Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki take sanar dasu cewar mai jego tafa farka.
Cikin murna Anty wadda daman bata zauna ba, ta nufi ɗakin bayanta kuma umma sahura dasu, kaka.
Zaune suka tadda ita a bakin gado jikinta sanye da doguwar riga redmate wadda oska yazo dasu.
Cikin nutsuwa Anty ta nufeta tare da rungumeta tana mai sakin kuka!.
Cikin rashin fahimta feena take duban Antyn, batare data iya furta koda kalma guda ba.
Ilah idanun ta dake rarrabawa tana binsu da idanunta, kafin kuma komai ya soma dawo mata daki-daki.
Tasan dai a masallaci ta soma naƙuda, kuma wannan matar data rungumeta yanzu ita ta taimaka mata, kuma tundaga nan bata kuma sanin komai daya faruba.
Shafa cikinta tai taji wayam da sauri taɗan zame jikinta, daga Anty tare da tsirawa umma sahura idanu cikin tuhuma.
Maganar kaka ita ta saka kowa ya soma magana kuma.
"Haba kekuwa nafi baki ganemu bane kin zubawa kowa idanu tamkar wata wawiya".
Muryar sakina matar imran ita ta sauka a bayan ta kaka.
"Haba iya kimata ahankali mana, shahida mikamata bebyn ta ganta dan naga alamun yadda take baza idanu".
Anan kam kowa seda ya dara amman banda nafisa wadda komai ya tsaya mata, kallon shahida take cikin mamaki wannan ai kwanaki ta ganta a wani plaza, kuma tasan dai daga cikin familyn sa take tomeya kawota nan.
Saukar ɗiyarta akan cinyarta shine ya dawo mata da hankalinta,.
Inda Anty ta kuma gyara mata ita cikin so da ƙauna.
Kasa daurewa dai Anty tayi seda ta kamo zuby ta ɗorata akan cinyarta.
Sannan ta dubi nafisa, "Kinsan wannan?".
Ta nunawa feenah zuby.
"A,a" tafaɗa cikin rawar murya.
Cikin sauri kuma umma sahura ta nufo anty, "Kinga hafsatu kibari har mu.koma gida yanxun bazata gane komi ba".
Da wannan Maganar yasa anty yin shuru.
Inda kuma ta bar nafisa da kallon zuby, wadda su shahida suka zo da ita.
Duk hasashenta ta kasa gane komai dan haka taja ta watsar da lamarin illah ita fatanta abarsu da umma sahura taji wannan lamari dan duk idanta ruwa yake ta kasa fahimtar miya kawo waɗan nan nan kuma.
Cikin haka doctor hassan ya shigo zema jinjirar allura, ya umarci dukkan ƴan ɗakin su fita.
Hakan ce ta faru kowa ya fita waje domun zaman jira.
Anan suka tarar da mama a zaune wadda ko motsi batai, ba tana nan inda suka barta, daga karshema seta mike taiwa imran magana akan su zo su wuce gida.
Hakance ta faru, sakina imran da mama da sauran kannansa harda zuby suka tarkata sukai gida aka bar Anty kaka da umma anan ɗin, daman kuma sun san mama bazata zauna anan ɗinba mace mai alkunya da kara kenan.

Kuma cikin ikon ALLAH basufi minti ɗaya da barin asibitin ba sega motarsu mai girma mas! nan ta kutso kai cikin asibitin shida oska da wani abokinsa.
Wanda tun sanda hidaya ta gama haukanta tai ɗaki tana kuka bai kuma gamuwa da itaba hakan yasa ya shirya ya fito danya kara duba lafiyar bebynsa.

Seda motar tai parking sannan suka firfito daga ciki.
Turo kofar sukai tare da sallama shine na karshen shigowa ɗakin, wanda tsananin mamakin ganinsa yasaka kaka zamewa daga kujera tabbas wananan shine ɗan majalisarsu.

Agurguje suka gaisa sannan sukai hanyar ɗakin datake.
Shiya fara tura kofar bayansa kuma salim da oska ne.
Hannunshi rataye bisa bayansa haka ya karasa cikin ɗakin.
Sam ita feena bata ma san da shigowarsa ba.
Illah kamkame yarinyar datai tsamm tana faman zubda ƙwallah.
Sukam su oska.
Ganin likita akanta yasa suka ja da baya suka koma tare da rufo kofar, shikam karasawa yay tare da tsayawa ya mikawa doctor hassan hannu.
"Aikam gwara da ALLAH ya kawoka, madam dai taki aiwa bebyn allura wai ai mata ita abakacinta".
Batare dayay magana ba ya saka hannunsa yaja yarinyar wadda ita feena sam batada masaniya akan shine cikin kuka tace.
"Nidai dan ALLAH karku mata wannan ƴar yarinyar mita sani nikam gwara ai mani".
Cikin dakakkiyar muryar dabatai zaton jiba taji yace.
"Dallah malama ki cikata ana gudun lafiyarta kinwani kamkameta".
Cikin tsananin tsoro feena ta ɗago kana ta saukar da idanunta akansa cike da tsoro ta saki yarinyar.wadda cikin zafin nama yay saurin tarowa tare da ɗorata a kafadarsa yana jijjigata domin wani kukan data saki.
Da wannan damar doctor ya tsirawa bebyn allurar tare da hade kayansa yabar masu ɗakin
Ya jima yana jijjiga ƴarsa ita kuwa nafisa kanta yana kasa jikinta yana faman rawa cikin zulumi da tsantsar mamaki.
Ganin kukan yay yawa yasa ya juyo gami da ɗora mata ƴar akan cinyarta kana ya tsareta da idanunsa.
"Ko yau ɗinma kwarton zaki cemin, dalla bata mamanta tasha bana son ɓata lokaci, kuma wallahi wannan shine na karshe dazaki sake yimin wasa da ɗiyata".
Yakai maganar yana maka mata harara!.
Kamar bada ita yake magana ba haka tama juya masa baya kana ta saka hannunta ta toshe kunnenta kuma bata dauki ɗiyar bama baki ɗaya.
"Magana nake".
Yakai maganar cikin yar tsawa kaɗan.
"Bani da abinda zan bata ai".
Itama ta gaya masa maganar kai tsaye.
Wani shegen killer smile ya sauke sannan ya tallafo yar kana ya direta a gefe.
Tattare hannun rigarsa yay kana ya haye kan gadon shima.
Tsananin kusancin da sukai da ita ya saka kowannensu yaji faɗuwar gaba ta xo masa.
Cikin jarumta irin ta karfafan maza ya tarairayota jikinsa, tare da ɗora hannunsa saman ƙugunta ya murɗa.
Wata irin zillewa tai tare da kwantowa ajikinsa batare data saniba.
Ƙamshin daddaɗan turarensa yasa ta cusa kanta a tsakiyar kirjin nasa tana kuma saka hannunta ta zagaye masa bayansa dashi.
Cikin rawar murya ta soma magana "ALLAH ya hana hakafa ka tuna hakan haramun kake kokarin aikata min". sabida ta gane nufinsa wannan dalilin nema yasa tai masa wannan cakumar dan karya aikata mata hakan.
Bai tsaya jin daga gareta ba ya ɓanɓare ta daga jikinsa kana ya harɗeta da kafafunsa ya kifata saman cinyarsa tare da saka hannunsa guda cikin saman rigarta.
Saukar hannunshi kirjinta shiya kuma sakawa tai wata irin xilliya wadda ta saka dole ya saketa ta mike tana faman zubbo da hawaye inda shi kuma ya maka mata wata uwar harara kana yace.
"Ina wasa dake nannaaahhhh"
Turo baki tai gaba tamkar yarinya sannan ta juya masa baya kana ta fiddo da abincin yarinyar waje.
Da baya ta juyo da hannunta zata dauki yarinyar.
"Wallahi zan ɓata maki rai ahaka zaki daukar man ɗiyar".
yakai maganar yana jan ƙwafa, jin saukar muryarsa yasa tai maza ta juyo tare da daukar ɗiyar ta ɗora akan cinyarta.kana taja bedshit ta rufo kirjinta.
Sauka yay daga kan gadon jin alamun su oska zasu shigo......!!
68 - 69



Bedshit taja ta rufe jikinta kana ta saka hannunta ta tallafi bebyn tata, batare data kuma fara feeding ɗinta ba, ahaka su oska suka ƙaraso Cikin ɗakin.
Salim ke gaba daga bayansa oska, dukkansu cikin shiga ta kamala.
Da kallo feenah ta bisu cikin rashin fahimta sedai kuma taso shaida oska kamar taso ta gansu tare lokacin dayaje school ɗinsu akan gardi issue.
Cikin sakin fuska tare da Mutuntawa su oska, suka shigo cikin ɗakin tare da zama akan ɗaya daga cikin dogayen kujerun dake ɗakin.
Muryar salim ita ta katsewa feenah hanzarinta.
"Congratulation madam ALLAH ya raya mana bisa sunnah".
Shima oska amshewa yay kana ya mike zuwa wajan mai girma mas! ɗin wanda yawani ja ya tsaya a tsaye yana faman sakar mata harar rashin shayar masa da beby da batai ba.
"Mai gida sannu da hutawa zamu ɗauki yarinyar tamu".
Oska ya kai maganar cikin tsananin ladabi da biyayyah.
Tare da komawa wajan zamansa ganin mai girma mas! bai tanka masa ba.
Har zuwa wani lokaci sannan ya karaso gabanta.
Tare da miko mata hannu.
Daman kuma ta basa haushi na yadda tai burus dasu oska ko gaisuwa Babu. tamkar ma bata san da halittarsu awajanba.
Da ƙyar ta amsa musu barkar da sukai mata ma.
Cikin halin ko in kula ta dunguro masa yarinyar saman hannun nasa tamkar ta saka ihu!
Haka kurum take faman jin haushin kowa sabida yadda ake nan nan da ƴar tata wanda ita hakan bai mataba, taso anbarta da ƴarta sunje can sunyi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.
Shi kansa dubi yadda yawani tsaya mata tamkar ze ƙwace ƴarma baki ɗaya.
Ƙwafa! yaja a fili cikin sautin ƙasa-ƙasa wanda ba lallai su oska sujisa ba sannan ya tallafi ɗiyar da farin showwel ɗin da aka rufeta ya mikawa oska wanda yay zumbur ya mike tsaye.
Karbarta oska yay tare da nufar wajan salim, da ita cikin zumuɗi salima ya saka hannu ya amsheta yana faman daga wayarsa yana ɗaukar ta a hoto.
"Kamar kumbo kamar katanta" cewar oska wanda yake tsaye bakinsa ya kasa rufuwa.
Salim ne ya amsa masa da cewar...
"Gaskiya nima dai ban taɓa ganin carbon copy tamkar wannan ba, kasan ALLAH hatta ɗan sajen nan nata irina na mahaifinta ne".
Dariya oska yay tare da furta "ALLAH dai ya raya mana little mamman mu".
Shikam miskilin yana tsaye a inda yake yana faman turawa hidaya massege.
_Ayi haƙuri madam a ɗoramin ruwan coffee tun safe banci komai ba, ina asibitine dana fito kuma zanje gidan mai martaba in masa gaisuwar hawan sallah pls komai ya zama redy kafin nazo_
Abinda ya tura mata kenan tare da sakin smile bayan ya kammala tura matan kana ya mayar da wayarsa cikin aljihun wandonsa ya naɗe hannunshi akan kirjinsa ya tsaya ahaka tare da sunkuyar da kansa a ƙasa.
Har zuwa wani lokaci kafin salim ya mike tare da nufar gadon ya miƙa mata ɗiyar yana dariya tare da mata fatan alkairi.
Cikin rashin far,a ta amsa masa.
Bandir ɗin ƴan dubu- dubu ya fiddo sabbi gadagau daga aljihun wondonsa ya dire mata agabanta.
"Asai mata madara".
yafada tare da barin wajan, salim abokin anwarr ne tunna kuruciya yanzun haka yana aikine a matatar man fetur kuma yana can, da xama shida matarsa.
Wallahi murnar haihuwar da anwarr ya samune yasa ayau ɗin ya biyo jirgi ya nufo garin cike da ɗauki, domin ya taya abokin nasa farin ciki.
Yadda ya aje kudin haka ta barsu a banzace batare datai koda godiya ba wanda sauran kaɗan anwar ya nutse dan tsabar kunya.
Tamkar kububuwa haka ya marawa su salim ɗin baya.
Abakin kofar fita yaja ya tsaya yana mayar da ɓacin ransa.
"Osk ka kai salim hotel ya huta sannan kazo ka daukeni muwuce emir palace,".
Yafadi hakan cikin bada umarni.
Sannan ya dubi salim cikin nutsuwa.
"Abokina zanzo by tmr idan ALLAH ya nufa akwai magana".
Ɗan murmushi salim ya saki shima tare da kaimasa duka kaɗan irin na abokai sannan yace.
"Gaskiya nima akwai zance abakina sedai goben dannima na ɗagu nai balance duk jikina ciwo yake mani".
Sallama sukai anwarr ya juya ɗakin sukuma suka nufi cikin falon inda su umma suke zaune domin su wuce.
Da ɗan karfi ya tura kofar, wanda tunma kafin ya shigo mayen daddaɗan turarensa ya mata sallama.
A ciki ciki yay mata sallama tare da tsayawa akanta.
"Ni babu macen data isa ta bani ciwon kai, Alhamdulillahi ALLAH ya wadatani da mace tagari, and kuma iyayena sun bani tarbiya mai kyau, dan haka idan kinsan wannan rashin ɗa'ar zakina min wallahi zan karɓi ƴata dan bazata taso cikin wannan gida danci ba,............"
Dan tsabar rashin tarbiya kinsan waye salim? a ƙasar nan ma baki ɗaya!! ayau ya taso dan ya tayani murnar samun karuwa shine zaki masa wannan kauyancin nonsense! kawai".
"Nifa........" "Rufemin wannan ƙazamin bakin naki" yay saurin tarar maganar dazatai sannan ya ɗora da bala'insa kamar ba shiba haka zalika itama nafisan ta kasa gane ma mai yake fada sakamakon saurin Bakin dayake faman yi.
Seda ya wanke ta tass da masifa tamkar ze ari baki har wani hucin zafin rai yake idanunsa yay jajir haka jijiyar kansa ta mike tsaye goshinsa yay wani irin ja!.
Wanda kallo guda tai masa tai kasa da kanta tana share ƙwallar data zo mata.
Ɗaukar ƴarsa yay daga kan gadon ya ɗorata akan cinyar nafin agabansa ta zaro maman ta turawa ƴar abaki, yana faman zabga mata harara danyaga idan ya tsaya sanya wannan yar rainashi xatai.
Iya zafi feena tana shansa sabida yadda ɗiyar take zukar nonon gashi kuma wannan shine na farko gareta haka dai ta daure ta shayar da ita cike da azaba sannan ta kwantar da ita ganin tai bacci.
Se alokacin ya ja kafafunsa yabar mata ɗakin yana amsa wayarsa wadda duk kusan bayan mintuna uku setaga ankirasa kuma kalma guda taji yana fada watakan Amin Amin.

Futarsa da mintuna uku su umma sahura suka kuma dawowa dakin kuma still da wannan matar data taimaka mata a masallaci wadda ita matarce ma ta hada mata tea mai kauri ta sakata agaba tasha duk da bakinta babu daɗi.

Ahaka doctorn ya kuma dawowa tare da ce musu zuwa dare ze basu sallama domin yanzun haka komai yay normal dan bata ma karuba duk da girman ɗiyar amman babu ɗinki ko guda ajikinta.
70


Doctor yana gama masu wannan bayanin anty ta dauki waya ta kirasa akan ta shaida masa abinda doctorn ya fada.
Sedai user busy hakan ya saka ta nemi layin imran bugu ɗaya ɗauka anan ta shaida masa bayan sallar isha yazo zasu wuce gida.
Fatan alkairi yay masu tare da amsawa akan babu damuwa ALLAH ya nuna mana lokacin.
Ɗakinne ya dauki hira wadda kaka take bawa umma sahura akan yanzu habu bama ya zaman gida kullum yana kan hanyar bibiyar matan banza da dai sauran abinda ba,a so.
Nafisa wadda tai tsai da ranta tana sauraran wannan lamari mai ɗunbin alajabi ita ta numfasa sannan ta dire cup ɗin shayin hannunta kana ta dibi kudin gabanta ta mikawa umma sahura tare da gaya mata abokinse ya bata godiya umma tai cikin mamaki tare da adana kudin awaje guda sannan ta cigaba da sauraran kaka wadda tai stop tana faman kallon damin kudin cike da tsoro.
Haka suka cigaba da hirarsu ita kam nafisan tana ɗan kishin giɗe tana sauraransu.
Ana kiran sallah kowa ya mike yay wajan alwala kaka falo ta fita itakam anty tana fashine.
Dan haka umma sahura ita ta shiga na nan ta dauro alwalarta.


Yana fita daga reciption ɗin asibitin ya fada mota wadda oska tuni ya dawo daga kai salim.
Direc emir palace suka wuce wanda anan suka gamu da mai girma gwamna shima yaje anan sukai salla sannan yayo gida bayan ya gama karbar barkar karuwar daya samu daga bakuna masu daraja.


Aparking space oska ya dakata tare da fitowa da sauri ya bude masa kofar cike da nutsuwa yake fitowa daga cikin motar tasa.

Batare dayay ma oska magana ba ya nufi sashensa.

Ganin sashen su maama akwai taron jama,a.

Sashensa ya nufa cikin rashin kuzari yake taka step ɗin harya samu ya karasa cikin falon nasa.

Hidaya na zaune ta harde ƙafa tana game a wayarta ko kallonsa batai ba haka ma kuma bata amsa masa sallamar saba.

Zama yay agefenta abinda bai saba ba waishi rarrashi tare da kama hannunta.

"Haba my queen yaya ina sallama ma baza,a amsamin ba ko bakiga sako na bane ba?".

Tureshi tai da hannunta tare da tashi daga wajan tai hanyar ɗakinta.

"Naga sakonka niba baiwa bace ba kaje karuwarka tai maka mana".
Tana kai maganar tabar wajan baki ɗaya.

Harga ALLAH maganar ta sokeshi atake kuma ya kumai wa ALLAH godiya tabbas inda nafisa ba matarsa baceba yau dayaji haushin komai ma amman cikin rahamar ALLAH yanzu yana jinsa free itama hidaya yasan kishine amman da zarar ta sakko ze kuma mata bayani yadda zata fuskanta kuma abinda yasa yake mata uzuri tabbas yasan kowa akaima hakan baxeji daɗiba.

Da haka ya mike yay bedroom ɗinsa tare da rage kayan jikinsa ya faɗa bayi wanka yay sannan ya fito bayan yay sallah ya kwanta akan gadonsa tare da fiddo da wayarsa yana kallon hoton diyarsa.

Sosai mama ta saka masu aiki suka kuma gyara part din anty sannan suka gyara ɗayan dakin na kusa dana anty wanda ya sami sauyin dukkan kayan ciki wanda aka jerawa feena nata aciki dana bebynta domin anan zatai jegonta.

Bayan sallar isha i imran yaje asibitin bayan mintunan da basu wuce gomaba suka fito tare da shiga motar da imran din yazo da ita wadda take mai ɗan girma.

Bebyn tana hannun anty umma da kaka sune suka daddauko sauran kayan suka nufi mota.

Tare da barin aibitin wanda tunda taga sun dauki hanya daban bata gidan umma ba take faman turo baki gaba tare kuma da mamakin ina zasuje wanda bata sha mamaki ba.........


BACCI YACIN😴
71


Tundaga yanayin tsarin anguwar da yadda anguwar takasance umma sahura da kaka harma da nafisa suka soma rarraba idanunsu cike da tsoro da fargaba, lallai kuɗi karshen zance ne.
Basu sha mamaki ba seda sukaga bakin ƙaton mahaukacin gate ɗin da imran yay parking wanda aka kusan haɗe girman wata anguwar.

Cikin sauri masu gadi kusan su biyar dukkansu da uniform ajikinsu suka rugo zuwa wajan gate ɗin tare da wangale masa, cike da nutsuwa imran ya fara tafiya cikin gate ɗin inda harya samu damar parking acikin katafaren parking space ɗin gidan.

Yakai kusan mintuna biyar yana gyara parking ɗin nasa gami da kashe motar kana ya bude ya fita bayan yaywa Anty magana akan zasu iya fitowa suma.

Cike da nutsuwa Anty ta bude marufin motar ta fito sannan umma kaka, da kuma nafisa, baki ɗaya sakin baki kaka tai wadda har jikinta ya soma rawa ganin tarin manyan motocin da suke zube awajan yanayin tsarin gidan kuwa bakaramin kaɗa kowannensu yayba.

Cikin lokacin da bai gaza mintuna ukuba, masu aikin gidan suka zo suka ɗauki kayayyakin da sukazo dasu sannan Anty ta basu umarnin akan dasu zo su wuce ciki.

Bangaren mama suka nufa kai tsaye tun daga bakin part ɗin su umma suka soma kallon yadda aka narka dukiya kafin daga bisani suka karasa babban falon maman wanda tsananin haduwar dayay abin ma baze faɗu ba.

Falon mama cike yake da ƴan uwa, da abokan arziki da suka zo mata barka, ita kuwa tana daga can kan wasu irin tum-tum azaune gabanta wani flate ne mai ɗan karen kyau an ƙawata shi da kayan marmari.

Bayan sallamar dasu umma sahura sukai basu damar zama akan luntsuma luntsuman kujerun falon akai sannan aka soma gaishe gaishe wanda yawanci dangin Abba mahaifin Anwarr sunfi yawa a falon se ƴan uwan mama harda Anty aisha nurse wadda tsananin mamakin ganin umma sahura ya hanata tai koda motsin kirkine.

Ita kuwa nafisa tana daga gefe akan wani pillow da sakina matar imran ta saka mata a ƙasa ta zauna akan sa bebyn kuwa anata mikawa jama,a suna daukarta.

Da ido anty taiwa nafisa sigina akan taje wajan maama kuma cikin ikon ALLAH ta gane mai antyn take nufi, cike da sanyin jiki ta mike tana gyara hijabin jikinta.

Gaban wata yayar Abba ta fara tsugunnawa ta gaishe da ita sannan ta nufi gaban mama wadda kake hango tsabar kamanninta da Anwarr wanda ko shakka babu kana kallonta kasan itace mahaifiyarta.

Itama mama ta ƙasan idanunta take kallon, nafisan tare da yaba nutsuwar yarinyar tare da rashin kazar kazar ɗinta wanda atake kuma tai na'am da ita harma ta bata gurbi a zuciyarta a matsayin ƴarta kuma surukarta.

Saukar muryar nafisa wadda ta tsugunna agabanta itace ta katse mata tunanin nata.

Cikin siririyar muryarta ta soma gaishe da mama, itama kuma maman cikin sakin fuska take amsa mata gaisuwar daga karshe kuma ta mata yaya jiki sannan taja bakinta tai gumm.

Wadda ke kusa da mama, nafisan ta ɗaga kanta ta gaisar da ita, wadda da alamun bata ma jitaba seda mama tai ɗanyi gyaran murya sannan tace "Umman hidaya ana gaisar dake" cike da far,a matar ta juyo tanawa nafisan alamun data zo gareta sannan ta soma amsa mata gaisuwar cike da tsantsar kulawa wadda kana kallo kasan akwai tsabar dattako awajan matar nan.

Ita dai nafi duk tajita a takure haka ta zauna gaban matar kafin kuma taga matar ta ɗagota tare da kama hannunta suka nufi kofar falon da ita.

Wani ɓangaren umman hidayan ta kaita kuma da kanta ta haɗa mata ruwan wanka da kanta kuma tai mata wankan wanda seda nafisa tai kuka dan tsabar azaba, sannan ta bata wasu kaya ta sauya tare da pad kana taja mata kofar tabarta akan ta kwanta wai ta ƙara hutawa tunda dare yayi.

Godiya nafisa tai mata kana ta ɗan gyara jikinta ta kwanta akan gadon.

Acan falo kuwa tsabar mamaki bai bar anty Aisha nurse zama ba seda ta tambayi umma sahura akan lamarin anan kuma umma sahura tai mata bayani akan cewar daman can nafisa matar Anwarr ce kawai sun ɓoyene sabida tsaro.

Bayani tai mata kamar yadda inna ta tsara cikin gamsuwa Anty aisha nurse ta dubi umma tare da cewa "haba ashe surukata ce shiyasa naji na damu da lamarinta, kai Amman wannan yaro bai kyautaba dayaje mata da ƙarfi haka" ahaka sukaita tattaunawa har zuwa sanda aka kawo masu abici na alfarma mai dan karen daɗi.

Umma sahura da Anty aisha a flate guda suka zuba suna ci kaka ma nata daban haka zalika sauran kowa dana sa bayan cin abinci da hutawa anty ta umarci su, umma akan suzo su wuce zuwa part ɗinta.

Fafur umma sahura taki yarda akan itafa bazata kwana anan ba zata wuce gidane da safe sa dawo driver aka umarta daya kaisu gidan umma sahura bayan an basu kuɗi masu yawan gaske.

Suma sauran ƴan barkan sallama sukai, suka wuce gidajansu, inda anty taima mama sallama ta wuce part ɗinta itama.


Falon ya rage tsitt babu kowa se shahida da mama tunda daman anty aishama mijinta yazo ya dauketa sakina tai part ɗinsu.

Cike da mamaki mama ta dubi shahida "Nikam yau ina antynku ne?"
Cikin ɗan nazari shahida tace.
"Wallahi nima rabona da ita tun safe, amman da ummanta tazo ɗazu naga ta shiga part ɗin kuma data rako umman bata zo nan ba naga ta koma".

Murmushi mama tai batare datace komaiba ta ɗauki flate ɗin gabanta tai sama.

Ita kuwa anty ta jima a falonta tanawa, yayunta waya sabida bata gayawa danginta ko ɗayaba, cike da mamaki sukace mata gobe zasu kamo hanya zuwa nan ɗin.

Zuby da afra takai daki ta kwantar sannan tai ɗakin da aka warema nafisa, zaune ta tarar da ita ta zabga tagumi ga ƴar jinjirar cikin net tana faman bacci.

Zama anty tayi agefen nafisa tare da kama hannunta kana ta soma mata bayani "Nafisa nice mahaifiyarki!"! dum dum! gabanta ya yanke ya fadi tare da zaro ido tana kallon antyn,.

"Kuma ina son ki saka aranki Muhammadu Anwar mijinki ne na sunna kuma mahaifin ɗiyarki" awannan karon fina kasa zama tai seda anty ta kamota jikinta sannan ta soma bata labari tundaga kan haduwarta da kabiru mahaifin nafisan har zuwa rabuwarsu.

"Bayan baffana yazo wajan kakanki liman danya masa gaisuwa anan su baffanki sukai mana cin mutuncin dabaxe faduba daga karshe suka karbeki.ta karfin tsiya daga wajena ina kuka ina komai muka nufi rugarmu tundaga lokacin na soma cuta kamar zan mutu ga nonona yay sake sake sabida babu mai sha,haka naita jinya ko abinci bana ci ganin haka yasa baffana yaje da kansa wajansu domin su dubi ALLAH su bamu ke amman daga karshe harda jifansa, wannan dalilin yasa baffana yay kaura daga garin baki ɗaya kinsan zuciyar fillo...


Tunda muka koma cikin burni nake satar futa naxo nan garin naku amman fafur bana gane gidanku ahaka har muka dauki shekaru ban taba kwana batare danai kukaba cikin ikon ALLAH baffana ya fara cutar aljali harya rasu dayake daman kuma innata ta jima da rasuwa ita, daga nan se rikona ya koma hannun hammana wanda daman mu biyu baffa ya haifa dagani seshi..........
Kuma gidanmu guda tare da shi tunda daman daga innata baffa bai kuma samu yay aureba, cikin haka wannan bawan ALLAH baban anwar yazo wajan hammana domin ya sai shanu da sallah, anan ALLAH ya haɗamu batare da ɓata lokaciba mukai aure dashi na taho nan Alhamdh bana da matsala da ƴaƴansa da kuma matarsa sannan kuma mun samu rabon haihuwa dashi ga sucan ƙannanki su biyu...........".
Daga nan kuma ta soma baiwa nafisa labarin aurenta da anwarr wanda bata san anyi maganar ba wadda aka yita a asibiti a ɗazu dasu uncle sa'idu sukazo.

Sosai nafisa ta kaɗu daman mijinta ne wani kukane yazo mata batare data shiryaba atake kuma tafara godema ALLAH akan tsallakar mata da ɗiyarta dayay akan fitowa batare da aure ba.

Sannan anty ta fara mata bayanin komai daki daki.

Tundaga kan matsayin mama, sakina anty aisha, sosai feena tasha mamakin ashe matar data mata wanka ɗazu babar matarsce kuma matar kanin mamansa, lallai wannan familyn akwai zaman lafiya acikinsa.

Itama feena cikin kuka ta soma baiwa anty labarinta har zuwa sanda ta soma school da yadda ta fara ganin Anwarr har sanda ta basa taimako a wajan kai masa hari, amman kunya ta hanata ta gayawa anty, fyaɗen daya mata daga nan ta soma gaya mata yadda umma sahura ta riketa wanda anan wajan anty har

Please Login or Register in order to submit comment