Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wawiya marar lissafi, an faɗa miki Hisham zai nemi taimakon ƙaskantacciya irinki ne, bari kiji wannan abin da na miki yanzu ƙofa na ƙwanƙwasa miki ba'a buɗe ƙofar ba tukunna kin sokeni a ƙirji kuma na faɗa miki idan na tashi sukanki a ƙahon zuciyar ki zan sokeki, wannan jifan da na miki mutum biyu zai samu na farko ke da kuma mahaifiyar ki domin kuwa itama sai taji ciwo kamar yadda kika saka tawa Mahaifiyar taji ciwon rufe mata ɗa da kika saka akayi, wasan ya fara daga yanzu mu buga mu gani tsakanin ni da ke waye zai faɗi."
Wani irin huci Jidda take sosai ranta ya hasala wato tarko Hisham ya ɗana mata da wadannan kuɗaɗen, zatayi Magana Manager ɗinsu ya shigo tare da katseta yana wurga mata takaddu guda biyu Basmah ce a bayansa cikin tashin hankali, idanunta sai zubar da hawaye yake duk abinda ya samu Basmah lallai itace sila.
"Baki isa kin ɓata mana sunan ofishin mu ba, kin san girman laifin da kika aikata kuwa amsar cin hanci almundahana a office ɗin mu a matsayinki na ƴar jarida da kece zakiyi kira da a daina, wannan takaddun na korarki ne daga aiki mun koreki karki sake doso mana office bama bukatar ki."
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo daga idanun Jidda babu wanda zai yarda da ita ko mai zata faɗa, shikenan ta rasa aikinta ta rasa damarta ta rasa hanyar da take taimakon ahalinta yaya zasuyi da me zasuci abinci.
Ɗagowa tayi ta kalli Hisham tare da girgiza kanta tace.
"Kaji daɗi ko, kaji daɗi ka zuba ruwa a ƙasa ka sunkuya ka shanye amma na rantse kayi danasanin taɓa min aikina."
Tayi Maganar dai-dai zuwaira na tura ta cikin cell ɗin murmushi HISHAM ya saki Nameer ne ya dubi Dpo tare da cewa.
"Wai me kuke aikatawa ne haka macece fa ita akan me zaku tozarta ta, wannan ba adalci bane Hisham meyasa Meyasa baka yafiya Dpo ka bani belin ta."
"Bazai yiwu ba domin kuwa bazataci banza ba, amanar ƙasarta taci dan haka dole a hukuntata, babu ruwanka a cikin wannan Case ɗin Nameer."
"Da ruwana Hisham bazan zuba idanu ku wulaƙanta mace ba."
Dpo ne yace.
"Sorry Nameer ko da za'a ba da belinta ba yau ba."
Numfashi Nameer ya saki tare ficewa a zuciye, hannu Hisham ya bawa Dpo sukayi musabaha, yana amsar kudaden sa kafin suka bi bayan Nameer shi da Sadiq.


"Manager me kake bukata naga kamar kana da abin cewa?"
Dpo ya jefa masa tambayar bayan fitar su Hisham.
"Sunan Jarida ta, karta ɓaci dan Allah ka rufa min asiri kar aji wannan Case ɗin Please Dpo kasan ni bani da laifi, idan wannan video ya fita tabbas zan samu matsala."
"Hakane Manager baka da laifi gaskiya ne insha Allah babu abinda zai faru zanyi magana da Hisham ɗin insha Allah zai goge video ɗin."
"Na gode Dpo."
Manager yayi Maganar yana hararar Jidda.

Basmah kuwa sosai take kuka hankalinta yayi mungun tashi, Dpo ne ya kalleta tare da cewa ta fice tabar masa wajen cikin tsoro Basmah tabar wajen.
Jidda tunda ta shiga cell ɗin ta haɗa kai da gwiwwa cikin matsanancin tashin hankali, idan Umma taji wannan labarin tasan hawan jininta sai ya tashi, hawaye ne ya biyo idanunta taja numfashi tare da furta.
"Hisham! Hisham! Hmmm.!"
Sai kuma ta daki bango da hannunta zuciyarta na tafasa tana jin wani irin haushi da tsanar Hisham.




************


Basmah a wajen station ɗin ta tsaya tare da kiran Ahmad tace yazo yanzu su haɗu a ƙofar gidan su, kafin ta katse kiran tana tare adaidaita sahu ta hau, yama rigata zuwa a tsaye jikin babur ɗinsa ta samesa, mai adaidaita ta biya kuɗinsa tare isowa wajen Ahmad yana ganinta ya tabbatar ba lafiya ba domin kuwa idanunta sunyi jajur alamun tasha kuka.
"Basmah lafiya ko jikin Abban ne.?"
"A'a Ahmad, Ahmad! Nasa Jidda a cikin masifa banyi zaton zata shiga cikin wannan balain ba, mai zan cewa ummanta me zan ce mata innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!."
"Basmah ki nutsu ki tsayar da kukan ki faɗa min meke faruwa."
Cikin shashshekar kuka take sanar da Ahmad abinda ya faru, numfashi Ahmad ya saki tare da furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ashsha! Basmah garin yaya kika bata wannan gurguwar shawarar, kin san hakan babban laifi ne, a yanzu rayuwa ta sauya ba kowa bane yake yadda yayi taimako saboda zaka taimaki mutum ne sai shi kuma ya jefaka cikin masifa yanzu ina ranar wannan taimakon, yanzu tana can police station ɗin kenan.?"
"Tana can ina cikin tashin hankali Ahmad bansan wacce irin masifa Jidda zata faɗa ba, nayi kuskure Ahmad ka kuɓutar da Jidda dan Allah."
"Hmmm! Babban kuskure ma kuwa amma ita kanta Jidda tasan bazaki mata haka saboda ta tozarta ba, na tabbata zata miki kyakkyawar fahimta, yanzu bamu da damar da zamuje muyi belin Jidda dole ne sai ta kwana, gobe zanje Police station, yanzu abinda zai faru muje gidan nasu wajen Umman ni zan fahimtar da ita."
"Amma Jidda tace bata son Umma tasan tana Police station hankalinta zai tashi tana da hawan jini."
"Karki damu nasan yadda zan fahimtar da ita."
Kanta Basmah ta ɗaga kafin suka nufi gidan su Jidda Basmah ce ta fara shiga ta samu Umma zaune cikin barandarta, amsa sallamar Basmah Umma tayi tana cewa.
"Basmah kece yanzu bakije wajen aikin naku bane yau."?
"Naje Umma ni da Ahmad zai shigo ku gaisa."
Murmushi Umma tayi tace.
"Ai sai kice min keda suruki na ne, kije ki shigo dashi Umma tayi Maganar tana ɗaukar hijabinta ta sanya a jikinta, da sallama Ahmad ya shigo suka gaisa Umma tace ya zauna a tabarma zama Ahmad yayi kansa a sunkuye.
"Barka da rana Umma fatan mun sameki lafiya."
"Lafiya lau Amadu ya aikin naka da can gidan naku."
"Komai lafiya Umma."
"Masha Allah! Allah ya muku albarka, Basmah yau ke kin tashi da wuri kenan kinbar ƴar Uwar taki a can."?
Kanta Basmah ta sunkuyar ƙasa idanunta ya ciko da hawaye Ahmad ne yayi saurin cewa.
"Umma dama ai munzo mu miki bayani dan gane da jiddan, amm Umma dan Allah ki nutsu ki saurare mu karki ɗaga hankalinki."
Cikin tsinkewar zuciya Umma tace.
"Amadu wani abunne ya faru da Jidda ko accident tayi ta mutu ne."?
"A'a Umma ki kwantar da hankalinki babu abinda ya samu Jidda tana lafiya, kawai ƴar hatsaniyar da suka samu da wannan yaron ɗan gidan Iyabo HISHAM shine yayi report ɗinta a police station bayan an gano ƙazafi aka yiwa ɗan uwan nasa shine fa Police suka kamata, amma Umma ba wata matsala ba ce insha Allah gobe zanje nayi belinta, dan yanzu bazai yiwu su bani belinta bane da tuni mun dawo tare da ita amma insha Allah gobe zata dawo sai kuma musan yadda zamuyi mu kashe Case ɗin."
Umma idanunta ta runtse tare da furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati! Subahanallah! Tana Police station wato da nace ta cire hannunta a case ɗin bata cire ba, sanda ta jawo min masifa, da Jidda taji magana ta da wannan tashin hankalin bai sameta ba abinda nake kiyaye mata kullum kenan bata da gata ta daina shiga cikin rigimar da bata shafeta ba, Amadu yanzu goben zata dawo kana jin kuma case ɗin zai iya mutuwa, kai ɗan sanda ne ka taimaka min Amadu kuje gidan Alhaji Iyabo ku bawa yaron haƙuri idan ta kama ni naje da kaina ne ma sai naje."
"A'a Umma ba sai kinje ba nima zan iya komai Jidda zata dawo insha Allah ki kwantar da hankalinki, Basmah ki zauna tare da Umma ni zanje asibiti sai na sanar da Mama abinda ke faruwa kar ta jiki shuru ki kula da ita."
Kanta Basmah ta ɗaga tare da tashi ta raka sa waje tsayawa sukayi Basmah tace.
"Ahmad baka sanar da Umma cewa ankori Jidda a aiki ba."
"A'a bai kamata ta sani yanzu ba hankalinta zai tashi fiye da yanzu dan haka karki sanar da ita mu jira har mu kashe case ɗin tukunna ke dai ki kula da ita tunda kinga tana da hawan jini damuwa kuma shine first abinda yake tayar da hawan jini ki tabbatar bata shiga cikin damuwa ba, ni bara naje."
"Shikenan zanyi abinda kace amma dan Allah gobe kayi belin Jidda da wuri."
"Insha Allah! Ahmad yayi Maganar yana tafiya komawa ciki Basmah tayi cike da zullumi.





_____________________________________




*Share and comments my fan's🥰*





_UMMU NASMAH CE✍🏻_






*FOR MORE INFORMATION 08147537180*
[5/19, 9:19 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*


_Ina miƙa sakon ta'aziya ta ga Hajiya Aisha Lawwali Allah ya jikan mahaifinki Alhaji Lawwali Isa Jalo Allah yasa can yafi masa nan yasa mutuwa ta kasance hutu a garesa idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da imani Allah ya karbi bakon cinsa._



*_bazan gajiya da jingina gareku ba JALALA FAN'S a duk inda kuke ina muku fatan alheri sharhinku yana isowa gareni._*



_Kuyi hakuri jiya na samu mistake ɗin page, page ɗin jiya shine 15 to 16 ba 17 to 18 ba na yau shine zai kasance page 17 to 18 mistake na samu._





*FREE BOOK ONE📚*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻





*_Page 17 to 18_*




Ciki Basmah ta koma gefen Umma ta zauna tayi shuru.
"Basmah da yawan yara suna faɗawa cikin masifa saboda kujewa maganar iyaye da sukeyi a ko yaushe uwa takan nunawa ɗanta hanyar da zai samu nasara ne a rayuwarsa, babbar musibace kin bin maganar iyaye na tabbata da jidda taji maganata to tabbas da bata shiga wannan halin da take ciki yanzu ba hankalina yana tashe."
"Kiyi haƙuri tabbas Jidda tayi kuskure amma na tabbata ita bata ɗauki hakan akan zai zamo mata matsala ba, ki yafe mata Umma ki yi addu'a Allah ya fitar da ita daga sharrin Hisham."
"Ameeen Basmah amma duk wanda baiji bari ba zaiji hoho, ina mata addu'a Allah ya tsareta."
"Ameeen Umma."
Basmah tayi Maganar cikin sanyin jiki.




***********


A parking space sukayi parking kafin suka fito tare dukkan su har Sadiq cikin falon suka shiga Abba da Ummi suna zaune yayin da Tutu ke kitchen tana abincin rana, sallama sukayi Ummi ta ɗago kanta ganin Hisham da Nameer yasa Ummi miƙewa da sauri.
"Alhamdulillah! Nameer welcome."
Tayi Maganar cikin farin ciki, shima Nameer cikin dariya ya tafi da gudu ya rungume Ummi.
"Welcome Ummi nayi missing ɗinki."
"Nameer kaine alhamdulillah! Allah na gode maka."
Tayi Maganar tana sakinsa, zama dukkan su sukayi NAMEER ya dubi Abba yace.
"Masha Allah! ABBA dama na faɗa muku mai gaskiya baya taɓa tozarta ba gashi na dawo ba."
"Hakane Nameer, Hisham da wani hujja ka cire Nameer daga wannan haɗarin."?
Murmushi Hisham ya saki tare da cewa.
"Tunda ya fito ai zance ya ƙare."
Hisham yayi Maganar a takaice yana tashi yabar wajen gudun kar Abba ya kuma jefa masa wata tambayar.
Kasancewar Abba ba mutum bane mai yawan ƙwaƙƙwafi yasa shi basar da maganar cikin farin ciki suke hira har Sadiq.
Tutu da ke cikin kitchen ne take jiyo tamkar Muryar Nameer, shuru tayi ta kasa kunne tabbas dai Muryar Nameer ɗin take jiyowa, da sauri ta fito tsayawa tayi turus tana kallonsa wani irin farin ciki ne ya lulluɓe mata zuciya, da sauri ta ƙariso kusa dashi.
"Yaya Nameer hmmn alhamdulillah! Yaya Nameer ka fito Wayyo daɗi."
Dariya Nameer yayi tare da ɗaga mata kai.
"Na dawo Tutu kin rame da yawa ko dai fargaba na ne ya ramar da ke haka.?"
"Yaya Nameer ai dole na rame gidan ne duk babu daɗi babu kai."
"Gashi ai na dawo bara na haura sama nayi wanka 2days ban samu na watsa ruwa ba."
"Shikenan sai ka fito."
Tayi Maganar tana komawa kitchen Sadiq duban Nameer yayi yace.
"Nima gida zan koma zuwa yamma in kun fito zamu haɗu."
"Okay shikenan na gode Sadiq."
"Ba komai."
yayi Maganar yana yiwa Ummi sallama.



A kwance ya tadda Hisham ya na famar zuƙar sigari hancinsa Nameer ya toshe tare da ƙarisawa da sauri ya wafce sigarin.
"Haba Hisham haba dan Allah, ka min alƙawarin ka daina shan sigari amma kuma ka karya min alƙawarin Hisham why.?"
Yayi Maganar yana take sigarin a ƙasa idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur Hisham ya ɗago ya kalli Nameer maganganun Jidda suna ƙara faɗo masa yaji zafi da ƙunar maganar.
_Amma dai anyi faɗuwar baƙar tasa ko nace faɗuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance, ka bada maza ina kurin ina barazanar shin ka fasa tozarta ni ne, Hmm andai ji kunya._
_kaji daɗi ko, kaji daɗi ka zuba ruwa a ƙasa ka sunkuya ka shanye amma na rantse sai kayi danasanin taɓa min aikina_
Da ƙarfi ya furta.
"Har yanzu bata rusuna ba, har yanzu kuri da baki take min, ni ne take cewa zanyi danasanin taɓa mata aikinta, lallai sai na ƙasƙantar da rayuwarta ƙasƙanci mafi muni, sai na sanya mata tsorona wanda sai ta gwammaci ganin mahaukacin zaki da ganina."
Tsuka Nameer yaja yana zama bakin bed ɗin.
"Mtsss aikin banza yanzu duk wannan haukar da jan idon da kake akan Jidda ne, Hisham wai Meyasa kake biyewa ruɗin zuciyar ka ne, yanzu duk wannan tozarcin da ka mata bai isheka ba har akwai wani abinda kake shirin mata wanda yafi wannan muni da aikinta fa ka rabata, Hisham ka rabu da jidda ka dakatar da wannan faɗan haka ya isa."
"Bai isa ba Nameer! Yanzu ma aka fara! Ka sani idan na yanke hukunci *KO KAINA BANA SAURARA* bazan ƙyaleta ba sai naga ƙarshen rashin kunyarta."
"Shikenan Hisham karka fasa, ni kuma zan kareta domin kuwa ta shiga wannan Case ɗin ne akan gaskiyarta kuma ni ta burgeni domin kuwa ba ta goyon bayan zalunci, idan yaso idan ka ɗebo masifar ka haɗa harda ni."
Bakinsa Hisham ya cije tare da cewa.
"Hmmm! Bata goyon bayan zalunci kuma ta amshi rashawa, Hmm! Na fahimci tun farko baka ga laifinta ba ai ba sai ka sanar min ba, ina jin haushi da takaicin zuciyar ka da bata nuna maka masoyanka, kafi ɗaukar maƙiya a masoya, tirr."
"Naji amma ka sani Hisham ba'a taɓa cin nasara akan maƙiyi ta hanyar zafin rai da hasala ka sani idan ka jawo maƙiyinka jikinka babu shakka gobe masoyinka zai zamo, HISHAM dan Allah na roƙeka a karo na biyu ka daina shan sigari dan Allah cuta ce gareka ka kiyaye lafiyarka Hisham bana ƙaunar ciwo ya kwantar da kai, domin kuwa sai na fika cutuwa."
"Naji."
Yayi Maganar a takaice, kansa Nameer ya kaɗa tare da ijiye wayoyinsa ya shiga wanka ya juma sosai a tollet ɗin kafin ya fito ya samu Hisham tuni har yayi bacci Kasancewar zafin da ake na damina yasa Nameer ko mai bai shafawa jikinsa ba turaruka kawai ya fashe jikinsa dasu kafin ya sanya boxer da vest ya kwanta a bayan Hisham, bai juma da kwanciya ba shima bacci ya kwashesa kasancewar gajiya da rashin samun bacci na kwana biyu da baiyi ba, Ummi jinsu shuru ya sata haurowa bedroom ɗin nasu da kanta gaba daya suna bacci murmushi Ummi ta saki cike ƙaunarsu zama tayi a gefen su tana zuba musu idanu.
"A ko da yaushe na ɗaga idanuna na kalleku sai naji wani farin ciki marar misaltuwa, damuwata sai ta kau, kaine jigona Nameer rashin ka gareni zaizamo macewar farin ciki na, a duk sanda ka shiga damuwa nima ji nake tamkar zuciyata ta fashe kaine haskena Nameer farin cikin gidana, tun kana ƙanƙaninka kake kore duk wata damuwata baka taɓa bari wani ya ɗaga min yatsa sai ka karya wannan yatsar, ina jin farin ciki a duk sanda kake nunawa ɗan uwanka hanyar dai-dai, kaine control ɗin Hisham domin kuwa baka taɓa bari ya aikata ba dai-dai ba, ta yaya zan kasa sonka a cikin raina Nameer bayan kafi kowa ƙaunar ta ni da ƴaƴana, muddun ina numfashi bazan taɓa barin rayuwarka ta shiga cikin matsala ba."
Ummi tayi Maganar tana sakin murmushi.
Idanunta ne ya sauƙa akan karan sigarin da Nameer ya ƙwace ya kashe, numfashi ta saki tare da miƙewa ta ƙara musu ƙarfin Ac jin garin da zafi, kafin ta fice domin tasan Hisham ke shan sigari tayi faɗan tayi nasihar amma ya gagara, abun ya zame masa kamar masifa.





************

Da misalin ƙarfe 4 na yamma Tunde ya fito yana jiran su Mamabisola a parking space.

Da shirin su na tafiya ƙauye Mamabisola da Wamimo suka fito duban Tunde Mamabisola tace.
"Kayi sauri mana ka jamu mu tafi kar dare ya mana a hanya."
"Ku shiga muje ai na fito nima."
Yayi Maganar yana shiga motar, suma shiga sukayi har tunde zai ja motar kiran wayar Hisham ya shigo wayarsa.
"Hisham kuma."?
Ya furta yana kallon Mamabisola.
"Ka ɗaga kiran muji meke faruwa."
Kiran ya ɗaga tare da kara wayar a kunnen sa yana danna handsfree.
"Ina jinka Hisham."
Daga can Hisham daya ke zaune bakin bed Nameer yana kwance har yanzu bai tashi daga baccin ba yace.
"Ka ƙara buɗe kunnenka da kyau domin kaji abinda zan faɗa maka da kyau."
"Wai me ya faru ne Hisham."?
"Kafi kowa sanin abinda ya faru, jifan da kuka yiwa Nameer ya faɗi ƙasa domin kuwa bai samesa ba, wai shin ance maka taɓa ɗan zaki wasa ne, ina neman mutuwa ne, kuma ka nema ka fara tseratar da rayuwarka domin kuwa nayi alƙawarin sai na baka kashinka a hannunka."
Idanunsa Tunde ya zaro ya kalli Mamabisola kafin yace.
"Me kake nufi Hisham ban fahimta ba."?
Murmushi Hisham ya saki tare da cewa.
"Zaka fahimta domin kuwa tsuntsuwar da kuka aikowa Nameer tana hannun Hisham sannan inda ka faɗo kayi waya da ita a gabana kuma na naɗi komai, kazo Amar garden ka sameni by 5:00pm idan ba haka ba zan tona maka asiri duniya tasan waye ku kai da wannan kakar taka lallai kazo ka sameni."
Hisham yayi Maganar yana katse kiran bai jira amsar Tunde ba, a gigice Tunde ya kira layin Hisham, switch 📴 ya kashe wayar gaba ɗaya.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Mama kina jin abinda yake faɗi asirin mu ya tonu ya gane, Hajara ta tona mana asiri, Hmm! Meye abun yi Mama.?"
Numfashi Mamabisola ta saki cikin tashin hankali ta furta.
"Lallai idan har IYABO yaji wannan maganar to tabbas naji kunya domin kuwa bai san zagon kasan da nake masa ba, wannan yaron ya zamo min ciwon ido a rayuwata ya zamo wajibi na ɗauki mataki a kansa, abinda za'ayi mu fasa zuwa ƙauyen sai gobe kaje da gaggawa kaji mai zaice ni kuma zansa a min maganinsa."
"Okay shikenan Mama ku fita daga motar bara naje wajen Oga Wale muyi shawara dashi domin kuwa bazan yarda naje wajen ni ɗaya ba."
"Shikenan kaje Allah ya baka Nasara."
Tayi Maganar suna fita daga motar da ƙarfi yaja motar yabar gidan wani irin tashi hankalin Mamabisola yayi, sai kaiwa da komowa take Wamimo ne tace.
"Mamabisola Akwai matsala wannan yaron shiya kamata a kawar idan ba haka ba shi zai ga bayan mu."
"Naga alamar haka Wamimo domin kuwa tuya muke muna mantawa da albasa, lallai dole ne Hisham ya mutu."
"Ƙwarai kuwa mutuwa ce ta dace dashi ki barmin komai a hannuna ni zan nemi wanda zai kashe mana shi cikin sauƙi ba tare da an zargi kowa ba."
"Hakan yamin duk yadda zanyi domin naga ƙarshen Hisham na rantse da sarkin da ya busa min numfashi bazan taɓa yadda na faɗi warwas ba sai dai muyi mutuwar kasko.









______________________________________





*SANARWA bazan dinga posting Asabar da Lahadi ba weekend ina da uzuri a wannan ranakun, duk weekend baku da posting.*




_Share and comments my fan's🥰_








*UMMU NASMAH CE✍🏻*





*For more information 08147537180*
[5/20, 8:20 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




_Tnx for comments my fan's i love You so much🥰_




*FREE BOOK ONE 📚*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻






*_Page 19 to 20_*




Mamabisola tayi Maganar cikin hasala da tashin hankali domin kuwa dukiyar Iyabo ba ƙaramin ƙona mata rai yake ba.
"Haka nake so karki damu burunki sai ya cika, kiyi haƙuri mu koma ciki."
Kanta Mamabisola ta ɗaga tana huci suka koma cikin falon nata.



Gudu kawai Tunde yake shararawa a tsakiyar titi tamkar mashayin da yasha giya ya bugu, masu abin hauwa sai kauce masa sukeyi yayin da masu Allah wadarai akansa suna yi, ikon Allah ne kawai ya kawo Tunde shagon Wale parking yayi ya fito a fusace shi kansa Wale ganin Tunde haka sai da ya razana sa.
Zama Tunde yayi yana huci dubansa Wale yayi yace.
"Tunde lafiya kuwa meke faruwa.?"
"Hmmm! Ina kuwa lafiya wale ina cikin tashin hankali da masifa.?"
"Tashin hankali da masifa kuma Tunde, faɗa min me akayi.?"
"Wale Hisham ya gano

Please Login or Register in order to submit comment