antada sallah.
Tsahon lokuta liman yay yana gudanar da sallah a nutse kafin a sallame tare da jan addu,oi bayan an kammala kowa yay hanyar fita daga masallacin kasancewar hatta maƙota bai ɗaukewa zuwa masallacin ba kowa ze iya zuwa yay ibadarsa aciki.
Sosai yake gaisawa da mutane da ƙyar ya samu kansa.
Sannan yaja ƙafafunshi cikin kasala ya nufi ɓangarensa.
A falo ya dakata tare da zama acikin ɗaya daga cikin manya manyan kujerun falon na kamfanin royal, sannan ya zaro wayarsa ƙirar iphone wadda ake yayinta a wannan shekarar wadda take da mugun tsada.
Number oska ya shiga nema wadda ringing guda oska ya ɗauka.
Cikin mutuntaka da ladabi oska ya fara masa bayanin yadda yaje ya gano masa aikin daya bayar acan wani ƙauyen ɗawisu waishi hayin buzuwa, tare da cigaban da aka samu.
Sosai yaji daɗin yadda oska ya gaya masa akan aikin nasu, daman kuma yasan halin oska babban yaronsa wanda sukaga yau kuma sukaga gobe dashi kasancewar oska mutum mai amanar gaske.
Sallama sukai tare da katse wayar.
Layin habu p.a ya kuma kira still.
Cike da rashin gaskiya p.a ya ɗaga wayan.
"Hellow mai gida! barka da yamma?" p.a ya faɗi hakan cikin ɗari-ɗarin magana.
Cikin son ƙure ƙaryar p.a *MAS* ya soma jefa masa tambaya cikin siyasa.
"Ban ganka ɗazu acikin tawagar tahowa gida ba?" halan ko lafiya?".
*MAS* ya jefama habu p.a wannan tambaya wadda ta kusan sakasa ya saki fitsari a tsaye.
Ɗan zaro idanunshi yay kamar marar gaskiya, sannan ya soma magana..
"Am....Ammm,Mai gida! wallahi madam ce babu lafiya shine aka kirani na tafi aguje!
Lumshe idanunsa yayi masu yalwar gashi a samansu gami da haske tamkar na madara sannan yace.
"Okey ALLAH ya bata lafiya idan ka gama kazo nan gida".
Yakai maganar tamkar bai san abunda su habu ke ƙullawaba.
Wawiyar ajiyar zuciya habu ya sauke haɗi dajin wani sanyi acikin ransa ganin tamkar Anwarr bai san abunda suke yiba.
Sannan yay masa godiya ya katse wayar.
Shikuwa Muhammad anwarr ɗan kishingiɗa yayi da wani lallausan pillowa dake ajiye ata gefen kujerar dayake kai tare da ɗora hannunshi asaman ruwan cikinsa ya kamo leɓansa na ƙasa yana tsotsa tare da faɗawa tunanin yadda ze ɓullowa babban aikin dayake son ya fara na titin daya biyo takan ɗawisu zuwa bakin ruwa.

Wannan kenan!!

******************


HOSTEL


Tagumi ta rafka tana tuna murmushin sahibin nata bayan ta gama ninke kayansu na hause ware data wankesu tun safe.
Cike da murna walida tashigo cikin kwanar tasu tare da ɗaka mata duka agadon bayanta.
Firgigit! ta waigo cikin sanyinta da tsananin haƙurinta sannan tace.
"Walida lafiyanki kika dukeni kamar bakki tausayin halin danike ciki?"
Jiki sanyaye walida ta zauna a gefenta tare da kamo hannunta.
"Haba feenah kinsan dalilin yi maki hakan da har zaki tafi wata fassara ta daban?"
Bata jira cewarta ba ta cigaba......
"Hoton mai girma Mas! na samo maki na pastar sa wadda aka liƙa mana jiya shine na salallaɓa na yago maki, nazo na gaya maki ne da murna.....,
Bata bari walida ta ida zancen nataba tai wani tsalle tare da cakumo walidar ta saka hannunta ta baya ta ƙwace pastar ɗin tare da ɗorata bisa ƙirjinta tana lumshe idanunta hawaye na biyo kuncinta.
Tsira mata idanu walida tayi tana kallonta cike da mamaki.
Walida bata gama tsinkewa da lamarin f.k ba seda taga ta aje paster ɗin a kan gadonsu ta tsugunna a gabanta.
Tare da ɗora hannunta adai dai.
Saman ɗan mitsitsin laɓɓansa na ƙasa tana zagayewa da hannunta idanunta alumshe ta fara magana......!

WACECE FEENA??



*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*NA*
AUTAR MANYA🌹


🅿️ *8*


Nafisa kabir shine asalin sunanta mai kimanin shekaru goma sha bakwai da haihuwa.
Suna zaune acan wani ƙauye Acikin ɗawisu waishi fanjam!
Nafisa ƴace ga malam kabir wanda ya fito daga gidan limamin fanjam,gida mai tarin iyalai masu tarin yawa.
Malam kabir shine ɗana biyar awajan malam liman, a bayanshi kuma akwai mata guda biyu, waɗanda suka kasance ƴaƴan kaka, mahaifiyarsu, kuma dukkan ninsu, suna zaune ne agida ɗaya wanda ya kasance ƙaton gaske irin na ƙauyen nan wanda akewa laƙabi da ɗebi da kanka.
Ƴaƴan iya bakwai, baba.lado baba.mudi baba.mati.baba bello,se malam kabiru, daga shi se sahura da hansatu.
Se ƴaƴan innah sukuma su goma ne ciff maza takwas mata biyu.
Se ƴaƴan baba waɗan da suke su shida maza uku mata uku.
Gabaki ɗaya ƴaƴan malam liman sun kasance su ashirin da ukune cif.
Se ƴaƴan ƙannan sa suma masu tarin yawa waɗan da basu da iyaka.
Kuma ko wanne yana zama acikin gidan mal liman ne yayin daze aure kawai zaka shati fegin kane ka gina yadda kakeso ka zauna da matarka.
Wanda ya kasance baka isa ka fita waje kai aureba dole sedai ka auri ƴar cikin zuriyar gidan kasan cewarsu masu ɗumbin yawa shiyasa auren bare yazama haramun acikin wannan zuriya.
Gidane ƙaton gaske mai uban tarin sassa-sassa masu yawan gaske.
Nafisa itace ɗiyar malam kabir ta farko kuma daga kanta bai sake samun wani ɗan ba har ALLAH ya dauki ransa.
Ta taso acikin maraici gaba da baya kasancewar duk gidan malam ana auren zumuncine tun malam liman yana yare haryazo ya rasu.
Malam kabir ya kasance mutum.mai son yawan fita ƙauyukan dake kusa da nasu dama sauran kauyukan daba anan ɗin sukeba, kasancewarsa mutum mai son neman na kansa.
Lokacin da mahaifinsu yana raye yana mugun son kabiru sabida yadda yayo halinsa da komai irin nasa da kuma ladabi da biyayya hakama kaka tana son kabiru sabida yadda yake lura da ita a duk cikin ƴaƴanta.
Lokacin da kabiru ya dauko munzalin girma anan malam ya dauki habi ƴar gidan ƙaninshi ya bawa kabiru ya aura sabida duk sauran ƴaƴan kaka maza sunyi auransu da matansu acikin gidan kuma duk ƴan cikin zuriyar ne babu bare.
Fafur kabiru yaƙi amincewa da tayin mahaifin nashi sabida yadda ya kamu da son wata ƴar fulanin ruga acan wani kauye waishi shashe, dake gabansu wanda har soyayyarsu tai nisa da ƴar fulani.
Wannan shine karo na farko da kabiru ya farawa malam liman musu atun tasowarsa.
Haka zalika itama kaka wannan ne karon farko daya taɓa yi mata musu atun tasowarsa.
Hankalin kowa ya tashi sabida yadda habi take suma akansa tana itafa idan bashiba se rijiya.
Babu abinda ƴan uwan kabiru suke se dariya sunawa malam ALLAH ya ƙara sabida yadda komai yace kabiru komai yace kabiru.
Ashe su haushin abin sukeji, kuma haushin labirun sukeji hatta ga ƴan ɗakinsu su mati bakaramun haushinsa sukejiba.
Babu yadda liman ya iya haka ya ɗauki ɗan uwansa sukaje rugar suka nemowa kaburi auran ƴar fulani saboda ya duba yaga babu haramci akan hakan.
Ita kuma habi aka bawa ɗan ɗakin inna sa'idu wanda yakebin kabiru ta wajan uba.
Wannan lamarin bakaramin kawo hargitsi yay acikin wannan zuriya ba haka akaita ɗauki ba daɗi wanda seda malam ya fito yay jan ido sannan aka rabu da maganar.
Bayan wani lokaci aka daura auren auran kabiru da ƴar fulani saidu da habi,
Ankawo ƴar fulani gidan malam liman inda aka ware mata sashenta daban.
Ba ƙaramar tsangwama ƴar fulani take ganiba acikin wannan family sabida ko moɗarta basa taɓawa wai barece.
Haka zalika kaka bata shiga sabgar ƴar fulani wai acewarta surkulle sukama ɗanta yay mata musu.
Awajan malam kawai takejin dadi wanda basu dauki wani lokaciba ALLAH ya karbi ransa.
Bakaramin kuka yar fulani taiba haka tsangawamarta ta dawo sabuwa acikin gidan bata wani jin dadi idan ba kabiru kenanba.
Cikin ikon ALLAH ta samu ciki lokacin da cikinta ya tsufa, lokacin shikuma kabiru yaje wani kauye yin sari anan ALLAH ya karbi ransa yay hatsari.
Wannan tashin hankali yasa ƴar fulani ta fara naƙuda babu shiri ta haifi ƴarta mace mai kama da ita.
Sak!
Dan tsabar rashin imani irin na ƴan uwan kabiru basu barta ta shayar da ƴartaba suka koreta wai mai bakin jini ce mayya ce tazo zata karar masu da dangi.
Lokacin baffa baban yar fulani yazo haka suka jefo masu kayanta agabansu suka kwace jinjirar suka kora ƴarfulani tare da yimata gargadi mai yawa.
Zuciya irin ta fulani yasa baffa ya hada yarsa sukai ruga yana kuka!
Wannan dalilin yasa suka tattara kayansu suka bar rigar ma baki daya sukai wata!
Riƙon jaririya ya dawo hannun kaka ga kaka kuma ta soma tsufa haka aka tatso nonon saniya aka dinga ɗirkawa ƴa har ranar suna yarinya taci suna nafisa.
Tunda nafisa ta taso take ganin tsangawa awajan kaka take ɗan samun afuwa itaman ma kuma bawai sosaiba.
Kowa ya tsaneta agidan babu mai shiga sabgarta damma kaka tana masifa wataran ne yasa ake lafa mata.
Nafisa akwai hakuri batada faɗa sam komai kuka take masa bata da hayaniya ko kaɗan gata da mugun tsoro.
Wataran kaka har munafuka take ce mata dan tsabar yadda take sum sum kullum cikin hijabi da carbi bata wasa da addini.
Gata da ƙoƙari wanda shiya kuma haddasa mata ƙiyayya acikin gidansu.
Ita kadai ke makarantar boko kuma cikin ikon ALLAH take samun cigaba.
Har ALLAH yasa taci makarantar kwana ta ɗawisu.
Wadda seda kaka tai tsaye sannan baffa babban ɗan kaka ya barta ta tafi makaranta wanda kaka take ƴan buga buga da ita da umma sahura mai bin babanta kabiru suke tsaye akanta sabida umma sahura bata taɓa haihuwa ba, kuma ita ba,a gidan take aureba ɗan kanin kaka take aure acan cikin garin fanjam.
Kuma babu laifi yana da rufin asirinsa shiyasa take taimakon nafisa sabida daman can tasu tafi zuwa ɗaya da kabiru kasancewarta sakuwarsa.
Wataran ma ko hutu nafisa taje tana zama ne agidan umma sahura wadda nafisan ce mata ta saka mata umman sabida yadda take son nafisa komai ta samu ita komai ta samu nafi haka kawai zata hada kayan abinci taje ɗawisu takaiwa nafi sabida basuda nisa da inda take aure.
Nafisa taga rayuwa tanama kuma kan gani sabida yadda ake nuna mata ƙiyayya acikin gidansu kasancewarta bare acewarsu.
Yanzu haka suna ss 3 wanda takai da ƙyar sabida baffa yace ze mata aure da ɗansa habu, wanda babu abinda habu yasani se sata da bin mata.
Da ƙarfin addu,a ta samu ta koma makaranta amman acewarsu tana candy zasu mata aure dan duk sa'anninta na gidan sunyi aure ita ce kawai tai karatu har takai ga candy.
Walida kawarta ce tun suna jss1 har zuwa yanzu walida ita acikin garin ɗawisu take kuma iyayenta masu haline dan sosai take taimakawa nafisa dan hatta provision ɗinsu a haɗe yake.
Ita kuma nafisa take taimakon walida ta sabgar karatu dan ko iyayen walida sun san nafisa sabida yadda walida ke maganarta, su biyu suke harkarsu basa shiga sabgar kowa sosai malamai suke son nafisa wadda akewa laƙabi da f.k nafisa kabir kenan.
Yanzu haka tanada mukamin shugabar makarantar.
Babu ruwan nafisa da kowa sabida bata da magana bare tai hayaniya.
Mutum ɗaya nafisa taji tana kauna duk duniya wanda daga kallo guda taji ta kamu da sonshi shine ɗan majalisarsu mai girma mas! tunda take bata taɓa son wani abu kamarshiba yanzun haka kuka biyu take dana maraici dana sonshi wanda takeji kamar zata rasa numfashinta.

Ganinta na farko dashi.

Suna ss2 ƙarshan term sukai hutu wanda idan suka dawo zasu tafi ss3 yau sauran kwana biyu su koma hutu tana zaune a dakin kaka tana hada kayanta.
Cike da murna kaka tayo dakin.
"ke nafi" dayake haka suke ce mata agidansu.
"kiyi maza ki kintsa kayan nan naki na aikeki can bakin rumbu kije ki sayo ƙuli-ƙulinki na daka maki ni bana son wannan sanyi jikin kiyi maza"
Ɗago idanunta tai masu yalwar haske da girma.
"Tom kaka bara na kintsa" takai maganar tana ɗan kintsawa da hamzari.
Tana gama kintsawa ta yayo mayafinta ta nufi kaka ta karbi aiken sa'annan tai waje.
Lokacin datazo zata saka kanta a waje taji maganar habi matar baba sa'idu cike da habaici.
"Boko koko da ƙosai zadai muga karshan wannan dirama" takai maganar tana sheqewa da dariya.
Sarai tasan da ita take amman bata ko daga kai ta kalletaba haka ta mayar da kanta ga abinda ke gabanta domun idan da sabo ta saba da jin fiye da haka daga bakin matan gidan musamman baba habi wadda tafi kowa tsanarta.
Abakin titi ta tsaya ta hau mashin yakaita naira ashirin taje ta siyo.
Bata dawo ba se gaf da magariba.
Cike da gajiya take sako kanta a cikin gidan nasu.
Da baffa taci karo ze fita sallah.
Dakatawa yay tare da binta da kallon tsana kamar ba ciki guda suke da mahaifinta ba.
"Ke daga ina kike daga yawon iskancinki na ƴan boko kike ko?"
Rintse idanunta tai bakuma tace komai ba.
"Dakata lado dakata" muryar kaka ta karade wajan wadda take fitowa daga sashen ta zata fita.
"Ni na aiketa kadaina jifan nafi da mugayen kalamai insha ALLAHU babu ɓatacce azuriyata" takai maganar tana jan nafisa ajikinta sukai hanyar sashensu nafi na kuka!
Zaunar da ita tai akan gado tare da amsar kulin tai waje.
Itakuwa nafi kwanciya tai saboda bata sallah alokacin.
Cikin bacci sama sama taji kaka ta shigo da ɓuɗa.
"Ke nafi tashi maza gobe asubanci zamuyi cikin garin ɗawisu zanje ganin likitan idanun nan dan yada man gashi naji wannan ɗan albarkar yaron yace duk mai wata matsala gobe ya dauki katinsa na asibiti yaje can asibitin"
Tura baki tai gaba tare da goge ƙwallarta.
"Haba kak kinsanfa gobe ni gidan umma sahura zani daga nan na wuce school sannan zakice muje ki nemi wasu mana koni ɗayace jikarki"
Sakin baki kaka tai tana kallon nafi sannan kuma ta kamo hannunta tana rarrashinta.
"Hab nafisatuna wallahi kallonki nake kamar kabiruna kawai sedai watarana idan na tuna takaicin abinda ƴan uwan kabiru sukaiwa mahaifiyarki senaji haushin kaina"
Takai maganar tana lallaminta.
"Nidai kaka dan dai kawai kinsan idan kika ambaci iyayena ina jin tausayinkine amman da wallahi sedai ƴaƴan so surakaki"
Takai maganar kamar ba itaba sabida watarana ita kanta kaka ba ragama takeba.
Da shirinsu suka kwanta.
Asubar fari suka gama kintsawa suka fita.
Mashin suka samu har tasha sannan suka hau mota sukai ɗawisu.
Basu suka saukaba se takwas na safiya abakin titi kaka ta tsaya ta saya masu kosai da koko.
Fafur nafisa taƙi ci aykuwa kaka tahau mitar wai ta cika girman kai.
Da tambaya suka ƙarasa cikin asibitin wanda ya kasance babban gaske daga gabansa anrubuta.
*ANWARR HOSPITAL*! kallo guda taiwa wajan ta kauda kanta har suka kutsa kansu ciki wanda yawan jama'a da motoci shiyafi bata mamaki.
Ansha ƙauyanci wajan kaka sabida tsaruwar asibitin dan wajan bude kofar ma seda akai dariya sannan sukaje suka zauna sukabi layi.
Nurse ce ta fito jikinta sanye da farin uniform.
Wajan dasuke zaune ta ƙaraso "wacece amina liman?" cike da sauri kaka ta miƙe "nice ƴar nan"
"Okey biyoni baba" nurse ɗin ta faɗa tare da kama hanyar wani lungu.
"Ke nafi taso mana kina nufin barinki zanyi awajannan ki ɓata abanza"
Sum sum nafisa ta miƙe tabi bayan kaka sukabi wannan nurse ɗin.
Wani katafaren office wannan nurse ɗin ta shiga sannan ta nunawa kaka wajan wanda zata ita kuma ta juya.
Da far'a likitan wanda aka rubuta Dr.safwan ajikin farar coat ɗin jikinsa ya nunawa kaka wajen zama har yana tsokanar nafi.
"Kaka kozaki bani wannan ƴarfulanin jikar taki marar far'a" yafada yana kallon nafi wadda sauran ƙirisa ta fashe dan haushi.
Dariya kaka ta saki sa'annan tace.
"Ay kam ɗan nan bada ban anyi mata mijiba damun baka" takai tana dariya tabar nafi da bakin cikin yadda kaka take kokarin bada ita daga zuwa gaban mutum zata fara zance.
Wata farar takarda ya mikowa nafi.
"Tom kanwata naganki ƴar boko maza leƙa office mai number 2 kicewa dr marwan gashi injini"
Karɓa tai ta saka kanta ga fita tana mai jin haushin kaka.
Kanta a sunkuye yake sam bata tsaya duba wata number ba ta kama wata ƙofa wadda tafi ko ina na wajan kyau ta murɗa.
Cikin ikon ALLAH tana murdawa kofar ta bude.
Wadda kofar ta tafi da ƙarfin gaske ta daki bangon office ɗin wanda ya amshi wata irin tsawa mai karfin gaske.
Da baya ta koma ta raɓe ta saka hijabin jikinta ta kare fuskarta tana kallon wani mutum kamar balarabe ko bature ya mike tsaye daga can cikin office ɗin yana sakar mata wani wawan kallo.
Tsoro damuwa fargaba soyayya mai ƙarfi duka a wannan lokacin ƙaddarar faruwarsu ta dirar mata.
Tsugunnawa tai awajan tana kare jikinta sabida yadda taga ya nufota cikin tafiya mai cike da izza isa miskilanci da rashin mutunci da rainin hankali.
Agabanta ya tsaya tare da daka mata wata wawiyar tsawa!!!
"Ke mahaukaciyace!! kalmar datafi saukar dalma zafi acikin zuciyarta kenan.
"Ke wace irin daƙiƙiyace!! yakai maganar cike da zafin zuciya jiyake kamar ya rufeta da duka.
Tana ɗago kanta taganshi tsaye akanta kamar ze daketa baki ɗaya idanunshi ya rine yay ja kamar za,ai ɓarin jini acikinsu.
Da sauri ta tattare zanin jikinta ta ruga da matsiyacin gudu tabar office ɗin tana dafe saitin zuciyarta.
Anan ta jira kaka harta kammala komai sukai gida kaka na mata faɗa itakam zuciyarta ta tafi ga tunaninsa da wata mahaukaciyar soyayyarsa mai zafin gaske.
Ko gidan umma bata jeba haka ta gama hutun ta ta koma school wanda baki ɗaya ta koma wata iri hatta ga karatunta bata mayar da hankalinta akai se tunaninsa wanda kullum dashi take kwana take tashi har ALLAH ya kawoshi makarantarsu ajiya wanda ita sam batai tunanin shi bane ba.

Kunji wacece nafisa

CIGABAN LABARI.



*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*NA*
AUTAR MANYA🌹


🅿️ *9*


Lumshe manyan idanunta tayi masu yalwar zara zaran gashi waɗanda suka sami damar kwanciya a saman idanun nata.
Tare da matsesu tana mai zubo da wani irin hawaye mai masifar gudu! batare data buɗe idanun nataba.
Cikin azabtuwa da masifaffiyar soyayya mai saka mutum a shiga tara bama uku ba f.k tafara magana.
"Ina sonka! ina sonka!! ina sonka!!! M.A wai yaya kakeso nai da rayuwata ne?" zan mutu nima nabi abbana akan da lilin soyayyarka ina fatan kazama mijina agidan aljannah"
Takai maganar kamar mai taɓin hankali..
Shuru kwanar tasu ta ɗauka babu abinda walida take se kallon mamaki wanda tsananinsa ya hana ta ce komai.
Shafa bakinsa take da siraran yatsunta waɗanda suke ƴan madai daita masu kyaun gaske.
Lalubar paster ɗin takumayi tare da kai ɗan mitsitsin bakinta dai dai kan nasa wanda yake manne ajikin poster ɗin yaci wasu shegun suite dark blue masu azabar kyau yana tsaye ya zube hannayensa cikin aljihun wandon suite ɗin face ɗinshi sanye da wani bakin glass wanda ya boye ƙwayar idanunshi.
Ɗora bakinta tai adai dai kan nasa tare da fito da harshenta taɗan lashi laɓɓansa kaɗan dayake jikin paster sannan ta kuma mayar da ita a saman kirjinta tana sakin wani wawan kuka!
Kamar kuma an tsikareta ta miƙe tai gaban walida wadda tai tagumi tana kallon ikon ALLAH tare da mamakin lallai so ba ƙarya ba, koda kuɗi aka ce mata feenah zatai abinda tai yanzu zata musa sabida tsananin kunyar nafisa amman yanzu jibi tsabar soyayya ta sakata ta manta ma a inda take may be.
Saurkar muryar fina ita ta dawo da walida daga duniyar tunaninta.
"Walida kaini wajan yaya nura yana ina inason naji labarin M.A dan ALLAH kada na mutu"
Kamo hannun walida tai ta ɗora a saman kirjinta.
"Walida taɓa kiji yadda zuciyata take harbawa wallahi walida inaga daga kallonshi sau ɗaya may be yay min addu,a ne"
Takai maganar tana rushewa dawani irin kuka!
Kamota walida tai tare da riƙo hannunta.
"Nafisa na gaya maki yaya nura yana can waje kusa da office ɗin baba vise yana jiranmu, please dan ALLAH zomuje koma.maye insha ALLAH nasan ya nura ze sanar dake".
Sannan walida ta kuma jan numfashi.
"Tabbas ƙawata kina cikin jarrabawa mai wahalar gaske domin da alama son maso wani ya kamaki amman zan horeki daki tsawaita addu,a matukar kuna da rabon ganawa ALLAH ze haɗaki dashi".
Takai maganar tana jan hannun feenah tare da share mata hawayen dake saukar mata suka bar cikin kwanar tasu.
Tafiya mai ɗan tazara a tsakanin hostel da area classes!
Sannan suka kai wajan daya nura yake faman baza idanun ganin zuwan nasu.
Da tsokana yabi feenah wadda daman kusan yana mata hakan idan sun haɗu amman ga mamakinsa seyaa yau bata tanka shiba.
Zama sukai a ɗaya daga cikin kujerun wajan sannan feenah ta kakalo murya da ƙyar ta gaishe shi taja bakinta tai tsitt.
Ɗan murmushi walida tai cikin siyasa ta dubi ya nurah.
"Yaya yau kaga sis so slient ko?".
Bata jira cewarsa ba ta kuma cewa.
"Yau ciwon kai take yi ne sabida abinda wannan ɗan majalisar namu yay mata"
Tafaɗi maganar cikin son bugar cikin yah nura sabida bata son ta tona sirrin zuciyar aminiyar tata wadda ita kadai tasan wannan magana.
Ɗan zaro ido yay tare da cewa..
"Lil sis miya faru badai wai mai girma mas! kuke maganaba anya kuwa shine wannan ay baida lokacin mace

Please Login or Register in order to submit comment