Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kukanta fitowa fili yake ita tana nan tana shan ac ɗiyarta na can cikin bala'i rungume juna sukai cikin so da ƙauna suka cigaba da kukansu.

har zuwa wani lokaci kafin anty ta mike ta zubo mata farfesun data zo mata dashi har wajan karfe ɗayan dare suna hirar yaushe gamo sannan anty tai mata sallama ta wuce ɗakinta.

Nafisa kam ta jima batai bacci ba gani take tamkar a shirin film ALLAH kenan mai yadda yaso a lokacin daya so ya jarabceta da ƙalu bale kala-kala daga karshe kuma yazo ya warware mata shi acikin sauki.

Ahaka wani bacci mai daɗi yay gaba da ita.

Amman cikin dare ƴar jaririyar tace bata san zance ba haka ta dinga rigima wanda tsabar tsotso bai bar nafi ta rintsa ba.....


IN KUNGA ERROS KUMIN UZURI🙏🙏🙏
72


Tun nafisa tana shayar da ita cikin kulawa hartazo ta fara ƙosawa sabida babu laifi yarinyar masha ALLAH badai tsotsoba.

daga ta juya seta kuma saka ihu haka nafisa tai ta faman tura bakinta gaba tamkar wani na wajan tana ayyana daman haka iyayenmu mata, suka sha wahala damu lallai jinjina ga mahaifiya.

Seda Anty ta shigo ɗakin jin kukan yay yawa, tare da ɗaukar jaririyar ta zura mata harshenta a kunne tana hura.mata aikuwa nan da nan tai shuru har bacci yay gaba da ita.

Juyowa tai ta dubi nafisa kana tace, "Kingafa kume take cikinta gaya nan ya kumbura kekuma se ɗura mata nono kike". tafaɗa tana miko mata yarinyar tare da barin ɗakin.

Kwantar da ƴar tai akan ruwan cikinta tana shafa bayanta.

Ahaka wani wawan bacci ya kwasheta, batare data farkaba seda asubahi lokacin anty ta kuma dawowa ɗakin ita dai mikawa anty ɗiyar tai sannan ta koma baccinta.


Goyota anty tayi tare da barin ɗakin dan nafisa ta samu ta ɗan runtsa.

Shikuwa anasa ɓangaren baƙaramin bacci ya samu jiyanba, dan yau yama so ya makara a sallar asubahi.

Cikin sauri ya shiga bathroom ya watsa ruwa sannan ya zira jallabiya ya wuce masallaci.

Bayan an idar da sallah a ƙa'ida yana zuwa wajan maamah ya gaisar da ita amman yau bai iya zuwa ɗinba kansa tsaye part ɗin nasa ya koma.

Ɗakinsa ya shiga tare da tube jallabiyar jikinsa sabida akwai wani aiki dayake son yaje ya gano wajan karfe bakwai.

Shirya kansa yay cikin wani milk ɗin yadi mai yankan sukari, tare da murza dakakkiyar hula wadda ta zauna akan nasa tai ras.takalmi da agogo masu yanayi da shigar jikin nasa ya saka tare da fesa turare mai daɗin kamshi.

Dayake da oska da p.a zasuyi wannan tafiyar shiyasa bai dauki makullin motaba haka yaja, kafarsa yabar ɗakin yana zuba uban kamshi.

Ɗakin hidaya ya wuce kai tsaye, sallama yay mata a bayyane, amman bai sami arzikin koda amsa mata ba balle ya saka ran gaisuwa.

Cikin mamaki da danne abun acikin ransa yaja stool ɗin madubi ya zauna gaf da kafarta.

Tana zaune akan gado cikin shigar kayan bacci masu santsi kanta ko ɗan kwali babu rike da wayarta wanda daga gani kasan chart take.

"Amincin ALLAH ya tabbata agareki".
Yafaɗi maganar cike da kulawa.

Ya tsine fuskarta tai alamun ko ajikinta kana ta juya masa baya tare da ɗaukar pillow ta rumgume batare data tanka masa ba.

Sakin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya yayi tare da danne ɓacin ran daya taso masa sannan ya kira complete name ɗinta.

"Amina magana nake maki tun jiya kinyi min banza kinsan ni arayuwata bana son irin haka ai wannan ma rainin wayone".
Yakai.maganar yana jan ajiyar zuciya da sauri.

Juyowa itama tai cike da rashin kunya gami da fitsara tare da furta..........


"Ahayee su rainin wayo manya ai kaine babban ɗan........"Amina!!!!!!!!!!!!!! ya kira sunanta da karfi tare da mikewa tsaye ya daki bangon ɗakin da karfi.

"Niba lusarin namiji bane ba kirike wannan aranki wallahi ki kama bakinki tun kafin ki tsinci hakoranki a zube".!

Yakai maganar ilahirin jikinsa yana faman rawa.

Tsit tai tana zaro idanu, cike da zafin rai ya fice fuwww! yabar mata ɗakin.

"Aikin banza aikin wofi ai wallahi zaman lafiya babu shi acikin gidannan ba dai ni za,a yaudara ba muzuba nida kai har itama tsakuwar dakake ƙiƙirarin matarka ce wallahi sena hana kowa sakat".

Takai maganar tana kuka! jefar da wayar tata tai ma baki ɗaya tai ruf da ciki tana gunjin kuka!.

Kamar ze tashi sama haka ya nufi part ɗin mama babu kowa a kasa sabida safiyace dan haka ya wuce sama.

Ɗakin baccinta ya nufa kai tsaye sallama yay a kasan ransa.

Mama wadda take zaune kan sopa da kur'ani a hannunta ta juyo ta dubesa tare da amsa sallamar tasa.

Tsugunnawa yay ya gaisar da ita cike da ladabi tare da ɓoye damuwarsa.

Itama amsa masa gaisuwar tasa tai gami da binsa da kallo tana noticing ɗinsa.

Bai tsaya ma sosaiba sabida yana sauri dan haka ya tashi yay mata sallama yabarta da tunani tare da auna damuwar data gansa aciki.

Da har ze nufi parking space sekuma, ya juya zuwa part ɗin anty.

Tun daga bakin kofar daze shiga falo yakejin kukan yarinyar har wani canyara taka kuma yi.

Jikinsa na tsananin rawa tamkar ze fadi ya nufi cikin ɗakin dayake jin kukan nata bayan ya shigo cikin falon baki ɗaya.

Sallama yay Anty wadda take zaune tanawa bebyn wanka ita ta juyo tana amsa masa sallamar tasa.

Gaishe da Anty yake amman idanunsa da hankalinsa yana kan ɗiyar har sanda anty ta cirota daga bahon, tare da naɗeta a towel, tare da miko masa ita, tana cewa karbeta karka ƙwarar dani tafadi hakan tana dariya tare da daukar ruwan tabar masa dakin.

Ɗagota yay tare da ƙura mata idanu yana kallonta cike da so da ƙauna.

Tunda yake baita ɓa ganin kama da kama sak kamar shi da yarinyar tasaba.

Sakata yay a kafadarsa yana kiran sunanta daya saka mata shi ɗaya "Miemah tah" ki bar kuka dady bai so" haka yaketa faman fadi tare da rungumeta amman fafur taki shuru wanda da alamun fa wannan ƴar yarinyar acicice.

Ahaka nafisa ta fito daga toilet jikinta ɗaure da guntun towel tare da ɗan mitsitsi akanta.

Ko kallonsa batai ba taɗanja tsaki akasan ranta kana tai gaban madubi tana kokarin jayo hijabi.

Shikam binta yake da kallo tundaga kanta har zuwa kafafunta...........!



*AFUWAN AFUWAN AFUWAN*🙏🙏🙏


_TABBAS MUNA TAMU SHI KUMA ALLAH YANA TASA, AMMAN TA ALLAH ITACE GASKIYA, WALLAHI BAN TSARA WANNAN LABARIN ZE KAI MIN BAYAN AZUMI BA AMMAN TUNDA ALLAH HAKA YA TSARAN BABU YADDA ZANYI, DA WANNAN DAMAR NAKESON IN BAWA MASOYANA MASOYAN WANNAN LITTAFI HAƘURI,ABISA JINKIR TASHI DAZANYI HAR ZUWA BAYAN SALLAH IDAN ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI YA KAIMU DA RAI DA LAFIYA, KU SANI INA MUKU TANADI ACIKIN WANNAN LABARIN TAFIYAR MIKAKKIYACE WADDA BATA DA KWANA BANA SON NAI MAKU KODA TSALLAKEN KALMA GUDANE NADA CIKIN WANNAN LABARIN SABIDA HAKA KUYI HAKURI AKWAI ƘURA A SHAFUKAN GABA WAƊANDA SE MAI HAKURIN BINA NE KAƊAI ZE GA ƘWAL UWAR DAKA_ !!! 👊
73

*Dubun godiya ga ALLAH ubangijin halitta daya bani damar sake dawo maku da cigaban wannan littafi ya ALLAH kabani ikon kammalasa lafiya amin*

_Inayiwa ɗaukacin musulmi barka da sallah ya ALLAH ya karɓi ibadunmu yasa muna cikin bayinsa ƴantattu amin_

*Masu fidda min da littafi waje kuji tsoron ALLAH kudaina domin harga ALLAH kuna shiga hakkina kuma duk wadda ta karanta min littafi batare data biyaba taje na barta da ALLAH*

                          ********

Ɗan kauda kansa yay kaɗan yana mai lumshe mayun idanunsa tare da sake matse ɗiyar tasa asaman kafaɗarsa,yana kuma jin kukan! yarinyar har cikin ransa.

Itakuwa nafisa yitai tamkar bata san ALLAH yay ruwan halittarsa ma a wajanba.

Cikin hukuncin ALLAH ta samu ƙaton hijabi wanda ya rufe mata dukkan jikinta, ta tafka tare da jawo kujerar gaban madubi tana kokarin zama akai.

Duba agogon hannunsa yay tare da ɗan jan tsaki kaɗan cike da jin haushi.
Yaja gyaran murya tare da furta.
"Malama bakkijin miemah tana kuka! ne?".
Yay maganar cike da muskilanci tamkar yana magana da wani cannn......,.

Sarai ta jisa amman setai mai kunnen uwar shegu, ma,ana tama juya tare da ɗauko cream zata fara gogawa a fatar jikinta.

"Naanah! kada na kuma mai mai ta maki miemah tana kuka!".yakai maganar a kaushashe.

Jin saukar muryarsa mai ɗan sauri bisa cikin dodon kunnenta yasa taɗanji tsoro kaɗan tare da ɗan ɗago wutsiyar idanunta taɗan saci kallonsa kaɗan.

Sannan ta aje man hannun nata sannu a hankali ta tako kafafunta har zuwa gabansa tana ɗan tura baki gaba kaɗan.

Awulakance ta saka hannu ta dafe bayan yarinyar ma,ana tana son ta dauketa.

Wani kallo ya watsa mata wanda babu shiri tai saurin saita kanta tare da maida hankali wajansa ta amshi yarinyar ta nufi gaban gado da ita tana jin kamar tai ta dukanta sabida haushin data bata yarinyar akwai ci masha ALLAH.

Zama tai abakin gado tare da ajeta sannan ta gyara cikin hijabi take kokarin zirya bebyn dan ta samu ta bata abincin nata.

"Malama kada ki zurmuƙamin ɗiya cikin wannan katon hijab sallon kimin asarar ta".

Taji saukar muryarsa yana tsaye idanunsa manne bisa screen ɗin tafkekiyar wayarsa yana kallo sam bazama ka ɗauka yana kallonta ba.

Tura bakinta tai gaba tare da ɗan janye hijabin nata kaɗan sa'annan ta saita kan yarinyar tare da fara bata abincin nata.

Cike da zalama yar ta cafki maman ta soma sha babuji babu gani, ita kuwa nafisa rintse idanunta take tana faman cije bakinta sabida wata irin azaba data keji acikin ƙirjinta sosai takejin zafin yadda yarinyar ke tsotsar jikin nata.

Tari miemah ta soma alamun ta ƙware cike da zafin nama naga mai girma mas! ya mayar da wayarsa cikin aljihun rigar yadin jikin nasa har yana tuntube wajan ƙarasowa wajansu.

Hannu na rawa ya kai jikin nafisa ya ɗago miemah yana bubbuga bayanta sosai take tari seda gyar yasamu tarin ya lafa, cike da masifa! ya juyo yana mai kallon feenah da manyan idanunsa tare da ɗan cije laɓɓansa na ƙasa batare daya ce mata komai ba ya dire mata miema akan  cinyarta yabar ɗakin sabida yadda yaji wayansa yana faman ringing! ko ba,a gaya masa ba dai yasan su oska da p.a ne suka karaso suna jiransa akan fitar dazasu yi.

Cike da mamaki ya ƙarasa wajansu oska akasan ransa yana ayyana anya baze nemi wadda ta ƙware a raino ba domin yana kallon yanayin sanyi wannan yarintar tamkar bazata iya wani abun kirki akan ɗiyar tasaba.( kuji fa ).
   

Cikin girmamawa oska ya rissina yana gaisar da uban gidan nasa kafin ya mike ya nufi bayan mota domin ya bude masa.

Shima p.a rissunawa yay tare da furta "barka da safiya mai gida, yaya kwanan mammarmu?" batare da walwala akan fuskarsa ba ya furta kalmar,"Lafiya". abinda ya iya fadawa p.a kenan tare da zira hannunsa cikin aljihunsa yabar wajan.

Cikin tararrabi p.a yaja jiki yabi bayansu, akusa da oska ya zauna shikma mai girma mas! abayan motar ya samu wajen zama ya baje yana kwasar raɓa, tare da ɗaukar wayarsa ya shiga cikinta yana danne dannensa wanda rabi akan duba wasu ayyuka da aka turo masa yanzun yake.

Har suka ƙarasa cikin yalwar ɗawisu bai ɗago fuskarsaba kasancewar motar mai tintack ce wannan dalilin yasa babu wanda yasan da zuwan sa cikin wannan anguwa.

Gangara motar oska yay har cikin gidan yarin na yalwar ɗawisu wanda mai girma mas! ya bawa kamfanin A.A.SALIHI constract kwangilar ginin wasu sabbin ɗakunan guda, ashirin sabida ƙarancin ɗakunan da mazauna cikin gidan ke fama dasu.

Cike da azama shugaban gidan, ya ƙaraso wajan motar su mai girma mas! wadda ta kasance ita ɗaya jall sabida wannan fitar ta musamman ce shiyasa bai sanar da excort ɗinshi ba.

Da sauri shugaban wajan ya saka hannu ya bude masa motar tare da jada baya yana rawar jiki.

Seda ya dauki mintuna kusan goma sannan ya soma zuro da kafafunsa kafin daga bisani ya fito baki ɗaya.

Batare da jin shiɗin mai mukami bane ba ya mikawa Alhaji atiku, shugaban gidan yarin hannu sukai musahaba, sannan Alhaji atiku yay masa barka da samun karuwa kana suka jera su huɗu har zuwa cikin, ɓangaren sabbin ɗakunan da aka gama aikinsu a jiya ranar sallah kenan.

Cikin jin dadi Alhaji atiku yake zagayawa da mai girma mas! wajan wanda tuni Anwarr ɗin ya soma ware idanunsa yana bin wajan da kallo sabida yadda wajan yay masa mugun kyau bai taɓa baiwa wani kamfani aiki yaji dadi ba tamkar na A.A.Salihi sabida anmasa har abun da yafi wanda yace ɗin.

Cike da jin daɗi ya dubi oska, "Kai gaskiya osk naji dadin aikin nan wallahi nikam bantaɓa jin daɗi aiki tamkar wannan ba". yakai maganar yana kuma duba manyan kofofin  da aka zuba waɗanda suke tamkar na glass da glass.

Cikin rawar jiki oska ya furta "tabbas mai gida ai Alhaji ALIYU (  RABON WANI  ) tsayayyen mutum ne sosai yake tsaye akan dukkan aikin da aka baiwa kamfaninsa mutum ne jajurtacce tsayayye yadda ka ganka" oska yakai maganar yana dariya, shima Anwarr ɗin dariyar yay amman marar sauti sabida bakaramin dariya oskan ya basa ba.

Sun ɓata lokaci sosai anan ɗin kafin suyi sallama su kuma ɗaukar hanyar sabon garin ɗawisu domin kaiwa kamfanin sardauna mamayar aikin daya basu batare dasu ƴan sardaunan sun sani ba.

                         *********


Cikin takaici ta mike ta nufi gaban madubi tube hijabin jikinta tai tare da ƙarasawa bakin gado.

Ta dauki wata yalluwar atamfa wadda anty ta kawo mata ta saka, riga da zani ne seda ta soma saka under wears kafin ta soma saka rigar wadda tai mata ciff sabida nafisa bamai jiki bace ba.

Ko ɗaurin kallabi batai ba ta koma wajan miema ta zauna tare da saka hannu ta zabga tagumi acikin ranta take mamakin halin mutumin nan gaba ɗaya lamarinsa mamaki yake bata tunda ta haihu yake mata faɗa ai koda ace miema badaga jikinta ta fito ba ai baxe dinga mata wannan faɗan, shi ko tausayinta ma baiji kenan.

Rintse idanun ta tai waɗanda ruwa yaɗan tarar masu kaɗan sannan ta furta "seda so ake tausayi" takai maganar cikin jin tausayin kanta tare da ɗago ɗiyar tata ta tsira mata idanu tana kallon tsantsar kamaninta da shi,  afili ta furta "ALLAH yasa kada kiyo faɗan abbanki" takai maganar tana ɗan jan laɓɓan yarinyar waɗanda suke jajur dasu tamkar an saka jan baki.

Sallamar shahida ta saka tai saurin janye yar daga cinyar cikin sauri sabida kunya tare da jan kallabinta tabar wajan ta nufi can bakin madubi tahau dube duben rashin makama, muryar shahida wadda take faman gaisar da ita itace ta katse mata tunanin nata.

"Maman miema barka da safiya yaya kwanan miemarmu?" shahida ta faɗa tana dariya gami da daukar miema wadda take faman cilla kafa sama zatai rigima.

"Lafiya ina mama dafatan tana lafiya?" cewar nafisa cike da kunya, zama shahida tai akan gadon tare da bata amsa "tana lafiya Alhamdulillahi tace ma na gaisar dake sosai kafin ta shigo". cewar shahida wadda taketa faman kallon ɗiyar yayan nata.

Ahaka anty aisha nurse wadda zuwanta kenan itama tayo sallama cikin ɗakin, wadda take tare da yayar mammah tare da matar dr ƙanin mammah, cikin alkunya wadda ta rasa inda zata saka kanta ta karaso wajan suka gaisa sannan ta koma can kurya bayan shahida ta zauna cikin rashin sabo dasu.

Tamkar kace mata ket ta arce daman can ita feena bamai son shiga jama,a bace ba.

Babu abinda take faman haɗawa se zufa haka ta zauna tanajin hirar ƴan uwan mai girma mas! ɗin dasuka zazzauna waɗanda yawancin ƴan uwan mammah ne mahaifiyarsa wanda taga kama tamkar an tsaga kara.


Ahaka suma su umma sahura suka shigo ɗakin tare da matansu baffa harma da kaka waɗanda sukai tamkar kace masu ket suma su arce bakaramin mamakin gidan suke ba watakan akwai gidaje kamar waɗan nan a duniya.


Koda suka zauna acikin ɗakin sosai suke mamakin yadda wai wannan ɗakin ƴar fulani ne matar kabiru, lallai inda ranka kasha kallo yanzu ƴar nafi ce take auren ɗan majalissarsu yarinyar da suka ɗauki karan tsana suka ɗorawa amman ita ALLAH ya daukaka haka.

Kafin wani lokaci masu aikin anty sun shake gaban kowa da kayan sanyaya maƙoshi tare da snacks waɗan da tuni ɗakin ya kaure da kamshin kayayyakin.

Cikin nutsuwa nafisa ta karasa gaban umma sahura tamkar zata shige mata cikinta take gaisar da ita kafin ta juya wajan kaka dasu inna hanse matansu baffa dukkansu ta gaisar dasu waɗanda suka zuba mata idanu tamkar wata tauraruwa.

Kaɗan-kaɗan suke hirar su da umma sahura wadda tsananin shakuwarsu tai yawa da nafisa, ahaka anty ta shigo cikin ɗakin bayanta,su zuby da afra ne waɗanda akaiwa shiga ta kaya iri ɗaya, da kallo feenah tabi ƙannen nata tana mamakin yadda taga suna ɗan yanayi da yaran musamman zuby wadda hatta sanyin nasu kusan iri gudane ma.

Hannunta ta saka ta jawo yarinyar wadda a dubara nafisa tabar ɗakin da zuby rike a hannunta sabida daman jinta take a takure.

Ɗakin anty zuby takai feena tana ɗanyi mata surutu kaɗan-kaɗan zama sukai akan sopa ahaka wani bacci mai ma,ana ya dauke batare data shirya ba.

Acan ɗakin kuwa sosai ya cika da ƴan uwa da abokan arzikin dasuketa zuwa barka amman sam basuga mai jegoba, wadda suka samu labarin tai bacci a ɗakin anty daga bakin zuby wadda ganin feena tai barci yasa ta baro ɗakin.

Dangin anty waɗan da sukazo daga rugar ɗawisu, sune suka sauka yanzun nan waɗanda suka yada zango a babban falo suna huce gajiyar da suka kwaso.

Cikin zumuɗi anty ta shige cikin dangin nata itama tana mai jin dadi acikin zuciyarta marar misaltuwa, matar hammanta wanda suke ciki guda ita ke dauke da ƴar jaririyar a hannunta tana gasa mata cibi, gabansu kuwa ancika sa da kayan ci dana sha.

Ahaka su kaka da matan kawu, suka fito daga ɗakin sukayo falon anan fa aka soma kallon kallo a tsakanin dangin anty da matan kawu, atake anan kaka ta saka kuka! tana mai bawa dangin anty hakuri, sekuma hira ta ɓarke tamkar babu abinda ya faru sabida saurin fahimtar junan data faru a tsakaninsu.

Anty ce ta koma ɗakinta ta tarar da nafisa kwance tana faman bacci, tada ta tai tare da haɗa mata ruwan wanka kana, ta fiddo mata da kayan dazata saka, cikin jin dadin yadda mahaifiyar tata ke bata kulawa ta faɗa bayin tana kuma godiya ga ALLAH.

Ita kuma anty cikin ranta tana kuma ayyana yadda zata baiwa nafisa kulawa sosai sabida yadda ƴar tata take bata tausayi domin sam ita bata samu kulawa ta mahaifiyaba shine yasa yanzun take kwatan ta mata.

Harta fito anty na ɗakin seda ta soma kiciniyar saka kaya sannan anty tabar ɗakin.


Cikin sanyinta ta kammala shirin nata tare da zira slippers ta fita zuwa falo.

Sosai jikinta yahau rawa idanunta ya kawo ruwa tana dafe zuciyarta ganin yadda dangin mahaifiyar tata suka cika wajan tare da dangin mahaifinta.

Ahaka ta karasa gwagwgwaji matar hamman anty ita ta aje jaririyar akan cinyar wata matar kawun anty ta mike da azama zuwa wajan feena tare da rungumeta tana sakin hamdala tofa anan fillancin ya motsa domin sosai, falon ya karade da murna kowa ka duba farinciki fall aransa idan ka cire matar kawunta wadda daman can bata kaunar nafisan.

Bayan komai ya lafa anan kowa ya hau cika cikinsa da kayan abincin da masu aikin suka jajjera.

Itakam gwagwgwaji miƙewa tai tsam rike da miema a hannun tare da kamo hannun nafisa tai ciki dasu.

Abakin gado ta aje miema tare da sakin hannun nafisa sannan ta koma falo tare da shigowa da wata babbar jaka, wasu kayayyaki ta fiddo sannan tai cikin toilet da kanta ta kuma haɗa wani ruwa a baho sannan tayo waje dashi, ta dauko wani ƙullin magani tare da wani ruwa a gora ta juye acikin bahon sannan ta ɗauko miema ta tube mata kayanta ta tsomata cikin ruwan.
Aikuwa miema ta tsanyara ihu! "Yimin shuru dole mu tsuma ku da maganin tsari wannan sakon tundaga baffankune".mijinta kenan yayan anty, sosai ta ma miemah wanka ta naɗeta a tawul sannan ta dauke ruwan taje ta zubda.

Itakam nafisa bata ce komai ba kuma batai gigin daukar miemah ba sabida itafa rigimar wannan yarinyar ta soma isarta.
Ahaka gwagwgwaji ta fito tare da ɗaukar miemah tana jijjigata sannan ta fita waje da ita.

Bayan kamar mintuna biyar ta kuma dawowa tare da shigewa toilet ɗin.

Nafisa ta ƙwalawa kira tare da umartarta akan ta shigo cikin toilet ɗin.

Wani irin ruwa mai ɗan zafi kaɗan ta haɗa mata tare da zuzzuba magungunan sannan ta fice tabar nafisa bayan ta bata umarni akan ta shiga cikinsa sosai ya ratsa mata ƙasanta.

Cikin tsoro feena ta shiga cikin katon bahon bayan ta tube sutturar jikinta kuma sosai taji ruwan yana ratsa mata jikinta sannan kuma tana jin dukkan nukurkusar da kashinta ke mata na gajiya babu.

Takai kusan mintuna talatin sannan ta ɗauro tawul ta fito, daga toilet tana kuma fitowa taga katon kaskon wuta wanda aka cikashi da garwashi a tsakar ɗakin saman tiles yana faman ruruwa.

Tsorone ya kamata ganin ana kuma gasawa miema cibiya ganin gwagwgwaji bata kulata ba yasa taja hamdala sannan tai gaban wadrov ɗin anty.

Jin muryar gwagwgwaji tai akanta tana cewa kada ta saka kaya tazo ta shiga cikin zani ta turara jikinta har ƙasanta maganin tsarine tare dana sanyi sannan kuma yana gyara mace.

Zaro idanun ta tai waje cikin tsoro ta karaso kasancewar nafisa yarinya mai biyayya da alkunya sam bata da musu a rayuwarta amman bada ban haka ba da baxata je gaban wutar nan ba.

Hawaye ta share a fakaice sannan taja kaskon ta tsugunna tanajin yadda zafin wutar ke ratsata tare da hayaƙin maganin mai hade da kamshin turare kaɗan.

Jin muryar gwagwgwaji tai akanta tana faman mita "Keko am nafisa bakya magana ne hala?" itakuwa nafisa tana cikin zani tana faman haki da dafe kirji tare da zubda hawaye sam ta kasa magana ma bare tai yunkurin wani abun har gwagwgwaji ta gama shirya miemah kana ta yaye zanin tana bin nafi da kallo.

"Kekam wace irin ɗiyace ai tun ɗazu ya gama konewa amman baki fitoba jiba fuskarki yadda tai jajur" tafada tana mamakin halin wannan ɗiya sannan ta dauke gaushin tabar dakin.

Da ƙyar feenah taja ƙugunta zuwa wajan wadrov ta dauko zani ta daura ta zame tawul ɗin tare da zama abakin gado tana faman haki.

Bata jin zata iya koda daga yatsanta sabida azabar yajin da idanunta da kirjinta ke mata, ga fuskarta tai jajur abin tausayi.

Gwiwarta ta sauko ƙasa tare da kifa kanta a saman gadon miema kuma na gefe tana faman cilla kafa sama.

Ahaka taji wani mayataccen kamshin turare ya kunno kai cikin ɗakin wanda take tunanin a wajan wanda ta sanshi.

Shikuwa mai girma mas! harya karaso cikin ɗakin sallama dauke a bakinsa, baiji ta amsa ba, daman dawowarsa kenan shima duk acikin gajiya yake amman nacin son yaga miema yasa ya kasa daurewa seda ya biyo ta nan ɗin.

Koma part ɗinsa baije ba amman ya tsaya afalo sun gaisa da ƴan uwan anty wanda yaji dama bai biyo tanan ɗinba sabida kunyar dayaji ta kamasa ganin yadda suke binsa da kallo musamman dangin baban nafisa waɗanda basu taɓa ganin saba seyau inda ba ajikin pasta ba.

Ta kalman ƙafafunsa ya tube da kansa cikin sanyin jiki ya tako ya karaso cikin ɗakin.

Akusa da nafisa ya ɗan zauna kaɗan a gefen gadon tare da daukar miemah yana cillawa sama sannan yay saurin komawa ƙasan carpet ya zauna sabida yana jin babu ɗa'a ya zauna a gadon surukar tasa, sam hakan bai dace ba a tarbiyarsu.

Ganin tamkar bata san da wanxuwarsa a ɗakin bane ba yasa yaja gyaran murya kaɗan tare daɗan saka kafafunsa ya gogi jikinta.

Firgit ta ɗago tare da kallonsa da jajayen idanunta waɗanda shi kansa seda suka basa tsoro.

Ɗanja baya yay kaɗan cikin ƴar basarwa ya dubeta "Mike damunki?" abinda ya iya fada mata kenan tare da maida kallonsa ga miemah.

Cikin jin haushin abinda ya mata ta mike tana dafe ƙugunta harta karasa gaban wadrov ta jawo doguwar riga tare da ƴan tarkacen su pad tai bayi.

Shikam dariya ya guntse kaɗan tare da furta "Raguwa" sabida yaga alamun kamar daga wanka take babu mamaki ko taji ruwane yasakata hakan.

Harta fito wannan dariyar bata bar kan fuskarsa ba "Sannu ALLAH kare gaba". abinda ya faɗa mata kenan tamkar bai damu ba.

Tura baki tai gaba tare da ɗan gunguni kaɗan sannan tabar masa ɗakin ma baki ɗaya.

Shikam mamakin halintane ya kamasa ita watakan haka ALLAH yayota bata magana kamar bebiya, kujifa har kura ce zata cewa kare maye.

Yafi karfin mintuna goma yana wasa da ƴarsa sannan ya mayar da ita kan gadon yana kokarin barin

Please Login or Register in order to submit comment