Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hasalima ni ciki kawai nasan nai maki amman bani na kaiki gidanaba, amman sabida adalci irin nawa naji na amince da komai amman shine zaki kirani da wannan suna? mi kikeso ai maki? idan wannan cikinne bakya bukata nagaya maki zamuje a cireshi ki huta na huta ni kuma nai maki alkawarin baki kudin dazaki gina rayuwarki ta har abada batare dakin sha wahalaba".
Yakai maganar yana ɗan jan numfashi kaɗan kaɗan.
"Idan har kai mani haka tabbas sunanka ze sauya daga mugu agareni ya juya zuwa AZZALUMI!! saboda kai nasarar rabani da abu biyu masu matukar mahimmanci acikin rayuwata. nafarko soyayyarka wadda tabi jinin jikina ta lafe, na biyu gudan jininka wanda yanzu shine bugun zuciyata tabbas idan ka mani haka zan kashe kaina na huta kabarni naji da abu guda pls pls pls" takai maganar aburkice tana gunjin kuka, wanda tasaka bai san lokacin daya jawota zuwa kirjinsa ya rungumeta tsam tsam ba.
Shafa mata gadon bayanta yake zuwa saman gashin kanta, yanajin kuma tsinin cikin dake jikinta tare da bugawar zuciyarta mai sauri.
Gabaki ɗaya ta riga ta gama basa tsoro ba,a son mace mai juna biyu tana waɗan nan abubuwan sabida hatsarine, wannan dalilin yasa ya hadata da jikinsa domin ya bata nutsuwa ta hakan amman bawai yana nufin yana sonta ba.
Sun kai mintuna kusan biyar ahakan harya samu ta daina kukan.
Wayarsa ce tai ƙara! safiyan ke kiransa kuma yasan halin safiyan da bin diddigi and kuma yasan wannan motar idan yaga bai ɗaukaba ze iya karasowa kuma shi bai son agansa da mace a motar sabida gudun zargin abin da yafi tsana.
Wannan dalilin yasa ya janyeta daga jikinsa tare da jinginar da ita a jikin kujera, sannan ya ɓalle marufin motar harya saka kafarsa guda a waje ya juyo yana kallonta.
"Bani minti goma please"!.
Batare daya jira amsarta ba yafita baki ɗaya.
Ɗagowa tai tana kallonsa cikin shaukin so.
"Tabbas kai ɗin nagari ne kamar yadda ake faɗa ka kasance mutum mai wa naƙasa dashi adalci tabbas kana da saukin kai kana da daɗin zama, duk da banga ko ƙwayar sona a idanunka ba amman na aminta da tausayinka gareni ƊAN BAIWA".
Tana kuma kai maganar ta duba side nata taji a rufe dajan jiki ta bude side nasa daya manta baiwa key ba ta fice daga motar tana share hawayenta.
Cikin zafin nama tabi ta karamar kofa ta fice, tana jin iska na kadata ta ko'ina kana ta sami napep ta haye......!!



*KAIIII NAFI KIN TARO PILLARS*😳😳😳😳😳😳😳
52 - 53


"Hajiya ina muka nufa naga garin yana kuma narkewa?"
Cewar mai napep ɗin da feena ta hau kenan bayan ya soma tafiya da ita.
Cikin wani irin yanayi ta dubesa sannan tace.
"Nan bakin hayin ɗawisu zamuje".
Takai maganar bayan ta sada kanta a ƙasa tana tsoron kada ya biyota hanya.
Har sukaje unguwar feenah bata dawo dai dai, ba gani take kamar ze iya biyota nan ɗin ma, sauka tai tare da ɗan sinkuyowa da ƙyar.
"Malam ɗan bani mintuna uku zanje na amso maka kudi a gida".
Takai maganar tana kallonsa.
Ɗan murmushi ya ƙaƙalo sannan ya dubeta.
"Haba baiwar ALLAH aiko da bani da imani na ganki a wannan yanayin zanji wani abu, wallahi ki bar kudinki nagode".
Yana kaiwa nan yaja baburinsa zebar wajan.
Ɗan jimmm tai kana taɗan ƙaƙalo murmushi.
"Nagode bawan ALLAH ubangiji ya biyaka da mafificin alkairinsa Ameen".
Takai maganar tana murmushi kanq taja kafafunta tai cikin layin nasu.
Ɗan ja tai kaɗan ta tsaya tana sakin murmushi ita ɗaya.
"Tabbas muhammad anwarr kai mutum ne nagari miyasa tundaga lokacin dana ɗauki cikinka ALLAH bai sa na wulaƙanta ba,mai yasa jama,a da dama suke tausayamin aduk sanda zan gamu da wani tofa seya nuna tausayinsa gareni.......tabbas wannan ma wata baiwa ce daga ALLAH kaiɗin mutum ne nagari wannan dalilin yasa jininka baze taɓa tozarta ba, domin ka rufawa mutane da dama asiri ka tausayawa mutane, kaima shiyasa,ALLAH yake tausayawa naka".
Takai maganar tana sakin murmushi kaɗan akan fuskarta haka kurum take hasko movement ɗinsu na ɗazu ahaka harta karasa cikin gidan umma sahura.
Tundaga bakin kofa take jin kamar alamun shashshekar kuka! cikin azama taja jikinta tai ciki hartana hardewa, sekuma ta gyara tafiyar tata azuciyarta tana, fina kula wannan mutumin baze taɓa ɗaga maki kafaba idan wani abun ya sami ɗansa ko ƴarsa ya ɗaureki a iska, da wannn tunanin ta karasa tana hango umma sahura zaune tana kuka! baba mijinta yana gefe yana mata nasiha.
Jin sallamarta yasa umma sahura ɗagowa da sauri.
"Nafi daga ina kike kin ɗagamin hankalina! nace daga gidan ubanwa kike tun yamma har yanzu kina ina newai?".
Rage tsahon ta tai sannan ta dubeta.
"Umma kimin alfarma wallahi ganin ruwa yasa na fake a hanya wanda na hadu da marasa imani.........." ta lafto mata karyar kare kai dan bata son umma ta gano komai.
Bayan umma tagamajin komai sekuma tahau hamdala tana fama sakin hamdalar sosai! "Allah nagode maka ni sahura inda waɗan nan mutane sun far maki dayaya xakiyi maza wuce daki ki sauya kaya kizo muci abinci danni ma na kasa kai komai bakina kedai barka, yau babu inda banjeba nemanki ba" takai maganar tana murna shikam baba mijinta fita yay yana dariya.
Itakam nafisa ɗakin tai tana dariyar itama dan umma ta bata dariya wannan gigitar haka.
Sauya kayan jikinta tai amman still kamshin mayen turarensa yana manne cikin kayan nata rungume kayan tai tana lumshe idanunta tanajin wata irin kasala na saukar mata wadda ta kasa gane kota maye.
Adaddafe ta sauya kaya, kana ta fita seda tai alwala tai sallar magariba sannan ta fita suka fara shan ruwan wanda seda baba ya siyo mata ayabar sannan aka zauna lafiya.
Da ɗaya a hannunta tai cikin ɗaki ta kwanta bisa gado tana kallon rufin ɗakin da haka aka kawo nepa da ƙyar ta tashi ta kashe ƙwai sannan ta kwanta tana jin yadda cikinta ke motsi tamkar ze bito duniya.
"Watakan kaima kaji hannun dadynka ko shine xaka damen" tai wannan maganar kamar cikin nata naganin ta tanayi tana cin ayabarta hartai bacci ahakan.



"Wannan zata shafa a ƙafar wannan kuma zata sha kafin ta kwanta, Amman but gaskiya wannan fa na masu cikine ALLAH sa dai hidaya ta samu karuwa ne".
Dr safiyan yakai maganar bayan ya zuba masa maganin a ledar.
Shikam kamar ze kaiwa safiyan maka haka yakejin kansa waftar ledarma yay kana ya saka kai ya fita a office ɗin tamkar ze tashi sama.
"Ikon ALLAH Nifa idan wannan yana wani abu wataran har dariya yake bani komai cikin zafi". dr safiyan yakai maganar yana dariya kasa kasa ganin bai gama fita ba karya dawo ya sauke masa kwandon
Wayarsa ke ringing! ganin mai kiran yasa yaja ya tsaya ya rabe awani kwana gudun kada wani ya gansa, sannan ya dauka maamah ce cikin alkunya gami da kara gefe guda kuma tsantsar damuwa dashi, take tambayarsa ina ya tafi tun ɗazu bata gansaba? amsa ya bata dayana asibiti amman gayanan zuwa gidan yanzu.
Cikin zafin nama ya mayar da wayar cikin aljihun jc ɗin kana ya cigaba da tafiya.
Abakin mota ya tsaya yana kokarin ya bude.
Yana kuma ayyana yar rigmar nan tai bacci may be, ko yaya zata masa kwatancen inda take oho? gashi ba,a son tashinsu idan suna barci, amman dole daman yaje yaga inda take ayau sabida zuwa gobe asan abunyi.
Wani irin duka gabansa yay lokacin daya bude kofar motar yaga ashe babu key, gashi kuma bai ganta ba.
Haka yayta faman lalube tamkar wani zautacce har bakin gate yaje yana faman baza ido kamar ze hauka.
"Lahhhhh wanake gani kamar ƊAN MAJALISARMU" yaji saukar muryar wasu dandazon samari a kunnensa cikin axama ya koma da baya ya fada mota ya fice daga asibitin ganin za,a tara masa mutane.
ALLA kaɗai ya kaisa gida lafiya amman tsananin tashin hankali ya gansa.
Part ɗin mama ya yada zango ya zauna tamkar yaro karami yana mata bayani yana ƙwallar takaici.
Seda yagama mata bayani sannan ya dubeta.
"Wallahi mama dana ganta kota haihu ko bata haihuba sena karbi abuna"......!
54 - 55

Ɗan nisawa maamah tayi kaɗan cikin zulumin wannan cakuɗaɗɗan yanayi da ɗan nata yazo mata dashi sannan ta ɗago ta dubesa.
"Kai yanzu idanma ta baka ɗan ko ƴar mizakai dashi ɗanda ba akan sunna aka sameshiba?".
Ta kai masa wannan tambayar tana mai tsareshi da idanunta.
Wani irin ɗaci yaji acikin zuciyarsa jiyake tamkar zuciyarsa zata faso a wannan karon.
Kuma yanajin itaɗin ce kaɗai zata iya kallonsa ta gaya masa hakan batare daya ɗauki matakin komaiba.
Ɗan cije ƙasan laɓɓansa yay kana ya ɗago rinannun idanunsa waɗanda daman tun can da kalar hakan ya shigo gidan dasu, tare da zuba mata batare daya tanka mata ba illah hucin dayake fesarwa kaɗai.
"Magana nake maka idan baka da amsa ni wuce kabani waje".
Takai maganar bayan ta maka masa wata katuwar harara.
Bai ce mata komai ba illah mikewa dayay tsaye tare da barin ɗakin nata cikin wani irin yanayi.
Itakam mamah tai masa hakan ne badan bata karɓi ƙaddararsu ba tai masa hakan ne domin ta nuna masa cewarfa ba komai ake samu ta sauƙi ba koda yay nasarar amsar ɗan daga wajan yarinyar tofa akwai wani ƙalubalen agabansa.

Tamkar bugagge haka yake haɗa hanya adai dai kwanar dazata sadashi da kofar fita, sukai kiciɓus da anty, cikin zafin nama, anty tasha gabansa tana mai tsareshi da idanunta.
"Ɗan gidana lafiya naganka ahaka?"anty takai masa wannan tambayar tana jinta acikin matuƙar damuwa.
Zama yay ragwajaf akan ɗaya daga cikin Royal ɗin falon tare da sada kansa ƙasa yana yamutsa sumar kansa, ganin haka yasa anty tai maza ta shiga kicin, ruwa mai sanyi ta ɗibo masa, acikin glass, cup tare da zuwa gabansa ta miko masa.
Batare da yayi musu ba ya amshi cup, ɗin ya kafa a bakinsa bai kuma direba seda ya shanyesa tass.
Sannan ya sada kansa a ƙasa yana jinsa acikin wani irin bakin ciki marar misaltuwa acikin xuciyarsa kuwa yana ayyana ALLAH kai ka jarabcen da wannan ƙaddarar kuma na amsa da hannu biyu koda duk kowa ze juyamin baya akan wannan kyautar dakamin to nifa na amsa kuma ina godiya gareka ubangijina.
"Azubo maka tuwo?"
Yaji saukar muryar anty kunnensa tana yi masa magana cikin damuwa, amman yasan duk damuwar dazata shiga bazata taɓa takurashi akan ya gaya mata meke damunshi ba sabida tasan halinsa mutum marar son tambaya.
Ɗagowa yay ya dubeta sannan ya girgiza kansa alamun a,a.
Itakam anty zama tai sabida tasan tunda yace baya bukata tofa hakanne.
"Muhammad meyake damunka?"
Takuma tambayarsa akaro na biyu.
Numfasawa yay kana ya ɗago ya dubeta batare daya ɗauke idanunsa akantaba ya soma labarta mata dukkan abinda ke faruwa.
Sosai ta kaɗu da wannan bayanin nasa amman seta basar tare da ɗagowa ta maka masa harara.
"Amman shine baku taɓa sakani acikin wannan maganar ba koko kuna zargin zan muku ba dai dai bane ba aciki?"
Awannan karon ranta ya ɓaci sosai.
Lumshe idanunsa yay kana ya ɗago ya dubeta.
"ALLAH ya huci zuciyar anty na duk a tunanina maamah zata gaya maki wallahi ban san baki saniba ni ayy".
Yafaɗi maganar iya bakin gaskiyarsa dan duk tunaninsa maamah ta shaidawa anty komai.
"Nikam bata gayamin hakanba, amman miyasa maamah zata faɗi hakan bayan ita da kanta tasan ƙaddara bata bar komaiba, mukam har suna zamuyi insha ALLAH ban da ALLAH waze baka ɗa".
Takai maganar tana jin mai farin ciki aranta tare da jin tausayin sa sosai yadda taga yaɗaga hankalinsa akan wannan haihuwar tasa.
Zama sosai anty tai tare da dubansa tana gaya masa maganganu masu sanyi tare da bashi shawara sosai akan hakan.
Kuma babu laifi yaji ya sami rangwamen wasu tarin damuwar acikin ransa sannan ya miƙe yay mata sallama ya tafi part ɗinsa.


Anty yana fita ta kwantar da zuby wadda tagama rigimar bacci sannan tai part ɗin maamah.
Sallama tai mata cikin nutsuwa sannan suka gaisa kamar ba kishiyoyiba abin sai san barka.
Anan anty ta zayyanewa maamah komai sannan ta ɗora da nuna ɓacin ranta akan yadda basu gaya mata maganarba.
Itama maama acikin ranta mamakine fall na yadda anawar bai gayawa anty ba lallai ta yarda ɗa da mahaifi se ALLAH.
Seta ɓoye laifinsa ta nunawa anty ita kunyar sanar matan take wanda ita ai yadda take ganinsa shida anty suna shiri duk atunaninta yariga daya gayawaa antyn tuni amman shi ashe bai gaya mata ba.
Sannan ta ɗora da cewa.
"Umman zubaida". ( sunan da mama ke kiran anty dashi kenan )
Abinda yasa na gaya masa wannan furucin na ɗazu naga sam wannan yaron baya tuna yarinyar nan data ɗauki rainon cikin harta haifesa shikam kawai a kullum burinsa ya karɓi abunda ta haifa wanda hakan sam banga adalci acikin lamarin ba wannan dalilin yasa na soma nuna masa rashin amincewata tuni sabida nasan ɗacin raba ɗa da mahaifi kasancewata uwa".
Maamah takai maganar tana kallon anty.
Itakam anty sada kanta tai ƙasa sannan ta ɗago ta saki murmushi kana tace.
"Adai sassauta mana maaman imran dan ALLAH kada abin nan ya hadewa ɗan gidana shi ɗaya ki barsa da tashin hankalin neman wannan yarinyar, kina fa kallo duk san sa da aiki amman yanzu bai fiye fita ba sedai ya saka yaransa pls mamah muhaɗu mukwantar masa da hankalinsa ALLAH ya shige mana gaba baki ɗaya".
Takai maganar tana duban mama. wadda tai burus kamar bata jinta, amman sarai tana jin antyn itadai tsarin daya ɗaukone bai mata ba akan mi zaka nemi raba ɗa da mahaifi.
Daga wannan maganar kuma suka faɗa wata hirar daban.
Se can dare anty tabar part ɗin mama ta nufi nata part ɗin.


Shikam yana zuwa part ɗinsa ya hau sama direct bathroom ya nufa cire kayansa yay kana ya sakarma kansa ruwa na tsahon mintuna 30 Sannan ya fito daure da tawul, agurguje ya shirya kansa cikin farar jallabiya tare da komawa toilet ya ɗauro alwala, yazo ya tayar da sallah, ko acikin sallar tasama addu,a guda yake nanatawa ALLAH ya bayyana masa ita cikin koshin lafiya.
Sanin hidaya bata nan yasa ya shiga kicin da kansa ya haɗa ruwan lipton zallah yazo ya zauna a falo yana sha.wanda da iya shi kaɗai yay buɗa baki,Sannan ya kuma kowama bedroom ɗinsa ya tube jallabiyar ya haye kan gado yana ayyana yadda suka haɗu ɗazu jiyake tamkar yay tsalle ya gansa agaban ɗansa ko ƴarsa.
Cikin haka baccin gajiya ya kwashesa.


Kimananin sati biyu kenan yana faman zaryar neman nafeesah agarin nasu amman ya nemi ko mai kamarta ya rasa.
Hatta hidaya data dawo ta kasa gane kansa haka zalika su oska sun kasa gane kan uban gidan nasu.
Damma ALLAH yayosa mutum mai barin abu arai ahakanma yana aje neman nata yay abun dake gabansa amman ana ce maka magariba tayi tofa dabino da ruwa kaɗai yaka iya sha daga nan se yawon neman nafi.
Baya dawowa gida seyay asham daga nan ya wuce part ɗin mama wadda yanzu ya koma mata tamkar bebe daga gaisuwa yake jan bakinsa ya tsuke wanda yake matukar bata tausayi ba kaɗan ba.
Ahaka har azumin yazo karshe karshe anwar yana faman bulayi amman babu nafi babu alamunta.
20 ga ramadan dai dai, suka ɗaga umara dukkansu harda su anty hidaya da sauran ƴan gidan.


Ɓangarenta.....!!
56 - 57


Ɓangaren nafisa.

Sosai ta mayar da hankalinta akan ibadunta sakamakon ƙaratowar ƙarshen wata mai daraja.
Kuma bata fasa yin azumin nata ba, duk da umma sahura ba son tai ɗin take ba amman ita kam bata, fasa ba kullum setayi azumin nata.
Gefe guda kuma ga watan haihuwar ta ya ƙarato sosai cikin nata yake sake yin wani irin girma na fitar hankali, yanzu idan ka dubeta sau ɗaya seka tausaya mata sabida yadda cikin nata ya turo gaba kamar wadda zata haifi ƴan uku.
Ga ƙafafunta sunyi wani irin kumburi tamkar zasu faso gaba,amman idan ka dubeta ta rame sosai sedai girman cikin kawai amman babu ita sam.
Sabida itafa a kullum ta kwanta babu abinda take tunani se yadda zata fara nakuda sabida taji ance akwai wahala abun babu sauki ko guda.
Haka aka cigaba da gudanar da azumin dukkan alummar musulmi sun mayar da kai akan ibadunsu domin rabauta da ramahamar ubangiji.
Haka zalika umma sahura ta samu ta kammala dukkan ƴan ƙananun siyayyarta ta haihuwa hatta bawon wanka ta saya hatta rezar daza,a yankema jaririn cibiya seda ta kammala siya ta aje waje guda.



Saudiya.

Tunda suka sauka acan ya tare a masallaci babu abin da yake se faman bautar ubangijinsa, babu dare babu rana hatta su maamah sedai su haɗu dashi a bakin harami haka lokaci yayta tafiya har ALLAH ya kawo karshen azumi ana ya gobe sallah jirginsu ya dira a kasarmu nigeria.

Sosai ya sami yan tarba da yawa duk da zuwan nasu na darene haka suka tattara sukai gida daga airport.

Yana kuma ji acin ransa ALLAH ya amsa addu,arsa domin tunda yaje yake addu,ar akan ALLAH yasa komai yazo masa cikin sauki agame da lamuran wannan yarinyar.

Itama mamah addu,ar tata kenan haka zalika anty tana wannan addu,ar dama wadda ta dameta.
Itakam hidaya addu,arta ALLAH ya bata haihuwa itama duk da ba wannan ne zuwansu na farko ba amman suna kokari duk ramadan idan sunje addu,arsu tafi yawa saboda garaɓasar watan.

WANNAN KENAN.

Yau ta kama ana yi gobe sallah tunda yamma baba ya kawo kajinsa guda biyu manya, tafasasu umma tai sannan ta soya, lokacin nafisa ita kuma tana ɗaki tana tsifar kanta sabida taci burin koda azaune ne setaje sallar idi.

Tana gama tsifar ta fito waje ruwa ta ɗiba tare da saka shamfo ta wanke kanta tass sannan ta gyarasa tare da shafa mai kana ta saka ribom.

Ɗaki ta koma ta tattare sannan ta fito waje gaban umma taja ta zauna wadda take zaune tana gyara kayan miyar taushen dazasuyi.

"Umma baba ya kawomin ɗinki?" takai maganar tana kallon umma sahura.
"A,a sedai zuwa dare har hijabin ze taho maki dashi sabida ki samu kije idin tunda kin matsa, amman ni senaga kamar nakudar tsaye kike?" umma takai maganar tana tsareta da idanunta.

"Wallahi umma ni bana komai ki yarda kawai dai ina ɗanjin ciwon mara ne amman shima ɗin ba sosai ba?'.

Murmushi umma sahura tai sannan tace "Ai alamun kamun gida kika soma ALLAH dai ya kawo ta lafiya".mikewa tai da ƙyar tana cije vakinta batare data kuma magana ba tai cikin ɗakinta.

Zuwa wajan sallar magariba umma ta kammala aikin komai har lokacin da baba ya dawo daga kasuwa, bayan ya huta ya mikowa nafisa sabuwar atamfar daya sai mata ta sallah wadda aka ɗinkata zuwa doguwar riga, kuma babu laifi ɗinki yayi kyau se katon hijabinta fari tas har kasa.

Sabida tsabar murna nafisa har kukan daɗi tayi na ganin yadda bayin ALLAHN suke kula da ita sannan tai masa godiya kana ta dibi kayan tai cikin ɗakinta dasu.

Bayan shan ruwa ta samu ta lallaɓa umma ta fita zuwa bakin layin tasiyo lalle awani gida sannan tazo ta haɗa ta ƙunsa a hannunta, ita dai umma dariyar nafisa kawai take tana mamakin yadda take abu tamkar yar yarinya karama.

Haka dare ya tsala garin ALLAH ya waye, wajan karfe takwas dukkan wani aiki umma sahura ta kammala shi tass, hatta tuwon gidan ta kwashe ta share ko ina.

Itakam nafisa tana gado tana barci bata ma san gari yay haka ba seda umma sahura taje ɗakin ta tayar da ita sannan ta mike tana mamakin yadda lokaci yaja.

Bayi ta nufa tai wanka sannan tazo seda taci tuwo sannan ta shirya cikin farin ciki.

Tana kammalawa umma sahura ta fito, itama tai shirin masallacin sannan, suka hadu da nafisa baba ma ya shirya sabida baki ɗayansu zasu wuce babban masallacin garin.

Karfe takwas da rabi suka fito kowa yaci gayunsa baba ne ya kullo gidan sukuma suka wuce zuwa titi domin tarar baburin dazasu hau.

Yau take sallah dukkan alummar musulmi suna kokarin shiryawa domin fita yin sallar idi, daga gefe ɗaya kuma mata suna gida suna faman haɗa girki, wannan lamarin shiya kasance dasu umma sahura da baba da nafisa wadda take taka kafarta daƙyar haka suka ɗunguma suka shiga napep zuwa babban masallacin dake cikin garin ɗawisu.

Koda suka sauka ran umma sahura ya ɓaci sabida yadda mutane sukai tai mata magana akan yaya tabar nafisa ta fito da wannan tsohon cikin haka.

Abinda yasa ranta ya ɓaci sabida ai seda tace mata kada ta fito amman ta kafe aikuwa sunsha magana wajan jama,a wasu na mata sannu wasu naiwa umma fada sabida yadda cikin ya koma yay wani irin mahaukacin girma.

Haka baba ya nufi bangaren maza sukuma sukai na mata wadda sallar ma se a zaune nafisa tayita.

Ana idarwa ta shafa addu,arta sannan ta soma kokarin ɗagowa.

Cikin mamaki taga wata farar mace mai kyau ga yarinya agefenta tana kallonta.
"Sannu kona tai maka maki?" cewar matar wadda taketa faman bin nafisan da kallo.
Da murmushi asaman fuskarta tace.
"A,a Umma zan iya bara ma kig.....kafun ta karasa taji mararta tai wata irin murɗawa cikin azama wannan matar tayo kanta tare da fara ce mata sannu cikin kiɗima umma sahura tana can gaba ga jama,a sunata tururuwar fita ganin haka yasa matar ta kwaɗawa ƴar budurwar dake gabanta kira.
"Shahida! maza ki ɗaukarmin zuby ki kama afra ku fita wajan su maamah ganinan zuwa".
Takai maganar tana tallafo nafisa jikinta wadda baki ɗaya tafara fita a hayyacinta dan da alama nakudar ce tazo ganga ganga.

Da dubara ta kamata sukai waje can wajan wata bakar mota ta nufa da nafisa a tallafe ajikinta tana faman zubda ƙwalla.
Itakam umma sahura tana can tana faman bulayin neman nafisa tana kuma tambayar mutan wajan ko sunga yarinya mai tsohon ciki.
Da ƙyar ta sami wadda tace aikam taga wata mata da mai ciki ajikinta sunyi waje.
Tun kafin ma matar ta gama fada umma sahura tai wajan aguje.
Wanda kuma a dai dai wannan lokacin maamah tabawa driver umarni akan asaka nafisa a mota su tafi asibiti.
Anty wadda take tallafe da nafisa data soma jijjiga kamar mai iska ita ta tallafamata suka shiga motar driver yaja sukai gaba cikin sauri.
58 - 59


Turus umma sahura tai tamkar wadda tai losing control ta ɗora hannu aka zata zuba ihu!

Cikin wannan yanayin sega shahida tare da hidaya sun nufo gaban ɗaya motar zasu shiga.
Cikin azama umma sahura tayo garesu ko gaisuwa bata tsayaba ta soma rokarsu akan suyiwa ALLAH su kaita wajan waɗannan mutanan.......tai masu bayanin komai kuma cikin sauki shahida ta gano komai saboda agabanta akai dan haka suka sakata a cikin motar tasu driver yaja suka tafi, amman a gida aka aje hidaya dan itakam tace bazata jeba tana da aiki agabanta

Shahida da umma sahura sune suka wuce asibitin.


Yana sanye cikin wata dakakkiyar farar shadda tass wadda tasha ɗinki sarauta ya zuba hula wadda ta dace da kayan jikin nasa daga kafarsa kuwa takalmine na zallar fata rufaffe, hannunsa yana ɗaure da agogon zallar azurfa mai uban kyau, gaskiya bakaramin kyau yay ba abin se son barka.
Fuskarsa babu abun da take illa daukar idanu tare da sheki da walwali,gefensa jama,a ne fal haka zalika ga ƴan jaridu dama sauran masu kafafen yaɗa labarai sunata faman daukar fitowarsa daga sallar idi tare dashi akwai mai girma governor, bayan sa mai martaba sarkin ɗawisu, damasu faɗa aji acikin wannan garin babu abin da ake awajan face gaisuwar girma da mutunci.

Sun ɗauki manyan lokuta suna faman gaisawar wadda hatta ciyamomi seda suka halarci wajan haka zalika shugaban jam'iyarsu shima ya sami halartar sallar wadda wannan gaishe gaishen shine ya cinye masa manyan lokuta a wannan masallaci.

Seda tawagar mai girma governor, tabar wajan sannan shima ya samu ya yakice jikinsa da ƙyar ya nufi mota, bayan ya gama.wa jama,ar wajan ɓarin naira.

Dagashi se oska acikin farar motar tasa kirar wannan zamanin ko driver bai daukaba yau haka kawai yakejin gavansa yana faɗuwa.
Guards ɗinsa ya dakatar tare da ce masu kowa yaje ga iyalansa yau take sallah suyi zarafin gabansu.
Bayan ya bawa oska kudi masu kauri ya rarraba masu.

Haka ko wannensu ya nufi gida yana yaba halin mai girma mas! na mutuncinsa da adalcinsa da kuma sanin ya kamatan sa.

Yana daga bayan motar yana jingine da jikin kujerar, oska yana gaba yana driving.

Wayarsa ya zaro daga cikin aljihun wondon farar shaddar dake jikinsa ,yana son yaje can family hause ɗinsu ya gaisar da kakanninshi wannan dalilin yasa ya shiga contact ɗinsa ya lalubo number maamah dan yay mata barka da sallah kafin ya dawo gidan.

Cikin kasa da murya kamar ko yaushe ya dubi oska.
"Kawuce dani gidan innah"
Cikin ladabi oska ya rissunar da kansa yana kuma sauya akalar motar tasa zuwa unguwar kakannin na uban gidan nasa wanda, aka haifi mahaifinsa acan.

Wayar mamah hartai ringing! kusan uku bata ɗaga ba hakan yasa ya kira

Please Login or Register in order to submit comment