Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*BAZAN FASA GODIYA GA JINJINA TA A GAREKU BA MASOYA NAJI DAƊIN YADDA KUKA AMSHI LITTAFIN NAN HANNU BIYU, KO WANI GROUP NA SHIGA COMMENTS NA GANI AKAN JALALA LALLAI KUN ƘARFAFA MIN GWIWWA KUNCE NA DAGE WAJEN TYPING, INSHA ALLAH ZAKU CIGABA DA NISHAƊI CIKIN WANNAN LABARIN BA'A MA FARA KOMAI BAI YANZU WASAN ZAI FARA, JALALA FAN'S HAR NA RASA ABINDA ZANCE MUKU TSABAR FARIN CIKIN SHARHINKU, ALLAH YA BAR ƘAUNA.*





*_FREE BOOK ONE_*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*_Page 13 to 14_





Washegari da safe bayan Hisham sun kammala breakfast ne wajajen 11:30am ya ɗauki wayarsa tare da duban Abba yace.
"Abba zanje Company yau saboda naga yadda abubuwan suke tafiya."
"Okay hakan yayi, amma baka sanar dani halin da ake ciki ba, ina yarinyar da ka ɗauke ɗin, Dpo ya fara zargin kaine ka saceta kuma yana gaf da tunkaro ka domin tuhumar ka sai ka shiryawa tseratar da kanka."
Murmushi Hisham ya saki tare da cewa.
"Nayi mamaki ai da basu zo da wuri ba, nasan dama dole ni zai zarga, karka damu Abba dai-dai nake dashi."
Ummi ce tace.
"Hisham wai Meyasa baka tsoron rayuwa ne kai wannan duniyar fa abar tsoro ce Hisham amma kai sam bata baka tsoro, meye ribarka idan ka ɓoye wannan yarinyar, to kaje ka buɗe ƴar mutane muddun kana gudun ɓacin raina idan ba hakaba sai na saɓa maka yau naga shashancin banza."
"Ummi bazaki fahimta bane amma ni naga ribar da zan ɗauka, kin sani Ummi idan na yanke hukunci *_KO UMARNIN ZUCIYATA BANA BI_* dole sai na aiwatar nake samun sukuni, *_ƊABIAR ƊANKI NE KIN SANI_*."
"A Wannan taƙin kuwa zan taka maka burki da ƙanin ubanka, kaje ka sau yarinyar nan dai na faɗa maka."
Duban su Abba yayi yace.
"Hisham na yarda da kai bana kuma jin zaka bani kunya kaje ka binciki yarinyar da kyau sannan ka sake cikin ƙoshin lafiya ta koma ga iyayenta."
"Ya haka Abban Hisham, kamar fa ɗaure masa gindi kake akan me zaka basa ƙarfin gwiwwa bayan kasan ɗanka ba ji yake ba, mutumin da ya kashe kansa da girman kai da izza harshi ne Mutum, Allah ya yiwu Nameer albarka shi sam bashi da wannan ɗagawar taka, ta inda ya fika morar Rayuwar Duniya kenan, amma ka zauna kana bin Bayan yaro kuma kasan halin zuciyarsa sarai, wannan ba gata bane."
Ummi tayi Maganar tana hararar Hisham murmushi Hisham ya saki ganin ummi na neman rikice masa ya sashi saurin fita, Abba murmushi yayi yace.
"To ai ya fita faɗan sai ya ƙare ko."
Shima Abba yayi Maganar yana tashi a wajen, bakinta Ummi ta taɓe tana kallon Tutu tace.
"Ke kuma meye yake damunki kin hana rayuwarki sukuni tunda Nameer ya bar gidan nan, wai ke bazakiyi tawakkali ba, ko ce miki akayi Nameer ɗin bazai dawo bane, to ki daina wannan damuwar bana so."
"Ummi gidan ne duk babu daɗi babu yaya Nameer."
"Insha Allah Yayanki zai dawo mu cigaba da addu'a, sai ki tattare daining ɗin."
"To Ummi Allah yasa."
Da ameeen Ummi ta Amsa tare da tashi ta haura sama.



Hisham yana cikin tuƙi yaji shigowar kuɗin da Aunty Halima ta masa alƙawari, wayar ya ɗaga ya kira Sadiq Ringing ɗaya ya ɗauka, daga nan Hisham yace.
"Mu haɗu Aminci News by 1:00."
Ya katse kiran Companyn ya shige ya je ya duba abubuwan da ke tafiya, Salisu ya aika BANK ya ciro masa wannan kuɗaɗen ya dawo, ya juma sosai cikin Companyn shine bai baro Companyn ba har sai da yayi Sallah kafin ya kira Sadiq yace su haɗu yanzu gashi nan zuwa, ya zari key ɗinsa ya fice daga Companyn.
A bakin ofishin Jaridar ya samu Sadiq yana tsaye da alamu saukesa akayi parking Hisham yayi tare da fitowa hannunsa riƙe da baƙar jaka ya nufo Sadiq yana dariya hannu ya basa sukayi musabaha.
"Kaddai ka juma kana jirana."
"Ina ban juma ba yanzu Ib ya sauƙeni ya akayi me zamuyi a ciki."?
"Muje kawai Sadiq kai dai ka min video record akan duk wata tattaunawar da zamuyi a wajen ta, muje amma karka fara ɗaukar har sai na taka maka ƙafa."
Hisham yayi Maganar tare da yin gaba Sadiq yabi bayansa.


"Jidda dama na sani ba lallai mu samu rancen kuɗin nan ba, Hmm! Bansan ya zanyi ba, Abbana yana cikin matsala ina son na ceci rayuwarsa babu wanda zai masa idan bani ba."
Cikin kulawa Jidda da alamun damuwa Jidda tace.
"Hmmm! Basmah akwai Allah kuma zai taimaka karki damu bari mu koma gida insha Allah bazamu rasa abin yi ba."
"Any................. ..
"Assalamu alaikum."
Sallamar Hisham ta katse Maganar da Basmah zatayi gabaki ɗaya idanu suka ɗaga suka kalli bakin ƙofar, ganin Hisham yasa Jidda sakin murmushi domin kuwa tasan yauma haukar ce ta kawosa.
"Ameeen wa'alaiku mussalam."
Shigowa sukayi Hisham ya harɗe hannunsa tare da tsayawa a gabanta.
"Bana hana maƙiyi abu biyu wajen zama da kuma ruwan sha."
Murmushi Hisham ya yi yace.
"Kina nufin mu zauna kenan."?
"Kwarai kuwa."
Zama sukayi Sadiq da Basmah dai kallon ikon Allah suke, Hisham gyaran murya yayi tare da cewa.
"Hisham ya faɗi domin kuwa ya gagara cire ɗan uwansa daga cell, shiyasa na dawo gareki durƙusawa wada ba gajiyawa bace neman taimako ne."
"Hmmm! Ashe dama matsiyaciya tana da rana duk da nasan ungulu bata jimar banza meke tafe da kai shin yauma kazo kamin barazanar ce akan wancan dabban ɗan uwan naka, kayi ikrari har yanzu ka kasa cikawa."
"Hmmm! Ko da zancena na farko ya nuna ba tashin hankali bane ya kawo ni."
Yayi Maganar yana taka kafar Sadiq.
"Meya kawo ka to.?"
"Neman alfarma ina son ki cire hannunki a wannan Case ɗin kije Police station ki nuna ke baki san komai ba, infact ma sharri yarinyar take yiwa Nameer, ba kyauta zaki min ba biyanki zanyi manyan kuɗaɗen da zasu saya muku gida abar na haya kiyi tunani ba gaggawa nake ba."
Kallon Hisham Jidda tayi wato ma ya raina mata wayo ya rasa mafita shine zai bata cin hanci, saboda tsinannen ɗan uwansa ya kuɓuta.
Za tayi Magana Basmah ta taka ta tare da sunkuyawa dai-dai kunnenta ta mata raɗa.
"Dama ce mai kyau da zamuyi amfani dashi wajen samun kuɗin da muke nema, ki amshi tayinsa da zummar zakiyi aikin mu amshe kuɗin banza, amma a zahiri baza kiyi aikin ba, ki duba halin da Abbana yake ciki ki cecesa Jidda kimin wannan taimakon, ba wai zakiyi masa aikin bane kuɗin kawai zaki amsa kuma ki ƙi yin aikin Please Jidda."
Shuru Jidda tayi zuciyarta na kai kawo.
_Anya kuwa hakan zata yiwu, to amma Basmah tana bukatar taimako, zanso ace na taimaka mata amma ba ta wannan hanyar ba, domin kuwa amsar cin hanci babban laifi ne duk da ba aikin zan masa ba, ko da yake koda na amsa babu wani laifi domin kuwa bazan taɓa take gaskiya ba, gaskiyar Basmah zan amsa na nuna masa bashi da yawo._
Murmushi Jidda ta saki kafin tace.
"Amma dai anyi faɗuwar baƙar tasa ko nace faɗuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance, ka bada maza ina kurin ina barazanar shin ka fasa tozarta nin ne, hmm an dai ji kunya, ba damuwa nawa ne farashin."
Murmushi Hisham ya saki yace.
"5million babu tayi idan sun miki shikenan idan basu miki ba zan koma da kuɗina."
Murmushi Jidda itama ta saki tace.
"Ciniki ya faɗa zanje na ƙaryata Hajara, Ɗan uwanka zai fito nan da dare."
jakar ya ijiye mata tare zazzage duka kuɗaɗen a ƙasa yace.
"Ga su nan, Sadiq muje."
Hisham yayi Maganar yana miƙewa Sadiq dake ɗaukar dukkan abinda ke faruwa ya tashi suka fice tare, Jidda duban Basmah tayi tace.
"Anyi banyi kuskure ba kuwa Basmah zuciyata bata kwanta da Hisham ba, anya kuwa babu wani abu a ƙasan zuciyar sa.?"
Numfashi Basmah ta saki tace.
"Babu komai Jidda karki wani damu kawai ɗan uwansa yake son ya fitar a cikin matsala, ya gagara ne kawai yaga bashi da wata mafita sai wannan, kuma ni a ganina wannan dama ce mai kyau tunda dama Umma tace ki cire hannunki a cikin wannan Case ɗin kinga kin samu riba biyu kenan, ga kuɗi ga kuma bin umarnin Umma kije kawai ki cire hannunki kalas magana ta ƙare."
A fusace Jidda ta kalli Basmah tare da cewa.
"Whatt! Kinsan abinda kike faɗi kuwa na cire hannuna fa kikace, amma sanda kike so na amshi kuɗin me kika cemin ko kin manta na tuna miki, ba cewa kikayi na amshi kuɗin naƙi masa aikin ba, shine yanzu zakiyi ƙoƙarin turani ga hallaka, to wallahi tashi zan naje har gidan su na mai da masa da wanannan kayan tsiyar tasa, domin kuwa bazan taɓa ganin gaskiya na take ta ba, bazai yiwu ba, kai amma nima mahaukaciya ce dana biye miki na amshi kuɗin nan, yanzu dana amshi wannan kuɗin naje gida na cewa Umma ina na samesu, kin san dai sai ta bincike ni ƙarshe ma raina yayi mungun ɓaci kin kaini kin baro Basmah."
Tayi Maganar cikin ɓacin rai sai yanzu ma taji haushin kanta da ta amshi wannan kuɗin shikenan zai rainata ya dinga mata kallon ƙasƙantacciya mai kwaɗayin abun duniya.
"Jidda baki fahimce ni bane Abbana yana cikin matsala kin sani sannan zaki cecemu ne idan kin amshi kuɗin kina gani fa cikin office ɗin nan abamu aron kuɗin sunsan za'a cire wannan kuɗin cikin salary namu amma sukace babu kuɗi a ƙasa kuma akwai kuɗin bawai babu ba, to ina zamuje a bamu, muna ganin dama tazo kuma muna bukata sai mu barsa, Jidda muje mu yiwa Umma bayani a nutse zata fahimce mu, sannan.......
Hannu Jidda ta ɗagawa Basmah tace.
"Sannan na daure na cire hannuna a cikin Case ɗin ko? To impossible."
Jidda tayi maganar tana tashi ta fice daga office ɗin nata, numfashi Basmah ta saki tare da dafe kanta tasan halin taurin kan Jidda sarai dama ba lallai ta amince ta cire hannunta a case ɗin ba.




"Ban taɓa ganin Hisham ya nemi alfarma a wajen wata ba sai yau ban taɓa ganin an faɗawa Hisham baƙaƙen magana yayi shuru ba sai yau, tabbas kana ƙaunar Nameer fiye da kowa a wannan duniyar, sai dai nayi mamakin da ka shanye maganganun wannan yarinyar."
Murmushi Hisham ya saki tare da cewa
"Hmmm! Hisham baya jewar banza kamar yadda ta faɗa, ba Nameer yasa naje mata da wannan buƙatar ba domin kuwa ina da hujjar da zai sanya Nameer ya fito yanzu haka Police station zamu wuce tare da Nameer zamu fito."
"Ban fahimta ba Hisham me yasa to kaje wajenta shin meye manufar, sannan shi kuma wannan video record ɗin da kasa nayi fa."?
"Ka sanya idanu kayi kallo Sadiq zaka fahimci manufata, wannan shine wasan da nace maka zamu buga kuɗina zai dawo Naira biyar bazaiyi ciwon kai ba, ko da kuwa ta kashe wani abu daga ciki na rantse da Allah dai ta biya."
"To Allah ya kyauta."
Sadiq yayi Maganar a takaice babu wanda ya sake magana har suka isa Police station ɗin.
Shigar su cikin station ɗin, Hisham darect cell ya nufa Nameer na zaune ya haɗa kansa da bango yaji muryar Hisham.
"Hmmm! Wata ƙila ɗan uwana yana cikin damuwa nasan dole izuwa yanzu ka fara gajiya da zaman wajen nan."
Kansa Nameer ya ɗago ya dubi Hisham kafin yace.
"Sadiq Barka da zuwa yaushe ka dawo ƙasar.?"
Murmushi Hisham ya saki domin kuwa ya hango fushi Nameer yake dashi ya kuma san fushin bazai wuce akan rashin dawowarsa station ɗin ba, Sadiq ne ya amsa da.
"Jiya shigowata sai kuma nake jin labari marar daɗi."
Kafin Nameer yayi Magana Hisham yace.
"Kayi haƙuri nasan fushi kake dani akan rashin dawowata, nayi hakan ne saboda bana son ganinka a cikin wannan halin nayi alkawarin bazan dawo station ɗin nan ba har sai da hujjar da zata kuɓutar da kai."
"Bana fushi da kai Hisham sai dai ina fushi da zuciyar ka, saboda ta cika rashin haƙuri zafinta yayi yawa, nasan Kaine ka sace wannan yarinyar meyasa zakayi haka Hisham kuskure ne babba ka tafka bana son ka shigo haɗari saboda ni, da ka shiga cikin tashin hankali Gara ace na rasa rayuwata."
"Ina zuwa Nameer Sadiq muje wajen Dpo tukunna."
Yayi Maganar yana juyawa domin kuwa bashi da amsar da zai bawa Nameer, ko inda su Sargent Bala yake Hisham bai kalla ba ya wuce office ɗin Dpo, babu wanda ya kulasa kasancewar sunsan halinsa nocking yayi Dpo ya basu damar shigowa sosai Dpo yayi mamakin ganin Hisham mutumin da yake da niyyar zuwa garesa sai gashi ya kawo kansa, zama Hisham yayi tare da sakin murmushi yace.
"Nasan dama dole akwai ranar da ɗan tsakon Police zaiji kunya sai ga kuma ranar tazo, har abada ahalin IYABO masu Nasara ne ko da alfarma ko babu."
Murmushi Dpo yayi yace.
"Na fahimta, wani tsuntsun tarkon ka kuma ya kama Hisham Abdulzahir.?"
"Ba tsuntsu ba dai sai dai tsuntsuwa domin kuwa na farauto tsuntsuwar kuma har na samu kwamishon farauta, ita tsuntsuwar da kuke nema tana gareni."
"Hajara tana wajenka kenan, ehh tabbas ƴar Jaridar nan tayi gaskiya da tace kaine zaka sace yarinyar, meye ribarka da hakan.?"
"Hmmm! Ita Zabiyar har ta hasashoni kenan, we'll ribar na kawo maka yanzu idan ka shirya amsa sai na gabatar maka."
Numfashi Dpo ya saki tare da cewa.
"Hmmm duk tsuntsun da yaja ruwa ka sani dole sai wannan ruwan ya dakesa, gabatar."
"Shikenan zan kuwa jawo babban ruwan da zai dake ku amma ni tuni na zillewa wannan ruwan."
Yayi Maganar yana ɗauko wayarsa a aljihu ya danna recording ɗin da yayi na Hajara ya ijiye, gaba daya shuru sukayi suna sauraron recording ɗin, Sadiq sosai yasha mamaki musamman da yaji wai Tunde ne yasa ayiwa Nameer wannan ƙazafin, Dpo kuwa wani irin gumi ne ya keto masa, domin kuwa duk binciken da sukayi nunawa yake Nameer ne ya aikata bayan recording ɗin ya ƙare ne Hisham ya kashe tare da mayar da wayarsa aljihu ya saki murmushi.
"Ya kamata ka cire wannan kakin naka domin kuwa sam wannan aikin bai dace da kai ba tunda har ka gagara gano gaskiya, Dpo na faɗa maka shiga komar Hisham ba abu bane mai sauƙi, amma zan kyaleka za kuma mu cigaba da bawa karnuka ƙashi, sai dai fa dole ne a wannan karon kamin wani aiki sannan a rufe babin Case ɗin Nameer gaba ɗaya kamar ba'a taɓa yiba bana bukatar ko Abba yasan da labarin Tunde ne ya haɗa wannan tarkon, sai kuma aikin da nace zaka min, idan ka amince zan ɗaukaka darajar ka ta hanyar samun ƙarin girma."
Shuru Dpo yayi tare da ɗago idanunsa ya kalli Hisham.





____________________________________




Share and comment my fan's.





*UMMU NASMAH CE✍🏻*







*For more information 08147537180*
[5/18, 7:34 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*FREE BOOK ONE📘*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*Page 17 to 18*




"Hisham ka sani akan gaskiya ta nake aiki, kamar yadda ka buƙata za'a rufe Case ɗin Nameer ba kuma za'a tuhumi Tunde ba kamar yadda ka bukata, sai dai ban san wani aiki zaka bani ba, idan har babu cutarwa a ciki ƙofata a buɗe take."
Kallon Dpo Hisham yayi kafin ya saki numfashi yace.
"Yarinyar nan wannan ƴar tashar da ta sanya ku kama Nameer nake son kuje ku kamota ina zaune ina jira ku jefata cell yayin da kuka fitar da Nameer wannan shine aikin da zaka min Dpo."
"Ban fahimta ba Hisham ta yaya zamu kamata bayan bamu da hujjar yin hakan ka sani doka ce baza'a kama mutum ba har sai da hujjar da take nuna yayi laifin da za'a kamasa ita kuma wannan yarinyar bata da wani laifi."
"Ita kuwa take da laifi ko sanya bakinta wajen yiwa Nameer ƙazafi wannan ma babban laifi ne kuma idan mun so zamu shigar da ƙara akan hakan kuma dole ku amsa, bar wannan ma tunda nace a rufe wannan babin Case ɗin, ni ina da cikakkiyar hujjar da za'a kamata domin kuwa naje mata da cin hanci kuma ta amsa har Naira miliyan biyar a hanuna da zummar zatazo ta ƙaryata kanta, wannan babban laifi ne a dokan ce sannan hukuncin wanda yayi wannan kora ne daga wajen aikinsa, ta muku furucin cewa zata iya sawa ku rasa aikin ku, to wannan kalmar zata dawo kanta domin kuwa ita zata rasa aikinta."
Yayi Maganar yana amsar wayar Sadiq ya kunna recording ɗin ya miƙawa Dpo amsa Dpo yayi kafin Hisham ya cigaba da cewa.
"Wannan shine shaidar gani da ido naje na gwada muku gaskiyar ta ne ta yadda zaku fahimci wacece ita ba tasan ina da hujjar da zan saka a saki Nameer ba, nayi hakanne saboda ku san wacece ita dan haka hukunci yana gareku."
Numfashi Dpo ya saki yana duban video ɗin murmushi ya saki tare da cewa.
"Mutum mungun ice, Hisham ko da baka nemi na kama Jidda ba, dole ne a kamata bara a kira Sargent Dogo suje suyi arresting ɗin ta, ina kuka baro ta.?"
"Tana can ofishin su, sannan a taho min da kuɗina."
Waya Dpo ya ɗaga ya kira Sargent Dogo babu jumawa kuwa ya shigo umarni ya basa da ya haɗa Police Uku suje suyi arresting ɗin Jidda, a office ɗin su sannan su taho da kuɗin da aka bata."
Sarawa Dpo Sargent Dogo yayi tare da furta.
"Yes Sir."
Yayi Maganar yana ficewa, takaddar belin NAMEER Dpo ya bawa Hisham.





***********



Jidda tunda ta fita daga office ɗin take tsaye a waje duk sai taji babu daɗi ta gwammace da bata amshi wannan kuɗin ba, zuciyar ta sai ayyana mata take taje ta mayar masa da kuɗinsa, juyawa tayi zata shiga office ɗin nata da niyyar ɗaukar kuɗin taje ta mayar wa Hisham taji kuwwar motar Police a bakin ofishin Jaridar tasu, juyawa Jidda tayi tare da tsayawa tana nazarin me kuma ya kawo Police wannan office ɗin.
Sargent Dogo ne suka shigo su Uku basu kula Jidda ba duk da Sargent Dogo ya ganta, darect ofishin shugaban nasu suka shige yana zaune suka shigo, miƙewa Manager yayi cike da mamaki yace.
"Yallabai lafiya kuwa."?
Sargent Dogo ne yace.
"Lafiya bata cika kawo mu ba, amma da zaka bamu dama zamu sanar da kai abinda ya kawo mu."
"Ina sauraronka meke tafe daku."
Sargent Dogo wayar Sadiq ya miƙawa Manager bayan ya kunna video record ɗin, nutsuwa Manager yayi yana kallon videon wani irin ɓaci ransa yayi Jidda da suke yiwa kallon mai ƙwazo da gaskiya yau itace take neman ɓatawa ofishin su suna ta rasa inda zatayi almundahana sai a ofishin su, numfashi ya saki cikin ɓacin rai yace.
"Kuje ku kamata zanzo office ɗin naku yanzu."
Manager yayi Maganar cikin tashin hankali domin kuwa yasan wannan video ɗin ya fita jaridar su ta gama yawo, fita sukayi daga office ɗin Manager har yanzu Jidda tana tsaye har Basmah ma ta fito Sargent Dogo a gabanta ya tsaya tare da cewa.
"Munzo mu tafi da ke ne.?"
Zaro idanunta Jidda tayi zuciyarta ta tsinke tace.
"Whatt! Ku tafi kuma laifin me na aikata.?"
"Idan munje zakiji umarni ne aka bamu mu tafi dake office."
Kanta Jidda ta ɗaga ta kalli Basmah kafin tace.
"Basmah karki sanar da Umma abinda yake faruwa ko da ban dawo ba."
Tayi Maganar tana shigewa gabansa Yar sanda mace ce ta rufa mata baya, Basmah shuru tayi cikin tashin hankali wani irin laifi Jidda zatayi wanda har za'a kamata bata shiga harkar kowa ba'a taɓa rabata faɗa da wani ba.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!."
Shine abinda Basmah ta furta cikin tashin hankali marar misaltuwa.




***********


Ko da suka isa Police station ɗin Sargent Dogo da kansa yaje ya sanarwa Dpo sun taho da ita, bayan sun gama tattaunawa ne da Hisham tare da alƙawarin da Hisham ya yiwa Dpo na zai sakar masa da Hajara muddun ya rufe masa Jidda na tsawon kwana Uku babu beli, yayi Maganar yana sakin murmushi tare da miƙewa Dpo shima miƙewa yayi suka fito tare, Jidda tana tsaye cikin tashin hankali taga Hisham da Dpo idanunta Jidda ta zaro tare da furta.
"Kaine!?"
Dariya Hisham ya yi tunda take ganinsa bata taɓa ganin yayi dariya ba sai dai murmushi sai gashi yanzu yana dariya.
"Yeah ni ne kinyi mamaki ne ko kin manta Ungulu bata jimar banza kina zaton zaki taka Hisham ne ki taka banza, ba'a taɓa ja da Hisham aci bulus ki shiryawa kare kanki domin kuwa nayi alƙawarin tozarta rayuwarki."
Nameer a zabure ya miƙe jin furucin Hisham yana mamakin me Jidda tayi aka kawota nan.
Bakinta Jidda ta cije tare da cewa.
"Kayi nasarar jefani cikin tarkonka Hisham amma ka sani wannan shine mafi girman kuskure da kayi a rayuwarka."
Shima murmushi yayi yayin da Dpo da kansa ya buɗe Nameer kusa da ita Hisham ya tsaya daf har yanzu bakinsa na ɗauke da murmushi.
"Na faɗa miki bazan waiwayo gareki ba har sai NAMEER ya fita daga komar hukuma, idan Banda ke jahilace

Please Login or Register in order to submit comment