Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikowa seda na jira sannan na samu na kammala komai". takai maganar tana ɗan jan numfashinta! kaɗan.
Da kallo umma sahura ta bita cike da gamsuwa kana tace.
"Miƙe kije kicin ki ɗauki abinci".waro idanunta tai waje "lah wai harkin gama abinci?".dariya umma tai sannan tace "aikinsan bazan tsaya jiranki ba na riga dana gama tuwone tun ɗazuma dana shigo". mikewa tai cikin zumuɗi har jikinta yana rawa sabida rabonta da abinci tun wannan ruwan shayin data sha ɗazu daman kuma aƙasan zuciyarta maitar tuwon takeyi.
Kicin taje ta zubo tuwon kana ta bude marufin miyar zata ɗiba, ƙamshin daddawar dataji, shine ya bugar mata hanci da sauri ta maida ta rufe tare da ɗibar man gyaɗa kaɗan daɗan maggi ta fita, batai wajan ummaba ɗakin dayake matsayin nata ta nufa.
Zama tai abakin gadon tare da ɗora kwanon a tsakiyar cinyarta,
Tana cin tuwon tana tuna haduwar dasukai dashi kamar a mafarki, wanda ta ɓoyewa umma sahura hakanne sabida gudun zargi.
Lumshe idanunta tai tana kuma hasko yadda taga kyakykyawar fuskarsa ta kuma yin wani irin sahihin kyau mai dakar zuciyata, kallo guda zaka masa kasan baya tare dawata matsala ko damuwa.
Wata zazzafar ƙwallah ta share da hannunta tare da furta "ALLAH ka yayemin abinda nakeji akirjina" sannan ta mayar da hankalinta gun cin abincinta.
Koda ta kammala ta mike ta koma waje ta wanke bakinta da hannunta sannan ta komo ɗakin ta miƙe ta dauko ragowar lemon tsaminta na ɗazu tacigaba da sha, tana mamakin yadda test ɗin bakinta ya koma kamar ɗaci-ɗaci.
Dahaka wani shegen bacci mai dadi ya dauketa bata kuma barkaba se can dare sannan tayo alwala tai sallar dake kanta.
Ta kuma komawa baccinta.


ƊAWISU G.R.A

Tunda suka koma gida ya haye sama ɗakinsa ya shiga tare da faɗawa kan lafiyayyan gadonsa na alfarma.
Ya lumshe manyan idanunsa batare daya budesuba.
Nan danan ya fada duniyar tunanin neman mafuta.
Ta ƙara masa girma a idanunsa fiye da da! ta ƙara haske amman bai kalli fuskarta sosai ba sedai kallo guda zaka mata kasan cewa tana cikin damuwa.
Daɗa gyara kwanciyar tasa yay tare da hasko yadda take sarrafa ɗan mitsitsin bakinta.
"Malam kasakar min hannuna idan ba hakaba nai maka ihun! kwarto" ya kuma mai maita hakan a fili tare da kwai kwayon yadda take maganar wadda kallo guda zaka mata kasan tanacin tsananin tsoro da furgici yayin datai wannan maganar ne.
Wani haushin kansa da kansane ya kamasa ta yaya ma yabarta ta gudu! ba tare daya san ta ka mai mai inda ze kuma ganinta ba "Ya ALLAH ka kawo mana mafita" abinda ya fadi kenan tare da watsar da lamarinta agefe dan kadama ta shiga zuciyarsa harya shiga damuwa danshi mutum ne wanda idan yasaka abu aransa da wuya ya fita ta daɗi.
Ganin magariba tayi yasa ya miƙe ya zame kayan jikinsa.
Tare da shiga bathroom yaɗan watsa ruwa sannan ya fito ya shirya kansa cikin wata blue jallabiya mai yankakken hannu tare da fesa turare mai sanyin kamshi, ya dauke yar jakarta ya adana acikin wani ɗan akwatu dake cikin kayansa, sannan ya fita waje jin anata kwaɗa kiran sallah.
Baiga hidaya a falo ba, dan haka yay saurin zira slipers ya sauka ƙasa.
Da sauri ya karasa cikin masallacin jin anata kokarin tayar da sallah.
Allah ya taimakesa ya samu jam'in dan haka ana idarwa yay saurin fita gudun kada wani ya tsai dashi.
Part ɗin maamah ya nufa tundaga bakin kofa yaji tashin hirarsu da alama ma harda su anty.
Dan gashinan duk suna zaune a falon ƙasa
Cikin nutsuwa ya tura kofar tare da sallama cikin bakinsa.
Mamakin yadda yaga harda hidayama da sakina matar imran duk suna zaune anata hira da alamun sallah ma suka idar, gefe guda mamah ce zaune bisa abin sallah tana lazumi anty kuma tana sakawa zuby dutse a kitsonta.
Sakinace ta fara gaisar dashi sannan shahida wadda take gaban filet ɗin abinci, sannan hidaya itama ta gaisar dashi.
Gaban anty yaje ya zauna yana kallonta sannan ya gaisar da ita yana ɗan jan gashin zuby.
"Waini kam anty wannan ƴar taki gashin watayine agidan nan naga kullum kara yawa yake?" yakai maganar cikin barkwanci baki ɗaya kallo suka bisa dashi sanin sa mutum marar magana shi dariyama bata damesa ba bare magana.
Amman ita anty dayake sun saba shiyasa bataji wani mamaki ba sema dariyan datai kana tace.
"Naka tayo mana aikai inda macene bamu san irin kuɗin dazamu ciba" murmushi ya saki yana makawa shahida harara wadda take guntse dariyanta.
Bai kuma cewa komai ba ganin su shahida da matar imran a wajan sema matsawa dayay can gaban maamah yana jiranta idan ta kammala su gaisa yay waje.
Wayansa ya zaro tare da faɗawa face book yana dan karan ce karancen sa anan kunnensa ya jiyo masa muryar shahida.
"Lah wai nikam ɗazu anty hidaya a plazar nan miya haɗaki da wannan mai bakin mayafin?" tafada tana dariya.
Jin an fadi hakan yasa yay tsai da ransa yay kamar yana danna wayan amman hankalinsa na kan hiran nasu, domin tabbas yasan wannan yarinyar suke nufi sabida daga wajan yaga ta fito kuma mayafin jikinta baƙine shara shara, dan iskanci ita bata san yana fitar mata da sura wajeba.
Sekuma yaɗan ja tsaki.
Tare da ayyana baze taɓa barin matarsa ko kanwarsa fita da kamar wannan gyalenba.
Jin muryar hidaya yasa yay tsai da ransa.
"hmm shahida nima ban santaba amman haka kawai dana ganta naji gabana ya fadi wallahi wannan dalilin yahana ni na iya bata amsar hakurin data bani, seda nai gabama naji tabani tausayi". takai maganar cikin nadama.
"Nima anty senaga kamar ma a tsokarce take, amman miya hadaku ne?".
Takai maganar cikin sigar jin taci miya hadasun.
"hoho shahida ƴar jarida" cewar sakina matar imran wadda itama haihuwarta koyau ko gobe ne.
Dariya hidaya taɗanyi sannan ta dubi shahida da kyau.
"Bigeni tai amman bata kulaba dan naga kamar yarinyar tana cikin wani matsalar ne, duba da yadda jikinta yake rawa seda na kalli idanunta da kyau kuma nagama kamar kuka take". takai maganar tana dariyar wannan tambayanta shahida.
"ALLAH Sarki anty hidaya nima wallahi tabani tausayi sosai kuma daga gani talakace sabida kwata kwatama inaga kamar ba wajan zatazoba tai ɓatan kai, dannaga farkon shigowarta miyau ne abakinta wai dan tsabar kauyanci ta shiga wajan da ake biyan kudi zata zubar a wajan shine naga wani ya daka mata tsawa to ina tunanin wannan firgitarne ya saka ta bigeki bata saniba".
Kirjinsa ne ya buga dumm!! miyau? name abakinta? innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, ya furta acikin zuciyarsa.
Muryar hidaya yaji tana dariya.
"Oh yar jarida shahida, nima wani zubin senaita tara miyau abakina musamman idan ina dattin ciki kinsan kowa da halintar sa amman wannan yarinyar ma ai daga gani bata da aure bare tai abinda kike tunani". takai maganar cikin son ta ganar da shahida.
"Eh kam anty nima wani zubin inayi wallahi".
Jin haka yasa ya saki wata wawiyar ajiyar zuciya wadda harta bayyana fili.
Tare da furta may be dattin cikine danshi kam baiga wani sign na wani abu agaretaba shiyasama yaji hankalinsa yayi ɗaya, kuma tinda yaganta hartana da kafar gudu yasan cewa lafiya ta samu shiyasa yaɗanji dadi.
Da wannan tunanin yaji zuciyarsa ta aminta.
Ganin mamah ta idar yasa yaja jikinsa gabanta suka gaisa baiga fuskar zama ba dan haka yay ma su anty sallama ya koma part ɗinsa.
Daman wani zubin mama bata basa fuskar zama gabanta musamman idan taga jama,a.
Tea ya haɗa yasha sanna ya wuce bathroom yay brus tare da wanka ya kuma dauro alwala yazo ya tayar da nafila.
Akan sallaya hidaya tazo ta tarar da shi itama bathroom ɗinsa ta wuce ta dauro alwalan tazo tabi bayansa suka kuma jera wata sallar daman sun sama duk daran juma,a basu fiye yin bacciba suna tsayawane sosai sukai kukansu wajan ubangiji akan ya dubi lamarinsu sannan suna barar neman haihuwa a taskarsa.
Basu bar kan sallayunsu ba seda akai kiran sallar farko sannan suka kuma mikewa suka bada raka'atul fijir, shikam masallaci ya wuce ita kuma tai sallar ta agida.
Bayan ya dawo daga masallacin ya kuma biyawa part ɗinsu mama ya gaisa dasu sannan yay nasa part ɗin.
Tunda yay azkar yay abinda zeyi na al,adar rayuwarsa ya kwanta bai tashiba se da zetafi masallaci yay wanka ya shirya cikin ɗanyen farin yadin boyel.
Oska ne yazo ya daukesa daga sallar juma,a kuma, yay gidan mai girma governor acan ya ɓata manyan lokuta sabida gayyatar da governor ɗin yay masa, cike da yunwa ya dawo gida haka ya zauna yaci abinci ya ɗan huta sannan suka dauki hanyar can hayin rafi inda zega aikin daya bayar.
Haka rayuwa ta cigaba da gudana a wajan mai girma mas! sam baya da lokacin kansama bare na wani kullum baya nan baya can yana wajan sabgogin gabansa.
Cikin watan kuma ya ɗaga ƙasa mai tsarki dan yana son yay umara daga nan kuma zeje london. bayan ya damƙawa babban yaronsa oska wasu daga cikin hidindumin dake gabansa.


WANNAN KENAN.




Ɓangarenta.

Kwanci tashi babu wuya awajan ALLAH yau nafisa tagama shirinta cikin uniform ɗinta masu kalar fari tas, tana tsaye gaban rijiya tana zira guga zata dibi ruwan dake rijiyar ta zuba a jarka wai ita yanzu tafison ruwan rijiyar akan na ko ina.
Umma sahura kuma tana zaune tana goge mata jakarta sega walida ta shigo cikin sauri.
Gaisawa sukai da umma sahura sannan ta dubi nafisa ta ce mata gafa ya nura can yana waje dan ALLAH tai sauri.
Seda ta ɗura ruwanta sannan tazo ta dauki jakarta tunda walida ta shigar mata da kayanta mota tuni.
Nan kuma idanunta sukai ƙwal ƙwal zataiwa ummah kuka!
Seda umma sahuran tai mata da gaske sannan ta mayar da ƙwallar tata, suka jera harda baba mijin umma sahura suka rakata wajan mota, amman anan ɗin seda tai kuka!
Itama umma sahura kukan ta saka tare da shiga cikin gida tana jin kewar ɗiyar ɗan uwan nata sabida sunyi muguwar shaƙuwa ba kaɗan ba.
Haka su nafisa suka shiga mota ya nura nata tsokanarta itakam ta sada kanta a kasa tana mayar da ƙwallar ta, tana tuna ƙaddarar data faɗa mata wadda ta ɗora rabin laifin akanta.
Muryar ya nura taji yana magana da walida.
"Kinji kuwa mai gida yau yabar saudi ya nufi london nan da sati biyu ze shigo 9ja". walida tai maza ta dubi ya nura.
"Eh ɗazu inajin hajiya tana gayawa baba a falo dasuna break wai anfada a labarai".Se kuma ta juyo ta dubi feenah" kefa mutumin mu yana out side" tafaɗa cikin far'a itakam feena juya kanta tai side na window tana shakar iskar datake kaɗo musu cikin jin ɗaɗi.
Seda walida ta kuma mai mai tawa.
"feenah nace maki mai girma mas! yana out side fa" to anan taɗan juyo tare da furta "Barkansa" ta kuma juyawa tabar walida cikin jimanta maganar.
Sun kusan kaiwa bakin gate ta ƙyallah taga wani koren mangoro, cike da zalama ta kaiwa walida cakuma.
Hartana karkarwa wajan tsaida ya nura kafin ta ɓalle marfun motar ta fita waje.
Gaban wanda ke bakin bishiyar ta nufa cikin tausayi take masa magana "assalamu alaikum babana dan girman ALLAH kasammun mangwaronka wallahi raina ya bita" cikin mamaki tsohon ya dubeta "ayya yarinya babu nu nanne fa se ɗanye ɗazunnan ƴan sari suka kwashe".yakai maganar bayan ya mayar da ƴar redionsa kunnensa.
"Baba ai daman ɗanyen nake so koda kudina nane baba katai makamin". bai ce mata ko ƙala ba ya nufi ciki mintuwa kusan biyar segashi nan ya taho da wata bakar leda ya cika mata ita da mangoron.
Karba tai gami da masa godiya sannan ta nufi motarsu cikin mamaki walida ta dubeta "kekuma mizaki da wannan kayan ciwon cikin keda ko mai nuna bakki sha" bata bata amsaba illama bude ledar tadai ta dauki ɗaya tahau sha duk yadda yake da tsami.
Haka suka karasa cikin harabar makarantar abakin office ɗin p.c ya nura yay parking nafisa ce ta futa wajan p.c taje tai singing kasancewarta shugabar makarantar sannan ta komo taiwa ya nura godiya, kana walida ta samo masu yara suka daukar masu kayansu har hostel, itakam wajan sauran ƴan uwanta masu ɗan kwali ta koma suna taya sauran malamai chakking na provision ɗin student's na yaji da sauran abinda hukumar makaranta bata yarda a shigo mata da shiba.
Bata bar wajan ba se can yamma koda ta koma cikin hostel ma kwanciyarta tai jin kanta na ciwo.


Duk yadda walida taso dasuci abincin data dafo masu agida ƙitai sema, mangwaronta data dauko ta zuba a kwano ta yayyanka sa ta zuba masa yaji zallah da mai tahau cinsa ahaka.

Seda akai magariba sannan ta nufi bandaki tayo wanka ta sauya kaya kana ta dauko farar shinkafa bata saka miyaba tahau cinta ahaka.
Sosai walida take shan mamakin wannan lamarin.

Haka rayuwar feenah ta cigaba da gudana acikin makarantar su kusan kullum sesunyi rigima da walida akan rashin cin abincin dabatayi ga yawan bacci langwai kala kala.

Kusan kullum da zafin jiki take kwana wataran haka zatai ta murƙususu akan gado ita bamai zazzaɓi ba ita bamai ciwon ciki ba.

Al amarin daya faru kuma agaba shine, yawan hararwa duk abinda taci seta amayar dashi wanda walida bata yarda tai agaban jama,a haka xata bata fonsu dasuke fitsari acikinsa idan dare yayi tai aman aciki idan ta gama ta tayata ta wanke jikinta sannan ta zubar dashi.

Sosai feenah ta rame tai wani irin haske watansu kusan biyu a school bata gane komai hatta karatunsu bata wani mayar da hankali akansa kullum tana bacci abinta ko dutynsu bata fita, haka zata kwanta sedai walida tai masu komai wadda kanta yagama kullewa da lamarin f.k


Yau kimanin watansu uku cif a school da faruwar lamarinta da mai girma mas! wata huɗu kenan kallo guda mai hankali da nutsuwa zema nafisa yasan da shigar ƙaramin ciki ajikinta wanda yanzu sam ta daina wannan hararwar sedai bacci da yawan kasala da zazzaɓi.
Ta murje ta kara fari kirjinta yay wani irin cika sedai kuma cikinta a shafe yake babu ta yadda yay alamun tasawa bare a gane cewar mai ciki ce.


Sedai ƴar ramar data ɗanyi. yau suna zaune ita da walida suna cin kwaɗon kwaki bayan sun dawo daga area class karatun yamma.

Da kallo tabi walida sannan tace "Nikam walida yaufa wajan wata hudu ban ga al,adata ba,". cikin ɗan firgici walida ta dubeta "kuma ai baki taba yin hakaba ko?".

"Inafa inda inayi aida kin sani ni wallahi tsoro nakeji". takai maganar idanunta na kawo ruwa.

Cike da kuruciya walida tai dariya "ke dallah share kima godewa ALLAH ai kita addu,a kuma ALLAH sa ba gamo kikaiba kinsan jinnu nasaka haka". nan kuma seta gasgata maganar walidar tare da kudurar niyar yawaita addu,a sosai.

Kwanci tashi babu wuya wajan ALLAH yau su nafisa suka fara zana jarabawarsu ta karshen term wadda kuma daga hutun idan suka dawo zasu fara zaman extension daga shi kuma ze final exam se kuma candy.

Wannan karon tai kokari babu laifi domin ta watsar da lamarin wani anwarr sam ta manta dashi arayuwarta sedai idan ta tuna rabata da kimarta dayay setaji komai ya fitar mata aranta.

Sam yanzu baya gabanta musamman dataji labarin ma bayanan ya dawo daga london ya kuma ɗaukar matarsa sun bar kasar setaji komai ya kuma fita akanta na lamarinsa.

Haka hutu ya zagayo, tun safiyar hutu suke faman koke koke itada da walida kamar bazasu kuma haduwa ba wai dan kawai wannan karon baxatabi motar tasuba habu wanda zata aura ɗan kawune zezo ɗaukarta.

Sabida daman sunyi da ummah sahura akan wannan karon can gidan kaka zata wuce bazata zo gidantaba.

Haɗa yan tarkacan su sukai sukai can area class inda ake zankun zuwan daukar dalibai.

Da habu taci karo yasha yadinsa mai suna ishurunka maraya ya ƙwama ƙaton gilashi baki shi bai yarda ba yay kyau.

Dariya dukkansu suka guntse sannan walida ta dubeta "a,a kalli mijin naki yasha gayu kamar gobe kuke aure". tsaki taja kana tabar wajan fuww tai gaba abinta.

Cikin takun na isa habu ya ƙaraso gabanta "ke baki ganni bane xaki wani koma can baya kamar baki san da mutum ba?" yafaɗa irin ni na isan nan, tsaki taɗan ja kaɗan tare da furta ko yashawo kayan mayen nasane aka san ranta.

Amman gudun abin fada yasa ta basar tare da gaisar dashi sannan ta hau bayan babur dinsa dayazo dashi wanda seta ta karanta addu,a kafin ta hau.

Itakam walida mika mata kayan ta tai sannan suka kumayin sallama kana suka rabu.

Gudu sosai habu yake da ita wanda take yin addu,a ALLAH ya kaisu gida lafiya.

ta hanyar ɗawisu expiress sukabi wanda kuma aka sanar ayau mai girma ɗan majalissar taraiya ze biyota dan ya shiga cikin sabuwar kasuwar wayar daya bude ta ɗawisu expiress sannan kuma ya duba aikin dayay acikinta.

Wannan dalilin yasa babu mahalukin daya biyo wannan hanyar ayau domin tunda waɗan nan mutane suka kai masa hari watannin baya yasa yanzu duk inda zebi yake zama safe babu yawan jama,a wannan dalilin yasa, aka baza labarai akan zezo tawajan inda ze duba aiyukan daya zuba kafin tafiyarsa kasar waje wanda kuma ya dawo jiya da safe ayau din kuma ya fito shawagin duba waɗan nan ayyukan dayay.


Sosai kuma aka zuba jami'an tsaro atawajan gudun faruwar wani abu marar kyau.

Tunda suka biyo hanyar nafisa take baza idanunta ganin kota ina an zuba securty's zagaye da manyan bindugu.

Habu wanda danasani ta rufe da tsoro shiya cigaba da falfala gudu kamar babu gobe daman seda abokinsa illah yace masa kada ya biyo ta hanyar amman tsabar taurin kai yasaka yabiyo ɗin.

A farkon hanyar idan jami'an sukaga da nafisa da uniform suna barinsu su wuce amman da sukazo tsakiyar hanya seda habu yadan dakata sabida yadda karar motoci da jiniya suka cika hanyar nan da nan idanun habu suka fara raina fata.

Itakam nafisa ganin lokaci na kuma ja yasa ta bude jakarta ta dauko carbin tahau ci sabida yunwar data addabeta, ita kuma bata da masaniyar wani ɗan majalisa zezo wucewa kawai ita tai mamakin yadda taga motocin jami'ai sunyi yawa a hanyar yasaka take tunanin ko sabida tsarone yasaka akai hakan.

Abakin wata bishiyar mangwaro suka tsaya sabida yadda motocin securty's suka kunno kai sannan kuma gawasu tsala tsalan motoci na kata'i da suka biyosu a baya.

Habune ya dakata ita kuma ganin haka ya saka ta sauka daga mashin ɗin ta nufi gaban bishiyar tai tsallan albarka ta tsinko guda biyu.

Habu baya da vakin magana datasha masifa amman ganin securty's yasaka bakinsa ya mutu.

Haka tayo wajan mashin ɗin hannunta dauke da mangwaronta tana sha.

Kuma adai dai nan motar mai girma mas!

Ta kawo kai suna kokarin shiga cikin sabuwar kasuwar wayar da akai ta ɗawisu expiress.


Jikinsa sanye da wasu irin kaya masu kyau se farar jacket daya ɗora a samansu sabida ɗan sanyin da ake agarin.

Hannunsa rike da waya suna magana da mai kamfanin sardauna construction akan aikin daya basa, magana suke cikin harshen turanci inda yake fitar da dukkan kalmomin cike da ƙwarewa kamar bai taɓajin hausaba.

Sosai suke magana da Alhajin sardauna wanda sam bai san da labarin yaronsa wanda yake ha'inci akan harkokin kamfanin nasa daya bar masaba, seda yanzu anwarr ɗin ke masa bayanin hakan wanda alhajin yaketa basa hakuri tare da ce masa ya kwantar da hankalin sa nan da karshen wata ze zo ƙasar.

Kamar ance ya ɗago idanun sa ya ɗan sauke glass ɗin motar karaf idanun nasa ya sauka akanta.

Jikinta sanye cikin uniform fari wanda ya bayyana masa daga makarantar data fito, sedai ɓacin ran daya riskesa yadda yaga tana yagar mangoro kamar wata akuya, bai gama shan mamakinta ba seda yaga ta tsallako aguje tare da ɗanewa babur harda dafa mai mashin ɗin sannan suka bar wajan dawani matsiyacin gudu.

Dafe kansa yay cikin takaici sannan yaɗan ja ƙwafa, ya mayar da hankalinsa kan wayar dayakeyi.

Abinda yasa hankalinsa ya kwanta yadda yagane uniform ɗin school data fito wanda ya kudura aransa zesa akira masa p.c ɗin makarantar ya tambayeta akanta.

Da wannan tunanin yabar maganar ya fada sabgarsa.


Itakam tana hawa mashin suka cigaba da tafiya hankalinta kwance domin sam batama kula dashi ba.

Basu sukaje gidaba se wajan la,asar.

Wanka ta farayi sannan ta haye gado se bacci kaka tun tana saka ran tashi suyi hira har abin ya fassakara.


Yau kimain satin ta guda acikin gidan kaka, wanda baki ɗaya bata fita koda waje se ɓanɗaki shima seya zama dole.

Sabida yadda tafarajin rade radin cewar wai bazata koma makaranta ba auransu da habu za,ai acewar kawu yagaji da zaman ta agidan haka babu aure.

Aranar dataji maganar kasa bacci tai haka tai ta kuka kuma adaren ta kira walida ta shaida mata sannan ta kira umma sahura wadda tayi ta bata hakuri kana ta ce mata ta kwantar da hankalinta tanan bisa hanya gobe.


Washe gari wajan goman safiya sega ummah sahura mijinta yayi mata rakiya koda suka samu baffa da wannan maganar kicin kicin yayi da ransa harda cewa umma sahura dan bata san ciwon haihuwa bane ba shiyasa take fatana nafisa ta zauna agida salon taja musu wani mummunar masifar.

Abin dai babu wani daɗin ji haka umma sahura tai ta bawa nafisa haƙuri sannan ta koma gida rai babu daɗi.


Kwanci tashi yau aka kawo kayan lefen nafisa akwatu 1 wanda seda walida tazo sannan tai ta rarrashinta harta samu tai shuru anan walida ta kwana sannan, washegari ta nufi gida sabida bikin sati uku aka saka kafin nan zata kuma dawowa.


Kullum nafi bata da aiki sena kuka ko abinci da ƙyar take cikinsa ga kuma wani ikon ALLAH tunda ta dawo gida cikinta ya soma girma kamar ana hurosa.

Kusan kullum tana ɗaki jikinta sanye cikin hijabi wannan dalilin ya saka sam babu wanda ya kula.


Yau takama asabar umma sahura tazo tun safe da nufin kwana sabida bikin nafisa da habu daya kawo kai yau sauran kwana biyar ciff.

Itama walida gove zata shigo garin tunda nafisa ta kwanta yau take kuka yau ga bikinta yazo amman babu dangin mahaifiyarta ko ɗaya wanda inda akwai su da bazasu bari ai mata wannan aureba.

Umma sahura kadai ke rarrashinta ita kuma amfi karfinta baxata iya ita kaɗai ba.

Yanxuma ita ke kanta tana tashinta ta mike ta shiga wanka.

Sabida yadda takejin jikinta ya saka ta mike tabar dakin ta nufi can tsakar gida ko mayafi babu ajikinta.

Rigar jikinta mai santsice wadda ta baiwa ɗan cubur bur ɗin cikinta damar bayyana a fili.

Ta fito daga wankan tana kokarin shiga ɗaki matar baffa mai suna safiya ta jawo hannunta cike da izgilanci.

"Munafukar ALLAH yau dai semun ganki tunda akai maganar aurenki kike zaman ɗaka bakya futa ko ina muna fukar ALLAH" tana fada ta kum jawo hannunta izuwa wajan cikin sauran matan kawunan nata.

Caraf harira ta mike "yauni ƴasu menake kallone anan " takai maganar tana kaiwa cikin dake jikin nafisa duka kaɗan wanda yasa nafisa sakin ƙara! kaɗan ta sauka ƙasa tana rintse idanunta.

Baba safiya ita ta tayar da ita anan fa matan gida suka hau shewa yau mizasu gani cikin buɗa harira tace "ikon ALLAH ai wannan ko makaho yasan ciki gareta baremu damukaga jiya mukaga yau" aikuwa kafin wani lokaci tuni sun zagayeta caaa!

Nan danan magana ta baza gidan aikuwa abinka da gidan yawa nan kowani sashi sukaita yowa kanta masu murna nayi masu jaje nayi.

Kafin wani lokaci magana taje kunnan kaka sosai nafisa ta shiga tashin hankali hatta hawayenta seda ya ƙafe sam bata kawo ciki gareta ba se yanzu da wannan masifar ta faɗa mata yasa ta tuna rabonta da priod 4mnth.

Kuka babar habu tahauyi tana cewa da za,a cuceta a ƙaƙa bawa ɗanta jaraba wannan lamari ya firgita kowa amman umma sahura tafi kowa shiga tashin hankali sabida wasuma cewa sukai sabida bata san ciwon ɗaba yasa ta dauki nafi hutu ta turata karuwanci.

Wannan lamari ba,a barsa anan ba har seda aka dangana da asibiti anan likita ya bada shaidar cikin dake jikin nafisa cikin koshin lafiya harna wata huɗu.


Bayan sun dawo gida kaka harda suma tana gunjin kuka! shima habu haka yazo yagama tijararsa yabar gidan al amarin dayasa su baffa sukai meating akan a ɓarar da cikin.

Wannan lamarin ya saka nafisa ta ɗago

Please Login or Register in order to submit comment