Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗakin.

Itakam nafisa kunyar ganin yadda ƴan falo suke binta da kallo yasa ta koma da sauri hartana tuntube.

Karo suka kusan yidashi baya tai zata faɗi yay saurin tallafota da hannunsa.

A karo na farko a rayuwarsu da suka taɓa kallon kallo a tsakaninsu, sosai mamakin kuruciyarta ya kamasa lallai ALLAH mai kyauta da kari idan ba idanunsa ke masa gizoba wannan shahida ma ta girme mata nesa ba kusaba.

Seda kallo guda zaka mata ka hasko shuru shurunta gami da sanyinta tare da raunin da ALLAH ya mata baiwarsu.

Itama kallonsa tai kaɗan, tare da saurin kauda kanta sabida baiwar kwarjinin da rabbi ya basa na cika idanun mutane.

Cikin dabara ya mannata a saman kirjinsa yana jin wata iriyar nutsuwa tana shigarsa tare da jin tausayinta yana ratsashi.

Da ƙyar ya ƙaƙalo maganar datake bakinsa "Mi aka maki ɗazu?" abin da ya faɗa kenan yana bin saman fuskarta da kallo.

Kirjinta ke faman bugawa tamkar ze faso ya fito, ALLAH ALLAH take ya saketa sabida baxata iya jure yadda kaifin dafin ƙwayar idanunsa ke yawo a jikintaba ga kuma yadda kirjinta ke faman dokawa tamkar ze faso wata iriyar sahihiyar kaunarsa ke sake bijiro mata jitake tamkar ta zauce ta haukace ta lalace akansa.

Cikin sanyi tare da karkarwa take kokarin zamewa daga jikinsa shikuwa yaki bata damar hakan sema sake azabtar da ita dayake kumayi da kaifafan ƙwayoyin idanun nasa.

Jin kamar za,a shigo yasa tai saurin zamewa ta faɗa daki aguje.......................



*Littafin ƊAN MAJALISSA na kuɗine akan farashi mai sauki normal grp 200 vip 500 ta private 1000 gamai bukata seya tuntubi wannan number 08142105218*


*Idan kuma kana bukatar littattafaina dana gama kammala complt *KOBA SO.....da kuma HASKE naira 500 cmplt ɗinsu*


*Idan kuma dukkan littattafaina kake bukata zaka biya naira 1000 anan zan baka sabbi harma da tsofin book ɗina dana gama harma da wanda nake typing yanzu*
74


Murmushi ya sauke a saman kamilalliyar fuskarsa tare da ɗan cije bakinsa kaɗan sa'annan yaja ƙafafunsa yabar part ɗin.
Itakuwa nafisa aguje ta faɗa cikin ɗakin tana jan numfashi tamkar mai cutar asma, hartana ɗan dungurin miemah kaɗan batare data sani ba.
Lumshe idanunta tai tana tariyo yadda tajita acikin lafiyayyen kirjinsa mai uban laushi da ƙamshi.
Cikin wani irin yanayi take lumshe idanun nata ahaka umma sahura ta shigo ta sameta.
Cikin mutuwar jiki ta mike ta zauna tana ɗan ƙaƙalo far'a kaɗan sannan ta dubi umma sahura kana tace.
"Umma se yanzu kika shigo wajan ƴar taki kenan ni wallahi umma senake ganin kamar kin daina sona". takai maganar tana tura bakinta gaba kaɗan.
Cikin dariya umma tace "faɗi ki ƙara nikam yanzu ta ƴar jikalleta nake bata taki ba". tafaɗi maganar tare da saka hannu ta dauki miemah wadda taketa faman cillah kafarta sama.
Dariya itama nafisan ta saki tare da duban umma sahura a karo na biyu tare da ce mata.
"Umma nikam wai ina labarin waleedah har yanzu suna can zaman extention ɗin ni wallahi na matsu na ganta har yanzu shuru mun juma bamu haɗu ba".
Cikin dariya umma sahura ta dube kana tace" aminan juna aiseki jeki kai mata ziyara ai kafin candyn naku yazo". cikin zolaya umma sahura tai wannan maganar amman ita kam nafisa ta dauka gaskene shiyasa tace.
"Aikam umma bara komai yay dai dai wallahi zanje ɗin". takai maganar tana dariya.
"Hmm nikam badani ba wannan katoɓarar"cewar umma sahura ta faɗa tana dariya, tura bakin ta tai gaba tana kallon umma sahura tamkar zata saka kuka!

Cikin haka anty ta shigo cikin ɗakin bayanta wasu matane ƴan gayu na ƙarshe cikin azama anty ta jawo masu wani lallausan carpet suka zauna sannan ta karasa gaban miema ta daukota gami da naɗeta awani shegen tawul mai uban laushi ta mika masu ita.

Itama nafisa saukowa tai daga gadon ta zo gabansu ta tsugunna tana gaisar dasu.
Sun jima acikin ɗakin suna faman ɗaukar miema a camera kafin su masu sallama tare da aje manya manyan bags ɗin da suka shigo dasu.
Har waje anty takaisu sannan tazo
Seda ta dawo take gaya masu cewar matan ƙannan mamaah ne , cikin mamaki nafisa take kallon anty tana kuma jimamin wannan yawa na zuriyarsu amman batace komai ba.

Seda maganar antyn ta katseta akan ta shirya zata leka part ɗin maamah su gaisa da ita.
Cikin nutsuwa umma sahura ta kintsa miemah duk da dai daman can ɗinma yarinyar a shirye take tadai daɗa gyarata ne sosai kana, itama nafisan ta shirya kanta cikin wani pink hijab mai kyau da anty ta dauko mata.
Fita falo sukai suka wuce su gwagwgwaji a yashe da almun baccin gajiya ya kwashe sune.

Daga umma sahura se feena suka karasa cikin part ɗin maamah domin ita anty tuni ta koma sabida bakin data kumayi.
Cikin haɗaɗɗen falon maamah suka shiga wanda ya cika da wani irin azababben kamshi tare da sanyi mai shiga jiki.
Tundaga kofar falon jikin feenah ya soma rawa har suka karasa ciki.

Wasu mata suka tadda zaune bisa carpet ɗin falon. se mama wadda take zaune akan wani irin tum tum tana dauke da casbaha a hannunta kamar koda yaushe.
Kai tsaye gabanta feenah ta nufa umma sahura tana bayanta seda ta nemi gu gaban mamar ta zauna sannan ta dago tana gaisar da sauran matan dasuke zaune waɗanda da alamun abokan arzkine sukazo mata barka.
Umma sahura itace ta soma gaida maamah cikin sakin fuska.
Itama mamar ta juyo fuskarta cikin hasken annuri take amsawa kana ta dubi nafisa da kulawa tana sakin far'a cikin sauri feenah ta rissuna ta soma gaida maamah cikin ladabi da biyayya ganin haka yasa umma ta dire mata miemah akan cinyarta tabar wajan ta koma can kan kujera ta zauna.
Taƙasan idanu feenah take kallon maamah tsananin kamarsu dashi tayi yawa kamar an tsaga kara haka take kama dashi.
Bata sha mamaki ba seda taga yadda mamar ta tsirawa miemah idanu tana kallonta cike da soyayya, itakam feenah mamakin wannan alkunya ta mama takeyi,wadda gatanan akan fuskar matar ta bayyana.
Ahaka shahida suka shigo cikin falon tare da wasu ƴammata se shahid mai bin shahidar shima, ai har ana rige rige wajan zuwa ɗaukar miema wanda daga karshe ALLAH yabawa shahid sa,a ya dauketa.
Cikin murna yake jijjigata yana cillata sama.
Cike da rawar jiki sakina matar imran wadda take shigowa falon tai maza ta nufi wajansa ta karbeta tana dariya.
"Umm yau shahid so kake mukasa gane kan Yaya anwarr kenan ƴar datake da kwana ɗaya jall a duniya kakewa haka" takai maganar tana zama a kusa da nafisa.
"Wallahi anty addu,ar danake kenan ALLAH ya kawo yaya daya ci...."bata ƙarasaba yayo kanta wanda tai sama aguje tana dariya.
Gaisawa sukai da sakina sannan sakina ta mika mata miema ganin tana son tai kuka amman fafur feena taki amsar ƴar sema kauda kanta datai tana tura baki wanda duk abinda suke maamah bata ce masu komai ba, amman cikin ranta murna takeyi tare da godiya ga ALLAH daya hade mata kansu wanda daga gani za,a samu zaman lafiya a tsakanin surukan nata.
Har akai kiran sallar magariba suna part ɗin maamah domin kuwa waɗan nan matan ma tuni sun tafi haka zalika itama umma sahura ta tafi itama sakina haka.
Seda aka shiga masallaci sannan maamah ta mike tare da daukar miema kana ta dubi nafisa gami da bata umarni akan ta biyota.
Haɗaɗɗan falonta na sama suk nufa aƙasan carpet fina ta yada zango itakuwa mama daki tai seda tai sallah sannan ta hada ruwa mai dumi tare da tubewa miemah kayan jikinta ta soma yimata wanka.
Bayan ta gama mata ta shiryata cikin kayan da imran ya shigo dasu ɗazu waɗan da ba,a riga da ankai can part ɗin su anty ba..
Fitowa tai falo tare da miemah a hannun ta anan nafisa tai mata barka da fitowa amsawa tai cikin kulawa, kana ta aje miema akan kujera tabar wajan.
Da kanta taje kicin ta hadowa nafisa kayan abincin tuwo ne tare da farfesu waɗanda sukaji kayan yaji.
Tazo ta aje mata gabanta.
Cikin sauri ta mike tana cewa "lahh maamah aida kin bari na debo da kaina" murmushi maama ta saki tare da cewa "ki zamanki ki huta". wannan kalma tabawa feena dariya dan haka ta koma ta zauna can nesa gami da tsirawa t.v idanu tana kallo.
Ta jima a falon ita ɗaya sannan sega shahida ta shigo cikin falon bakin ɗauke da sallama..
Cike da far,a ta karaso gabanta"anty barka da warhaka nima zuwa nai na raka ƴan school ɗinmu sauri nake naga yaya a compound yana waya kada ya ganni" tafaɗa tana mikewa cike da azama tai cikin wani ɗaki dana gansa gaff da ɗakin maamah wanda da alamun ɗakin tane.
Bayan kamar mintuna uku sega mamah ta kara dawowa bayanta wasu matane waɗanda da alumu ƴan aikintane kayan abinci suka jere a saman daining sannan ɗayar ƴar budurwar ta aje gaushin wuta a gefe sannan sukaiwa feena sannu da hutawa suka bar wajan.
Da ƙyar mamah ta tilas ta mata akan taci tuwon cike da alkunya taja kular da tuwon ke ciki ta bude gami da daukar wani ɗan filat ta zuba tare da zuba miyar wadda taji wadataccen naman rago acikinta se tashin uban kamshi takeyi.
Jawo kular maamah tai da kanta ta ƙaƙƙara mata sosai ta wadata filat ɗin da nama da ishashshiyar miya, ta tura mata gabanta.
"Maza ki cinye ni bansan wannan sakalcin" cewar maamah bayan ta ɗaga rigar miemah tana gasa mata cibiyarta da gaushin wutar.
Cikin alkunya ta furta "nagode" sannan taja tuwon tai bisimillah bayan ta wanke hannunta acikin wani ɗan kwano wanda aka zuba ruwa acikinsa ta soma kai loma bakinta.
Sosai tuwon ya mata daɗi..........



Shikuwa bayan yabar part ɗin anty kai tsaye nasa part ɗin ya wuce baibi takan hidaya ba sabida ta kona masa ransa a ɗazu.
Daki ya shiga ya kulle kansa tare da tube kayan jikinsa ya watsa ruwa kana ya shirya cikin bakar jallabiya jawo system ɗinsa yay yana turawa Aliyu wani ɗan zane ta gmail. dayake so ai masa acikin gidan dayake ginawa, ya jima yana faman aiki akan system ɗin tasa kafin ya mike ya shiga cikin ɗan kicin ɗin dake manne a dakin nasa wanda yake dauke da katon fridge se ƴan tarkacen kayan maƙulashen dake cikinsa domin ba,a girki akicin ɗin.
Coffeee ya haɗa cikin ɗan madaidai cin cup tare da ɗaukar biscut kana yabi ta wata ƙofa wadda ta ɓille babban falonsa wanda yawanci acikinsa yake hutawa.
Masauki ya samawa kansa akan lumtsumemiyar royal ɗin dake falon tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, gami da ɗaukar remote control yana serching channel. tashar kallon ƙwallon ƙafa ya kamo tare da tsirawa t.v idanu yana jin daɗin kallon gefe guda kuma yana kurɓar coffee ɗinsa yana ɗan cin biscut ɗin kaɗan.
Ya jima yana kallon seda aka kira sallar magariba ya mike ya kashe komai na ya mika cup ɗin kicin sannan yabar falon, ta bedroom ɗinsa yabi ya dauki wayarsa ya zira acikin aljihun rigar kana yabude kofar ya fita.
Cikin azama hidaya data gama hadewa cikin wani uban less mai shegen kyau se daukar idanu yake ta karaso gabansa.
"Ranka ya dade inata faman jiranka shuru kuma naje ɗakin ka naji sa a rufe".
Kallon kin rainama kanki hankali yake mata kafin ya ratseta ya wuce.
Cike da zafin nama tasha gabansa tai kalar tausayi tamkar zata kurma ihu! tace "Dan ALLAH my love kai hakuri wallahi bacin raine amman komai ya wuce yanzun ma zuwa zanyi naga bebynmu" takai maganar tana kallon cikin ƙwayar idanunsa.
Batare daya tanka taba ya wuce jin ana kokarin tayar da sallah yabar mata wajan ya nufi masallaci.
Cije baki tai kaɗan tare dajan ƙwafa "anya kuwa zan iya?" murmushi ta saki wanda bai kai zuciyarta ba kana tabar falon ta sauka kasa daga nan tai part ɗin anty.
Koda taje tundaga falo ganin yadda ake baza harkar arziki yasa ta koma da baya tana jin bakin cikinta yana kuma karuwa.
Dahar zata koma part ɗinsu sekuma taga ta riga data gaya masa zata ganin beby dan haka setace bara kawai tai part ɗin mama ta rage zafi acan ɗin.

Falon kasa babu kowa se masu aiki suna faman gyarashi dan haka seta hau sama.

Ciki ciki tai sallamar wadda fina datake ta faman zuba lomarta ta ɗago ta dube.
Cikin sauri tuwon data saka abakinta....




afuwan babu editing

75.

Cikin sauri tuwon data saka abakinta ya soma ƙoƙarin fitowa sabida ƙoƙarin amsa sallamar hidayan datake son tayi.
Da sauri ta bawa tuwon muhalli acikin maƙogaranta kana ta dubi hidaya cike da rashin sanin ko itan wacece sa,annan tace.
"Amin wa'alaikisssalam". kana taja bakin ta tai shuru amman batai gigin sake kai tuwon bakinta ba.
Cike da sanyin jiki da rashin sanin tartibin wacece hidaya ta ɗan saki fuska kafin ta karaso baki ɗaya har ta samu ta ƙaraso gaban maamah.
Cikin ladabi take gaishe da maman wadda take amsa mata itama cike da kulawa.
Ɗanjan gefe tai ta zauna tare da janyo pillow ɗaya waɗan da ke watse a falon ta ɗora akan cinyarta ta ƙurawa wuri guda idanu.
Cikin kulawa mamah ta dubeta.
"Hidaya ga ɗiyar taki naga kamar baki ganta ba, ana gasa mata cibiyane".
Wani ɗan murmushi ta sauke wanda bai kai har cikin ranta ba sannan taja numfashi.
"Wallahi kam maamah ban kula da itaba,abani na ɗauka".
Tafaɗa tana miko hannunta fuskarta kadaran kada hakan.
Itakuwa nafisa wadda baki ɗaya wannan lamari yasakata a kwana takasa gane wacece wannan hidayar sakato tai da baki tana bin kowannen su da kallo.
Seda maamah ta mika mata, miemah sannan ta juyo da kulawa ta dubi nafeesah.
"Maza kici abincin naki mana, kinsa zakuyi wanka anjima, sannan banga kin gaisar da yayar taki ba?".
Takai maganar tana kallon nafeesah.
Cikin daburcewa feena ta kalli maamah sam ita ta dauka ƙanwar sace shiyasa taɗan daburce kaɗan sannan tace.
"Wallahi mamah ina shirin yi kika faɗa dan ALLAH kiyi hakuri, ita a ina take? itama ƙanwarsa ce banga tana kama da shahida ba".
Wata iriyar zuface take karyowa hidaya tsabar takaicin wannan kalamin yarinyar bai barta ta iya ɗaga idanunta ba.
Murmushi maamah ta saki wanda baya gushewa asaman fuskarta.
Kafin tace.
"A,a banƙi ta, takiba nafisah, ƙanwarsa ce itama sunanta Hidaya ɗiyar ƙanina ce, amman a yanzu itace yayarki itace matar sa ta farko, nasan daman ba lallai ki santaba".
Takai maganar tana mai miƙewa gami da ɗaukar kaskon gabanta ta nufi hanyar data ɗeboshi.
Kallon hidaya take ta ƙasan idanunta batare data ce mata komai ba baki ɗay kanta ya kunce.
Lallai daman haka matar tasa take gaskiya babu laifi tana da kyau.
Cewarta kenan akasan ziciyarta.
Itama hidaya kallon ƴar ficiciyar yarinyar gaban nata takeyi wato wannan itace amaryar bogin da ake laƙani da anyi, domin kuwa ta bogice tunda ita haryanzu bata da tabbas akan yes matarsa ce.
Gefe guda kuwa wani malolon takaicine ya dirar mata ta yadda taga yarinyar na mata kallon ƙasa ƙasa takuma kasa gaisar da itan kamar yadda mah ta umarta.
Jitake tamkar ta jefar da jaririyar dake hannunta dan tsabar takaici tare da bakin ciki amman ta danne sabida ta cimma manufarta wadda hausawa sukan ce yaƙi ɗan zamba ne.
Tsintar siririyar muryar nafeesah tai wadda har tana shakking wajan gaisar da ita.
"Ina yini anty dan ALLAH kiyi hakuri wallahi ban shaidaki ba......., bata barta ta rufe maganar ba, taja wani shegen tsaki mtswwwwww!!!
"Aikin banza" takai maganar tamkar wata kububuwa.
Kafin ta kuma yunkurawa tai magana ta biyu suka jiyo sallamarshi.
Da sauri feenah tai kasa da kanta wanda kafin ta ɗago taji kamar mutum a kusa da ita aikuwa idanunta bai mata karyaba.
Domin hidayar ta gani a zaune gaf da ita tamkar abin arziki tana ta ɗaga miemah tana murmushi.
Cikin jin daɗi tare da kyakykyawan zato, ya karaso cikin falon.
Abinda ya hangone ya kuma sanyaya masa zuciyarsa.
Tabbas daman yasan hidaya mai sonshi ce bazata taba ɓata masa raiba ko abinda tai masa ma ɗazu da jiya yasan tsabar ɓacin raine da kuma kishi irin na mata.
"A,a kaga babban maigida barka da zuwa" tafaɗi maganar tana dariya ƙasa ƙasa wadda ta cika da tsabar kirsa gami da makirci.
Imran wanda yake bayan Anwar hannunsa ɗauke da wata bakar leda mai tambarin Ɗawisu gas meat, shi yay saurin karasowa tare da cafkar maganar.
"Yaya akai aini kuma yanzu kin yarda ni da alamun zan sauya sheka" dariya ta saki tare da ɗan matsawa kaɗan tana mikawa imran miemah.
"Karɓi hajiya maamah ka ganemin dan ALLAH wannan badani take kama ba? amman dan tsabar son kai irin na yaya jiya ina jinsa yana waya wai bebyn dashi take kama".
Dariya imran yay sosai yana yaba halin kirki tare da kara irin na hidaya sannan yace.
"Gaskiya kam wannan antyn mu ce tabbas wannan dake take kama". yakai maganar da suffar zolaya.
Awannan karon kowa dariyar ya saki hatta shi mai gayya mai aikin shima dariyar ya saki amman banda.............




*AFUWAN NASO NAI MAKU MAI YAWA AMMAN YADDA KUKA DAMU AKAN NA BAKU YASA NA DAKATA A NAN AMMAN INSHA ALLAH NAN DA ZUWA DARE ZANYI WANI MANAGE*




*ƊANMAJALISSA* NA KUƊINE IDAN KINA BUKATAR SAYA NAIRA 200, katin mtn or airtel vip 500, sp,1000, ki nemi wannan number 08142105218.


Idan kina bukatar dukkan books ɗina dasuke complt guda 7 zaki biya 1000 domin samun dukkan ninsu......👌

76.






Amman banda feenah wadda tsananin mamakin wannan mata ya sakata tai tsuru tamkar wata sakarya.

Surutu falon ya ɗauka, sosai musamman lokacin da sakina matar imran ta shigo se hirar ta kuma ɗaukar armashi, haka zalika shahida ma wadda ta fito daga ɗakinta yanzu jikinta sanye da hijabi wanda da alamun sallah ta idar, itama haka tazo ta zauna a falon tana faman dariya sabida bayyanar imran a wajan danshi kam ɗan shaftane shiyasa duk ƴan gidan suka rainashi.


Shikuwa mai gayya mai aiki baice komai ba tundaga murmushin dayay a farko sedai kuma kana kallon fuskarsa zakaga zallan farin ciki tare da annashuwar murnar kasantuwar sa acikin AHALINSA.

Zuwan maamah yasaka surutun ya lafa wanda daman muryar mutum uku hidaya da imran da sakina ita tafi ɗaguwa acikin falon , domin ita nafisa batace ko ƙala ba haka zalika shima uban miemah bai ko ɗaga idanunsa sama ba bare ya tankawa wani acikinsu.

Murmushi mai kayatarwa maamah ta saki tanajinta acikin matsananciyar murna tare da godiya ga sarki buwayi gagara misali ALLAH kenan AHADUN SAMADUN MAJIDU, wanda ya raya mata dukkan iyalan nata yakuma haɗa mata kansu sannan ya wanzar da haɗin kai garesu tare da farin ciki da zaman lafiya da kwanciyar hankali lallai yabo da godiya su tabbata ga ALLAH maɗaukakin sarki.

Saman wani ɗan matashi mai laushi ta zauna idanunta akan imran tana kallon yadda ya zauna yana faman dariya, koda wasa bata kalli ANWARR ba sema mayar da ƙwayar idanun nata tai bisa kan nafisa wadda tai tamkar ace mata ket ta arce.

Ɗan murmushi ta sauke tare da furta.

"Ki saki jikinki mana kina cikin ƴan uwanki ko zaki koma wajan antyn takune?".
Ta jefa mata tambayar cike da tsantsar kulawa gami da soyayya mai ƙarfi.

Cikin rawar murya wadda ta aro ta da ƙyar tace.
"A,a nan ɗin ma yayi".
Iya abinda ta iya fada kenan sabida yadda takejin kirjinta yana faman dokawa, sakamakon zamansa a wajan wanda ta saka aranta inama baya wajan domin yadda takeji acikin jikin nata.

Cikin danne ɓacin rai hidaya ta dubi maamah tanajin tamkar ta kunna wuta awajan kana tace.
"Kai maamah kema dai tafa saki jikinta ɗazu mun ɗan taɓa hirama da itafa".takai maganar tana dariya wadda tabaiwa fina mamaki.

Sosai maamah taji daɗin hakan hartana shi mata albarka kana ta miqe tai cikin ɗakinta.

Kamar jiranta yake tana mikewa ya take mata baya

Haka zalika suma su imran sallama sukaiwa feenah suka bar wajan itama shahida ɗakinta ta koma.
Waje ya rage daga hidaya se feenah wadda tsabar mamakin barikin wannan mata ya hanata koda motsi.

Wata ƴar ƙaramar shewa hidaya ta saki tare da mikewa tare da saɓa miemah a kafadarta tabar wajan ta nufi ɗakin maamah suka barta ita ɗaya.

Wata kwallar takaicin hakan taji musamman shida ya nuna tamkar bai san da halittarta a awajan ba.

Tagumi ta rafka tana ALLAH ALLAH ace ta koma wajan anty domin acan ɗin tafi jinta a sake, kodan hausawa sunce uwa uwa oho!


Yana zaune gaban maamah ya tanƙwashe ƙafafunsa tamkar wanda yake neman wani abu, tsuru itama tai masa tana mamakin wannan nacin nasa duk da bata sakar masa karewa ma bata yadda wata hira ta hadasu kasancewarsa ɗanta na fari amman ta rasa wannan jarabar ƙwaƙwar tasa shi tun yana yaro yake da ƙulafuci kuma har gobe idan baijishi a kusa da itaba baya jin daɗi.

Tamkar wani yaron goye haka ya zuba mata idanu kafin ya furta.
"Maammah dan ALLAH ko zan samu fura, babu a wajena kuma ni idan ban shaba bazan iya bacci ba".

Ko uffan bata ce masa ba sema kauda kanta tai, tana kokarin tashi daga wajan sukaji sallamar hidaya.

Ɗauke da miemah a hannunta.

Dukkansu sunji dadin yadda takewa miemah musamman shiɗin domin ga farin ciki nan akan fuskarsa ya bayyana ƙarara.

Shifa jiyake tamkar ya dauki hidaya ya goyata sabida tsabar murna domin duk mai son wannan bebyn tasa tofa yagama dashi babu wata kauna daxaka nuna masa a yanxu face ka so masa meimansa.

Zama take kokarin yi maamah ta tare ta da cewa.........
"Hidaya ina kanwar taki naga kin shigo nan?".

bata jira cewarta ba tacigaba.........

"Maza koma wajanta kaima tashi ganinan zuwa kazoma ka rakata can ɓangaren anty taku".
Tafaɗa masu cikin bada umarni.

Murmushi hidaya ta saki tana ɓoye damuwarta aranta.

Dan ita kam ba haka taso ba, taso sun zauna anan ɗin sosai domin tasan hakan ze batawa yarinyar rai ainun.

Sedai hakan ma wata damar ce, dan haka caraf ta miqe tabar dakin zuwa can falon.

Shima baya da zabi face ya mike ɗin.

Akusan tare suka zauna akan daya daga cikin kujerun dake falon.
Dan tsabar rashin kunyar hidaya a kujerar daya zauna anan itama ta zauna duk da kujerar one siter ce amman haka ta ƙwaƙume sa har suna gugar juna.

Miemah ta ɗora a tsakiyarsu tare da amsar wayarsa tafara jera masu hotuna ita dashi da miemah wanda seka rantse itace mai jegon sabida yadda sukai kusan kama da shi ɗin kasancewarsa ɗan uwanta na jini.

Ta ƙasan idanu nafisa ke kallonsu abin na tsananin bata mamaki su basa kunyar wani yazo ya gansu a haka.

Cike da kirsa muryar hidaya ta karade falon.

"Ƙanwata maza taso nai mana vedio nidake da cwt heart da bebynmu" takai maganar batare data matsa daga inda take ba.

Girgiza kanta tai alamun "A,a".

Ɗan tura baki tai gaba.
"Ahhhh yayah love kagafa Nafisa wai batta so dan ALLAH kace tazoooooo" taja maganar cike da salo.

Lumshe idanun sa yay sabida kasalar data soma saukar masa sabida yadda take goga jikinta anasa cikin ƙwarewa wadda tai amfani da ita danta karya masa dukkan wani kuzari nasa.

Batare daya tanka ba.

"Yahhhhhhhhhhhhhh" taja maganar sosai.

"Pls kibarni hakannan ita tajiyo kartayi mana".abin da ya faɗa kenan muryarsa tana ɗan rawa kaɗan sabida yafara fita daga notice ɗinsa.

Sarai feenah taji abin da yace amman hakan bai saka ta ɗago koda idanunta bane ba sema sake yin kasa da kanta datai tana ayyana.
Dama duk wanda yasai rariya ai yasan zata masa yoyo.
Tafadi hakan cikin ƙasan zuciyarta.


Cikin ƙwarewa hidaya takai hannunta gefen wuyansa tana ɗan shafowa kaɗan "My yanajin tem ɗin jikinka ta sauya?" bata jira cewarsa ba tafara yawo da hannunta zuwa saman wuyansa, caraf ya rike mata hannun yana lumshe mata idanu, abinka da anjima ba,a haduba.

Sosai wannan lamari ya baiwa feenah mamaki lallai ta yarda ba kowa keda kunya a rayuwansa ba jibi abun da suke.

Ita kuwa hidaya tai hakanne domin ta cisgunawa feenah ta baƙanta mata ranta.

Cikin haka sukaji mama na kokarin fitowa wanda hidaya batai koda gezau ba se shine yay saurin tashi.

Ƙarasowa tai cikin falon.

"Hdaya maza jeki kicin ki dama masa fura kinsan baison ai masa blanding".

Sannan ta dubi nafisa "tashi karbeta kuje ya rakaki can ɗin seda safe.....



NAKUƊINE 08142105218
200naira

*77*


Maamah tafaɗi hakan cikin bayar da umarni.
Wani takaicine ya kama hidaya sam bata so maamah tai mata hakan ba, cikin zafin zuciya ta mikawa nafisa miemah tare da nufar hanyar kitching.
Ita kuwa maamah juyawa ciki tai abinta.
Nafisa sakin baki tai rike da miemah ahannunta sam ta kasa koda motsi.
"Muje mana".
Taji saukar muryarsa akanta.
Firgigit! ta ɗago kanta nan ta hangosa harya kusan kaiwa step.
Cikin sanyin jiki tabi bayansa,kafin ma tai wani yunkuri harya sauka falon kasa, mamakin zafin namansa tai ace mutum kamar iska daga tafiya harya kai.
Cikin tunanin hakan ta sauka falon ƙasa.
Abakin ƙofar dazata sadaka da hanyar compound wanda ze kaika ragowar part's ɗin gidan anan ta tarar dashi a tsaye yayi folding hannunsa, harta ƙaraso bai motsaba.
"Kekam narasa irinki wallahi kincika ganda".
Yafaɗi hakan yana kokarin amsar miemah daga hannunta.
Baki asake bata iya bashi amsar komai ba,haka ta miƙa mashi ita

Please Login or Register in order to submit comment