Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hidaya wadda take zaune anci uban ado na kece raini tana faman jiran mijin nata.
"Hellow dee"
Hidaya ta faɗa a yangance, cikin ɗan saurin bakinsa kaɗan wanda ya zamar masa jiki ya furta.
"Na,am kinga zanje gidan inna na kira layin maah bata ɗauka ba, ki haɗamun abinci da ALLAH" Yakai maganar cikin alamun bata umarni.

Ɗan nisawa hidaya tayi kana tace.
"Eh ai gidan ma babu kowa nice kaɗai nima natahone domin nahaɗa maka abinci".
Waro manyan idanunshi yay tare da cewa.
"Suna ina kenan?"
Yay mata maganar cikin sigar tambaya.
"Nikam ban sani ba amman kamar dai naji sunje hospital".
"What"!!!
Yaɗan faɗi maganar cikin kaɗuwa kafin ma yace wani abun ta karasa maganar.
"Ka kwantar da hankalinka fa bawani serious problem bane bafa, but kasan maamah kusan halinku guda da ita, anty ce ta gamu da wata mai ciki a masallaci wai tana naƙuda shine fa suka sakata zuwa can ɗin". takai maganar cikin halin ko in kula.
Tun kafin ma tace komai ya datse kiran tare da shafar kansa.
"Ya salam yaya maamah zatai man haka tasan yadda garin ke fama da rashin tsaro gashi na kirata bata dauka yanxun haka idan wani ya kula dasu se a cutarmin dasu cikin sauki ko ai amfani dasu aci galabata tunda babu securty's atare dasu". yakai maganar a bayyane.
Tare kuma da umartar oska akan ya sauya akalar motar zuwa asibitin sa dan yana da yakinin nan zasuje.

Oska na driving shikuma yana try number mamah amman still ba,a dauka ba.
Ahaka suka isa cikin asibitin wanda kafin lokacin ya kira layin maamah yafi nawa.
Duk yadda yakai da dauriyarsa seda yaji babu dadi ahaka suka karasa special place, wanda acikin asibitin an waresa ne dominsu isu isu familyn su sabida asibitin daman nasane.
Kuma wajan babu wata hayaniya ta kofar baya oska yabi har suka samu suka karasa cikin wajan.

Tun kafin ma oska yay wani yunkuri anwarr ya balle marufin motar yafice zuwa cikin wajan.

Ajiyar zuciya ya sauke yayin dayaga motar gidan afake daga can ciki bai tsayaba haka yayta zuba sauri kamar bashi ba har zuwa reciption ɗin. da shahida yaci karo tana jijjiga zuby a kafadarta wadda take kuka!

Bai tsaya jin gaisuwarta ba yay ciki a zaune ya tarar da maamah akan wata kujerar karfe daga gefenta wata mata ta rafka uban tagumi.
Sallama yay masu cikin kamilar muryarsa, cikin nutsuwa kuma ya rissuna yanawa mama magana wadda se a wannan lokacin ta ɗago tana amsa gaisuwar sannan itama umma sahura wadda duk tawani hargitse ta ɗago idanunta tana kallonsa cikin mamaki tana ayyana miya kawo wanda take gani a t.v nan kuma.,?
Amman kallon mama yasa ta ɗan hasko wani abu game dasu ɗin tunda akwai kama ta jini.
"Maamah mike faruwa ne kizo na kaiki gida baze yuwu ku zauna anan babu cikakken tsaro ba"
Yakai maganar cikin ladabi.
Cikin tsananin tausayi mama ta juyo tana kallonsa.
"A,a itakam antynku ma tana ciki bazan iya tafiya ba domin idan shahida ko hidaya ce anan babu inda zani inaga wannan yarinyar se dai a yankata a cire ɗan sabida tana wahala antyn ka na wajan doctor" takai maganar tamkar zatai kuka!

Numfashi yaɗan ja tare da mamakin wannan hali na maamah haka kurum baki san mutum ba amman ku dage akansa.
Kallon umma sahura yay sannan yace.
"Baba ina mijin ta yake, kinga mamah baze yuwu ai mata wani abu batare da permission na mijinta ba".
Yakai maganar yana kallon umma sahura wadda tai wuki wuki nan da nan kuma idanunta ya kawo ruwa.
"Mijinta ya rasu nice kuma mahaifiyarta idan har kunyi niyyar tai makonmu to kuyi dukkan abin da ya dace domin ALLAH".
Takai maganar tana share ƙwallar ta, sannan ta ɗora.
"Bawan ALLAH nasanka tunkafin na ganka a yanxu Alkairinka yake xuwa kunnena amman ban sha mamaki ba seda nagani yanzu da idanuna ashe abun ajininku yake kaiwa ALLAH ka taimakemu ka saka hannu aiwa nafisa aikin nan wallahi tunda ta sami cikin nan muke walaha" takai maganar cikin kuka.
60 - 61


Babu abin da ke tashi a wajan face kukan! ummah sahura wadda ta karyawa maamah ta,ta zuciyar itama nan da nan ta soma share ƙwallah da tsadaddan farin babban mayafin dake jikinta
Shikam mas! sunkuyar da kansa yay yana nanata Nafisahhh!! acikin zuciyarsa atake shima tasa zuciyar ta karye tunanin tasa nafisar yay masa kaaaa sannan tsananin tausayin matar ya ratsa masa jikinsa dama zuciyarsa baki ɗaya.
"Katashi kaje ka saka hannu ai mata c,s" mamah ta fada cikin bada umarni.
Cikin damuwa gami da kasala ya mike duk jikinsa yana amsa kuwa! yanufi cikin wajan.
Katafaren office ɗin doctor hassan wanda ya kasance babban likita a ɓangaren ya shiga.
Da anty yaci yakaro tana kokarin fitowa duk jikinta ajike da zufa, da kallo ya bita sannan kuma suka juya ciki atare da ita.
Cikin mamaki doctor ya mika masa hannu suka gaisa sannan yay masa bayanin dukkan abin da ake ciki sannan ya umarcesa daya saka hannu domin har yanzu takasa haihuwa sannan kuma tana faman jijjiga wadda ba,a son mai nakuda tayita.

Ɗan numfasawa yay kasancewarsa shima ƙwararren doctor kana ya dubi doctor hassan sannan yace masa, baza,a iya bata taimako ta wata hanyar ba dole sedai an yankata? murmushi doctor hassan yay sannan ya mike tsaye ya dauki kayansa na aiki sannan ya umarcesa daya biyoshi can ɗakin dan yaga halin datake ciki idan da taimakon daze bata sabida yafishi sanin wasu abubuwan.

Ɗan jimm yay sannan ya dubi doctor wanda ya mike tsaye itama anty ta mike baya da zabi face binsu zuwa levour room ɗin..wata kwana sukabi bayan, sun fito daga office ɗin.


Adai dai bakin kofar yaja yatsaya yanajin kirjinsa yana bugawa kamar ze ɓalle ya fito waje.
Dafewa yay sannan ya aro jarumta yabi doctor.
Tamkar gizo ya hangota tana faman wani irin abu bakinta yana fitar da dafara, tana faman ciccije bakinta, tsananin mamakin abun shiya daskarar dashi a wajan ya kasa gaba balle yay baya.
Itakam daman anty a bakin kofar aka dakatar da ita. haka itama ta tsaya cikin zulumin lamarin.
Seda yay tamaza sannan ya ƙarasa shiga cikin ɗakin baki ɗaya nurses ɗin wajan sun gama jigata bayyanar doctor hassan yasa suka ɗan ragu aka bar sister naja ita ɗaya tana rike da kayan aikin.

Nafisa kuwa iya wahala ta ganta tun tana kuka! da hawaye har seda tazo tana kuka babu hawaye bata gane komai hatta kanta.
Ikon ALLAH kuma da shigarsa tamkar an karo mata nakudar haka ta kawo kai kan jiki kan karfi.

Baya da wani zaɓi face ya bata iya taimakon da ALLAH ya nufesa domun yanzu babu lokacin tsayawa doguwar hira.

Cikin dabara ya sallami doctor hassan shine ya tsaya akanta sister naja tana taimaka masa har ya samu yay mata wata allura wadda ta tsayar mata da wannan jijjigar kafin kuma cikin amincin ALLAH faya ta fashe wadda nan da nan kuma nakudar ta dawo sabuwa.

Cikin amincin ALLLAH kafin wani lokaci karar kukan jaririyar ya cika ɗakin, cikin azama ya tarota bayan ya sabule safar hannunsa, mikawa sister naja yay yarinyar sannan ya koma ga nafisa wadda ta sume taimakon gaggawa ya bata kana ya saka naja ta kirawo nurses suka wuce da ita ɗakin hutu.

Itama yarinyar an samu nasarar gyarata tass cikin kayan sanyi farare wanda aka samosu a office ɗin doctor.

Gava ɗaya rigar jikinsa ta jike da jini haka ya tattara ya nufi waje cikin tsananin murna marar kwatance.

Anty ya mikawa yarinyar yana gaya mata itace wadda yake nema.

Cikin tsananin mamaki anty ta dubi yarinyar katuwa wadda se a hade yara biyu saboda tsabar girman yarinyar.


Wadda hatta yatsar hannunta irin na mahaifinta ne babu abin da ya raba kamanninta dana sa sak suke kama da mai girma mas!

"Anty kimin addu,a ALLAH ya rayamin ita, na sameta a yayin danake tsananin bukatar ganinta, sedai abin da yasaka nai hawaye shine ƴata aka haifa a yau amman an rasa rigar daza,a saka mata se ata ƴan sadakar asibiti". yakai maganar cikin kunar rai.

Itakam anty mamakin wannan lamari da kuma tsananin farin ciki sune sukai mata dirar mikiya ashe wannan yarinyar ita ɗan nasu yaketa faman nema yanxu wannan yar ta hannunta mallakin anwar ce?.
Haka anty tai ta nanata maganar har zuwa sanda taji yana mata magana akan suje wajan su maamah danshi kam ze koma gida ya gyara jikinsa.

Anty ce ta rungume bebyn ajikinta suka nufi wajan dasu mamah suke cikin tsananin murna.

Take mikawa mamah bebyn batare data ce mata komai ba.

Shikam jayay ya tsaya akansu yan faman sakin murmushi.

Cike da mamaki umma sahura take duban jinjirar kana tace "Alhamdulillahi mungode ALLAH sannunku bayin ALLAH".

Cikin farin ciki anty ta ɗago kanta ta zubawa umma sahura idanu tana doka far,a.

Cikin rawar baki umma sahura ta furta.
"Ƴar fulani" duk da abin akwai sauyi amman hakan baze saka ta kasa gane taba.

Cike da mamaki anty ta ɗago kana ta dubi umma sahura da kyau sannan ta furta.
"Lahhh adda sahu!!! takai maganar da ƙarfi tana kuma dubanta d kyau.


Kallon kallo aka shigayi a tsakanin umma sahura tare da anty inda kuma mai girma mas! da mama suka zama ƴan kallo.

Kuka anty ta saka tare da tsugunnawa wajan tana zaman dirshan tamkar taɓaɓɓiya.

"Adda sahu daman kuna duniya naje garinku yafi sau dubu ban gane ko ina ba adda sahu ina jaririyataaaaaa......?"

Itama umma sahura share hawayen tai kana tace.
"Labari mai tsaho ƴar fulani amman ina maki albishir da cewa jaririyarki ita ce ta haihu yanxu kuma wannan ƴar da kika ɗauka jikarki ce ɗiyar wajan nafisa wadda....."
Bata karasa ba kukan anty ya cika wajan.
"Adda sahu kina nufin wannan mai nakudar jaririyata ce kina nufin ɗiyatace?" tafaɗi maganar tamkar ta zare tare da saurin kai hannu jikin mama ta warci jinjirar ta rungumeta tsamm tana faman kuka!!

Cikin tsananin kuka umma sahura tace. "Tabbas yar fulani baki kyautawa rayuwar ɗiyarkiba tindaga ranar da kabiru yabar duniya baki kuma waigenta ba yanxu gaya nan har kaddarar....." batai maganar ba taji saukar muryar mai girma mas! akanta.
"Baba ba kaddara bace kaddara da warwara zakice domin nine mahaifin wannan jinjira.....yakai maganar yana tsugunnawa agaban umma sahura tare da bayyana mata komai.

Sannan ya mika hannu ya amshi yarinyar ya kara ajikinsa yana zubda kwalla.

Sosai mama ta kadu da wannnn lamari haka zalika umma sahura ta kadu lallai nafisa tacika munafuka dabata taɓa bayyana mata komai ba, amman koda yake rabon saduwarta da mahaifiyarta yasa ta ɓoye.

62 - 63.


Babu abin da mama take faɗi se kalmar.
"Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi!!.

Kana ta ɗago kanta ta kuma sauke idanunta akan anwarr wanda yake tsaye da ɓatattun kaya ajikinsa ga kuma bebynsa rungume a kirjinsa.

Cikin wani yanayi wanda yake cikin sarƙaƙiya ta dubesa tare da yi masa alamu da hannunta akan yazo.

Cikin ladabi da biyayya ya karaso gareta tare da ɗora mata bebyn akan cinyarta.

"Maza kiramin uncle ɗinku" ta gaya masa hakan.
Cikin mutuwar jiki.
Cike da ƙwarin gwiwa ya zaro wayarsa ya fara laluben, layin uncle sa'idu abokin mahaifinsa kuma ɗan uwa agaresa wanda suka kuma taso tare da marigayi alhaji sameer.

Bugu uku uncle sa'idu ya ɗaga wayar bayan sun gaisa anan ya mika mata wayar magana sukai da mama cikin harshen fillanci wadda auta ta kasa fahimta.

Bayan kamar mintuna biyu ta katse kana ta baiwa anwarr wayar tasa, sannan kuma suka mike zuwa cikin ɗakin hutun da aka warewa nafisa dukkansu.

Da ƙyar aka lallaɓa anty ta zauna anan falon ɗakin wanda aka ƙawata shi harda kayan, kallo cikinsa kuma nafisa ke kwance an jona mata ƙarin ruwa.

Seda umma sahura tai wa anty nasiha sannan ta daina kukan datake wanda baki ɗaya ta kasa zama tana zama take kuma mikewa ta nufi cikin ɗakin ganin ko nafisa ta farka amman ko motsi.

Umma sahura wadda itama ta ɗagu abasu sallama su wuce gida kodan ta sanarwa da ƴan uwa wannan lamari itama kanta ta kasa zama.

Daga kan kujerar gefe kuwa mama ce zaune rike da ƴar bebyn se shi uban gayyar a tsaye yana faman danna waya yana daukar bebyn a hoto.

Babu ko kunyar idon mama wadda tai kasa da kanta ta kasa magana sabida yadda yake bata mamaki.

Cikin haka sukaji an turo kofar sallamar uncle sa'idu ce ta saka suka mayar da hankalinsu kofar.

Bayansa baba Ali ne kanin abban anwarr mai bi masa.

Daga bayan baba ali kuma akwai inna mahaifiyar abban anwarr.

Waɗanda duk suka shigo ɗakin cikin kyakykyawar shiga ta kayan sallah.

Bayan gaishe gaishe kuma anan hira ta ɓarke sosai kuma su uncle suka karbi yar jaririyar sukai mata huɗuma da suna khadija kana suka mikawa mama ita.

Ɗakinne ya dauki tsit..

Mama ce ta juyo ta dubi inna mahaifiyar mijin nata sannan ta soma yi mata bayani tundaga haduwar anwarr da nafisa cikin daya mata da komai da komai.

Har zuwa yau da suka tabbatar da yarinyar ɗiyar anty ce ashe.

Sannan mama ta ɗora da cewa.
"Abinda yasa na nemeku tun anan shine ina son ai komai cikin sirri sedai babban abun da ya dauran kai ga wannan lamarin shine, wasiyar alhaji wadda ya bayar a gabanki". ta nuna inna da kuma baba ali da kuma uncle sa'idu.

Sannan ta cigaba..


"Lokacin wannan yaron baya garin nan, sannan antynsu ma bata wajan, Alhaji ya baka wasiya sa'idu dan ALLAH kamar yadda na rokeka a waya akan kazomin da wannan akwatun da alhaji ya baka yace kada a fito dashi se anga ƴar wajan antyn su nakeson ka nuna mana".
Takai maganar tana haɗa hannun ta waje guda.

Cikin zulumi uncle sa'idu ya fito da akwatin yar karama wadda tun a waya mama ta roki dayazo da itan sannan ya mikowa baba ali.

Baba ali ya karba ya budeta wata takarda ce ta bayyana.

_Assalamu alaika ya ɗana Muhammadu anwarr hakika ni mahaifinka nai maka wani ɗan abu kaɗan wanda ban saniba ko zakaji dadinsa ko bazakaji ba, ni mahaifinka wanda nai sanadin kawoka wannan duniyar a yau asabar 2/ 2 nida aminina sa'idu munje wajan mahaifin tsohon mijin matata hafsatu mai suna liman nane mamaka auran ɗiyar wajanta nafisa kuma alhmdh an bamu kuma mun bada sadaki wanda yazama abokina sa'idu shine shaidata kuma haka zalika mai gari abokin malam liman shine shaidar mu domin abokina sa'idu shine waliyinka haka zalika mai gari shine waliyin wannan yarinya.nayi wannan haɗinne domin na wankewa hafsatu kuncin abinda dangin mahaifin yarinyar suka mata, haka zalika na boye wannan lamarine domin gudun ɓacin rai. wanda na boyewa hafsatu hakan domin na nuna mata laifin yin burus da ƴar tata datai, naje wajan malam liman domin na amso nafisatu ta dawo wajanmu sedai na tarar rai yay halinsa haka na nemi wani daga cikin danginsu domin muyi magana amman ban samu ba, naje wajan mai gari baya nan, dan haka na dawo gida kuma babu dadewa nima wannan lalurar ta ajali ta saukar min wadda bana da tabbacin ko zan tashi, ina rokonka daka gaggauta karɓo matarka domin na hango sarkakiya daga dangin mahaifinta,idan sun musa maka ka nemi kawunka saidu da kuma mai garin domin sune shaidar komai, ina fatan zuri'ata da dukkan wanda ya raɓeni yaywa wannan takardar kyakykyawar fahimta_

Baba Ali yagama karanta wannan takardar jikinsa duk yana rawa.

"Innalillahi wainna ilaihirraju'un yanzu sa'idu inda anyi gangancin aurar da yarinyar nan da mai kenan akai? ai wannan ba hujja bace mai yasa kai sa'idu kuka ɓoye mana hakan yanxu bada ban wannan kaddarar ta miko ba dayaya akai kenan?" inna takai maganar tana share hawayenta.

Gyaran murya uncle sa'idu yay sannan ya dubeta "daman inna ina da niyyar bayyana wannan kulli sabida halin rai da mutuwa,domin na fuskanci sam ita hafsatu batama san cewar marigayi yana zuwa can wajan tsohon surukin nataba, sannan ita kuma tace bata gane wajan kotaje sakamakon surkullen da mahaifinta yay mata domin ya dauke hankalinta daga kan ƴar tata sabida zafin wulakancin da aka mata".

Yakai maganar yana murmushi.

Mama kam kuka ta saka haka zalika anty umma sahura babu mai bakin magana se kuka, shikam uban gayyar bazaka tantace wani hali yake cikiba illah sujjadar dayay awajan yana godewa ubangijinsa abisa wannan rufin asirin daya masa cikin sauki abisa tserar dashi dayay daga samun ƴar fari ta zina.

Muryar anty ce ta karade wajan.

"ALLAH nagode maka! hakika wannan itace isharar ubangiji, Anwarr hakika ALLAH yanawa bayinsa rufin asiri tare da rahama alokacin da yaso tabbas ALLAH ne ya wankeka ya kuma duba lamuranka bai kuma nufa dakaji kunya a idanun makiyankaba masoyanka kuma suyi kuka ba........ALLAH ya kaddara maka kaddara ka amsa daga karshe kuma ya wankeka acikinta......ashe duk wannan abun wannan yarinyar matarkace ta sunna kai ka kuma godewa ALLAH tabbas wannan shi ake kira da ƘADDARA DA WARWARA!!...............
Hakika tsakanina da alhaji se addu,a yadda yaymin ALLAH yay masa ALLAH yakai haske kabarinsa ALLAH yasa dashi da annabin rahama, hakika nidaman jikina yana bani akwai ɓoyayyen kulli acikin wannan lamari, nagartaccen mutum kamarka anwarr baze aikata abunda ALLAH baisoba duk da ALLAH babu wanda baya jarabta amman ni naji ajikina Anwarr bazaka aita zina ba sabida ka fito daga tsafta taccen family cikin tsarka,kakkun iyaye.

Anty takai maganar tana kuka!

"Nima tabbas Babu abinda zancewa da ALLAH se godiya, wallahi tun sanda yazo ya shaidamin bana bacci kullum cikin rokon ALLAH nake akan ya yafe mana laifukan da mukai har ya ƙaddara wannan yaron ya samu rabo ta hanyar da ba,a so, ashe shi ubangiji akwai nufinsa dayin hakan lallai ALLAH ALHAKAMU!".

Kowa godiya yakewa ALLAH acikin wannan lamari, musamman umma da mama da anty.

Ita kanta umma sahura wannan lamari ya kaɗata so kawai take asamu faraga ta fice oh yau ina su baffa masu kuri suzo suga ikon ALLAH.....!!



HOHO MY FANS WASA FARIN GIRKI.


ANAIWA AUTA UZURI🙏🙏🙏🙏
64 - 65



Hoho umma sahura bakinta kam ya kasa rufuwa se uban far'a take faman saki tamkar babu gobe.

Cikin nutsuwa inna kakarsu ta dubi mama sannan ta soma magana........
"Hadiza ina ganin idan an basu sallama ku wuce gida can da ita, idan yaso baza,a shaidawa kowa cewar ga abun da ya faru ba. illah za,ace masu kawai matarsa ce, tunda ya aureta bata cikin gari ya ajetane acan garinmu sabida ta sami ƙaruwa, gudun cutar da ita yasa aka boye maganar".
Inna takai maganar tana kallon mama sannan ta juya ta kalli sauran tana jiran miza,a suce.
"Eh kam inna maganarki tayi tunda ALLAH yasa matarsa ce ta sunna ai ba wata matsala se a faɗi hakan kodan gudun bakin mutane".
Cewar baba Ali kenan kanin marigayi.
Kowa yay na,am da maganar illa mama wadda bata ce komai ba hasalima sunne kanta tai a kasa tana jan carbinta, kuma daman kusan hakan ne gareta bata fiye tsoma kanta a cikin sabgar Anwarr ba.
Ita kuwa umma sahura suna gefe da Anty suna tattauna hirar yaushe gamo.
Cikin dubara kuma ta ari wayar anty ta kira, baba mijinta wanda ya gama firgitar rashin ganin ko ɗaya acikinsu wanda tsananin firgicin nasa yasa har ya dangana da gidan kaka, ya sanar dasu halin da ake ciki.
Yanzunma haka yana wajan kakar wadda ta saka ƴaƴanta agaba tana faman kuka!
Cikin nutsuwa umma sahura tai masa bayani atakaice.
Sannan ta ɗora da idan yana da hali yazo da kaka gidansu na nan zuwa anjima zata taho daga asibitin.
Tunda ta boye musu zancan auran nafisan.
Fafur su baffa sukace bazasu je barkar shege ba itakam kaka babu yadda ta iya haka ta biyo baba sukayo gidan umma sahura.
Bayan umma ta kammala wayar ta juyo ta dubi anty tare da mata godiya sannan ta bata wayar.
Sukam su inna sunyi sallama dasu mama tare da barin asibitin bayan inna ta shaida masu cewar a yanzu base anjima ba zata tara dukkan zuriyar tasu ta shaida masu wannan lamarin.
Haka suk fice daga ɗakin wanda yay saura daga shi se mama tare da umma da anty wadda take abakin kofar tamkar tai tsalle ta dauko nafisa.
Cikin kwantar da murya mama ta dubesa.
"Yakamata kaje gida ai kodan matarka sannan ka sauya kayan jikinka".
Wata kunyace ta kamasa shi sam yama manta dawasu kayan dake jikinsa.
Shafa sumar kansa yay tare da furta mata "tom" cikin kasan laɓɓansa sannan ya mannawa ɗiyarsa kiss bisa goshinta kana yay ma su umma sallama yabar ɗakin.
Tun sanda ya hau mota yake faman ɗora hotunan yarinyar tasa cikin dukkan kafafan sadarwarsa.
Wanda zuwa wannnan lokacin zancen haihuwar yacika gari.
Tuni kuma ƴan jarida sukaima kofar gidansa caa suna jira daga garesa.
Tsananin yadda ake faman doko masa waya yasa yama kashe wayar tasa baki ɗaya, bayan ya sanar da oska akan yaje yayma jaririyar siyayya harma da mamanta.
Tundaga bakin kofar gate din gidansa yake arba da jama,a da ƙyar securtyn gidan suka taimaka ya wuce a falon, kasa ya tsaya yay wanka a gurguje sannan ya shirya cikin kananun kaya, tare da fita waje danya warware ƙullin dake gabansa.
Tundaga bakin kofar farko.
"Yallaɓai waishin da gaske an maka haihuwa a yau wanda iya sanin duniya ba,a san kai wani auren ba, sannan kuma ba madam ta gida bace, shin mezaka iya faɗa danka warwarewa mutane wannan ƙulin wanda yacika kowa da mamaki amman babban abunda yafi bawa kowa mamaki yadda akaga kai da kanka kake watsa wannan bayanin?"
Cewar wani ɗan jarida dake faman karo masa abun magana bakinsa.
Lumshe idanunshi yay kana ya bude.
"Alhamdulilahi ya ALLAH, abinda zan iya gayawa masoyana dama maƙiyana shine ayau takama ɗaya ga ranar karamar sallah ALLAH yay min kyautar Nana Khadija, ta wajan amaryata wadda mukai aure da ita bada jimawa ba abin da kuma yasa na ɓoye wannan auren harma cikin sabida yadda makiya sukai min caa duk da bana tsoronsu Amman ance a ɓoye nema a Bayyana samu, kodan gudun matsala".
Yana gama fadin hakan kuma ya juya part ɗin nasa baki ɗaya yabar taron yan jaridar rike da abun daukar rahoto suna watsawa duniya.
Cikin awa ɗaya zancan haihuwar amaryar ɗan majalisa ya karaɗe garin baki ɗaya, wasu na mamaki wasu alajabi wasukuwa tsorone ya kamasu
Kuma cikin kankanin lokaci inna ta tara dukkan wasu iyalan mai carbi ta sanar masu da maganar.
Kamar yadda ta tsara tun a asibiti wanda tsananin mamaki yacika wannnn zuriyar amman murnar haihuwar yasaka kowa ya kasa zama.
Haka kuma mutan gari sukaita ɗora tayasa murna akan kafafan sada zumunta.
Hatta mai girma gwamna zuwa wannan lokacin ya kira wayar sa dan yamasa barka yafi sau nawa amman akashe haka zalika ƴan jam'iyarsu da sauran jama,ar gari.
Cikin asibiti kuwa ilahirin ƴan gidan sun halarci asibitin hatta su imran waɗanda har kukan murna seda sukai haka zalika shahida da sauran kannansa dasu sakina matar imran duk sun hallara a asibitin wanda shelar inna tazo musu daga gidan innar sukayo nan suka kuwa kama yar jaririyar suka rike tamau suna faman yi mata hotuna.
Duk wanda yaga mahaukaciyar siyayyar da oska yayo.seya zabura sabida siyayya akai tamkar kanti sabida haka anty tace shahida tai gida da wasu kayan.
Acan cikin gidan kuwa tuni labari yakai ga hidaya wadda kawarta ta kira tana mata barka cike da mamaki take sauraran kawar tata.
Cikin haka ya shigo falon.
Cikin nutsuwa yake dubanta danya mata bayani.
Amman abunda tai ya basa mamaki matuka harda kiransa ɗan iska, itafa sam bata yarda da wannan munafurcinba
Duk yadda yaso ya fahintar da ita ya kasa haka ya tattara ya watsar da ita yay cikin ɗakinsa danya shirya ya fita.

Acan asibiti kam mama waya ta kuma ɗagawa ta kira baba Ali dayake yana kusa ya kuma zuwa anan ta roki daya dauki anty da umma ya kaisu can wajansu kaka, sabida tafison a gama komai kafin tashin nafisan dan ta fison suyi gida kai tsaye.

Haka kuwa akai ya dauki umma da anty A gidan umma aka dauki kaka da baba suka nufi can gidansu kakan wanda daga nan akai wajan mai gari harda su baffa.
Sosai baba ali yaywa mai gari bayani wanda tunkafin ma ya karasa mai gari ya cafke anan fa aka soma kallon kallo, xuwa wani lokaci zancan ya cika wannan zuriya ta liman wanda tuni wasu suka soma dana sani, anty kam zama tai tamkar tauraruwa awajan su baffa sabida yadda ta koma.
Haka aka gama tattauna komai kana sukai masu sallama suka barsu cikin zulumin wannan lamari wanda hatta matan su baffa mamakin lamarin ya hanasu sakat.
Kaka kam kuka take tana kuma godewa allah sukam su baffa mamaki kunya sune suka masu caaa!

Mijin umma sahura kam harda kukan murna.

Bayan kammala komai cikin sauki haka baba Ali yayo asibitin da kaka da umma da baba da anty wadda kaka taketa zumuɗin ganin nafisan.
Wadda duk suka shaida yanzu matar ɗan majalisarsu ce kuma tai masu zarra.

Lokacin da suka nufi asibitin.
66 - 67



Shigowar su umma kuma yayi dai-dai da farkawar nafisa.
Cikin azama nurse ɗin dake kanta tana kula da ita, ta fito waje cikin farin

Please Login or Register in order to submit comment