Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
01
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
Madugun Taska
¤
¤
A ranar da Sadiya ta rasa Amir masoyinta ta gudu cikin daji tana kuka. A ranar ne kuma ta hadu da masoyinta Khalifa, wanda ya maye mata gurbin tsoho masoyin ta Amir.
Ga yadda al'amarin ya faru.
¤
¤
**~**
¤
¤
A duk bayan wata uku, wani lkcn wata hudu Hafsatu matar Dakta Hamza ta kan xo qauyen Gazari ta kawowa 'yan uwanta xiyara, dangin mahaifinta da suka rage mata a duniya idan zata xo yawanci mijinta ke kawo ta a motarsa, idan zata yi kwana biyu sai ya barta a nan, ya koma Abuja inda suke zaune, sai lkcn da ta shirya komawa sai ta yi masa waya ya xo ya dauke ta.
¤
Dakta Hamza babban likita ne, wanda yake da asibitinsa mai zaman kansa, bayan nan yana aiki a asibitocin gwamnati jefi-jefi. Musamman idan wani aikin gaggawa ya taso wanda ake da buqatar qwarewa, sai a kirawo shi yaxo ya yi.
¤
Dakta Jamza ba zai wuce shekaru arba'in ba a duniya, kodayaushe ana dangantashi da mutumin da ya samu nasara a rayuwar shi, yana da manyan kadarori wadanda suka hada da filaye da manyan gidaje da kuma uwa uba katafaren asibitinsa wanda mutane suke turuwar xuwa sbd qwararrun ma'aikatan da ya xuba da kum isassun kayan aiki na zamani dke a cikin asibitin.
¤
Dakta Hamza mutum ne da yake dora rayuwarsa kullum daidai da zamani, idan har akwai abin da yafi tsana a rayuwar sa, bai wuce hanyoyin rayuwa na gargajiya ba. Duk qarshen shekara ya kan dauki hutun kwana uku xuwa hudu, kuma yawanci baya tsayawa a Najeriya, ya fi tafiya qasashen waje ya shaqata. Motocin da Dakta Hamza yake amfani dasu duk wadanda ake yayi ne, komai tsadar mota idan har yayinta ya wuce, ya kan yi sauri ya rabu da ita.
¤
Dakta Hamza yana fita filin qwallon qafa da sassafe kafin ya fita wajen aiki. Da yamma idan ya dawo da wuri kuma, ya kan sa kayan qwallon kwando ya tafi wajen wasanninsu na manyan mutane tare da abokansa. Ga wanda bai san Dakta Hamza ba idan ya yi abin sai ka ji kunya, don kuwa ya kan yi rayuwarsa kamar ta yaro dan shekara goma ba tare da ya damu ba.
¤
matarsa Hafsatu da qanin sa Khalifa wanda yake karatu a Jami'a. Dakta Hamza yana da 'ya'yansa biyu Alfat da Abba, yaran biyu sun saba da ganin yadda mahaifinsu yake gudanar da rayuwarsa. Dakta Hamza kan yi wasan qwallon teburi shi da qanin shi Khalifa, su yi ta jayayya akan makin da kowa yake iqirarin ya samu, duk kuwa da yake Khalifa qanin sa ne na biyar. Shekarunsa ashirin da bakwai a duniya.
¤
Sannan kuma ya kan yi wasan dambe shi da babban danshi Alfat dan shekara bakwai a duniya, wanda suke raba rana kowa yana kaiwa kowa duka, wani lkcn Hafsatu ta kan fito harabar wasannin su tayi kallo. Idan kuma ta ga zai cuci danta sai ta xo ta janye shi ta ce.
¤
"wasan ya isa haka nan, lkcn cin abinci ya yi."
¤
Idan za a lissafo abubuwan da Dakta Hamza ya fi so a rayuwarsa fiya da komai, in har za a yi la'akari da yadda ya kan nuna ne a zahiri, to ya fi son qaninsa Khalifa, daga nan a iya sako 'ya'yansa a mataki na biyu, matarsa kuma ta qarshe.
¤
A farkon auren su sa'ar da Hafsatu tana amarya, da ta ga Dakta yafi son qannin sa, sai ta fara nuna qyashi da kishi. Da Dakta Hamza ya fahimci haka sai ya zaunar da ita suka yi magana.
¤
Khalifa shine kadai dan uwansa da ya rage masa a duniya. Iyayensu biyu sun rasu tun suna qanana, a sannan Khalifa shekarunsa hudu a duniya, shi kuma Dakta Hamza yana da shekara goma sha bakwai. Mahaifinsu soja ne wanda ya rasu a wajen fadan kwantar da tarxoma. Bayan shekara biyu kuma mahaifiyarsu ta rasu. Kafin ta rasu ne ta kamo hannun Hamza ta hada da hannun qaninsa Khalifa ta ce dashi.
¤
"Wannan ciwon ba zai bar ni ba Hamza, ina son kayi mani alqawarin ko bayan raina zaka riqe qaninka Khalifa, ka kyautata masa fiye da kowa a duniya, ynx baka da wanda ya fishi."
¤
Hamza wanda shima yake kuka, ya ce da mahaifiyarsa ya yi mata alqawarin zai kula da qaninsa, kuma zai kyautata masa.
.
A haka da fadi-tashi Hamza ya kammala karatun shi na likita a Jami'a, ya kuma ci gaba da kulawa da Khalifa wanda yake zaune a wurin wani abokin aikin mahaifinsu da suka yi aikin soja tare.
¤
Basu da dangi a kusa, mahaifinsu mutumin Taraba ne, wanda har ya rasu bai nunawa 'ya'yansa biyu inda danginsa suke ba. Ita kuma Mahaifiyarsu bafillatanar Adamawa ce, wacce ya aureta a wani qauye shima ya dade da tashi, sai dai tarihi,wannan ne dalilin da yasa Dakta Hamza da qanin shi Khalifa basu da wasu 'yan uwa da zasu nuna. Sai dai abokan arziqi da suke zaune tare. Ynx idan ba Dakta Hamza ba Khalifa bashi da kowa a duniya, sannan idan ba Khalifa ba Dakta Hamza bashi da kowa a duniya.
¤
Wannan shine asbin da Dakta Hamza ya fadiwa matarsa Hafsatu a taqaice, kuma tun daga lkcn da ta san haka ta daina damuwa.
¤
Idan Dakta Hamza baya nan Khalifa ne yake gudanar da komai na gidan.
¤
¤
Lp=02¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
02
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun taska
¤
¤
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
¤
¤
Ida Dakta Hamza baya nan Khalifa ne yake gudanar duk wasu aikace-aikace dake gidan, shi yake kai yara makaranta, sannan kuma idan Hafsatu zata je wani wuri shi zai kai ta a mota.
¤
A daidai wannan lkc ynx, Dakta Hamza yana qasar Jamani, zai yi kwana shida, ynx kwanan shi biyu da tafiya, saura kwana hudu ya dawo, tun kafin ya tafi Hafsatu ta fadi mashi cewa an yi wata rasuwa a qauye, zata je tayi gaisuwa, amma ba zata kwana ba, a ranar da ta je zata dawo, Dakta Hamza ya ce da ita idan ta tashi tafiyar ga Khalifa nan ya kai ta, tunda dai shi baya nan.
¤
Da yake tafiyar ta kama ranar Asabar ce, Khalifa bai damu ba, tunda ba ranar Karatu ba ce, ya shirya Hafsat ta fito tare da 'ya'yanta Alfat da Abba suka shiga mota suka dauki hanyar xuwa Zariya daga Abuja. Daga Zaria xuwa qauyen Gazari kilomita hamsin ne idan sun bi ta doguwar hanya, idan kuma sun bi ta yanke, sun bi ta garin Galadimawa, kilomita arba'in da biyu ne. Da zasu xo ta doguwar hanya suka bi, sai a dawowa ne da suka ga sun yi yamma, don tafiyar tayi masu sauri, sai suka yanke shawarar su bi ta yanke su shiga qauyuka, har su hau kan titin Kaduna ba tare da sun bi ta Zariya ba.
¤
Da qarfe shida na yamma su ka xo wani qauye mai suna Gogi, a nan ne kuma motarsu ta lalace, Khalifa ya fito ya bude murfin injin ya fara duba inda matsalar ta faru. Hafsatu ta fito tare da 'ya'yanta suka zauna a dakalin qofar wani gida kusa da inda motarsu take. Suna jiran Khalifa ya gyara su tafi.
¤
A qauyen Gogi suka yi sallar Maghrib da Isha'i, har qarfe takea tayi Khalifa bai gano matsalar da ta samu motar ba, kuma gashi babu mai gyara a qauyen, dole sai da aka taimaka masu aka hau Babur aka je wani gari dake a gaba aka nemo masu mai gyara ya xo da kayan aiki. Hafsatu da 'ya'yanta suka shiga wani gida suka zauna a cikin damuwa, don kuwa basu ta6a fuskantar irin wannan matsalar ba a duk tafiye-tafiyen da suka dade suna yi.
¤
Sai da qarfe goma na dare makaniken ya gyara masu motar, ya ce dasu hanyar da suka biyo ce akwai ruwa da ta6o, shi ne ya shiga cikin kafireton motar, sai da aka wanke. Khalifa ya sallami mai gyaran, mutanen qauyen suka yi masu tayin wajen kwana, da suka ga dare ya yi, bai kamata su keta daji da wannan xundumemiyar motar tasu ba.
¤
Khalifa ya yi masu gdy, ya ce zasu tafi haka nan suna so ne su kwana a gida, ya kira matar yayansa ya ce ta fito su tafi an gyara motar. A lkcn tuni 'ya'yanta sun yi barci, ta dauki Abba shi kuma Khalifa ya dauki Alfat suka shiga mota, Khalifa ya tayar da motar suka tafi, shi kadai zaune a gaba, Hafsatu ta zauna a baya tare da 'ya'yanta, suka tafi a hankali don kada su sake samun matsala a hanya, farin watan dake ci kamar rana a sararin samaniya tare da manyan fitilun motar sun taimakawa Khalifa wajen ganin hanyar da suke bi a cikin dajin. Duk da haka sun yi nadamar rashin bin doguwar hanyar da titi yake, don kuwa saurin da suke yi ya jawo masu sun haifi nawa, sun wuce qauyen Turunkawa da kadan motar ta sake lalacewa a rami. Khalifa ya 6ata kusan minti talatin yana ba motar wuta, yana fitowa yana qwaqule qasar data toshe tayoyin motar, lkcn da Khalifa ya fitar da motar sha daya da kusan rabi.
¤
Hafsat ta shawarci Khalifa dasu samu wani qauye su kwana tunda dare ya yi, washe gari sai su tafi hasnkalinsu a kwance. Khalifa wanda ranshi ya 6aci sosai, yayi kamar zai fashe da kuka, ya ce da ita kada ta dau komin dare a gida zasu kwana in Allah Ya yarda, matsalarsu kafin su hau titi ne, ta yi haquri.
¤
Suka wuce wasu qauyukan guda biyu, da kuma wata tsangayar fulani wadanda suka yada zango a wata faffadar gona. A sannan qarfe goma sha biyu ta wuce tuni, sun fara tunkarar daya na dare. Hafsatu wacce take matuqar jin tsoro, ta kifa kanta a bango motar tana addu'a, 'ya'yanta kuwa tuni sun yi barci a jikinta.
¤
Lkcn da suka bar tsangayar fulanin ne a baya, sun xo inda wani Jar gargari yake, babu yawan bishiyu da itatuwa, sai dai tsakuwa da duwarwatsu akan hanyar. A sannan ne fitilun motar suka haskowa Khalifa wata kyakkyawar matashiyar yarinya a kwance a bakin hanyar, da kuma wasu qunshin kayan a cikin zani a gefe guda.
¤
Khalifa wanda shi ya fara ganinta ya ji gabanshi ya fadi, yayi saurin yin salati a bayyane, don kuwa jikinshi ya bashi cewar aljana ce taxo ta kwanta masu a bakin hanyar. Ya dade da jin labarin yadda aljanu ke xuwa bakin hanya su zauna in dare yayi nisa. Salatin da yayi yasa Hafsat tayi sauri farkawa daga gyangyadin da ya fara daukarta. Ta tambaye shi cikin sauri.
"Khalifa....mene...ne?"
ya kasa magana, qafarshi ta fara kyarma, ya kasa taka motar, wanda hakan yasa suka tsaya dab da inda budurwar take. Hafsatu wacce ita ma taga abin da Khalifa ya gani. Ta yi saurin dauke numfashi da taga budurwar wacce take a kwance ko gezau bata yi ba a cikin hasken fitilun motar. Khalifa da Hafsatu suka yi ta karanta addu'o'in su na tsammanin zasu kori aljanar.
¤
¤
Lp=03¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
03
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun taska
¤
¤
Khalifa da Hafsatu suna ta karanta addu'o'i, suna tsamanin aljanar zata 6ace ta basu hanya su wuce.
¤
Suna nan a haka a tsorace cikin motar, sai suka ga kamar tana motsawa tana qoqarin tashi zaune. Budurwar ta tashi zaune ta kalli fitilun motar wadanda suka kashe mata idanu ta sa hannu ta kashe mata idanu, tasa hannu ta kare fuskarta wacce take sharkaf da hawaye. Sannan akwai alamar tsoro da razana a fuskar tata, a lkcn ne Hafsat tace da Khalifa.
¤
"Ina jin wannan baiwar Allah mutum ce ba aljana ba ce, wataqila wani abin ne ya same ta na tashin hankali yasa ta shiga cikin wannan halin, amma yadda muka haskata haka da aljanace da ynx ta 6ace, ba zata tsaya muna haskata ba tun daxu."
¤
Khalifa wanda har xuwa ynx bai warware ba daga tsoratar da yayi, ya ce da Hafsatu.
¤
"Anti ba mutum ba ce, idan kuma mutum, idan mutum ce me zai kawo ta nan cikin wannan uban daren ta xo ta fadi ita kadai. Aljana ce Anti, mu ci gaba da addu'a, in Allah Ya so sai ki ga ta 6ace. Ta bmu hanya mu wuce."
¤
Budurwar ta ci gaba da kukan da take yi tana share hawaye, a lkc guda kuma tana tarbe fuskarta daga hasken fitilun. Hafsatu ta sake qarfafawa Khalifa guiwa ta ce dashi. "na fadi maka wannan yarinyar mutum ce Khalifa, bude ka fita ka je ka same ta, ka ji me yake faruwa da ita? Wataqila akwai wani taimako da zamu iya yi mata, kada ka mance, duk wanda ya taimaki wani, to shima Allah Zai taimake shi."
¤
Khalifa ya juya baya ya dubi Hafsatu cikin tsoro. "Anti na san da haka, amma gsky ba zan iya xuwa wajenta ba, ta xo ta kama ni mu 6ace tare? In dai kin san ba aljana ba ce, kina ganin ba zata cuce mu ba to mu rufawa kanmu asiri kawai mu wuce ta, bakinmu qanin qafarmu, kada mu jawowa kanmu masifa muna zaune lfy."
¤
Hafsatu ta ce dashi.
¤
"ni bari in fita komai zai same ni ya same ni tunda mace ce 'yar uwata, in har akwai taimakon da zan iya yi mata, to zan yi, 'ciwon 'yan mace na 'ya mace ne'."
¤
Hafsatu ta bude qofar motar tasa qafarta waje ta gyarawa 'ya'yanta kwanciyarsu, wadanda suke ta sharar barci basu san wainar da ake toyawa ba. Da Khalifa ya tabbatar da gaske matar yayansa fita zata yi wajen aljanar, sai shima ya yi qarfin hali ya kashe motar, amma bai kashe fitilun ba, ya ja burkin hannu ya bude tasa qofar ya ce da ita a lkcn da ta fito daga cikin motar.
¤
"Mu je mu gani tunda kin matsa sai mun je Anti, amma ki tsaya tukuna mu karanta 'Ayatul kursiyyu' qafa uku-uku, sannan mu je wajenta, ba gaggawa zamu yi ba."
¤
Hafsatu tawuce gaba abin ta ta ce dashi.
¤
"In Allah Ya yarda babu abin da zata yi mana koda aljana ce, ka kuntar da hankalinka Khalifa."
¤
Hafsatu ta tafi kai tsaye ta tunkari budurwar, Khalifa ya biyo ta a baya yana ta taka-tsan-tsan kamar wanda zai shiga ramin maciji, jira kawai yake yi yaga wani abu wanda bai amince dashi ba, ya juya baya aguje ya koma cikin mota.
¤
Da Hafsatu ta isa kusa da yarinyar tayi mata sallama da qarfi, yarinyar ta amsa ba tare da ta daina kukan da take yi ba. Hafsatu ta tambayeta.
¤
"Baiwar Allah ke mutum ce ko aljana?"
Yarinyar ta ce.
"ni mutum ce."
¤
"Me ya faru ki ka xo wannan dajin a cikin dare haka kika zauna a nan? Baki jin tsoron kada wani abu ya same ki a nan?"
¤
Yarinyar ta bude baki zata yi magana kuka ya qwace mata, ta kasa cewa komai, Khalifa ya matso dab da Hafsatu da ya tabbatar yarinyar ba aljana ba ce, mutum ce, ya tambayeta.
¤
"ina za ki je ynx? Muna a hanya ne. Ko akwai wani taimako da zamu iya yi maki?"
¤
Yarinyar ta girgiza kai alamar babu wani taimako da zasu iya yi mata a halin da ta tsinci rayuwarta. Hafsatu ta ce da ita.
¤
"kina nufin mu tafi mu barki a nan?"
¤
Yarinyar ta gyada kai alamar suna iya tafiyarsu kawai su barta. Uk wanna avu dake faruwa har ynx yarinyar bata cire hannunta daga kan fuskarta ba, Khalifa da Hafsatu sun kasa ganin kamanninta a zahiri, suka tsaya suna kallonta cikin tausayi da jimami, sautin kukanta wanda take jan shi hade da dogon nimfashi yayi matuqar tayar masu da hankali, kuka ne wanda yake bayyana tsananin baqin ciki da damuwar wacce take yin sa. Khalifa da Hafsatu suka kalli juna suka kasa cewa komai...suka kasa tafiya su barta, ga yarinya a gabansu cikin qungurmin daji tana kuka basu san kowace ce ba. Hanya dai ta biyo dasu sun xo sun same ta a wajen tare da qullin kayanta a gefe guda.
¤
Yarinyar ta cire hannunta daga kan fuskarta, ta tona asirin hawayen dake xuba a cikin dara-daran idanunta dake motsawa a cikin tekun qwalla kamar qanqara a ruwa. A lkcn ne Khalifa ya fara ganin fuskarta a karon farko, jikinsa ya mutu, ya samu kansa yana kallon wata budurwa wacce ta fada cikin xuciyarsa da sauri....ta riqa tafiya...tana tafiya har sai da ta kai xuxxurfan lungun dake qarshen xuciyarsa, inda babu wata mace data ta6a kusantar wajen a duniya.
¤
Hafsatu ta ce da Khalifa.
"zo mu tafi tunda ta ce bata buqatar wani taimako daga wajenmu.
¤
Ta juya cikin sauri sbd duhun dare da suke ciki. Khalifa ya kasa motsawa, sbd ba zai iya tafiya ya bar.
¤
¤
Lp=4¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
04
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun Taska
¤
¤
Khalifa ya kasa motsawa don kuwa ba zai iya tafiya ya bar wannan yarinyar a cikin wannan yanayin ba. Tsoronta ya fita daga xuciyarsa, sonta yaxo ya maye gurbin shi da sauri. Hafsatu ta sake yi masa magana, Khalifa bai ji abin da ta fada ba, sautin kukan da yarinyar take yi shi ya riqa ratsa kunnuwanshi yana narkewa yana gangarawa har jijiyoyin jikinsa.
¤
Khalifa ya durqusa gabanta a sanyaye, yayi tagumi idanunshi sun cika fal da hawayen da bai san ko daga ina suke ba, wataqila sun fito ne daga wani guri mai nisa a cikin jikinsa, wanda sabuwar soyayyar da ta kama shi ta keta ko'ina. Kamar yadda wuqa mai kaifi take keta tsoka da jini. Bai san ta yadda aka yi ba har ya fara yi mata magana ba ya ce da ita.
¤
"ba zamu iya tafiya mu barki a cikin wannan hali ba, bamu san ki ba, kema baki samu ba, wani abu a cikin xuciyata yana raya mani kamar na anki, kamar na ta6a ganinki a wani wuri, kamar mun ta6a yin rayua tare a wata duniya ba irin wannan ba, don Allah ki daina kuka ki yi mani magana, ki fadi mani ko ke wacece."
¤
Yarinyar ta dubi Khalifa sosai, ta saita idanunta akan sa, a 6angarenta bata ji komai ba, xuciyarta ta dade da bushewa ta zama kamar dutse babu sauran wata soyayya da zata sake ratsa ta, ta daina kukan ta ce da Khalifa.
¤
"Ku matafya ne, don ku tafi ku barni nan inda kuka same ni, ban so kuka xo kuka same ni a nan a raye ba, na tsaya nan ne ko wani abu yaxo ya kashe ni, don in huta da halin baqin cikin dake nuqurqusar rayuwa ta."
¤
Hafsatu wacce take sauraren kalaman yarinyar ta ci gaba da tsayuwa tana mamakin yadda akayi wannan kyakkyawar yarinyar mai qarancin shekaru ta fada wannan bala'i har take fadin ta gwammace ta mutuwa taxo ta dauketa. Khalifa ya sake cewa da ita.
¤
"Duk da bamu san abin da ya faru dake ba ina tabbatar maki da cewa idan har kika miqo hannunki kika amshi taimakonmu, zaki fita daga cikin koma wane irin qangi ya same ki a rayuwarki. Suna na Khalifa, wannan matar yayana ce sunan ta Anti Hafsatu, mun kai xiyara wani qauye ne motarmu ta lalace a hanya har dare yayi, ashe da rabon zamu hadu dake ne, ki taso mu tafi dake gida, idan hankalinki ya kwanta, sai muyi magana akan koma me ya faru dake, daga nan sai mu san irin taimakon da zamu iya yi maki, ki yarda damu, ba zamu cutar dake ba."
¤
Yarinyar ta share hawayenta, bata yi masu turjiya ba ta amince zata bi su, koma ina za su je, koma ina ne garin su. Hafsatu ta juyo ta kama hannunta tana rarrashin ta, Khalifa ya dauko mata qullin kayan ta suka tafi a hankali har xuwa inda motarsu take, wacce ta basu gudunmawar haske da fitilunta har suka gama abin da zasu yi a wajen.
¤
Khalifa ya budewa yarinyar qofa a 6angaren gaba, ya qarfafa mata guiwar shiga ta hanyar nuna mata kujera da hannun shi. Ta shiga ta zauna, sannan ya miqa mata kayan ta ta dora su a jikinta, Hafsatu ta bude qofa ta shiga baya inda 'ya'yanta suke ta sharar bacci nasu san duk abin dake faruwa ba. Khalifa ya shiga cikin sauri ya tayar da motar suka tafi.
¤
kafin su yi nisa ne Hafsatu ta ce da yarinyar.
¤
"Baiwar Allah baki fadi mana naki sunan ba, lkc ya yi da ya kamata ki saki jiki damu, ki daukemu kamar 'yan uwanki da kika baro a gida."
¤
Yarinyar tayi ajiyar xuciya ta share hawayen da ya rage a cikin idanunta, ta ce,
¤
"Suna na SADIYA"
¤
¤
**~**
¤
¤
DA GARI ya waye aka fahimci ba a tashi da amaryar Sarkin noma ba wato Sadiya, sai gidan ya rikice aka fara neman ta ana sanarwa maqwabta da sauran mutane, cewar Sadiya ta kwashe kayanta ta gudu a cikin dare.
¤
Sarkin noma Alh. Mamuda ya fusata sosai, ya shiga dakin Sadiya ya tsaya yayi tagumi, yayi shiru, mutanen gidan 'ya'yanshi da jikokinshi, suna ta leqowa ta taga suna kallon shi suna tafa hannuwa a cikin jimami, suna fadin sun bani sun lalace da wannan abu da wannan abu da yake ta faruwa a gidan nasu.
¤
Sarkin noma ya fito ya bayar da cigiya, ya ce aje ko'ina, ya aiki wani qaninsa a babur ya ce ya je Gidan rijiya ya gani ko gida Sadiya ta koma. Da ya dawo ne ya ce iyayenta sun ce basu ganta ba, wadanda suka hau kekuna da babura suka bazama qauyukan dake a lardin suma suka dawo suma suka ce basu ga ko sawun ta ba.
¤
A ranar ne da yamma Sarkin noma ya fusata sosai, ya ce ba zai iya ba, ya rubuta takardar saki ya tashi takanas tare da wasu fadawanshi biyu suka taka shi qauyen Turunkawa, ya je ya samu iyayen Sadiya suka zauna a zaure.
¤
Mal. Buba a gefe daya tare da Mal. Kalla mahaifin Sadiya, sai Limamin qauyen wanda ya daura mata aure a gefe. A daya sahin kuma Alh. Mamuda ne tare da muqarraban shi.
¤
Bayan Liman yayi addu'a

Please Login or Register in order to submit comment