Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

antashi da rashin wuta ga rana dole seka samu kankara zaka zauna lafiya.
46 - 47


*Wannan shafin kacokan sadaukar wane gareku ANTY ƊAN ASI, FATIMA ALI ADAM, FA'EEZATION, JAMILA AZI, FATIMA AZARE, ANTY RABI ADO,HALIMA UMAR OGA, ZAINAB DA ZAINAB, HALIMA MADOU BAMA,DAMA SAURAN DABAN LISSAFOKUBA, KUJI DAƊINKU DA WANNAN PAGE ƊIN SON SO DOMIN ALLAH* 💅💅💅


*JIN DAƊI GAREKU MY S.P FANS MUSAMMAN AMINA NADAMA, HAUWA A CHINDO,MAMAN BAFFA, ALHAJI KABIRU, NAFISAT BASHIR,ANTY HAMIDA, DA SAURAN DABAN LISSAFOKUBA KUSANI INA MUKU SONSO DOMIN ALLAH* 💅


Tawani baje a tsakar gida akan tabarma tana tsintar shinkafa ƴar hausa, wadda da gyar tagama tsince baƙi-baƙin Cikin nata sannan ta busheta kana ta mike da gyar tana dafe saman cikinta sabida yadda cikin nata ya tutso gaba sosai kamar yau zata haihu.

Ta dafe wani ɗan tudu na gefen wajan inda suka adana turminsu, kana ta soma tafiya kamar zata faɗi ƙasa, zaman daɓaro tayi abakin rijiya bayan ta debo ruwan da gyar ta zuba a saman shinkafar wanda ya baiwa wannan ɗan mataccen ƙuntun damar watsuwa zuwa sama.

Sannan ta wanke hannunta na dama, ta soma yamutsa, shinkafar ma,ana tana cuɗa dattin cikinta, seda tai mata ruwa mai kyau har wajan biyar sannan ta zubata a ƙwalanda, domin taɗan sha, kasancewar shinkafar hausa tanada saurin damewa idan ba,a kulaba.

Takai wajan minti goma a wajan sannnn ta ɗibi, ruwan dake cikin wani bokiti, ta watsa a saman kanta jin kan nata ya dauki zafi. sannan ta mike da ƙyar, ta dauki wannan shinkafar tai hanyar kicin da ita a hannunta.

Leƙawa ɗakin umma sahura tayi bayan ta aje shinkafar a saman bencin dake adane acikin kicin ɗin, ganin tana kwance tana hutawa yasa ta jamata labule ta koma bakin aikinta wanda sam umma sahura bata so amman itan ta kafe sabida dokar da likita ya bata akan tana ɗan yawan motsa jikinta sabida koda naƙuda tazo mata kan ɗan baze wahalar fitowaba, wannan dalilin yasa duk bayan magariba ma take ɗan tattakawa zuwa bakin titin buxuwar ɗawisu, da ƙafa ta kuma dawo da ƙafa.

Kicin ɗin ta shiga ta zauna a saman kujera ƴar tsugunno sannan ta saka hannunta ta bude marufin tukunyar, wadda taketa zaɓal,ɓala alamun ta tafasa. kana ta soma zuba wannan shinkafa cikin nutsuwa.

Sannan ta rufe bayan ta saɓa marufin saboda, in case koda ze tafaso ya watso sama.

Zafine ya dameta abinka da kicin ɗan mitsitsi ta fito waje tare da ɗauko ledar salak, ta soma fito dashi tana gyarasa silla-sillah.seta da gama tsaf sannan ta miƙe ta dauko, gishiri da wuƙa ta nufi gaban rariya seda ta wankesa tass sannan ta koma ta zauna ta fara yankawa bayan ta gama yankawa nan ma seda ta kuma ɗaurayesa sannan ta aje acan saman bancin dake kicin.

Alokacin shinkafar ta fara watsowa sama tana kumfa, kwando da wani ɗan bokiti ta dauko ta fara kwasheta bayan taɗan saka hannunta ta latsata alamun taji yanayin laushinta. sannan ta kwasheta ta zuba a kwandon kana ta ɗauraye wannan ruwan mai kamar sitati. kana ta mayar da ita tukunyar domin ta turara, anan ta zauna tsahon wasu ƴan lokuta har shinkafar ta ƙarasa kana ta kwasheta ta zuba bisa kula, sannan ta soma kiciniyar haɗa miyar jajjage wadda ta wadata da kifin da mijin umma ya kawo ɗazu.

Seda ta kammala komai wanda ya shafi hadin miyar sannan tai kasa da rishon kana ta komo waje ta zauna akan tabarma tana firfita da maficin gabar dake kusa da ita, jin jikinta yana wani irin ɗigar da zufa wadda tunda cikinta ya tsufa take masifar jin wannan gigitaccen zafin mai haka ka.

Tana nan zaune aka soma gabatar da tafsirin da ake a masallacin dake kusa da gidan lokacin take tunanin karfe biyar ɗin yammaci tayi, cikin dauriya ta koma kicin ta kashe rishon sannan ta nufi ɗakinta wata doguwar rigar atamfata ta dauka ta sauya sanan ta dauki katon hijabi ta zura kana ta ɗauki ƴar jakar datake aje ƴan kuɗinta,wanda baba yake bata a yayin daze fita kasuwa.

Ta zira wani bakin takalmi marar dubu, hannunta ta saka ta kare cikin nata sabida kunyar fita haka take gashi yay wani irin girma wanda ya kasa buya acikin hijabin nata, duk da ALLAH ya taimaketa anan ɗin babu wanda yasan cikin bana halak bane ba sabida unguwar kamar kazo nazoce babu ruwan wani da wani, kauye kuwa gidansu wajansu kaka daman tunda akai wannan rikicin babu mai zuwa nan ɗin bare taji wata magana marar daɗi gwarama kaka tazo sau biyu, wanda da kuka suke rabuwa idan tazo ɗin.

Kuma duk zuwa takan zo mata da ƴan kayayyakin amfani, sabida acewar kaka hannunka baya ruɓewa ka yanke kayar, duk tsiya itaɗin jinin tace.

Dawanan tunanin ta share hawayen daya zubo mata kana ta fita tsakar gida.

Da umma sahura sukai kiciɓis tana kokarin fitowa daga ɗakinta.

"A,a nafi ina zakuma kije kina fama da kanki, nifa bamma so kikai azumin nan ba amman kin kafe yaya zanyi?". matsowa tai gareta sannan tace.

"Zanje babban titi na samo kankara dan wallahi bazan iya shan ruwa babu sanyi ba umma sahura bakiji yaddq cikinnan ke mini ba".

"A,a ki bari malam yazo seya je ya samo kekam kina fama da kanki ina zakije a haka".
Murmushi tai sannan ta kuma kallonta.
"Tabb nikam garau nake hajiya duba ma kiga babu abinda ban makiba kawai koma ki kwanta" takai maganar tana dariya dayake daman wataran kamar jika da kaka suke idan suna wata dariyar ma seka rantse batada wata damuwar wadda ita umma sahura tana hakan ne domin ganin ta mantar da ita bakin cikin dake cikin ranta.

Itama umma sahura dariya ta saka sannan tai saurin shiga kicin, ɗin da sauri tana duba tukwanan cike kuma da ɗumbin mamaki ta fito waje.

"Ke ƴar albarka wadda aka haifeta a yayin da tsiya ta kwanta ubangiji ya baki mijin arziki yadda kikai min kema rabbana yay maki fiye da hakan yakuma rabaki da abinda yake cikin jikinki lafiya". takai maganar cikin tsananin murna tare da yaba ƙoƙari irin na nafisan.

Itakam dariya take sosai a wannan karan sannan ta dubi umma, "kai umma wannan addu,a haka to nagode ALLAH ya amsa sena dawo".

Tafaɗa tana jan kafarta wadda ta ɗan soma kumburin ɗaitar haihuwa, tai waje ganin garin ya soma lumshewa da alamun hadarin daya haɗo tun asubahi yana shirin zubar da ruwa, kuma tasan muddin umma sahura ta ankara da wannan hadarin bazata barta ta fitaba.

Cikin tsannin dauriya gami da hakuri irin nata take taka kafafunta.

Har ALLAH ya kaita bakin titi lafiya sannnn ta samu mai napep.

"Malam babban titi?"

"To naira talatin zaki bada hajiya".

Ɗan murmushi tayi "Tom babu damuwa ALLAH ya kaimu lafiya".tafaɗa bayan ta shiga cikin baburin.

Tafiyar mintuna goma ta kaita babban titi ta sauka ta basa kudin sannan ta nufi wajan ƴan ƙanƙara wadda ake zubota a irin katon buhun nan wadda ba,a yarda ashataba sedai a zubata acikin ruwan sanyi ya sanyaya da ita.

Abakin wajan ta tsaya "Assalamu alaikum malam kan kara nakeso ƴar naira ɗari da hamsin". tafaɗa tana zaro kudin ta mika masa ya amsa ya bata bayan ya saka mata a bakar leda sannan ta karɓa ta fita daga wajan.

Wajan masu saida kayan marmari ta nufa sabida tana bukatar ayaba zata haɗata da kwakwa ta markaɗa ta zuba mata kankara haka kawai yau take marmarin yin hakan.

Tana tsaye a wajan tana bada kudi aka soma wata irin iska mai ƙura gami da duhu, a gurguje ta amsa sannan ta nufi hanyar titi ganin har an soma yayyafi kaɗan-kaɗan.

Kafin takai titin ruwa ya kece wata yar rumfar kwano ta samu ta laɓe cikinta ga ruwan duk ya jika mata jikinta.

Ganin jama,a kowa yanata kama gabansa masu shaguna suna rufewa guri ya soma tsit! yasa tai ta maza tanajin gwara ta sai maganin mura akan ta zauna anan ita ɗaya, ga tsohon ciki bata son umma sahura ta ɗaga hankalinta.

Tafiya tai kaɗan ta isa bakin titi tana aje kayanta a gefe guda taja ta tsaya tare da tsirawa ƴan motocin da suke wucewa tsilla tsilla idanu.

Yau tunda ya tashi baya jin daɗin jikinsa sabida kwana biyun nan da baije wajan training ba seyake jin kamar ana masa duka acikin ƙashinsa, yau an tashi da rana ga azumi hidaya bata nan tun jiya tana wajan mahaifiyarta wadda bata ɗan ji daɗiba, shiryawa yay cikin red j.s waɗanda sukai masa matukar kyau tare da farin kwambos, sumar kansa ya gyarata tai wani irin kyau mai burgewa, ga kayan jikin nasa sunyi masa mugun kyau abinka da farin mutum.

Rigar j.s ɗin mai kajeran hannun ce seya saka fara mai dogon hannu ta cikinta wadda take da tsukakken wuya, dogon wondon j.s shima ya zomasa har ƙasa kasancewarsa mutum marar son fidda jikinsa waje.

Cikin sauri yake fita daga part ɗin nasa, ya nufi harabar gidan ya faɗa mota ya nufi A & A ƊAWISU TRAINING PLACE. wajene da aka zuba kayayyakin motsa jiki kala kala harda ma wajan da aka ware domin mai buƙatar buga ƙwallon kwando kota ƙafa da dai sauran kayan motsa jiki, wanda wajan ya kasance na se wanda ya amsa sunansa acikin wannan gari ze halarcesa duba da yanayin tsaro da kuma tsadar wajan.

Bai wani jima ba kasancewar garin ana azumi ba kowane ma ze iya motsa jikinsa a wannan lokacin ba, shima sabida wannan nukurkusar ƙashin nasa yasa ya fito a wannan lokacin.

Ya fito daga wajan yana tsane kansa da wani farin towel wanda baki ɗaya jikinsa ya gama jika da zufa. sannan ya bude motarsa ya wurga towel ɗin kana ya fito da ruwan gora, ya wanke fuskars dashi sannan ya tube rigar sa ya wurga baya, ya rage dagashi se wannan farar ta ciki wadda ta fito da ainihin surarsa ta cikakken namiji maji karfi da lafiya.

Hanyar babban titi ya ɗauko sabida itace privacy seyafi tafiya cikin salama sabida karancin jama,ar wajan.

Ganin wani irin baƙin hadari ya haɗo a garin yasa yaɗan sassauta tuƙin nasa yana bi cikin salama.

Ruwanne ya kece kamar da bakin ƙwarya.

Tundaga nesa yake hango, kamar mutum a tsaye ruwa na faman dukansa ga hanyar kamar babu kowa.

Harya kai can gaba sekuma ya fara revars yana dawowa da baya, daga can ɗan nesa da ita ya tsaida motar dayake glass ɗin mai tintak ne shiya basa damar gane macece.

Cikin tausayi ya kashe motar sannan ya bude marufin motar ya fito waje duk da ruwan yana jikasa amman shi burinsa ya taimaketa, saboda wannan ruwan shi namiji ma yana jinsa bare mace wadda yake ganin kamar ma tana daukene da juna biyu.

Ita kam nafisa harta gaji da tsaiwar ga ƙafarta ta ƙara yin yimm sosai.

Sam bataji ƙarar tawowar mutum ba sedai kawai ganin sa tai tsaye akanta kamar hoto.

Shikam tsananin mamakin daya kusan kaisa ƙasa yaja ya tsaya yana kallonta jinsa yake kamar a mafarki sosai yaja ya tsaya yana binta da kallo ga ruwan na dukansu duka su biyun wanda daga nasa ɓangaren ma hatta sumar kansa ɗigar da ruwan takeyi.

Jin kamar anan kallonta yasa ta ɗago kanta cikin tsananin tsoro..


MANAGE🙏
48 - 49


Cikin wani irin tashin hankali firgici da tsantsar tsoro mai cike da wani irin rawar jiki, feenah ta ɗago tana kallonsa cike da ɗunbin mamaki.

Bakinta har yana rawa wajan furta kalmar "WA'INNAHU SULAIMANU WA'INNAHU BISIMILLAHIRRAMANIR RAHIM". Tana kuma dire kalmar ta soma jan ƙafafunta dasuka soma wata irin karkarwa kamar zasu ɓalle.

Gam-gam taji saukar hannunsa akan nata ya riƙe tamau rikon tsauri rikon da bata isa ta ƙwaceba.

Bakinta ya riga ya gama bushewa haka zalika idanunta babu alamun ruwa ko guda bare asaka ran zasu zubar da hawaye.

Ɗago kanta tai tare da tsira masa idanunta tana kallon yadda ya kafe cikin jikinta da ido kamar mai son gano wani abun.

Baki ɗaya jinsa yake kamar ba,a cikin wannan duniyarba, sabida tsabar yadda ya kaɗu da wannan lamari saka ɗayan hannun nasa yay yana goge idanunsa gani yake kamar suna masa gizo, tare da ɗago idanunsa ya dire akan ƴar ledar dake gabanta, tabbas ƙanƙarace aciki domin gata nan tana faman zubo da ruwa.

Wani irin ɓacin rai gami da tausayi sune suka tsirga masa,yanxun macen datake dauke da ɗansa ko ƴarsa itake tsaye anan ruwa na duka ita ke tsaye anan tare da wannan kazamar kankarar wadda kilama idan tasha tai masa asarar ɗansa.

Hannunsa har yana karkarwa wajan dagosa ya ɗora a saman tsinin cikin nata yana son ya taɓa yaga yes da gaskene cikin ne kokuwa.

Cikin wani irin hargitsats tsan kallo tare da zafin naman gaske, tai saurin saka hannunta ta doke masa hannun nasa sannan ta fara kokarin fincike ɗayan hannun nata daga cikin nasa, amman duk yadda taso yin hakan ta kasa.

"Malam wannan wani irin rainin wayone da rainin hankali zakazo kana kai hannunka kan cikina" takai maganar a dake batare dataji tsoro ko shakkarsaba.

Bai kulataba har seda ya ida nufinsa ma,ana ya shafi cikin nata kana ya ɗago jajayen idanunsa waɗanda nan take suka sauya kamanni saboda wannan kalmar data gaya masa sam baya kaunar rainin wayo haka zalika baya shiri da marar kunyar mutum.

"Ni bake na shafaba ajiyar danai anan na shafa wadda naketa nemanta tsahon watanni ban sameta ba se yau".yakai maganar yana dubanta ta ƙasan idanunsa, yana mamakin ƙarancin shekarunta.

"Ni bansan kaba malam kuma ban gane wata ajiyarka ba ka iya sakarmin hannuna na wuce dan nagaji da dukan ruwa".
Takai maganar tana murguɗa masa bakinta.
Dariyar kin rainan wayo yay sannan ya kuma damƙe hannunta tamkar zata kufce masa.

"Bani da lokacin baki wata doguwar amsa amman ki sani wannan cikin nawane baya da mahaifi seni, cikin da kikai kokarin zubar dashi tunkafin ya bayyana amman tsabar addu,ar mahaifa data ƴan uwa ALLAH ya tserarmin dashi, idanma bakya bukatarsa ni a yau zan maki viza zuwa waje aje aciren ɗana ko ƴata ki tafi abinki nagode ƙwarai". yakai maganar cikin daure fuska babu alamun wasa.

A tsorace ta ɗago da kanta tana kallonsa kamar yau ta soma ganinsa sekuma ga hawaye kamar famfo sun zubo mata.

"Kasani koda zaka kawo dukkan mutanan dake cikin wannan ƙasa akan naje aciren cikin nan wallahi sedai su kasheni, miye halaƙarka da cikina, tunda naje gidanka ka turmusheni ka makamin ciki ka san dashi, se yau daga ganina sama taka zakazo kana min wani magana kaje can da juyar matarka, idan fitsari banzane kazama tayisa mana, haka kurum baka san wani hali na shigaba baka san da yaya na raini cikin ba kawai samataka zakawani ce na baka to baza,a bada ba kai duk abinda zakai" mtswwwwwwwww! taja tsaki tare da fincike hannunta,

Awannan karonne ya ɗago idanunsa ya dubeta tare da sakin murmushin takaici, aransa yana aiyana tun yanzu tafara bani ciwon kai.

Cikin rashin damuwa da furucin nata ya dubeta a karo na biyu, shifa kurari ko firgici bai fiye tsorata shiba, yasha jin Barazana daga manyan ƙwarin dasuka fita waɗanda ma su ta ransa da lafiyarsa suke amman bai taɓa damuwaba bare ya saka hakan aransa hasalima idan suka haɗu awaje yana kokarin jansu ajikinsa ya nuna kamar bai san komaiba bare wannan ƴar wadda bada ban albarkar cikin jikinta dataciba da meze sa ya tsaya da ita.

"Amman dai kinsan bazaki ma kanki cikiba ko?" bai jira amsartaba.

"Niba mugu bane akanki bazaki saka na soma muguntaba, salin alin kibani ɗana nikuma zan gina maki rayuwar da har abada bazaki nadama ba".

"Wannan cikin tunkafin ya fito kowa ya gansa yasan nawane sabida daga zafin naman yadda yake motsi ajikinki da yadda yay girma ai ni yayo babu ko tantama". yakai maganar yana binta da idanunsa.

Ɗan ɗaure fuska tai kana ta ƙwaɓeta kamar xata kurma ihu cikin ranta tana kuma mamakin yaya akai yasan tanada ciki oho?.

"Kaifa babbane agarinnan malam abun kunya bai karɓekaba kabar ni nizanji da dukkan wata matsalar dazan fuskanta banson sunanka ya ɓaci akan abinda nina jawa kaina dan haka kamanta daka taɓa haɗuwa dawata nafisa nina amince zan rike duk abinda ALLAH ya bani cikin nagarta".

Takai maganar tana saka ɗayan hannunta tana sharce ruwan dayake ɗigo mata.

Kallon mahaukaciya yay mata.

"Baki da wayo akan wannan cikin zan iya bada rayuwata bama kujera ba, mutuncin da kike faɗa ze bani ɗane? koko tunda nake kan kujerar ita ta taɓa bani ɗa? to kowa datasa ƙaddarar ni anan tawa take kuma na amsa bana kuma shakkar nunashi aduk inda nake, dan haka kima cire wannan gangancin acikin ranki" yagama faɗin hakan tare da fincikarta ya nufi mota da ita cikin zafin nama.

Ya buɗe gaban motar ya sakata tare da rufowa ya zagaya shima ya shiga.

Hanyar babban asibitinsa ya nufa da ita.

Babu abinda take se kuka harda majina"amman wallahi kai azzalumine kuma duk abinda kai min se ALLAH ya sakaaaaaaaa......"bata karasaba ya bige bakinta da hannunsa cikin ɓacin rai ya cigaba da driving ɗinsa bayan ya kure motar da karar redio.

Dafe bakinta tai kana ta ɗago idanunta "Ina zaka kuma kaini kaimin ciki na farko wani cikin xaka kuma min? dan ALLAH kabarni hakan nan yanzu nasan.............................

Duk inda marikiyata take hankalinta atashe yake".

Murmushi yay mai sauti kana ya ɗan dubeta ji shirme daman antaba ciki kan ciki lallai wannan ɗanyace.

"Inda ALLAH ma ze taimaken na kuma maki cikin kan cikin aida nazama ɗan gata". kawai taji saukar maganarsa a dake akanta.

Wani kukan ta kuma kecewa dashi"na rantse da ALLAH wancan ma tsautsayine amman yanzun da hankalina, daman lokacin ma soyayyar danake maka ita takaini yanzu kuma tunda ina da cikinka nasan ko banza zan sami mai kama dakai ko babu kai atare dani matukar ina kallon abinda zan haifa zanji dadi.

Kallon kuruciya yay mata "ato dakuma kince cikin banawa bane bakima sanni ba, amman gayanan kin tonawa kanki da kanki asiri".mtsw yaɗanja tsaki ganin surutun nata ya soma hawar masa kansa.

Har suka ƙarasa cikin wani katafaren asibiti wanda yaji kayan more rayuwa kamar babu gobe anata zabga kiran sallah, suka ƙarasa ciki. parking ya gyara yana kokarin fita daga motar bayan ya kasheta.

sekuma ya juyo ya tsareta da idanunsa,batare dakuma yace mata komaiba, ya zira hannunsa ya ɗauko gorar ruwa ya miko mata, seda ta karba sannan se kuma ta kallesa.....!

MANAGE.
50 - 51




Taɗan dubeshi tare da kau da kanta gefe batare data amshi ruwan dayake miƙo mataba.
"Ki amsa malama zanje nai sallah kafin nan nai abin da zanyi anan ɗin semu wuce" yafaɗi hakan cikin kaushin murya!.
Tura baki tai gaba tamkar karamar yarinya sannan ta saka hannunta taja ruwan, cikin ranta tana masa ALLAH ya isa.
Kafawa tai abakinta tana faman sha kamar zata haɗa da gorar, shikam ya zuba mata idanunsa yana binta dasu cikin tausayawa batare daya, yi fitar dayakeson yay ɗinba.
Harta gama shan ruwan kana ta dire gorar ruwan tana lumshe idanunta.
Can kuma seta ɗago ta dubesa tare da yatsina fuskarta.
"Ina ayaba ta da ƙanƙarata tunda bazaka kaini gidaba kabani, abuna nasha yunwa nakeji". tafaɗa cikin tausayin kanta.
Shikam tsare ta yay da idanu kamar wani tsohon maye batare dayace mata ci kanki ba.
Can kuma setaga ya bude marufin, motar ya fita kamar, wanda yay mantuwa, tana ganin ya fita ta soma kiciniyar bude motar ta fice, amman ta makaraso sabida ya saka mata key, haka ta kifa kanta akan cinyarta tana kuka! gefe guda kuma tana tunanin yanxu awani hali umma sahura take oho??.
Mintuna kusan biyar segashi nan ya dawo cikin motar amman a wannan karon fuskarsa daɗan ƙasa daga gani sallah yaje yayo ya dawo.
Hannunsa rike da wata ƴar leda mai sheƙi ya miko mata, cikin tsananin, buƙatuwa da yunwa tai maza ta karɓi ledar, kamshin soyayyan dankali mai hade da nama da ɗan taruhu shiya daki hancinta, cike da zalama abinka ga mai bukata ta fara daukar guda ɗaya ta saka abakinta tana kuma kallonsa ta gefen idanunta shikam ko ruwama da alamun bai shaba, sema wayansa dataga ya rike yana faman daddannawa mintuwa kusan biyu taji yana magana.
"Hellow safiyan nifa zan wuce inada abubuwa agabana, kawai ka gayamin drugs ɗin sena, siya base kazo ba naga time ɗin yaja da yawa, gayanan maamah tana ta min waya tajini shuru" bataji amsar dana wayar ya basaba tadai ga ya katse wayar tare da ɗan jan tsaki kana ya saka hannunshi ya yamutsa sumar kansa wadda taci uban kuɗi.
Duk yadda taso ta danne wannan dankalin ta kasa, daman wannan matsalar take da ita, ma,ana ita cikin nan nata yanada wani irin salo, duk abinda ta ɗora ranta akansa tofa idan bata cisaba babu lafiya, wannan dalilin yasa tunda ta dauki wannan dankalin ta saka abakinta takejin amai na taso mata, kamar ze fito mata ta hanjinta.
Tun tana daurewa har idanunta ya fito waje sosai tana kuma zubar da hawaye.
Kakarin amai ta somayi.
Cikin daure fuska taga ya juyo yana maka mata harara!
"Ke bani son sakarci wallahi kikai min amai amota sekin lashe abinki" yafaɗa cikin taking serious batare data alamun wargiba.
Kafin ma yaja wani lokaci ta soma zubo da aman dukkan dankalin dataci ɗin tare da saka hannunta ta dafe wuyanta wanda takejin kamar ze tsinko ya fito, wannan feshin aman kuma har rigarsa ya samu inda ma ALLAH ya taimaka bata zuba masa sosaiba.

Babu abinda take se uban haki da nishi!
Tana firfito da idanunta waje.
Shikam fasta yay yana kallonta baki ɗaya ta gama basa tausayi.
Daman haka masu cikin ke fama jiba daga cin abinci harta maido dashi yana tunanin ma ko ruwan bai zauna a cikintaba.
Seda ta gama aman tsaff sannan ta ɗago idanunta jajir! tana kallonsa kana ta ciro ɗan kwalinta mai kyau ta soma goge wajan hardama kan cinyarta.
Saukar hannunsa akan nata shiya kwance mata dukkan notikan da sukai saura ajikinta.
"Ke bani son ƙazanta da ɗankwalin naki kike goge aman?" yakai mata tambayar yana kallonta.
Bata kulashiba harta kammala sannan ta buɗe, glashin motar ta jefa kallabin kana ta komar da kanta ƙasa tana ƙyafe bakinta.
Can kuma ta dauki, sauran dankalin ta jefa a waje.
"Mizakici?" yafaɗa mata maganar yana mai kusanto da fuskarsa gareta sabida yadda yakejin wani irin mugun tausayin yarinyar daga gani wannan cikin nasa yana bata wahala.
"Ƙanƙarata zaka kawomin".
Takai maganar kamar zatai kuka!
"A,a bazaki sha kankara ba salon ki sakamin yarinya tai mura" yakai maganar still yana binta da ido.
Azuciyarta tana ayyana yadda yake kamar maye yawani tsirata da idanu kamar ze cinyeta domin acikin jikinta tana jin yadda idanun nasa ke yawon kallonta.
"Nidai ita zansha wallahi idan ban shaba bazan iya cin komai ba" takai maganar kamar zata kurma ihu!!
Hannunsa guda ya saka ya ɗago fuskarta yana binta da lumshashshun idanunsa masu mugun kaifi gami da dafi.
Baki ɗaya ta daburce ta susuce jin saukar hannun nasa bisa fuskarta, nishi taɗan ja kaɗan kana ta soma lumshe idanunta tana zubo da ruwan hawaye waɗanda shi kansa yakejin saukar ɗuminsu acikin tafin hannun nashi.
Sam bazata taɓa iya kallonsa ba, shiɗin wani irin mutum ne mai mugun ƙwarjini karyar ka,kaiya hada idanu dashi koda na minti ɗayane bare ka sami damar yi masa kallon kurulla tabbas bazaka iya ba.
Jikinta yana wani irin karkarwa ta saka hannunta guda,ta ture hannun nasa sannan ta cusa fuskarta cikin tsakiyar cinyarta tana sakin gunjin kuka!!.
"Miyasa mutanan gari da kowa ke maka kallon mutum nagari? amman ni miyasa kazama mugu agareni ka cutar dani da yawa sabida kaganni marainiya? koko domin kaga zuciyata mai rauni ce akanka?"
Takai maganar tana kuka sosai.
Tsit cikin motar tai harna tsahon mintuna biyu sannan taji amon muryarsa acikin kunnenta.
"Naannahhhhhhhhh, taji saukar muryarsa pls ɗago muyi magana mi kikeson nai maki?" yakai maganar yana jan Numfashi kamar mai cutar asma.
Mamaki fal ranta,duk duniya malam liman kakanta ɗaya ke ce mata nanah kuma tunda ya rasu babu wanda ya taɓa gaya mata wannan sunan sedai nafisan ta amman shi yau ya kirata da wannan suna dan haka cikin wani irin birkitaccen yanayi ta ɗago fuskarta fall hawaye tana dubatan sa da ita.
Hannun nasa still ya kuma kaiwa kan fuskarta a wannan karon goge mata hawayen dake zubo mata yay sannan ya mayar da kansa saman kujerar motar ya jingina.
Kamar kuma an tsikareshi taga ya sunkuyo zuwa kasa, ƙafarta ya ɗago ya ɗora akan cinyarsa, tare da saka hannunsa yana ja mata yatsun kafafun nata, waɗanda sukai wani irin kumburi, kamar sunja ruwa, wannan dalilin dama yasa ma ya biyo da ita cikin wannan asibitin dan ya karba mata magani lura dayay kamar kafar tata tana bukatar hakan.
"Niba mugu bane ba kamar yadda tunaninki ya baki

Please Login or Register in order to submit comment