Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiyo yace grany kibada Lipton dina akamun tace to shi kuma ya fice


Misalin karfe 8 na dare Asma'u ce da hkadeeja zaune a Palo suna kallon shirin akushi da rufi Wanda ake atashar arewa24 can khadeeja ta waigo ta kalli Asma'u race amma alalan nan dagani zatayi dadi ko ??Asma'u tayi murmushi tace sosai ma ko kina sone ?
eh wallahi ina so zaki mun ne? Asma'u tace mezai hana khdy ko wannan din da suke girkawa yanzu in kina so se inje in karbo maki
Khadeeja ta shagwabe fuska tace uhm uhm nifa da gaske nake
Asma'u tayi dariya tace gobe zan maki naki khdy ta washe baki tace Allah ya kaimu Asma'u tace ameen suka ci gaba da kallon

Washegarin ranar ta kasance asabar misalin 10 nasafe Asma'u ta gyara wken alale tashirya ta tafi kai nika

ABID ne yafito daga bangaran sa cikin shiga ta kananan Maya wando light brown da faran riga ga fitinannan kanshi dake tashi daga jikinsa yayi kyau bakadan ba fitowarsa yayi daidai da fitowar Sarah daga nata part din da far'arta takaraso wurin shi tana gaida shi ya amsa shima dauke da murmushi afuskarsa yace bari inje ana jirana murmushi tayi tace AHMAD ko?? yace eh sannan yafara sauka har yakai kasa tace yaya kace mashi...se kuma tayi shuru kanshi ya dago ya kalleta yace ince mashi kina gaidashi ba??fuskanta ta rufe da tafukan hannayanta ๐Ÿ™ˆta shige bangaranta shikuma ya wuce yama grany sallama daga nan ya nufi wajan motocinsa guards dinsa suna ganinsa suka tashi tsaye yadubi wani daga cikin su yace yahya bani makullin atare suka hada baki but sir !!!!
Fuska ya hade yace just give me the key Wanda aka kira da yahya ya mika mashi makullun ya karba naga ya nufi wata dakkareriyar Jeep baka se sheki takeyi ya fice daga gidan ahankali yake tukinsa kamar mai koyo har ya iso life camp akofar wani katafaran gida naga yayi parking mai gadin ne ya liko ya ganshi yace ah yallabai yafara kokarin bude get din ABID yace no barshi sauri nake yanzu zan fito kai tsaye cikin gidan ya nufa tare da sallama ya kutsa kanshi cikin palon wata matace ta amsa sallamar tana ta kokarin shirya abinci a dining Da murmushi ya karasa dining din yaja kujera ya zauna kana ya dago ya kalleta yace momy ina kuana bata dago ta kalleshi ba bare ta tankashi Shima kuma bai kara cewa komai ba Ya bude kula ya fara zuba soyayyan dankali da pepper soup yafara ci seda ya gama kana ya leka kitchen din ya iskota tana loda lemu a frig daga kofan kitchen din yace momy zan wuce se a lokacin tace toda wa yarikeka?? Murmushi yayi baice komai ba yafita daga palon wani bangare naga yanufa acikin gidan yana zuwa yatura kofar palon ya shiga babu kowa hakan yasa yawuce bedroom karasawa yayi kusan gadon tare da yaye bargon yana fadin AHMAD!! Ahmad ya gyara kuanciyarsa tare da Jan bargo ABID ya janye bargon gaba daya yace malan dallah tashi kai ko kunya baka ji tun baccin jiya har yanzu bai isheka ba Cikin murayan bacci Ahmad yace AK wai miye haka da sassafe kazo gidan mutum kahana shi hutawa ABID ya katse shi kai dallah tashi lokaci ya kure mukadai ake jira Tashi Ahmad yayi yana gunguni yanufi toilet ABID yace wai me kama Momy ne ?? Ya juyo ya harereshi da jajayan idon shi na bacci yace Ohoo!! meyasa baka tambaye taba yashige bayi ABID ya girgiza kai ya mike yaje drowan Ahmad ya Ciro masa kananan kaya wando baki da riga milk color bayan Ahmad yafito wanka ABID yace kashirya zan jiraka awaje kuma wallahi kadade kazo kaga bana nan Ahmad yace dadin abun dai Nima inada abun hawa ABID ya wuce ya barshi atsaye yana kallon kayan dake kan gadon


Asma'u ce tadawo daga kai nikan dataje tundazu tana tafe tana mitar dadewarta ita kadai shi yasa bataji horn da ake mata ba seda motan tazo kusa da ita Drivan yadaka mata tsawo afirgice tayi baya zata fadi Taji ta bige da wani har robar nikan ta karkace kadan ya zuba juyawan dazatai taga ashe mota ce ajiyan zuciya tayi tace kai amma Allah mai motanan albarka dayanzu nikan alalan khdy ya zube robar ta Dora akan motan tana gyara wanda yabata bakin robar tsawar da taji andaka mata ne yasata tajuya afirgice ABID tsaye abakin get Ya murtuke fuska kamar bai taba dariya ba ganin yana nufota gadan gadan yasa ta hadiye yawu tare da kura mashi ido tsabar tsoro yasa tama kasa motsa kafarta bare tayi yunkurin guduwa yana zuwa dap da ita bai yi watawata ba ya fisgota tare da zabgamata lafiyayyan mari a firgice ta dafe kuncanta ๐Ÿ˜จ Cikin Muryan kuka tace malam lafiya me namaka zaka mareni?? ABID da yagama hasala wato bata ma san abunda tayi bakenan cikin kakkausar murya yanuna motarshi da yatsa yana fadin
Dan ubanki nan yamaki kama da bola ko kwata dazaki zubamun wannan kazantar akai??
aranta tace ga mai mortar nan juyawa tayi takalli motar ita se a lokacin ma ta lura da Wanda ya zube akai maganar ABID ne yasa tamaido da dubanta garesa aranta take fadin hmm yanzu haka ma ita ce motar da yafara mallaka arayuwarsa shi yasa yaketa rawar kafa akanta ABID ne ya katseta da cewa ina magana kin wani kure in da ido sunkuy da kanta tayi kasa tace yi hakuri
What!!! apology dinki zai sa motata ta gyaru ne itama hade rai tayi dan abunshi yafara isarta kallonshi tayi tace inazuwa da Sauri ya sagabanta yana fadin ba inda zaki se kin... Bai karasa ba takatse shi dacewa dallah malam matsamun to in ban nemo abun gogewa ba da harshe na ka keso in llashe shi ko me ?? Tana gama fadan haka ta shiga gidan da ke kallon nasu Ahmad
ABID dai da kallo ya bita yana mamakin wai yau shine yake fada ana fada yayi danasanin rashin zuwa da guards dinshi da tuni sun tattaka wannan baby doll din ba Ba adau lokaci ba segata tafito daruwa aroba da wani dan karamun towel tazo tafara goge motar har tagama yana tsaye yana kallonta ko Inda yane bata kalla ba tadauki robar ta maida tadawo tadauki robar nikanta se alokacin ta kalleshi yana kokarin shiga mota tace Hey!!!
tsayawa yayi cike da mamaki yana kallonta matsowa tayi kusa dashi cikin sansanyar murya tace kasamu wani waje koda dan kadan ne acikin zuciyarka dazaka rika yafema Wanda yamaka laifi to gashi nagoge maka motar ka nikuma idan nace banyafe marin da kamun ba ya kenan tana kai tajuya tafara tafiya can kuma takara juyowa tace ohhh yes ina farin cikin sanar da kai
Kaine mutum na farko da yafara marina A tarihin rayuwata juyawa tayi tayi tafiyanta
Wani dogon tsaki ABID yaja se a lokacin ma yaji haushin kanshi da yatsaya sauraronta motan ya shiga ya zauna ba adau lokaci ba se ga Ahmad yafito yana daura agogo ahanunsa motar yabude ya shiga ya kalli ABID yace ๐Ÿ˜ŽAK nayi Sauri ko??
tsaki yaja baice komai ba ya tada motar suka wuce

Ahmad kenan yakasance aboki kuma amini awurin AK wato ABID tun suna yara suka taso tare koda wane lokaci suna tare Akwai shakuwa maikarfi atsakanisu Ahmad yakasance fari dogo mai dan matsakaicin jiki yanada surutu da barkuanci sabanin AK dabaicika yawan magana ba

Asma'u tana isa gida sukacikaro da khadeeja cikin muryar tausayi tace khdy yunwa ko ??
Khadeeja tace amma meya sami fuskar ki??
Asma'u ta kakalo murmushi tace ba komai muje in maki alalan rana tayi ko Umma ta aike ki ne
Khdy tace a'a wurinki naso inje naga kinjima Baki dawo ba batace komai ba taja hannun khdy suka karasa ciki..........
[18/07, 15:03] Hubbey Frd Ameena Kn: ๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š
๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘งDOMUN KANWTA๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง

๐Ÿ–ŠNa marubuciya Husnah kabir zarewa ( the mammah girl)


๐Ÿ–Šdasunan Allah mai rahama mai jinkai ...

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘งDOMUN KANWATA๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง

1โƒฃ0โƒฃโญ1โƒฃ5โƒฃ


Bayan sati daya da faruwar hakan misalin 11 na rana Asma'u ce da khadeeja a kitchen suna girka abincin rana khadeeja tasa wakar harsashe awayanta suna aiki suna bin wakar idan anzo baitin da namiji keyi se khadeeja tabi na mace kuma se Asma'u tayi sundage se yi suke kai kace su suka rera wakar
Khadeeja har da kwaykwayon muryar maza ta nuna Asma'u da yasa tace " tadaban ce ke ta kadaban aciki ke nawware!!! Araba mu anyi....." har dai zuwa karshe tadake kuwa kamar da gaske
Asma'u ta kwashe da dariya ita ma ta karkace tana kikkifta ido tana kallon khadeeja irin na moyannan tace " niii taka tun asali ba mai kuacema!!!
Khadeeja ta kwashe da dariya tace ammah dazakiyi acting zaki samu kudi
Umma ce ta leko kitchen din tace kuna nan kuna shirman da kuka saba ko to nidai kuyi sauri ku gama Asma'u zan aikeki kasuwa daga nan kibiya wurin inna tana nemanki tana kai nan tafita
Asma'u ta juyo ta kalli khadeeja tace khdy zaki rakani ??
Khadeeja ta zaro ido ta dafe kirji tace wa?? Niii dama bazaki biyo wajan inna bane dana rakaki amma kinfi kowa sanin bama shiga inuwa daya da ita Asma'u tayi murmushi suka ci gaba da aikinsu....


sarah ce da aysha zaune suna shirya yanda tafiyan su zai kasance can aysha ta dago ta kalli sarah tace wai nikan sarah ina dan gidanki ne kwana biyu banga yazo gidan nan ba sarah tayi murmushi tace yana nan dazuma muka gama chart dashi he is just busy that's why aysha tace ahh ahh kice kun fara soyewa kenan ?? Sarah tayi fuskar tausayi tace wace soyewa kuma aysha bayan nikadai nake azabtuwa da sonsa shi bai ma San inayi ba aysha ta gyara zama tace to shin wai ke meyasa bazaki fadamasa halin da kike ciki bane nasan dai ko giyar wake ya sha baza yayi rejecting din ki ba Sarah ta saki baki tana kallonta se can ta yi dariya tace wa?? ni?? Da matsayina da Class dina kanwar the richest man in town inje insamu namiji ince ina sonsa never!!!
Aysha tadaga kafada tace nidai shawara nabaki kina nan sake da baki wata zata kwacemaki shi sarah tayi wani malalacin murmushi tace ai ba'a haifi macan da zata kuace AHMAD a hannuna ba wallahi ke ni maganar nan ma da mukayi kinsa naji ina son ganinshi bari inje company nasan zan same shi aysha ma tamike tace muje narakaki toh daga nan nima naga AK
suna fitowa suka hadu da grany itama tafito cikin shirin ta nafita cikin rada sarah tace ita kuma wannan tsohuwar ko ina zata ohoo aysha ta matsa kusan grany tace ahh ahh grany ina zuwa haka? Grany ta tsuke fuska tace inda kika aikeni aysha ma tahade fuska tace shi mutum ba'a iya mashi idan kashareshi yace ka raina shi in kuma kamai magana ya gaya ma nakar magana cikin fushi grany tace zan bige maki baki wato futsarar da kika ga waccan mai kama da kazar yan burin tanamun shi ne kema zaki soma ko to kufita a idona aysha ta wuce tana gunaguni grany tabita da harara tace mace kamar pal waya kome ma ABIDI yagane anan da har tabirge shi ohoo koda tafito su sarah sun tafi guards suna ganinta suka mike Driver yaje ya fito da dai daga cikin motocin gidan grany ta juyo ta kalli guards din da ke biye da ita ta kankance ido tana kallon su cikin masifa tace kai wai lafiya kuke biye dani kamar kaza da yan tsaki?? Sunkuy da kai sukayi basu ce komai ba tace toh Ku koma bazani da Ku ba daya daga cikin su ne yace sorry ma but umarnin yallabai ne kar mubar kowa na gidan ya rinka fita shi kadai Grany ta wuce tana fadin ai kuma se kuyi naga Wanda zai biyoni acikin Ku mota ta wuce tana waiwayo su tare da nuna su da yatsa har ta shiga driver yaja suka fita se da suka hau titi driver ya juyo yace grany ina muka nufa fuska ta daure tace baka iya gaisuwa bane ?? kai ya Sosa yace ina wuni tace lafiya kasuwa zaka kaini ...

asma'u ce a kasuwa tazo wucewa taga grany a tsaye se waige waige take ga tulun kaya agabanta har ta wuce se kuma ta dawo wurin grany tace ina wuni grany ta washe baki tace lafiya kalau yarnan sannu Asma'u tace kina son keke napep ne grany tace a'a da driver mukazo anan ya saukeni kuma kinga nafito ban ganshi ba Asma'u ta waiga ko ina bata ga mota ba ta kalli grany tace bari muje can bakin hanya muga ko yana nan grany ta washe baki tace to Asma'u tadauki kayan da kyar take tafiya har suka iso bakin hanya grany tace kinga kwa gashi can zo muje suna isa wurinsa grany ta haushi da fada baice komai ba se hakurin da yake bata ya karbi kayan ahannun Asma'u yasa a boot grany ta kalli Asma'u tace sannu yar albarka baki gayamun sunanki ba Asma'u tayi murmushi tace ASMA'U suna mai dadi ni kuma sunana... Asma'u tace grany ko?? Grany ta washe baki tace ina kikasan sunana Asma'u tayi murmushi tanuna driver tace damuka zo nan naji ya kiraki da sunan grany tayi murmushi tace eh hakane jika nane yake kirana da sunan shine ya Bini hannu tasa ajaka ta dunkulo kudi masu yawa tamikama Asma'u amma Sam taki karba se ma juyawa datayi ta tafiyanta grany tayi tsaye tana kallonta cike da sha'awa aranta kuma tana fadin inama ABIDI na yasamu irinki amtsayin mata da yamore har saida Asma'u tabace mata sannan ta shiga mota suka fice...

Daga kasuwa Asma'u direct gidan kawunsu tanufa tana isa ta tura kofar palon tare da yin sallama fa'iz ne kadai azaune yana duba wani magazine karasawa tayi ta zauna adai daga kujerun palo fa'iz ya ijiye magazine din hannunsa suka gaisa Asma'u ta mike ta nufi dining tana cewa bakowa agidan ne fa'iz yace Ummi taje barka nusaiba kuma tana ciki Asma'u tace inna fah yace tana Akurkinta Asma'u tayi dariya tace wallahi kai da khadeeja kunraina inna ranar da Abba ya kama Ku bazakuji da dadi ba abunci ta zuba tafara ci nusaiba tafito suka gaisa da Asma'u tace Asma'u inada dinki fah Asma'u tace to se ki kaimun shago Nusaiba tace tab!! Wannan shagon dinkin naku mai Nisan tsiya ina zan iya Asma'u tadaga kafada tace ba kishirya dinkin ba kenan nusaiba tahade fuska tanufi palo kusa da fa'iz ta zauna tana leka magazine din dake hannun shi baki ta washe tace kai ji wani gado kamar na sarauta fa'iz yayi murmushi yace Shi zan maki na auranki dukan shi tayi akafada tace Allah yaya bana so Wani page ya juyo sega photon AK yana sanye cikin shiga ta kananun kaya ga agogon Rolex daure ahannunsa yana murmushin da yake kara masa kyau nusaiba tace WOW!!! AK hausawee gayan nan yana bala'in birgeni fa'iz yace Ashe bani kadai ba ai gayan ya hadu ga gayu ga money
Daga can dining Asma'u tace waye ake cewa ya hadu fa'iz yace AK hausawee Asma'u takai loman tuwo bakinta tace waye kuma shi fa'iz yace ammah kina Abuja amma kanki na kauye to ai duk yan matan garinnan daya daya ne basu San shiba Wanda yakeda Hausawee interior decoration (HID) import company suna shigo da kayan gida irinsu Gado kujeru da sauran su tasowa tayi tana fadin ina jinshi abakin khdy Amma ni ban taba ganinshi ba murmushi yayi ya mika mata magazine din ta miko hannu zata karba kenan akaturo kofar palon tareda sallama wata dattijiwa ce tashigo palon kofar suka kalla suna Amsa sallamar tsaye tayi abakin kofar tarike haba tana zabga salati asma'u tanuna da yatsa fuska ahade tace ke yanzu asama'u dama nan kikazo wajan wa'innan sakarkarun kika shanyani ina jiranki? Asma'u tayi murmushi tace yi hakuri inna dama yanzu zanzo inna batace komai ba takada kai kafita Asma'u tabita da kallo fa'iz yace kin tsokano mana tsuliyar dodo hararar shi tayi tace ya isheka malam itama ta fita daga palon bangaran inna tanufa azaune ta iskota tana ninke kayanta da aka wanke da sallama takarasa cikin palon inna ta amsa sallamar ciki ciki ita adole tashaka kusa da ita Asma'u tazauna itama tafara ninke kayan kusan minti 10 bawanda yace wani Abu atsakanin su asma'u ce takatse shurun da cewa kince kina son ganina nazo kuma bakice komai ba inna tace yau wace rana?? Asma'u tace Dama dan kitambayeni hakan yasa kika kirani? inna tayi shuru batace komai ba Asma'u ta sauke ajiyar zuciya tace yau asabar menene inna tadago ta kalli Asma'u tace magani na yakare jibi ya kamata mu koma asibiti gashi abbanku bai dawoba kuma ni gaskiya ina jin kunyar inje ince ma Maman nusaiba tabani kudi inje asibiti Asma'u tayi shuru na dan lokaci can tadago tayi murmushi tace Karki damu inna Allah ya kaimu jibi kishirya da safe zan zo se mu wuce asibitin inna tayi fuskar tausayi tace asama'u ina ruwa yaci makadi ke kina ganga ta jiki yo dawane kudin zamuje asibiti? Asma'u tace Dama akwai dunkunan da nakare Se inkira a amsa kedai kawai kishirya da wuri Inna tawashe baki tace ai insha allahu tun asuba zan shirya Asma'u tace dakin kewta mun kuwa dan daga can shagon dinki nakeso in wuce Bazan samu damar zuwa makaranta ba inada aiki dayawa gaskiya inna tace to Allah ya taimaka amma asama'u kinaida wasa da karatunki kinje Asma'u batace komai ba tadauki kayan da suka gama ninkewa tashiga dasu ciki inna tabita da kallon tausayi tana fadin allah sarki Asma'u mace mai kamar maza kenan tana tsananin son yan uwanta da kishinsu tun tana Karama take zuwa gidan wata ameena makwabciyar su tana koyon dinki har ta kware aharkar dinki tana fitar da style masu kyau intayi dinki kai kace injin ne ya buga kayan ganin haka ne yasa lokacin da ameena ta bude shagon dinki tadauki Asma'u tana mata aiki Dawanan aikin Asma'u take rike da gidansu da kuma karatun khadeeja dawasu bukatun su kasacewar shi kanshi kawusu bawani karfi gareshi ba fitowar Asma'u daga daki ne ya katse ma inna tunaninta ledan da tashigo dashi daga kasuwa tabude ta Ciro wata Leda aciki tamika ma inna tana fadin inna ganshi ba yawa kidan yi brush inna takarba tana washe baki tabude gasashshiyan hanta ne Wanda bazasu wuce yanka 10 goma ba Inna anata lashe baki asma'u Tamata sallama tafita dayan bangaran Ta koma ta iske Ummi tadawo tana zaune a Palo wajanta ta karasa suka gaisa Ta kalli nusaiba dake gefe tana goge uniform tace ji ki kawo dinkin naki tashi tayi tanufi daki tana jin dadi Ummi tace Asma'u badai har zaki wuce ba murmushi tayi tace Ummi sauri nake yamma tayi Ummi tace namanta ban tambayi yar lelanki ba khadeeja it's dai bata zuwa nan gidan se in an aikota Asma'u tayi murmushi tace tana nan makaranta ne ya riketa nusaiba ce tafito dauke da turmin atanfa tamika ma asma'u tace buba nakeso Asma'u ta karba tare da fadin sedai singlet nusaiba tace kai ammah wane irin singlet kuma๐Ÿ˜ง
Dariya suka sa Asma'u tamusu sallama tawuce

tafe take tana sauri ganin magariba ta gabato ta tsallako titi kenan ledan hannunta ta tsinke dogon tsaki taja ganin lemun da tasiyo ma khdy duk ya waste Hakanan ta tsugunna tafara tsincewa tanaji ana mata horn amma bata motsa ba AK dake bayan mota a zaune ya jingina kanshi akan kujera ya lumshe ido jin driver nata horn yasa yace menene? Driver yace wata yarinya ce a hanya Shiru yayi bai CE komai ba driver yakara danna horn Ita kuma haushi duk ya isheta ga karan horn duk ta rikice tarasa ma mezatayi jin shuru yasa Ak bude idonshi ya leko ta window ya ganta tana kokarin Gyara ledar da tayage komawa yayi yazauna yace ma driver taka motar driver yace sir???
tsaWa yadaka ma driver hakan yasa ba shiri ya taka motar suka nufota a guje duk dacewa Asma'u ta tsorata amma ko motsawa batayi ba bare tayi yunkurin guduwa seda motar tazo daf da ita har tana jin hucinta kana driver yaja birki mutanan dake wurin suka dau salati aka zagaye wurin AK kam yagama shaka a hasale ya fito daga mortar ya nufota yana zuwa ya fincikota ya daga hannu da nufin marinta se kuma yadakata yace you???Asma'u kuwa takafeshi da ido ko kiftawa batayi zuciyanta na azalzala aranta take fadin nufinshi da yakara marina ai kwa da na nuna mashi cewa ba kullum ake kuana agado ba ganin yadda take kallonshi babu ko alamar tsoro afuskarta yasa ya kalleta da mamaki yace ke anya bakyada tabin hankali kuwa?? Batace komai ba se hannunta da tafizge tadauki ledanta ta raba ta gefenshi ta wuce yana tsaye kamar Wanda aka dasa a gurin se binta yake da kallo aransa yana fadin anya kuwa wannan mutun ce tokodai gamo nayi ne ahankali ya furta (Wa innahu min sulaimana wa innahu bismillahi rahmani rahim) mota ya koma ya zauna driver yaja suka tafi yana karanta duk addu'ar data zomai Abaki...

[18/07, 15:03] Hubbey Frd Ameena Kn: ๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š
๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘งDOMUN KANWATA๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง

๐Ÿ–Šna marubuciya HUSNA kabir zarewa( the mammah girl)

๐Ÿ–Šda sunan allah mai rahama mai jin kai....

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘งDOMUN KANWATA๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง

1โƒฃ5โƒฃโญ2โƒฃ0โƒฃ

AK yana isa unguwar su ana kiran sallah se da ya tsaya yayi sallah a masallacin unguwar su kana ya shiga gida yana isa ya iske mutanan gidan duka zaune a babban Palo suna fira kusa da grany yaje ya zauna bayan sungaisa da kowa na palon ya kalli inna ladidi yace ina su salma ne? Murmushi tayi tace sunje weekend gidan ameena uncle jamilu ne yace AK dama gobe nakeso nayi tafiyar da sassafe AK yace ok allah ya kaimu sarah ce ta zo tazauna kusa da shi tace yaya mu yaushe zamu tafi murmushi yayi yace sarah kinkasa ganewa ni bana so kiyi nesa da nine bana jin dadi idan bana ganinki
baki ta zunburo tace to amma yaya ai 1 week ne kawai fa kanta ya shafa yace to shi kenan next week se kuje tsalle tayi tace nagode yaya dagude ta wuce dakin aysha dan tasanar da ita AK ya bita da ido yana kallonta cike da so da kauna Bashir dan inna ladidi ne ya shigo palon ya zauna kasa kusa da kafan AK yana matsa kafan AK yayi murmushi yakalle shi yace kaga nagane wayon me kake so? murmushi yayi ya sosa kansa yace yaya dama account dina ne yayi low shine nake so adan taimaka murmushi AK yayi yace ba damuwa zan maka transfer grany ce ta daure fuska tace ABID abinda kake ba ka kyautawa yanzu kamar wannan gardin ace yagama karatu amma bazai nemi aikin yi ba sedai kullun yana yawan banza inyaso kudi kuma yazo yana Sosa gemu yana roko
Dariya suka sa apalon shi kuma ya zunbura baki yana gunaguni AK ya dafa kafadansa yace karka damu kabani takardunka inga wane aiki yadace da kai se insama maka baki yawashe yana dariya inna ladidi dake kusa dashi tasa kafa ta zungure shi da kafa ya waigo ya kalleta tamai alama da ido juyowa yayi yarike hannun AK yayi saurin cewa yaya ni a company dinka nake son aiki ?? murmushi yayi yace to komai yazo da sauki se kashirya munday kazo baki ya washe yana godiya inna ladidi na tayashi uncle jamilu ne ya buga tsaki ya tashi ya wuce bangaransu aunty sadiya tabi bayansa ladidi tabiso da harara bawanda ya lura da su kowa yana kallon AK da ke waya da Ahmad ta dayan bangaran Ahmad ya ce guy sakwaran Umma tayi dadi kayi santii AK yace kamar ya??
Ahmad yayi dariya yace kamanta file dinka anan tsaki yayi yace kataho mun dashi gobe Ahmad yace sarah tana nan Ak yace ya akayi?? Ahmad yace gaskiya bazan samu zuwa gobe ba kawai kazo ka karba yana kai nan ya kashe waya AK yayi tsaki aranshi yana fadin wai meyasa idan sarah tana

Please Login or Register in order to submit comment