Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanunta da sukai jajur ta dubesu "kawu kuyi hakuri kubarni naji da wannan ƙaddarar data sameni amman banajin zan iya zubda cikin jikina wanda kaddara ta samar dashi gwara na bar maku gidanku" tana fadin haka ta saka kuka tana mikewa tai cikin dakin kaka.

Tana kuma jin tausayin kanta "ina zan ganki ummata?" takai maganar tana kifa kanta akan gado tana kuka "na cuci kaina soyayya ta kaini ta baroni gashi ina cikin tashin hankali kai kana can cikin farin cikinka" bataji shigowar umma sahura ba sejin maganarta tai a bayanta.

"Babu komai nafisa nina ɗauki ƙaddara kamar yadda sukace nina kaiki harkikai ciki nikuma zan daukeki na kaiki gidana ki haifarmin shegen na goya idan ALLAH ya saukeki lafiya ni zan dauki ɗawainiyarki data abinda zaki haifa saboda haka ki maza ki haɗa kayanki mubar musu gidansu ni baxan wulakantaki ba".

Cikin mintuna kadan suka hada kaya suka bar gidan wutsiya a zage wanda kaka har lokacin kuka take sukam su baffa yi sukai kamar basusan nafisa ba harda cewa kila halin uwarta tai sukam zuriyarsu babu mai abun kunya.

Haka umma sahura tasakata agaba sukai gidanta nafisa na kuka har suka kai.

Yau kwanan ta kusan biyu agidan umma wanda babu abinda take se tsabar kuka seda mijin umma sahura ya fara yi mata tofi sannan ta soma iya magana ma.


Cikin tsananin tashin hankali walida ta fito daga gidansu kaka bayan tagamajin abinda ya samu feena daga bakin harira wadda ta tsaida ita tundaga soro bayan walidar tazo da shirin biki.

Da kuka walida ta fito tana haɗa hanya ta dauki mashin ya nufi unguwar da ummah sahura take......!



IDAN KUNGA TYPING ERROS KUYI HAKURI....



*AUTAR MANYA*
42 - 43


*MASU FIDDAMIN DA LITTAFI KUJI TSORON ALLAH*



Cikin lokaci kaɗan walida ta sauka a ƙofar gidan ummah sahura, mai mashin ta tsaya ta bawa kuɗinsa sannan ta shiga cikin gidan a gigice.

Da baba mijin umma sahura taci karo yana kokarin fitowa daga cikin gidan, ɗan ja da baya tai kana ta tsugunna ta gaisar dashi sannan ta ƙarasa shiga tsakar gidan.

Sallama ɗauke abakinta ta ƙaraso ta samu umma sahura a tsaye tana bushe gyaɗa, cikin ladabi walida ta rissuna ta soma gaisar da umma sahura.

Kana ta dubeta batare da wani jinkiriba tace "Umma daga can gidansu kaka nake naje akan maganar bikin nafisa, amman senaji wani magana daban marar daɗi. anan ta zayyanewa umma sahura dukkan abin da harira matar ƙanin baban nafisan ta gaya mata.

Sannan ta cigaba tana mai share hawayenta "Umma idan har wannan lamari da gaskene to waye yay mata wannan zaluncin daman wallahi ninaga alamunta tun a school bata cika lafiya ba?" takai maganar cikin sigar tambaya.

Umma sahura bata iya cewa komai ba illa aje gyaɗar hannun nata datayi sannan tajawo hannun walida sukai cikin ɗakin da nafisan take.

Zaune suka tadda ita, ta rafka uban tagumi kallo guda zaka mata kasan tana cikin tashin hankali.

Da ɗan sauri walida ta saki hannun umma sahura ta karasa gabanta tana sakin gunjin kuka! ganin haka yasa umma ta juya tabar masu wurin.

Itama nafisa a wannan karon kukan take sosai mai cike da ma'anoni da dama.

Cikin shashshekar kuka! walida ta soma mata magana "Feeanah garin yaya wannan mummunar ƙaddarar ta samemu waye ya maki haka! waye ya zalunci marainiyar ALLAH wallahi koma waye se ALLAH......." Tai saurin saka hannunta ta rufe mata bakinta.

Sannan ta dubeta da jajayen idanuwanta daman kuma gasu sun ƙara yin wani iri na alamun ciki atare da ita.

"Walida nina jawa kaina wannan ƙaddarar gwara da kika kirata da mummuna domin kuwa mummunar ce agareni. walida soyayya tajamin na kai kaina ga bala'in dayafi ƙarfina a yau zan gaya maki abinda ban gayawa wani mahaluki ba...........sedai ina son ki ɗaukar min alƙawarin da bazaki taɓa shaidawa wani mahaluki wannan maganarba".


Tafaɗa tana tsare walida da idanunta.


"Nai maki alƙawari ƙawata bazan taɓa tona wannan sirrin namuba insha ALLAHU".

Tai maganar cikin gamsuwa....


"Walida na tafka babban kuskure acikin rayuwata.................ta gama bawa walida labarin kaf abin da ya faru a tsakanin ta da mai girma mas! batare data rage kota ƙara ba.

Jan numfashi walida tayi sannan kuma ta ɗan dubi nafisa cikin tausayawa.

"Tabbas kawata kaddararku ce a haka dagake harshi amman bamu san mai ALLAH ya ɓoye acikin wannan lamarin ba kuma nai maki alƙawarin bazan taɓa gayawa kowa wannan maganarba amman tabbas senai dalilin da mai girma mas! yasan da cikinsa ajikinki, amman ko ze kasheni bazan taɓa nuna cewar nasan inda kikeba".

Waro idanu nafisa tai sannan ta dubi walida.

"Walida kada kimin hakan ki tuna matsayinsa da girman sa nasan bazeso wannan abun kunyar daga wajansaba dan ALLAH kada ki futar da wannan sirrin wataƙil ma yasaka a koremu daga wannan garin kokuma yace azubar da cikin wanda nakejin gwara na rasa raina akan a rabani da wannan cikin najikina".

Takai maganar tana kuka!

Dafata walida tai sannan tace.

"Sam ba wannan tunanin daga wajena amman meze hana a zubar dashi ɗin tunda kina gudun matsala gakuma makarantar ki?".


Da baya taɗanja kaɗan sannan ta dubi walida.
"Walida na hakura da karatuna matukar wannan cikin nawa ze rayu, nasan ba lallai nai aure a duniyaba saboda wannan abun kunyar danai dan haka zan zauna na raini ɗana ko ƴata cikin amincin ALLAH sabida bani da wani sanyin idaniyata idan ba wannan cikin ba a yanzu".

Sosai wannan furucin nata ya saka walida kuka haka suka hade kansu sunata kuka abin gwanin tausayi.

Seda umma sahura ta shigo hannunta dauke da kwanon dambun da nafisan ta kafe akan shitake so sannan suka ɗan tsagaita da kukan nasu.

Aje masu shitai a kasa sannan ta dubi walida..
"Walida ni abin da yafi ɗagamun hankalina yadda ita kanta nafisan ta kasa shaida wanda yay mata wannan aika aikan amman babu komai akwai ubangiji".

Umma sahura takai maganar tana share hawayenta itama.

Walida ce ta dubeta sannan tace "tabbas umma inaganin wani azzaluminne yay mata wannan zaluncin alokacin da bata hayyacinta kinga kuwa bazata gane kowaye ba amman koma waye shida ALLAH".

Walida takai maganar cike da son bagarar da umma sahura wadda ta amsa mata cikin gamsuwa tare da barin ɗakin.

Ganin walida yasa tadanci dambun kadan sannnn walida ta taimaka mata sukai sallah.

Har isha walida tana gidan se wajan taran dare sannan ta masu sallama ta wuce gida itama.

Cikin dare nafisa idanunta ya ƙanƙance babu abinda take se faman tunanin wannan lamari daya kunno mata kai tsaye..

Washe gari da safe segasu baffa nan sun diro gidan umma sahura.

Irin tashin hankalin dasu nafisa suka gani se wanda yagani, sabida cin mutunci sukaiwa umma sahura tas akan lallai ta kori nafisa ta, tafi bariki su bazasu hada zuriya da wadda tai cikin shegeba.

Seda mijin umma sahura yay tsaye akan babu inda nafisa zata tunda su basu rike zumuncin ALLAH sun ɗauki ƙaddara ba to su sunji sun aminta babu kuma inda nafisa zata tafi zasu riketa muddin rai.

Haka su baffa suka juya baram-baram abun babu kyawun ji. kaka dataji wannan maganar seda tai gudawa dan tsabar kidima haka ta tara yayanta ta saka masu kuka akan kada wanda ya kuma zuwa gidan umma akan nafi tunda su bazasu riketaba to subar su suɗin su riketa.

Abin da yasama kaka bata tsaya kan nafi ta dawo nan ɗin ba sabida tasan zaman nan ɗin baze mata dadi ba gwara gidan umma sahura duk tsiya.

Gidan umma sahura kuwa nafisa tai kuka kamar ranta ze fita seda ƙyar suka samu tayi shuru sannan kuma baba mijin umma sahura yayita bata baki yana kwantar mata da hankalinta.


Yau kimin sati biyu da faruwar komai haka zalika sosai nafisa ta murje tai kyau amman ta ɗanyi rama kaɗan, sabida damuwar data saka acikin ranta.


Yau tun wuri suka fita ita da umma zuwa asibiti sakamakon maleria ɗin da nafisa take fama da ita kuma anata faɗakarwa akan kada abar masu ciki da maleria domin tana cutar da jaririn dake ciki ɗin.

Fafur nafisa taki amincewa dasuje wannan clinic ɗin se general hospital sukaje bayan ammata gwaje gwaje da sauransu aka bata magani sukayo gida.


Walida na yawan ziyartar ta har hutun su ya kare sosai kuma walida tai kuka yayin dazata koma school taga fina bazata koma ba sabida cikinta ya girma dan ya fito sosai.


Haka rayuwarta ta cigaba da tafiya agidan umma kwanci tashi babu wahala yanzun cikin nata ya shiga wata na bakwai kuma idan ka dubeta seta baka tausayi sabida yadda cikin yay wani irin girma wanda yasa ko fita batai indai ba zuwa awo ba wanda ada bata zuwa amman baba yace dole ta dinga zuwa kodan lafiyar ta.


Al amarin mai girma mas! kuwa sosai ya mayar da hankalinsa akan aikace-aikacen dake gabansa wanda a yanzun haka baya da wani lokacin zaman kansa bare yay wani tunani akan wata nafisa.

Sam yama manta da ita ko hidaya iya hakkinta na aure ke haɗasu sabida baya son shiga hurumin hakkinta amman bada ban haka ba seta wuni bata gansa ba sabida aikin dake kokarin shigar masa dukkan wasu lokutansa.

Yau kimanin wajan wata ɗaya kenan daya bada aikin babbar makarantar ƴammata ta ɗawisu.

Tun safe ya shirya motocinsa domin fita ran gadin aikin daya nuna kamar yama manta daya bada shi.

Yana sanye cikin wasu irin suite bakake masu kyau yana daura tie hidaya ta shigo dakin nasa.

"My dear inada magana dakai".

Agogon hannunshi ya duba tare da ɗaukar glass ɗinsa.


"Kibari na dawo tukunna sabida kinga anata jirana".

Cikin gamsuwa hidaya tace.
"Ba damuwa ALLAH yadawo min dakai lafiya".

Dayake gidan nasu akwai taron ƴan uwa sabida matar imran ta haihu wannan dalilin yasa bai tsayaba sabida yasan yace ze tsaya za,a ɓata masa lokacine dan haka kawai ya wuce abinshi.

Cikin zafin namansa ya nufi wata farar motar ƙirar wannan zamanin wadda oska yay saurin bude masa ita ya shiga driver yaja sauran guards ɗinsa suka mara masa baya acikin sauran motocin nasa.

Wajan titin expiress ya soma zuwa tare da duba ayyukan da aka masa.


Sannan ya wuce makarantar daya bayar a gina wadda za,a wareta domin koyon karatun aikin jinya.


Adai dai wannan saitin bishiyar mangoron ya ɗaga kansa anan dukkan tunanin ta daya mance sabida uzurin gabansa ya faɗo masa.

Dafe kansa yay wanda yakejin yana barazanar sara masa.

Atake ya umarci oska daya saka driver ya juya kan mota zuwa dawisu bording school.

Cikin mintuna arba'in karar sautin jiniyar motocinsa ta cika cikin babbar makarantar ƴammata ta ɗawisu, wadda zuwa lokacin tuni cikin p.c ya ɗuri ruwa.

Dakatar da kowa yay tare da bude marufin motar da kansa ya nufi office ɗin p.c wadda sabida tsabar kidimar datai hatta jikinta rawa yake.

Cikin katafaren office din yaja kujera ya zauna gefensa oska yana tsaye wanda shi kaɗai ya amincewa daya biyosa.

Malaman makarantar kowa jikinsa rawa yake da wannan on expected visit da mai girma mas! yay masu cikin wannan rana.

Cikin mutuntaka da sanin kima da mutunta ɗan adam kamar yadda ake son kowani mutum ya kasance. mai girma mas! yake amsa gaisuwar da malaman school ɗin ke shigowa ɗaya bayan ɗaya suna kawo masa.

Seda ya kammala dasu, sannan ya dubi p.c wadda take gurfane gabansa duk jikinta ya jiƙe da zufa kamar wadda taiwa sarki ƙarya.

Cikin ƙwarewa da sigar siyasa ta yadda ƙaryarka ka gane miya kawosa ya dubeta.

"Ina buƙatar ganin students ɗinki nafisa kabir" yafaɗi hakan a dake batare daya bar wata kofar daza,a gane mike ransa ba.

Sannan kuma karyarka ka gane wani abu agame dashi sannan kuma ga mamakin yadda ya rike sunan tamau kodan ya kasance mutum mai rike abu acikin ransa.

Ɗan jimm p.c tai kana ta kirawo baba vise wanda yake tsaye abakin office ɗin.

Cikin azama baba vise ya kunno kai office din bayan ya rissuna masa.

"Amm vise ka shaida nafisa kabir acikin wannan makaranta?" cewar p.c kenan wadda baki ɗaya ta gama tsurewa.

"Eh mana wadda kwana kifa sukai magana dashi akan haurowar gardi shugabar ɗalibai fa hajiya".

Baba vise yakai maganar cikin ƙwarin gwiwa.

Se a lokacin p.c ta gane domun ada ta ɗan tsorata wanda dalilin hakan yasa ta kasa shaida wayake nufi.

"Ayyah ƴar aljanah ashe yake nufi, sannan ta dubi mai girma mas! wanda yay kamar bai san mi sukeba amman a ransa yana nanata ƴar aljannah!.

"Ranka ya dade wallahi bata dawo ba wannan term ɗin kuma muma mun kasa gane transper sukai mata ko wani abu daban na kasa fahimta yarinyar tana da brain sosai rashin sanin gidansu yasa banjeba".

Takai maganar cikin ladabi.

Waro manyan idanunsa yay alamun bai damu da lamarin ba sannan ya ɗan kaɗa kafaɗarsa alamun ko ajikinsa a ƙasan ransa yana cewa. may be ko aure za,a mata dan daga ganinta villager ce.

Yana kokarin mikewa ya fita baba vise ya dakatar dashi cikin son nuna gwaninta da ƙwaɗayin ɗan na cefane.

"Ranka ya dade, inaganinta da wata yar baƙar yarinya habiba usman mai lafiya, ƙila tasan ta yi hakuri bara naje na turo maka ita".

Ɗan tsaki! yaja cikin ransa sannan ya koma kamar an masa dole ya zauna shikuma baba vise ya fita a 360

SS3A Ya shiga ya kira habiba usman walida wadda ta koma kamar marainiya a school sabida rashin feenah ta dago ganin baba vise yana kiranta.

Jikinta yana rawa tabiyisa seda taga manyan motoci sannan kuma jikinta ya koma yay sanyi dan da ita tai tunanin yan gidansune sukazo dan yanzun jinta take kamar a cell rabuwarta da feenah.

Cikin sanyin jiki ta bisa har cikin office ɗin p.c wanda baba vs yace ta biyosa ita dai mamakin rawar jikin dayake taketa yi a ranta, amman ganin yadda malamai sukai tsitt a falon farko na office ɗin yasa tasha jinin jikinta.

Sallama tai cikin nutsuwa kana ta lumshe idanunta jin wani sassanyan kamshi yana ratsata.

Gaban walida ne yay wata irin faduwa ganin wanda batai tsammani ba agabanta yana zaune ya dora kafa ɗaya kan ɗaya yana danna wayansa.

Duk yadda taso ta basar da kallonsa hakan bai yuwuba se a wannan lokacin tasan dole nafisa tai hauka akansa lallai ALLAH yay halitta awajan nan tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci wannan mutumi ALLAH kenan sarki ɗaya gagara misali.

Da kallo yabita ta ƙasan idanunsa minta ɗaya ya ɗago ya umarci oska dasu p.c su basu wuri.

Cikin rawar murya walida ta fara gaisar dashi wanda shi daga lafiya bai kuma amsa mataba.

"Ina ƙawarki take?"

Tambayar daya cillo mata kenan kamar ba shiba.

Cikin dakewa itama nafisa wadda tai ta maza ta basa amsa da.

"Nima ban san kotana ina ba a yanzun haka".

Cikin daure fuska ya dubeta tare da kallon ke bana son rainin wayo sannan ya kawar da kansa.

Lallai ana mulki anan bayan sarauta walida ta furta sanin mi kallonsa yake nufi gareta ta soma magana bayan ta karo sautin kukanta na sharri.

"Ni dai ranka ya dade bani da wata ƙawa se nafisa duk da dai ban sa wakake nufi taka mai maiba amman kawata ɗayace nafisa wadda mummunar ƙaddara ta faɗa mata wadda tai dalilin rashin dawowarta school ɗinnan wadda wannanɗ kaddarar ta saka ni kaina bansan ina ta shiga ba a yanzun".....bata jirasaba ta cigaba "nafisa kawata ce marainiyar ALLAH marar cikakken gata babban kuskuren danai da ban nemi gidansuba tsahon shekarun da mukai da ita amman ita kam tana zuwarmin sosai kuma nasan dukkan halin datake ci..kawai wannan hutun mun koma segata ta zomun da sassafe da ɗaurin kayanta akanta akan itafa tafiya zatai sabida ayanzun haka tana dauke da ciki wata hudu wanda bazata taba yarda ya zauna ajikinta ba zubar dashi zatai ta koma karatunta ko ALLAH yasa tazama wata nan gaba amman tai alkawarin bazata taɓa gayan wanda yay mata cikin ba sabida danginta duk sun ƙita bata da wanda zata nufa da wannan abun kunyar,ina kuka tana kuka tabar gidanmu dan wallahi cikin harya fito amman daga ranar ban kuma ganintaba har yau ɗinnan......!!
44 - 45


*KUJI DAƊINKU ƳAN P.C DA WANNAN PAGE ƊIN NAKUNE KU ƊAYA*

_Typing 9:36 pm 2apr 2021_




Walida takai maganar tana kuka! sosai wanda ya fito fili.

Ɗan ɗago kanta tai a sace jin yayi ɗuff kamar babu halittar ɗan adam a office ɗin.

Bata kuma ji komai ba illah karar takalminsa alamun ya mike zebar office ɗin.

Cikin tsoro walida ta wara idanunta sosai tana kallonsa, sekuma tai saurin yin ƙasa da kanta.

Ƙaryar mai nazari ya gane a wani hali yake ciki sedai ƙwayar idanunsa data fidda zallan ɓacin rai wadda ta sami damar kaɗawa tai jajur kamar wadda akaima aman jini.

Daga saman kansa kuwa wata irin jijiyace ta miƙe tai wani irin shata layi kamar zata faso waje. har wani irin huci mai fitar amo! numfashinsa ke fitarwa amman sabida tsabar zurfin ciki gami da zafin rai tare da tsantsar miskilanci wanda ya game masa jini ya kasa bawa walida damar fuskantar a wani irin yanayi yake ciki.


Bai kuma ce mata ci kanki ba illa barinta dayay da mugun ƙamshinsa yabar office ɗin.

Saranda walida tai "anya feenah da gaske take shi yay mata wannan cikin?" walida ta furta hakan a fili cikin wani irin yanayi..

"Banga alamun firgita ko rikita agaresaba, naso naga yadda ze gigice amman ko alamar hakan ban ganiba, anya feenah ba sharri zatai masaba".

Ganin malamai suna kokarin kutsowa yasa tai saurin watsar da batun ta fita daga office ɗin ma baki ɗaya.


Cikin tangaɗi mai kama dana wanda yay maye ya nufi wajan motarsa jikinsa na wani irin tsuma, da sauri oska ya bude masa marufin mota ya faɗa baya tare da sada kansa a ƙasa.


Bai kula guards dinsa dake zagaye da motarba illa hannu daya ɗagama oska alamun su tafi kawai..

Duk sauran malamai da p.c dasuke tsaye suna jiran tsammani sakin baki sukai ganin yadda motocin suka barsu da ƙura.

Hannunsa ɗaya ya ɗora saman gorar ruwa ya ɓalle marufin tare da ɗorata a saman bakinsa bai kuma cireba harseda ya shanye tass sannnn ya cillata waje.

Sunkuyar da kansa yay ƙasa yana nanata kalmar "hasbinallahu wani'imal wakil" a bayyane amman cikin sautin ƙasa-ƙasa yadda babu mai jinsa.

"Zaka zama sila ta shigar rayuka biyu a ɓacin rai sannan zaka zama waraka garesu tare da warwara daga karshe ina umartarka daka ambaci kalmar hasbinallahu wani'imal wakil insha ALLAH komai ze warware da izinin ALLAH"!!!!

Sautin muryar wannan dattijuwar matar data taɓa gaya masa kenan ayayin dayaje zagayen aiki.

Tabbas wasu mutanan koba aljanu ba akwai waɗanda ALLAH yake wankewa idanunsu suga abinda kai baka ganiba shiyasa kada ka raina mutum duk ƙanƙantarsa gareka.

Duk da bai yarda da maganar tataba alokacin amman a yanzu yana ganin akwai lauje cikin naɗi acikin maganar tata.

Tabbas wannan yarinyar ƙaddarace ta kawota gidansa, harya mata ciki domin yasan shi kaɗai ya soma saninta a mace dan haka babu tantama wannan cikin nata gudan jininsane!

Daɗa ƙasa yay da kansa yana murɗa ƴan yatsunsa suna bada sautin ƙas! ƙas!! yana kuma cije lips ɗinsa kamar ze ciresu daga jikinsa baki ɗaya.

Babu abinda yake se aikin tunanin mafita wanda duk dai mafitar tasa ɗaya ce tak.

Har suka isa gida sautin karar horn ɗin motarsu yasa ya ɗago birkitattun idanunsa yana kallon window dasu har suka karasa cikin compound din gidan.

Da kansa ya bude marufin motar ya fice kamar wani kumurcin zaki batare daya tsaya jinta bakin su oskaba wanda atake oska yafara tunanin miyasamu ogansune hakan? ganin baya da mai basa amsa yasa ya bawa sauran guards ɗin umarni akan zasu iya wucewa shima ya kama hanyarsa kansa a kulle.

Cikin yanayi mai wuyar misali, ya ƙarasa cikin ɓangaren nasa bai samu hidayaba may be kotana ɓangaren su mama ne domin sakina matar imran ta haihu.

Dan haka se kawai ya wuce bedroom ɗinsa daman kuma a yadda yake a wannan yanayin yafi buƙatar ya kaɗaice shi ɗaya tak batare dawani ya damesaba.

Takalmansa da suka kasance rufaffu kawai ya tube tare da fara kai komo acikin katafaren bedroom ɗin nasa, iska yake faman kaiwa naushi kamar wani taɓaɓɓe.

"Babban kuskuren dazaki tafka shine kiyi gangancin zubdamin da ciki. wallahi! tallahi!! kika zubarmin da cikin dani kaɗai nasan yadda nasha walahar yi maki shi sena daure dukkan zuriyarku sekin ƙare rayuwarki agidan yari"!!

Yakai maganar kamar tana gabansa tamkar wanda ya taɓu ya zube a ƙasa tare da ɗaga hannunsa sama.

"Ya ALLAH nagode maka ina kuma sake gode maka ya ALLAH ka yafe mani abisa aikata laifin da ƙaddara ta haddasa man shi, ya ALLAH kabani kyauta ina kuma godiya gareka na kuma amsa! ya ALLAH kada ka nufi wannan baiwa taka data zubarmin da gudan jinina ya ALLAH ka tserarmin da ɗana ko ƴata ya ALLAH ka sadani dasu cikin sauki".

Yakai maganar yana shafawa tare da zubo da wata zazzafar ƙwallah.

"Bayan kin haihu zan karbi abinda kika haifa na bawa hidaya ta shayar man dashi zan biyaki iya abinda harki gama rayuwar ki bazakiyi talauciba, na yarda na rasa kimata martaba kujerata muddin zaki haifamin wannan cikin dole na nemoki a duk inda kike".

Abayyane yakai wannan maganar wadda hatta hidaya wadda take kawo kai taso taji sautin muryar tasa amman kuma bata ji ainihin mai yake faɗa ba.

Duk yadda taso gane kansa kasawa tai daga karshema ya mike yay bathroom anan ya ɓata lokaci sannan ya fito ya shirya kansa cikin coffee jallabiya, ya nufi part ɗin mama.

ALLAH yasoshi part din maamah babu kowa dan haka ya sami space na sakata agaba kamar wani karamin yaro yau babu zancen wata kara haka ya sakata agaba yan kuka da idanunsa kamar ba jarumin mazaba.

"Maamah kimin addu,a" yake shaida mata hakan bayan ya gama zayyane mata yadda sukai da walida.

Sosai maamah ta firgita da wannan bayanin nasa amman dayake akwaita da ilimin addini yasa ta soma rarrashinsa gami da kwantar masa da hankali itama kuma ta aminta da maganar tasa akan suna son duk abinda aka haifa din.

Bazasuki baiwar da ALLAH yay masuba wannan ma kuma wata jarabtace daga ALLAH wanda babu wani bawa daya isa ya ketare tasa kaddarar.

Sosai mamah ta zauna ta cire kunya tana kwantar masa da hankali sabida taga baki ɗaya tamkar baya cikin nutsuwarsa ma.

Bai baro part din ba se wajan sallar magariba abin mamaki yana idar da sallah ya fice a sace, bakaramin wuya yashaba sabida bai fiya dogon tuki kamar hakaba wasu daga cikin layukan gari ya soma bi koze ganta sedai ko alamunta, haka ya dawo gida yana faman bakin rai.


Koda yazo bacci seda yay ƙwalla.

"Ni ina nan cikin A/C ko ina my unborn child ntake kwance oho?" yafaɗi hakan kamar wani zautacce.

Da ƙyar bacci ya kamasa amman tsakiyar dare nayi ya mike yafara kaiwa ubangiji kukansa.


HOSTEL.

Cikin sauri p.c ta nufi wajan baba vise akan ya kira mata walida taji mike faruwa.

Koda walida tazo bata bar wata ɓaraka ta fita daga wajantaba illa ma kawo wata karyar datai ta maka akan cewar daman akan maganar haurowar gardine wanda yay ma nafisa alkawarin ze dawo wai yaji mi ake ciki kuma da ya manta amman se yanzu wai yazo rangadi ya tuna shine ya viyo dan yaji yaya ake ciki kasan cewarsa mutum mai son cika alƙwari da waɗannan ƙaryaryakin walida ta shigar dasu.

Dayake sun san da wannan maganar shiyasa basu wani jata da tsahoba suka sallami walida tabar wajan.

Haka walida ta zauna tana faman nanata maganarta wadda take tan tamar anya nafisa ba sharri tai masa ba dan babu ta yadda zaka gane akwai wani abu agame dashi.

Amman koma dai maye ta barsa har suyi candy ta koma ta kara jin wata wainar suke toyawa tare da bawa feenah lavarin yadda sukai duk da tana tunanin kafinma lokacin ai ta haihu.
WANNAN KENAN.

Ɓangaren anwar kam.

Sosai ya rage walwala wataran ma ayyukansa se yaransa amintattu ke kular masa dasu.
Baya da lokacin wani abu se addu, sadaka ya dorata akan tada taimakon alumma akullum kuma yana kwana da tunanin ɗansa ko ƴarsa batare dayay tunanin feenah ba dan bata gabansa fatansa a kullum yay tozali da ita ta basa abinda ta haifa idan kuma ayanzu suka hadu ze riketane harta haihu tukunna. ( son kai com. )

Tun hidaya na damuwa da yadda ya koma harta kuma dangana sabida daman can ya lafiyar kura.

Haka rayuwar ta cigaba da tafiya kuma kusan kullum seya fita zagaye batare da sanin kowaba ko ALLAH ze saka yay tozali da ita.

Ɓangarenta.
Kimanin watanni takwas da samun cikinta yau ranar juma,a wadda tai dai dai da ɗaya ga watan azumin ramadan wanda ya rage sauran wata guda ta haihu.
Babu yadda umma batai da itaba akan kada ta dauki azumi amman taki gashi

Please Login or Register in order to submit comment