Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

macijai suna fito masu sannan kuzo ku wani liqe gefe da gefe batare dakunyi abinda nace ba ai wannan shashanci ne, to.wallahi tallahi na baka daga nan zuwa gobe ku kammala komai idan ba haka ba!! yaja qwafa tare da baza babbar rigar saman kayan jikinsa yabar wajan a fusace....!
Gabaki ɗaya su p.a sun sha jinin jikinsu sabida sunsan waye ANWARR mutum mai tsatstsauran ra'ayi ɗan aqida na bala'i sam baya wasa da duk wani abu mai mahimmanci a rayuwarsa musamman tallafawa alummah da kawo gyara acikin qauyuka da biranan dake qarqashin kujerarsa, daya baka aiki kai ha'inci gwara ka saci kuɗinsa ka gudu sarai sunsan shi zumane shi ga zaqi ga harbi.
Gumi ke faman tsatstsafowa habu p.a cikin zulumi ya kalli, na kusa dashi "Anas kana kallon yadda mai gida ya fusata fa wallahi idan bamuyi wasa ba wannan tafiyar ze zubar damu ya kama wasu" cikin zulumi anas ya dubi p.a "kaine ai sam haryau baka kula da halin MAI GIRMA MAS! ba shi baya son maci amana wallahi nidai babu ruwana bazaka jamin asarar na cefane ba idan ma zakaje kabawa sardauna ragowar kudin aiki acigaba da mai kyau ka basa idan kuma ba hakaba babu ruwana" anas yakai maganar tare da saurin barin wajan ya nufi wajan motar uban gidan nasu a guje ganin yadda jama,ar gari ke faman shigowa aguje sakamakon labarin daya je masu akan bangon sukari ya shigo unguwar tasu.

Atsaye yake fuskarsa babu yabo kuma babu fallasa dama kuma can Tun fil azal shi mutum ne ba mai son hayaniya ba, kuma shi bai fiya son far'aba sedai zakaga idan anyi abun dariya yay murmushi koya kauda kai wannan shine tsarinsa amman dariya bata daga cikin halinsa. cike da son talakawansa yake ɗaga masu kyakykyawan farin hannunsa mai kama dana larabawa kafin ya ɗan tabo babban yaronsa wanda duk wata tafiya yake dashi yace yaje mota ya fito da kuɗi ya rarrabawa jama,ar dake wajan sannan yaja kafarsa ya nufi mota wadda cikin mintuna ɗaya security's ɗinshi suka bude masa site ɗin baya ya faɗa.
Cikin sauri wata ƴar dattijuwa ta matso gabansa har masu tsaronsa suna hanata qarasawa wajan nasa da sauri ya ɗaga masu hannu ta cikin glass ɗin motar sannan ya zuge tare da zuba mata idanu yana kallonta.
Saukar muryarta akan dodon kunnensa yasa ya qara waro manyan idanunsa yana kallonta.
"ALLAH Yay maka albarka MUHAMMADU! ALLAH yasa kagama da duniya lafiya yadda kake taimako kaima ALLAH ya taimaka maka ubangiji ya tsare gabanka da bayanka ALLAH yabawa matarka ciki ka sami ɗan kanka.......cike da mamaki ya ɗago idanunsa yana kallonta.
Jin wata maganar daga bakin dattijuwar ya kuma sakashi a ɗimuya.
"MUHAMMADU rayuwar ka akwai jarrabawa anan gaba amman ka riqe kalmar HASBINALLAHU WANI'IMAL WAKIL!! ALLAH ze kareka zaka shiga sarqa nan gaba kaɗan amman ALLAH ze taimakeka.
Zaka zama sila kuma zaka zama warwara akan wani kulli wanda ze riski rayuka biyu.........!!





*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*Mallakar*
_AUTAR MANYA_🌹


~~~~~~~
📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS*
~~~~~~~

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_


🅿️ *4*


Cike da tsananin furgici wanda tsantsar jarumtarsa bazata taɓa baka damar gane acikin yanayin dayake ba, yaɗago rikitattun idanunsa yana bin dattijuwar dasu wanda kafin ya sami zarafin magana oska babban yaronsa ya matso tare da kawar da wannan dattijuwar ya umarci driver dayaja mota su tafi.
Cikin ɓacin rai ya doki gaban site din da oska yake kokarin zama cike da masifa yafara magana "Oska waya baka damar korarta shin kasan mitake cemin koko kasan itan wacece?"!! ya bugawa oska wata firgitacciyar tsawa!!
"Mai gida....."shii!!!! bana son jin ta bakinka" yay saurin tarar bakin oska cike da matsananciyar damuwa ya mayar da kansa jikin kujerar dayake kai ya lumshe idanunsa yana jin kansa na mugun sara masa kamar ze fita daga jikinsa.
Kafin wani lokaci tuni yafara jin wani irin mugun sanyi wanda seda ya umarci oska akan ya kashe A/C'n dake cikin motar.
Tattausan hannunshi yasa ya qara jan babbar rigar dake jikinsa ya qara curewa guri ɗaya yana mai lumshe narkakkun idanuwansa, yana jin kansa kamar ba shiba.
"YA SALAM" Yafurta aƙasan laɓɓansa yana jin inama oska bai masa wannan katobararba yaya za,ai ya koreta yana hango gaskiyar wasu abubuwan agame da tsohuwar.
Addu,a yake furtawa acikin ransa yana neman tsarin ubangijinsa akan kada yasa yazama silar shigar wani ɗan adam a damuwa tun fil azal shiba mutum bane mai son yaga wani adamuwa ba sabida haka wannan kalaman suka haɗu suka ɗaga masa hankali.
Har sanda motarsa ta karya kwana ta shiga wata irin rantsatstsiyar unguwa wadda zaman faɗin yanayin kyawun unguwarma ɓata bakine.
Abakin wani katafaren gate driver ya tsaya tare da danna horn.
Cikin mintunan da bazasu gaza goma ba wasu qattin sojoji suka taho a guje tare da wangale gate ɗin.
Cike da nutsuwa motar take danna hancinta cikin compound ɗin har sanda ta shiga cikin parking lot tare da gyara tsaiwa sannan ragowar motocin suka mara mata baya.
Cikin sauri oska da sauran excort ɗinshi suka fito aguje tare da bude marufin site ɗin dayake zaune.
Seda yakai kusan mintuna 20 acikin motar batare daya fito da koda qafarsa ba.
Sannan kuma ya fito da qafarsa tare da wayoyin dake hannunshi yana mai kara ɗaya akan kunnensa.
Ɗaya site ɗin oska ya zagaya tare da ɗauko masa jakarsa sannan ya rufa masa baya shi ɗaya sauran excort's ɗin kuma suka dakata anan.
Hanyar wani haɗaɗɗan part naga oska ya nufa wanda yafi ko ina kyau acikin gidan.
Cikin azama ya saka hannunsa ya buɗewa uban gidan nasa kofar glass ɗin wajan sannan ya ɗan dakata kaɗan tare da rissunawa seda ya bari MAS ya shiga ciki sannan ya mara masa baya.
Abakin wani corridow suka rabu oska ya aje jakar anan sannan ya rissuna yay masa sallama ya nufi juyawa.
"Oska" yaji amon muryar uban gidan nasa ya kira sunansa.
"Na am maigida! oska yay saurin juyowa yana rissunar da kansa a qasa.
"Idan kunci abinci kun huta ina son ka ɗauki mota kaje wajan hayin buzuwa ka ganomin aikin ruwan nan yaya yake tafiya amman pls kada kaje da kowa wannan yazama secret ɗina" yafaɗi maganar yana ɗan dafe kansa.
Cike da tsantsar ladabi oska ya dubi uban gidan nasa sannan yace."angama mai gida bama zan tsayaba yanzunnan zan wuce" yakai maganar yana qara jin son uban gidan nasa aransa sabida adalcinsa.
"No osk kaje ka huta tukunna mubi komai a sannu" yana kaiwa nan ya cigaba da tafiya batare daya tsaya jin me oska ze faɗa ba.
Cikin corridown yake taka qafafunsa akan wani azababban carpet mai bala'in kyau wata hanya naga ya nufa wadda zata sadaka da step ɗin bene.
Cike da sanyin jiki yake taka step ɗin har ya karasa shiga ciki.
Wani katon falo wanda ya sami damar lamushe manyan kujeru har saiti huɗu shiya shiga a tsakiyar falon ya tsaya tare da karya kwana ya nufi wata kofa wadda ta rabu guda biyu.
Ɗayar ya bude ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.
Cike da murna wata ƴar kyakykyawar mace wadda bazata gaza shekaru 26 ba tayo gabansa tana murna.
"Sannu da zuwa dear" tafaɗa cike da farin ciki bayan ta rissuna kasa tana cire masa takalman dake qafarsa.
Seda ta cire ta ajesu a gefe ɗaya sannan ta kamo hannunsa kamar wani yaro qarami ta nufi bakin gado dashi.
Zaunar dashi tayi a bakin katon royal bed ɗin dake ɗakin.
Sannan ta tsugunna a gabansa idanunta cike da qwallah.
"Aminci da rahamar ubangiji su tabbata ga abokin rayuwata mijina abin alfaharina shin meya taɓa ka ne harka shigo gida da yanayin daban sanka dashiba, kafin naji komai daga wajanka ina son kadinga haquri sannnn ka kwatanta adalci acikin mulkin da ALLAH ya baka domin abin tambayane gareka aranar gobe qiyama"
Takai maganar tana kallonsa kamar zata masa kuka!
Cikin jarumta da tsantsar saka abu acikin zuci ya ɗago jajayen idanunsa ya kalli matar tasa dashi tare dajin tsananin qaunarta acikin ransa sabida ayanzu samun kamarta se antona mace mai ladabi da biyayya uwa uba ga tarbiya sannan tana mugun son mijin nata.
"Hidaya" ya kira sunanta.
"Karki damu ba wani abu bane kawai gajiyar office ce" yakai maganar yana jawota jikinsa.
Zaunar da ita yay akan jikinsa sannan ya tallafo fuskarta.
"Ina sonki matata samun kamarki ayanzu da kamar wuya, ina rokon ubangiji daya azurtamu da zuri'a ɗayyiba"
Yakai maganar yana haɗe fuskokinsu waje guda.
Cikin damuwa ta fara magana.
"Dear nima a kullum burina kenan inga ɗanmu ko ƴarmu kasan wannan damuwarfa harta soma bayyana asaman fuskar mama!"
"Shekararmu kusan bakwai da aure dear ko ɓatan wata ban taɓa ba wallahi abin akwai damuwa" takai maganar tana matso da hawayenta.
Rungumota ya kumayi jikinsa sosai sannan yace.
"Karki damu mucigaba da addu,a ALLAH ze kawo mafita tunda dagani harke bamuda wata matsala face lokacine bai ba" yakai maganar yana mayarda kuncin zuciyarsa dan karta gane.
Duk duniya babu abinda ya nema ya rasa sama da haihuwa yana da komai a rayuwarsa babu abinda ya nema ya rasa face haihuwa wadda babu gwajin da ba,ai masu ba kuma dik inda akaje za,ace babu wata matsala kowa a family addu,a yake masa akan ALLAH ya basa haihuwa wanda yanzu duk qannansa na ɗakuna dasukai aure babu wanda baida ɗan kansa, tun mahaifinsa nada rai yake nemo masa taimko akan haihuwa amman har yanzu shuru.
Mahaifiyarsa mama mace mai alkunya da dattako sam bata iya haɗa idanunta dana sa sabida alkunya ta ɗan fari.amman seda tai masa kuka akan rashin haihuwa anty kuwa matar mahaifinsa wadda take uwar ɗaki agaresa da kanta take rakasu duk wata qasa dasukaji bayyanar likitan matsalarsu domin ganawa dashi duk da shima kasancewarsa cikakken likita.
Numfasawa yay tare da zameta daga jikinsa ya mike tsaye "Hidaya bara naje part ɗinsu mama, wajan anty.......!!



*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_

🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*NA*
AUTAR MANYA🌹


🅿️ *5*


Ya zira slipers tare da ɗaukar wayoyinshi dake yashe a saman bed ya nufi kofar fita hidaya na bayanshi, cike da ladabi da biyayya ta tako masa har zuwa falo, kana ta juya ciki bayan tayi masa fatan dawowa lafiya kamar wanda ze tafi unguwa.
Cike da tsantsar ladabi da biyayya ma'aikatan dake farfajiyar gidan suke zubewa a qasa suna masa barka da fitowa cikin kulawa da sanin daraja da qimar ɗan adam yake ɗaga masu hannu tare da ɗan sakin killer smile kaɗan ta gefen kumatunshi.
Ya shiga part ɗinsu mama kofar falo ya danna tare da kutsa kansa aciki bakinshi dauke da sallama.
Larai mai aikinsu tana ganin shi tayi saurin takowa daga hanyar daining area inda take shiryawa su mama abinci ta tsugunna a gabanshi tare da gaisar dashi cikin ladabi da biyayya.
Cike da kulawa ya amsa tare da kama hanyar wani corridow dayay hannun hagunshi.
Wata kofa ya kama ya murda handel ɗin bayan ya shiga cikinta ya turota sannan ya cire takalmin kafafunshi ya taka ciki bakinsa dauke da sallama.
Wani dadda ɗan kamshi mai sanyaya zuciya ya shaka acikin hancinsa ga wani sanyi mai dadi daya hade da wannan kamshi se faman tashi yake acikin falon.
Lumshe idanunshi yayi sannan ya budesu tarr a bakin kofar wani bedroom wanda kofar ta kasance kamar ta karfe amman mai glass nan ma seda yay sallama sannan ya murda ya shiga, tare da wata sallamar still a bakinshi.
Kamshin dayafi nada dadi ya shaka kana ya karasa cikin ɗakin.
Babbar mace far tass mai kimanin shekaru hamsin aduniya na hango zaune akan sallaya hannunta dauke da casbaha tana lazumi.
Kallo guda nai mata na gane itace mahaifiyar wannan bawan ALLAH.
Cike da ladabi da tsantsar biyayya ya karasa gabanta tare da zama ya tankwashe kafafunshi akan lallausan carpet din dake shimfide a tsakar dakin ya sunkuyar da kansa a qasa yana danne danne akan faffadar wayar dake hannunsa wadda aka lamushe maqudan kudade wajan siyanta.
Yakai kusan daqiqa arba'in a zaune a wajan kafin kuma ya dago kai ya kuma duban matar wadda ta daga hannunta sama tana addu,a shima tsintar kansa yay da ɗaga nasa hannun sama suka shafa addu,ar tare sannan ya ɗan saki murmushi kaɗan kana yace.
"Bar ka da rana Maamah" ya karasa maganar a rarrabe saboda yasan idan ma ya cika zaqe mata korarsa zatai
Cikin tsananin kunya wadda mafi akasarin iyaye waɗanda suka shafi da suke nunawa ƴaƴansu na farko Maamah ta dubesa sau ɗaya takk sannan ta amsa batare data bari yaji ba.
Ganin ya sakata agaba yana kallo.tare da saka hannunshi yay tagumi seta miqe ta nufi gaban ma'adanar kayanta ta bude sannan ta ɗan juyo kaɗan.
"Bawan ALLAH katashi kaje wajan babarka ni kasakani agaba koda wani abunne?" takai maganar tana mai danne soyayyar ɗan nata acikin ranta wadda takejinta har zuciyarta amman tsananin kara da kawaici irin na fulanin usul yasa maamah kasa sakewa dashi.
Ɗago kansa yay kamar ze saka kuka shikam abin nan na maamah mamaki yake basa, shifa har tausayin kansa yakeji wallahi bada ban anty da hidaya ba daya zama maraya sabida yadda mama take masa kamar bata sanshiba.
Shiya rasa wannan irin hali na maamah amman yana kallo zata zauna dasu imran kaninsa suna hira harda dariya amman daga yazo waje zata kama sunkuyar da kai shikuma gashi ALLAH yayosa mai masifar maqon uwa.
Danne abin da ke ransa yay sannan yace.
"Dama zuwa nai in maki barka da rana sannan ina neman addu,arki akan aikin dazamu saka gobe acikin unguwar bakin rafi" yakai maganar kamar ze kuka.
Ɗan jimm tayi kamar bazatai maganaba secan kuma tace.
"ALLAH ya tsare" daga haka taja bakinta tai gumm, bata kuma magana ba amman kasan ranta cewa take ai addu,a kam kullum cikin yi maka nake ɗan albarka.
Miqewa yay tsaye tare da zube hannayanshi acikin aljihun wondon shaddar dake jikinsa, sannan ya nufi hanyar barin ɗakin duk jikinsa yay sanyi.
Har ya bude kofar ze fita yaji amon muryarta ya shiga cikin kunnenshi.
"Kacewa matarka anjima su asiya zasu shigo mata" tana gama fadin haka ta juya tacigaba da aikin gyaran cavet dinta.
Ɗan murmushi ya sauke kaɗan shi halin mamah yana kuma kara basa mamaki, wai ace hatta hidaya bata sakewa da ita, dan tsabar kunya bata yarda ko waje ɗaya su zauna da ita, haka ya karasa wajan anty wadda ya tarar da ita zaune akan kujera a falonta tana tsefewa zuby kitso cike da tsananin far'a anty ta karbesa sannan ta ture zuby daga jikinta, ta miqe taje ta wanko hannunta sanin baya son yaga gashi awaje.
"Ɗan gidana yaya rana?" anty ta tambayesa cike da kulawa.
Ga mamakina senaga ya sake kamar bashiba yana zabgawa anty labarai hatta ga fitar dayay yau seda ya gaya mata.
Haka suka dauki lokaci suna hira kafin ai kiran sallar la'asar ya miqe yay mata sallama ya fita.


WANENE ANWAR ƊAN MAJALISA???



TUSHENSHI.....




*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*NA*
AUTAR MANYA🌹


🅿️ *6*


Asalin sunanshi muhammad Anwarr Sameer wanda mafi yawancin abokansa suke masa inkiya da MAS ma'anar hakan shine,muhammad anwar samir, shiɗin ɗane na farko ga marigayi alhaji sameer mai carbi wanda a yanzu yake a matakin ɗan majalissar taraiya mai wakiltar kananun hukumomi guda goma sha huɗu acikin babban birnin jaharsu ta ƊAWISU.

Muhammad anwar yayi karatunshi baki ɗaya a ƙasar indiya inda yayi dukkan karatunshi akan harkar aikin likitanci na ɓangaren mata, ya shafe shekaru masu yawa yana harkar karatun nasa inda kafin ya dawo mahaifinshi ya gina masa ƙaton asibiti anan cikin babban birnin ɗawisu,bayan ya dawo kasar sa ta haihuwa ya soma aiki cikin asibitin nasa batare daya bata lokaci ko sanyaba.

Cikin shekarar daya dawo kuma ALLAH yay ma mahaifinshi alhaji samir mai carbi rasuwa wanda rasuwarsa bakaramin daga hankalin dukkan zuriyar mai carbi taiba.

Alhaji samir ya rasu yabar manyan kaddarori da dama wanda acikinsu harda kamfanunnuka da sauran manya manya kaddara waɗanda sukafi gaban kwatance.

Ya rasu yabar matansa guda biyu.
Hajiya Khadija itace matarsa ta farko wadda ta kasance bafulatanar usul, tana da yara guda biyar Muhammad anwar shine na farko se mai binsa imran bayan sa akwai saifu se shahid da shahida.

Sannan kuma akwai hajiya hafsat wadda suke cema anty wadda mahaifin nasu ya aurota daga baya. agidan tana da yara guda biyu zubaida da zuhura.

Gabaki ɗaya zuriyar alhaji samir suna da mugun haɗin kai sam bazaka gane ɗan wancan ɗakin da ɗan wancan ba sabida yadda suke a haɗe kaf.

Hajiya khadija ( maamah) mace mai tsananin kunya da halin girma sam bata yarda wata alaqa ta hadata da babban ɗanta sabida kara ta ɗan fari.

Shiyasa komai na anwar yake a wajan anty wadda ta zama kamar uwar ɗakinsa sosai suke mugun good time dashi dan wani abun ma idan sunyi sedai antyn ta bawa maamah labari tai ta dariya.

Imran tare akai masu aure da anwar bayan rasuwar mahaifinsu inda yanzu haka imran yana da yara uku amman matar anwar hidaya wadda ta kasance ƴar uwar maamah ta jini ɗiyar kaninta har yau ko ɓatan wata bata taɓayi ba.


Wannan abu yana mugun ɗaga masu hankali hatta kai ga sun fara biyar likitocin wasu kasashen domin gane taka mai man matsalar gashi yanzu har kaninsa na uku yay aure shima yana da ɗan kansa amman sukam har yau shuru.


Bayan aurensa da shekara guda ya faɗa harkar siyasa wadda ba karamin kai ruwa rana yay da manyan cikin familyn suba kafin subarshi ya fara wadda tsananin tausayin halin da talakawa suke ciki yasa ya faɗa harkar bisa tilashin kansa da ra'ayin kansa, wanda ya kasance mutum tsayayye jajuryacce mai mugun tsayawa da ra'ayin kansa.


Seda yaje kasar waje yay wani course akan harkar polities na tsahon shekara ɗaya sannan ya diro kasar sa ta haihuwa wanda babu wata sanya yafara gudanar da harkarsa ta siyasa cike da ƙwarin gwiwa da kuma goyon bayan alummah.

Sosai ya bawa ƴan adawa mamaki waɗanda tashi guda ya wujijjigasu ya basu kashi tun a primary election suka san karon babu dadi.


Tashin farko seda yakai ga ya baiwa abokin karawarsa tazarar kuri'a fiye da miliyan goma wadda ta kuma ƙara masa hope akan harkar tasa takuma ƙara cusawa maƙiyanshin mugun tsanarsa shidin wanda ya zama zakaran gwajin dafi turmin tsakar gida shalugudan mahassada gamji sha sara sha sassaka murucin kan dutse bai fitoba seda ya shirya.


Akaf cikin garin na ɗawusi da sauran ƙauyuka da biranan dake cikinta babu inda sunan MAI GIRMA MAS!! bai zaga ya kewaya yayi yayoba hatta ga yaran goye zakaji suna waƙarsa wadda mawaƙa suka rera masa mata na murna maza na murna kasancewarsa mutum nagari kuma nagartacce jajurtacce mai tsatstsauran ra,ayi akan abinda yake kai.


Muhammad anwar ya kasance kyakykyawan matashi mai jini ajika farine tas mai kimanin shekaru talatin da takwas dogone irin ingarman namijin nan wanda kallo guda zaka masa kasan cewa babu wasa ko wargi a tattare dashi.

Yana da manyan idanuwa waɗanda suka kasance farare tas yana da tabon abun sallah a goshinsa fuskarsa tana zagaye da saje wanda ya kwanta yay luf se ɗan gemunsa wanda yake tsaye carr cike da gashi mai kyau wanda yake samun gyara akai akai.yana da dogon hanci tare da madaidai cin ɗan karamin baki.
Sumar kansa irin mai kanannaɗar nan ce baƙa irin wadda take samun kula gami da kashe kuɗi akai akai.
Anwar mutum ne mai tsananin tsafta kamala da kunya sannan yana da kamun kai dan shi ko lokacin daxe auren farko yawanci anty ke rakasa zance sabida baya iyawa shi acewarsa baisan mema zecewa hidayaba.
Yana da tausayi tare da son zumunci sannan yana da muguwar kyauta.
Yana da tsananin bukata wadda bai san yanada da ita ba se bayan aurensa da hidaya wadda taso basu matsala a farko kafin yanzu ta goge tadena raki.

Arayuwarsa sam baya da son hayaniya bare yawan surutu sedai shidin mutum ne mai kwakwalwar gaske wanda har mamaki yake bawa mutane akan yadda yake sauri ɗaukar abu acikin kansa ko yaya yake yana da mugun kokari kamar kamarme.

Ayanzu haka dayake matakin ɗan majilissa hakan bai hanasa kaiwa asibitinsa ziyaraba harma ya gana da marasa lafiyan cikin asibitin tare da duba lamuransu.


Yaje majilisa ya kawo motion acikin jaharsa dama kananun hukumomin dayake wakilta saboda jajurcewarsa.

Sam baya mu'amala da matan banza sabida shi atsarinsa ma kule kule baya cikinsa, sannan shi yana da tsananin tsafta wadda ta saka a kaf duniya babu abunda yafi tsana kamar zina,


Yana da mugun kwar jini wanda ya saka babu macen daxata iya masa kallo ɗaya tai gigin ƙarawa wanda hatta mazan ma shayinsa suke basa yarda suyi four eye's dashi sabida tsabar kwar jinin da ubangiji ya basa.

Baya zama da mai ha'inci ko maci amana daya baka aiki kai ha'inci koka gudu da kudin kokai son ranka gwara ka saci kudinsa ka gudu!

Yana da tsantsar riqo da addininsa wanda kowa ya shaida sa da hakan sam baya wasa da ibada sannan baya wasa da dukka abunda ya shafi mutuncinsa.


Yana da zafin rai da saurin fushi wanda idan ba zama dashi kaiba bazaka kula da hakan ba saboda tsabar miskilanci da taurin kan daya masa yawa wanda ya haɗe da rashin magana wanda ya gada a wajan maamah mahaifiyarsa wanda zaka iya kwana dashi idan baiga dama ba baze tanka maka.

Mutum ɗaya ke iya zama dashi suyi hira itace anty.


Agaskiya Mas yana da kyawawan hali wanda yasa jama'a suke sonshi musamman idan ya lafto wata kyautar yay maka sekace bama a hayyacinsa yay ba wannan dalili yasa jama'a suke masa laƙani da bangon sukari bakai farin banza ba damuna baki mugunta!!



Yayi ɗan majilissa a karon farko ya haye yanzun ma haka a karo ba biyu ya kuma hayewa wanda ada baiyi niyyar komawa ba amman yadda yaga jama'a suna nuna masa ƙauna yasa ya kuma komawa akaro na biyu.


Yana zaune anan cikin ƊAWISU G.R.A a ƙaton gidan daya gina masu shida iyayenshi inda ya ware nasa sashen shida hidaya yakuma ware na maamah dana anty ya warewa ƙaninsa da matarsa nasu, ɗayan kanin nasama ya

Please Login or Register in order to submit comment