Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kota ina, ganin abun yay yawa yasa yay maza ya aje miema a gefen gado yajanyota jikinsa yana bawa anty hakuri "Anty dan ALLAH kiyi hakuri laifina nane wallahi, dan ALLAH anty kiyi haquri". Abinda yaketa faɗa kenan Cike da xafin rai anty tai waje fuww tabar ɗakin jitake kamar tai kuka ancuceta an ɓata mata tarbiyar ƴa.
Tureshi tai ajikinta tare da zaro masa idanunta tamkar mai cutar aljanu "Dalla ni kasakeni aida kabari ta kasheni karewar kiyayya kenan".takai maganar tana kuka sosai.
Tallafota yayi zuwa jikinsa yana bubbuga mata bayanta, "Ni kasakeni wallahi seka rabu dani bana sonka bana kaunar ka indai haka soyayya take batai min adalciba dan ina sonka zakana gaya min dukkan maganar datazo bakinka banasoooooo" wata iriyar murya tamkar ta rodi ce ta cika masa dodon kunnensa kafin yaji kuma ɗuf! tamkar gawa ta kife ajikinsa dawani irin karfi taja dogon numfashi tare da bankarewa baki ɗaya, a nitse ya fuskanci komai wata iriyar ƙara! ce takaraɗe ko ina na ɗakin kafin yaji dirin sautin wani irin kuka! wanda yasa da gudu anty da innatu harma da su afra kunnowa cikin ɗakin, wata irin banƙara take tana haniniya tana wata iriyar dafara, kafin wani lokaci tagama jigata jikinta ko ina na jikinta rawa, yake haka zalika ko ina na halittar jikinta ta sauya idanunta sun koma wasu iri, sosai anty ta gigice tana kuka! kafin wani lokaci maganar taje kunnen maama wadda zuby taje ta sanar da ita, ganin tana kokarin illata yasa yay ta maza ya isa gabanta, da ƙyar ya samu ya rike hannunta saboda wani irin karfin dabai taba jiba shiyaji acikin ƙashinta, duka take kaimasa ta kota ina, cikin ƙwarewa tare da gwancewa yafara karanto (suratul baqra) yana yi yana tofa mata mamah wadda itama jikinta ke rawa tana gefensa tana karanto dukkan addu,ar datazo bakinta, sun jima suna karatun kafin ta fara sauke ajiyar zuciya sekuma kuka! mai ƙarfi ya zo mata tashi tai tsam ta hade kanta da gwiwa tana kuka! "Anwarr bakai mana adalci ba! Anwar bakai mana adalci ba!! wata iriyar murya mai kama data yara ce ta karade ɗakin, Cikin dakewa yake tsareta da idanunsa baki ɗaya tausayinta ya gama kamasa, "Muba macuta bane ba hasalima mu ƴan gadone duk wanda yasan gidan liman yasan akwai mu acikin gidan, mukanzo jikinta idan ranta ya ɓaci, tabbas a yau zuwanmu yazo maka acikin alkairi domin yadda muke tafasa mata zuciyarta a ɗazu zaku iya samun matsala, da ita, Anwarr ka tuna matar data xo maka lokacin dakaje zagaye cikin makarantar kwana? toba wata bace ba seni tun alokacin na baka labarin dukkan abinda yake faruwa a cure nace maka zaka zama warwara zaka xama sila na fitar da rayuka biyu daga cikin matsala ka kuma zama sila na shigar da rayuka biyu cikin damuwa, to rayuka biyun daka warware daga matsala sune waɗannan! ta nuna anty da nafisa, rayuwakan daka jefa cikin damuwa sune! ta nuna miema da nafisa, Cikin ƙudurar ALLAH kuma komai yazo ya wuce meze saka kuma yanzu kazo kana jefa mana jaririya cikin matsala? zamu ɗauketa zamu rabaka da ita kawai!!!! wannan maganar ita ta kuma karade ɗakin, awannan karon karo sautin karatunsa yay sam bai saurari maganganun nasu ba, yacigaba da karatunsa mama tana ɗorawa cikin kuka suka soma bashi haquri "Wallahi zamu fita zamu fita kada ka kona mu" "Sena kona ku domin niba jahili bane ALLAH shi kaɗaine masanin gaibu duk abinda kuka faɗa ban yarda dashiba domin komai ze faru a ƙaddararmu yake babu wanda ya isa ya sauya mana ita".sosai ya cigaba da karatun har sanda suka soma rantse rantse akan bazasu kuma haurowa ba har zuwa sanda sukai atishawa suka fita, zaitun anty ta miqo aka goga mata ajikinta mama ta rungumeta tana share mata gumin dayake keto mata.
Baccine ya kwasheta da ƙyar aka tada ita aka ɗauro mata alwala sannan taxo ta kwanta.
Tagumi yayi ya tsira mata idanu yana kallonta.
"Katashi kaje ka kwanta dare yayi".cewar anty wadda take tsaye duk tausayin ƴar tata ya kamata ashe ɗazu harda sharrin iska a lamarin nata wato damuwar data mata yawane yasaka take shiga wannan hali, Shima anasa bangaren wata kunyar anty da tausayin nafisan ne ya kamasa, duk akan soyayyarsa ƴarta take cikin wannan hali? ashe damuwa tana kusantowa mutum shaiɗanu su dinga kusantar sa, yana ji aransa kodan anty ze tilas tama ransa ya dinga kula da ita sabida gudun faɗawarta halaka duk da dai yana da yakinin seya miqe tsaye da izinin ALLAH ze kawo mata karshen lalurar tata.
Shafa kansa yay tare da furta "Kije anty ki kwanta zan kula da ita kafin anjima".murmushi tayi, tare da kallon su mama waɗanda suke kokarin fita daga ɗakin.
Itama juyawa tai tabar ɗakin tabi ayarinsu.
Ya jima yana kuma tofa mata addu,a yana jin zuciyarsa ta karye akanta musamman idan ya kalli miemah seyaji komai ya kunce masa.
Kamar gawa haka ta koma koda miemah ta farka tana kuka duk iya dubararsa ya kasa bata mama tasha haka ya ɗorata a kafada yana bata ruwan fida harta koma.
Da kallo yabi agogo karfe ɗayan dare harda kwata alokacin kuma ta tashi tare da hade kai da gwiwa tana kuka! maganar duniya yay mata tai masa banza haka ya ɗora mata miema a cinyarta yabar ɗakin alokacin innatu ta shigo.
Harya koma part ɗinsa yana juya lamarin aransa, hidaya tai barci shima alwala yay tare da kwanciya washe gari daya koma wajanta ko kallonsa batai ba gaisuwa ma da ƙyar tai masa daya matsa mata da tambayar meke damunta yanzu seta saka masa kuka! karfe goman safiyar laraba ya nufi can kauye wajan malamin sa sosai ya karbo mata taimako ya kawowa anty babu laifi yanzu tana ɗan sakin jiki dasu anty amman shikam daga gaisuwa bata kuma tanka masa, kuma Alhamdulillahi yanzu jikinta ya warke sedai kuma aranta ta kudira ta daina shiga sabgarsa indai hakan zesaka taja mutuncinta, kwanci tashi babu wuya gashi yau har sunyi kwana arba'in koda tace masa zataje gidansu wajansu kaka bai mata musuba sabida shima yana ta shirye shiryensa domin zaɓe yazo.
Taje gidansu kaka tai kwana uku wanda kusan kullum seyay waya akan ta dawo sannan taje gidan umma sahura tai kwana biyu, tabi innatu can wajan dangin anty tai kwana biyu.
Dawowarta da kwana biyu anty ta soma mata shirye shirye na gyaran jiki akan zata koma can part ɗin su hidaya, duk jikinta babu wani sukuni take karbar gyaran anty.
Hidaya ma tana zuwa dan tare ma sukaje gidansu hidayan da ita, kuma tare sukaje danginsa, shikuwa sosai tadau zafi dashi sarai yanzu ta warke bata da wata matsala dan gane da mutananta sedai ita da kanta taɗau alwashin karɓarwa kanta ƴanci ta hanyar fita daga duk wata sabgarsa, koya shigo bata kulashi, daga gaisuwa take bar masa yarsa ta fice falo wannan abun yana mugun kona masa rai amman sabida shima ɗin miskiline yasa yake basar da ita.
Yau tunda suka tashi ake gyarata mai gyaran jiki musamman anty ta ɗauko wadda ta zage tana gyara ko ina na jikinta sabida anjima kaɗan za,ai walima tare da saukar alqur'ani zuwa dare kuma zata koma can part ɗinsa.......!
*83*



Ba,a gama gyara mata jikin ba se wajan ƙarfe biyu da rabin rana, ruwa mai ɗumi mai gyaran jikin ta haɗa mata a bathroom tare da zuba mata wasu irin turarurrukan wanka masu uban ƙamshi, bata umarni tayi akan ta shiga tai wanka, ita kanta taji daɗin yadda jikinta yake wani irin sheƙi tare da fitar da wani irin sihirtaccen ƙamshi mai ma'ana, ta jima tana gasa jikinta,acikin bathroom ɗin kafin ta gama ta ɗauro babban tawul ajikinta ta kuma yafo wani ƙarami asaman kitson kanta wanda anty ta zauna jiya tai mata, mai uban yawa ƙanana mai kyau, alwala ta dauro sabida kiran ƙarfe uku da rabin rana da akai, tana fitowa ta zira doguwar riga ajikinta seda ta fara rama sallar da ake binta sannan ta ɗora ta la'asar, bayan ta idar ta miqe tare da tube rigar jikinta ta ɗauro zani, wani kaskon wuta ke gefe ancika shi da turare da wasu irin kayan gyara waɗanda suka saje da turaren cikin kaskon, tsugunnawa tayi akai matar ta yafa mata wani katon zani ta rufeta ruf takai kusan minti goma a haka, ko ina na jikinta yana ɗaukar wani irin kamshi kuma tana jin yadda ƙasanta, ke wani irin yamm yana fidda wani irin gumi wanda daga ji kasan an kuma kunno mata wani ruwan ni'imar, bayan anɗauke kaskon zama tai a gefen gado ta soma shiri cikin doguwar rigar shadda wadda aka mata paint work, tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwali, mai gyaran jikin ta kuma shigowa cikin sauri hannunta rike da wani kwano na samira na ainihin da! miko mata tayi "Aida baki soma shiri ba sabida bamu gama ba ai".tura bakinta tayi gaba aranta tana itafa tagaji da wannan ɗurar ga mararta se ciwo take mata komai na jikinta ya sauya, amman dayake bata da musu karba tai tare da godiya, ɗora zani tai akan rigar ta bude samirar, dafaffun ƴan shilane waɗanda aka masu haɗi na musamman, babu wani ɗan ɗano haka ta cinye da ƙyar, ta shanye romon, amman matar bata barta ta taune ƙashinba, tana gama ci aka miko mata kofi wanda aka cikashi da haɗin madara da zuma hardasu kankana da dabino kayayyaki dai kala kala, na mata haka ta shanye shi tass ta miko mata kofi,"Yauwa koke fa ai wallahi idan oga ya shiga hannunki da wuya yasan asuba tayi" ita dai bata fahimci komai ba haka tai murmushi ta miqe ta soma shirinta, daman tun ɗazu miema tana wajansu hidaya suna mata shiri, shiyasa ta samu ta shirya a nutse faɗin yadda tai kyau ma bata bakine,ta fito falo sosai sauran jama,ar da'aka gayyata waɗanda yawanci ƴan uwane da abokan arziki suke yabata harda masu mata hoto. Anty Aisha nurse ce ta mata jagora part ɗin maamah anan ta kuma gaisawa da sauran danginsa ashe dai su taro suke sosai, kai tsaye sama suka nufa ɗakin maamah bayan tagama gaisawa da ƴan falon, wasu saitin akwatuna guda biyu ta gani a jere masu kyau a ɗakin maamah bayan sun gaisa da maamah da kanwar ta wadda Anty aisha nurse kebi anan maamah ta umarci anty aisha data bude mata kayanta tagani, wai ɗazu ya aiko oska ya kawo mata ita ɗaya hidaya ɗaya, miemah ɗaya to ita hidayar an bata nata wannan nasune ita da miemah, wanda atake anan tunaninta ya bata cewar a madadin lefen da bai mata bane ba yayo masu wannan uwar siyayyar domin faɗin irin dukiyar da aka, lafta cikin waɗannan akwatunan bata bakine, seda anty aisha tagama nuna mata kayan, sannan ta dubi mama tana godiya, sannan ta miqe ta fita, waje koda ta koma can part ɗin anty su kaka da sauran matan kannen babanta da yayyensa duk sun zo haka zalika su umma sahura, ma duk sunzo, zama tai suka gaisa kowannen su yana binta da kallo.
Lokacin da mai gabatar da wa,azin tazo a lokacinne hajiya mahaifiyar walida tare da yayyenta da walidar suka shigo suma, wani tsalle tai ta ɗane walida harda kukanta na murna, sosai take farin ciki tana ce mata walida wai munyi candy ban dani se hawaye sharr, kowa dariya yake mata, cikin haka sega masu aikin maamah nan ɗauke da akwatunan da aka nuna mata acan part ɗin anan fa kallo ya koma kansu ita dai jan walida tai suka bar wajan.
Kowa ya dubi kayan cikin akwatunan seya san harkar ta manya ce, sosai matan baffanninta suka tsorata da dukiyar da suka gani nan danan jikinsu yayi sanyi, bayan angama kallon lefe anan masu aikin anty suka soma shigo da kayan ciye ciye da shaye shaye waɗanda seda su kaka suka tsorata, anan fa suka soma Fakar ido suna zubawa a jaka.
Wajan da aka ƙawata ya cika da taron jama,a harda ƴan waje sosai mai wa,azin ta zauna tana bayyana komai daki daki bayan ta kammala akai addu,a tare da soma gabatar da abubuwan da aka tana da domin rarrabawa jama,ar wajan, bayan komi ya kammala, aka soma hotuna waɗanda duk abin da ake miema tana hannun hidaya cikin dangi suna faman hotuna.
Se magariba aka kammala daga nan kaitsaye part ɗin maamah aka nufa da ita, sosai maamah tai mata nasiha mai ratsa jiki sannan dangi suka, wuce da ita, can part ɗin nasa.
Wanda akwai tazara a tsakaninsu dana su mamah sosai.
Sama aka kaita corridow ne ya rabasu ita da hidaya se babban falo wanda nan ne general falo kowa ze iya zama, ɗakuna ne jere acikin ƙaton falon nata guda uku, se kicin tare da store, sosai aka narka dukiya acikin dakunan nata waɗanda ko tsinkensu babu duk maamah ce tace su barshi shi ze mata kowa yana yaba wannan tsari na ɗakunan nata musamman dangin mahaifinta waɗanda suka gane cewa ashe bayan wuya se daɗi a rayuwa.
Nasiha mai ratsa jiki umma sahura tayi mata sannan suka watse suka barta ita da walida sabida miema tana wajan hidiya.
Hirar yaushe gamoce ta ɓarke a junansu seda walida ta gama bata labarin yadda sukai dashi a school sannan itama ta gaya mata komai daya faru wanda walida har kukan daɗi tayi.
Tashi sukai sukayi sallah sannan suka zauna a falo, mintuna kaɗan hidaya ta miqo mata miema itama ta zauna suna hirarsu.
Ganin lokaci yaja yasa walida yimata sallama ta wuce akan gobe ko jibi zata dawo.
Har akai isha bai shigoba.......
*84*


Har akai sallar isha'i bai shigoba jefi-jefi suke ɗan taɓa hira da hidaya wadda rabi akan miemah ne wai yarinyar tana da haƙuri, amman kuma bini-bini tana lura da yadda hidayan ke ɗaukar wayarta tana danna wata number wadda aka rubuta MY CWT MAN wadda take zaton tasa ce amman yadda hidayan bata nuna mata shitake kira ba yasa taja bakinta tai gum dan ita ALLAH ALLAH ma take tabar mata part ɗinta tai sabgar gabanta.
Har wajan 9pm bai shigoba lokacin taɗanja pillow ta kwanta tare da rintse ido (hoho ke hidaya baki san feena bamai son shiga jama,a bace😂) tun hidaya tana hirar harta gaji ganin feena na bata amsa sama sama, kanta a likafa taja ƴam matan ƙafafunta tabar falon,Bayan tayi mata sallama, hidayan tana fita tajawo miema saman ruwan cikinta ta kwantar tana ayyana rashin mutuncin dazata shuka masa tabbas! yana sane yay tafiyarsa sabida baya ɗaukin ganinta a part ɗinsa, ai amarya kota buzuzu ce, Ana ɗaukin ta bare kuma ita da martabar ta.
Cikin zafin rai ta ɗago miema tare da nufar bedroom ɗin da aka fara ajeta acikinsa kwantar da ita tayi ita kuma ta faɗa toilet ta ɗauro alwala, tana fitowa ta shinfiɗa darduma ta fara gabatar da sallar isha'i, tana shafawa taji anturo ƙofa bata ɗago ba sabida jikinta ya bata shine, seda ta kammala komai na dangane da ibadarta, sannan ta nade sallayar, ta aje a gefe guda.
Hijabin jikinta ta rage wata mahaukaciyar yunwa takeji, dan haka tana aje hijabin ta juyo domin fita kicin ta sami abin da zataci.
Karaf idanunsu suka sarke dana juna, zaune yake akan sopar ɗakin yasha farar shadda mai ɗinkin tazarce se bakar hula wadda tai marching da zaran aikin gaban shaddar, babu abinda fuskarsa take se ɗaukar haske gami da annuri, kana ganinsa kasan babu wata damuwa a game dashi 0 tension, kallo guda tai masa ta zare idanunta anasa, ciki ciki tai masa sannu da zuwa tamkar ammata dole shima kuma anasa ɓangaren da ƙyar ya amsa mata, sabida shifa ya soma kosawa da wannan miskilancin data ke masa a kwanan nan yarasa gane inda ta dosa. kafin ya ɗago harta bude kofar ta fice.
Iska ya kaiwa naushi tare da dafe kansa yanajin wata iriyar damuwa akan abin da ta masa.
Ita kuwa kicin ta nufa na cikin falonta ganin babu komai na kayan abinci yasa, ta fita babban falon gidan kanta tsaye kicin ɗin dake cikin falon ta shiga wanda komai yake a dire,kofi ta dauka ta wanke a sink kana ta zubo ruwan tea tare da sugar, biscut ta ɗauko sabida bata shan madara ta fito, waje zata shiga falon ta taga hidaya na kokarin fitowa a wannan karon fuskarta babu walwala ta juya ciki batare data kula hidayanba domin tana hango kamar hidaya irin mutanan nan ne masu bin diddigi tare da son shiga kamar dutsen niƙa.
A falo ta zauna tana sassaita shayin cikin yunwa ta soma sha abinka da mai jego,
Shikuwa wani bacin rai yaji mai tarin yawa acikin ransa da kimarsa da komai wannan yarinyar take wulaƙantashi, wallahi babu macen data isa yabita ɗakinta amman ita sabida mama tai masa nasiha yasa ya biyota amman xata masa banza.
Cike da bacin rai mai yawa ya kwashe wayoyinshi, ya nufi waje bayan ya mannawa miema kiss yana jin ko hidaya bata taɓa masa wannan cin kashin ba.
Ko kallonta baiba haka ya buga mata kofar ya fice.
Tsaki taja aranta tana ayyana kafi ruwa gudu sannan tacigaba da sabgar gabanta.
Zaman kallo ta zauna har wajan 12 dan haka anan ta soma bacci secan kuma ta miqe kamar an tsikareta tai cikin ɗakinta, wani tsorone ya kamata jin shurun tai yawa ga miema tana sharar barci, dan haka ta juya tai falo tattare kayan datai amfani dasu tayi kana ta fita waje domin baxata iya, zama da dattin kayan data sha tea dasuba.
Tana murɗa handle ɗin kofar ɗakin ta tahango abinda ya dakar mata zuciya, hidayace zaune bisa cinyarsa da alama ma kamar basa cikin wannan duniyar tamu, da karfi taji zuciyarta tana rawa nan da nan hawaye masu ɗumi suka soma gudana akan fuskarta kofin hannunta, ne ya faɗi wanda karar! sa ta dawo dasu duniyarmu cike da sanyi jiki ta koma ɗakinta direct kan gado ta faɗa tana gunjin kukan kishi.
Ɗan zame hidaya yayi yana mayar da ajiyar zuciya, cike da kirsa da barikin sanin kan miji hidaya ta dubesa "Haba my man kaima dai kasan baka mata adalciba, nidai kaje na baku sati guda" tafaɗa cikin jin daɗi saboda a yanzu ta tabbata cewar ita kadai ce mai guri a zuciyarsa ganin yadda ya haukace mata.
Shikuwa cikin jarumta da ƙwarewa wajan nuna shiɗin namijine ya dubeta yana sakin murmushi domin baya san tagane akwai wani abun a tsakaninsa da yarinyar "Au bakki san in miki na ƙarshe kenan?" yafaɗa yana tsareta da jajjayen idanunsa ɗan hade rai tai kaɗan "Ban gane na karsheba sekace mutuwa," "Eh mana na karshe bagashi kin bamu sati guda ba" yafaɗa yana gyara rigarsa tare da miqewa daga wajan dan kar ta gane barakarsu yasa ya nufi cikin ɗakin nafisa yana danne dariyar sa.
Da sassarfa ya tura kofar bedroom ɗinta jin yadda take faman sakin kuka, farar rigar jikinsa ya rage tare da hayewa kan gadon baki ɗaya.
Birkito da ita yay zuwa saman cinyarsa yasa hannunsa yana ɗage mata gashin kanta wanda jelar kitson ta kare.
Cikin fusata ta ɗago da rinannun idanunta "Dalla malam ni sakeni wallahi wajan anty zan tafi" tafaɗa tana sakin kuka! sosai take gaya masa maganganu waɗanda babu komai cikinsu se tsabar kishin tsiya, shi dariya ma ta soma bashi, ganin miema zata farka yasa ya hade bakinsu waje guda.
Ɗan zamowa yay kaɗan tare da tsirata da idanunsa jin ya kashe bakin tsiwar.
"Bara nai maki abinda naiwa matata tunda shi kikewa kuka" wannan kalmar ta matarsa bakaramin bata mata rai take ba, ganin tana son ta zame yasa ya ɗora dukkan hannayensa a kafaɗunta ya haɗeta da kirjinsa ya rungumeta tsam.
Birkitaccen turarenta shiya soma kwance masa notikan dake kansa, babu abinda yake se fesa mata hucin sassanyar iskar cikin bakinsa mai kamshin mint.
Tsam ya miƙar da ita tsaye tare da furta mata taje ta dauro alwala, sam bata kawo komai aranta ba ta koma toilet ta dauro alwala shima danata yay using atare suka kammala shiri ya shinfiɗa masu sallaya,sallah raka'a biyu sukai ya jima yana masu addu,a kafin ya miqe da kansa ya dauke miema a gadon ya kaita kan ɗan karamin gadonsu na yara can nesa dasu.
Zame rigar jikinsa yay lafiyayyen gashin dake kwance bisa kirjinsa ya bayyana, babu abinda fatar jikinsa keyi se fitar da kamshi da haske.wajanta ya nufa kai tsaye cikin zalama, tana zaune gefen gado duk idanunta sun firfita waje dan tsabar tsoro.
Kamota yayi da kansa ya zame hijabin jikinta, rigar jikinta ya zame tai saura daga ita se skirt ɗan karami, jawota yay ta faɗa samansa ya saka hannunsa ya rungumeta tsam tsam, tanajin sautin saukar bugun zuciyarsa wadda take gudu da sauri da sauri.
Hannunsa ya ɗora a tsakiyar ramin gadon bayanta yana shafawa kamar mai tsoron kar wani abun ya sameta, ita kuwa hannunta duka biyun ta ɗora a saman kirjinta sabida daga ita se bra, sannan kuma tana kare idanunta daga ganinsa a yadda yake dagashi se guntun wando na maza.
Ɗorata yay bisa gefensa yay mata filet yana binta da kallo ta cikin ɗan hasken dake cikin ɗakin wanda yake fitowa kaɗan kaɗan.
Tureshi tai tana goge hawayenta.
"Ni dan ALLAH ka rabu dani kazo kana ta min abubuwa kamar wani........."Shiiiii Ya faɗa a dai dai saman bakinta tamkar wani tsohon maye kafin ya cafko bakinta yana faman tsotsa tamkar ya samu swt, hannunta ya ɗauke daga kirjinta ya mayar danasa akai yana yi masu wata iriyar sahihiyar shafa, babu abinda take se sauke ajiyar zuciya shima anasa bangaren babu abinda yake se sauke zazzafar ajiyar zuciya kamar wani maye.
Bakinsa ya ɗora asaman dokin wuyanta yana goga mata sajen dake kwance a saman fuskarsa yana ɗan jan fatar wajan kaɗan, alokacin kukanta ya tsananta shima kuma alokacin yake jin ya kasa controlling kansa, sosai yake sucking dokin wuyanta kamar ya samu cwt harya gangaro da bakinsa saman kirjinta yana ɗan ja kaɗan kafin ya mayar da bakinsa baki ɗaya awajan yana musu wata iriyar zuƙa, kuka take tare da kokarin turesa sabida ta kasa gasgata abinda yake yi mata, cikin sauri taja baya tana kuka! "Kabarni na huta na gajiiiiiii" ta furta tana kuka! shima a wannan karon hawaye yake amman hawayen daɗi cike da ƙwarewa ya bita ya jawo jikinsa "Nooooo bazan barki bahhhhh" yafaɗa tamkar wanda yaci yaji!
Mazauni yay mata a saman kirjinsa yana wasa da duk inda yaci karo ajikinta da hannunsa mai uban laushi baki ɗaya ya rikiɗe mata tamkar ba wanda ta saniba jin hannunsa a ƙasan mararta yasa tafara sauke ajiyar zuciya, ganin yadda ya gigice ya zauce wasan nasu ya sauya,yasa naja ƴammatan ƙafafuna nabar ɗakin

Nadai jiyo ihu da sumbatunsa kaɗan kafin na karasa ɗakin madam hidaya.

Sosai take kukan kishi da ƙyar bacci yay gaba da ita wanda rabi na kaɗaicin mijinta ne.

ASUBA TAGARI F & A.
*85*


Jinta take cikin wani irin bakin ciki marar kwatance tana jin kewar mijin nata tare da jin kunci ya kuma ziyartar ranta.
Ganin abun ze bata matsala ya kuma haifar mata da damuwa yasa ta miqe tare da nufar bathroom alwala ta dauro gami da shinfida sallaya ta soma kaiwa ALLAH kukanta, ta jima tana addu,a tare da korar shaidan da kuma neman tsari dashi sannan ta rage kayan jikinta ta kwanta nan da nan nutsuwa ta sameta tare d bacci mai daɗi.

*****

Yajima yana gudanar da sha'aninsa akanta bai sarara mata ba se can cikin dare, jawota yayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa rungumeta yayi tsam a cikin faffaɗan kirjinsa yana shafa mata gadon bayanta har zuwa ƙwanƙwasonta, sosai take kuka ƙasa ƙasa tana jan ajiyar zuciya, sabida yadda yaje mata ɗin be mata zuwan wasa ba sosai ya murji gajiyarsa ajikinta ya zubar mata da dukkan wani sinadarin sa acikin jikinta.
Ɗago fuskarta yayi yana share mata hawayen dake gudu a saman fuskarta da harshensa, sannan ya tarairayeta zuwa bathroom jinginar da ita yayi asaman top ɗin ciki, da kansa ya tarar musu ruwa mai ɗumi acikin bathtube zuwa yay gabanta tare da zare mata ƴar guntuwar rigar dake jikinta, bata da ƙarfin kare kirjinta haka ta barshi ya rungumeta ya haɗa ta da fatar kirjinsa, ya matse har ya kaisu cikin tube ɗin, zaunar da ita yay akan cinyarsa shikuma ya zauna acikin tube ɗin yana

Please Login or Register in order to submit comment