Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

AMMAN MAGIYAR DA WASU SUKAI MIN TA WAYA YASA NA AJE KOMAI NA BAKU WANNAN ƊIN MANAGE PLS*
*80*



Shuru ɗakin ya ɗauka babu mai cewa komai se sautin kukan! nata dake faman tashi, "Waini kam bazaki ma mutane shuru ba ko an dukekine".anty takai maganar cikin ɓacin rai, share hawayen nata tai cikin sanyin jiki ta miqe tsaye tare da nufar cikin toilet tana share ragowar hawayen nata,zama tai akan ɗan top ɗin dake cikin toilet ɗin tana kuka!mai cin rai A cikin ɗakin kuwa anty ce ta dubi innatu cikin zafin zuciya tare da cewa "Inna inaganin anjima idan ƙanwar babanta tazo zamuyi magana idan babu dama ta koma can ɗin idan yaso intai kwana arba'in seta wuce ɗakin mijinta".takai maganar cikin ƙunar rai, "Aykuwa nima tunanin danakeyi kenan Amman idan banda tsabar cutar kai ALLAH yay miki rahama kidinga butulcewa cikin lokaci kaɗan rayuwarki ta sauya komai ya zamo maki labari amman kina wannan botsara haka kamar wata sakarya".innatu takai maganar tamkar zuciyarta zata faso..........Ɗaga murya sosai anty tayi tare da cewa."Wai ubanki kike acikin banɗakinne wallahi nafisa ki kiyayeni kada kibari raina ya soma ɓaci akanki".Sum sum ta turo ƙofar banɗakin ta fito waje tana yarfe ruwan data wanko fuskarta dashi, zama tai a gefe gado tare da sunkuyar da kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, cikin jin haushi anty taja yaranta tabar ɗakin, aranta tanawa dangin uban nafisa ALLAH ya isa domin tana hango rashin shaquwa a tsakanin ta da ɗiyar tata itama innatu tsaki taja afili cikin jin haushi tabar ɗakin, shuru ɗakin ya dauka tamkar babu kowa acikinsa,kukan miema shiya bashi damar tashi daga inda yake tare da jawo Stoll ɗin madubi ya dawo gabanta, ya zauna tare da miqa mata miemah, batare data tallafeta ba ta tura mata maman cikin bakinta tana sha tana share hawayenta, tsira mata idanunsa yay yana noticing ɗinta harna kusan mintuna biyar,sannan ya amshi miema ya kwantar da ita ganin tayi barci, ita kuma juya masa baya tai batare data juyo ta dubeshiba, murya can cikin ransa ya furta maganar"Kijuyo zamuyi magana pls"..........Ƙin jiyuwa tai bare yasa ran zata ɗago ta dubeshi,"Ko matata bata juyamin baya bare kuma ke dalla malama ki jiyo" yakai maganar cikin fusata kaɗan, Cikin zafin zuciya abinka da mai haquri daman bai iya fushiba idan ya tashi ta juyo tare da zuba masa jajayen idanunta kana ta furta"Nikuma karuwa ba niba dallah bace ba idan baka san sunana ba kada ka kuma kirana da dalla".Takai maganar tana zuba uban huci...............Tsit yay yana tsira mata idanunsa sam hayaniya bata cikin tsarinsa dan haka abin seya zo masa cikin bazata "Auzubillahi niban haɗaki da karuwaba ALLAH ya baki haquri".yakai maganar cikin ɗan nuna rashin jin daɗin furucin nata sannan ya ɗora da cewa "Idan rai ya ɓaci tauna magana ake niban kiraki da karuwaba, kuma batun matata danace miki ina nufin ita na soma aura kafin ke! itama bata juyamin baya saboda ba,a bamu wannan tarbiyar ba.yakamata kina tauna magana kafin ki furta tata, oh koda yake ba tarbiyar antynmu bace ba, wallahi harkinsa nafara jin tsoron tasowar miema a gabanki".yakai maganar yana gintse dariyarsa.......ɗiff tai tana nazarin maganar tasa tabbas babu ko shakka magana ya danƙara mata cikin ruwan sanyi batare da tashin hankaliba wanda se mai nutsuwa ne kaɗai ze san abinda yafaɗa ɗin"Kana nufin ni bana da tarbiya kenan? ka raina tarbiyar da aka bani? hmm bazanyi mamakin faɗar hakan daga bakin mutum marar sanin ƙimar ɗan adam irinka ba,amman kasani idanma ina da tarbiya kobani da ita kaine jagaba wajan tarwatsamin ita".takai maganar cikin ƙunar rai............Amai makon taga ya fusata sema murmushin daya saki ta gefen bakinsa tare dajan stol ɗin sosai ya matso gabanta har ƙafafunsu suna gugar na juna sosai ya tsira mata munafukan idanunshi yana kallonta dasu kafin ya kai babban ɗan yatsansa kan bakinta ya talle sa kaɗan, Cikin jin zafi ta ɗago ta maka masa ƙatuwar harara tare da kauda kanta gefe tana murguɗa masa baki "Nidai shawarar dazan baki kiyi kokarin ganin kin farantawa mahaifiyarki rai akan tunanina dakike kada kije ki ɗorawa kanki haqqin uwa!" Ɗiff tai tana sauraronsa cike da tsananin mamakin furucin nasa Tunaninsa! Tunaninsa!! Ta nana har sau biyu,"Nikam ba tunanin ka nake ba ALLAH yay min tsari na zauna ina tunanin abinda baxe ƙareni da komaiba".takai maganar cikin aro jarumta"Ƙarya kike Nafeesahhhh" yaja sunan cikin wani irin salo mai jan hankali tare da kashe jikin ma,abocin sauraro, uwa uba kuma wannan shine karo na farko daya taɓa kiran sunan nata, Sam batai tsammani ba sejin hucin saukar numfashinsa tai adai dai dokin wuyanta cikin wani irin burkitaccen salo ya furta "Ko mahaukaci ya dubeki yasan kin faɗa tafkin soyayya mai wuyar kwatance! kuma bata kowa ba seta ANWARR! wadda kike ƙuntata zuciyarki akanta har kike fito da halin da kike ciki filiiiii".yakai maganar yana ɗan hura mata zazzafar iskar cikin hancinsa wadda ta gauraye da ƙamshin mayen turarensa.............Wani irin abu takeji acikin jikinta hatta farcen ƙafafunta zugi yake mata wani irin electric shork takeji acikin dukkan sassan jikinta, lumshe idanunta tai tare da zubo da zazzafan hawaye tanajin wata iriyar masifaffiyar soyayyarsa jitake dama su dauwama ahakan yana tare da ita koda baze furta mata kalmar soba, fatanta ya zauna da ita ko kallonsa kaɗai tai tanajin sauqi acikin zuciyarta................Ɗora hannunshi yayi akan kafaɗunta tare da mayar da fuskarsa saman wuyanta yana mai lumshe idanunsa ɗumin jikinta tare da ƙamshin turarenta na ƴan maiduguri shine ya shagalar dashi, wani irin laushine da jikin yarinyar wanda tun ranar daya fara raɓar jikinta a duniya ya shaida wannan baiwar tata...............Cike da gwanan cewa awannan sabga ya tura kansa a tsakanin dokin wuyanta tare da fara Goga mata kwantaccen gashin dake cike a fuskarsa wanda ya zagayeta yay wani irin kyau mai burgewa, wani irin nishi! kaɗan ta sauke dukkan ilahirin jikinta ya ɗauki rawa jin yadda yake faman goga mata sajen nashi ajikinta, hannunta tasaka ta ture shi ajikin nata tare da kifawa a kan gado kuka mai cin rai ta saki, ita kaɗai takejin yadda zuciyarta ke fama akansa, hannunshi duka biyun ya ɗora a saman west ɗinta cikin wani irin salo yake murza mata shi, wani irin zillo tayi tare da mirginawa tai baya tamkar zata faɗi ƙasa, gwiwarsa ya ɗora a saman gadon tare da tarairayota baki ɗaya ya dawo da ita kan cinyarsa ya aje yana binta da idanunsa waɗanda suka sauya kala zuwa launin jah! Tsira mata idanunsa yay yana kallon yadda take rintse idanunta alamun bata son kallonsa, kwantota yay a jikinsa tare da ɗora fuskarsa a saman tata gami da fito da harshenshi ya ɗora akan bakinta yanajin yadda bakin nata yake da wani irin laushi, cikin dubara ya sami damar tura harshen nasa cikin bakin nata sosai ya lashe dukkan miyoun dake cikin bakinta, sannan ya ɗagota"Kibuɗe idonki kice bakya sona" yafadi maganar yana kallon saman idanunta wanda ya kumbura kaɗan, tura bakinta tai gaba jitake kamar ta miqe tabar wajan, ɗora bakinsa yay a saman idanunta ya tsotsa kaɗan, sannan ya mayar da idanunsa saman rigarta wadda saman yaɗan bullutso kaɗan na shanunta ya ɗan fito wanda yake ganiyar sa a yanzun, hannunsa ya ɗora a saman wajan yana ɗan shafawa kaɗan, tureshi tai tare da tashi aguje! tai cikin bayi ta danna key, tana jin jikinta yana amsa dukkan sakonnin nasa amman tuno da nasihar innatu ya fargar da ita a lamarin nasa.

Cikin wani irin yanayi ya ɗan saki killer smile kaɗan tare da sauka daga gadon yay hanyar waje jin wayarsa tana ringing!

Afalon anty babu kowa hakan ya bashi damar saka kansa yabar wajan kai tsaye parking space ya nufa gaban wata bakar prada ya tsaya yana amsa wayar tasa, hidaya wadda take faman jefa masa ƙorafi acikin wayar itace ta fito cikin shirinta bayanta afra ce da shahida duk sunci kwalliya cikin shiga ta alfarma.

Kansu tsaye wajan motar suka nufa suka bude back seat suka shiga ita kuma hidaya ta bude front seat ta zauna tana faman tura bakinta gaba sabida ya ɓata masu lokaci.

Seda ya gama abinda ze ya bude driver seat ya zauna yana ɗaura belt ajikinsa, da sauri sarkin gida ya rugo gabansa "Mai gida nace naga zaka fita yau babu su oska kenan amman mai gida baka ganin fita a haka kai ɗaya babu matsala?" sarkin gida ya faɗi maganar cikin ɗan damuwa kaɗan.
Murmushi ya saki acikin ransa sannan ya dubi sarkin gida "Karka damu sarki insha ALLAH babu matsala kaga yau week end kowa yana cikin iyalinsa baxan taso suba, nan nan zamuje unguwar goba gidansu madam sister ɗinta ce ta haihu". yakai maganar cikin kulawa. murmushi sarkin gida yay cikin jin daɗin yadda uban gidan nasu yake kulawa dasu tare da furta "ALLAH ya tsare oga" da ameen ya amsa tare da yin addu,a ya kunna motar yay revars tare da nufar gate. da gudu masu gadi suka bude masa gate ɗin. motar tasa ta halba kwallata ɗoɗar...............
*81*


Cikin mintuna talatin suka isa anguwar goba, gidan ƙanin maamah mahaifiyarsa kenan,kuma gidan mahaifan hidaya matarsa, parking yayi abakin ɗan madai daicin gate ɗin gidan, batare daya ƙarasa wajan masu gadi ba, buɗe motar yay ya fito suma su hidaya fitowa sukai suka taka da ƙafafunsu har gaban gate ɗin, bude ƴar ƙaramar ƙofar da ake shiga yay tare da yiwa masu gadin sallama, cikin nutsuwa batare daya tuna shiɗin wani bane ba, ya miƙa masu hannu sukai musabaha, Cikin matuƙar farin ciki masu gadin sukaita washe baki, batare daya ɓata lokaci ba ya zaro bandir ɗin ƴan onek ya mika masu sannan yasa kai yabar wajan ya nufi cikin gidan magan ganun masu gadin gidan ne ya karade kunnuwansa "ALLAH yaja daran hajiya hadiza ALLAH yajikan Alhajin mai carbi gado se ɗan gado sukari bakai farin banza ba! ALLAH ya raya zuriya insha ALLAHU sekai shugaban ƙasa" murmushi kawai ya saki tare da nufar ciki, da saurinsa, babbar ƙofar sitroom yaja ya shiga ta wajan saukar baki wanda daman tun asali idan zeje gidan anan yake zama, acikin ɗaya daga cikin kujerun sitroom ɗin ya zauna tare da sada kansa a ƙasa yana jin wani iri acikin jikinsa tunda ya rabeta yakasa samun sukuni acikin jikinsa, tabbas baya sonta so ɗayane tak! yana kuma wajan hidayansa, amman kuma yana ishirwarta tabbas idan bai da gaskeba ze iya yin abin kunya ma,ana ze iya jawowa kansa raini, uwa uba kuma idan bai nisanta kansa da itaba tabbas ze shiga matsala sabida jegon datake, taune ƙasan laɓɓansa yay tare da jan numfashi kaɗan, sallamar Abba ƙanin maamah baban hidaya ita ta dawo dashi daga tunanin daya faɗa, cikin sauri ya diro daga saman kujerar tare da tsugunnawa ya gaisar da abban sannan suka soma ɗan tattaunawa wanda rabi akan abubuwan dasuke addabar wannan ƙasar tamune musamman cikin jaharsu ta ɗawisu, zaman abba da ƴan mintuwa umma itama ta shigo gaisawa suka kumayi kafin ƙannan hidaya su shigo tare da kayan abinci,cikin mutuntawa suka gaisa da kannen hidaya sannan suka fita suka barshi shida abba da umma wadda itama tana gama gaisawar dashi tabar wajan, mai jego ma tazo yay mata barka yaga ɗan nata harya mata kyautar kuɗi masu yawa sannan abba ya mike ya fita yana ce masa ya daure yaci abincin koda kaɗanne,acikin gida kuwa, ɗakin umman hidaya cike yake da ƴan uwanta waɗanda suke ciki guda, umma ce ta dubeta "Hidaya ina son magana dake".cikin sanyin jiki ta furta ina sauraranki".da kallo umma tabi sauran ƴan uwan hidaya waɗanda hakan ya shaida masu mai umman take nufi, sum sum suka fita zuwa falo inda su shahida ke zaune suna kallo, sosai umma ta mayar da hankalinta kan hidaya "Kinfi kowa sanin tarbiyar dana baki sabida haka bana goyon bayanki akan kishin hauka irin na dabbobin mata idan har kikai abinda zumunci mu ya ɓaci ko kikai abinda za,ai tirr da ke wallahi!tallahi! ban yafe maki ba".cikin zaro idanu hidaya ta furta "Wallahi umma sam tunani na bai kai haka ba, ada tabbas na fito da wasu halaye na kirsa da riya wanda, ƙawata shafa tai min huɗubarsu amman dana zauna nai nazari sena gane ba kowace ƙawa bace takeson ganinka a ni'imah! wata ƙawar a kullum burinta ta sauya maka farin cikinka zuwa bakin ciki wata ƙawar kullum burinta ta fitar dakai daga rahamar dakake ciki domin tana bakin ciki da rahamar da ALLAH yay maka".ta numfasa tana kallon umma "Amman wallahi umma duk na watsar zan rungumeta tare da ƴarta kuma zan rungumi mijina domin bai sauya min ba wallahi umma yadda yakemin ada yanzun ba bata sauya zaniba tabbas shiɗin adaline sabida haka zanyi kokarin ganin na so ƴarsa domin shine tukwicin ƙaunarsa gareni, amman kuma umma kema kinsan kishi ajininmu yake mu mata zanyi dai iya yina insha ALLAH dan ALLAH kema ki sakani acikin addu,arki". takai maganar tamkar zatai kuka!
Shafo kanta umma tayi cike da tausayawa sabida daman duk cikin ƴaƴanta hidaya tana da saukin kai tare da sanin darajar mutum sam duniya bata dameta ba, "Zan miki addu,a hidaya kema ALLAH ya baki ɗan kanki sabida haka kema ki kuma ɗorawa akan wadda kike fatana ALLAH ya baku zaman lafiya ALLAH kuma ya ƙara nisataki daga sharrin zuciya dana muyagun ƙawaye". murmushi tayi tare da share hawayenta sannan tace "Ameen Umma nagode".Anan kuma hira ta karade a tsakanin ta da mahaifiyar tata tabbas taji 80daga cikin 100 na damuwarta sun ragu a ƴar tattaunawar da sukai da ummanta, kuma acikin ranta tana addu,ar ALLAH ya bar mata ummanta sabida uwace nagartacciya mai tsage gaskiya sam bata damu da duniyaba, wannan dalilin yasa suke aminai ita da maamah mahaifiyar mijinta. Sun ɗauki lokaci mai yawa suna hira cikin haka Aminu mai binta ya shigo ɗakin dayake yana da barkwanci sosai suka zauna ana hira har zuwa sanda sakon sa yazo mata akan tafito, zasu wuce gida.Koda suka tashi tafiya seda umma ta kuma bata shawarwari masu kyau daga ƙarshe kuma tace mata "Komai zakiyi kidinga tunawa da cewa da mahaifiyar mijinki da mahaifinki cikinsu ɗaya komai zakiwa matarsa ko ƴarsa kidinga tuna wannan dangantakar wadda nasan ko babu aure a tsakaninku keɗin mai iya rike masa sune, ALLAH ya tsareki daga sharrin shaiɗan, ban hanaki kula da mijinki da riritashiba amman komai zaki kiyi sa domin ALLAH kada kiyi domin ki bakantawa marainiyar ALLAH rai".share hawaye hidaya tai tare da kallon umma tana murmushi "Umma senaga kamar ma kinfi sonta naji ance ranar farkoma keki ka mata wanka".dariya umma tai "Idan banda abinki hidaya aikome lauje ya yayo ciyawa ai anwarr ɗana ne koda baya aurenki kituna yadda mahaifiyarsa take sona itafa tai silar kawoni gidan nan ita ta haɗa aurena da abbanku, bayan haka kuma nafisa abar tausayice kituna ke kina dani kinada abbanki ita fa? daga fa mahaifiyarta bata da kowa". dariya hidaya ta kuma saki tana rataya jakarta tace "tana da abban miemah ai wallahi umma bara kiga setai alfahari dashi sabida na yarda da ya anwarr managarcin mutum ne".ahaka ta fita daga falon mahaifiyar tata tana jin ranta sakayau. ko a mota anwarr yay mamakin yadda ta saki jikinta tanata sabgarta bakamar fitowarsu ba, awani store suka tsaya bayan tsabar takurar data masa da sauri ta fita bayan ta ɗan leko da kanta "Afuwan dadyn miemah ina zuwa kabani mintuna uku" da kallo ya bita tare dajin wani sanyi aransa "dadyn miemah! ya maimaita a fili tuni wani farin ciki ya kamasa dama zega wannan rana, Cikin kamala ta karasa cikin tsore ɗin ɓangaren beby's dream ta nufa, Atm ɗinta ta fito dashi wanda daman indai zata fita tare dashi take fita sosai ta jibgi kayan beby kala kala na dubunnai sannan ta koma kan kayan shafarsu nan ma tai siyayya bata wasa ba, ta kaso iyayen kuɗi bayan an mata bill aka shigar da kayan cikin leda masu kula da wajan suka ɗaukar mata kayan har zuwa mota, a boot aka zuba mata seda tai masu alheri dayake itama hannunta a bude yake sannan ta bude motar ta shiga tana basu haquri da kallo ya bita batare dayace mata komai ba yatayar da motar suka nufi gida, yawan amsa wayan dayake yasaka basu wani yi sauriba ana kiran sallar isha'i suka karasa a bakin gate ɗin farko ya tsaya tare dayin parking ya ƙarasa gaban mutanan dake jiransa dayake daman baya rabuwa da mabukata ya sallamesu sannan yazo yaja motar ya karasa ciki, shi baima shiga part ɗinsu ba alwala yaje famfo ya dauro ya nufi masallaci seda yay salla sannan ya nufi part ɗinsu, direct bedroom ya nufa rage kayan jikinsa yayi tare da fadawa bathroom, yayi wanka sannan ya fito ya shirya kansa cikin farar jallabiya, lokacin daya fita falo daining yay redy sabida haka zama yay hidaya tai serving ɗinsa itama tai nata suka soma cin abinci wanda rabi wasanninsu suke cike da burgewa.
Seda komi ya kammala sannan ta miqe tsaye hijabi ta ɗoro asaman ƴar sleeping dress ɗin dake jikinta sannan tazo gabansa manyan ledojin daka shigo mata dasu ɗazu ta ɗauka guda biyu ta tura masa ɗaya gabansa, "Dady kazo kaimin rakiya" da kallo ya bita tare da lumshe idanunsa "Kinsan dai matsala bazan iya fita a haka ba".yafaɗa yana nuna mata yadda abar tasa ta miƙe acikin jallabiyar tasa, Murmushi tayi tare da aje ledar gabanta kana ta miqa hannunta kan abar taɗan ja kaɗan! "Afuwan beby ta kimin uzuri yanzu zamu dawo na baki kulawa". Tafaɗ cikin wani irin salo mai rikitarwa, tunma kafin takai aya.ya jawota jikinsa ya matseta yana fesar da zazzafan huci! tare da lalubar bakinta yafara tsotsa seda yaɗan rage zafi da ita sannan ya miqe yana ɗan dafe rigarsa, ahaka yaja ɗaya ledar suka fita.
Ganin ta nufi part ɗin anty ya basa mamaki amman dayake miskiline bai ce mata komiba, a falo suka tarar da inna tu tana gasawa miema cibiya cikin barkwanci suka gaisa da ita, sannan hidaya ta tambayi anty? cemata tai tana cikin ɗakinta tanawa afra wanka, ita kuma nafisa tana ɗaki, tashi hidayan tai shima ya miqe suka karasa cikin dakin da nafisa ke ciki. Sallama hidaya tayi,tare da tura kofa zaune take agaban madubi tana sharce kanta jin sallamar bai saka ta rufeba ta juyo tana tsare kofar da ido tare da amsa sallamar cikin muryarta mai karkarwa.
Ganin hidaya yasa taɗan kame kanta sabida bata san dame tazo ba, gogan yana baya ganinsu su biyu yasa ta miqe ta jawo mayafin data aje a gefe ta yafa tare da karasowa kan center carpet ɗin ɗakin taja pillow ta zauna, hidaya itama zama tai a kusa da ita shikuma yana tsaye ya harde hannunsa a saman kirjinsa azuciyarta tace oh jibi namiji kenan kamar bashi ɗazu yagama yamutsataba.
Cikin sakin jiki hidayan take mata magana "Zuwa nai dama na kawo miki tawa ƴar tsarabar babu yawa dai asakawa miemah ta" takai maganar tana jawo ledar gabanta sosai nafisa tasha mamakin kayan mai ɗa wawa nan danan ta saki jikinta tana mata godiya shima kansa ganin kayan bakaramin mamaki ya bashiva aidaman duk kudinka kana son kaga anyi maka, sosai kuma yaji hidaya ta kuma shiga ransa.
Hira sama sama suke ita da hidayan inda atake anan nafisa taga sauyi sosai a fuskarta bakamar rannan ɗinba.
Koda wasa batai gigin kallonsa bare yasaka ran gaisuwa, wannan lamarin ya bashi mamaki sema kara washewa hidayar baki take sunata hirarsu kamar ma sun manta dashi awajan.cikin ransa yake tuna wani lamari daya taɓa ji wai idan mata suka hade kansu gasa miji suke, ganin kamar ya tafi tunani yasa hidaya ta dubesa "Dady hirarfa ta ɗau daɗi koza zauna ga waje" bai tanka mata ba sema sake gyara tsaiwar sa dayay ita kuwa nafisa batama kalleshi ba tacigaba da sabgarta, itama hidaya atake anan ta gano nafisa yarinyar tana da saukin kai fiye da zato.
Turo kofar akai innatu ce riqe da miema tana ta far,a bayanta wasu mazane su biyu.
"A,a haba sekace baki ku shigo mana tana ciki".cewar innatu sanin hali yasa hidaya ta kame kanta waje guda bayan ta amshi miema ta koma can gefen gado ta zauna tana gyarawa miemah parmpas, ita kuwa nafisa zama ta gyara tana washe bakinta tare da furta "Gabakin dare ai wallahi nayi fushi ace yayye guda se dare zasu zo".Cikin barkwanci babban cikinsu ya kai mata ranƙwashi da sauri ta goce tana dariya tare da furta "Wallahi yaya baffa har yau halinka yana nan bai sauyaba". bummmmmmm!! sukaji ƙarar rufe kofarsa da ƙyar yake taka kafafunsa wannan wani irin haukane da sakarci.........


AFUWAN FOR TYPING ERROS🙏


ina jiran comments
*82*



Wannan wani irin sakarcine, ace ƙatunan garada su shiga har cikin ɗakin matar aure ta sunna, abin baima tsaya a hakanba harseda wancan mai fuskar alalan yake ƙoƙarin kai mata ranƙwashi aka, bai san ina yake taka ƙafafunsa ba har yakai cikin falonsa, a tsakiyar carpet ya baje yana mayar da ajiyar zuciya, kai menene na damuwa da hakan bayan ba sonta kake ba? cewar zuciyarsa kenan, shafo sumar kansa yay tare da furta "Ina kishin aure na ne" yabaima kansa amsa a bayyane, cikin sauri ya miqe jikinsa haryana tsuma kai tsaye fita ya kumayi a hanya suka gamu da hidaya tana kokarin shigowa ko kallonta bai ba ita ma kanta haushin take basa duk maganar datake masa bai kulata ba, cikin mamaki tabi bayansa da kallo, kansa tsaye part ɗin antyn ya koma jikinsa har yana rawa, koda suka gamu dasu a hanya suna kokarin fitowa baiko dubi inda suke ba, hasali ma wani mugun kallo ya watsa musu tare da banka kofar ya faɗa tamkar wani zararre, tana kokarin gyara gyalenta domin raka ƴan uwan nata, su ya baffane ƴaƴan yayan mahaifinta su a birni suke xaune da matansu kuma babu laifi sukam bata da matsala dasu, domin sosai suke sonta dan duk wata matsalar ta idan ta tashi ta kirasu a waya babu laifi zasu taimaka mata dai dai ƙarfinsu, hankaɗa ta yay tai taga taga zata faɗi, cikin basarwa tai maza ta miqe batare data kulashi ba takuma yunkurin fita, da ƙafa ya kwarfota ta faɗi akan tiles kanta yayo ganga ganga, cikin tsoro taja baya tana dafe bakinta, wanda ya fashe saboda buguwar datai akan tile ɗin, cikin wani irin zafin nama ya ɗagota cak! ya tsaidata a gabansa jikinsa yana rawa bakinsa ma haka Saurin bakinsa yafi nada, "Ke watakan baki san darajar aure ba shine har kike barewa waɗancan garadan baki" yafaɗa cikin ƙaraji! tureshi tai da iya ƙarfinta tana mai dafe bakinta "Ƴan uwana ne maye dan na sakar masu fuska, kai xan iya sauya ka amman sukam bazasu sau......" batakai maganar ba ya kife bakin nata da tafin hannunsa "Ƴan uwan banza ƴan uwan hofi waɗanda basu san darajarki da ciwonkiba, to wallahi bara na gaya miki na tsani danginki bana ƙaunarsu bana bukatarsu a rayuwarki waɗanda suka kasa rikeki alokacin da gudan jini na ke jikinki"!!! yakai maganar cikin tsawa! "Kaima bana ƙaunar ka bana buƙatarka a rayuwata" fuwwww ta wuce cikin fushi ta yayo miemah wadda take cikin nate tana barci, gabansa tazo ta dire masa ita "Gata nan indai ƴarkace gatanan ina ita ta haɗani dakai to ga abarka nan nima kabarni na rayu da ƴan uwana, wannan wani irin bala'ine Anwarr kai ɗayane namiji ko ance maka dole seda kai zanyi rayuwa bana auren kabani takarda ta ga ƴarka nan kowa ya kama gabansa, kuma wallahi a yanxu kabani sena bar maka wannan kaddararran gidan na......." bata kai karshe ba ya bata wani kyakykyawan mari mai shiga jiki, kafin ya sauke hannunsa taji wani bakon marin a ɗaya side ɗin nata, kafin kuma daga baya taji duka kota ina acikin jikinta, muryar anty ce ta karade ɗakin "Matsa Anwarr kaban waje karna sameka ɗauke miema daga ƙasa, maza, Dan ubanki ni yau sena illataki haka tarbiyar gidan naku take to wallahi ba,a gabana ba wani shegen ne yabaki tarbiyar mayarwa da mijinki magana,billahillazi ko mahaifiyarsa kishiyata ban taɓa mayarwa da maganaba bare mahaifinsa akan biyayyata aka cucen aka rabani dake, mijina koze yanki naman jikina wallahi bazan masa abinda kikewa anwar ba". sosai take jibgarta

Please Login or Register in order to submit comment