Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aunty Halima."
Hisham yayi Maganar yana ture plat ɗin abincin tare da miƙewa, ummi ce ta dubesa tace.
"Hisham meka aikatawa ƴar mutane."?
Aunty Halima ne ta cewa Ummi.
"Muddun Nameer zai fito to kawai ki sanya idanunki, muje Hisham."
Itama aunty Halima tayi Maganar tana tashi suka bar wajen ita da Hisham Ummi duban Abba tayi tace.
"Abban Hisham, kana jin abinda yaron nan yake faɗi kayi shuru karfa ya ƙara jawo mana wata fitinar bamu gama da wannan ba, ga kuma Halima tabi bayansa."
"Hmmm! To me zance Ramata, nasan dai ko mai Hisham zaiyi bazai cutar da yarinyar ba, sannan na yarda da maganar sa amfani akayi da Yarinyar ki ci abincin ki kawai zanyi magana dashi a nutse."
"Shikenan Allah ya kare."
Da ameeen kawai Abba ya amsa.



Bayan sun fito compound ɗin gidan ne Hisham ya dubi Aunty Halima tare da cewa.
"Aunty Halima, naje na sace yarinyar da tace Nameer ne yayi ƙoƙarin mata fyaɗe, yanzu haka gareta nake son muje tare da ke."
"Hisham da gaske ka ɗauko yarinyar, amma garin yaya ka ɗauketa ba'a ganeka ba."?
"Aunty Halima wannan abu ne mai sauƙi a gareni zan iya ɗaukar ko wacce irin kasada akan Nameer bazan yafewa kaina idan na kasa fitar dashi a wannan halin daya shiga kawai muje."
Yayi Maganar suna nufar parking space bayansa Aunty Halima tabi suka shiga mota, tunda suka shiga babu wanda ya kuma magana har suka shiga gidan gonar Abba parking sukayi suka fito tare fa shigewa can ciki wani ɗaki Hisham yasa key ya buɗe, Hajara ce zaune tayi shuru jin an buɗe ƙofar ya sata firgita ta ɗago kanta ido huɗu sukayi da Hisham, murmushi ya saki tare da shigowa ya zauna gefenta, Aunty Halima ma shigowa tayi tana kallon Hajara kafin tace.
"Yanzu wannan yarinyar ne ta yiwa Nameer sharri.?"
"Itace Aunty Halima."
Hisham yayi Maganar yana kallon Hajara hannu yasa ya ɗauketa da wawan mari wanda sai da taga taurari Uku, da yatsa ya nunata yace.
"Waye ya biyaki kuɗi domin ki tozarta ahalina ki ɓatawa gidan mu suna waye shi."?
Fuskarta Hajara ta dafe da shatin yatsun Hisham suka bayyana a kai idanunta kuma sai hawaye yake kanta ta girgiza tace.
"Babu wanda ya sani ba sharrin na masa ba tabbas yaso min fyaɗe."
Murmushin gefen baki Hisham ya saki Aunty Halima ne tace.
"Okay bazaki faɗi ba kenan okay kin zaɓi ki wahala akan ki tonawa wanda ya saki asiri ko, Hisham ka ɗauko belt ka bigeta har sai jini ya fita a jikinta karka ƙyaleta har sai ta faɗa."
"No Aunty Halima ba dukanta zanyi ba, akwai sistern ta zansa a mata fyaɗen idan yaso sai ashiga kotun da dalili wallahi aunty Halima da gaske nake zansa ayiwa ƴar Uwar ki Zainab fyaɗe muddun baki faɗa min gaskiya yanzu ba kuma na sanya a tozarta mahaifiyarki."
Wani irin firgita Hajara tayi jikinta na rawa bakinta na karkarwa tace.
"A'a dan Allah karka min haka karku taɓa Zainab bata san komai ba dan Allah ka rabu da ita."
"Hmmm! Idan ita bata san komai ba to ke ai kin sani kece kaɗai zaki iya ceton ta ki faɗa min waye ya sanyaki.?"
"Idan na faɗa maka zaka ƙyale Zainab idan har zaka rabu da ita zan faɗa maka gaskiya."?
Numfashi Aunty Halima ta saki tare da cewa.
"Gaskiyar muke bukatar ji muddun mukaji gaskiyar zamu rabu daku."
"Nameer bai sanni ba bai taɓa ganina a cikin rayuwarsa ba, tabbas kuɗi aka biyani domin na masa sharrin da xa'a ɗauresa na tsawon shekaru."
Kansa Hisham ya girgiza tare da cewa.
"Waye ne ya sanyaki.?"
"Tunde shine ya biyani dubi ɗari biyu domin nayi wannan aikin dan Allah ka rabu da ƴar uwata na tuba bazan kuma ba kayi haƙuri."
Murmushi Hisham ya saki aunty Halima kuwa bakinta ta riƙe cike da mamaki.
"Tunde! Hmmm! Ni nasan za'a rina wai an sace zanin mahaukaciya, tom riƙe wayar nan na mai da layi na no number ki kira Tunde kar kuma ki nuna masa cewa kina cikin damuwa kuyi Magana dashi."
Hisham yayi Maganar yana dannawa Tunde kira tare da sanya handsfree, ringing ɗaya kuwa ya ɗaga saurin sanya recording.
"Hello dawa nake magana."
"Ni ce Hajara Tunde."
"Hajara! Ina kikaje akace kin ɓata har muna zargin ko Hisham ne ya saceki domin mungun wayo garesa zai iya tunanin mune muka ɗana musu wannan tarkon kina dai lafiya ko.?"
"Ina lafiya Tunde babu wanda ya sace ni kawai guduwa nayi daga asibitin, ƙarin kuɗi nake bukata wanda ka bani sunyi kaɗan domin kuwa ba ƙaramin kasada na ɗauka ba, idan ba haka ba zan tona asiri."
"Haba Hajara yanzu 200k ne tayi kaɗan, kinga yanzu kina ina zan zo na ƙara miki 50k hakan yayi.?"
"Yayi zan sake kiranka anjuma."
katse kiran Hisham yayi tare da sakin murmushi ya dubi Aunty Halima yace muje.
"Dan Allah karku tafi ku barni anan tunda na faɗa muku gaskiya ku sakeni."
Juyowa HISHAM yayi ya kalleta tare da cewa.
"Kamar yadda na miki alkawari bazan cutar da ƴar Uwarki ba tunda kin faɗa min gaskiya sai dai fa ki sani ke bazan sakeki ba sai kin gane kuskuren ki zaki gane wanda aka biya ki taɓa."
Yayi Maganar yana saka kai ya fice bayansa Aunty Halima tabi tana dakawa Hajara harara, ko da suka shiga mota Aunty Halima cewa tayi.
"Meye ribar Tunde idan ya tozarta Nameer.?"
"Babu wata riba da zasu samu kakarsa ce maybe ta sakasu, shi Abba har yanzu ya kasa fahimtar su waye Mamabisola, kawai ƙiyayyace da hassada take damunsu a rai."
"To Allah ya kyauta amma dai ya kamata yaji wannan voice ɗin ko.?"
"A'a Aunty Halima bazai ji ba bana son abinda zai tayar masa da hankali bare ma yadda Abba yake ɗauka duk duniya bashi da gatan daya wuce su, sanin halin da ake ciki kan iya tayar masa da hawan jininsa zan kashe Case ɗin ba tare da su Abba sun san komai ba."
"Hmmm! Hisham naji daɗi da kayi hakan Allah ya shirya su su kuma, amma daga nan Police station zamuje ko."?
"A'a gidan ki zan sauƙeki daga nan Police station sai gobe ki turo kuɗin yau gobe nake son zanyi amfani dashi."
"Okay baka da matsala."
Har bakin get ɗin gidan ta ya sauƙe ta kafin ya yi shigewarsa yana murmushi domin kuwa shi ya juma da fahimtar Mamabisola ba ƙaunar su take ba shuka take a idanun makwarwa wanda har yanzu ita bata fahimci Hisham yasan abubuwan da take ƙulla musu ba.




_____________________________________



Share and comment my fan's




*UMMU NASMAH CE✍🏻*




*For more information 08147537180*
[5/16, 8:31 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*_FREE BOOK ONE_*




*PAGE 13 to 14*




Isar ta cikin gidan Ta samu Umma sunkuye tana tsintar shinkafa, sallama tayi Umma ta amsa tana ɗago kanta.
"Kin dawo."?
"Eh Umma na dawo bamma samu Basmah ba sai na biya gidan su Zainab."
"Tana ɗakin ki ma ai tana jiranki, ta juma a ciki da alamu dai kamar tana cikin damuwa na tambaye ta ko akwai abinda yake damunta sai tace babu wai abbanta ne yake asibiti jikinsa ya tashi sai kije ki sameta ki rarrasheta."
"Subahanallah! Jikin Abban ne kuma ya ƙara tashi bara naje na sameta."
Jidda tayi maganar tana tashi da sauri ta shige ɗakin nata, tana zaune tayi shuru hawaye na biyo idanunta ko kaɗan bata kula da shigowar Jidda, ta yi nisa sosai a cikin tunani, sai ji tayi ta dafa kafaɗarta.
"Basmah abun har ya kai ga kuka, jikin Abban babu daɗi ne.?"
Numfashi Basmah ta saki tana goge hawayen fuskarta tace.
"Jidda jikin Abbana ba daɗi, dole sai an masa cs ana neman dubu arba'in, mu kuma bamu da ita bamu da wanda zai bamu, ga kuɗin hayar gidan namu ma ya kare suna bukatar Kudi masu gidan, salary na kuma na wannan watan kuɗin makarantar su hafiz aka biya, gacar Mama ta shiga cikin damuwa."
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati! Lallai dole hankalinki ya tashi Basmah, yanzu ina zamu samu wannan kuɗin ko Abba a fara masa cs ɗin 14k ne kawai a cikin account ɗina, bansan kuma ina zamu samu 26k ba, mutanene yanzu basa taimako kowa kansa da iyalansa ya sani, bashi ma ba kowa bane zai baka wani ma yana da shi sai ya gama jin sirrinka yace maka babu, amma yaushe ne za'a masa cs ɗin."
"Sunce jibi zasu masa, bansan inda zan samu kuɗin nan zuwa jibi ba, shiyasa kikaga hankalina ya tashi Abba bashi yake da shi ba, kaf ƴan uwansa babu wanda zai taimaka masa wallahi, suna da kuɗi sai dai basa taimakon sa, abinda yake sani kuka kenan."
"Karki damu Basmah akwai Allah muyi addu'a insha Allah, Allah zai kawo hanya, gobe ai muna da aiki idan yaso sai muje mu tambayi accounter bashi zuwa ayi salary idan yaso sai su bamu aron 26k ɗin sai mu haɗa da 14k ɗin wajena in akayi salary sai su cire 10k cikin kuɗina kema su ciri 16k karki damu Allah ya bawa Abba lafiya."
"Ameeen, amma Jidda bazan amshi kuɗin ki ba, kema kina fama da ɗawainiyar gidan ku, dan haka ki bari muje mu nemi bashin 40k ɗin insha Allah zan biya amma bazan sakaki cikin wahala ba."
Numfashi Jidda ta saki tare da girgiza kanta ta ɓata ranta.
"Saboda ni Abba bai haifeni ba ko shiyasa bazan masa ɗawainiya ba, idan kika min haka baki min adalci ba, tamkar mahaifina haka nake masa kallo yadda baki isa hanani yiwa Ummana abu ba, haka baki isa ki hanani na yiwa abbanki abu ba, dan haka karki sake cemin komai ki share hawayen ki kukan ya isa haka insha Allah Abba zai samu lafiy."
"Hmmm! Shikenan Jidda Allah yabar zumunci, amma asibiti kikaje ko nasan karya kika yiwa umma ba gidan mu kikaje ba, wato har yanzu baki fita a cikin wannan sha'anin ba ko Jidda.?"
"Basmah na faɗa miki bazan fita ba dole sai na taya Hajara kwato ƴancinta yanzu haka maganar da nake da ke an sace Hajara."
"An sace Hajara, kamar yaya sai kace wata kaza."
"Da gaske ansace ta kuma ni gaskiya wannan Hisham ɗin shi nake zargi babu wanda zai sace Hajara sai shi Saboda ya kuɓutar da ɗan uwansa."
"Amma abun da mamaki Jidda Hisham bazai sace Hajara ba domin yasan dole shi za'a zarga, Allah ya bayyana ta, amma dai Jidda ina ƙara faɗa miki ki fita cikin wannan Case ɗin bana son ki jawa kanki matsala."
"Hmmm! Naji mubar maganar, ki tashi muje mu taya Umma aiki sai mu koma asibitin."
"Okay."
Basmah tayi Maganar tana tashi suka fita.




************


"Wai Tutu bazaki daina wannan damuwar ba, zafa ki sawa kanki ciwo."
"Hmmm! Samira dole fa na shiga cikin damuwa, gani nake kamar yaya Nameer baya sona, yaƙi bayyana Soyayyar mu, harta ga yaya Hisham da suke ƙaunar juna yaƙi bayyana masa akwai wani abu tsakanin mu, hankalina yana tashi idan na tuna da hakan zuciyata sai ta dinga tsinkewa ina matukar son yaya Nameer Soyayyar da ban san iyakar ta ba."
Numfashi Samira ta saki tare da dafa kafaɗar Tutu tace.
"Tutu ni kaina kullum ina wannan tunanin Soyayyar da kike yiwa yaya Nameer kamar shi baya miki, da Yaya Nameer yana sonki Tutu to wallahi da zai bayyanawa kowa Soyayyar ki, bazai ɓoye ba anya ma kuwa ba da gaske Nameer shi ya yiwa wannan yarinyar fyaɗe ba Tutu."?
"A'a Samira na rantse da Allah Yaya Nameer bazai aikatawa wata mace fyaɗe ba, domin kuwa Mutum ne mai ƙyanƙyami bare kuma wannan Yar talakawa, da zaiyi lalata da wani to da dani zai fara saboda yadda na sake masa jiki nasan yaya Nameer mutum ne shi mai tsananin sha'awa, amma hakan bazai sa ya zalunci ƴar wata ba, na fi kowa sanin waye shi."
Bakinta Samira ta taɓe tana yiwa Tutu kallon mahaukaciya kafin tace.
"Na sani Soyayyar da kike yiwa yaya Nameer bazai taɓa barinki ki faɗi aibunsa ba, wannan Soyayyar ita take cutarki, da ita yake amfani yake cutarki ya kasa bayyanawa duniya yana sonki, soyayyar gaskiya ba'a ɓoye ta, ko da an ɓoyeta ita da kanta take bayyana kanta, ya mayar dake mahaukaciya sai wasa yake da tunaninki, Allah ya ganar da ke Tutu yasa ya aureki."
"Ba karesa nake ba Samira nasan halin yaya Nameer nasan abinda zai aikata da wanda bazai aikata ba, wallahi bazai yiwa wata fyaɗe ba, ki yarda Samira ba halinsa bane, Hmm! Amma ke ba lallai ki yarda ba, Samira kece kaɗai wacce kika san wannan sirrin nawa muddun asirina ya tonu to kece zan zarga, dan Allah ki ɓoye min sirrina, ki bari har shi ya bayyana Soyayyata."
"Bazan taɓa tona miki asiri ba Tutu domin kuwa na san menene amana, amma ina baki shawari muddun yaya Nameer ya dawo gida ki tabbatar Soyayyar ku ta bayyana idan ba haka ba zaki tura mota ta tashi ta barki da ƙura."
Samira tayi Maganar tana miƙewa tare da ɗaukar mayafinta ta kuma cewa.
"Ni kinga tafiyata Allah ya fiddo miki dashi."
Kanta Tutu ta girgiza tare da tashi ta raka Samira har bakin get kafin ta dawo a falo ta tarar da wayar Hisham tana ringin hannu tasa ta ɗauka taga Sadiq ya bayyana a screen ɗin wayar bata ɗauki kiran ba ta haura bedroom ɗin su nocking tayi Hisham dake zaune yayi shuru yana saƙa da warwara akan Tunde, yace.
"Yes come."
Turo door ɗin tayi ta shigo cikin sanyin jiki gefen Hisham ta zauna sai kuma idanunta ya ciko da hawaye, sanin hawayen fuskarta yasa HISHAM sanya hannu ya share mata hawayen cike da ƙaunar ƴar uwarsa domin kuwa a rayuwarsa ya tsani abinda zai ɗaga mata hankali su biyu kawai Ummi ta haifa bashi da wani yaya ko ƙani itace ƴar uwarsa guda ɗaya tilo.
"Tutu wai meyasa bakya jin rarrashi ne, ba nace miki Yayanki Nameer zai dawo gobe ba, ko baki yadda dani bane, kin damu akan Nameer sosai Tutu dole kuma ki damu domin kuwa Nameer shine hasken gidan mu, ɗan uwa ne na gari bazan bari wani abu ya cucesa ba zan karesa da jikina da kuma rayuwata."
Kanta Tutu ta kaɗa tare da miƙa masa wayarsa.
"Ya Sadiq ne yake kiranka."
Amsa yayi tare da cewa.
"Okay kije ki wanke fuskarki."
"To Yaya."
Tayi Maganar tana tashi tabar wajen kiran Sadiq Hisham yayi Ringing ɗaya ya ɗaga.
"Malam kazo airport ka ɗaukeni."
"Whatt airport, serious."
"Yeah da gaske wallahi ina jiranka ko su Daddy basu san dawowata ba."
"Shegen gari, okay gani yanzu dama kuwa akwai game gobe."
Yayi Maganar yana katse kiran tare da tashi ya zari key ɗinsa ya fita.




***********



Motoci huɗu ne sukayi parking a police station ɗin, da sauri Soja ya fito ya buɗe wata baƙar mota Abba ne ya fito hannunsa riƙe da waya shida commissioner bayansa masu tsaron nasa suka bi har cikin Police station, gaba ki ɗaya ƴan sanda miƙewa tsaye sukayi cikin girmamawa, kujera aka ɗaukowa Abba, zama yayi shima commissioner aka kawo masa kujerar ya zauna.
Commissioner ne yace
"Ku buɗe Nameer."
Cike da bin umarni Sargent Dogo yazo ya buɗe, miƙewa Nameer yayi ya fito tare da nufar Abba Abba yana ganin Nameer ya miƙe suka rungume juna cikin soyayya da kulawa kafin Abba ya zauna Nameer gefen ƙafar Abba ya jawo kujera ya zauna tare da kwantar da kansa a kafaɗar Abba.
"Nameer ka takura da zaman nan ko.?"
"No Abba ban takura ba rayuwa ce ba inda bata kai mutum Abba ina ummina ita kawai nake tunani nasan zata fi kowa damuwa."
"Hmmm! Umminka ta damu ƙwarai Nameer sai dai ɗan uwanka yana kwantar mata da hankali, munyi magana da commissioner gashi nan yace dole ne sai an kaika kotu, zamu nemi lauyer insha Allah zan tsaya domin ganin ka samu adalci."
"Abba bani da damuwa da zuwana kotu har yanzu bana jin koda tsinkewar zuciya saboda nasan ban aikata laifin da ake zargina dashi ba, Abba ina tunanin Hisham yayi fushi dani ko tun shekaran jiya daya zo bai kuma dawowa ba."
"Ka sani Hisham bazai taɓa fushi da kai ba Nameer kasan zuciyar sa bazai iya jure ganinka cikin wannan halin bane sannan ya sanar dani baya son ƙara ganin fuskar Dpo wata ƙila hakan yasa yaƙi zuwa amma yana can yana ƙoƙarin ganin ya kuɓutar da kai."
"Idan ka koma Abba kace masa ina kewarsa."
"Shikenan zan isar masa da sakon."
Commissioner ne ya tambayi Sargent Bala Dpo tare da basa umarnin ya shiga ya sanar dashi sunzo babu ɓata lokaci ya shiga kiran nasa.
Babu jumawa Dpo ya fito cikin girmamawa ya sarawa commissioner tare da gaishe da Abba shima cikin girmamawa kafin ya zauna, commissioner ne yace.
"Dpo ya ake ciki game da case ɗin Nameer me kuka tattara ga binciken da kukayi."?
"Sir har yanzu muna kan bincike bamu kammala ba shiyasa ma bamu kai case ɗin kotu ba tukunna, amma binciken asibitin dai ya nuna cewa an ya kushe ta sosai ma'ana anyi kokawa da ita sannan kayan jikinta duk sun yaga, kuma the Best ma mun samu agogon hannun Nameer a jikinta wanda maybe bai san ya maƙale a jikinta ba domin kuwa doctor sunce a jikinta suka samu sanda aka kawota asibitin wannan agogon dai shine yake tabbatar mana da cewa Nameer shine yayi ƙoƙarin keta mata haddi, sannan ita yarinyar ma ansaceta jiya, sai dai sir Hisham muke zargi da saceta saboda shine kawai zai iya hakan duk da zargi muke, yanzu ma niyyar zuwa wajensa muke sai kukazo."
Commissioner duban Nameer yayi tare da cewa.
"Amma har yanzu 2days a wannan binciken kawai kuka tsaya, Dpo ganin agogon Nameer a jikin ta tabbas hujja ce sai dai fa ku sani za'a iya masa sharri saboda mahaifinsa babban mutum ne kuma yana da maƙiya shiyasa nake son kuyi bincike da kyau, dan haka na baka zuwa yau da gobe ka tabbatar ka gama tabbatar da gaskiyar binciken, maganar Hisham kuma kuna iya zuwa kuyi binciken ku duk da ba lallai ace shi ɗin bane."
"Shikenan Sir insha Allah zanyi yadda kace."
Numfashi Abba ya saki tare da cewa.
"Commissioner ina son idan ta tabbata za'a kai Nameer kotu, to karku sanar da Hisham ranar Shari'ar."
"Meyasa."?
Commissioner yayi tambayar yana kallon Abba.
"Saboda zai iya ɓata komai."
"Shikenan, zamu iya tafiya."
Duban Nameer Abba yayi yace.
"Zan koma Nameer insha Allah komai zaizo cikin sauƙi dan Allah karka ɗaga hankalinka."
"Insha Allah Abba ka cewa Ummi ina gaisheta kuma nayi kewarta, Abba Tutu kace injini tayi haƙuri karta sa damuwa a ranta ta dinga cin abinci."
"Saƙon duk zai isa garesu ka kula Nameer."
Abba yayi Maganar yana tashi suka fita kafin Sargent Dogo ya mayar da Nameer cikin cell, shuru Nameer yayi yana nazarin maganganun su Abba, cikin ransa yace.
(Meyasa Hisham ya iya wadannan kwanakin baizo ya ganni ba, me yake shiryawa tabbas Hisham ne ya ɗauke wannan yarinyar domin ganin ya kuɓutar dani to amma ko ta ina Case ɗina a dabaibaye yake ta yaya Hisham zai iya warwarewa, nasan halinsa sarai zai iya aikata komai domin idan ya yanke hukunci baya jin Muryar kowa, lallai na kuɓuta Dpo bazai shaba a wajen Hisham, nasan yanzu yana can yayi target ɗin Jidda zai kuma iya aikata mata duk abinda ya kudurta a ransa sai dai bazan so hakan ba.)
Ya yi maganar yana sakin numfashi, jingina kansa yayi jikin cell ɗin tare da yin shuru.




**********


"Yau tsawon kwana biyu babu labarin ki ko wayarki na kira baya tafiya."
Gyara zamanta Wamimo tayi tace.
"Naje ƙauye ne kinsan na kira yata dake ƙauyen Agunjin, nace idan taji labarin wani shahararren matsafi wanda yake karya kafi ta min magana, to ranar da mukaje gidan Iyabo da ke bayan na koma gida shine sai ta kirani take cewa wani mai tsafi yazo shi, kuma aikinsa yana yi sosai yana karya kafi, to shine fa naje ƙauyen naso dawowa a ranar to layi yayi yawa a wajen matsafin shiyasa na kwana biyu, babu network ne ma a ƙauyen shiyasa ban kiraki ba."
"Wamimo da gaske kike min wannan Maganar.?"
Mamabisola ta tambayeta cikin zakuwa.
"Ƙwarai kuwa na samu ganawa da matsafin na kuma masa bayanin ki, yace dole sai kinzo da kanki ya duba ya gani idan aikin zai yiwu."
Numfashi Mamabisola ta saki tace.
"Hmmm! To ki shirya jibi muje Wamimo Allah yasa aikin nan ya yiwu ina son ganin bayan Iyabo ina son ganin dukiyar sa ta tarwatse ina son ganin ya rasa komai a rayuwarsa idan hakan bata kasance ba hankalina bazai taɓa kwanciya ba."
"Karki damu Mamabisola wannan aikin sunansa ya yiwu domin kuwa ance wannan matsafin bai taɓa aiki bai yiwu ba, indai yayi aiki to tabbas sai aikin yayi, yanzu bara naje kasuwa anjuma zan dawo."
"Shikenan kije dawon."









_______________________________________



*Share and comments my fan's🥰*







*_UMMU NASMAH CE✍🏻_*





*For more information 08147537180*
[5/17, 7:36 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga

Please Login or Register in order to submit comment