Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk shirin mu ya gane mune muke musu zagon ƙasa, meye abun yi yanzu haka yace mu haɗu a Amar garden lallai ko ya tona mana asiri wayar da nayi ranar da Hajara a gabansa nayi."
"Kaga idan har Hisham ya gano to tabbas bazai ƙyale ka ba, sai ya zamo barazana ga rayuwar ka, Hmm! Tunde kaje ku haɗun duk abinda zai faɗa maka marar daɗi to ka danne zuciyar ka, sannan Hajara taci amanar mu ya zamo wajibi ta mutu domin kuwa barinta babbar hujja ce ga Hisham zamu iya sa ko Nameer ya sanya Hisham ya goge wannan record ɗin saboda wawa Nameer muna nuna masa nadamar mu shikenan mun gama dashi, yaushe yace ku haɗu."?
Numfashi Tunde ya saki yana dafe kansa yace.
"By 5:00pm."
"Okay to kaje babu abinda zai maka na cutarwa a yanzu ni na sani."
"Okay shikenan amma hankalina ya tashi tabbas Hajara ta tafka babban kuskure kuma zata girbi abinda ta shuka, na tsani na buɗe idanuna na kalli Iyalan Iyabo suna cikin walwala, ka duba yanda suka sanu sukayi suna a duniya, ni kuma mahaifina har ya mutu babu wanda ya sanshi, haka IYABO ya barsa ya mutu a wulaƙance Wale bazan taɓa barinsu suyi nasara ba a rayuwar su ko ta halin yaya sai sun ƙasƙanta."
"Hmmm! A hankali ake dukan ƙarfe har yayi laushi Tunde dan haka a juri zuwa rafi."
"Bani ruwan sanyi nasha zuciyata hura take."
Tunde yayi Maganar cikin matsanancin damuwa, tashi Wale yayi yaje ya kawo masa ruwan.






************


Tun biyar saura Nameer ya shirya cikin ƙanana kaya, ya fito Hisham dake zaune a falo shi da su Tutu da Ummi ne ya cewa Nameer.
"Ina kuma zakaje haka, ka fito da key ɗin mota."?
"Unguwa zanje."
Tutu ne tayi carap tace.
"Yauwa Yaya Nameer sauke ni a gidan su Samira."
"Okay ɗauko mayafinki ina mota, Ummi bara naje yanzu zan dawo."
"Allah ya dawo da kai lafiya amma dan Allah ka dawo da wuri tunda ka dawo dai kasan bamu zauna munyi hira ba ko, ina bukatar lokacinku dukkan ku."
"Ba matsala Ummi insha Allah a gida zanyi sallar magaruba."
"To Allah ya tsare."
Da ameeen Nameer ya amsa yana fita, bai juma ba tutu ma ta biyosa a baya, da kansa Nameer ya tuka motar suka fita.
Sunyi nisa da tafiya Nameer yace.
"Farin ciki na, kinga yadda kika rame kuwa, ashe dai kina yina da yawa."
Murmushi Tutu ta saki tace.
"Yaya Nameer ai ba iya rama kawai nayi ba zuciyata ma so tayi ta buga gaskiya dai naga masifa, yauwa Yaya Nameer wai ina maganar mu ta kwana ne, ya kamata zuwa yanzu ace Soyayyar mu ta bayyana amma har yanzu banga alamun hakan a tattare da kai ba, Soyayyar da nake maka yaya Nameer ta wuce misali."
"Na sani tabbas kina sona fiye da komai a rayuwarki Tutu, sai dai fa ki sani na faɗa miki idan lokaci yayi dole Soyayyar mu zata bayyana har yanzu akwai sauran lokaci tukunna."
"Wani irin sauran lokaci meka rasa wanda zai hanaka Aure kana da kuɗi to meyasa lokacin baiyi ba.?"
Tayi Maganar dai-dai sunzo kofar gidan su Samira, parking yayi tare da cewa.
"Lokacin ne dai baiyi ba, bana son doguwar magana, kije idan na dawo ma karisa Maganar."
Kanta Tutu ta kaɗa tare da cewa.
"Shikenan zan jiraka kazo ka ɗaukeni."
"Okay."
Yayi Maganar Tutu na fita motar ya yiwa key tare da shan kwana yabar layin, darect kofar gidan su Jidda yayi parking, yaro ya hango ya kirasa tare da cewa ya shiga yace wa mamar Jidda tayi bako.
Yaron ya ɗan juma da shiga kafin suka fito da Basmah har bakin motar Nameer ganin Nameer yasa Basmah razana tare da zaro idanunta a tunaninta yazo ne shima ya ciwa Umma mutunci cikin nauyin baki Basmah tace.
"Kaine! Kazo ne kaima ka rama abinda Jidda ta maka, Umma tana da hawan jini dan Allah na rokeka, karka ɗaga mata hankali ka dubi darajar mahaifiya ka kalleta a matsayin uwa dan Allah."
Murmushi Nameer yayi yace.
"Ko ɗaya ni banzo na ɗagawa wani hankali ba, ina son ganinta zanyi magana da ita."
"Shikenan muje."
Basmah tayi Maganar tana yin gaba Nameer yabi bayanta, a baranda Basmah ta shinfida masa tabarma kafin ta shiga ta yiwa Umma magana babu jimawa suka fito tare da Umma, a bakin kofa umma ta zauna cikin girmamawa Nameer yace.
"Barka Umma ina yini."
"Lafiya alhamdulillah! Basmah ta ce min kaine wanda Jidda tasa aka kulle ko, kayi haƙuri ina baka hakuri Jidda yarinya ce, tayi hakanne bisa kuskure duk da bansan meya kawo ka wajena ba amma banga tashin hankali a tattare da kai ba."
"Hakane Umma ni sam banga laifin Jidda akan kamani da akayi ba, nasan tayi komai ne akan gaskiyarta, nima zuwa nayi na baku haƙuri akan abinda ɗan uwana yasa aka mata ba kulleta bane matsalar aikinta da yasa ta rasa, saboda nasan insha Allah gobe ina zuwa Dpo zai saketa, kiyi haƙuri Umma insha Allah zan samowa Jidda aiki mai kyau wanda yafi wanda ta bari."
Idanunta Umma ta zaro tace.
"Bayan kamata da yasa akayi harda aikinta yasa ta rasa yanzu an kori Jidda daga wajen aiki innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Wannan ɗan uwan naka yana da zuciya kuwa a ƙirjinsa, kasan mutum nawa aikin Jidda yake taimakawa kuwa, itace ci da sha na gidan nan, ita komai na makarantar ɗan uwanta suturar da muke sawa a jikinmu duk da aikinta muka dogara meye ribarsa idan ya toshe mana hanyar ci da sha ɗinmu, ashsha wannan yaro bai kyauta ba, amma babu komai bakin da Allah ya tsaga bazai hanasa abinda zai ci ba Allah ya shiryesa."
"Umma Hisham ba mutumin banza ba ne, zuciyar sa ne tayi yawa amma bayan haka ɗan uwana mutumin kirki ne, zuciyarsa na hasala akaina muddun za'a ɗaga min yatsa to wallahi Hisham bazai iya riƙe kansa ba, na ji daɗi da kika masa addu'ar shiriya, ki ƙara hakuri gobe ƴarki zata dawo kuma insha Allah kamar yadda na faɗa zan sama mata aiki mai kyau."
"Bakomai Allah ya mana mai kyau kaima Allah ya maka albarka."
"Ameeen Umma." Nameer yayi Maganar yana ciro kuɗi dubu hamsin a aljihun sa ya ijiye a gaban Umma Basmah dai tana zaune tayi shuru ga damuwa da tunanin abbanta.
"Ga wannan Umma kwayi wata bukatar da ita."
Kanta Umma ta girgiza tace.
"A'a yaro ka barshi bama buƙata muna da komai."
"Ba'a mai da hannun kyauta baya Umma ni ma ɗanki ne ki amsa kimin addu'a albarkar ku ita muke bukata."
Wani irin kaunar Nameer Umma taji take taji ya burgeta domin kuwa da alamu yaron yana da dattako da mutunta na gaba dashi murmushi Umma tayi tace.
"To na gode sosai Allah ya saka da alheri, Allah ya maka albarka."
"Yauwa Umma haka nake so ameeen na gode ni zan koma."
"To ka gaishe da mutanen gida."
Tashi Nameer yayi ya fita cike da farin ciki da ƙaunar Umma matar sam bata da hayaniya ko kaɗan matar kirki tabbas wannan ƴaƴanta sunyi sa'ar samun uwa ta gari.
Basmah har bakin motarsa ta rakasa.
"Nameer mun gode sosai nayi zaton kamar yadda Hisham yake kaima haka kake sai gashi kunyi banbanci sosai kai mutumin kirki ne na gode sosai da kulawarka garemu dan Allah ka dakatar da faɗan dake tsakanin Jidda da Hisham."
"Hmmm! Karki damu Basmah insha Allah komai zaizo ƙarshe, shima Hisham mutumin kirki ne zafin zuciya ne kawai ya masa yawa, wanda yake zaune dashi kullum shi zai faɗi waye Hisham."
"Hakane mun gode."
Murmushi Nameer yayi dubu talatin ya ɗauka ya bawa Basmah, amsa tayi cikin farin ciki tana godiya tana kallon Nameer yaja motarsa yabar ƙofar gidan, murmushi ta saki maganar Jidda ne ya faɗo mata a rai
_Insha Allah Basmah Allah zai mana zamu samu kud'in aikin da za'a yiwa Abba."_
Numfashi ta saki ta koma ciki ta nunawa Umma kuɗin murmushi Umma tayi ta ƙara mata dubu ashirin tace ta haɗa aje a yiwa Abba aiki sosai Basmah taji daɗi, sun juma sosai a wajen suna zancen kirkin Nameer.




*************


5:14pm



Zaune Hisham yake a Amar garden shida Sadiq, Motar Tunde tayi parking a parking space, Cike da zullumi Tunde ya fito yasan babu inda Hisham yake zama sai wajen coffee nan ya nufa kamar yadda yayi zato kuwa haka ya samu yana wajen, da ke zuciyarsa yayi ya nufi teburin da suke, zama yayi a kujerar da babu komai hannu ya miƙawa Hisham.
"Ƙazanta ne bawa hannu mai datti hannu mai tsafta, Tunde good job."
Murmushi Sadiq ya saki yace.
"Good Tunde gaskiya ka yi bazata da yawa amma abun mamakin Tunde kana zaton zaka wurgawa zaki Dutse ya samesa, mtsss! Kayi kuskure Babba."
Murmushi Hisham ya saki yace.
"Maybe ya manta ne, amma yanzu zan tuna masa da Zaki zai yi faɗa, kai ɓarawo ba iya satar ka iya ba kenan harda tuggu, da naso da na tona maka asiri Tunde ta hanyar kunnawa Abba wannan record ɗin, sai dai bazanyi haka domin kuwa bana bukatar ɗagawa Abba hankali a yanzu, amma fa ka sani dole ne wannan video record ɗin yaje ga Abba, Saboda zan sanar dashi ne ta hanyar da hankalinsa bazai tashi ba, saboda yasan waye ku ƙazantar da kuke rufe masa zai bayyana kasan meyasa na kiraka saboda na baka saƙo ka kaiwa wannan tsohuwar kakar taka, kace mata Lulluɓin biri zai yaye ta fara neman hanyar tsira domin kuwa asirinta ya kusa tonuwa."
Wani irin suya da raɗaɗi zuciyar Tunde ke yi, bakinsa ya buɗe yace.
"Hish............
Mari Hisham ya ɗauke sa dashi bai dasa aya ba yace.
"Karka kuskura ka ambaci sunana da wannan ƙazamin bakin naka, ka sani bana bukatar jin Muryar ka a nan, kuma ka tuna da wannan ko wani Aji akwai malaminsa sai dai amma Malaman suna suka tara, wani malamin hoti ho ne baya sanin ana kallon sa, kaje ka faɗawa Tsohuwar kakar ka, malamin zamani yazo ta shirya sauyawa wannan tsohon malamin Aji, ka ce mata komai gudunta bazata kamo gobe ba, dole sai ta jira yazo da kansa, mu gobe ne munfi ƙarfin yau, kowa da burinsa, haka zalika muma da burin mu, ku naku burin shine ganin bayan mu, yayin da mu namu burin shine mu tunbatsa a duniya labarin mu ya zaga ko ina, baku isa kuma ku toshe wannan hanyar ba dole ku kallemu ku barmu ko baƙin ciki ya zamo ajalinku, ka faɗa mata cewa shuka take a idon makwarwa tar Hisham yake kallonta da idanunsa, tashi ka fece ko na karya maka muƙamiƙinka ɓarawon banza."







_____________________________________



Share and comments my fan's🥰






*UMMU NASMAH CE✍🏻*





_For More Information 08147537180_
[5/23, 7:31 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*FREE BOOK ONE📚*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻





*_Page 21 to 22_*




Tunda Tunde ya dawo ya sanar da Mamabisola abinda ke faruwa hankalinta ya kuma tashi damuwarta ta ƙaru sai kaiwa da komowa take ta kasa samun nutsuwa, hankalinta duk a kaɗe ta wacce hanyar zata toshe wannan ɓarakar meyasa Hisham yake son ya shiga rayuwarta ne, numfashi ta saki tare da samun waje ta zauna.
"Tunde lallai Hisham zai zamo karan da zai tsokale mana ido muddun mukayi wasa."
"To amma Mama ya kike ganin zamuyi kar fa asirin mu ya tonu shi nake tsoro."
Girgiza kanta Mamabisola tayi tace.
"Ka daina jin tsoron yau muji tsoron gobe kamar yadda ya faɗa saboda bamu san da me zata zo mana ba, tunda har Hisham ya fita daga Police station bai tona asiri ba to a wannan wasan ruwa tasha, bazai fasa wannan ƙwan ba, ka bari zansan yadda zamuyi dashi kafin ƙwan yayi wari zamu aikasa shida hujjar gaba daya, yaro ne shi bai san wuta ba sai ya taka."
"Amma dai Mama karki ja lokaci muna bukatar ɗaukar mataki akan Hisham da gaggawa, saboda matsala ne shi a garemu yasan abinda muke shirya musu."
"Karka damu tsalle ɗaya ake a faɗa rijiya sai ayi dubu ba'a fito ba dani yake zancen."
Tashi Tunde yayi yace.
"Okay shikenan."
Yayi Maganar yana barin falon, da kallo Mamabisola ta bisa cike da ƙaunarsa tanayin komai ne saboda shi.



***********


Washegari da misalin 12 na rana motar Nameer tayi parking a police station ɗin, har ciki ya shiga cikin Sa'a kuwa ya samu Dpo yana nan waje hannu ya basa sukayi musabaha suna dariya.
"Ɗan sanda abokin kowa."
Cewar Nameer murmushi shima Dpo yayi yace.
"Nameer Abdulzahir jiya akayi belinka yau har kazo belin wata."
Dariya Nameer yayi yace.
"Harma ka fuskanci abinda yake tafe dani kenan, to Allah yasa dai za'a baka belin nata amma Dpo ni fa a nawa tunanin Hisham shiya yaudari yarinyar nan ta iya yiwuwa gadar zare ya ƙulla mata, kasan halin Hisham zai iya aikata komai domin ganin ya tozarta yarinyar nan da zaka min alfarma tunda babu wani na sama da kai da yasan wannan Case kawai a rufe Case ɗin ya zamo baya da file a cikin Police station ɗin nan saboda hakan tamkar ɓata mata suna ne."
Girgiza kansa Dpo yayi.
"Impossible a rufe file ɗinta, because an riga da an buɗe zan baka belinta amma dole zamu cigaba da bincike a kanta wannan shine abinda zan iya yi maka."
Murmushi Nameer ya saki wai Police ne zai cigaba da bincike akan rashawa.
"Dpo in dai akan rashawa ne bai kamata aji bakin ku ba saboda kune kukafi kowa cin hanci da rashawa a ƙasar nan, sorry amma ka sani dole ne za'a rufe file ɗinta, ni ba Hisham bane komai da lissafi nake yinsa, kasan me da ace Hisham kuka rufe na rantse da Allah bazai kwana ba domin kuwa ni nafi Hisham basira da lissafi nake komai iya basirar Hisham a neman fitar dani wajen commissioner of police kawai ya tsaya amma ka sani akwai baban commissioner Minister governor da sauransu, shi kansa Abba bai so fitar dani bane saboda gudun abinda al'umma gari zasu faɗa akansa sannan yasan ina da gaskiya dole zan kuɓuta bawai dokar banza ta gwamnati bane tasa ban fito ba, amma ka sani a wannan karon file ɗin zai rufu ba kuma za'a ƙara buɗesa ba har abada."
Murmushi shima Dpo yayi yace.
"Okay shikenan a rufe file ɗin mu gani na baka nan da 24hr."
Bakinsa Nameer ya taɓe yana girgiza kansa tare da kallon agogon dake saƙale a hannunsa.
"No 10minute 24hrs is over, hmmm bara muga."
Nameer yayi Maganar yana ɗaga waya ministan Jiha ya kira ringing ɗaya ya ɗaga bayan sun gaisa Nameer ke sanar dashi abinda ke faruwa da kuma bukatar sa, kafin suka katse kiran, bai 5minute ba da katse kiran commissioner ya kira Dpo tare da umarnin a rufe Case ɗin Jidda a sallameta, Dpo yaso magana amma commissioner ya hanasa magana numfashi Dpo ya saki yana kallon Nameer shi kuwa Nameer murmushi ya saki tare da miƙewa tsaye yana cewa.
"Na faɗa maka ni ba Hisham bane da zan dage wajen neman alfarmar ka, dama ɗaya kawai nake bawa Mutum a rayuwarsa da zarar yayi wasa da wannan damar zanbi ta kansa na shige gargadi ne wannan Dpo, nafi Hisham tsauri zafin zuciya kawai ya fini da gaggawa, kuje ku sako yarinyar mutane."
Cikin ɓacin rai Dpo yaje ya buɗe Jidda dake zaune tana sauraron su a cikin cell, domin kuwa a bakin cell suke tsaye, fitowa Jidda tayi a kwana ɗaya har ta faɗa idanunta kuma sun zurma bata jira Nameer ba ta fito waje tana fitowa Ahmad yana shigowa da babur ɗinsa numfashi Jidda ta sauƙe tare da nufar Ahmad da sauri, tsayawa tayi gaban babur ɗin daya kashe.
"Ahmad ina Ummana tayi fushi dani ko, Allah yasa bataji labarin na rasa aikina ba, bazata iya jurewa hakan ba, Allah yasa baku faɗa mata ba, Hisham ya cuceni Ahmad ya min mungun illa bazan taɓa kyalesa ba wallahi sai ya girbi abinda ya shuka."
Gyara tsayuwar sa Ahmad yayi yana kallon Jidda kafin yace.
"Waye yayi belinki.?"
"Ni ne nan."
sukaji muryar NAMEER daga bayansu juyowa Ahmad yayi duk wanda yake cikin kwara state kuma yake ganin gidan tv to tabbas yasan Nameer ko da kuwa bai taɓa kallonsa a zahiri ba.
"Nameer Abdulzahir Iyabo, Barka amma nayi mamaki ace ɗan uwanka shine yasa ta cikin wannan halin amma kai kuma kazo ka fitar da ita duk da itace tayi sanadiyar shigarka cell, hmmm! Sorry da tambayar da zan maka Nameer meyasa kayi belinta."?
"Bani da amsar tambayar ka saboda nima bansan dalilin ba, Jidda muje na mayar da ke gida saboda na yiwa Mahaifiyar ki alƙawarin cewa zan dawo mata da dake a wannan lokacin."
Juyowa Jidda tayi cike da mamaki tace.
"Ummata ka yiwa alƙawarin zaka dawo mata dani gida, kunje gidan mu ne kun gwada mata rashin mutuncin ku, meya kaika gidan mu, Meyasa zakuje ku ɗagawa mahaifiyata hankali meye laifina saboda na nemawa talaka ƴar uwata ƴanci, meye laifin hakan, anfi bukatar a tozarta talaka ne saboda shi talaka bashi da ƴanci meyasa yawancin masu kuɗin mu azzalumai ne marassa iman...........
Bata ƙarisa ba Nameer ya katseta cikin tsawa mai firgitarwa.
"Ya isheki haka! Nima ɗin talaka ne kamarki, wataƙila ma ke kin fini wadata tunda har kina da aikin yi a wannan lokacin, Masu kuɗin mu ba duka suka haɗu suka dawo azzalumai ba, akwai na gari a cikin su, domin kuwa ni Alhaji Iyabo yamin sutura a rayuwata, iyayena ƙasƙantattun talakawa ne marassa gata da ƴanci a rayuwa wadanda abinda zasu saka a bakin su ma yake gagararsu, wannan mai kuɗin shine yamin riga da Wanda domin ya suturta rayuwata, karki sokesa Jidda gara ni ki sokeni sunmin hallacin da babu wanda ya taɓa minshi a rayuwata ciki harda jinina, domin kuwa ya ɗaukoni ya sani a jikinsa ya mai dani ɗan da ya haifa a cikin sa dani da Hisham bamu da banbanci a wajensa."
Gabaki ɗayansu shuru sukayi musamman Jidda da tayi suman tsaye tsabar mamaki da ƙin yadda da abinda kunnuwanta ke jiyo mata, cike da mamakin tace.
"Kai ba ɗan Abdulzahir Iyabo bane, me kake son faɗa min Nameer.?"
Kansa Nameer ya ɗaga mata idanunsa na ƙoƙarin ciko da hawaye ya dubi Ahmad yace.
"Ƙwarai ka ijiye Babur ɗinka muje na baku mamaki Ahmad."
Mashin ɗin Ahmad ya yiwa key tare da duban Jidda yace.
''yana da kyau muje mu saurari labarinsa Jidda domin kuwa na kaɗu sosai da jin Nameer ba ɗan Alhaji Iyabo bane."
Kanta Jidda ta kaɗa tare da bin bayan Nameer motarsa suka hau ya Nameer ya jasu har unguwar Ile-Ire unguwa ce ta talakawa sosai infact ma kamar ƙauye haka unguwar take yawancin gidajen unguwar irin gidajen lakan nan ne na da can wasu gidajen ma babu gini sai rufin langa-langa, wani dogon layi sukabi mai yawan kwatoci, a ƙofar wani tsohon gida na laka rabinsa duk ya rushe fitowa sukayi Nameer ya musu jagora har cikin gidan, wani ƙaramin dakali da yasha ƙura Nameer ya kaɗe da kansa suka zauna gabaki ɗayansu kallon gidan suke ita Jidda tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin tsohon gida lalatacce irin wannan ba.
Nameer numfashi ya saki tare da dubansu mamaki ya hango ƙarara a idanunsu.
"Kuna mamakin wannan gidan ko, shine gidan mahaifina a nan aka haifeni anan na fara rayuwata bari na baka labarina yadda zaku fahimci cewa Alhaji Iyabo wato Abbana yamin Rana a rayuwata.





*_SHEKARU 27 DA SUKA GABATA_*




Ruwa ake sosai tamkar da bakin ƙwarya garin duk ya narke yayin da Ruwan ke tafiya da iska, zaune nake takure a gefe yayin da ɗakin mu ke yoyo kwanon ɗakin duk ya huje gefen gabar ɗin ɗakin mu yafi ko ina yoyo kwano Mamana tasa take tare ruwan dubanta ta mayar gareni da nake takure tace.
"Babana yunwa kakeji ko, kayi haƙuri bari Babanka ya shigo muga me zai dawo dashi bani da abinda zan baka Babana kayi haƙuri kaji."
Kaina na kaɗawa Mamanmu nace.
"Mama yunwa nakeji sosai gashi Baba yaƙi dawowa, ni dai Mama ko garin rogo ne ki bani zansha ko ba Suger."
Zama Mamanmu tayi gefena ta kamo hanuna tace min.
"Babana bani da komai na faɗa maka nima raina baya jin daɗin halin da kake ciki na yunwa, kayi haƙuri kaji insha Allah yanzu baban naka zai dawo."
"To Mama Allah ya dawo dashi lafiya."
Nayi Maganar cikin sanyin jiki, yunwa kuma tamkar zata kasheni, hanjin cikina kuwa ji nake tamkar sun naɗe, ga feshin ruwa dake shigo mana bayan yoyon da ɗakin keyi kana kallon Mamana a wannan lokacin zaka fahimci tana cikin damuwa.
Muna nan zaune Baban na ya dawo duk ya jiƙe jikinsa sai karkarwa yake yana layi, idanunsa sunyi ja, babu komai a hannunsa hakanne ya tabbatar min Baban mu bai dawo da komai ba, zuciyata ne ya tsinke domin nasan daƙyar idan ba da yunwa zan kwana ba, duk da nasan iyayena suna bakin ƙoƙarin su wajen ganin ban kwana da yunwar ba, ko da su zasu kwana da ita, zama yayi gefe har yanzu jikinsa rawa yake ko magana baiyi ba, Mama ne tace.
"Baban Nameer lafiya kuwa, ya akayi ka bari ruwan nan ya dakeka haka, ka tashi ka sauya kayanka ko sanyin zai ragu maka.?"
Kansa Baba ya girgiza cike da damuwa yace.
"Ba sanyin bane damuwata Usaina abinda zaku ci shine damuwata kun wuni baku ci ba, bazai yiwu ku kwana baku ciba, ban samu komai ba nayi iya yina amma babu abinda na samu yau babu kasuwar Raken da ƙyar na sai da sanda ɗaya naira 70 kinga itace

Please Login or Register in order to submit comment